Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kansa a jikin ta yace "Naikaina na san Jalal yana sonta sosai, daga baya na yadda da maganar ki soyayyar 'yan uwatanka ne tsakanina da ita, hankalinta akan rayuwar Jalal take, a tunanin ta tausayinsa take ji, amma da haka sonshi yayi mata illa bata sani ba, kaman yadda ban fargaba naki son yakusa karasani"
Ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata
"I Love you my Hanan"
Makalkale shi tayi tace "I love you too Haidar"
Daga nan hirar kuma ta canza salo zuwa wani abu na daban, tun Hanan tana daurewa tana biye masa, taji abun ya wuce tunanin ta, ta fara neman taimako, 'yan gidan su ba wanda be sha kira ba dama an hadu da uwar shagwaba, A wanna daren Jawwad ya saukewa Hanan wannan rawan kan nata.
(nima me rahoto naga abun yafi karfina dan haka na dawo da baya, na fito πŸ˜œπŸ˜œπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚)



Gaba daya Nana ta takurawa Jalila da waya, har sha biyun dare tana manne a waya seka ce wata mara aikinyi, haushi duk ya ishi Jalila tana ganin ta fiye zakewa, ji ta ke kaman suna karama ta takaicin da take ciki, ta ja bargo ta rufe har kanta dan ta dena jin abunda Nana take fada.



Washegari tunda safe Su Nana suka fara haramar tafiya.
Wayar Nana Jalila ta karba sukayi waya da Maama, har daki aka kawowa su Jalila breakfast, Nana kanta ba ta sake taci ba, saboda gaba daya ji take ba dadi, zata daga tabar kasarta ta haihuwa Aure kenan.
Karfe sha dayan safe su Nana suka gama shirinsu, suka shirya domin tafiya airport, nan ma seda aka sha daru Da Jalila saboda kuka, haka sukayi Sallama Nana da Mahmud suka tafi.
Hajiya Salma bata bisu ba ita seda ga baya zata koma.
Bayan tafiyar Nana Jalila dakin ta koma ta kwanta gaba daya ji take duniyar tayi mata fadi, ba abokin hira an kawota inda ba wanda ta sani. Ta lura nan gidan Antyn Jalal ne, tana da yara 'yan mata guda biyu, daya zata girmi Jalila, Husnah da Amal, Amma sam basa san mutane basa shiga harkar mutane, dan haka ko sannu bata hadasu da Jalila, sedai sukan gaishe ta.

Hajiya Salma ta shigo ta samu Jalila a kwance tace "Jalila har yanzu jikin ne?"
Jalila tace "A' a naji sauki kaina ne kawai be dena ciwon ba"
"ko dai likita za'a kira"
"A'a Anty naji sauki"
"to shikenan, Amma Jalila ki kwantar da hankalinki, ki cire duk wata damuwa a ranki, Kicigaba da raguwarki kaman yadda kike yi a da kinji"
Jinjina mata kai kawai Jalila tayi.

Koda Hajiya Salma ta fita dakin da Jalal yake taje, yana zaune yana kallon labarai a tashar CNN.
"Sannu Jalal kana nan kana kallo, kai ko tambaya matarka bakayi, ka sameta a sauki, dan haka baka damu da ita ba ko?"
"to me zance? Kokuma me zanyi? Nima ai bata nemana"
"Au hakama zakace ai shikenan, yaushe zaka koma?"
"gobe insha Allah"
"zakaje kano ne kokuwa?"
Jalal ya dan yamutsa fuska yace "daga nan gurin aiki zan koma, bazanje Mummy ta hargitsa min kai ba, lagos zan wuce"
"Shikenan Allah ya kaimu goben" Jalal yace "Ameen Amma, se yaushe Zaku bani ita mu koma kano"?
Hajiya Salma tace

"ita wa kenan?"

"Matata mana" ya bata amsa
Hajiya Salma tace "au ashe matarka ce, baka da kunya Jalal, se lokacin dana shirya yayi tukuna, ashe dai ka damu da ita"
Dan dage kafada yayi irin i don't care din nan.
Jalal idan ya tuna yadda Jalila ta ce bata sonsa a gaban kowa da kowa, yana tunanin wani irin zaman Aure zasuyi? Tsawon lokacin nan dama bata taba sonsa ba kenan? To meze sa ya cigaba da bibiyar ta tunda tace bata sonsa.



Bayan Hanan tayi sallar Asuba komawa tayi kan gado, wani wahalallen bacci ya kuma dauketa. Koda Jawwad ya dawo ya tarar ta koma bacci, ya hau kan gadon ya ďan tsira mata ido, baccin ta take hankali kwance, tuno darun da tayi jiya yayi, ya danyi murmushi ya janyo ta jikinsa ya kwanta shima baccin ya dauke shi.

Wajen karfe tara Jawwad ya tashi, Amma Hanan bata farka ba, ya je ya dafa musu tea ya fita, ya fita ba dadewa Hanan ta tashi daga baccin, taje tai brush tai wanka ta saka wata doguwar riga mara nauyi, ta fito parlour amma bata ga Jawwad ba, ta nemi guri ta zauna a kan kujera, befi mintuna goma da fitowarta ba se gashi ya dawo hannunsa dauke da kaya, yayi sallama ta juyo ta amsa suna hada ido ya kashe mata ido, hakan yasata sunkuyar da kai tana murmushi, ya karaso ya ajiye kayan yace
"good morning dear, kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau, kaima ka tashi lafiya?" tai maganar tana kokarin kaucewa hada ido da shi
"lafiya kalau na tashi lafiya, How was your night?" ya kuma jefo mata tambayar.
Pillow ta dauka ta rufe fuska tana murmushi haka Jawwad ya cigaba tsokanarta yana bata kunya.

Ya dakko cups yana kokarin hada musu tea tace "Haidar waye ya dafa tea din nan?"
"ni na dafa" ya bata amsa
"Allah yasa dai baka bari yayi kanzo ba, dan na san baka iya girki ba"
Dariya ta bashi sosai
"Ai nafi ki iya girki in gaya miki, zaki kuma gani"
"to ai shikenan hada min yunwa nakeji"
"Ai wannan tea din nawane ni kadai, bazaki sha ba ke kazarki zaki warming a oven ki cinye"
Zare ido tayi tace

"gaskiya bazan ciba na koshi"
Jawwad yayi dariya yace
"se kin cinye ta kuwa"
"aikuwa bazan ci ba, tsaya in baka a baki" ta dinga bawa Jawwad Abinci a baka, yana bata haka sukayi breakfast cike da kulawa da kaunar juna.




Wunin ranar yau Jalila ji tayi duniyar ta kara mata fadi, ga har yanzu Bata kuma sa Jalal a idonta ba balle ta sa ran karbar wayarta.
Bangaren Jalila ma tunanin ta yaza'ayi tayi zaman Aure da Jalal be damu da kansa ba balle ita, tana ganin shima an cusa masa ita ne kawai baya sonta, banda haka kwanan su nawa da zuwa be nemeta ba ga rashin lafiya tanayi amma ko keyarsa bata gani ba balle tasa ran ze mata sannu.



Ko parlour bata fita tana ďaki, Hajiya Salma da Antyn Jalal suna monitoring din Jalal da Jalila domin ganin actions dinsu, Amma abun mamaki kowannensu yana nuna be damu da ďan uwansa ba, tunda sukazo kwana uku ba wanda ya nemi wani a cikinsu.


Antyn Jalal tana zaune suna hira a parlour su Husnah suna cin Abinci Jalal ya shigo, su Amal suka gaisheshi a ciki ya amsa, dan sun fidda ran ze amsa musu, suka cigaba da cin Abincin su.
Anty tace "Jalal ina zuwa haka?"
"Zan koma lagos ne"
Anty sukayi ido hudu da Hajiya Salma.
Hajiya Salma tace "to wannaan tafiya haka kaman wanda ake kora? Ka gayawa matarka yau zaka koma?"
Cikin ko in kula yace "in kun ganta ku gaya mata"
Anty tace "dan kaniyarka mu zamu gaya mata ka tafi, Anya Jalal ka shirya rike yarinyar nan?"
A ransa yace "ita zaku tambaya in ta shirya zaman Aure dani?"

Hajiya Salma tace "nima dai haka nagani, tunda muka taho bata da lafiya, Amma yaron na ko ta kanta bebi ba, balle in sa ran ya duba ta, ya mata sannu" da sauri yace "bata da lafiya kuma? Me yasa me ta?"
Hajiya Salma tace "ban sani ba" mikewa yayi ya kalli Husna yace
"ina ne dakinta"?
"tana upstairs kusa da ďakina" ta bashi amsa, be kuma bi takansu Anty ba ya haura saman.
Kai tsaye ya bude dakin ya shiga, ya sameta ta dukunkune a cikin bargo, a hankali ya karasa gaban gadon nata ya kai hannu ya janye bargon.

Wata sleeping dress a jikinta blue me matukar kyau, kanta babu dan kwali, dukda tayi parking din gashin nata amma gashin ya hargitse, bacci takeyi sosai, Amma tayi rama a baccin ma se ajiyar zuciya take.

Ya kura mata ido fatarta se sheki take, a hankali ta motsa ta mike hannyen ta wajen kirjinsa, hannayenta sun sha ado da jan lalle, hannunsa yasa a nataa ya rike yana kuma kallon fuskarta, bacci take amma tayi kyau sosai. Ya bata lokaci sosai yana kallon ta. A hankali ya saki hannunta
Ya dakko wata 'yar takarda a Aljihinsa da biro yayi rubutu ya ajiye mata akar kashin pillow dinta, ya mayar mata da hannun ta kan gado ya lullube ta ya fice.
Koda ya sakko bekuma ce musu uffan ba yayi waje abunsa.

Anty tace "kinga danki ko?"
Hajiya Salma tace "ai bari kawai, Jalal Akwai taurin kai, suna son juna amma taurin kai neke damun su, se nunawa suke kaman basu damu da juna ba, Allah shi yabarwa kansa sanin dalilin dayasa ya hadasu, Amma wannan zaman Auren nasu da kallo"

"hakane amma zamu cigaba da yi musu Addu'a, zasu dai daita, bari kiga sukoma gidansu da zama, bazaki sake jin kansu ba"

"hakane Allah ya tabattar da alkhairi, Amma bazata koma kano yanzu ba, sonake hankalin ta ya kwanta ta sake nustuwa, daga nan ma waccan jarababbiyar watakila ta sakko"

Anty tace "tab haba sister Salma, kin manta wacece khadija kenan, ai babu batun ta sakko yanzu, kawai dai mu tayasu da Addu'a" haka suka cigaba da hirarakin su.

Koda Jalila ta tashi ji tayi gaba daya dakin ya gauraye da kamshin Jalal, dan tabe baki tayi ta shiga toilet tayi wanka ta sa kaya, tazo tana kokarin gyara gadon tana cire bedsheet din taga takadda ta fado, ta dauka ta bude, wani tsararren handwriting tagani a jiki.

Am going back to lagos, get well soon
ABDUL JALAL se signing dinsa da date

Juya takaddar tayi ta jefar da ita a gurin tayi tsaki, "kwana nawa bani da lafiya, tunda aka daura auren ko ta kaina bebi ba, se yanzu ze wani rubuta min wata banzar takadda, ya tafi abunda yafi lagos ma ni be shafe ni ba, kuma maimakon ya ajiyemin wayata amma yakuma tafiya da ita sekace tasa.
Haka Jalila ta cigaba da mita, har ta gama gyaran gadon.

Parlour ta fito dan ta gaji da zaman dakin ga shi ba waya a hannunta balle ta debe mata kewa.
Anty na ganin Jalila tayi murmushi tace "Jalila kin fito? Ya jikin naki kuwa?"
"naji sauki Anty"
"to Allah yakara sauki, dazu Mijinki ya shiga dubaki ai"
Dan tabe baki Jalila tayi tai shiru.
Tundaga Ranar kullum cikin turara Jalila suke da samfurin turaruka daban2, a rana se ayiwa kayan sawa turare kusan sau hudu, banda wanda ake tuarar mata jikinta, hatta ruwan wankan Jalila akwai turaren da'ake zubawa, sabulun wankan ta ma na musamman ne aka hada mata, ga mayukan shafawa dana kai, nan da nan Jalila jikin Jalila yara canzawa, duk inda ta gifta kamshi take, duk rashin son kitson Jalila wani na tsufa me kitso take zuwa tayi mata wani, hakama lalle, gaba ďaya wannan gidan sun maida Amfani da turaruka kamar ibada, babu wani aiki da takeyi sedai taci ta kwanta, ko ta yunkura zatayi aiki se a hanata, ga kyan gyra da'ake bata dan haka har wani kiba tayi abunta tai kalau da ita. Jalila idan tana son yin waya sedai ta ari ta Anty tayi, ta mata magana akan wayarta tace tabari Jalal yazo.
Tunda Jalal yazo ko a waya be kuma neman inda Jalila take ba itama ba ta nemi jin inda yake ba.



Mummy ta cigaba da tayarwa da Daddy hankali akan maganar Auren Jalal, amma sam yaki saurararta, ya tattara ya koma Dubai, duk abun nan da ake Ilham bata sani ba.

Daddare Ilham na kwance tana chatting, ta shiga Twitter kamar wadda aka saka ta shiga profile din Jalal Alhamdilillah got married to Jalila Aliyu Imam shine abunda Ilham ta gani zumbur ta tashi Zaune tana kuma mutsukke ido, Amma still taga ba mafarki take ba.
Da sauri ta kira layin Nana, Amma bata shiga, se lokacin ta tuna ai Nana Mahmud ta aura, a England zasu zauna.
Fitowa tayi da sauri ta tafi ďakin Mummy tana kwala mata kira
"ke lafiya kuwa kike min wannan kiram, meya faru ne?"
Nunawa Mummy wayar tayi, mummy tace "me zan gani?"
"Mummy wai dagaske ne Jalal yayi Aure"
Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "tun satin da Daddy yaje daurin auren Jawwad, ya hada baki da 'yan uwansa suka masa Aure, nayi2 ya gayamin wacece yaki"
Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Mummy kin san wacece kuwa? Jalila ce fa, kalli Abunda ya rubuta ita ya aura Mummy, na shiga uku, Mummy ki kashe Auren nan kafin sun tare, Wallahi idan suka tare na kade, zan rasa komai, komai nawa ya rushe"
Gaba ďaya Mummy tsayawa tayi tana kallon Ilham
"dolene in kashe Auren nan, baze yuwu ba, wallahi ko yana so koba ya so sena kashe auren nan, ni Hajiya zainab zata munafunta, a hada kai da ita a Aurawa ďana wannan makirar yarinyar, in abun gaskiyane ta aurawa nata ďan mana, indai nina haifi Jalal seya saketa, a ďaura masa Aure ko ya nemi inda nake, rabona da shi wata biyar kenan, baze yuwu ba wallahi"








Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣1️⃣ 104

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Tunda aka gama biki Maama bata dawo ba, seda takuma kwana goma a Bauchi, taji dadin zaman garin sosai, gashi mutane ne masu karamci da son 'yan uwa, Abba ne yazo ya dauketa suka koma gida kanon dabo.

Bangaren Angwaye da Amare da sukayi Auren soyayya Se shan soyayya da kauna suke, tsakanin su banda Jalila da Jalal da babu wanda yake neman wani a tsakanin su,
Jalila ita wannan zaman hutun ya isheta, ita dama kano suka batta tayi zamanta a gurin Maama ya fiye mata wanna zaman.
Tana ta zancen zuci ne Husna 'yar gidan Anty ta shigo da waya ta mikowa Jalila, Jalila tasa hannu ta karba, video Call ne ta ďaga wayar tana ďagawa taga fuskar Jawwad cikin sauri ta mike zaune

"Yaya Jawwad kaine?"

"Nine Baby, yaya borno yasu Anty?"

"lafiya kalau Yaya Jawwad, kayi kiba sosai kaman ba kaiba, ina Hanan?"

"tana kitchen tana girki, kema gaki nan kinyi kibar ai, ya mijin naki?"

Tabe baki Jalila tayi tace "yana can lagos" Hanan ce ta taho da gudu ta haye kan cinyar Jawwad tace

"Hi queen, ya kike?"
"Wow Hanan, wannan kwalliya haka, masha Allah, naji dadin ganinku wallahi nayi farinciki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku, yara muku kaunar juna"

Tausayinta yakama su Jawwad, Hanan tace "Jalila kunyi waya da Nana kuwa?"
"Eh munyi waya da su, ya Abuja ya zaman kadaici?"
Jawwad yace

"muba ma zaman kadaici ko My sugar, masu zaman kadaici suna Azabtar da zukatansu sun san kansu" yai maganar yana kallon Hanan, Hanan tace "Sosai makuwa, ba wani kadaici, kullum muna tare, kema kice akaiki gidan mijinki kigani in zakiji wani kadaici"

"Allah ya kiyaye" Jalila ta fada tana harar Hanan. Wayar Jawwad ta fara ringing, Jalal ne yake kiransa, Jawwad yace
"Baby mijinki ke kirana, bari inje in amsa" Hanan ta zauna akan kujera tace "Jalila wai yaushe zaku sauke wannan taurin kan ke dashi ku fuskanci juna?"

"Hanan ya kikeso inyi ne? Nagaya muku Jalal ba sona yake ba, kawai an lika masa ni ne, tun lokacin biki nake rashin lafiya be nemeni ba, ko ta kaina bayabi, se ranar da ze tafiya ya ajiyemin takadda, sam be damu dani ba, Hanan ku kukayi dacen Auren soyayya amma bani ba, nasan da Ahmad na Aura baze watsi da lamarina ba" kan Jalila ta gama maganar har hawaye ya wanke mata fuska. Cikin taushin murya Hanan tace

"Jalila, kina da Aure yanzu be kamata kidinga ambaton wani namijin ba, Sannan Jalila kinsan halin mijinki tun kafin kuyi Aure, bashida shiga sabagar mutane, dukda ke matarsa ce yanzu, Amma kiyi hakuri, komai ze wuce Jalila, kalli yadda kikayi kyau kamar a saceki a gudu, i wish yana nan yaga wannan kwalliyar taki se ya rude, waima me suke bakine kikayi wannan kyan"

Murmushin takaici Jalila tayi tace

"Hanan kenan, kina tunanin zanyi wani abu daze gani ya yabane? Ko ya burgeshi, shi ba sona yake ba kawai an aura masa ni, be damu da yasan a halin da nake ba balle ya yaba kwalliya ta, se an jima ki gaida Yaya Jawwad.
Jalila ta ajiye wayar ta dora sabon kuka me sauti.
ji tayi an dafata, ta dago ta kalli wanda ya dafata Husna ce fuskarta dauke da damuwa tace

"Sorry dear, please stop crying, kidena kuka ko tunanin broz Jalal baya sonki, is not like that, ina kula da yadda kuke share juna kedashi, which is total bad, an riga an daura Aurenku, kamata yayi ku manta da abunda ya wuce, Jalal has a social disabilities at times, tun lokacin da yakoma drunker, mutane suke kyamarsa he decided to isolate himself from the people, he dint interact with people as before, believe me he loves you bazaki gane hakan ba sekin zauna da shi, yanada kirki sosai, ki dena yawan kukan nan please "

Jinjina mata kai Jalila tayi Husna tace

" Yawwa mrs Jalal, Jalal bashi da matsala bayan ta shaye2, zaki maida shi yadda kikeso, yana sonki ne shiyasa yakeyin abunda kike so, ba dan haka ba a duniya akwai abunda ba wanda ya isa Jalal yayi wani abun yayi. Husnah ta cigaba da rarrashin Jalila, a lokacin take gayawa Jalila Tanada Aure, mijinta baya gari ne, shiyasa itama tazo tayi zamanta a gida.


Ilham takasa zaune takasa tsaye, kwanata kusan shida a gidansu suna sakawa da warwara akan yadda zasu bullowa lamarin ita da umanta, yanzunma zancen da suke kenan

"Umma kin san kashinmu ya bushe idan yarinyar nan ta tare da Jalal, aikin ze lalace ne fa, zamu rasa komai, jiran da mukayi tsawon shekaru mu dauki fansa ze tashi a banza ne, indai yana tareda yarinyar nanmun rasa komai, daular da muke hange bazamu sameta ba"

Umman Ilham taja numfashi ta hura hanci tace
"Bazan taba yadda tsawon wannan lokacin daukar fansa ta ya tsaya akan lalacewar Jalal ba, dole in wulakanta khadija in mallake dukiyar da take takama da ita, sena ga ta wulakanta daga ita har Habib din"

Ilham tace "Umma to tayaya?"

"ki kylaeni kawai, nasan abunda zanyi, tunda ke kinkasa abunda ya kaiki gidan tsawon lokaci"

"Umma kenan, ba kasawa nayi ba, nayi iya yina, ba daban wannan Jalilan ba da tuni an wuce gurin, Amma ni hankalina a tashe yake umma, kin san abunda Aure ga Jalal yake nufi fa a shirin mu, so soyayya da wata mace bayanni ga Jalal kim san barazana ce a garemu, wallahi ko bacci bana iyayi"

"ni nace ki bar komai a hannuna, nasan me zanyi"
"Shikenan Umma"

Mummy har gidansu Jawwad taje da kanta, ta tarar da Maama tana ta fama da aikin gida. Cikin fara'a Maama ta tareta tana mata sannu da zuwa

Aikuwa a fusace mummy tace
"kinga niba yashe bakinki nazo gani ba, ba hakoranki nazo ki nunamin ba, baban su Jawwad na nan ne?

" A'a baya nan lafiya kuwa? "

" ina fa lafiya, saboda tsabar munafunci a haďa kai da ke a cuceni, a Aurawa Jalal wannan yarinyar dake kanki kinsam bata da cikakken Asali, meyasa baki yadda an
An aurawa ďanki ba se nawa ďan, wannan yarinyar mara mutunci akan me? Sumi2 da ita kamar ta Allah amma tana bin ďana"

Maama tace

"Subhanallah ni kaina ban san da batun ďaurin aurensu ba se ana i gobe ďaurin Aure, kuma iyayensu mazane suka yanke wannan hukuncin baniba, da amincewar mahaifinsa aka aura masa ita"

"ke kikasani koma suwaye suka amince, saboda tayi kwantai tarasa miji se abawa ďana, Allah kadai yasan abunda aka dukunkune aka bashi"

"Mummy Jalila ba kwantai tayi ba, tanada masoya, Allah ne yayi matarsa, Sannan be kamata kidinga wannan maganganun ba karkizo kiji kunya wataran kamar yadda naji kunya nima, Ni data zauna taredani tayi zaman hakuri dani na tabattar Alkhairi ce ga rayuwar Jalal, a irin zamanbda tayi a hannuna nasan halinta"

"kinga dan Allah ki sauraramin bana bukatar jin wa'azinki, tunda baya nan, ki gaya masa ya shirya karbar karamar bazawara, dan sena kashe Auren nan, ban ga dacewar Jalal da wannan yarinyar ba"

Maama tace "Shikenan duk yadda kika gani, komai ya samu bawa mukaddarine, dadinta ma ďan naki ba wani kintsatse bane balle aji haushi dan an rabu da shi, naga ke kanki baki isa da shi ba, temaka masa akayi aka bashi yarinyar nan, kuma duniya da gaskiya baki isa ki biya Jalila da mahifiyarta abunda tayiwa ďanki ba"
Maama takarasa maganar tareda shigewa ta bar Mummy a gurin.
Mummy ta dawo gida tana cizon ya tsa, tana tunani iri2 a ranta.

Jalila hankalin ta ya ďan kwanta, Husna na debe mata kewa suna hira lokaci zuwa lokaci, sannan duk lokacin da ta keso zata ari waya takira wanda takeso, Mijin Antyn Jalal professor Aliyu Ishaq yana koyar da darasin turanci a saudiyya, be fiye zama ba, yana da tarin Ilimi, gashi mutumin kirki ne, yana da barkwanci da raha, Girmama shin da Jalila da take da yadda yaga tana gudanar da Al'amuranta yasa take burgeshi, yayiwa Jalal murnanr samun yarinya me kwazo da tarbiyya kamar Jalila. Be kara sarewa da lamarin Jalila ba seda Antyn ta bashi labarin irin Abubuwan da Jalila ta dingayi da kokarinta akan rayuwar Jalal, ya zamana Jalila tana sakewa da shi fiye da kowa a gidan, kamar yadda Ake kiransa Abee haka take kiransa, Jalila tana son mu'amala da mutane masu ilimi dazata Amfana dasu, indai Abee ze fito parlour Jalila zata zauna Suyita hira tana masa tambayoyi akan abubuwa da dama, shikansa duk lokacin da be ganta ba ya dinga tambaya tana ina kenan, yana mamakin kaifin hankalin ta da basirarta, gata da ilimin Addini "

Yauma na gama dinner, Amma Jalila tanata hira da Abee tana bashi labarin irin fituntunun data dingayi lokacin kuruciya suna ta mata dariya, Hajiya Salma tace
"Nikam Alhaji Aliyu me kayiwa Jalila haka take sakewa da kai hada hira, mu kaman tsoronmu ma takeji"
Jalila tayi murmushi tace "Bahaka bane ba, Jalila Aliyu Imam, shine cikakken sunana, kuma Kafin Babana ya rasu Abee nake ce masa"

Anty tace "Haba shiyasa wannan shakuwa haka, Ashe ya da uba ne"
Abee yace "Eh ya ranku, yata kuma sirikata kuma malamata"
Zare ido Jalila tayi tace "Wace ni, se dai in durkusa a koyamin, Seda safenku" Jalila ta fada

Please Login or Register in order to submit comment