Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana mikewa tsaye, sukayi Sallama ta tafi dakinta.

Bayan tafiyarta Abee yace "Kuna ganin raba yaran nan yanada wata fa'ida ne? Yana can matar tana nan"

Anty tace "Eh mana, muna so mugane dagaske yana sonta ne kokuwa?"

Abee yayi murmushi yace "Lallai kun manta waye ďan naku ne, shikenan Allah ya tabattar da alkhairi, Amma nayiwa Jalal murna samun yarinyar kirki kamar ta, tanada hankali sosai"
Haka dai suka cigaba da tattaunawa.

Jalalila kamar kullum ta gama wannan wankan turaren, ta shirya a cikin wata doguwar riga, dayake Anty sunyiwa Jalila sayayyar kayan sawa dana kwalliya tana kan wani karamin kujera tana gyara gashin ta.
Husnah ce ta shigo dakin tana murmushi tace

"Maigidanki yana hanya, broz Jalal zezo ba sanarwa ba komai, kuma nasan badan ke ba bazamu ganshi ba, tashi muje ayi masa girki, Anyiwa me kitso waya tana hanya, ki taso muje"

Hade rai Jalila tayi tace "ba wani girki da zanyi, kuma ni ku kyalemin kaina a haka"
Husnah tace
"Haba Sister meyasa haka ne?" (nikam nace baki san halin Jalila da taurin kai ba)
Jalila tace "wai meye Amfanin inta bawa kaina wahala akan wanda be damu dani ba? Watana daya da kwana Goma a gidan nan ko ta waya baya kira balle yaji ya nake, seni zan ta faman wahala akansa"

Ajiyar Zuciya Husnah tayi tace

"Kina da gaskiya Jalila Amma hakurin dazakiyi yanzu baze kai na baya ba, ki bari ki kama shi a hannu, daga nan seki rama, taso muje su Mummy suna parlour"

Jalila bata da zabi sena ta mike tabi bayan Husnah, suna zuwa parlour Hajiya Salma tace

"Yawwa Jalila, Jalal yayi waya yakusa isowa maiduguri, me kitso tana hanya, dama lallanki jiya akayi shi, in an gama kitson kafin ya karaso ayi masa girkin.
Jalila ta samu guri ta zauna ba tareda tace komai ba, Husnah ta zauna a kusa da ita tana mata magana kasa2

"please sister idan yazo karki hade masa rai haka, karki biye masa dan Allah, ki bawa mara ďa kunya"
Ita dai Jalila jinsu kawai take.

Tunda Daddy ya tafi be kara dawowa Nigeria ba, Mummy tarasa me yake mata daďi, in dai Jalal ya zauna da yarinyar nan to zata kwace mata shine gaba daya, dan tun kafin ya aureta ma yana sonta tunda yanajin maganar ta, tarasa ta inda zata bullowa lamarin, gashi a yanzu tasan bata isa taje maiduguri tayi musu tijara ba.


Kafin Jalal ya karaso har angama yiwa Jalila kitso, kitso akayi mata kanana sosai, gashi hannunta ya sha lalle, duk inda ta gifta kamshi take, ga fatarta ta kara kyau se sheki take.

Anty tace " Jalila me yakamata ki girkawa Jalal ne? Mara nauyi sosai tunda naga alamar shigowar dare zeyi"
Dan zumbura baki Jalila tayi tace "befiye cin Abinci da daddare ba yafi shan tea ko fruit, wani lokacin koya ci Abinci seya sha tea da daddare" ta fada tana dan tura baki cikin ko in kula

Boye dairiyar su sukayi, banda Husna da seda ta dara, tace "Ya akayi kika san haka?"

"Nike musu girki shida Yaya Jawwad a gida" tabata amsa

Anty tace "Ke Husnah ina ruwanki ne? Jalila ki dafa masa abunda kika ga ya dace kawai"
Jinjina kai tayi ta tafi ďakinta.
.

Seda ta tafi sukayi dariya, Hajiya Salma tace "Kai lamarin yaran nan sesu, ni ban san wanda yafi wani taurin kai a cikin su ba, ana so ana kaiwa kasuwa"
Anty tace "Jalal yafita taurin kai, bafa yanzu yafara sonta ba shi, Jalal ya dade yana sonta, nasan komai, Dan yaga ya samu yanzu shine yake basarwa kaman be damu da ita ba"

Hajiya Salma tace
"Aike ta hannun damansa ce kinsan komai akansa, Allah ya daidaita tsakani"

Suka Amsa da Ameen

Lokacin sallar magariba Jalal ya iso gidan, ya sha tafiya dan a mota yazo ya gaji sosai, Jalila bata san ya karaso ba, har bayan sallar isha'i tana palourn Abee yana mata bayani akan wani littafi da yake son wallafawa, Husnah tana gefe tana dan tsoma musu baki lokaci zuwa lokaci, zaman da Jalila tayi da su tafara gane yarensu kadan2, kaman gaisuwa da yaren.
Suna hira kai kace 'ya da ubane, Anty ta shigo palourn tace

"Jalila kina nan, tun dazu Jalal ya iso fa, nazata kina can kina shiryawa ne, kije ki shirya ki kaimasa Abincin"
Jalila ta dan langabe kai tana kallon Anty. A ranta tace "Sekace wani mijin kirki ko wadda zata biki anata in shirya, bayan nasan ko kallo ban isheshi ba"

Abee ya kalli Anty yace "Madam jeki zamuyi magana da' yar auta ta"

"to shikenan nidai ayi Sauri, in ba sokuke yayi zuciya ba ya tafi" ta fada tana shirin barin palourn tareda yin murmushi, Ameera tana zaune bata fita ba.
Abee yace
"Jalila tambayar ki zanyi, ki gayamin tsakani da Allah, in dai kin baban dani ki gayamin kina kuwa son Jalal?"
Taji ya mata tambayar ba tareda ta shirya jin hakan ba.

Hade fuska ta danyi tace "Ni dai ban sani ba ko ina sonshi, shima fa baya sona" ta karasa maganar kaman tana shagwaba
Fuskarta ya kalla, Akwai alamar kuruciya sosai a tareda ita, yarinya ce me tunani irin na manya, Amm lokuta da dama kuruciya tana dawainiya da ita.

Yace "Shikenan daughter Allah ya daidaita ku, ki cigaba da hakuri zaki fara sonsa, Mijin kine yanzu, ki manta da halinsa kinemi Aljannar ki, kuma insha Allah komai ze wuce"
Jalila tace "to Abee nagode" harzata fita Husnah tace "Jirani muje in miki kwalliya, nasan idan na kyaleki ba zakiyi ba"
Ta tasa Jalila a gaba zuwa ďaki, ta ďakko mata wani material baki da adon jan flowers, riga da skirt ta mikawa Jalila ta karba tana zumbura baki ta saka, tayi kyau sosai, Husnah ta bata turaruka ta shafa, kamshi dai kam ya riga yagama kama jikin Jalila a gidan nan, Husnah tace
"bari in miki kwalliya"
"ni ba wata kwalliya daza'a yimin"
"Jalila ya hakane? To sa kwalli da jan baki mana"
Jalila ta saka kwalli se jan baki Ja, tasaka kwalli, tayi kyau sosai, Husnah ta bata karamin gyale Ja akanta, Jalila ta kalli kanta a mudubi, kayan nan sun kamata sosai ta kalli Husnah tace "Nikam gyalen nan yayi min karami gaskiya, ki bari in saka babba"

"Haba Jalila, gurin mijinki zaki fa, Mijinki ne ba wani ba, in kuma kinki in barki da su Mummy"

Husnah tasata gaba zuwa Kitchen ta shirya mata kayan Abincin a tray ta rakata har kofar palourn da Jalal yake tace
"please Jalila don't mess up, karki bani kunya dan Allah"
Jalila ba tace komai ba ta shiga gabanta se faduwa yake yi, Sallama tayi sannan ta shiga, bata tabaccin ya amsa sallamar nan tata. da farko dakin kamshin turarensa yakeyi, Jalila na shigowa kuwa temperature dakin ta canza zuwa kamshin turaren jikinta, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, kanan kayane a jikinsa amma yayi kyau sosai sumarsa se kyalli take, duk ya dena saka wannan kalar dayake wa gashinsa, ya dora kafarsa akan center table, ko a ina zata ajiye tray din oho, ta gefen ido ya dan saci kallonta, tana zuwa bata kula shi ba ta ajiye tray din a kasa, ta juya zataje ta zauna hakan ya bashi damar kare mata kallo, tubarkallah she has a very beautiful heart and body structure, Jalila tana da kyau ga kyakywan surar jiki, ga zuciyarta me matukar tausayi, matsalarta taurin kai da Izza wani lokacin.
Taje ta nemi guri ta zauna a kujerar da take kallonsa ta dora kafa daya kan daya tana kada kafa tareda dauke kanta gefe tana wasa da yatsun hannunta.
Jalal a ransa yace 'Tsabar wulakanci ko ta gaisheni kota ce min ya hanya ba ruwan ta dani, hakan na nufin dagaske bata sona ne? Ko kuma tsabar rigima da taurin kaine? " Jalal ya gaza gano amsoshin tambayoyin sa, to bata kulashi da sannu da zuwa ba ma balle yasa ran zata zuba masa Abincin.
Kallon ta ya kumayi, kayanta cif jikinta ga mayafin iyakarsa wuyanta, hanun nan yayi kyau da lalle, kanta ba dan kwali dan haka yana iya ganin tsagar kanan kitso dake kanta.

Itama Jalila a ranta mita take "tsabar wulakanci koma ya tambayeni ya nake, bayan tafiyar sa ya na karke, ya tafi ya barni ba lafiya koya bugo waya yaji ya jikina, ya sani a gaba da kallo yaki cin Abincin in baze ci ba ni in tafi, mtseww ta danyi tsaki, tsakin ya fito fili ba tareda sanin ta ba.
Saurin dagowa yayi suka haďa ido ta basar.
Mikewa yayi ba tareda ya kalli inda Abincin yake ba ya mike ze fice, itama ta mike da sauri tasha gabansa suka tsaya suna kallon Juna, lokaci na farko da suka kasance tare tun bayan daura Auren su
"lafiya meye haka?" ya tambayeta
"ya zan kawo Abinci ka tashi baka ciba? Salon in koma ayita tuhuma ta"
"in sun tuhumeki kice su koya miki yadda ake kula da miji, dan baki iya ba" Ta dan yatsina fuska ta kalleshi

"Waye mijin? Aini banga miji anan ba, kaima yakamata a koya maka yadda ake kula da mace dan..... Se kuma tayi shiru ganin yadda ya kura mata ido, Ashe fa yanzu mijinta ne, ba kowace magana yakamata ta gaya masa ba

"Ni kike cewa bakiga Miji anan ba ko?, Nagode sosai, matsa kibani guri in wuce"
Hanya ta bashi ya fice daga dakin, bata bi ta kan kayan ba itama tayi waje abunta.

Washegari ma da Safe Aka sa Jalila ta kai masa Abinci, haushin taki kulashi jiya yasa beci Abincin ba yakuma barinsa.
Yana fita ya tafi gurin Abee, bayan sun gaisa Abee yanata tsokanarsa, Jalal yace
"Abee so nake kasa baki su kaimin matata, ko in dauketa mu tafi basu sani ba"

Abee yace "A'a baza'ayi haka ba ai, kwantar da hankalinka, ko gobe kake so za'a kaimaka ita zan saka baki suba ka ita, na goyi bayanka tunda Daddynka yana jin nauyinsu, ina dalili kanada Aure amma sun barka kana ta fama sun rike maka mata" haka Abee ya lallaba Jalal ya tafi.

Yaje yasamu Anty yace mata "kinga tun wuri kubawa yaron nan matarsa yana son abarsa, yamuku kawaici amma kunki ganewa"

Anty tace "Abee Akwai dalilin da yasa muka riketa anan ne"
"A'a Ku bashi matarsa kawai, in baso kike kiga tafara miki laulayi a gidan nan ba, sannan ku kwasheta ku kaita"
Zare ido Anty tayi "Haba dai"
"Eh mana, yanzu da muka rabu da shi yake gayamin insa baki ku bashi matarsa"





Aimin hakuri fa rashin posting akan lokaci, abubuwa sunyimin yawa, adinga min uzuri nagode da kulawarku

Vote and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣2️⃣ 105

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _



Zare ido Anty tayi tace "gaskiyane Abee, tunda ya iya budar baki yace a bashi matarsa he mean it, zanyiwa Anty Salma magana gaskiya, a bashi iga suje can su karata, tunda be san abun Arziki ba"

Abee yace "gara dai kuyi tunani, wannan ba mafita bace ku bashi matarsa kawai"


Tunda Abee ya bashi goyon baya A ranar Jalal ya shirya ya tafi kano ko sallama basuyi da Jalila ba, dan in dai suka hadu fada zasuyi.
Yayi waya da Daddy ya gaya masa yana son zeyi magana dashi, Daddy yayi masa Alkawarin zezo Nigeria su hadu a kano.



Ba zato ba tsammani Ilham ta dawo taga motar Jalal a harabar gidan, ai a guje takarasa cikin gidan ta nufi dakin Mummy tana kwala mata kira,
"Mummy Kinsan Jalal ya dawo kuwa?"
Mikewa Mummy tayi "dagaske ko wasa"?
"Wallahi dagaske nake, ga motarsa can"
Jinjina kai Mummy tayi tace "Shikenan rabu dashi, nasan tunda yazo Akwai abunda ya kawo shi, kyleni da shi kawai"

Ilham ta koma dakinta tana cigaba da tunanin wani mataki Ummanta ke shirin dauka akan wannan lamarin, Itakuma me yakamata tayi?
Wasa2 kwanan Jalal uku da dawowa amma sam Mummy bata sa Jalal a idonta ba, da kanta taje dakin Jalal amma baya nan.
Ilham ma duk yadda taso taga Jalal bata ganshi ba, ko ina yake tafiya oho?.


Bangaren Jalila kuwa sekuma shan gyara takeyi, basu gaya mata Jalal yace zasu koma kano ba.


Kwanan Jalal hudu a kano sannan Daddy ya dawo, koda ya dawo babu wata tarbar Arziki daya samu daga Mummy se mita da masifa, Bebi takanta ba ya cigaba da sha'anin sa, babban abunda yake kular da ita kenan, tasa shi agaba taita masifa Amma ya kyaleta yaki kulata.

Ranar da Daddy ya dawo da daddare Jalal ya shigo, ba kowa a palourn dan haka ya wuce part din Daddy, shikansa Daddy yaji dadin ganin Jalal,

Daddy yace "Ango, Ango se wani kyau ka keyi, alamu hankalin ka a kwance"

Jalal ya dan bata fuska yace

"Ina wani hankalina a kwance yake, Kawai su Anty sunje sun rike ta a can gurinsu ko mene amfanin hakan oho?"

Daddy yai murmushi yace "Tunda sukayi haka Akwai dalili"

Jalal ya dan hade fuska yace
"koma meye dalilin nasu ni munyi magana da Abee zan dakkota tazo ta tare"

"Jalal meyasa kai haka? Zasu ga kaman bakayi musu kara ba"

"Daddy sati guda da komawa makaranta yakamata ace ta koma itama, sannan kasan in dai da Auren nan idan nazo kano bani da masauki, bani kwanciyar hankali saboda masifar Mummy indai nazo gidan nan, nasan bata son Auren nan, nikuma inason abuna, kaga ko nazo Kano a gidana zan sauka baseta ganni ba bazan zo mata gida ba"

Murmushi Daddy yayi yace "koma dai meye she's your Mum, yakamata ka dinga mata uzuri sannan ka dinga hakuri da ita"

Jalal yace
"Daddy maganar gidan da zan zauna ne yasa nazo Kano fa"

"to wane gidan zaka zauna, gadon kayan zaka koma kokuma yaya?"

"No bazan koma gadon kaya ba, zamana a gidan nan zena tunamin abubuwan da suka wuce masu batamin rai"

"to ya kake so ayi?" daddy ya tambayar yana bawa Jalal attention dinsa

"gida zan siya a tarauni, a can zan zauna in danyi nesa daku, bana son yawan fitina ko hayaniya, Gobe in Allah ya kaimu se muje ka tayani zaban gidan"

"hmm Jalal kenan, to ai tunda bani zan zauna ba, kai da ita matar taka yakamata ku zabi gidan da kuke so"

"Kyaleta kawai duk gidan dana zaba baza tace beyi ba"

"to shikenan ina fatan kun daidai ta kanku babu matsala"

"karka damu Daddy, in Allah ya kaimu gobe muje a siyi gidan, ka gayawa Abba, next week Insha Allah in basu kawo ta ba, zanje in dakko ta"

Daddy kallon Jalal kawai yake, jalal din maganar sa yake kansa tsaye kuma hankali kwance ba wata kunya ko makamancin haka a tare da shi.
Suna ta hirarsu ba zato ba tsammani sega Mummy ta shigo ďakin, seda ta danyi turus ta tsaya, ganin Jalal da tayi kanan kayane a jikin Jalal kaman yadda yasaba sakawa, Amma abun mamaki dogon wandone har kasa a jikinsa, da riga me dogon hannu, wuyansa babu sarka, sannan babu wannan askin banzan da yakeyi kuma ya sawa kan color duk babu, yayi kiba abunsa kuma fuskarsa ba laifi a sake yana murmushi, sabanin da da kullum fusakarsa a murtuke.

Idan lissafinta dai2 ne kimanin watanni shida bata ganshi ba ko a waya baya kiranta, dama ina ta kai matsayin da Jalal ze aje lambarta balle ya kirata.

Jalal yace "Daddy in aka siyi gidan se a sai furnitures ma in saka, kayan kitchen ban san kansu ba maybe su Anty sa saimata, kokuma muje da ita ta siya"

Wannan statement din data ji yafi kowanne bata mata rai, su Jalal basu san ta shigo ba, dan sun bawa kofar baya, nan Take ta shakunu ta karasa shigowa dakin fuskarta babu walwala ta zo ta tsaya.

Jalal na ganinta ya maze ya jingina da jikin kujera ya dora kafa daya kan daya
Ta kalli Jalal tace

"Sannu mara mutunci wanda be san ciwon kansa ba, Jalal saboda ba ka maidani komai ba tsawon watanni shida ban saka a idona ba, kuma saboda kai ba dan mutunci bane har a hada kai ai maka Aire ba tareda izinina ba, saboda munafunci baka tuntubeni ba tunda akayi Auren nan ka hada kai da dangin ubanka kayi tafiyarka inda ta zaba maka, se yau ka dawo kana zaka saimata gida da furnitures, kudin na ubanta ne? Ko shi ya tara maka? Wallahi Jalal se an kashe Auren nan, ban yadda ka zauna da yarinyar nan ba, seka saketa kuma seka baro wannan tsinan nan aikin data samo maka a lagosa, tunda ba ita ta haifamin kai ba"

cikin masifa Mummy take wannan hakilon Masifar, har Daddy ya fusata zeyi magana Jalal yace

"No Daddy yi hakuri, ban sanka da fada ba, kayi shiru kawai, bari zanje in dawo" Jalal ya mike ze fita, Mummy ta kuma fusata tace
"Nizaka mayar 'yar Iska ina maka magana, Wallahi Jalal in baka saki yarinyar nan ba sena maka baki" cak Jalal ya tsaya ya waigo yana kallonta.
Daddy dafe kai yayi, dan shi a rayuwarsa sam baya son tashin hankali.
Jalal yazo gaban Mummy ya kalleta yace

"Mummy idan kikamin baki akan na wasu zaki ďora, inkin min baki baze dameni ba, tunda wanda yake dawainiya dani be ishekiba, baki da wata cikakkiyar hujja na kin Aure na, bazan saki Jalila ba saboda ina sonta, kema soyayya ce tasaki zama da mahaifina, nima na Auri wadda na rayu da sonta, baze yuwu amin Auren dole ba, tunda kema bashi aka miki ba"
"Jalal ni kake gayawa haka?"

Kai tsaye yace

"Yau na fara gaya miki gaskiya? Bazan Auri macen da bana so ba saboda san zuciyarki, da in saki mata ta gara kimin bakin, dama can a lalace nake, in kika min baki kinga dorawa zanyi"
Yana gama maganar ya fice.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji un, nashiga uku, dan dana haifa ya tsaya a gabana yana gaya min wannan maganganun, Habib Jalal ua zabi mace akaina da na haifeshi, ban taba zaton haka ba, tunanina Jalal shaye2 kawai yake, yaushe Jalal ya fara son Jalila da har yake gayamin wannan maganar akanta, tun yanzu, wallahi na tsani yarinyar nan"

Daddy yace "Khadija be kamata kiyi wannan maganar ba, bari in tuna miki wani abu, Soyayyar da nake miki tasa na zauna dake tsawon shekaru, na fifita ki fiye da Ahalina, kika rabani da kowa nawa, Ashe ba dadi, na fuskanci Soyayya bazata yiwa Jalal da wasa ba, dan haka ki shirya sa hannu ki karbi irin abunda kika aikata kema"
Mummy cigaba da rusa kuka tayi tama fadin

"Wallahi baze yuwu ba, ni na haifi dana ba'a isa amin iko da shiba, babu wadda ta isa ta juyamin yaro, nasan wannan makircin Salma ne, zata ďau fansa a kan ďana, tana tunanin zata mallake min ďa saboda wannan banzan shirin nata? Wallahi bata isa ba" tuni Idon Mummy yayi jawur tana kuka tana masifa, Daddy ba shi da zabin da ya wuce yabar mata ďakin, dukda yadda yakejin kukan nata a zuciyarsa, Amma wannan faďan rashin gaskiyane kawai take yi.



Ilham kuwa tana kitchen tana hada abunda zata ci, sama bata san Jalal ya shigo part din ba, tana daga kai ta window taga shigar Jalal part dinsa, gabanta ne ya fadi, ya wani kara kiba, wani tunani ne yazo mata, hakan yasa ta fito da sauri ta tafi part din nasa, tana zuwa ta tarar baya palourn dan haka kai tsaye itama ta bishi bedroom din nasa, Amma tana zuwa ta tarar har ya shiga toilet, gefen gadonsa ta samu ta zauna ba tare da fargabar komai ba, tayi a kalla mintuna Ashirin sannan ya fito sanye da gajeren wando jikinsa babu riga se karamin towel yana goge ruwan jikinsa, Sam Jalal be kula da Ilham ba, yayinda Ilham ta daskare a zaune tana karewa surar Jikin Jalal kallo,
Gaskiya Jalal ya kai a so shi koba dan dukiyar sa ba, ko ina na jikinsa kwance yake da gashi tun daga kansa har kafafunsa, dogone jikin sa a murde yake, dama ga jikinsa yana cin karfe, kallo daya zaka masa kasan namiji ne me matukar kwarjini, yana ďaga kai yayi ido hudu da Ilham zaune akan gadonsa, a fusace yace "Ke meye haka? Uban me yakawo ki dakina a daren nan? Ta shi kifita ki barmin daki"

Mikewa Ilham tayi ta tako gaban sa ta tsaya tana kuma kare masa kallo, "Jalal dagaske kayi Aure ko?"

"Tambayata ma kike? Ban sani ba, fita ki barmin daki"

Towel din hannunsa ta karba, ta ajiye ta zuba masa ido, Hawaye ne ya fara bin idonta

"Jalal namaka son da ban taba yiwa wani namiji makamancin sa ba, Jalal why? Ina sonka Jalal, meyasa zaka Auri wata bani ba, Wallahi ina sonka, Jalal ka shmmace ni, ka Auri yarinyar da nafi tsana a rayuwata, Haba Jalal meyasa kamin hakan?"

"kina son Jalal ko kina son cutar da shi? Kina sona nikuma na rayu da son yarinyar da kika fi tsana, saboda a duniya a yanzu babu wanda ya gwada min so kamar yadda tayi, I love Jalila with all my heart, ba abunda bazan sadaukar akanta ba, i am sorry, kema Allah yabaki me sonki"

Wani kululun takaici ne ya tokare kirjin Ilham, Amma ta maze, hannu ta mika kirjin Jalal zata shafa kirjinsa amma ya rike hannunta, ya girgiza mata kai,

Ya dan lumshe ido ya bude yace

"Abunda yasa nake kara Son Jalila kenan, ba ruwanta da abunda ba nata ba, karki tsallake iyakar ki, karki taba mata miji kin san halin ta dai base na gaya miki ba, Abunda kike hari tsawon lokaci ya zama nata, a gaskiya ta miki ba dadi, ta rusa shirinki gaba ďay" ya karasa maganar yana ďanyin murmushin mugunta, sekuma ya haďe rai yace

"malama get out from my room"
Ilham tace "Amma Jalal"
"ki fitar min daga ďaki malama, ko ba kya banbance abunda ya dace da wanda be dace ba? Kifita bana son ganinki" Jalal ya katseta

"Yaya Jalal..."

"kifita nace ko in miki Illa, natsaneki bama son ganinki, ki fita ki bar min daki ko in kakkarya ki"

Yadda yakoma yana maganar a fusace ya sa Ilham ta fita da sauri ta bar dakin. Wani dogon tsaki Jalal ya ja ya saka doguwar Jallabiya ya kwanta.

Ilham kwana tayi tana

Please Login or Register in order to submit comment