Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma dayake akwai abunda sukeyi ai baze iya hakura ya tafi ba, yanzu ki kwantar da hankalinki kawai dai kiyi kokari ayi mana Aure da shi a wuce gurin "
" Ke kina batun inyi kokari ke wani kokarin kikayi?, tsawon shekaru kina gidan nan amma kinkasa janyo hankalin sa, Amma kanwar kanwarki wannan 'yar yarinyar hartasan taja hankalinsa duk taurin kansa, da uwar me tafiki? Niba ina nufin ki zubar da mutuncinki ba amma abun ya dauremin kai, ace har taci mutuncinsa agabana amma dayake bashida zuciya har tasamu kusanci dashi fiye dani da kema gaba daya Kinga tashi kibani guri ni raina ya gama baci"
Ilham ta mike ta fita tana zunbura baki, Amma dai tayi Nasara tunda har Mummy tafara daukar zigarta ta harzukata haka yanzu saura next plan dinta.

Jalila ta tsaya ta kalleshi tace "to ni zan shiga gida, Amma kabawa daddy hakuri"
"Hakurin me zan bashi? Jiya da daddare ya tafi U.K ai"
"to Mummy fa?"
"mezan mata, akanta nake kokuma wani abun nayi mata? "
"Ohh God kanada taurin kai, Just recently kace you want change, kuma yanzu kana wata magana, she's your Mother, komene halinta kuwa, Aljannarka tana karkashin kafarata, ko kanaso kashiga wutane?"
Tayi masa tambayar kaman tana tambayar karamin yaro
Kallonta yayi amma bece komai ba
"Kadinga zuwa inda take, kayi hakuri da duk yadda take, kadena bata mata rai, kaji dan gidan daddyn sa, your Mum is so kinda, she loves you, you have to show her love too, batun Ilham kuma babu dadi kace baka son mutum agabansa kaji"
Tai maganar tana murmushi sannan ta shige gida.
Sumar kansa ya shafa yayi murmushi shima.
Gida ya shige yayi wanka ya ci Abinci ya tafi gurin Jawwad, Jawwad na ganinsa yafara dariya "mutanen Dubai ya akayine?"
Jalal ya dan hade rai "naga alama da hadin bakinka kanwarka tasa aka hanani tafiya"
"niba hadin bakina, amma nasani daddyn Hanan tagayawa, tun a lokacin nasan za'a soke visa dinka, amma nayi shiru ban gaaya maka ba, Amma ya akayi kasan itace tasaka, ina fatan zakayi hakuri karka hukunta ta"
"Hmm Jawwad kenan, yarinyar nan nasan halinta sarai, tun ana gobe zan tafi take dariya tace taga ta inda zan tafi, kaga inba itaba babu memun haka, akwai abunda tayi da har yanzu yake bani mamaki shiyasa akwai abubuwan da idan tayi bazan mamaki ba. Sannan yazan mata ta riga tayi, ban mata komaiba tare muka dawo ma"
Murmushi Jawwad yayi yace "zoka bani Labari, yaushe kuka dena fada ne? Ya akayi ka sakko da wuri haka? Nazata inka gano itace semunzo ban hakuri kar a hukuntata hukunci me tsanani"
"ta fini gaskiya ne, a da dinma abubuwan da take fada akaina gaskiya take fada, nina nake fadan rashin gaskiya, sedai tafiya tsiwa a gadarance take gayamin magana abunda yake harzikani kenan"
"to yanzu fa?"
"Bansaniba babana kasani agaba se antayamin tambayoyi kake, sekace EFCC, kaje ka tambayeta mana"
Dariya Jawwad yayi tareda dan jan kunenen Jalal dake cin Abinci ta sigar wasa yace "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade nidai tunda baka hukunta taba kagama min komai"
Murmushi Jalal yayi sannan yacigaba da cin Abincin sa.
Sunata hirarsu shida Jawwad gwanin sha'awa,

Naja tana gaban mudubi, tasha kwalliya kaman zata gasar rawa, duk tabi ta tsuke jikinta, ta feshe jikinta da turare se taunar chewing Gum takeyi
Nana tace "Ehemm su hajiya Naja ko anyi sabon kamune wannan wanka haka?"
"bawani Sabon kamu, gurin Masoyina zanje tunda shi bezoba ai gara inje inda yake"
Jalila kallin Naja take kawai dan ba karamin tausayi take bata ba yanzu, rashin sani yafi dare duhu, da Jalila zata fadi wani abu data rusa duk wannan rawar kan da farincikin Naja har karshen rayuwarta, abunda ita kanta Najar bata san dashi ba "Allah ka kiyayemin Yaya Jawwad dina ka tsaremasa Imaninsa tareda dukkan Musulmi, dan a wannaan shigar da Naja tayi tana wannan masifaffen Kamshin indai Lafiyayyane namijine da wuya ya iya shallake wannan mugun tarkon na shedan.
Nana ko cewa tayi" kekam dan rashin aji dan yaki zuwa ke sekije inda yake, Sannan kalli shigar ki bata daceba kayan sun matseki"
"A'a ke kyaleni, A haka zanje irin wannan shigar da ita ake kama zuciyar masoyi kuma tana kara kusanci da kauna"
Itadai Jalila batace komai ba har Naja ta fice, sedai girgiza kai datayi tana cigaba dayiwa Jawwad addu'a.

Jalal yagama cin Abincin sa ya dakko system dinshi yana dubawa yace

"Jawwad next month fa zaka tafi Abuja gurin Aikinka"
Da sauri yace
"Saboda me?"
"Saboda nima haka na shirya maka kafin intafi, dan haka seka tafi"
"haba Jalal meyasa, Abba na kokarin bude mana store ne muyi ruining dinsa da kanmu kaga base nayi aikin gwamnati ba mun huta"

Dan tsurawa Jawwad ido yayi a ransa yace "mezanmaka a rayuwa Jawwad in biyaka kauna da alherinka, Sarai Jawwad yasan Jalal yanada tarin dukiya a kasa, Amma bayason ya kashe masa zuciya kar ya nemi na kansa"

"Kaga idan ka tafi nika barni da harkar kasuwancin zanyi mana, Amma seka tafi fa"
"Amma Jalal hakan......
" Salam Alaikum "
Muryar Naja ta katsesu gaba daya suka juyo suna kallonta
Wato har wani pink take saboda tsabar bleaching, saboda daganin wannan farin banata baneba, ga gaba daya dakin ya gauraye da kamshin turarenta tareda karnin mayukan da take Amfani dasu, tasaka riga da skirt na material dasuka kama jikinta matuka duk saman kirjinta a waje.
Dauke Kai Jalal yayi, yacigaba da danna system dinsa
"Masoyina gurinka nazo fa"
Tai maganar tana kokarin zama a kusada Jawwad, Jalal kam mikewa yayi ya shige bedroom din Jawwad, yana tunanin meyasa wasu matan basuda kunya basu san ciwon kansu ba, ace mace budurwa kaman wannan amma tana nanikar namiji haka ba kunya ba tsoro, hakama Ilham take masa wani lokacin, To Amma meyasa ita Jalila bata haka? Shidai yasan ba ruwansa da mata hasali yana gudun taba macen daba maharramarsa ba, Amma ita Jalila bayajin komai dan ya tabata, yana jin kaman hakan shi a gurinsa ba laifi bane, sannan duk lokacin da hakan tafaru a tsakanin su yana ganin matukar tsoro da rikicewa a idonta. Haka yacigaba da zancen zuci yanata tunani daban2.

"Haba masoyin, Meyasa baka zuwa inda nake Yaya Jawwad, wallahi banajin dadin abunda kakemin sam baka nunamin soyayya"
Matsawa yayi daga kusada ita yace "Naja soyayya daban Aure daban a yanzu keba halalina bace ba meyasa zakimin irin haka? Ke ko kunya ta bakyaji ne haba Naja kidinga kama kanki mana"

Matsowa takumayi jikinsa tana kashe murya tace
"meye wani kama kai, Aurena fa zakayi dan Allah kasaki jiki ka nunamin soyayya haba Jawwad" takai hannu tana shafo fuskarsa

Gaba daya jikin Jawwad rawa yakeyi Tsaki yayi yana kokarin mikewa, tunda ya fuskanci bazata ganeba
Riko hannunsa tayi tana kokarin Rungumeshi, A fusace ya hankadeta kasa yana kokawa da numfashi,
Tashi takuma yi tace "bazanyi zuciya ba" sekace mayya take kuma shanye ido kamar tana maye, ta rungume shi.
"Ke!!!" ya daka mata tsawa a fusace wadda seda yasa Jalal fitowa a sukwane yayi jifa da ita
"ki tashi kibarmin dakina, Allah ya shiga tsakanina dake ban taba aikata mummunan sabo ba bazan fara akanki ba, get out from my room ko in illataki" idon Jawwad yayi jawur jikinsa yana rawa, gaba daya ta kasa gane dama Jawwad yana fushi haka? Jalal ya karaso ya rike Jawwad yace
"Jawwad kyaleta yi hakuri, calm down"
"bazanyi hakurin ba ka kyaleni, wallahi takuma zuwarmin daki sena bata mamaki, bata san a bisa umarnin Maama zan Aureta ba, in bahakaba me zanyi da ita? Me take dashi daza'a kalla a ce wannan mace tagari ce ya dace a Aureta? Itada mahaifiyarta sun shiga sun fita sun rabani da kanwata shekara da shekaru suna uzzuramata suna bata mata rai suna cimata mutunci, na hakura, ance sena Aureta na hakura nayi biyayya, be isheta ba seta nemi tasana aikata laifi me muni"

Kallon Naja Jalal yayi, kaddai ace wannan yarinyar ya yadda ze aura, Amma Jawwad hakurin nasa yayi yawa. Naja ba karamin mamakin abunda Jawwad yayi mata tayi ba, ita babban mamakinta bata taba ganin yana fada ba, saboda tasan mutum ne me kunya da kawaici.
Jalal yace "Naji kadaiyi hakuri"
"bazanyi hakurin ba Jalal"
Jalal yace "da nine da yanzu kacemin masifaffe, haba dan uwa Aliyu Haidar zakin Allah, katangar sikari na Hanan kowa ya jingina da kai seya lasa, fari me farar aniya kai a cikin masu sunan ma na dabanne kayi hakuri" Jalal yana lallaba Jawwad ne saboda yasanshi be iya fushi ba, seya shafe shekaru be fushi ba amma idan yayi abun baya kyau.
Naja tace "kagama duk masifunka, wallahi nidin dai ni zaka Aura kuma zaka gane baka da wayo, bari Maaman ta dawo zaka gane ka taka tarkon mace.
Jalal ya hanashi magana, suka kyaleta a gurin yaje ya dinga rarrashin Jawwad, ana haka Hanan ta kira wayar Jawwad, Jalal yai murmushi yace "kaga ka daga wayar nan ayi maka kalamai, zaka huce"
"A'a ka kyaleni, am not in mood"
Aikuwa Jalal ya daga wayar suka gaisa yace "Hanan ga mutumin naki, Amma ransa a bace yake fa"
"Subhanallah dan Allah wayakai min zuciyarsa bango har akasamin shi fushi, dan Allah ka bashi wayar"
girgiza masa kai Jawwad yayi alamar baze karba ba
"kiyi hakuri, baze karba ba fa, ransa a baci yake"
Hanan a shagwabe tace "Shikenan tunda baze karba ba amma zuciya ta bazataji dadi ba, Allah kuka zan tayi duk daren nan, wallahi har naji tawar zuciyar tafara nauyi"
Ai tuni Jawwad ya zare wayar a hannun Jalal yasa a kunnensa yace
"Hello Hanan kina jina?"
"haidar dina me akayi maka?"
"wani little issue ne, kuma yanzu komai yayi settling"
"little issue baze bata maka raiba"
"ki manta kawai, kar inga abunda yasamin ke kuka"
Jalal yaji Jawwad ba kunya anataya masa kalamai agabansa. ya minstili kafar Jawwad yace "dan rainin hankali kawai"
Jawwad yai murmushi
Jalal ya daga masa hannu ya wuce gida.
Yanayin maganar Hanan kaman Jalila, tuno moments dinsu yayi dazu dayake ta dage bilhakki tana masa fada, da yadda take da ido idan batada gaskiya murmushi ya dingayi shi kadai, har ze kwanta ya tuno maganganun Jalila game da Mummy.
Mikewa yayi ya nufi cikin gidan, babban palourn Mummy yasa hannu ya bude kofar. Salla takeyi yanemi guri ya zauna, rabonsa da dakin nan harya manta yana jiranta yana sake2 a zuciyarsa mema ze ce matane?.
Ta idar tagama lazimi, ba karamin mamakine yakamata ba ganinsa a part dinta
Ta kalleshi tace "Lafiya kuwa? Ashe baka tafi ba, uwarka wadda tafini, wadda take baka abunda bana baka ka fasa tafiya saboda ita.
" Wakenan? "
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣7️⃣90

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]





_MY FIRST NOVEL _

"wakenan?" ya tambayi Mummy yana kallonta
"eh da ita yarinyar daka dawo dan ita mana, tunda tana maka abunda bana maka, wallahi kaji tsoron Allah, ba irin Magiyar da banyi maka ba, Amma kayi biris amma yanzu dayake tafini ai gashi kadawo"

Tsyawa yayi ya zubawa Mummy ido tagama, Yayi tsaki ya tashi ya fice yana masifa.
Haka yakoma dakinsa yana mita yana tunanin meyasa ma yaje inda take.

Jalila tanata lissafi gobe su Abba zasu dawo, dan haka ta tsananta Addu'a Allah yabata sa'a yasa Abba ya janye batun Aurawa Jawwad Naja.

Yauma Jalila taje school, sun kammala lectures, sunfi to itada Zahra, Zahra tace
"Yawwa nikam Jalila naji Wata suna hira tace wai jiya wani hadadden gaye yazo yasaki a mota ya tafi dake, amma wai dagani dan shaye2 ne dan wuyansa hada sarka, ga wani irin Aski akansa, ina fatan lafiya ba wata matsalar bace?"

Dan karamin tsaki Jalila tayi aranta tace"
dan jaraba da masifar mutane komai kayi idonsu akanka
"Eh haka akayi, seme kuma?"
"A'a ba komai dama nayi tunanin ko mutanen baban Saleema ne"
"basu bane, Yayana ne" Jalila tabata amsa a takaice, Dan zare Ido Zahra tayi
"dama kinada yaya dayake shaye2, na zata Yaya Jawwad ne kawai Yayanki"
"Akwai wani to, kuma akansa nayiwa Alhaji Kabiru baban Saleema, abunda yanzu yana daf da zuwa prison shida 'yan tawagarsa"
"Amma Jali....
" Ke zahra kin isheni wallahi, nagaji ga yunwa ina ji se faman tambayoyi kikemin, sekace wata likita, haba se Allah ya kaimu gobe"
Inda sabo Zahra tasaba da halin Jalila, tanada saukin kai Amma tanada tsari a komai nata, in bakasan halinta ba zakace batada kirki ne kawai, bata da san yawan tambaya.

Mummy ta bawa Ilham kudi tace ta kaiwa Nana ta ajiyewa Maama in ta dawo a bata, Ilham ta karba harta shiga gidansu Nana wani tunani ya fado mata a rai, dan haka tayi murmushin mugunta tashi. Tana fitowa hakan yayi dai2 da dawowar Jalila daga makaranta sukayi karo a kofar gida. Ilham ta tsare Jalila da ido tana mata kallon zaki gamu dani ne.
Jalila tace "Ilham wai kin manta maganar danayi mikine? Ki dawomin da Al'qur'anina tun muna sheda juna dake"
Ilham ta rike kugu ta kalli Jalila "idan naki fa? Me zakiyi?"
"Aimeyi baya fada se dai kigani a aikace, zakiga matakin dazan dauka, ki kawomin abina na gayamiki"

"ina jiran ganin matakin dazaki dauka din, amma kafin ki dauka ni ki saurari nawa"
"banida lokacin saurarar duk wani shirmenki, ba abunda kika isa kiyi min, nagama magana Ilham"
Jalila tasa kaii ta shige gida.

Kwana hudu kenan basu kara haduwa da Jalal ba, haka nan yaji yana kewarta sosai. Koba komai yayi missing neman maganar ta.
Sannan tunda abun nan yafaru tsakanin sa da Mummy be kuma shiga cikin gidan ba. Mikewa yayi yafito zetafi gidansu Jawwad.
Yana kokarin fitowa daga part dinsa Ya hango Ilham a jikin mota tanata boye kudi a jikinta, yana ganin haka yasan bata da gaskiya amma bebi takanta ba ya fice.

Jalila tana zuwa ta dire Jakarta ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar Azahar ta kwanta bacci, se la'asar ta tashi, tayi sallar la'asar sannan taji tana jin yunwa.
Jalila tana zaune akan dadduma kafin tabar kan daddumar ta, Ahmad ya kirata suka dinga hira har kusan 40 minutes, Nana kallon ta kawai takeyi seda tabari tagama sannan tace
"Jalila wai dan Allah ina kika samo wannan Ahmad din, iya sanina ba kya son duguwar waya amma kalli yadda kika zage kina waya"
Jalila tayi murmushi sanna tace
"Nana a Bauchi na samo shi, yanada kirki sosai"
"kinga niba wannan ba magana nakeso muyi masu mahimmanci"
"inajinki amma ki hanzarta inajin yunwa"
"bawani in hanazarta, ki zauna kigama wayar se yanzu zakiji yunwa?
Jalila dan Allah ki gayamin hakikanin meke tsakanin ki da Yaya Jalal?"
Jin maganar tayi wani banbarakwai, batayi zaton jin wannan tambayar ba
"kamar yaya? Kinga wani abune da baki yadda dashi ba? Meyasa kikamin wannan tambayar"
"Jalila ruwa baya tsami banza yadda Ilham ke takura tsanarki tabbas wani abun tagani, tana claiming kuna soyayya ne, nima da nayi wani nazari zancenta yana kusada gaskiya"
"Mtseww niban san yakuke so inyi ba, da muna fada da shi, ance banida kunya inamasa rashin kunya, yanzu na dena ance ina sonsa to ya zanyi, Nana niba son Jalal nakeba, ina tausayinsa ne musamman danaji labarin waye shi, Nana a baya nikaina nasan na bata masa rai dayawa, yadda nake masa rashin mutunci da bakaken maganganu, naga ban kyauta ba sannam ba'a gyara da barna, muddin kanaso ka temaki mutum ya dena aikata laifi indai zakayi masa hayaniya baze dena ba, zaka kara tinzira shine, na fuskance shi yanada mataukar saukin kai, na gane hakanne a zuwan dasu Hanan suka danyi, Hanan gashi sa'ata ce, tafini tsiwa amma yana sakarmata fuska har yayi mata wasa, ita bata masa rashin mutunci kamar ni, shiyasa nima na sassauta yi masa wulakanci,
Amma babu soyayya tsakanin mu, ina fatan kin gane"
Mikewa tsaye Nana tayi tana shirin fita ta waigo tace
"Naji amma ban yadda ba" Nana ta fice daga dakin, tunani Jalila ta dingayi kozata gano wani dalili ne yasa ake kallon soyayya ce tsakanin ta da Jalal amma bata ganiba share wannan tunanin tayi ta mike ta fito itama domin neman abunda zataci dan ba karamin yunwa takeji ba.
Koda ta duba kitchen ba'ayi girki ba bakomai tayi tsaki ta fito daga kitchen din.
Daki takoma ta hado goldenmorn dinta ta fito farfajiyar gidan domin shan iska, tasamu kujera ta zauna tana cin Abincinta, Abba takira a waya yakara tabattar mata da gobe Insha Allah ze dawo, ji take kaman ta Jawo gobe Abba yadawo dan ta kagu ta dau mataki akan Naja.
Tanata wannan tunanin aka kira wayarta, A zatonta Ahmad ne amma se taga bakuwar lamba dagawa tayi tasaka a kunnenta tareda yin Sallama
Caraf taji matar ta Ambaci sunan ta "Jalila yakike ya gida?"
"lafiya kalau Alhamdilillah"
"Antyn Jalal ce, nasan baki gane me maganar ba"
Murmushi Jalila tayi tace
"yi hakuri Anty ban dau muryarki bane, ya gida ya kukaje gida ranar"
"lafiya kalau nasan baki dauki muryata bane, Jawwad nakira nace ya turomin lambarki mudinga gaisawa, ya mutan gidan naku?"
"lafiya kalau Anty, yasu Mahmud?"
"Ahha Mahmud Nana zaki tambaya shi, muntafi da kwana uku yakoma U.K"
"Allah sarki, aikam kullum suna tareda Nana a waya"
"Aikam naga shi can nasa hankalin ya karkata, se fatan Allah ya tabattar da alkhairi"
"Hakane Ameen ya Allah"
"Jalila ya Amanata dana bar miki?"
Dan murmushi Jalila tayi tace
"Yana nan Anty"
"Kundena fadan dai ko?"
Murmushi Jalila takumayi tace "Anty kenan"
"Au kunya na baki? Jalila bamuda kalaman dazamuyi Amfani dasu gurin gode miki akan namijin kokarin da kikeyi keda Jawwad akan Dan uwanmu mungode Allah yasaka maki da Alkhairi"
"Haba Anty meye wani abun godiya kuma? Ni banga wani abu da nakeyi ba"
"inke baki ganiba mu mungani ai, ko iya yanzu kin taka rawa gurin canza abubuwa dayawa a tareda shi, munyi waya dashi yacemin daze bar kasar nan kika hanashi"
"hmm sa'a kawai nayi, nazata ma ze min duka, Allah yakara shirya shi, nima nagani ya rage Abubuwa sosai"
"Ameen Jalila, haba baze iya dukanki ba ai, he respect you fiye da yadda kike tunani, ki kulamin da amanata Jalila, inaji a jikina abubuwan da Jalal yake zezama tarihi sanadinki"
"Allah yasa, Munagodiya Jalila, Allah ya jikan magabatanki"
Jalila ita bataga me tayi ake mata wannan godiyar ba, Jalal din da banda fada ba abunda ke hadasu, dan haka Tace
"Anty yaushe zanzo abani turaren maiduguri ne? "
"Kibari in Aurenki yazo har kano zanzo in hadaki, kamshi sekin gaji, Allah ya nunamin Aurenki"
Dariya Jalila tayi ta kashe wayar, Antynsa tanada saukin kai, gata da abun dariya, Amma ita bataga me tayiba daza'ayita yimata wannan godiyar ba.

Washegari da safe Jalila bata tafi makaranta da wuri ba, seda tagama gyara gidan dan kusan kwana biyu Naja bata gidan, Halima dama Maama ta dade da sallamarta, Manu direba be dawo daga kai Nana ba, tunda ita Nana da wuri ta tafi school yau,
Taita gyaran gida, da kokarin dora girki saboda dawowar su Abba, be kamata abar gidan bakowa ba gashi ba'ayi girki ba.
ta fito ta leka part din Jawwad, taga inya tashi ta kaimasa Abinci, Amma ta hango Jalal yana shan sigari, Jawwad kuma baya palourn, da niyyarta ta fadawa Jalal bakar magana amma tafasa ta shiga palourn. Batayi sallama ba unexpected ya daga kai ya ga Jalila, hade rai tayi sosai taki kulashi shima be kulata ba, ta duba ta kalleshi tace "Ina Yaya Jawwad?"
"ki duba mana" yabata amsa a takaice
"Ina zan duba?" ta tambayeshi a ransa yace "lallai yarinyar nan kyaleta yayi bekuma kulata ba yanata shan sigarinsa, tambayarsa takuma yi
" wai yana ina? "
"Zoki duba rigata kona sashi a ciki"
Bude baki tayi tana kallon sa, Jalal dan rainin hankali ne, amma ta shareshi ta dakko wayarta takira Jawwad be dauka ba, tsaki ta danyi taje tayi knocking kofar bedroom din Jawwad amma ta tarar yana bacci. Mayarwa tayi ta rufe ta juyo zata fita, Amma Jalal bashida niyyar dena shan taba, gashi yana kallon boom TV ne music ne kawai yake tashi, yana shan sigarinsa yana lumshe ido, ya jingina a jikin kujera. Dan girgiza kai tayi tazo gabansa ta tsaya ta dauki remote ta mayar saudi qur'an, bude ido yayi ya kalleta sannan yace "Meye haka?"
"Abunda ka gani" ta bashi amsa
"mayarmin inda take da farko"
"Bazan mayar ba" dago Jan idonsa yayi yana kallon ta, wani tunani tayi a ranta, ta fuskanci fitsarar da rake masa baya sashi dena abunda yakeyi, dan haka tace
"Ka karyane? Da safiyar nan kake shan sigari, kamanta me likita yace maka ne? Kobaka son lafiyar kane?"
Shiru yayi ya dauke kai, ba karamin haushi takeji tana masa magana ya mata banza ba amma ta dake tace
"Am talking to you, kamanta you said you want change, and i promise to help you out, please badanni ba a kashe sigarin nan please, na zata dena mu'amalarka da wannan jakin Jejen zesa ka canza kadena shaye2, amma meyasa har yanzu baka dena ba?"
Juyowa yayi yana kallonta, tayi kalar magiya, a hankali yace
"ba lokaci daya nafara shaye2 ba, don't expect me to stop it at once, Jeje ya dade yana cutar dani, na dade ina shaye2 bazan iya dena wa lokaci daya ba"
Tausayinsa ne yakamata, dan haka tace "I understand, kadena sha dayawa, a hankali zakaga ka dena" gyada mata kai kawai yayi, ta dan kalleshi maganar zahra ta tuna, "wani handsome guy"
Ba karya Jalal yanada kyau, inama ba ya wannan shaye2, da seyafi haka kyau, Amma tana fatan Allah yasa abunda ta shirya akansa yayi tasiri ya dena shaye2.
"inaso kamin wata Alfarma"
"fade ta Allah yasa zan iya"
"zama ka iya, ba me wuya bace ba"
"inajinki"
"Dan Allah kadena saka sarkan nan, you are Muslim, bekamata ace kana yawo da itaba, da dinma nasan saboda Jeje ne kaima ka kwaikwaya please ka cireta"
Kallonta yakeyi amma bece komai ba, can kuma ba tareda ya cire sarkar ba yace
"meyasa idan aka kirani da dan shaye2 kike jin haushi bayan kema kina gayamin? Dan shaye2 mara tarbiyya wanda ya raina iyayensa, idan wani ya gayamin kinajin haushi, Amma kekina gayamin"
Gaba daya taji jikinta yayi sanyi, har bataso ta tuna irin bakaken maganganun datake masa abaya, musamman idan ta tuna labarin Rayuwarsa tabbas tayi wauta, amma tace
"Waye ya kiraka da dan shaye2 naji haushi?"
"mutane dayawa, bari in tuna miki daya, Oga KB mahaifin Faruk, ban taba tunanin yadda kika tsaneni a wannan lokacin ranki ze baci dan anci zarafina baa"
"har yanzu kanajin haushin abunda nayi maka abaya ko?
" ko kadan gaskiya kika fada ai, banida tarbiyya, ban cancanci zama
Abokin yayanki ba kaddararsa ce tareda tawa shi.......
"Enough dan Allah, wannan abune daya riga ya wuce please"
Kallonta ya kumayi sannan yasa hannu ya cire sarkar wuyansa yace "Insha Allah nayi alkawarin bazan kuma saka sarka a wuyana ba"
Murmushi tayi "Are you serious"
"dagaske nake miki"
"kai gaskiya na yadda you want change, Allah ya shirye ka da gaggawa" murmushi yayi yace
"Ameen ya Allah"
daga nan ta mike tayi waje a ranta tace
"da haka Insha Allah kafin inyi Aure seka dena shaye2 in Allah ya yarda"
Yau fasa zuwa school tayi ta zauna ta shirya Abinci saboda dawowar su Mummy, bayan tagama ta kaiwa Jawwad nasu, ta gyra ko ina a gidan se kamshi yakeyi.
Bayan tagama komai ta zauna tana tilawar Alqur'ani, wajen karfe daya Abba suka dawo gida, ta dinga murna tana musu barka da hanya, duk hassadar mutum yasan gidan nan ya sha gyara amma Abba ne kawai ya yaba, Maama nunawa tayi bataga ma me akayi ba.
Bayan sunyi salla ta kawo musu Abinci. Takoma dakin su.
se la'asar Nana ta dawo daga school nan ta dinga murna su Maama sun dawo, Jawwad seda magariba ya shigo cikin gidan yayiwa Su Abba barka da dawowa, wannan karon

Please Login or Register in order to submit comment