Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jawwad amma bayanan, takira wayarsa harta katse be dauka ba, daki takoma tazubawa Jalila ido data kwanta ta rufe ido, amma hawaye nabin gefen idonta
"Jalila dan Allah kitashi kici Abinci, wallahi gaba daya zuciya ta babu dadi, na damu matuka, dan Allah kici wallahi inbaki ciba nima bazanci ba" A hankali Jalila ta bude ido, ta mike zaune ta kalli Nana tace "zubo muci, banason kizauna da yunwa"
Nana ta zuba Abinci amma Jalila ta dan cakala ta barshi.
Wunin Ranar Haka Jalila tayi duk surutun nan amma yau tsit kakeji, Nana tayi tambayar harta gaji ta samata ido.

Da daddare Jawwad ya shigo yasamu Maama a palour yake gaya mata Ankai Jalal Asibiti. Da sauri Jalila ta mike ta fito palour ta labe
Maama tace "meysameshi haka?"
"kinsam jiya yan maiduguri sunzo, kuma dai kinsam babu jituwa tsakaninsu da Mummy, andai bata masa rai yaje ya kulle kansa a daki, yafasa abubuwa sosai sannan cikinsa da yunwa ya sha wani abun bansan meyasha ba, da kyar na bude dakin dazu, naganshi a sume shine muka kaishi Asibiti, yanzu can zantafi zan kwana dashi"
Maama ta kalleshi "ohhh Jawwad Allah yayemaka wannna Jaraba, wannan yaron Jalal kullum seyajanyo abun daze hanaka hutawa, sekayi tayi ai wahalalle"
Murmushi Jawwad yayi yace "Maama kenan, ai duk dan halak baya manta alkhairi, bari in tafi seda safe" ko kallonsa bata kumayiba, har ya juya ze fita Nana tace "Yaya Jawwad amasa sannu dan Allah, kuma wallahi Baby ma inaga wani abu na damunta tunjiya kuka takeyi, taki cin Abinci da kyar nasata taci kadan"
"Haba dai? Kuma kin tambayeta meyake damunta?"
A fusace Maama tace "fita katafi inda zaka, bazasu hadu sukasheka ba kowa ya kwaso iskancinka akanka ze sauke, kaidabaka san ciwon kanka ba"
Jiki a sanyaye Jawwad ya juaya yafita, Jalila takoma daki ta kwanta tai shiru tamarasa tausayin wa yakamata taji.
Jin batun Jalal na gadon Asibiti abun yadameta.
Har gari yawaye Jalila nata kasa kunne taji wanda zeyi zancen halin da Jalal yake ciki, har wajen azahar shiru, Jalila tace "Nana naji kaman yaya Jawwad yace an kai Abokinsa Asibiti?"
"Eh acanma ya kwana, har yanzu kowaya beyoba, dazu Maama takirashi a waya amma bata shiga"
"to ya jikinnasa?"
"Nima bansaniba wallahi, amma bari mujira zuwa anjima"
Jalila ta gyada kai, ta dakko wayarta tana dubawa taga missed calls rututu
Call logs dinta tashiga tatarar da missed calls na Zahrah, Jalila ta kirata a waya bugu biyu ta dauka
"Salam alaikum, Jalila ina kika shiga tun jiya nake kiran wayarki amma ba kya dagawa"
"Am sorry ina wani mahimmin abune, se yau na dakko wayar, ya akayine?"
"Hmm Jalila sarkin Sabga, dama gayamiki zanyi anbada belin Baban Samir Fa shida duk wanda aka kamasu, shine nace kina ganin ba abunda ze faru kuwa insuka ganomu"
"Zahrah karki damu babu abunda ze faru, koda anganomu muka shirya wannan abun, to ki zame kibanni ba ruwanki balle baza'a gane ba, Burina ya cika na tonawa duniya asirin ya da Uba, duk wani cin zarafi da wulakanci dasu Saleema sukeyi dole sudena, saboda wannan mummunan abu. Kunya dasuka aikata, Amma tabbas zankuma gauraya dasu, Alhaji Kabir da Jeje, Nagode kigaida Umma" Jalila ta kashe wayarta, tacigaba da duba kiran da akayi mata takuma cin karo dana Hanan, da sauri ta kira Hanan, seda takusa tsinkewa sannan Hanan ta dauka, tace "Se yanzu zaki kirnaiko? Tun jiya nake kiranki amma kinki dagawa yar wulakanci kawai"
"Yi hakuri Hanan, lokacin bana tareda wayar se yanzu na duba nagani"
"To na hakura Allah ya temakeki, dama zamuje Bauchi nan da 2 weeks, Daddy yace zamuzo mu tambayi Abba inya yadda mutafi dake Inna taganki"
Jalila tace "Hanan zanyi murna da zuwanki, ina cikin matsala inason inganki"
"Matsala kuma Jalila? Meyafaru?"
"Hanan na dade ina tafka kuskure, yanzu ina nadamar abunda nayi, abun baze yuwu ta waya ba, nafison mu hadu"
"Subhanallah Jalila nadamar mekuma? Zaki banni cikin damuwa da tunani, ki gayamin menene?"
Jalila ta dan share Hawaye tace "Hanan for all this time i have hurting Jalal, calling him with different bad names, he is innocent, Hanan an gayamin tarihinsa, Jalal abun a tausaya masane, inajin kunyar hada ido dashi, Hanan ban kyauta ba"
"Is ok kidena kuka, ai duk dan adam baya wuce aikata kuskure, Calm down, abunda na dinga nunamiki kenan a baya amma baki ganeba, baka yankewa mutum hukunci kai tsaye akan abunda kaga yana aikatawa, idan nazo zamuyi maganar, amma ya akayi kikasan ba laifinsa bane?"
" Ai baze yuwu a waya ba, se mun hadu"
"Amma yakamata ki wanke lefinki"
"Hanan tayaya, tunda na riga nayi"
"Hakuri zaki bashi mana"
"Hakuri kuma?"
"Eh mana, yakamata kinemi ya yafe miki"
"mhmm Inasu Yaya Abdallah? Inason ganinsa ma ina neman yamin wata Alfarma inze iya"
"Wace Alfarma kenan?"
"Ina ruwanki semun hadu nida shi, ki gaida Baba"
"Hmm shikenan zeji Insha Allah" sukayi Sallama
Jalila kasa jurewa tayi ta dau waya takira Jawwad amma baya dauka, haka ta hakura.
Washegari shiru2 Jawwad be dawo ba. Har bayan Azahar gashi baya daga waya, hakan yasa Jalila ta kara shiga damuwa, ta fito harabar gidan, dan tasamu ta kadaice tayi tunani, tana nan Zaune tayi nisa sosai a tunanin tarasa ta ina yakamata ta fara, gaba daya abubuwa sun hargitse mata.
Motsi taji abayanta yasatayi saurin waigawa, Jawwad ta gani a tsaye tai sauri ta mike tsaye.
"Baby meke damunki hakane? Tun dazu nake magana amma kinyi shiru, gayamin meke faruwa?"
Murmushi Jalila ta kakalo, "Yaya Jawwad bakomai kawai dai banji bane, ina ka shiga bana ganinka nakiraka a waye baka dagawa"
"Jalal ne ba lafiya, na kaishi Asibiti na manta wayata a gida"
"Meyasameshi?"
Ajiyar Zuciya Jawwad yayi sannnan yace "jininsa ya hau, yana damun kansa dayawa, Jalal baya iya controlling bacin Ransa, yanada saka abu a ransa, ga kinsan shan taba yana kara saka hawan jini, amma Alhamdilillah jikinsa da sauki an sallameshi tare muka dawo gida" jinjina kai Jalila tayi "Allah yabashi lafiya"
"Ameen Baby, meyasamin ke kuka kika kasa cin Abinci Nana ta gayamin"
"Nikuma ai kaina ke ciwo kawai itakuma tabi ta damu, amma na warke ai"
"Anya kuwa, karya ba halinki bane, fuskarki ta nunamin kina cikin damuwa"
"bana cikin wani damuwa ni, kako ci Abinci naga kaman a gajiye kake"
"Hmm wato ba kyason incigaba da tambayarki ko?"
"bahaka bane, banaso ka zauna da yunwa ne"
Murmushi Jawwad yayi, "Ina jin yunwa kam, samomana wani abun, Jalal ma beci Abinci ba, yaki cin Abinci wallahi, nayi2 amma yaki, Yana cikin damuwa sosai, anyway samo mana abunda yasamu in lallabashi koze ci" gyada kai Jalila tayi ta juya da sauri ta tafi cikin gida.
Tana shiga palour ta tarar da Maama tana mata wani irin mugun kallon banza, Jalila ta dauke kai kaman bata san meke faruwa ba tai kitchen abunta. Ta dafa masa jallof spaghetti, ta hada da juice bayan tagaama take tunani yanda Maama ta zauna a palou tana mata kallon banza, yanzu in tace zata kaimasa Abinci wani bacin ran zata jawa kanta dan haka ta kirashi a waya tace yazo ya dauka, befi minyi bakwai ba sega Jawwad yaje kitchen ya dauki Abincin. Har yazo ze fita Maama takirashi, yadawo ya zauna a gabanta yace "Maama gani, Allah yasa ba laifi nayi miki ba"
"laifi kuma tun yaushe kake sabawa umarnina, minyi magana akan muna son hada Aurenka Naja amma har yanzu baka kumabi takan zancen ba, sekara shigewa wannan algungumar yarinyar kakeyi, ban isa ingayamaka magana kajiba ko?"
"Maama dan Allah kiyi hakuri, na yadda in Auri duk wadda kikeso, amma bazan iya Auren Naja ba"
"Jawwad kake kallon tsabar idona kake cemin bazaka iya Auren Naja ba"
"Maaama Naja yar uwata ce bazankita haka kurum ba amma...
" Yimin shiru badai akan waccan hatsabibiyar kake rawar kaiba, idan ina raye ayi ingani, tashi kabani guri"
Jiki a sanyaye cike da damuwa Jawwad ya mike yabar palourn.

Tunda yan maiduguri suka tafi Jalila bata kara saka Jalal a idonta ba dan sam yadena zuwa gidansu, ga Jawwad yanata complain akan Jalal bayacin Abinci yana damun kansa sosai, ga matsalar da Jawwad yake ciki shima Maama nata tursasa shi tace se ya Auri Naja, amma ita Nana ta tirje tace bazata Auri faruk ba an kyaleta, Jalila tarasa yadda zatayi taga Jalal, duk abun yafara damunta. Ga yaya Jawwad dinma ta dena ganinsa ko waya basa yi, yadena shigowa cikin gida. Zaman cikin gida ya isheta dan haka ta fito danta sha iska, ta fito ba dadewa Jawwad ya shigo yayi parking, duk taga ya dan rame, yafito ya kulle motar, takarasa inda yake "Yaya Jawwad wai meyake damunka hakane, ka rame kuma tun shekaranjiya ban kuma ganinka ba" cike da damuwa yace mata "Baby Jalal, yana nema ya kashe kansa"
"Kamar yaya?"
"Ankuma kwantar dashi a Asibiti, tun shekaranjiya ina can, banason inkira Daddy kar adaga masa hankali, idan Mummy taje gurinsa, seyace seta tafi bayason ganinta yanzu haka jikinsa yakuma rikicewa, yanzu haka tun jiya yana ICU, maybe yau zasu fito dashi" nan da nan jikinta ya hau rawa, cikin rawar murya tace
"Subhanallah Allah yabashi lafiya, if you don't mind zan rakaka in dubashi"
"Shikenan naji amma kibari seda safe in Allah ya kaimu zanzo muje" ta jinjina masa kai takoma cikin gida

Yau Hannah har gidan Jeje taje nemansa tayi sa'a kuwa yana nan, Jeje yayi mamakin ganinta sosai "yau kece da kanki a gidana"
"Eh nice amma kasan duk lokacin daka ganni bukatace ta kawoni, almost one week ina nemanka, bana ganinka layinka baya shiga, amma naji ana rumors ankamaka kai da megidanka a gidan karuwai meye gaskiyar lamari" shiru Jeje ya danyi ya kalli Hanna
"Ni ina zargin dasa Hannunki akan abunda yafaru dani, shekara da shekaru inawa Oga Kb aiki inasamun rufin Asiri a gurinsa, ina hutawa da 'yarsa ba tareda yasani ba lokaci daya aka masa cunen gidan danake zuwa yakamamu, yanzu ya sallameni tareda cin alwashin seyaga bayana, wallahi Hannah indai dasa hannunki a wanna cin zarafin da' akamin bazaki tsira daga sharri na ba"
Murmushi Hanna tayi sannan tace "Aidama karshen alwa kasa, kuma ramin mugunta kurarrene, Jeje idan har zanmaka wannan manakisar yan sanda suka maka kaida uban gidanka to wallahi da duk yadda zanyi bazaka fita daga hannun yan sanda ba daga kai harshi, dara ce taci gida kawai, kakoma kayi tunani ka sake nazari waze iya aikata maka haka, kasan innice nayi maka wannan aikin bazanji tsoron gayamaka bako? tunda irin tarbar danasamu daga gurinka kenan shikenan nagode ni na tafi, amma kakiyaye shiga hanyata, kasanni ban da kyau"
tanagama fadin haka ta juya tanufi motarta, yayi Yunkurin ya biyota amma ta tashi motar tabar gurin.
Yauma Jalila ba bacci, saboda tashin hankali da damuwa, se addu'a da takeyi, Nana kam ta gaji da tambayar ta meyake damunta. Da Asuba Jalila tai wanka tai salla ta shiga kitchen ta dama kunun gyda da dankalin turawa, karfe bakwai tagama shiryawa tsaf tana jiran Jawwad, Nana tai juyi akan gado ta kalli Jalila
"wai shirin mekikeyi hakane?"
"Asibiti zan raka Yaya Jawwad muduba Yaya Jalal" dan zaro ido Nana tayi, sannan tai murmushi
"Yaukuma da kanki kike cewa Yaya Jalal" takuma murmushi tace "Zanso inje nima induba shi, amma wallahi bacci nakeji, kuyi masa sannu in an sallamoshi naje in duba shi, kokuma in Maama zata semuje tare" Nana ta juya tashige bargo, Jalila na nan zaune, wajejen karfe takwas Jawwad yakirata a waya yace tafito su tafi, da sauri ta dakko kwandon kayan Abincin ta fito, Jawwad ya kalleta yace "Baby hada hidima haka, Abinci kika mana"
"Eh Yaya, koba kwaso?"
"haba mu mun isa, taho mutafi" ta shiga mota suka tafi, suna zuwa Jawwad yaimata jagora har dakin da Jalal yake, suka tura kofa suka shiga ta tsorata da ganin Jalal, yana kwance akan gado dagashi se dogon wando da singlet, yanata sauke numfashi a hankali, ya rame matuka gashi yayi duhu se dogon hancinsa yakara fitowa sosai, drip yana shiga jikinsa a hankali, hawaye yafara bin idon Jalila a ranta tace "idan har Jalal ya mutu ina da alhaki, ninakara assasa bata masa rai"
Jawwad ya dora hannunsa akan gadon da Jalal yake ya sunkuyar da kai, Yana dago ido Jalila taga kwalla a kwance a idonsa
"Yaya karka karaya mana, zeji sauki" Jawwad yai murmushi yace "Baby Jalal wani bangarene na rayuwata, inajinsa a raina kaman wani bangare na rayuwata, banason rasashi, banason wani abu yasameshi da inada yadda zanyi in kawar masa da damuwarsa, danayi amma ba yadda na iya kaddara tariga fata, haka Allah ya kaddara masa, ina fatan Allah ya musanya masa da kyakyawar kaddara " Jawwad yai ajiyar zuciya yace "Bari inje gurin doctor inji meze ce, kizauna anan anjima su Ilham zasuzo nima yanzu zan dawo, inkuma ya tashi kafin in dawo kikirani beci Abinci ba" ta jinjina kai, Jawwad yafita yabar dakin guri ta samu ta zauna akan kujerar gaban gadon Jalal, Hawaye tacigaba da sharewa lokaci zuwa lokaci tana dorawa kanta alhakin wannan rashin lafiyar da yake,
A hankali Jalal yai juyi, da sauri ta goge idonta ta tsaya tana kallonsa bude idonsa yayi a hankali ya saukesu akan Jalila dake goge hawaye, kura mata ido yayi ko kyaftawa ba yayi.





Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣5️⃣78

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]





_MY FIRST NOVEL_


Ya dau lokaci yana kallon ta, cikin rawar murya Jalila tace "Sannu ya jiki?" shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa, "Ko inkira maka Jawwad" still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi "Inkira maka likitane" takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta "Kukan mekikeyi? Nakumamiki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?"
Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace "kidenamin kuka, nagaya miki kincikamin kunne"
"Yi hakuri na dena" tasa hannu ta share hawayenta, Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace "Sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni" murmushi likitan yayi sannan yace "kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma dawo da kai Rai a hannun Allah"
Jawwad yace "rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza'a sallameshi ba seya warke gaba daya"
Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace "Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi" Sannan likitan ya kalli Jalal yace "Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni"'imar ubangiji meze daga maka hankali haka? " kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa " Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo'in ciwon ido dake sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic " shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace "Shikenan doctor za'a kiyaye Insha Allah"
"Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki" doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace "Kaji abunda doctor yace ko? Please and please kakiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa" Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace "Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin"
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace "Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba"
Jalila tace "Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye" takarasa maganar tana dan tura baki, Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace "itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin" Jawwad ya mike ya fita, Jawwad na fita Jalal yai kokarin komawa ya kwanta beci Abincin ba da sauri Jalila tace "Ai bakaci Abincin ba" ya kalleta "Bazanci ba" yakuma kokarin kwanciya Abincin ta dauka ta dora a inda ze kwanta tace "wai meyasa kafiye taurin kaine? Cewa fa akayi kaci Abinci"
"Ke har na kaiki taurin kaine? Waima ina ruwanki danine? Dan giya, mara tarbiyya, zan lalata miki dan uwa, me kike nema a gurina, dauke Abincin ki bazan ciba, kintaba gayamin idan na mutu bakida Asara to meye naki na damuwa da banci Abinci ba?" yasa hannu ya dauke Abincin ya dora akan drower na kusa da gadon sannan yace "Dama a duniya daga daddy se Jawwad ne suke sona se yan uwan daddy, nan duniya idan na mutu ba wanda yakeda Asara, sesu"
kura masa ido tayi "Meye kuma kike kwalalamin idanuwa haka, kidena kallona" yai kwanciyar sa.
Kawai Jalila ta mike ta fice daga dakin, Ajiyar zuciya Jalal yayi dayaga ta fita ya dakko Abincin data zuba ya ci ya aje sauran. Jalila na fita tasamu guri ta zauna a waje ta dakko wayarta tafara chatting tana daga kai ta hango Ilham da mahaifiyarta a harabar Asibitin kallo daya tayiwa Saudat tagane itace mahaifiyar Ilham,
da sauri Jalila ta tashi ta koma dakin Jalal, tana zuwa taga yaci Abincin yana kashingide ya lumshe ido, yana jin motsinta ya bude ido,
"Ke meya dawo dake, ko dama bakida zuciya?" cikin tsiwa tace
"dama ina naga zuciya, tunda kaima bakada ita"
Dan zare ido yayi, ashe halin nata yana nan
Ta fara hada kan kwanuka, Ilham ce da Mamanta suka shigo da sallama yanajin muryarsu yai Sauri ya rufe idonsa. Kai kace bacci yake, Tunda Ilham taga Jalila a gurin Jalal ta hade rai kaman taga kashi
Jalila ta maze tace "Sannunku da zuwa" yawwa maman Ilham ta amsamata, tabasu guri suka zauna Ilham se harar Jalila take, ita kam Jalila data kalli Ilham seta mata murmushi Maman Ilham tace "Yame jiki?"
"da sauki Mama"
"naga alamar kaman yana bacci ne ko?"
Jalila ta waiga ta kalleshi yawani rufe ido kaman gaske amma idonsa biyu, se Jalila ta kudurce wani abu a ranta dan haka Jalila tace "
eh likita yamasa Allurai yasamu bacci, likita yace baze farka ba se bayan Awa biyar, yanzu besan me ake ba"
Maman Ilham ta kalli Jalila tace
" Sedai bangane wannan ba, bakowa a gurinsa seke? ko itama a dangin babanasa take?"
Ilham tai farat tace "Inafa," yar shishshigi yar wahala dai, me hana ruwa gudu, me cusa kanta inda Allah be kaita ba" Jalila tace "haba Ilham, wani ma se yazata banida kirki, menamiki haka ina laifin kice, Sauro me hana giwa bacci, Raina kama kaga Gayya" Jalila ta karasa maganar tana murmushi tace "Mama bari in saka wayata a caji, in karbo muku ruwa a waje" Jalila ta mike ta dau wayarta ta dan daddana sannan tasaka ta a caji ta fita. Ba'a wani dade ba, Jalila ta turo kofa ta shigo da ruwan roba ta ajiye musu ko sha basuyi ba suka tashi sukace tafiya zasuyi. Tai musu sallama suka mata banza Ilham nata gaya mata bakaken maganganu bata damu ba suna fita taje ta dauki wayarta ta bude, maganganun dasukayi tsaf tayi recording dinsa tai Saving tajuya ta hada kan kwanukan da Jalal yaci Abinci, bude idonsa yayi yana kallon ta tana dagowa suka hada ido
"Akwai matsala ne?" Jalila ta tambayeshi
"Wani Apple kika hanani ci kika musanya ranar da mukayi baki?" tambayar tazo mata a bazata, ta dan tabe baki sannan tace "Apple kuma ni ban san zancen ba"
"Karya kikeyi" Hade rai tayi sosai
"Eh kasan na saba" tacigaba da abunda take, ko ina yasan wannam maganar oho masa, ta mike tsaye taji ya janyo ta da karfi kan gadon, take jikinta ya hau rawa ta tsorata sosai ta ware ido tana kallon sa
"Ina tambayar ki kina rainamin hankali wani Apple kika hanani ci, kuma meyasa?"
"ni nace maka ban san zancen ba, ka tambayi wanda suka gayamaka mana, ni kacikani" kara karfin rikon yayi taji kaman ze karya ta, sannan yace "ke bana son karya, for the last time ki gayamin" kawai ta fashe da kuka, mamakine yakama shi, in wani ya shigo se a zata wani abun yayi mata, dan haka a hankali ya sake ta ta mike da sauri ta koma waje, tana fita ta dakko wayarta kunna maganganun Ilham da mamanta. Kawai taji maganar Ilham tana cewa
"Umma wannan itace munafukar da nake gayamiki duk lokacin danayi wani yunkuri zanyi wani aiki akansa itake lalatawa, na dade da gane take takenta sonshi take, amma taki yadda tana rainamin hankali, tasamun Ido ta hanani sakewa, duk lokacin danayi Yunkurin wani abu idonta na kaina, seta wargaza gashi ta hadani dawata tsinanniyar karuwa wai budurwar Jalal ce, hatsabibancin yarinyar nan ya wuce tunaninki, harda wani alwashin indai tana Raye seta rusa shirina akan Jalal" mamanta tace
"Ke sokuwar inace? Kika kasa gayamin tuntuni mu dau mataki akan shegiya"
"Umm har gurin Malam na kaita amma yace baze iya komai akanta ba, dakike ganinta ita ta musanya Apple din dana sawa maganin ranar, makira tsinanniya" umma ta girgigiza kai tace
"Tab aikuwa da sake, dole muyi wani abu karta bata mana aikinmu, amma Khadija kuwa tazo taga halin dayake ciki?" Ilham tace "Ai ingayamiki baya son ganin ta, kinga abunda ya dinga yi kuwa sekace ya haukace, dakinsa na nan kaman kantin mahaukaciya ya fasa komai a dakin, sangartacce ubansa na dawowa za'a canza masa komai" suka cigaba da maganganun su a zatonsu duk Jalal bacci yake besan mesuke ba, ita kuwa Jalila tana sane tayi haka.
Shiru Jalila tayi tana tunani "Kenan Jalal yaji duk maganganun da sukayi shine yake tambayata? Kafin kuga bayana zanga naku"
Jawwad ta hango ya taho da leda a hannunsa, yana zuwa inda take yace "Am sorry na tafi nabarki ko? Na dade bansamu maganin bane, bari inzo in maida kw gida nasan kin gaji"
"To Yaya sannu da zuwa"
"Yawwa babyn Yaya" yai mata murmushi ya wuce, yakai minti goma sha biyar sannan ya fito ya dauki Jalila suka tafi gida. Suna zuwa gida gaban Jawwad yafara faduwa, sakamakon tarar da Maama a harabar gidan da sukayi a tsaye da alamu a zuciye take, Jalila ta fito daga mota, Maama ta

Please Login or Register in order to submit comment