Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar kullum Abba yarabawa kowa tsaraba sunata murna, sun hadu a palour ana hira.
Abba yace "Jawwad ranar Asabar Insha Allah za'akai kudin Aurenka kamar yadda Maamanka ta bukata, inda wani shiri da kake ganin zakayi to kaje kayi, Jalal yagama komai next month Insha Allah zakafara zuwa gurin Aikinka"
Wani irin gumi ya dinga tsatstafowa Jawwad, yariga yagama karaya, sannan yana jin matukar kunya da nauyin ya bude baki yagayawa mahaifinsa baya son zabin da mahaifiyarsa tayi masa, Jalila ta kurawa Abba ido alamar bata gamsu da abunda yafada ba, Abba ya kalleta yace "ya dai 'yar Baba? Kokinada magana ne?"
Juyawa tayi ta kalli Maama data tsareta da ido, magana kam akwaita a bakinta amma ba' a gaban Maama ba, girgiza kai tayi alamar A'a, ta mike ta tafi dakinsu tanata safa da marwa, tana tunanin ta ina zata fara yiwa Abba bayani, tasan kotayi Maama karyata ta zatayi.
Gajiya tayi da sintirin datake taje ta bude wardrobe zata dau towel tayi wanka, ta bige wata jakar Naja ta fado kayan ciki suka zubo dayake bata zugeta ba, a sama inner wears dinta ta dora a kai, amma kwayoyi ne da kwalaban syrup a cikin jakara, binsu da ido Jalila ta dingayi yayinda tayi mutiwar tsaye.
Da sauri ta durkusa ta tattare mata su ta mayar mata da jakarta yadda ta ganta, nan tunani yakara yiwa Jalila yawa bazata taba bari a Aurawa namiji kamar Jawwad wannan tanbadadiyar ba,ko Nana bata gayawa abunda ta gani ba, tayi shiru da bakinta.

Wasa2 duk yadda Jalila taso ganin Abba personally Maama ta kankane, ta tattare a part dinsa bata matsawa ko nan da can, seda aka kai kudin Auren nan, naira dubu dari Abba yaje ya kaimusu, su Yaya mairo hada kira wayar Maama tana mita wai duk Arzikin da Allah yayi musu amma ace kudin Aure akawo dubu dari, mecec dubu dari a kudin da suke dashi, Maama taita lallabata tace tayi hakuri zasu hade a kayan lefe.
Yayinda gefe abun duniya ya damu Jawwad, begayawa Hanan halin dayake ciki ba, ko Abinci baya iyaci, duk ya rame. Jalila da kanta taje ta dinga bashi kwarin gwiwar yacigaba da Addu'a komai zeyi dai2.
shikansa Jalal abun ya dameshi, meyasa za'ayiwa namiji Auren dole, ko mace be kamata ayiwa ba balle Namiji, shima Jawwad saboda nusaranci da kunya baze iya cewa baya sonta ba, wani lokacin kawaicin Jawwad yana batawa Jalal rai.
Jalal yanata tunanin wani taimako ze iyayiwa Jawwad, dan shima baze bari ayi wannan Auren ba, tunda Jawwad baze iyaba zeje yasamu Abba da kansa yagaya masa Jawwad baya son yarinyar nan, yana wannan tunanin yaji message ya shigo wayarsa,
Koda ya karanta, tsayawa yayi yanata juya message din shidai yasan tabass wannan message bana sa bane saba lamba akayi, dan haka ya barshi a matsayin anyi missing number ne aka turo masa, dan hukumar dasuka turo message din da sun san wayeshi sun san laifin dayake aikatawa da basu turomasa abunda suka turoba.

Jalila ta yanke hukuncin yau zata samu Abba ko agaban waye, zata nuna masa illar abunda yake shirin yi
Kai tsaye part din Abba taje, ta shiga da sallama a bakinta, ya amsa sallama sannan yace "dama ina son ganinki, Baby ankaiwa yayanki kudi ze Auri 'yar uwassa, kune' yan mata kunfi sanin menene kuke so, kuma kuna tareda ita, maybe a kayan lefe akwai abunda takeso maybe ku tayi hirar daku, ba lallai tagayawa iyayen ta ba, dan haka inda wani abu da take bukata kokune tagayawa kota rubuto, saboda asan me za'a samata a kayan lefe"
"Abba wannan Auren fa bame yuwuwa bane?" mamakine ya kamashi yace "meyasa Jalila?"
"Baya sonta fa"
"Amma na kirashi na tambayeshi yace min ya yadda"
"Haba Abba zuwa yanzu yakamata kagane halin Yaya Jawwad, tunda kake ka taba nuna kana son Abu yace bayaso? Wallahi Abba Auren nan tamkar kasa hannune da kanka ka rusa doguwar tsaftataciyar katangar rayuwar Yaya Jawwad ne, Abba please kayi bincike"
"karya kikeyi bakar munafuka, ba wani bincike daza'ayi, yarinya 'yar dangice, me tarbiyya da sanin yakamata suna son junansu, Amma dan munafunci shine kike bata mata suna a gurin sirikinta, kedai Azzaluma ce, ni ina kudina ma da Mummy ta bayar akawomin? Ilham tace tabaki amma dan son zuciya baki baniba seda na buga waya aka gayamin ke aka bawa"

Daga Abba har Jalila tsayawa sukayi suna kallon Maama, Jalila takasa gane inda Maama ta dosa
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


*ABDUL JALAL*


_Story and writing_
By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girls_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️


PART 2
_PAGE 3️⃣8️⃣91

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724






_MY FIRST NOVEL _

Abba ransa ya baci dajin kalaman da Maama ke fadi dan haka yace

"zainab meye haka kuma? Kibar ta ta fadi abunda yake bakinta mana, be kamata ki katse mata hanzari kidinga jifanta da wannan muna nan kalaman ba akanme? Na dade ina tunanin Jalila bata jin dadin zaman gidan nan, Allah ka dai yasan mekike mata inba na nan, nayi shiru ne dan bata taba gayamin wani abu akan irin zaman da take ba, kallonki kawai nakeyi zainab "
Se yanzu Maama ta shiga hayyacinta take tuna maganganun data fada idonta ya rufe ta manta shaf agaban Abba tayi su, cikin kokarin kare kai tace
" kayi hakuri Abban Jawwad, raina ne ya baci, iya sanina Naja batada wani aibu amma Jalila se kokarin kushe Auren take, kuma da ina cuzguna mata aida zata gaya maka tunda kasan bakinta baya shiru"

Jalila kallon Maama kawai take, Abba yayi tsaki yace "Inajinki Jalila cigaba da maganar ki"
Jalila tace
"A'a Abba base muncigaba ba, Amma Maama ni Ilham bata bani kudinki ba, tsawon zamana a gidan nan ban taba daukan cokali da sunan ha'inci ba, kina aikena gurare da dama da kudi, har banki kike turani da ATM card dinki ban taba batar miki da ko kwabo ba abaya, wallahi ni Ilham bata bani kudi ba"

Yadda Jalila take maganar kasan zuciyarta a cunkushe take da bacin rai, dan har idonta yatara Hawaye, Maama kuwa fakar idon Abba tayi ta watsawa Jalila wani kafirin Kallo.
Abba yace
"ke Zainab kikoma can kuyi maganar kudinku, ni 'yata bata sata, bata ha' inci na yadda da ita, Jalila tashi kije Allah yayi miki Albarka, karki sake ki zubar da hawayenki a banza"
Jalila jinjina masa kai kawai tayi ta mike, tana fitowa taji hawaye nabin fuskarta wani bayan wani, koda Jalila ta koma daki Nana tana bacci dan haka ta samu guri ta takure ta fashe da kuka, hada sheshsheka tana kuka tana surutai
"Ummi kingani ko? Da tun farko kin tafi dani da kome zefaru tare ze samemu amma kinmin Nisa, kin barni inata fama da wahalar Rayuwa, banida matemaki se Allah"
cikin bacci Nana taji kukan Jalila, koda ta bude idonta Jalila ce ke faman sharbar kuka, da sauri ta sakko daga kan gadon tazo gabanta tareda fadin
"Jalila lafiyarki kuwa? Gayamin me yasamiki?"
Shiru Jalila tayi se kuka data cigaba, duk yadda Nana tayi Jalila taki gayamata me yafaru, Nana ta rumgumeta tana fadin
"tunda bazaki gayamin ba bazan takuramiki ba, Amma dan Allah kidena kukan nan, Jalila banajin dadin ganin kina kuka haka dan Allah kidena in bahakaba nima zaki sani kukan"
Jinjina mata kai kawai Jalila tayi, ta zame ta kwanta akan cinyar Nana, ta juyarda kanta hawaye na cigaba da zuba.
Da Naja ta dawo gidan seda Maama tagaya mata abunda ta tarar da Jalila tana gayawa Abba, Naja ta dinga masifa taana zataga bayan Jalila, setasa ta bar gidan da kafarta, tunda ita mayyace, Maama ta gaya mata wai Jalila ta cinye mata kudi dubu tamanin Abba yace karta kuma daga maganar shi yasan Jalila bazatayi haka ba, suka kuma haduwa sukasa Jalila a gaba da gori, Maama ta hade kai da Naja suka cigaba daYiwa Jalila barin miyagun maganganu, Amma sam Nana bata san meyake wakana ba, zuwa makaranta ne kawai kesa Jalila samun raguwar pressure dake kanta, shima yanzu makarantar idan taje kuka takeyi bata jin lectures din. Jalila batayi mamakin abunda Ilham tayi mata ba dukda abun yamata ciwo, Amma a yanzu ita ba wannan ne ya dameta ba, maganar Auren nan ce yake damunta.

Wasa2 Jawwad yayi rama ta ban mamaki, yana cikin tashin hankali an saka biki a kusa watanni shida, ko Abinci baya iya ci, nutsuwarsa daya idan yana waya da Hanan, kokuma Idan Jalila tana masa nasiha da bashi kwarin gwiwa, ko Abinci baya iyaci, duk haskensa seda yayi duhu, Jalila tarasa ta ina zata fara shawo kan matsalolin nan.
Yanzuma gurin Jawwad ta tafi don ba karamin tausayi yake bata ba, taje ta kaimasa Abincin rana, ta tarar ya idar da salla ta jira Jawwad yayi Addu'oin sa ya shafa, sannan tace
"Yaya Jawwad nasan kana cikin damuwa, amma kadinga kokarin kwantar da hankalin ka, ina nan inata kokari sannan ina Addu'a Allah ze kawo mafita"

Murmushin yake yayi wanda yafi kuka ciwo yace "ina Addu'a baby, ina fatan Allah yabani ikon cin Jarrabawa"
"Insha Allah komai ze wuce sannan nace ya batun zuwan ku kaduna kuwa? Bana son plan dina ya tafi a banza"

"Ina sane Jalila, zamuje Insha Allah, kafin lokaci ya kure"
"to shikenan, amma ka dena wannan damuwar kaji Yayana?"
"Na dena babyn Ummi"
Murmushi tayi masa
"yawwa haka nakeson ji, bari in dawo in gyara maka dakin nan, naga yayi kura"
"to shikenan Autar Ummi nagode sosai, Allah ya sanyawa Rayuwar ki Albarka, Yadda kike kokarin faranta min Allah yabaki mijin daze kula dake ya soki ya rikemin ke Amana, a lokuta da dama kina sadaukar da farincikinki dan ganin wasu sun samu nasu farincikin, Allah yabaki wanda ze kulada ke, yabaki mijin marainiya, wanda ze kula dake da maraicinki"
Taji dadin Addu'ar yayan nata, Amma takasa cewa Ameen sema Hawaye daya taho mata.
Tagama abunda take a cikin gida, taje domin gyara bangaren Jawwad, Jalal na kalmashe akan kujera yana game a system, sukaci Abinci shida Jawwad, yacigaba da game dinsa, tunda ta shigo ba wanda ya kula wani tsakanin ta da Jalal, Maama takira Jawwad a waya tace yaje cikin gida tana son ganinsa, jiki ba kwari ya tashi ya tafi, dan yasan be wuce akan maganar Naja ba.
Jalila tasan babu alamun Jalal yayi sallar Azahar, ta duba taga system din a jikin caji take yake amfani da ita, tasa hannu ta kashe main socket na dakin, system ta dauke dama babu caji, kallonta yayi a fusace ze masifa amma yakasa, ganin irin kallom da take masa,
"Kayi sallar Azahar kuwa?"
"ban Sani ba, ko innayi ke zanyiwa?"
"Subhanallah karkayi sabo, ai ba fada bane, Salla fa, haske me girma ga tarin lada ga ma'abota yinta akan lokaci, kaga da kana bata mahimmanci sosai da yanzu Rayuwarka ta canza, da abubuwa dayawa kadaina aikata su, karfe uku ta wuce amma bakayi salla ba, wanda ya mutu baya salla kasan makomarsa wuta ce ta saqara, wadda ake sa wanda basa salla, Ai baka son shiga wuta ko dan gidan daddy? Ta tambayeshi kaman tana magana da yaro karami"
Be Amsa ba se kallon ta dayake, tasa hannu ta janye system din
"Yawwa abokin Yaya, kayi yaki da shedan, ka yaki zuciyarka ka daure, kaga in kayi sallah sekayi Addu'a, Allah na karbar addu'a bayan sallar farilla, kaje kayi salla"
Mikewa yayi ya nufi bedroom din Jawwad ba tareda yace mata kala ba yaje yayo Alwala, yana shiga tayi Ajiyar zuciya mutum kaman wani dan karamin yaro, komai se an lallabashi Allah ya shirye ka, yanzu tagama gane halinsa, ba yasan fada ne sam, indai zaka gaya masa magana da fada, to zakuiyi fada dashi. Jalila tanata goge2 ta kunna TV takai sunna tv ana karatun Al'qur'ani, tana aikinta tanayi, sosai takejin dadin karatun suratul Yusuf, dauke wuta akayi dan haka tv ma ta dauke, ta danyi shiru, kawai taji an dora daga inda ta tsaya, waigawa tayi ta ga Jalal yana karasa mata ayar, ya iya karatun qur'ani, bata manta randa ya kaita makaranta ba ranar data fara jin yana karatu, Murmushi tayi tace
"cigaba mana"
"A'a kedai kicigaba, na manta Aya tagaba, bana tilawa, bana tuna haddata duk na manta, kwakwalwar ta toshe"
"Ahh waika manta, ba wani kamanta"
"Am serious na manta, cigaba maybe inkin cigaba in tuna"
Ba musu kuwa ta dora, tana cikinyi setaji yakama yanayi,
"Amma kace ka manta? Dama ka iya karanta Al'qur'ani haka, inama kana yawanyi da ko a hanya kaga giya zaka dauke kanka ne, waye ya koya maka karatu haka?"
"A islamiyya sannan kuma Ummi, bazan manta ba"

Maama ta cazawa Jawwad kai akan Naja, yana zuwa dakin ta shiga yi masa fada "Wallahi Jawwad ka kiyayeni tun ban bata maka rai ba, shine ka hada kai da wannan makirar yarinyar take kokarin ziga mahaifinka akan Auren nan ko? To wallahi ka kiyayeni akan Auren nan zan iya cimaka mutunci, kuma in har muna raye baka isa ka kuskurewa Auren nan ba, indai zanyiwa yayata biyayya kai waye da bazaka yimin ba? "
Sunkuyar da kai Jawwad yayi yace" kiyi hakuri Maama, niba ina kokarin kuskurewa Auren nan bane, kiyi hakuri dan Allah "
"ni rufemin baki, se anyi magana kadinga wani ayi hakuri, Naja tagayamin wulakancin dakake mata, ka fifita waccan yarinyar akanta shima ka kiyayeni Aure zakuyi da Naja, dole ka dinga janta a jiki ku fuskanci juna"
"to Maama yadda kikeso haka za'ayi insha Allah" duk abun nan Naja na gefe a zaune tana tauna chewing gum, tana hararsa, da Nana tana dakin Maama itama, amma bacin rai yasa tabar dakin.
Har Jawwad ya yunkura ze fita yabar dakin, Naja tayi karaf tace "Yaya Jawwad dan Allah zan shirya zaka kaini anguwa" shiru yayi bece komai ba, Maama tace "kobazaka kaita bane?"
"zan kaita bari inyi sallar la'asar"
Haka ya taho ransa babu dadi, yarasa me yake masa dadi, gaba daya Maama ta canza yaya mairo kullum cikin zigata take kansa har wani sarawa yake yi, ya nufi dakinsa amma yana zuwa dakinsa abunda ya tarar ya bashi mamaki, kunnuwansa suna jiye masa kira'ar Jalal, yana karanta qur'ani , wanda rabonda Jalal ya karanta Al'qur'ani baze iya tunawa ba, to mutumin dabe damu da salla ba, ina zeyi karanta alqur'ani.
Jalal yana cikin biyawa ya kakare, Jawwad yakarasa masa, tuni Jawwad ya manta da bacin ran dayake yi yace "Jalal yau kaike karatu haka? Amma naji dadi, yaushe rabo"
"kanwarka ke kokarin ta kureni, nace mata na manta tace senayi shine nake tunowa naji ashe da saura, haddar bata gama zubewa ba"
Jalila tace "niba kureka nake ba, aiba takura maka nayiba"
Jawwad yace "Baby kinga Jalal, wallahi ba karamin kwarone ba da muna yara, kwakwalwar sa tana kawo wuta, duk lesson din daza'ayi a kansa yake daukewa, gaskiya yau kinciri tuta baby, yanzu dai mu cigaba da tilawar nima ayi dani"
Murmushi Jalila tayi, Jalal yabata mamaki yau sosai, da Jalal yacigaba da karatu da al'umma zasu amfana yanada kwakwalwa sosai, Jalila tace "to kucigaba ni zanyi Alkalanci"

dariya Jalal yayi wadda take masa kyau dan be fiyeyiba yace "Jawwad kai zaka fara, nifa babu haddar ta zube, shekaru Ashirin baya da yin haddar kuma kaga bayi nake ba"
Jawwad yace "hakan ma ka yi kokari fa, amma dan cigaba zan na tuna maka, nayi missing din karatun ka" murmushi Jalal yayi, yafara kokarin dorawa, yana cikinyi ne kawai yafara tari, jikinsa yana rawa, Jawwad yace "lafiya meyafaru Jalal?"
Tari sosai Jalila ta dakko ruwa Jawwad ya karba yana kokarin bashi amma yasa hannu ya make ruwan, ya fadi kasa, nan take idonsa yafara juyewa jijiyoyin kansa dana fuskarsa suka mimmike, nan take fuskarsa tayi murtuk yakoma Jalal dinsa na ainihi dan shaye2 wannan murmushin da Annurin na fuskarsa ya dauke gaba daya, tashi yayi daga kan kujerar dayake yakoma kan doguwar kujera ya kwanta ya rufe idonsa.
Jalila tace
"Yaya Jawwad meyasameshi kuma?"
Ajiyar zuciya yayi yace "Jalila haka yakeyi wani lokacin, ko yana cikin nishadi inka fara masa nasiha gaba daya jikinsa ze hau rawa, ya canza Amma ze ware Insha Allah"
Jinjina kai tayi takarasa aikinta tana mamaki sannan ta fice.
Jawwad yayi mamakin yaushe suka shirya haka har take sashi abu yayi, Amma da ya tuna kokarin da Jalila ke tayi akan Jalal, da kuma Alkawarin data taba yi masa akan zata taya shi addu'a da kokarin ganin Jalal ya shiryu, murmushi yayi yace "lallai baby kinada sa'a mace ta farko daya ji maganar ta tun bayan lalacewarsa"
Jawwad sam ya manta da batun wata Naja, seda Maama ta kirashi a waya, haka ya tashi ransa ba dadi ya dakko key din motarsa ya fito.
Shigar data saba yice yauma tayi, jikin nan duk a matse se wani dan ficicin gyale, ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga gaba daya motar ta bule da kamshin turarenta dayake hawa ka, ya kunna motar yace "Ina zaki?"
"Shopping zaka kaini zan sayi kayan kwalliya"
Bekuma ce mata komaiba ya kunna motar yaja, ya kaita kofar wani store ya ajiyeta, ta kalleshi "to muje mana"
"Ba inda zani, in bazakiba inada abun yi" yafada a hasale
Tsaki tayi ta bude motar ta fita, tana fita ya kashingida ya kira Hanan, seda ta kusa katsewa ta daga cikin muryarta na shagwababbu tace "My Haidar am sorry bana kusada wayarne" murmushi yayi yace
"gaskiya ban hakura ba, seda ta kusa katsewa za'a daga wayar"
"ni gaskiya kayi hakuri ko inyi kuka"
"No don't cry, Ya kike?"
"Lafiya kalau sedai ina missing dinka"
"Insha Allah zan shigo Kaduna next week zanzo in ganki, na kusa tafiya lagos Daddy ya samo min Aiki a can"
"masha Allah can't wait to see you my dear, wallahi naji dadi Haidar, Allah ya kawomin kai lafiya, ina yayana kuma sirikina?"
"Wake nan?" ya tambayeta
"Yaya Jalal mana"
"Eh ina sa ran tare zamuzo dashi, Amma yaushe yazama sirikinki?"
"Yacemin yabani kai yazama sirikina, nikuma zan masa tukuici da Jalila dan ita zan bashi shine tukuicin dazan bashi" dariya Jawwad yayi yace
"ba ruwana kunfi kusa keda su"
Sosai ya manta da batun Naja, yaketa murmushi, Kuruciyar Hanan tana birge shi, yanzu duk wata kunya ya ajiyeta, She's so kind
Har Naja ta dawo motar wayarsa yakeyi da Hanan.
Naja ta fusata matuka a hargitse tace "wannan wane irin rashin mutunci ne? An samana rana Amma kana waya da wata wannan ai wulakanci ne kuma a gabana"
Karaf a kunnen Hanan, Jawwad kashe wayar yayi dan yasan yanzu kome zece Hanan bazata saurareshi ba yanzu, dan taanada matukar kishi, ya kalli Naja yace
"Ke zabin Maama ce" wannan kuma zabina ce, dan haka ki kylaeni"
"ni kake gayawa haka ko? Wallahi zakaga rashin mutunci, kuma ko bakaso seka Aureni, kacigaba da yimin wulakanci, nikuma zancigaba da hadaka da mahaifiyarka"
Bece mata komaiba ya kunna motar yatafi, shi gaba daya hankalinsa da tunanin sa yana kan yaze shawo kan Hanan.
Suna zuwa gida yafita ya barwa Naja motar, daya koma daki ya tarar Jalal ya tashi, yazo ya zauna kusada shi yace "Sannu ka tashi kenan?" Jalal ya jinjina masa kai
Jawwad yace "Jalal dan Allah sati me zuwa, inaso inje kaduna" murmushi Jalal yayi yace "Zakaje gurin Hanan kenan?"
"Eh amma tare zamuje da kai, zaka rakani"
"meyasa sena raka ka?"
"kaima naka zuwan yanada mahimmanci, dan Allah ka rakani"
"to naji, amma senayi shawara"
Jawwad yace "ba wata shawara da zakayi, Akwai damuwa ne?"
Jalal yace "damuwar menen?"
Nan yagayawa Jalal yadda sukayi da Naja, har Hanan taji, Jalal yace "tun farko bekamata ka boye mata halinda ake ciki ba, Amma yanzu ka kira kanwarka ka gayamata, tafara yimata bayani kafin kaje kaduna" Jawwad yace "Hakama za'ayi ka kawo shawara, kai Amma Inajin kunyar Jalila sosai"
"meye kuma Abun jin kunyar? Kirata ni zan gaya mata" ba musu ya kira Jalila a waya yace tazo farfajiya yana kiranta.
Befi 3 minutes ba sega Jalila tazo, Hannunta dauke da wani karamin teddy da kuma wayarta, bakinta kuma dauke da alawa me tsinke, Jalal kura mata ido yayi aransa yake zancen zuci in be manta ba, saura watanni shida Jalila tacika shekaru gome sha tara Amma har yanzu bata dena halin yarinta, kana kallon ffuskarta zaka san yarinyace, sedai Kwakwalwarta ba kowane babbane ze iya lissafin da kwakwalwarta takeba tasamesu akan fararen kujeru a harabar gidan, tayi mamakin ganin Jalal kaman bashine dazu ya canza gaba dayaba.
Taja kujera ta zauna tace "gani Allah yasa ba lefi nayi ba?"
Jalal yace "ke tunda kin saba lefi, duk lokacin da aka kiraki bakya kawo komai a ranki se laefi kikayi, kodayake ke ai aikata laifi a jininki yake"
Bakinta yayi jawur saboda Alawar datake sha, kallonsa tayi ta harareshi ta dan murguda baki tace "Eh tunda kullum 'yan sanda sesunzo sun tafi daniba, aidole kace laifi a jinina yake"
Yadda bakinta yayi jawur din nan tana juyashi ba karamin birge Jalal yayi ba, Jawwad yayi murmushi yace "Allah yabaku hakuri, dazu gwanin sha' awa naji dadin yadda naganku, Amma yanzu kuma zakuyi fada"
Jalila cikin shagwaba tace "toba shine yace ina laifi ba"
"to kice ba kyayi mana? Shekarun baya ina seda kikasa Abba zuwa kaduna kin tabo 'yar gidan masu bullet"
gaba daya sukayi dariya, saboda Jalal da sigar tsokana yayi maganar" gaba daya Jalila mamakin Jalal takeyi, ya iya barkwanci da tsokana, Amma inbaka zauna dashiba bazaka gane hakan ba, kuma abun mamaki lokaci daya seya birkice yakoma Jalal dinsa mashayin giya.
Jawwad yace "Baby wani taimako nakeson kiyimin"
Ta gyara zama takara rungume teddy tace "with due respect, ina jinka babban yaya"
Ya yunkura zeyi magana suka jiyo hayagagar Maama ta nufosu itada Naja,
"saboda ka cimin mutunci kake gayawa Naja wai baka sonta kanada wadda kakeso, Jawwad yaushe kakoma haka? Yaushe kafara bijirewa umarnina? Ya koyamaka ko? Zama da Jalal yasa kafara bijiremin, har kake waya da wannan shedaniyar yarinyar a gabanta, na samaka ido tsakanin ku kar mahaifinka yakawo wani abu aransa amma duk baka ganiba ko? "
Jawwad yace" Maama nifa bahaka mukayi da itaba, kuma ba ruwan Jalila bada ita nake waya ba, na gayamata ita zabinkice, nima inada zabina"
Tas Maama ta dauke shi da mari, gaba daya sukayi tsit dan ba karamin mamaki abun yabasu ba,
Shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai ko tari beyiba, cigaba tayi da zazzga masa masifa Jalila tace
"haba Maama, biyayyar da Yaya Jawwad yake miki in baki gode masa ba bekamata ki zageshi ba, kuma da ze canza hali da ya dade da canzawa dan Allah karki kuma dukansa"
"rufemin baki kasurgumar munafuka kawai, bake kike zigashi ya bijirewa umarnina ba, jarababbiya wallahi zanyi maganinki, kuma baki isa ki hana Auren nan ba, jarababbiyar banza"
"Kuma makira barauniya ba, mara usuli gata barauniya abun kunya itace ke kokarin kusheni wai kar a Aureni, ai garani da dangina uwa da uba,

Please Login or Register in order to submit comment