Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batace komai ba ta juya tai tafiyarta
Malaman nan suka dinga jinjina tarbiyyarta, saboda a wannan zamanin a yan matan jami a asamu me durkusawa har kasa ta gaida malamai abunda wuyar samu "hmm bakusan halinta bane, tsabar iya makircine dakikiyace gata fitsararriya, nayi test ta faďi shine takamo hanya tazo".
Bayan kwana ďaya sir hafiz yakuma sawa a kira Jalila Aliyu Imam, tareda kashedin in batazoba zesakamata zero a test dinsa, kuma zuwa office dinsa Jalila tayi, yau wasu yan matane a ciki se iyayi suke suna yauki, gani tayi bashida niyyar saurarta dan haka tazo gaban tebur dinsa tace "Sir tunda baka da lokacina karka kara turawa kace inzo, zuwana nawa office din nan kaki saurarata, bayan kaikace inzo" daga kai yayi ya kalleta, yayinda yan matan suka bita da kallo "ni nace kizo? Kizo in miki me" "bakai kace inzoba karka kara tura captain yana shelar wacece Jalila Aliyu Imam dan bazan kuma zuwa ba, kaitasamin zeron inka ga dama kasamin abscent se wani wulakanci kakemin menayi maka hakane? , in akwai abunda be kai zeroba kasamin" da sauri ya kalleta "What kece Jalilan?" zumbura baki tayi "Eh nice" "karya kikeyi" ba tace komai ba ID card dinta ta dakko ta diremasa a gabansa, dauka yayi ya karanta ya kalleta tabbas itace
"Ya akayi kikacinye test dina gaba daya alhalin wani abunma banmuku ba, kaf ajinku ba wanda yaci ko 30,ko satar amsa kikayi? Kallon yan matan dake office din tayi tai ta kalleshi tace
" Sir Hafiz , Never Judge book according to it's cover, bana satar amsa kuma bantabayiba, kana muzantani agaban yan aji kana cemin dakikiya, abun ba anan takeba, kayi alkalanci, idan baka yadda da wannan test dinba ka canzamin wata, amma karkayi tunanin zaka tambayeni a gaban yan aji in baka amsa" shiru ya danyi, ya kalleta yafarayi mata tambayoyi, a nutse take bashi amsa, gashi ta iya turanci matuka, ga mamakinsa har abunda be koya musuba inya tambayeta seta bashi idea dinta, ajiyar zuciya yayi "shikenan zaki iya tafiya zan nemeki" Jalila ta juya ta fita. Sir Hafiz ya dade yana mamakin kwakwalwarta, gata gentle, amma meyasa tsarin rayuwar ta daban da saura ko maganarta ma daki daki kuma a tsare, kuma ba ruwanta maganar kozatiwa wanda ta fadawa dadi ko a a seta fada kuma ko a gaban waye. haka yaita mamakinta.
Yau weekends dan haka tun sassafe Jalila taketa gyaran wardrobe dinta, tagama tsaf seta ga qura'nin da daddyn Jalal ya taba bata, ta jujjuya qura'nin yana nan kar dashi a cover dinsa "Yakamata in dinga tilawa da qura'nin nan, Allah ya bawa daddyn Jalal ladan" tagama gyaran drower dinta, ta tafi kitchen, wainar masa suka tsiriyi itada halima, a matsayin abincin rana, seda suka gama Jalila taje tai wanka ta dawo ďaki ta zauna tana kwalliya wayarta tafara ringing, tana dubawa taga bakuwar lamba ce, bata san wayeba dan haka ta saka wayar a silent.
Tunda daddy yazo garin nan Ilham take kasa kunne taji, anyi batun aurensu da Jalal amma shiru yau kwanan daddy uku da dawowa amma bataji Mummy tace komai ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa tasamu Mummy, dakin Mummy taje bata nan, dan haka ta tafi kitchen, aikuwa Mummy na can tana hadawa daddy fruit salad
"Mummy sannu da aiki"
"Yawwa daughter, kin tashi daga baccin ne?" "ina wani Bacci Mummy alhalin duk ina cikin zullumi da damuwa" "akan mefa?" "Mummy maganata da Jalal mana, har yanzu naga Daddy ya dawo amma bakice komai ba fa"
"Ilham kenan akwai gajen hakuri, ina nan zan gayamasa insha Allah kafin yakoma za asa ranar aurenku" Murmushi Ilham tayi "Allah yasa Mummy, dan na kagu inganni na mallaki yayana" "hmm daughter ba kunya ko" Ilham ta dan rufe ido tana dariya.
Jalila tagama kwalliyarta tasaka turare, ta mike taje ta dauki Abincin Jawwad ta nufi part dinsa dashi, tana zuwa ta tarar bakowa a palour, ta ajiye abincin tasamu guri a palourn ta zauna, tana jiransa koyana wanka ne, ta dora kafa ďaya kan ďaya tana danna wayarta, hankalinta yana kan wayar sosai, tana game tanayi tana murmushi, warin sigari taji ya daki hancinta, da sauri ta ďaga kanta, tai tozali da Jalal ne ya fito daga bedroom din Jawwad, kallo ďaya tayi masa ta ďauke kanta taji tsigar jikinta ta tashi, dagashi se gajeren wando, kana ganinsa kasan yana cin karfe, a murďe jikinsa yake, ga ko ina na jikinsa lullube yake da gashi, fatarsa se sheki take, babu alamun wahala a tareda shi, ya nufo inda Jalila gadan2 zazzare ido Jalila tayi, kirjinta ya shiga dukan uku2 tanaso tayi magana amma takasa.



More Comments
More Typing.....................

🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️

Koda yaushe bazan manta da gudunmuwarku ba ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 inajin dadin comments dinku, sauran masoya wanda nasani da wanda bansaniba ina godiya
If you want Join the what's app group via this link 👇👇👇👇👇
@https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Or contact me via my number, i mentioned at the above page
If you are not reading the novel please don't join.
[09/04, 12:29 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE7️⃣ 60_


Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]



_MY FIRST NOVEL _



Jalila da kyar take fizgo numfashi, nufota yacigaba dayi, yana zuwa seya wuceta yatafi gurin Tv yanata shan tabarsa, yaje yasaka wayarsa a caji, Jalila kuwa se binsa take da kallo, yagama sa cajin ya taso yakuma dawowa harya wuceta ya dawo ya zauna a gabanta ya kura mata ido, dauke nata idon tayi, "naga kina son kallona ne shiyasa na zauna kigama karemin kallo" ya busamata hayakin sigari a fuskarta, da sauri ta dago tareda toshe hanci, ta dan fara tari, "wai meye haka, Allah ya sawwake inzauna ina kallonka, kato da kai kazomana gida tube sekace dakinka" "dakin Jawwad dakina ne, dan haka ko tsirara naga dama zanyi yawo" yunkurawa tayi zata mike, ya maida ita kan kujerar ya kafeta da ido, yasa kafarsa daya a gefenta, ta kalli inda yasa kafarsa aranta tace kalli jikinsa duk gashi kaman wani dan biri, lighter ya jefomata yasa wata sigari a bakinsa, yaimata alama ta kunna masa, wani mugun kallo tayi masa ta dauke kanta "Allah ya kiyaye ya rufamin asiri, nikabani hanya in wuce, kalleka dan Allah" hannunta daya yakama cikin mugunta ya murde mata yatsu, ihu tayi saboda zafi, take tafara zufa cikin tsawa yace "Kunnamin ko tarihi ya maimaita kansa, inkuma duramiki sigari yanzun nan" jiki na bari ta kunna lighter ta mika hannunta ta kunna masa, "dan Allah ka sakarmin hannuna, yatsuna zasu cire" a hankali yasakar mata hannu, idonta har yayi ja, yacigaba da busa mata hayaki, gashi ya tareta da kafa bazata iya guduwa ba, hannu ta kai zata toshe hancinta, "wallahi kika toshe hancinki sena wanka miki mari, sena baki mamaki da hannunki zaki shata" bashiri ta ajiye hannunta yana busa mata hayaki, se tari takeyi tana dauke numfashi "gaskiya Jalal dan iskane bashida mutunci, yanzu inna matsa da rashin kunya ze iyayimin akuya" seda ya shanye tabarsa tsaf sannan yadubeta "nine Namiji mara daraja ko? Ni Jalal nikike zagi ko?" shiru tayi tana kallonsa, daka mata tsawa yayi "ba dake nake ba kike wani kallona mara kunya" cikin dakewa tace "karya nayi, aiba kadyanayi ba namiji me daraja baze abunda kake ba" "hakane Amma kin bar kari tun ran tubani, kinyi sake namiji mara daraja yamiki Illa, wadda bazaki ganetaba a yanzu, idonki kawai ya nuna a tsorace kike kar in miki wani abu, ba abunda zan miki a yanzu, amma kisani bana yafiya, bana mantuwa, sena hukunta ki akan cin mutuncin dakikemin bazan kyaleki ba, sena gwada miki abunda nakeji idan kika ci zarafina, kidena shishshigi akan abunda baki saniba" Yayi ajiyar zuciya "tashi ki tafi kibani guri kuma kar inkuma ganinki a part din Jawwad dai 2 wannan lokacin, dan kinsan baya nan inkuma kika kuma zuwa to nasan abunda kikazo gani"
Sumi2 ta tashi, taje bakin kofa ta tsaya ta kalleshi "to me zanzo gani, kaikanada abun kallone jiki duk gashi ba kyan gani sekace jikin biri, kokuma wannan jijiyoyin zanzo kallo, jiki kamar dan wrestling aikai ko kyan gani baka dashi, kasa wannan katon hannunka ka matsemin yatsuna Allah yasakamin dan ban yafeba kuma duk barazanar ka bazan dena fadan gaskiya ba, sannan kayi kadan kayimin Illa ko a yanzu ko a gaba, mugu kawai "tai ficewarta, Jalal kam yana jinta tana banbaminta ko dago kansa beba balle ya kalleta.
Ta wuce cikin gida tana yarfa hannu saboda zafi, tana zuwa daki taga Nana ta shirya da alama fita zatayi
" Ya dai naganki kin hade rai, me akayi miki ne? " Jalila ta yamutsa fuska "Bakomai" "Shikenan dama kenake jira kizo ki rakani gidan, Yaya mairo, tace tana son ganina"
"Tab amma badani Jalilan bako?"
"Kamar yaya?" "kamar yadda nagaya miki mana, haka kurum ketace tana son gani baniba, dan haka ba inda zani, banje gidanta ba ma cimin mutunci take, inaga innaje mata gida, kitafi kawai, ba inda zani" "Shikenan tunda bazakiba, dama banason tafiya nikadai ne" "sauka lafiya ki gaishesu"

Bayan Jawwad ya dawo daga school suka zauna domin cin Abinci rana shida Jalal, Jalal ba karamin dadi yajiba ganin wainar shinkafa ce, sunci Abincin nan sosai, Jalal yace "Jawwad dan Allah in da sauran Abincin nan ka zubamin in kaiwa daddy, kasan yana son wainar shinkafa" "Hakane Allah yasa akwai, bari inje cikin gida in duba" Jawwad ya tafi domin dubawa koda Abincin, Jawwad na fita aka kirashi waya, Jalal ya daga wayar ya duba, seyaga sunan Hanan, Murmushi yayi ya daga wayar
"Jawwad ka manta dani ko? Baka daga wayata, nashiga wani hali banajin dadin abunda kakemin" gyara murya Jalal yayi
"ba Jawwad bane, Jalal ne" "Jalal kaine yakake ya gida" "lafiya kalau ya Abdallah, kodayake muna waya dashi" "Yana lafiya, Jalal kaga abunda Jawwad yakemin ko? Banajin dadin hakan, dan Allah kasa baki, Jalal inason abokin ka da wasa na dau abun amma yanzu serious nake sonshi, Jalal help me, so masifa ne, da ban yadda da hakanba se yanzu" "kinaji Hanan, kiyi hakuri Jawwad inyace baya Sonki karya yake, kawai yana duba alkar dake tsakaninki da kanwarsa, amma karkidamu zamuyi magana dashi" (🙄🙄🙄 nikam nace su Jalal dama an iya rarrashi haka) Ajiyar zuciya Hanan tayi "to nagode sosai Jalal, agaida su Ilham"
Jawwad ya shigo da food flask a hannunsa, ya ajiye ya kalli Jalal, "gashi nan Abincin Baby ne tace abawa daddy, amma dawa kake waya haka a wayata"
"Jawwad" "Na'am ina jinka" "Meyasa kakewa yarinyar nan hakane" "Wace yarinyar kenan?" "Hanan mana, ta damu da kai, kamanta kaikake min fada akan Ilham segashi kaima kanayi, meye marabar Hanan da waccan fitsararriyar banzan, ba gara Hanan din bama tafita nutsuwa da saukin kai" "Haba Jalal, Jalila da soyayyar ta na tashi, banason yin abunda zan bata mata rai, tarayyata da Hanan baze haifar da da me idoba, kuma Hanan da kake ganinta itama rigimammiyace, kaikewa Jalila wani kallo dan bakwa jituwa"
"Jawwad yakamata kakoma hankalinka, kayi wani abu akan yarinyar nan mana, kana ganinta so classic nasan da wanine ba kaiba zata sauke ajinta tace tana sonsa ne? Kayi wani abu mana" tsaki Jawwad yayi
"Ina tsawon shekaru Ilham ta dauka tana nuna maka so, kai mekayi akai"
"Jawwad kasani nasani, nida Ilham bamu dace ba, kuma kasan dalili, kuma bari in sake jadadda maka, kokuma in tunamaka wani abu, mahaifiyarka bazata taba bari ka auri Jalila ba, musamman in wannan magananniyar matar tana nan, kaima kasani, kayi tunani Jawwad kafin al'amura su kwabe maka" yana gama fadin haka ya kwashi food flask din yai ficewarsa, yabar Jawwad a zaune yana tunani.
Jalal yana zuwa gida ya tafi part din daddy da fara'arsa, "daddy ina fatan bakaci Abincin rana ba? " "banciba ina shirin ci dai" "Abincin daka fiso nakawo maka" Jalal ya turawa daddy flask din ba karamin murna daddy yayi ba daganin Abincin da Jalal ya kawo masa, "Jalal inaka samo wannan Abincin?" "a gidansu Jawwad" "yaushe rabon da inci masa" daddy ya dan kalli Mummy "Madam kindenamin Abincin gargajiya, mussaman favorites dina" "hmm ba gashi danka yakawo maka ba sekaci ai" daddy yai murmushi "Jalal wayayi girkin nan yayi dadi" "nima bansaniba" Mummy tace "nasan baze wuce Jalila ce tayishiba, dan Maama bata fiye yin girki ba Nana kam dama ba a maganarta akwai son jiki" daddy yace "Jalal inka koma ka turomin takwararka, kafin inkoma England inason inkuma cin irin Abincin nan" hade rai Jalal yayi "daddy waibaka san sunanta bane zaka dinga cemata takwarata" murmushi daddy yayi irin na manya "hmmm to ko in tunamaka tarihin yadda aka samata sunan ne? Dan naga kaman ka manta" "Wai daddy meyasa kake son yimin haka, abune yafaru shekaru da suka wuce kuma kuruciyace baya wuce ba" murmushi daddy yayi "kaji tsoro kenan" "niba wani tsoro danaji" "hmm Jalal kenan, a shikenan tunda kaki yadda" ganin daddy yana neman takura masa yasa yatashi ya fice, bayan fitar Jalal ne Mummy ta kalli daddy "daddyn Jalal, inason muyi magana da kaine" "to ai gani ina jinki"
"Dama gani nayi lokaci yayi daya kamata mucika muradin yaran nan, ina ganin Jalal idan akayi masa aure ze samu nutsuwa, ze rage abubuwan dayakeyi" Ajiyar zuciya daddy yayi
"to yanzu wace yarinyar kike gani zata auri Jalal a wannan halin dayake ciki?" "to ai Jalal yanada wadda yakeso, ga Ilham nan suna son junansu, yakamata kawai ayi magana asaka rana" "kin tabbatar da duk su biyu suna son junansu" "Eh mana sun son junansu, yakamata ayi magana kaje kasamu baban Ilham ayi maganar auren nan" "Kina ganin ba matsala a yin hakan, sunada banbancin halayya, kaman zamansu bazeyi dadi ba" "kaga tunda dai suna son junansu a haka ai shikenan" "Amma ni Jalal be taba yimin wannan zancen ba" "to aini gana nagaya maka" daddy yayi Ajiyar zuciya, be kuma cewa komai ba".
Jalila kwance akan gadonsu ta dakko wayarta ta kira Alhaji Kabiru amma be daga ba, dan haka ta sauka tafara chatting, tana what's app tana hira da zahra, setaga Alhaji Kabiru yakirata, ta daga wayar amma batace komai ba, setaji yana cewa
"Jabir Nakiraka bata shiga, se yanzu tashiga, kayan sun taho daga kudu, munyi waya sunkusa karasowa kano za a sauke a gidan gonata, kaje ka karba se ka rarraba musu cikin dare, kayiwa Jeje magana shima yazo ya karbi nasu" shiru Jalila tayi, wane irin kayane wannan? ta kashe wayar , ta maimaita "Kaya a rarraba cikin dare, kuma hada Jeje" what's app ta koma da sauri tai masa sallama, amma beyi reply ba, ajiye wayar tayi tanata tunani, besan lambar waya kiraba kenan, "Allah nagode maka nafara samun hint akan mutumin nan, Allah kabani mafita" wayarta takuma dubawa setaga ya amsa mata sallamar
"barka da rana, ranka ya dade yakake ya harkoki"
"lafiya kalau, wake magana?" shiru Jalila tayi tana tunanin wani suna zata gayamasa, kawai setace masa "Halima ce" "Wace haliman?"
"hmm duniya da gaskiya kuwa? Wadda kabawa complementary card a banki" "ohhh am so sorry, kuma seda na kawo kece dan na dau muryarki, sedai dan bansan sunanki bane, ina fatan kina cikin koshin lafiya, Gimbiya Halima" "Ina lpy" "Amma nayi mamaki, dakika nemeni, danaga kin yaga card din banzaci zaki nemeni ba, nayi farinciki gaskiya" Jalila ta biye masa suka dinga chatting, daga baya ta sauka ta rufe data dinta,
Jinjina kai tayi, "lallai wannan mutumin zakayi saurin fadawa tarkona, Kuma abun mamaki, wani kayane ake rabawa cikin dare, ga sunan Jeje ya ambata, to me hakan ke nufi, wannan ya tabbatar da yana hulda da Jeje, to wace irin hulda Alhaji Kabiru yakeyi da JeJe haka, wanda yasashi zuwa gurin birthday din Jalal a boye, kai akwai lauje cikin nadi" tana tsaka da wannan tunanin still aka kuma kiranta a waya, koda ta duba tagane lambar Dan sandan nan ne, tsaki tayi harta ajiye wayar sekuma ta yi wani tunani ta daga
"Salamu alaikum" amsamata yayi sanna yace "beauty barka da wannan lokacin ya kike seda ta dan tura baki gaba "Lafiya kalau" "dama cewa nayi bari inkiraki inji lafiyar ki, sannan inaso inzo gidanku in ganki"
"What gidanmu kuma mezakayimin" "Meye abun tashin hankali, inasonki ne aurenki nakeso inyi, please" ture wayar gefe tayi takama dariya sannan ta maida wayar kunenta "Ni wallahi kabani kunya yar baby dani yaushe na isa aure, kuma ya za'a yi Abbana ya aura maka ni, ni gaskiya yarinya ce" yadda take shagwabar ba karamin birgeshi takeba
"Haba yar baby wayace miki baki isa aure ba sannan kuma babu kunya a soyayya" "Babana bazemin aure yanzu ba kuma yariga yabadani, amma nima bansan wayabawa ba" Ajiyar zuciya yayi "bayarwa ba aure bane dan haka zancigaba da neman aurenki"
"Hmm shikenan se anjima, zanyi karatu yanzu" "To Baby tunda kinki gayamin sunanki, ayi karatu da kyau, inkinki mu hadu zannemo gidanku inzo gurin Abbanki da kaina" "Sekazo" daga nan ta kashe wayarta "tab ina zan kai wannaan mutumin"
Bayan sallar la'asar, Jalal yakoma gurin Jawwad, koda yaje ya tarar dashi wani iri kaman mara lafiya, Jalal bebi takan tambayar meyake damunsa ba, saboda yasan akan maganar dazu ne,
"Jawwad daddy yace yana son ganin kanwarka"
"wacce daga ciki?" "wadda ta yi Abincin yau"
"Jalila ce tayi, Allah yasa ba laifi tayiwa daddy ba" "nima bansaniba yace dai taje yanason ganinta"
"zangaya mata Insha Allah" "yayi kyau bari in tafi in kyaleka naga kana cikin damuwa tunda mukayi magana dazu, karka bata lokacinka gurin dogon tunani, maganata itace gaskiyar lamari, duk inda zaka juya kayi tunani kasani maganar dayace mahaifiyarka da yan uwanta basa som wadda kakeso kuma bazasu bari ka aureta ba, dan haka mafita kacireta a ranka ka maye gurbinta da Hanan"
"Jalal tayaya wannan abun ze yuwu, ni Jalila nakeso, Kuma maganar Maama nasan zata amince ne in na lallabata" murmushi Jalal yayi "Shikenan Allah yabada sa'a, amma karka manta da batun kiran daddy" yana gama fadin haka ya fice.
Tunda Jalal yafuta tunani ya damu Jawwad, wayarsa ya dauka ya kira Jalila suka dinga hira, har ya manta da abunda yake damunsa, daga nana yagaya mata daddyn Jalal yace taje yanason ganinta.
Jalal yana komawa gida, kozama beyiba kiran Hannah yafara shigowa wayarsa, tsaki yayi ya ajiye wayar ya shiga sabgoginsa amma tacigaba da kiransa, takirashi yafi sau goma, a fusace Jalal ya dau wayar
"Hannah kina bina bashine? Wannan kiran haka meya faru?"
"Niko nake binka bashi Jalal, meyasa kake wahalar dani hakane? So seya koma kiyayya bana sukuni idan banganka ba, Jalal dan Allah ka tausayawa zuciyata, Jalal kasan Masifar So kuwa? Na tabbatar dakasani dabakaimin haka ba, Jalal ka dubi girman Allah ka tausayawa zuciyata" murmushi Jalal yai kaman Hannah naganinsa
"Hannah kenan, ina mamakin sanda soyayyar da kikemin ta rikide zuwa ta gaskiya abun akwai mamaki gaskiya, but don't mind me akan abunda na fada kinji, nagaya miki gaskiya tun farko, baze yuwu ace nayi yawon club sannan ace matata ma tsohuwar yar club bace, dukda zuwa club dinmu yanada banbanci, kiduba a samarin club dinnaki kisamu wani ku daidaita amma ba Jalal ba"
"Amma Jalal ai nace maka na tuba wallahi inka aureni zandena"
"Ni ABDUL JALAL nafi karfin ragowar garorin bariki, ki kiyayeni" yana gama maganar ya kashe wayarsa.
Daddy sam yakasa yadda da batun Mummy gameda Jalal, shidai yasan Jalal ko zancen mata bayaso ayi masa, amma ya akayi haryake soyayya da Ilham besaniba dukda yana dadewa baya nan, amma yasan da zeyi masa zancen, dan haka ya yanke shawarar kiran Jalal yaji tabakinsa.
Hanan na kwance akan katafaren gadonta, tayi zurfi a tunanin ta, taji an turo kofar dakinta, dan daga kai tayi taga mum dintace, batace uffan ba tai shiruu tacigaba da tunani, gefenta Mum tazo ta zauna ta dafata "Auta meyake damunkine, yan kwanakin nan kullum cikin damuwa kike meyake damunkine" a hankali Hanan ta tashi zaune "Mummy na ba wata damuwa, damuwar school ne kawai kinsan akwai tension na makaranta"
"Hakane Hanan, amma yusuf yakawomin kararki fa" dan ya mutsa fuska Hanan tayi "Meyace miki?"
"gaba daya kin canza masa yakasa gane kanki, meyake faruwa ne?"
"mummy kinsan tun farko dama ni bawani yimin yaya ba kinsani, Mummy kinsan wani abu kuwa"
"A 'a sekin fada"
"tun farko kinsan ba son Yusuf nakeyiba, Mum zuwana kano naga Yayan Jalila cousin dinta wanda takeso, da saboda in tsokaneta nace ina sonshi, amma daga baya abun yakomamin Gaske, Mum ina son Abunda Jalila takeso ne, kuma yazama dole tabarmin dan basu dace ba".



Share please
More Comments More Typing.............................

Daga Alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

Comments dinku yana sani nishadi ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ina yinku irin sosai din nan Allah yabar zumunci yabar kauna

Join the what's app group via this link ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP :https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Don't join in ka/kinsan baka karanta novel din
07063065680

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 8️⃣/61_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]


_MY FIRST NOVEL _


Wani irin Kallo Mum tayiwa Hanan
"I don't think you are in your senses, Hanan, kawartaki dukda yarinyar ba wani yimin tayiba, amma son da kike mata yasa na kyaleku tare, amma hakan bazesa inkasa gayamiki gaskiya ba, Hanan inkikayi haka baki kyautaba, hakan ba daidai bane, Jalila taana kaunarki meyasa zakiyi mata haka" kwalla ce ta taru a idon Hanan
"Mummy ki fuskanceni banyi haka dan cin amanar Jalila ba, Mum wallahi makauniyar soyayya nakewa Jawwad, Mummy he is very nice and gentle, gashi salihi, Mum soyayyata da Jawwad mafita ce kuma ceton Jalila ne, inajinta a zuciyata kamar yar uwata ta jini, dan haka bazan iya cutar da itaba all i know is that inason Jawwad "
"Kamar yaya kenan, tayaya kike son maida karya gaskiya"
Labarin abunda ke tsakanin Jalal da Jalila tabawa Mummy, ta nisa tace
"Mum ko bankuma cewa komai ba kinsan Jalal is her e destiny, ita kadaice zata iya sadaukarwa domin ceton sa, Mum mahimmanci Jalal a rayuwarta ne yasa ake mata nuni da halin dayake ciki a mafarki, Mum kibani karfin gwiwa, zanyi meyuwuwa in dauke hankalinta daga kan Jawwad, sannan zan temaketa akan rayuwar Jalal" Jikin Mum ba karamin sanyi yayiba dajin labarin da Hanan tabata,
"Shikenan Auta, zancigaba dayimuku Addu'a Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi".


Please Login or Register in order to submit comment