Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jawwad Aure da Naja an zalunceshi, gashi tasan Maama bazata taba barin Jawwad ya Aureta ba, nan duniya tasan inta Auri Jawwad tayi sa'ar miji, salihin bawa da baruwansa da hayaniya"da taga tarasa mafita taje ta janyo trolley dinta ta fara shirya kayan dazatayi Amfani dasu dan tafiya bauchi, taji gara ta dan bar garin tayi nisa maybe ta huta da wannan abubuwan daga wannan se wannan.
"Kayan me kike hadawa haka?"
"Kayan da zan tafi dasu Bauchi mana"
"Jalila bana son kitafi, badan hutunmu next week ze kareba da binki zanyi"
"Allah sarki my Nana, nikaina zanyi missing dinki da kiriniyarki"
"Mtseww Allah raka taki gona, inkin tafi karki dawo bakar kaya kawai, daga nan kema kitafi inda uwarki ta tafi"
Nana ta juyo ta kalli Naja a fusace tace
"Wai Naja ke wace irin mahaukaciya ce" da sauri Jalila ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ke Nana wayagaya miki in kare yana Haushi ana kulashi, kyaleta dan Allah, innaje Bauchi me kike so in kawo miki" Naja tace "Ke kin isa kice min Karya, uwarki ce Karya baniba" Jalila tai sauri tace
"Nana naji kaman muryar Maama tana kiranki yi Sauri kije" Jalila ta tura Nana waje ta dawo ta zauna ta kalli Naja tace
"Uwata batada katon baki da zako zakon fika kuma bata haushi kaman uwar wata, ki kiyayi ranar da bomb dina ze tashi dake, Naja har inda Yayarki Sa'adah ke zuwa a zubar mata da ciki nasani, tsohuwar karuwar Alhaji Kabiru ce dayanzu yake can ana shirin gurfanar da shi a kotu ko karya nayi? "
zaro Ido Naja tayi
"Karya kike ubanwa yagaya miki haka? Waye yayiwa Sa'adah sharri "
"Kinga bana son wani borin kunya, ganina kawai kike amma bakisan waceni ba, bana zama da mutum ba tareda nasan wayeshi ba, karkiyi mamakin kema nasan komai akanki Jalila ta wuce tunaninki Naja, kibini a sannu im bahakaba zanmiki tonon sililin da sekin kasa hada ido da mutane, tun ranar dana ji kina waya cikin dare da Saurayi kema na fara bin diddigin ki dan haka ki kiyayeni"
Gaba daya jikin Naja ya sanyi, yayinda gumi ya shiga tsatstsafo mata ta goshi, tunani tafarayi ya akayi Jalila ta san wani abu akansu haka, bakowa yasan wannan abubuwan da Jalila ta fada ba amma ita ya akayi tasani, Jalila ta tashi tabar inda Naja take tacigaba da hada kayanta. Tundaga Ranar Naja takejin tsoron yiwa Jalila rashin mutunci dan ta tsorata da kashedin datayi mata.
Shikam Jalal yakara takure kansa, tun ranar bekuma haduwa da Jalila ba, yana son ya ganta amma baya samun damar hakan, dan ko a waje baya ganinta, Jalal baya son kowa yaje inda yake, baya iya cin Abinci idan ya tuna abunda Jeje da uban gidansa yayi masa saboda laifin da banashiba seyaji duniyar takara yimasa Zafi, ga abunda yaji Da kunnensa Ilham na fada akansa itada mahaifiyarta, Gakuma Jarumatar da Jalila ta gwada saboda shi abun ya dade yana bashi mamaki ya akayi Jalila ta gano Jeje da uban gidansa akansa suke Aiki harta hada wannan gwaramar, yana son jin wasu abubuwan daga gareta, idan yaji duniyar tayi masa zafi, seya sha giya ya bugu sannan yake jin dadi.

Jalila tashirya kayanta tsaf tun dare, ji take kaman za'acireta daga prison zata tafi kwana biyu ta huta da tension din da suke kanta.
Tun safe Jalila tayi wanka, tai waya da Hanan tace mata zasu karaso da wuri.
Jawwad yaje ya takura Jalal yaci Abinci ya dinga yi masa Nasiha akan wannan takura Rayuwarsa da yayi, Jalal yace "Dan uwa, Nayiwa Kanwar ka laifi fa, nikuma tayimin Abunda har in bar duniya bazan manta ba"
Jawwad yasan Jalila yake nufi yace
"Allah yasa ba wani laifin tayi maka ba? Nasan Halin Baby sarai in wani abun tayi maka Allah yabaka hakuri"
Jalal yai murmushi yace "Ba laifi tayimin ba, Amma tayimin abunda banida abun biyanta, inajin kunyarta abubuwan danayi mata abaya" Jalal ya karasa maganar idonsa fal kwalla
"Subhanallah haba Jalal, haba 'yan mazan daddy, hawaye a idonka, kadena damuwa kaji, komai ze wuce banason ganin ka cikin damuwa muje kaci Abinci, Yau Jalilanma zata tafi bauchi"
"Bauchi kuma?"
"Eh Jalal, nima ban soba amma tasamu ta huta, zaman gidanmu sam baya mata dadi, Maama tana takuramata kuma Yaya mairo ce take zigata, banajin dadin abunda suke mata, inta tafi ta huta kwana biyu, tashi muje ka karya"
Jalal be kuma cewa komai ba yabi bayan Jawwad suka fita. Da kyar Jawwad ya takura Jalal yaci Abinci shima kadan yaci yace ya koshi. Jawwad yaita tunanin me Jalila tayiwa Jalal haka har yake cewa baze manta ba?.
She kusan karfe daya na Rana su Hanan suka karaso kano gidansu Jalila, a guje Jalila ta fito daga cikin gida ta rungume Hanan cikin farinciki, Hanan tace "Nayi missing dinki 'yat Baba" suka kuma rungume juna suna murna, Jalila ta kalli Abdallah tace "Babban Yaya sannunku da zuwa ya hanya?"
"Hanya Alhamdilillah, da tuni munzo amma Hanan tasa muka makara"
"Aina sani ita tahana kuyi sammako" Hanan tace "to mukoma kenan?"
"A'a ni bance ba, ina Baban yake?"
Hanan tace "Daddy shida Mummy zasuje su tarar da mu acan, dama zamuyi biki, yarinya har Anko daddy ya dinka mana nida ke"
Jalila tai musu jagora har cikin gida a palour tabasu gurin zama, taje ta sanarda Abba su Hanam sunzo, dukda wulakancin da Maama takewa Jalila, amma ta sakarwa su Hanan fuska ba laifi, Jalila taje tagayawa Nana su Hanan sun karaso. Naja najin haka ta biyo su dan ganin wai wacece Hanan din nan ne tana zuwa palourn tayi turus, se yanzu ta tuna suntaba haduwa a gidan kamarta daya da Jalila, Amma Hanan takara kyau sosai seda Gaban Naja ya fadi, Hanan tanada kyau sosai gata ta iya gayu, Nana ta fito palour suka gaisa dasu Hanan nan aka shiga hira a palourn, Abdallah yace "Nifa banga Jawwad ba da mutumina Jalal" Nana tace bari inje in kiramaka shi, nasan besan kunzo ba tashi tayi ta fice a palourn Maama da kanta ta kawo musu Abinci, Abba ba ruwansa ya zauna suka dinga hira da Abdallah, Jalila ta janye hannuna Hanan zuwa dakinsu, Nana ta dawo itada Jawwad, Jawwad yashigo da fara'a ya zauna kusada Abdallah suka gaisa daga nan sukayita hira.
Naja ta babbake a daki, dan haka Jalila bata samu damar yiwa Hanan hirar datake so ba sukayita hirarsu ta rayuwa, Hanan taji muryar Jawwad a palour tacewa Jalila zanje wanke Hannu"
"baga toilet ba kishiga mana ki wanke"
"Ba wanke Hannu zanba Jawwad nakeson gani"
Naja tace "Ke mekikace meye hadinki da shi dazaki ganshi?"
Ko tsayawa Hanan batayi ba tayi waje, amma kafin takarasa palourn ta tsaya ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito palour,
Da sauri Naja ta fito itama, unexpected Jawwad ya daga ido yasauke akan Hanan, takara kyau dressing dinta ma yayi ba karya, gaba daya besan lokacin dayake kallonta ba, tabass Hanan kamarta daya da Jalila a ransa yace "tsarki ya tabatta ga Allah, ba dangin iya bana Baba, amma ya halicci masu kama daya kuma ba twinsa ba, sedai sunada dan banbanci"
Cikin kasaita ta wuce shi a palour ta nufi kitchen.







❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku 😍😍😍😍

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣0️⃣83

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]






_MY FIRST NOVEL _


Hanan takuma dawowa zata wuce
Abdallah yace "Auta bakiga Jawwad din naki bane" dan kallon Jawwad tayi, tayi murmushi tace "Naganshi mana" Naja kamewa tayi a gurin musamman dataga Jawwad yana kallon Hanan, da alama beji dadin yadda Hanan taki kulashi ba.
Abdallah yace "Wallahi Hanan totally dinta se a hankali, duk ta takuramin wai muyi Sauri muzo taganka amma ta ganka ta wani basar" Jawwad yai murmushi yace "Kyaleta Abdallah zamu shirya ne, maybe gajiyar Hanya ne ya hanata yimin magana"
"Bawani gajiya tsabar wulakanci ne kawai" Hanan ta murgudawa Abdallah baki, suna hada ido da Jawwad ta kashe masa ido daya, gaba daya ya rikice, gani yake kaman kowa yaga Abunda Hanan tayi gaba daya yakasa sukuni,
ita kam Hanan ta wuce Naja takoma inda tabar Jalila a daki, ba kunya Naja takuma biyota dakin, Hanan tana shiga tace "Ohh God, Jalila Haidar yakara kyau yakuma zama babban mutum, wayyo dadi kasheni, naga farincikin zuciya ta" Jalila tace "Waye kuma Haidar?"
"So kike indinga kiransa da sunan da kike kiranshi ne, kowa yace Yaya Jawwad nima ince Yaya Jawwad, Haidar dai kaman in sace shi in gudu haaka nakeji, yawwa Queen ranar muna waya dake naji wata namin kashedi akan abunda yake mallakina, wacece dan Allah?"
"Nice nan, kuma wallahi duk maitarki iyayenmu sun tsaida magana, bashida wata mata in baniba, mayun banza dana wofi marasa zuciya" Naja ce taketa fiffika tana fadan maganganu Hanan taja wani dan tsaki tace
"Jalila aina dauka wadda take cewa zata auri Jawwad din mace ce, ashe mata maza ce mata ta rako duniya, ke cewa akayi ya Aureki, nikuma Jawwad yana sona ne" , dan saurin kallonta Jalila tayi, lokaci da dama Jalila tana daukar abunda Hanan take a matsayin wasa, dukda tana ganin tsagwaron gaskiyar abunda Hanan din ke nufi a idonta Jalila na cikin wannan tunanin Hanan tace "zan tabattar da hakan anan kusa ba a nesa ba, ke Queen ina mutuminne tunda nazo ban ganshi ba"
"Wakenan?"
"kinfini sani, Jalal mana" tsaki Jalila tayi tace "Nifa bana son maganar wannan shirmammen"
"Jalal dinne shirmamme?"
"Eh shidin, ke Akwai Labari amma semun je bauchi Lafiya insha Allah"
"To Allah ya kaimu lafiya"

Abdallah yace "Jawwad nikam ina Jalal ne naganka kai kadai?" Jawwad yace
"Yana part dina baya jin dadi"
"Allah sarki, muje inganshi, muyi salla Azahar sannan mu wuce"
Suka tashi suka tafi part din Jawwad, suka tarar da Jalal zaune akan kujera, yana kallon TV amma sam hankalin sa baya kan Tv, shigowarsu yasa ya daga kai, murmushi yayiwa Abdallah, ya mika masa hannu suka gaisa
"Jalal ashe bakaji dadi ba? Sannu gaskiya ka rame, Allah ya sawwake"
"Abdallah aini na warke tuntuni, Jawwad ne da zuzuta abu"
Jawwad yace "Au ni nake zuzuta abu, dadinta kallo daya za'ayi maka asan baka da lafiya" sukayi Salla, suka zauna sukayi ta hira, Jalal ya sake sosai.
Can aka jima Abdallah ya kira Hanan a waya yace su fito yanzu zezo su tafi, Hanan tace masa to, Jalila ta nunawa Hanan akwatinta tace "Hanan kaimin mota, bari in sa kaya" Nana tace
"bari inje ingayawa Abba zaku tafi" Hanan ta ja trolley Jalila ta kai bakin mota, amma motar a rufe, tasan Abdallah suna part din Jawwad kanta tsaye ta tafi part din, tundaga waje take iya jiyo hayaniyarsu, shiga tayi da sallama duk suka amsa mata, ta fadada murmushin fuskarta ta Kalli Jalal tace "Yaya Jalal kwana dayawa, Yakake ya gida amma naga ka rame sosai" shima murmushi yayi mata yace "lafiya kalau Hanan, amma aini hakanake dama can ban rame ba, yagida ya hanya?"
"Alhamdilillah, ina wannan kanwar taka, yama sunanta?"
Abdallah yace "Kai Aku me magana, daga zuwanki kinfara zuba kaman kanya"
Dan hade rai tayi "kace mufito kuma ka kulle mota, ga kayan queen can na fito dasu, kazo ka bude in samata a mota"
"Sedai kizo ki karba kibude, bari mugama hira"
"Gaskiya Abdallah ka dinga jin tsoron Allah muka katse namu hirar kace mu fito kaikuma ka zauna"
Taki kallon inda Jawwad yake, balle yasaka ran zata kulashi, Jawwad ya karbi key din motar a hannun Abdallah yace
"muje in bude miki motar, Abdallah bashida niyyar tashi yanzu"
Dan murmushi tayi ta juya, Abdallah yace "tasamu abunda takeso, dama ba dan Allah tazo nan dinba, sarkin gulma wani inzo in bude mata mota, kawai kice Jawwad yataso gurinsa kikazo, sewani Iyayi kike"
Hanan taji kaman kasa ta bude ta shige, Abdallah mugun dan rainin hankali ne Jalal yace "Ahha kai Abdallah ina ruwankane? Yada shishshigi haka?"
"Auto nayi shiru, tunda ka goyi bayanta"
Suna fitowa Hanan ta nufi hanyar komawa cikin gida, Jawwad ya kira sunan ta, ta tsaya amma bata juyo ba, ya karasa gabanta yana kallon ta amma ta sunkuyar da kai,
"Hanan, menayi mikine? Tunda kikazo kin kula kowa amma ni kin shareni"
"Bakomai"
"Ban yadda ba komai ba, laifin menayi miki?"
"Haidar dan Allah ka kyaleni, banason matsala, kace baka sona, gaa nazo na tarar da wata tana gayamin ita zaka Aura ya zanyi? Ina kokarin in cireka a raina amma nakasa, ganinka din nan ma yana karamin pressure ne, na damu da kai sosai kaikuma ka nuna baka sona, base in hakura ba, mezesa incigaba da shishshige maka?" Abun mamaki hawaye ke kokarin fita a idon Hanan, hakan na nuna maganganun da take fada har cikin ranta, Jawwad yace
"Zannemi wata alfarma daya a gurinki, zakiyi min? "
"Alfarma kuma? Wace iri"
"Sekinyi min Alkawari zakimin Alfarmar"
"Inkuma bazan iya bafa?"
"Bazan tambayi abunda bazaki iyaba ai, abune me sauki"
"To fadi in zan iya" yai murmushi yace
"Sonake inkuma jin sunan dakika kirani dashi please, yanamin dadi"
Dan zumbura baki tayi ta noke kafada, "Niba wani suna"
"Kince fa zakiyi min Alfarma" cikin shagwaba tace
"ni banyi Alkawari ba ai"
"Please, ko inyi kuka ne sannan ki fada"
"Eh to yi kukan in gani tukuna" sukayi dariya a tare, yanayin irin tsokanar Jalila haka Hanan takeyi, amma Hanan bata iya komai ba akan Jalila, Jawwad yace
"Hanan da bakina ban taba cewa bana sonki ba, ban taba soyayya ba, amma nasan ina son Jalila so ba na wasa ba, kinga akwai alaka me girma tsakanin ki da ita, sannan batun Naja da kikeyi Wallahi Hanan yanzu haka ina dauriya ne kawai, Naja zabin Maama ce, tanason in Aure ta ni inason yiwa Maama biyayya amma bana tunanin zan iya Auren Naja,
Hanan nasan kinshiga damuwa saboda ni but am very sorry, banason kowani rai ya shiga damuwa saboda ni, ta mussaman ke ce a gurina" Hanan tai murmushin da seda hakoranta suka fito, ta jingina da motar tace
"Kasan meyake kara burgeni da kai Haidar?"
"A'a sekin fada"
"A dukkanin maganganun ka kana kokarin fadar gaskiyane, sannan kanada tausayi shiyasa nake kara sonka, Amma bari ingaya maka wani abu, alakar dake tsakanina da Jalila bazan so ta baci ba, saboda ina mata so na gaskiya, bazanyi wani abu in cutar da ita ba, Amma maganar gaskiya kanawa Jalila so ne irin na 'yan uwantaka ba soyayya ta Aure ba, haka ma zuciyar Jalila tana maka sone na' yan uwan taka, nasan zakayi mamaki, Jalila bata taba soyayya da wani ba, tanada Samari Amma har yanzu taki yadda zuciyarta akwai wanda takeso saboda taurin kanta, kaima zan baka lokaci zaka gazgata abunda nake nufi"

Gaba daya zuciyar Naja ta gaama tsinkewa, Ganin Hanan taki dawowa yasa ta fito harabar gidan, amma tayi tozali da Hanan da Jawwad se murmushi yake, tunda take da Jawwad maganar minti goma bata hadasu balle yaita wannan murmushin, Nana ma befiye shiga harkarta ba, a da tayi tunanin ko Jalila yake so, wato wannan yarinyar me girman kan bala'i ita yakeso, koma dai duka yake sonsu ne tana tsaye tana kallonsu
Jawwad yafara magana "Hmm Hanan ina kika samo wannan ideology din, yazakice Baby Akwai wanda takeso, kuma munayiwa juna son 'yan uwan taka?"
"Ban fada domin in shiga tsakanin ku ba fa, nawa hasashen ne haka, Ita kanta Jalila bata son wa take so ba, bakowane lokaci take yadda da zuciyarta ba tana karbar abubuwane da lissafin kwakwalwarta"
"Hanan ya akayi duk kika san Jalila haka ne?"
"Haidar a zaman danayi da Jalila motsi tayi nasan abunda take nufi, nasanta fiye da yunwar cikina"
kyar yake kallon Hanan ko kyaftawa bayayi yana juya maganganun ta a ransa, ganin yanata kallonta yasa tace "ya dai kona bata maka raine?"
"Ina so kicigaba da magana ne, komai kikayi kyau yake miki" murmushi tayi tana rufe fusaka,
yace "masha Allah yanzuma bakiga yadda kika kara kyau ba"

Abdallah da Jalal suka fito daga part din Jawwad, ba karamin matching Jawwad da Hanan sukayi ba, suka nufosu Abdallah na shirin sukarasa ya tsokane su, shikuma Jalal Jawwad kawai yakson ya titsiye yau, amma kafin su karasa Naja ta rigasu dan Naja ba karamin kulewa tayi ba, dan haka ta taho kaman wata kura, ta nufo su Jawwad, tana zuwa ta rike kugu tace "ke wace irin matsiyaci ya ce haka? Nace miki Jawwad shine wanda zan Aura na meye zakizo kina wani shige masa, kina wani salon karuwanci meye haka?"
Hanan kaman tayi magana, sekuma ta fasa tace bari inga matakin daze dauka
Aikuwa Jawwad yace "Naja meye hakane wai? Yazaki kirata da karuwa me tayi miki? Wannan wace irin magana ce"
"Eh dole kace wace irin magana ce mana, kasan ni zaka Aura amma kazo kunfi minti Ashirin a nan gurin alhalin niko hirar minti goma bakayi dani"
Jalal yace "wai dan Allah meyake damun wasu matanne, yanzu meye hakan kuma?"
Abdallah yace mata se Addu'a ai, se yanzu Naja ta lura da shi, wancan zuwan ma tare sukazo, ita da Abdallah ze Aureta aida ta hakura da Jawwad
Abdallah yace "kinga baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah, Kekuma Auta, Jawwad fa Ustaz ne, kinzo kin wani kanainaye shi tun dazu, kina kashe masa murya kina fari, Ashe ma ankusa Aurar dashi, ai seki hakura" gaba daya sukayi dariya suka maida Naja kaman wata mahaukaciya,
Hanan tayi murmushi cikin kasaita tace "Macen data kai mace, itace idan tace tanason take samu, ba ragowar muna mata ba" shikam Jawwad ba karamin kunya Abdallah yabashi ba
Sannan Hanan tace "gaskiya Abdallah kai dan hana ruwa gudune, Yaya Jalal ka shiga tsakanina da Abdallah, My Haidar karka damu da Abdallah haka yake da wannan takurar"
Jalal yace "Inyee ashe har suna aka canza maka abun masoya kai Jawwad, se anyi magana ya dinga sunkuyar da kai waishi kunya, bayan yagama zuba kalamai shima"

Da sauri Naja ta shige cikin gida, tanata kumfar baki a palour ta tarar da Nana sun fito Jalila daga part din Abba
"Ni za'ayiwa hauka, ni wannan yarinya zatayi wa karuwanci, wallahi yau duk bala'in da za'ayi se anyi, shegiyar yarinya a gabana kaman zata hadiye Jawwad kan bala'i, a fusace Nana tace
"Ubanwa ya hana kiyimusu can sekinzo mana nan, inkina yiwa Jalila tana kyaleki, ita wannan a yanzu intaga dama wallahi zata saka sojoji sumiki dukan mutuwa, dan ko a ina take a a fadin kasar nan akwai yaran babanta"
Jalila tace "Nana, bari inje waje inga meke faruwa, Nasan halin Hanan sarai, ba kanwar lasa bace, dukan sojoji yafiye maka dukan wannan bakin nata, koba komai yau na huta, Anamin maganin karya me remote"
Aikuwa Jalila takara angizo Naja, "ke dan abu ta kazakazanki, nikike cewa karya?" Ai Jalila bata jira taji metake cewa ba ta fito.

Jawwad duk yarasa ya zeyi dasu Jalal, se tsokanar sa sukeyi shida Abdallah yana sunkuyar da kai, itakuwa Hanan ko a jikinta data fuskanci sun takura masa, se tace
"cwt Haidar don't mind them, kaga Abdallah aiba a magana shima haka yake zuwa ana kashe masa murya, idan ana masa wannan kashe muryar seka sace shi ka gudu be saniba" seda ta danyi murmushi sannan tace "Kaga yaya Jalal Allah kadai yasan shime ake masa, shima nasan yana zagayewa yaje akashe masa muryar dayake takura maka, kaima ka dinga ramawa amma zanso inga budurwar Yaya Jalal inga in an kashe masa muryar shi ya yakeyi, sweet Haidar sena koya maka magana, adena takuramana"
Jalal yai dariya yace "Ni Hanan aibana soyayya, ban santa bama balle inje a yimin wasu kalamai,, in aka fara yimin kalaman zan kiraki kizo kigani, sedai fatan Allah ya hadamu da masoyanmu na gaski..... Jalila ya hango tana sakkowa daga steps, tayi kyau sosai, amma abunda yabashi mamaki ta rame, "ko bata da lafiya ne? Tayi rama sosai, itama tana daga ido sukayi ido hudu, taji gabanta ya fadi "kaddai ace har yanzu Jalal bashida lafiya, wace irin rama yayi haka?" kallonta yake yadda take tafiya step by step, Hanan kam tuni taga abunda yake faruwa tai murmushi a ranta
Jalila ta karaso tace "Yaya Jawwad ina fatan komai lafiya, naji Naja tanata masifa, Hanan me kikayi mata ne?"
"meko zanmata? Dan kawai ta ganni da Haidar ne"
Abdallah yace "karya takeyi tun dazu ta tsareshi anan tana zuba masa kalamai, tun yana jinkunya naga alamar kalaman sun fara shigarsa, murmushin yake Jalila tayi tace" nikam ki lallaba ku rabu lafiya"
"karma a rabu lafiyan ba abunda ya dameni bane, haidar dina ne agabana"
Abdallah yace "ke Hanan kinfiye zakewa, ance miki anbadashi amma kin nace" Hanan ta lura yadda Jalal ke kallon Jalila, itama Jalila tana satar kallonsa amma bata bari su hada ido, Hanan ta gyar murya tace
"Queen kinga Yayyenki nan biyu sun takuramana, shi Abdallah nasan yadda Siyama ke kasheshi da kalaman soyayya, amma shi Yaya Jalal ban saniba, da nasani da na ramawa Haidar, amma gayamin ko kin san budurwarsa?" hararar Hanan tayi tace "Aiba tare muke yawo ba balle in san budurwarsa, seki tambayeshi ai"
Hanan ta tintsire da dariya dama tana sane tayi hakan?
Jawwad yace "Baby ina Abba ne?"
"Yana cikin gida, yaya Abdallah ku shiga sekuyi sallama da Abban"
"ok bari muje"
Jawwad ya musu rakiya suka nufi cikim gida
Jalila tayi mamaki yadda Jalal yake hira bazakece shine ba, Jalila tafara kokarin saka jakarta a mota
Jalal ya dan kara kurawa Jalila ido, yazo kusada ita ya tsaya, ya danyi kasa da muryarsa yace
"meyake damunki kika rame haka?" bata dago ba tace
"ni ban wani rame ba, dama haka nake"
"hmm, shikenan tunda kince haka, amma yaushe zaki dawo?"
"Ka Aike nine, wai ina ruwanka danine?"
"Aiba abun zafi bane, meye nayin fushin kuma?"
"idan na tafi bazan dawo ba, idan na tafi zan hutawa raina indena ganin masu ba kanta min rai, kaima ka huta dame yi maka shishshigi, kaci karenka babu babbaka, inka gadama kaima ka gina club din shna giya"
"meyasa ba kya mantuwane? Abu baya wucewa a gurinki kenan?" Su Hanan ya gani suna fitowa dan haka yace mata
"zaki iya zuwa ki zauna a wani garin, kibar Jawwad din naki da Nana tsawon lokaci?, idan ina ganin ki inajin kwarin gwiwar dena wani abun, dama zan miki sallama ne dan inaga kafin ki dawo, zan koma Dubai da zama, bazan kara dawowa Nigeria ba, har abada, ina fatan kiyafemin kura kuran danayi miki, Sannan Nagode da kokarinki a kaina, keda Ummi bazan tabawa mantawa daku ba, sannan A shekarun baya, wani zuwa da kikayi, Su daddy sun baki kyaututtuka, ciki hada wani Jan Alqur'ani me red din box, nina baki kyautar wannan Alqur'ani sannan Akwai Ajiya ta a ciki.







❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku

Please Login or Register in order to submit comment