Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin suke tattaunawa shida wanda ya kira shin, dukda zuciyarta a kule take da haushi, Amma bayan ya gama wayar tace
"Ya Aikin kuwa?"
Kamar jira yake tayi magana yace

"ban sani ba, bakida kunya, saboda ke na tafi aikin nan for almost four months baki nemeni ba, Rayuwa ta kaman wanda yake cikin rijiya ne yake neman taimako, kin mikomin abu ina kokarin fitowa kin saki nakoma ruwa, dan kinga ina lallabaki kikemin wulakanci ko? "

" ni wani wulakancin nayi maka? Mekake so in maka kuma? In cigaba da bibiyar ka mahaifiyarka tana min kallon mazinaciya? Da kazo garin nan kana kallona shekaran jiya, har kusa faduwa nayi saboda dalilinka, ko kallona bakayi ba, so kake inta binka, kokuma goyaka zanyi? Ni kawai ana can ana Ta shagali nikuma ka dakko ni, duk gurin nan nika dai na tsole maka ido, ga Ahmad ma yama jirana, yanzu se yayi ta jirana, idan ya tarar bana nan bazeji dadi ba"

ya lura gaba daya a fusace take, yai mata shiru taita mita, yadda Jalila ke kuma fadar Ahmad yafi komai bata masa rai, dan haka yaja wani uban birki a kan titi da seda ta firgita, ya juyo yana kallon ta, ya matso da fuskarsa daf da tata, har suna jin numfashin juna, Jalila najin saukar numfashinsa a fuskarta, gaba daya Jikin Jalila ya hau rawa, taji numfashinta na kokarin tsayawa, gaba daya kamshin turarensa ya cika mata hanci, ga kuma wani mugun kwarjini da yayi mata, cigaba da matso da fuskarsa yake daidai tata, har dogon hancinsa na shirin taba nata, rintse ido tayi sosai jikinta na cigaba da rawa.
A hankali ya dauke fuskarsa, yace mata

"stop shivering, kina tunanin wani abun zan miki? Ba abunda zan miki, sedai ina kokarin nuna miki illar shigar da kikayi ne, look at yourself,"
Jin abunda ya fada, Yasa A hankali ta bude idonta tana cigaba da sauke numfashi.
Ya kuma kallon ta yace

"kalli jikinki babu mayafi, kin hau stage kina Rawa, kowa ya zubo miki ido kina rawa, kalli jikinki, kalli yadda kayan nan suka matse ki, hakan ya dace? "
Kallon kanta tayi, taga yadda rigar ta zauna a jikinta, taga irin yadda Jalal yasata a gaba da kallo, gaba daya seta ji kunya ta kamata, Amma ta maze ta dake, takuma hade rai tareda dauke kanta tace
"Ai dai bahaka na keyi ba, dan dai yau daya, ana biki zaka wani takuramin, naga kai da gajeren wando kake yawo a layi, waye ya dameka?"
Jalala seyayi kamar besan dashi take ba, ya fuskanci rigima takeji, idan ya biye mata fada za suyi a titi, banzan da yayi da ita, hakan ba karamin batawa Jalila rai yayi ba, wayarta ta fara ringing, tasa hannu ta ciro wayar daga jakarta, ta daga wayar tasa a kunnenta, beji me aka ce ba, sedai Jalila cikin shagwaba tace

"please my, na dan fitane yanzun zan dawo Insha Allah, ka jirani semu tafi tare"

Cigaba da wayarta tayi hankali kwance, ta gama tana kokarin ajiye wayar, Jalal yasa hannu ya fizge wayar daga hannunta yace

"Wallahi bazaki koma gurin nan ba"
"Saboda me? Ni gaskiya ka maida ni, wai meye haka?"
"Wallahi kika kuma yi min gaddama, Kano zamu nufa a daren nan, daga nan zuwa a Asuba ma isa kanon, babu abunda yayi min zafi da wani zargi ko wani abu daza'a ce akan hakan, kinsan ni bana gudun magana"

A firgice ta kalleshi, babu alamun wasa a idonsa, he mean what he said, yadda fuskarsa take murtuk din nan, ta tabattar ze aikata abunda yace dan haka taja bakinta tayi tsit, tana kallon wayarta tanata ringing, Amma Jalal ya share, ga shi tana tsoron abunda ya fada, dan ze aikata.

Tanaji tana gani ya maida ita gida, yayinda ana can ana rakashewa, gaskiya Jalal ya kwafsa mata, suna zuwa harabar gidan taga motar daddy, da sauri tace "laa motar daddy yazo"
Nan ma shiru Jalal yayi mata, yana parking ta bude motar ta fice, cikin Sauri ta nufi wata kofa, da ya kasance bangarene da Daddyn Hanan yake saukar manyan baki idan suzo, kamar yadda aka nuna mata.
Tana zuwa ta bude kofar ta shiga da sallama, Daddyn Jalal ne, da Daddyn Hanan sekuma Abba, da wani babban mutum wanda Hanan tace mata baban Yaya Yusuf ne, suka amsa mata cikin sakin fuska.
Tana zuwa ta zauna a gefen Abba, ta kalli daddyn Jalal tace "Daddy sannu da zuwa ya hanya?"
"lafiya kalau Jalila ya taro?"
"lafiya kalau Daddy"
"to Masha Allah, Allah yasanya Alkhairi, Allah ya kaimu naki da rai da lafiya"
Suka amsa da Ameen amma banda Jalila da ta sunkuyar da kai.
Daddyn Hanan yace " 'yar baba, keko ganinki bana yi tunda aka fara bikin nan, ina kika shiga haka?"
"Baba ayyuka ne dayawa, kuma naga baka dawowa se dare"
"Hakane kam, sannun da aiki, Allah ya kaimu naki auren ' yar Baba"
Abba yace
"Baby ya akayi kika dawo ke? Naji ance kuna gurin walima, ina Kika baro Amaren?"
"Suna can ba' a tashi ba, ba Yaya Jalal ne... Bata karasa ba Jalal ya turo kofar dakin ya shigo da sallama"

Shikan sa daddyn sa rabon da ya ganshi wata hudun kenan, ya sha manyan kaya yayi kyau, babban abunda ya daurewa daddyn sa kai be wuce yadda yayi sallama ba kuma ya risina yana gaishesu, suka amsa
Daddyn Hanan yace "ABDUL JALAL ashe kazo, Amma ban ganka ba, bamu hadu ba sam"
Jalal yayi murmushi yace "banfiye fitowa ba shiyasa baka ganni ba"
"Masha Allah, Yaya gurin Aikin na ka?
" Lafiya kalau, ina jin dadin Aikin, Amma nafison zama na a kano, gashi sunce sena kara watanni, bana son zaman lagos din nan"

Daddyn Hanan yace "Nayi farinciki ganinka ABDUL, kayi kalau da kai, me yasa baka son zaman lagos din?"
Daddyn sa yayi murmushi yace "baya son sabga da Mata, kasan kuma lagos babu ruwansu da Addini ko Al'ada, in munyi waya yana gayamin ;shi baya son Abunda matan kabilun nan sukeyi" suka kwashe da dariya, Abba yace "Karka damu Kaji Jalal, kana da gaskiya"
Daddyn Hanan ya kalli baban Yusuf yace

"Kaga yaron dana ce ka samarwa Aiki, Ansamu improvement kwarai a tattare da shi, gaskiya 'yar Baba tana da kai sosai, ita tayi wannan tunanin a samo masa aiki, tace min in aka samo masa aikinyi hakan ze dauke masa hankali da ga barna da yake kuma ya rage masa damuwa da kadaici, a haka gata kaman bata iya komai ba se shagwaba da tsokana amma tafi Hanan kai"

Baban Yusuf yace "ABDUL JALAL karka damu kaji, haka sha' anin Aiki yake, ba inda baya kai mutum, kai dai kayi gaskiya ka rike Addininka kuma kaji tsoron Allah"
Sukace hakane, daddyn Hanan yace

"Karka damu Jalal, za'a san abunyi, babban farincikin danayi, daga can lagos din sun kirani suna yaba maka, naji dadi sosai wallahi, Abunda yake kara shashi shaye2 da wannan phobia din na rashin son mutane, hadda psychological issues, yana bukatar me jansa a jiki, be kamata saboda halin da yake ciki na shaye2 ayi watsi da shi da lamarin sa ba, kokuma a dinga yi masa mummunan furuci ba, ko mutane su kyamace shi gaba daya ba, kuma wannan yana daya daga cikin matsalar society dinmu, wallahi wanima ko masallaci yaje baza'a hada sahun salla da shi ba, daga haka suke fara janye jikinsu daga mutanen kirki, se na banza su janye su, maimakon a jasu a jiki da nasiha da rarrashi"

Daddyn Jalal ya dan girgiza kai yace

"Wallahi you said it all sir, Jalal gaba daya gudun mutane yake se tsirari, musamman mata, saboda yarasa wani babban jigo a rayuwarsa da duk wanda yarasa dole yayi kuka, shiyasa da Wannan 'yar tawa Jalila da Jawwad banida abunda zan biya su da shi, ko iya haka aka tsaya sun kawo gagarumin sauyi ga rayuwar ďana, bani da bakin godiya, ban taba tsammanin za' a samu sauyi kwatankwacin haka akansa ba"

ya karasa maganar yana kokarin hadiye kwalla da ta taru a idonsa, gaba daya sukayi tsit cike da tausayin Jalal da mahifinsa, Jalal ya sunkuyar da kai, yana tuna Abubuwan da suka shude na rayuwarsa, Ya fuskanci kaddara daban2, gaba daya tausayin kansa dana daddy ya lullube shi.

Jalila kam cikin sanyi jiki, tace
"Haba Daddy, ni me nayiwa rayuwarsa dana cancanci wannan godiyar da kuke tayimin, wallahi banga abunda nayi masa dana cancanci hakaba, ni yakamata in baku hakurin cin zarafin sa dana dingayi a gabanku, nake kiransa da kalamai marasa dadi Amma....
Sekuma maganar ta kasa fitowa saboda kuka, dan Haka ta mike, da sauri tabar dakin.
Shikam baban Yusuf mamaki ne ya cika shi, ace kamar wannan yarinyar ta sauya akalar Rayuwar matashi da ya riga ya dilmiya a gurbatacciyar rayuwa, itakuwa wace irin baiwa ce da ita, ko dayake ance mata 'yan baiwa ne, sedai kowacce akwai sigar da take Amfani da tata.
Jalal yace "daddy seda safenku, zanje in kwanta"
Abba yayi karfin halin cewa "to shikenan Allah ya tashemu lafiya"
Ya amsa da "Ameen" ya mike ya fito kaman wanda kwai ya fashewa a ciki.

Jalila takoma part dinsu ta canza kaya, tayi wanka, har tayi ta fito tausayin Jalal da daddy ne fal a ranta, se goge Hawaye take lokaci zuwa lokaci.
su Hanan suka dawo, suna zuwa suka tarar har tayi bacci.
Nana tasa hannu tasheta, Jalila ta mike zaune tana kallonsu tace "meye kuma na tashi na?"
Nana tace
"ya akayi kika taho ne? Tun a can Maama take nemanki, Ahmad se kiranki yake a waya baki daga ba"
Se yanzu ta tuna wayar tana gurin Jalal.
"Su Abba ne sukazo shiyasa na dawo gida" ta basu amsa
Hanan tace "keda wa kuka dawo, dan nasan baki san hanya ba"

"ban sani ba, uwar kwakwakwafi a isak na dawo"
Hanan tace "daga tambaya? Allah yabaki hakuri"
Siyama tace "Jalila wallahi Jalal ya hadu, kinata masa wulakanci, wani kallo da yake miki kamar ze cinye ki"

Sukasa Jalila a gaba da tsokana tayi musu banza ta kyalesu.


Jalal yana zaune yana ta tunanin abubuwan da suka faru dashi a baya, shi kansa yana sarawa namijin kokarin Jalila, ta iya lissafi gata da himma da kokari, duk rashin kunyarta da taurin kai, akwai kawaici da tausayi, duk zamansa da Jeje besan Cutar shi yake ba, Amma ita a ranar da suka fara haduwa ta gane hakan, ta saka rayuwarta a hatsari da dama saboda shi, besan mezeyi ya saka mata ba" kallon wayarta data ke faman ringing yayi, sunan My yana yawo akan screen din wayar, har wayar ta gaji ta katse, hotonta ne akan screen lock dinta tana murmushi, ya kurawa hoton idon na dan lokaci, ya sa hannu ya shara screen din, wayar ta babu key a kai, wallpaper dinma hotonta ne da Nana, kanta babu dan kwali, ta dan turo baki Nana kuma tana dariya, ya dade yana kallon wallpaper, yayinda kiran Ahmad ya shigo ba'a dadi, ya gaji sa wayar a silent ya ajiyeta ya cigaba da tunani,
Yana cikin tunanin ne, Angwaye suka dawo.
Jawwad beyi mamakin ganin Jalal a gida ba, dan ba karamin aikinsa ne gurin dinner din ma yaki zuwa gaba daya ba.
Gaba daya Ahmad ransa a bace yake yana ta tunanin ina Jalila ta shiga haka? Ya kira har ya gaji amma bata dagawa, kuma ya duba hall din nan be ganta ba, sukayo wa Angwaye rakiya yana shirin fita daga dakin yace
"Jawwad zan tafi seda safe, Dan Allah ko Jalila ta dawo ne ? Nakirata har nagaji bata dagawa"
Jawwad yace
"Aini tunda ta sauka akan stage din nan ban kuma ganinta ba, Amma ka kira wayarta mana"
"Aina kira wayarta ta bata dagawa"
Jawwad yace
"Idan ma ta dawo yanzu nasan tayi bacci, Amma bari in kira wayar ta ta"
Jalal yana jinsu amma be tanka musu ba, Jawwad na kiran wayar Jalila yaji ringing dinta a dakin, da yake yasan tone din wayarta, Jawwad ya kalli inda ringing din wayar ke tashi, tana kan teburin dake gaban Jalal tareda wayoyinsa,
Jawwad ya tafi gaban tebur din, yaga tabbas wayar Jalila ce, Jawwad ya kai hannu ze dau wayar, yace "ya akayi kuma wayarta tazo nan?"
Jalal ya sa hannu ya dauke wayar ya kashe wayar gaba daya yace
"wayar tana gurina, tare muka taho"
A fusace Ahmad yace

"Amma dan wulakanci kanaji ana maganar kayi banza? Meyasa zaka dakko ta? Na lura tunda kazo kake wani jin kai da nunawa mutane gadara, ubanwa kafi? Zaka dinga nunawa mutane jin kai, meye naka na shiga sabgarta? Waye dinta kai? Dama ana fadin kana shaye2 wallahi kamin hauka kurata zansa sumaka duka"
Jawwad da sauri yace

"yi hakuri Ahmad, baka fahimci Jalal bane, shima yayanta ne yana da iko akanta, Bekamata ka dinga wannan maganganun ba, an riga an zama daya"
Zuciyar Jalal wata irin tafasa take, ba dan Dalilin Jawwad ba wannan banzan ya isa ya tsaya gabansa yana zaginsa, dan takamarsa yanada kaki, idan takamar Ahmad kakin soja, shikuma yana da abunda ze siye shi da kakin nasa yasa Aljihunsa
Kawai Jalal ya jingina da kujera ya zaro karan sigarinsa ya kunna yana kada kafa.
Karshen kuluwa Ahmad yayi, wai uban me Jalal ya taka yake wannan gadarar.
Abdallah ne ya shigo dakin da sauri yana fadin "Jawwad ana nemanku a part din daddy, kaida Ahmad"
Jawwad yace "Allah yasa ba wani abun mukayi ba?"
"ba abunda kukayi ance dai in kiraku"
Jawwad yace "Amma a daren nan haka?
" kuzo dai muje, ko menene kwaji a can"
Seda Ahmad yayiwa Jalal wani banzan kallo, yayinda shikuma Jalal yakara yawan hayakin da yake fesarwa a iska, yana lumshe ido Ahmad ji yake da da bindiga se ya harbe Jalal, haka suka fita suka tafi.

Su Jalila kam, babu alamar zasu kwanta yanzu, hira kawai suke suna shewa, Maama ta shigo dakin tace "har yanzu baku kwanta ba?"
Hanan tace
"Wallahi Maama, mun kasa baccin ne, shiyasa muke ta hira"
Maama tace
"lallai kam, ke Nana magana fa ta canza, da mun zata nan da sati biyu zaki tafi, Hajiya Salma tace; dake zasu tafi maiduguri, visar ki ta samu, in aka daura Aure gobe in Allah ya kaimu ranar Asabar zaku tafi maiduguri, litinin zaku tafi can England keda Mahmud, dan haka za'a kawo miki kayanki da zaki tafi dasu, bayan kun tafi"
Take jikin Nana ya hau rawa, cikin rawar murya tace
"Maama litinin fa, yayi kusa da yawa"
Jalila tace "dan Allah Maama a barmin ita se nan da sati daya"
Gaba daya suka fashe da kuka daga Nana har Jalila, Maama taga bazata iya zaman rarrashi ba ta tafi ta kyalesu, Ai Jalila har tafi Nana shiga damuwa, Hanan da Anty fiddo ba yadda basuyi ba amma suka ki yin shiru musamman Jalila, kwana tayi tana kuka, bata taba tunanin zataji haka ba in Nana ta tashi Aure,
Kamar wasa har wayewar gari ranar daurin Aure kuka take, hakan ya saukar mata da ciwon kai da zazzabi me zafi.
Hajiya Salma ta samu labarin halin da Jalila ke ciki, tazo ta dinga rarrashin Jalila, aka nemo likita yabata magunguna, aka samu tayi wanka.
Daddyn Hanan yace akai Jalila bangaren sa ta samu ta huta saboda hayaniya.
Haka kuwa akayi, wunin ranar bata fito ba daga bacci se salla, ta sha kuka shikenan Yaya Jawwad ya tafi da Hanan lagos, Nana ta tafi England, shikenan se ita kadai.
Har aka gama wunin ranar tana kwance saboda zazzabi ga ciwon kai, ita kanta Nana wunin ranar da kuka ta yi shi, se bayan magariba, Mummyn Hanan ta shigo dakin da Jalila take dauke da Akwatin Jalila tace "Jalila maza tashi ki wanke fuskarki, ki sa hijjabinki ki biyoni ana san ganinki"
Jalila tace "Nikuma? Amma me za'ayi da trolley dina anan"
"in munje zakiji, tashi maza" jiki a sanyaye ta mike ta saka hijjabi, har yanzu kanta ciwo yake, dukda zazzabin ya sauka.
Tabi bayan Maama har wani katafaren parlour da yake wani bangare na gidan, suna shiga taga Angwayen nan gaba daya da Amare, sekuma iyayensu maza. Jalal na gefen Jawwad a zaune.
Ta samu guri kusa da Mummyn Hanan ta kwanta a jikin Maama saboda dikinta ba kwari. Sukai tai mata sannu.
Da alamu an dade ana tattaunawa ita kadai ake jira, Maama ta rage murya ta radawa Jalila Daddyn Jalal ya gabatar da kyautar da Mummy ta bayar abawa Jawwad, kyautar gida a Kano, sannan ita ta bayar da sadakin da'aka biyawa Jawwad naira dubu dari.
Jalila tayi mamakin hakan kwarai
Kowacce aka mika mata sadakinta a hannunta, akayi musu nasiha da fada sosai tareda Addu'oi, aka sallami su Hanan, da Nana, Siyama bayan daurin Aure suka koma Kaduna, daddy yace Jalila ta tsaya, Jalal ma yana zaune a gurin.
Abba ya mikowa Jalila bandir din kudi, Mummyn Hanan ta mika mata, ta sa hannu ta karba cike da mamaki
"Abba wannan na menene?" ta tambayeshi tana juya kudin
"Sadakin ki ne" a tsorace ta zare ido ta kalli kudin
"Sadakina kuma? Waye mijin?" ta fada a firgice
Daddyn Hanan yace
"kwantar da hankalinki gashi nan a gefenki ABDUL JALAL ne ba wani ba!!!!
Ai a zabure ta zubar da kudin ta ja da baya tana kallon Jalal da ya sunkuyar da kai tana zazzare ido.





In ba'ayi Comments yadda nake so ba, in na tafi se bayan sati zanyi posting
Ina son jin comments dinku, predictions, and your opinions thank you 😍 😍 😍 😍 😍 😍 😍 😍 😍 😍

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣9️⃣102

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724




_MY FIRST NOVEL _



Jalal ya dago yana kallon Jalila, cikin kuka Jalila tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Abba me yasa? Laifin me nayi a kayimin haka?"
Abba yace
"kwantar da hankalinki, nasan bazaki watsa min kasa a ido ba, ba laifin da kikayi, ganin da cewar hakan mukayi shiyasa muka yanke wannan hukuncin"
Girgiza kai ta shiga yi tana kuka, daddyn Hanan yace

"Calm down my daughter, kinga bakida lafiya, meye abun damuwa? Jalal ne kin sanshi ba wani aka Aura miki wanda baki sani ba, bakomai kiyi hakuri, Allah yabaku zaman lafiya, Kuma nasan kina sonshi ai ko?"
Girgiza kai tayi da sauri tace

"Ni wallahi bana sonshi, Allah bana sonshi haba daddy, duk 'yan uwana ba wanda akayiwa haka seni, daddy Why? Wallahi ni ba son Jalal nake ba tausayin sa kawai nakeji"
Abba yace

"ba cinya ba kafar baya"
Daddy yace
"to wa kike so"?

"Ni Ahmad nakeso" ta fada kanta tsaye tana kuka.
Jalal yasan za' a rina, yasan setayi daru, Amma be taba zaton Jalila zata iya furta bata sonsa ba agabansa haka"
Mummy tace

"Ke rufewa mutane baki, kaunar da'ake miki yasa aka zaba miki Jalal din, in kun zauna zakiji son, kar in kara jin wannan maganar a bakinki, Ahmad yana da mata, ko yanzu yaga dama ze iya neman wadda yakeso a bashi, kamar yadda kikace tausayin Jalal kike, to kiyi hakuri kicigaba da tausayin sa"

Maama kanta jikinta yayi sanyi, seda ta bada shawarar a ji ta bakin Jalila kafin a yanke wannan hukuncin amma basu bi shawarar ta ba.
Jalila ta mike da sauri ta fice daga palourn tana kuka.
Baban Hanan yace

"Jalal sekayi hakuri, kasan yarinya ce karama, kuma an shammace ta, ba zato ba tsammani aka daura mata Aure, kuma tana ganin duk 'yan uwanta su suka kawo wanda suke so, kayi hakuri da abubuwan dazata yi maka ze wuce kamar ba'ayi ba, gata nan Amana ka rike ta da amana"

Sallamar Hajiya Salma, da kannen Mahifin Jalal, da shi kansa daddyn Jalal, ya katse wa Daddyn Hanan maganar da yakeyi, suka amsa musu sallamar.
Suka karaso suka zauna, daddy yafara magana
"Dukkan yabo da godiya da jinjina da kirari sun tabatta ga ubangiji ma daukakin sarki, me kowa komai, Alhamdilillah anyi taro lafiya an gama lafiya, muna fatan Allah yasa anyi kenan, Allah yabasu zaman lafiya, sannan Alhaji Usman, bazan gaza gurin kuma nuna godiya ga dawainiyar da iyalanka suka dingayi da ďana ba har kawo wannan lokacin da kukayi masa ko ince kuka yimana wannan karamcin, iyalanka sun Rungumeshi lokacin da mutane kowa ke gudun sa, Mungode mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yabiya ku da gidan Aljannah ya jikan magabata, Kuma Insha Allah bazamu baku kunya ba"

Abba yace

"Masha Allah, Alhaji Habib duk abunda nayiwa Jalal tamkar Jawwad nayi wa ne, ABDUL JALAL tun tasowarsu da Jawwad yake kaunar sa, kusan kaso mafi yawa na Rayuwarsa a gidana yayi ta, dan haka yiwa kaine Allah yabasu zaman lafiya"

Itama Hajiya Salma godiya takuma yi da nuna farincikinta akan wannan lamarin.

Jalila kam tana zuwa ta zube a jikin Hanan tana wani irin kuka me sauti, Hanan ta kalli Nana suka hada ido ta dan jinjina kai, sannan tace

"Wai Jalila lafiya kuwa? Meyafaru ne haka?"
Jalila ta dago idonta da tuni yayi Ja tace

"Hanan wai an daura min Aure nima"
Nana tace
"Aure, dawa aka daura?"
"Nana wai Jalal aka auramin, meyasa a kayimin haka? Takuma fashewa da kuka
Hanan tace

" kece baki sani ba, mu mun riga munsan za'a daura muku Aure"
Zumbur Jalila ta tashi zaune ta kalli Hanan
"Amma meyasa baku gayamin ba?"
"Saboda ana gudun wannan shirmen dazaki yi, aka gargade mu karmu sake mu gaya miki, kuma ni banga aibun abunda akayi ba, hakan shine dai2"

"Haba Hanan meyasa zakimin haka? Ko dan na tsaya tsayin daka kin samu wanda kikeso, shine ni zakimin haka?"
"Jalila abunda ya dace akayi, nasan abunda akayi miki babu dadi, Amma iyaye basa zabawa yaransu abunda ze cutar dasu, wallahi Jalila sekin fi kowa Alfahari da shi nan gaba, Yana sonki, kuma kema kina sonshi, sann......
" Dan Allah dakata Hanan "
Jalila ta katseta
" dan bake akayiwa ba ko? Ina da wanda nakeso amma an Auramin wani daban, shine ya gaya miki yana sona, babu wani abu makamancin soyayya a tsakanin mu, ta yaya zan fara rayuwar Aure da Jalal, bahagon mutum me wani irin murdaden hali,
Mahaifiyarsa bata kauna ta, ko kinsam tana zargina da ďanta, Mahaifiyarsa tana da wanda takeso ya Aura, ta yaya zanyi zaman Aure da wanda mahaifiyarsa bata sona, Hanan nasha wahalar Rayuwa, yakamata ace lokaci yayi da zan huta, wannnan Auren tamkar kara jefa Rayuwa ta cikin wata wahalar ne, nasha wuya Ina bukatar zuciyata ta huta Nashiga uku ni Jalila "

" Subhanallah ke Jalila meye hakane kikeyi? "

Muryar Mummyn Hanan

Please Login or Register in order to submit comment