Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta fado dakin bako Sallama tayo kan Khadija, da sauri khadija ta tashi zaune ta kashe wayar
"Khadija wane Habib din zaki Aura?
Waye Habib din?" dama khadija tasan wannan ranar zatazo, dan haka ta mike da sauri ta rufe kofar dakin, saboda yan biki sunfara zuwa gidan da mutane, ta dawo ta kalli Saudat tace
"ina jinki, mekike cewa?"
Cikin fada tace "tambayata ma kikeyi? Waye Habib din dazaki aura?"
Cikin dakewa tace "Habib Kamal me Gwal, mijin Salma kawarki shi zan aura" A razane Saudat ta kalleta "ke yanzu khadija bakji kunyar gayamin haka ba, macuciya Azzaluma, na yadda dake kici amanata, mijin kawata, wanda nakeso nazo nagaya miki matsalata, kikace zaki temakamin ashe cuta ta zakiyi khadija, na yadda dake amma kimin haka"
"ke dalla dakata, mekikace mijin kawarki, aigara ace nina aureshi akanki abun kunyar seyafi sauki, ni abun kunya gaba na bashi ba bayaba, kekikace ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba, kema Auren cin amana kikaso kiyi ai, Saudat na dade ina mafarkin Auren miji irin Habib tun ranar da naganshi naji nakamu da sonsa amma abun mamaki, kika rigani gayamin kema kina sonshi, a lokacin nan dana gayamiki ina sonsa nima toda biyu babu za'ayi, shiyasa namiki shiru, na gargadeki da kinemi wani karki tsaya jiran Habib amma kimayi bris dani, kisani mutuwa ce kadai zata iya hana Auren nan, duk wani shige da fice dazakiyi a yanzu aikin gama ya gama baki isa kiyi komai ba, dan ba karamin shiri nayi ba"
Fashewa da kuka Saudat tayi tace "khadija da tun farko kin sanardani kina son Habib, dazan iya barmiki shi, da ban wahal da kaina haka ba, amma kika bari na dinga lalube kina rainamin hankali, tun tasowarmu kaf cikin yan uwana uwa daya uba daya dake na yadda, amma kinmin cutarwa mafi muni khadija!!!! Kinsa na zubda hawaye kin bakantamin rai kinmin tabo me muni da bazan manta ba, kin kwace abunda na kallafa raina aki, shikenan ki shirya ki rubuta ki Ajiye idan harni Saudat yar halak ce haihuwar uwa da uba, wallahi senamiki mummunan tabo kema ki Auri Habib ga daula nan kinsamu, amma ki saurar zakiga nima abunda zan iya" ta juya da sauri fuskarta duk hawaye zatayi waje khadija ta rikota, karo na farko dataji tausayin Saudat amma ta basar tace
"Saudat ki fawwalawa Allah lamarinki, kiyi wanka da fetur, sannan ki hau risho da wandon leda yafimiki sauki akan hana Auren nan, kisawa zuciyarki salama kibi a sannu kema sekiga kin samu ko wanda be karasa Habib bane, kinfi kowa sanin hatsarina karkije garin daukar fansa kikuma ruftawa wani tarkon wanda bazanso hakan ba, har yanzu ina kaunarki yar uwata, kar abunda nayu miki ya shafi zumunci da kaunar dake tsakaninmu"
Fizge hanunta tayi da karfi ta bude dakin ta fice, Ajiyar zuciya khadija tayi ta koma ta zauna tayi murmushi tace "Saudat kenan, na dade ina ankarar dake amma baki gane ba, naciki wasa se hakuri"
Tundaga lokacin nan Saudat tafara rashin lafiya har akayi gama bikin khadija, tarasa nutsuwarta gaba daya, banda tunani babu abunda take, so take ta samu hanyar dazata turawa khadija bacin rai dan ta huce, tarasa mezatayi danta huce, kasa samun mafitane yasata takara shiga damuwa da halin rashin lafiya, yayinda khadija ko a jikinta hidimar bikinta kawai takeyi, anyi hidima sosai a bikin khadija anci an sha, anyi watsi da nera yadda yakamata.

Kabir yashiga matsanciyar damuwa gameda Auren khadija, yayi kuka, yayi kukaba adadi, ga fushi da mahifiyarsa keyi dashi, ga basussukan mutane saboda yadda yakecin bashi yana kashewa khadija, gaba daya duniya tayimasa zafi, yarasa meyake masa dadi.

Tunda Allah yasa khadija ta shiga gidan Habib komai yafara rushewa, gaba daya hankalin Habib yakoma kanta, Salma dama bata da surutu, khadija tafita baki, dan haka ta shiga hadasu fada, dama khadija bata kaunar dangin Habib tunda taji labarin basa son Aurenta, da Habib baya wata guda cikakke beje maiduguri ba amma tunda ya auri khadija seyayi watanni bejeba, Salma sedai ta zauna tasha kuka, ya shirya musu tafiyar wata daya Dubai shida Salma da khadija, Salma tace bazataba, ya dauki khadija suka tafi basu dawoba seda sukayi wata uku, gaba daya Salma ta zubawa sarautar Allah ido.
Idan yan uwan Habib sukazo gidan ta dinga rashin mutunci kenan tana habaici
Tunda taje dakin miji Saudat bata taba zuwa gidanta ba balle takirata a waya, hakazalika seda ta shekara guda cif sannan ta yadda tabi Habib maiduguri ta gaida mahaifiyarsa, tunda mahaifiyar Habib taga khadija taji sam bata kwanta mata ba dan sam babu alamar kunya ko kara a tareda ita, tunda ya aureta shekara guda sannan tazo ta gaishesu. Ta lura khadija a tsaye take ga Salma ta rame matuka tayi duhu, dan bata gayawa kowa meyake damunta, kota fada ba a goya mata baya sedai ace tayi hakuri kishine ke damunta.
Maman Habib ta kirashi dakinta, ta dinga masa fada, akan yadinga adalci tsakanin matansa, in bahakaba seyayu danasani, dan taga alamun wannan tsagerar daya aura kamar suna cutarda Salma, dan ita sam wannan yarinyar batayi mata ba, banda rashin mutunci shekara guda da aure sannan sukazo yakawota gida sugaisheta shi kansa ya canza gaba daya,
Haka yaita bata hakuri, yace insha Allah ze gyara amna yana kokarin yimusu adalci.
da kyar khadija ta hakura ta kwana biyu a garin tace ita ya maida ita gida ta fuskanci danginsa basa kaunarta.
Watan khadija biyar a gidan ta fuskanci tanada ciki, koda tagayawa Habib yayi murna matuka, tunda ya auri Salma shekara biyu kan na uku amma bata taba ko batan wata ba, sunje Asibiti ance lafiyarta kalau, dan haka yayi murna da wannan cikin
"Habib kadena murna da wannan cikin zubar dashi zanyi wallahi!"
Cike da mamaki ya dubeta "kamarya ya? Ina neman abu in samu kice zaki zubar khadija why?"
"ban shirya haihuwa yanzu ba wallahi, da kuruciyata bazan tsufa ba wahalar yaya ta kasheni ba, tun kafin muyi Aure kasan burina inason yin karatu me zurfi a kasar waje, tayaya zanyi karatu da ciki, kwata2 yaushe nayi Auren zanyi ciki, wallahi sena zubar"
"khadija kiyimin rai dan girman Allah kiyi hakuri, kibari ki haifamin cikin nan seki tafi karatun"
"sekuma kayi, in kanason cikinka seka dauka ka maida shi jikinka ka haifa, amma indai a jikinane bazezo duniya ba gara ka hakura inkun matsu kaje kaimata cikin ta haifa maka"
Saroro yayi yana kallonta, ba kunya take gasa masa wannna maganganun.




.
A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu 'oinku
Sannaan masu rokon adinga posting a Facebook insha Allah za' a fara posting din Littafin ABDUL JALAL Facebook tundaga farko
Insha Allah, za'afara posting a group din
AISHA HUMAIRA NOVEL FANS (Daddy's girl) dakuma sauran groups nagode sosai ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣1️⃣74

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]





_MY FIRST NOVEL_

"haba khadija, yanzu dan sunnan zakice zaki zubarmin, ina son yara sosai, ki haifamin ko dayane seki tafi karatunki bazan hanakiba, mama tana matukar son yara, tanason jikoki, dan Allah kibari ki haifamin"
Mikewa tayi ta shige toilet tabarshi a gurin a zaune. Tana shiga bandaki tayi tsaki tace "in maman nason yara, se itama ta haifa aiba abun kunya bane, aikin banza nibahakane yakawoni ba"
"ikon Allah Salma nata nema ido rufe tana Addu'a, itakuma Allah yabata zata zubar"
Haka Habib yaita fama da Khadija, a haka har yakoma Dubai, ta shirya ta tafi gidansu sunyi murna sosai da ganinta, khadija tanada kyauta tanayu musu aike sosai, kama daga Abinci sutura da kudi, amma idan Habib yayi niyyar yiwa yan uwansa kona Salma wani abu, indai tasani seta hanashi, amma itakuma ta nayiwa yan gidansu.
Ranar dataje gida seda ta tsorata dataga Saudat tayi rama matuka, tayu duhu duk wannan kwalisar babu, har cikin ranta taji babu dadi yanayin dataga Saudat, dan haka ta dan damu, daki tabi Saudat tacewa sauran kanensu sufita subasu guri, b musu kowa ya watse, tazo kusada Saudat ta zauna ta kalleta tace "yar uwata, meyake damunki haka? Saudat kinga yadda kikakoma kuwa?"
Tsaki Saudat tayi, ta juya mata baya
"Saudat nasan ban kyauta mikiba, amma rayuwa bazata tafi a hakaba, kisani dama can Allah be rubuta Habib mijinki baneba, idan kika cigaba da wannan rayuwar tozaki kashe kanki a banza ne, tunda kinsan Bazaki samu Habib ba, Saudat inaso mucigaba da zumuncinmu, kimanta da abunda yafaru ki karbi kaddararki, Allah yafito miki da miji, indai kudine Saudat duk abunda kikeso zanmikishi Insha Allah" mikewa zaune Saudat tayi ta kalli Khadija
"Zumunci nidake har abada wallahi, kin riga kin rusa alakar dake tsakanina dake, ke kinama yaudarar kanki ne da kike cewa wai mukoma kaman da, naji tawa kaddarar kenan da tasameni a sanadinki, kema ki saurari taki kaddarar, malama ki tashi kibaani guri, ficemin a daki"
"Saudat nikike kora haka?"
"na korekin ko uwata ce tamin abunda kikayi min sena rama, dalla malama fita munafuka"
"shikenan tunda haka kika ce, inkika dawo hayyacinki zaki gane me nake nufi" khadija ta mike ta bar dakin.

Bayan tafiyar Habib da yan kwanaki khadija Taje chemist tace subata maganin abortion, me chemist din yace shi gaskiya baya irin wannan harkar, take ta zube masa uwar kudi, take jiki na rawa yabata magani da yadda zata bi cikin ya zube, ta dauki maganinta ta tafi gida, yadda yace mata haka tayi amfani dashi, aikuwa ba adau wani lokaci ba mararta ta dinga ciwo wuni tayi tana murkususu a haka har seda cikin nan ya fita, tasha wahala matuka, gashi ba wanda tagayawa, ko Salma da suke zaune gida daya bata mata magana, haka tai wahalarta ita kadai ta gama.
Saboda daukin cikin da Habib yakeyi, sati uku yayi ya dawo gida, gurin khadija yafara sauka, se wani sabon kalan soyayya yake nuna mata sabida duk zatonsa cikin yana nan.
Da daddare yana cin Abinci shida khadija, ya kalleta yace "cwt Deejah, Wani suna kikeso musakawa babynmu inkin haihu, ina son in sanarwa su yaya hajjo, cewar munsamu rabo, ko baby" dan ya tsina baki tayi
"mhmm kaga dakabar wannan batun gayawa mutane ansamu rabo, bayan tafiyarka na fadi a toilet cikin ya zube, ban gayamaka bane saboda kar hankalinka ya tashi"
Abincin daya hadiya ne yaji ya makale masa a makogwaro yaki wucewa,
"kin zubarmin da ciki ko khadija?"
"niba zubarwa nayi ba zu.....
" Shut up!!! "
Yafada cikin tsawa da sedata razana
" saboda kin rainamin hankali kike cewa zubewa yayi, wato baki hakura ba shine kika zubarmin da ciki, dan kinga ina lallaba ki ko? Nikikayiwa haka ko? Har innuna miki abunda nakeso amma ki shure kiyi son ranki, kin zubar Minda ciki nagode "
"Ahhh Hayatee wallahi.....
" yimin shiru"
Ya katseta, ya tashi ya dau wayoyinsa yabar palourn, dafe kai tayi bata taba tunanin Habib ya iya fada haka ba, saboda gaba dayansa silent ne, bashida hayaniya sam. Amma fushinsa baze hanata cinma burinta na rayuwa ba.
Wasa2 tunda yabar part dinta seda yai sati guda bata ganshi ba, ko ta waya, dan haka ta shirya ta nufi part din Salma, tana zuwa ta tarar Salma na kitchen tana girki batabi takan Salma ba ta nufi palour na biyu,
"lafiya zaki shigomin ba sallama ki wucemin daki?"
"ba ruwanki ba gurinki nazo ba" ta shige tabar Salma a gurin, tana shiga kuwa ta tarar da Habib a palourn yana karanta jarida, karasawa tayi ta zauna kusada shi
"Hayatee kwana bakwai banganka ba, meyasa dana gayamaka abunda yafaru baka yadda daniba" shiru yayi yaki dagowa ya kalleta, hannunsa ta riko ya dago a fusace
Amma seyaga fuskarta sharkaf da hawaye, nan take jikinsa yayi sanyi
"Hayatee, duk lokacin danakiraka Hayatee i mean it har cikin raina kai rayuwata ne, meyasa ka karyatani baka yadda bani na zubar maka da ciki ba, inason abunda kakeso tsautsayine ya gifta cikin ya zube dan Allah kayi hakuri" ta zube akan gwiwoyinta tana kuka, hannu yasa ya dagota ya rungumeta yana share mata hawaye
"is ok am sorry my deejat, ya wuce kidena kuka" a hankali tace "I miss you Hayatee, dan Allah karka kara fushi dani haka"
"I miss you too baby, bazan kuma ba"
Khadija yar duniya ce yanzu kana zaune zata siyeka.
ganin shirun yayi yawa yasa a fusace Salma tanufo palourn, Amma abunda idonta ya gane mata yasata ja da baya da sauri, jitayi kaman andoramata dutse a zuciyarta, kitchen takoma ta toshe bakinta tana kuka, tanaji tana gani anzo har cikin gidanta an kwace mata miji.

Antyn Jalal ta kalli Jalila data tattara duk wata nutsuwarta kaman tana daukar karatu tace
"kinga rana tayi, shabiyu takusa, kuma da azahar zamu koma maiduguri, zan kara takaita miki labarin nan dannima bakomai nasani ba, Amma kinsan meyasa khadija tayi nasara ta kwace mijin Salma?"
Girgigiza kai Jalila tayi
"Salma ta zurawa Habib ido tana ganin kaman yadena sontane, maimakon ta tashi tsaye tayi fighting ta gwada masa soyayya, ta kwaci mijinta, seta karaya da wuri tana ganin kaman bazata iya kishi da khadija ba tafi karfinta, ta zuba musu ido"
Haka rayuwa tacigaba, seda Khadija ta zubar da ciki kusan hudu Habib be saniba, data fuskanci tasamu ciki setaje ta zubar, daga karshema taje tai planing hankalinta kwance ba wanda yasani, tacigaba da cin amarcinta, yau suna wannna kasar gobe suna waccan kasar, khadija tayi duk me yuwuwa takara farraka tsakanin Habib da Salma baya Jin maganar kowa se khadija, khadija yar kwalisa ce yar gayu, ta iya gayu ga girki da iya magana, yanzu zatayi laifi amma take zata mantar dashi duk wani laifi datayi, seda khadija ta shekara uku tana cin duniyarta da tsinke ta taka wanda takeso duk meson wani abu a hannun Habib seya biyo ta gurinta, Salma kam yau da lafiya gobe babu saboda bacin rai kullum cikin guma mata khadija take, duk wani abu datasan zatayi ta bata mata shi takeyi. Sedai ta shiga daki tayi kuka.

A yan shekarun nan Saudat haka takeyinsu ba walwala tayi iya tunaninta taga hanyar dazata rama abunda Khadija tayi mata amma takasa samu, kuma tayiwa kanta Alkawarin kozata mutu wajen daukar fansa setayi, zata nunawa khadija ba ita kadai ta iya makirci ba, zata rama inda babu wanda ze gani balle ya tausayawa khadija. Saudat haka tasamu FCE ta shiga take zuwa makaranta dan ta ragewa kanta zafi. Tsawon shekarun nan uku zazzafar gaba Saudat tajeyi da khadija duk abunda tasan ya shafi khadija nuna masa kiyayya take muraran, har mutane suka fara fuskantar hakan, yan gidansu sunyi mamakin dama akwai abunda ze hada khadija da Saudat dazesa sununawa juna kiyayya kasancewar ba'ajin kansu.

Khadija ta hurawa Habib wuta kan lallai ita seyasamo mata Admission a Dubai ko Egypt tafara karatu, ya nunamata yan uwansa bazasu yadda da hakaba, tayi hakuri duk makarantar datakeso a Nigeria ze kaita amma banda kasar waje, amma fafur ta badawa idonta toka taki, haka yafara nema mata Admission a Dubai ba wanda yasani seshi da ita, Allah ya temaketa tasamu, yasamu Salma yace itama ze nema mata se sukoma can gaba daya, Salma tace bazata ba sedai su barta anan duk sanda yayi niyya in yasamu lokaci yazo yaganta, ya kada ya raya amma Salma tace itafa bazata ba suje se sun dawo.
Haka Habib da khadija sukaje suka tare a Dubai, ita tana karatu shikuma yana kasuwancinsa, seyafi wata uku bezo Nigeria ba gurin Salma ba inma yazo bayafin kwana goma ze juya, hatta mahaifiyarsa ta zuramasa ido, tana masa Addu'ar Allah ya shiryeshi, yana daga cikin kaddararsa Auren hatsabibiyar mace.
Wani zuwa da mahifiyar Habib tayi itada kannensa mata nida yayata,
Gidan bakowa se Salma kawai mama ta tambayeta ina Habib ina khadija nan ta fashe da kuka tagaya mama duk abunda yake faruwa, Mama hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta dinga yiwa Salma fada, danme bata gayamata irin rayuwar da takeyi agidanba kenan, nan da nan ta kira Habib tace kome yakeyi ya yanke su dawo Nigeria tana nan tana jiransa. Yagaywa khadija tace wallahi bazat bar karatunta ta taho ba, shidai ya tafi shikadai, haka Habib ya taho yabarota a can.
Ba karamin bacin rai mama ta nunawa Habib ba tace masa yazama wajibi yadawo da Khadija Nigeria bata yadda da batun karatu a kasar waje ba tunda bashida hankali, ya tare a gindin mace yana zaluntar yar uwassa, yaita bata hakuri, gefe yana fargabar yadda ze sanar da Khadija batun fasa karatunta.
Yaita bawa mama hakuri amma fafur taki yadda tace se khadija ta dawo kasa Nigeria, hankalin Habib ya tashi yarasa ya zeyi da wannan batuna A
Mama, haka ya shirya ya koma dubai yasanarwa khadija hukuncin mama, amma tace ita bazata dawo ba, yasan yadda zewa mama ta hakura amma ita karatunta yafara nisa dan haka yayi hakuri.
Mama tanata matsa masa lamba akan ya dawo da khadija gida, ana cikin wannna halinne khadija ta fuskanci tana dauke da juna biyu abun ba karamin mamaki yabawa khadija ba, yaza'ayi ace tana planing amma tasamu ciki, nan da nan ta shiga damuwa. Tabass barin cikin nan shize hanata da ciigaba da karatunta, gashi bata san kowa ba a Dubai balle tanemi maganin zubar da ciki, dan haka ta samu Habib tace masa ta yadda sukoma Nigeria, ba karamin mamaki yayi ba yadda akayi ta yadda ta dawo Nigeria.
Bayan sun dawo ne, taje inda tasaba samun maganin zubarda ciki tazo ta sha, seda ta kwana biyar tana zubarda jini ba wanda yasan me yafaru, da kyar tasamu jinin ya tsaya amma ba karamin galabaita tayi ba.
Ammame bayan jinin ya dauke haka tacigaba da rashin lafiya, kullum ba lafiya tana kwance kusa wata biyu taki zuwa asibiti seda taji tana neman ta mutu sannan ta shirya ta tafi Asibiti lokacin Habib baya nan, Asibitin dasuke zuwa taje sukayi mata gwaje2 suka tabattar mata tanada cikin wata uku da sati biyu, abun yabata mamaki dama cikin nan yana nan be fitaba, suka dubata suka bata magunguna, tana barin Asibitin bata zame ko inaba se chemist din da take karbar magani, tai masa bayani yabata wani maganin dayafi wancan karfi, sannna ta tafi gida.
Khadija na barin Asibitin, doctor Hisham yakira Habib ya sanar masa yanzu amaryarsa tabar Asibitinsu kuma tana dauke da juna biyu na wata uku da sati biyu. Habib yayi murna a take yaiwa Hisham transfer na kudi, tukuicin Albishir, yana katse wayar ya kira khadija
"Madam sannu ya jikin naki"
"Wayace maka banida lafiya?" *"Hisham ya sanarmin kina dauke da babyna, na wata uku Ashe shike wahalar min dake, Allah maji rokon bawa abunda nake ta nema tunda kikayi bari se yanzu Allah yasa aka kuma samu, Masha Allah, Allah yarabku lafiya my deeja" hade rai tayi kaman tana gabansa amma ta maze
"Hmm Hayatee ka kyaleni, nasha magani duk jikina ya mutu"
"Eyya sannu, i wish ina kusa danamiki tausa, amma a satin nan zan dawo Insha Allah"
"shikenan se anjima" ta kashe wayarta, lallai doctor Hisham munafikine shine har ya kira yagayawa Habib, to gara ma yadena rawar kafa dan "kafin kadawo na zubar dashi ta rariya sedai kai yadda zakayi se burina yacika, senayi karatu me zurfi a abroad "

Haka takuma shan maganin zubar da ciki ta dinga malalar da jini, ta kira Habib tagaya masa hankalin sa ya tashi sosai, amma bata gayamasa wani abu ta shaba, yakira doctor Hisham ya sanar dashi, har gida sukazo don duba khadija, dole suka dauketa zuwa Asibiti, da kyar aka ceto ta saboda tasha wahala sosai, a satin Habib ya dawo an rike Khadija a Asibiti ana bata kulawa ta musamman still akayi scanning still cikin yana nan be fitaba, doctor Hisham ya gano tayi Amfani da Abortion pills amma be gayawa Habib ba.
Ya sameta ya dinga mata nasiha, sannan yace idan makamancin haka yakuma faruwa ze sanarda Habib gaskiya, ze gayamasa tana shan Abortion pills ne.
Sannan doctor Hisham ya sanar da Habib cewa zata samu sauki ya kwantar da hankalinsa.
Tunda Habib yasamu labarin cikin nan yakuna tattare a gurin khadija, yake matukar lallabata, itakuwa khadija batun cikin nan ya tsaye mata a rai, sam bata kaunar cikin nan, ga cikin ya hanata sakat saboda laulayi yauda lafiya gobe ba lafiya Habib yana bata kulawa iyayinsa amma ita kawai yadda zata zubar da cikin nan takeyi, takuma shiryawa ta tafi tasamu me chemist din nan tace masa ita so take inba ze iyaba ya hadata da wanda zasu ciremata cikin nan.
Me chemist din nan ya nuna mata illar yin hakan zata iya rasa ranta kokuma tajawa kanta mummunan ciwon daba lallai ta warke ba. Haka khadija takoma gida, duk yadda zatayi cikin nan ya zube wannan karon kin fita yayi, dukda basa jituwa da dangin Habib amma sunyi murna da cikin nan nata,
Abun duniya yakara hadewa Salma, tarasa meyake mata dadi, gaba daya Habib ya canza kaman ba Habib dinta dasuka sha soyayya a bayaba, ga sharri da khadija take mata taita hadasu rigima da Habib, ga rashin lafiya data ketayi, tana zuwa Asibiti Akai mata gwaje2, aka sanarmata mata jininta ya hau sam hankalin Habib da nutsuwarsa ya tattarasu akan Khadija.
Salma ta shirya taje maiduguri tasami mahaifiyar Habib tace mata dan Allah tasa baki Habib ya saketa bazata iya zama dashi ba ta gaji, mahaifiyar Habib tai kokarin bata hakuri amma ta fashe da kuka "mama wallahi in Habib be sakeni ba zan iya rasa raina, dan Allah ki amince ya a raba Aurenmu" mahaifiyar Salma ma ta yadda tace a sakar mata yarinyar ta baze yuwu a kashe mata ya da bakinciki ba. Mama takira Habib tace tanason ganinshi ya shirya ya tafi.
Koda yaje maiduguri mama tagaya masa abunda Salma ta bukataHabib kuma yace besan zance ba, mama tace yadda Salma takeson Habib harta bude baki tace ya saketa lallai abun ya kai makura dan haka ta goyi bayan ya saketa ta huta haka,
Salma taje ta samu Habib tace
"Habib nasoka tun bansan meye soba, ka koyaddani sonka, Habib ina maka sona gaske shiyasa banason ka kasance cikin wanda Allah ze hukunta ranar Alkiyama, Habib banason Allah yakamaka da laifin rashin adalci a tsakanin matanka, shiyasa nakeso ka sakeni dan Allah Habib, sakina shize kara tabattarmin har yanzu akwai tausayina da kaunata a zuciyarka ka sakeni Habib " tana zuwa nan a maganarta ta sume a gigice Habib ya dakko ruwa ya zuba mata amma bata tashiba haka aka kaita Asibiti jininta ya hau sosai, kwanam ta guda da wuni a asibiti sannan ta farfado, koda ta farfado da kuka ta farfado akan dan Allah Habib ya saketa,
Mama ta titsiye Habib tace seya saki Salma,
"Mama wallahi bazan iya sakin Salma ba ina sonta"
"Kana sonta ka hada kai da makirar matarka kuke neman kasheta, Ka Saketa kokuma in maka baki"
Jiki a sanyaye ya furta ya saketa saki daya. Take Salma tayi ajiyar zuciya tareda murmushi tace "Nagode Habib ina maka fatan rayuwar Aure managarciya da matarka, Allah yabani mesona har abada"
Habib yayi zarya maiduguri akan Salma ta dawo amma fafur aka rasa me goya masa baya, Salma kuma tace itada gidansa har gaban

Please Login or Register in order to submit comment