Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo dasu, tai salla ta shiga gyaran gida, saboda duk yayi kura kusan wata guda kenan bakowa a ciki, ta share ko ina tai mopping ta wanke toilet da glasses na window harta gama tana tunanin kayan nan.

Seda akayi sallar magariba Jalal ya dawo hannunsa da ledoji, a parlor ya tarar da ita tana kallon zee world

"Waike ba kya gajiya ne, daga dawowarki kin tsiri aiki"
Batace komai ba se murmushi da tayi ta karbi kayan hannunsa

"ina ka tafine haka?"

"na tsaya nayi salla ne, sannan naje nayi mana siyayya abunda zamuci base kinyi girki ba"

Jalila ta dan numfasa tace "Akwatinan me ka ajiye a dakina?"

"Nakine na lefe ko ba suyi miki bane?"

"Amma Jalal....

Yatsan sa ya dora akan lips dinta yace

"Shhhh bana bukatar sharhi, tuhuma, ko godiya, a cigaba da yimin kwalliya kawai, babu bukatar kimin wata godiya dakko plate da cup muci Abinci"

Jiki a sanyaye ta dakko plate tazo ta ajiye ya zazzage ledar kaza ce da dogayen kwalayen madara, ya zuba a plate ya mika mata yace

"feed me"

Gaba daya ya lura a tsorace take da shi yau, da dane da yanzu watakila ta haye cinyarsa tana tsokanar sa, Amma yau ko kusa dashi taki zuwa karshe dai shi ya dinga bata amma taki ci se kyaleta yayi.

Bayan ta idar da sallar isha'i tai wanka ta haye gadon ta tai kwanciyar ta dan tana jin bacci sosai harta fara bacci taji an kunna wutar lantarkin dake Dakin ta, dan rintse ido tayi, sannan ta bude a hankali ta sauke akan Jalal

Murmushi yayi yace "shine yau ko azo muyi azkar din ko? To ni nazo muyi"

Janyo bargo tayi ta shige ta rufe har kanta ta dunkunkune, ba karamin dariya ta bashi ba, ya kashe fitilar ya hau kan gadon yace
"ni kike gudu haka ko Baby?, fitowa zakiyi"
Ya fara kokarin janye bargon nata,
"nifa bacci nake ji ka kyaleni"

Banza yayi mata seda ya cirota daga bargon, gaba daya Jikin ta yayi sanyi,

"Jalila ni kike gudu haka ko? Hada shigewa bargo, ance ana sona amma ana guduna haka akeyi, burina ya cika ummi na ta warke, Baby na ta hadu da Ummin ta, yakamata a tausayamin haka Baby na azabtu fa"

Haka yai ta mata surutai, Bata gama firgita ba seda taji abunda Jalal din ke kokarin yi ya shallake tunanin ta,
Yau dai Jalila baki ya mutu, ko kwakwaran motsi takasa se kuka da kiran Ummi, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunanin ta, seda Jalal fanshe soyayyar sa ta tsawon shekaru.
Kaman ba Jalal din nan me mugun jin kai da hade rai ba.

Bayan komai ya lafa Jalal ya rungume Jalila tsam a kirjinsa yana so yayi magana amma sam yakasa, a hankali taji jikinsa na daukar zafi fiye da kima, ganin yakasa magana yasa shi sakinta ya juya mata baya,
Ji tayi kamar ana girgiza gadon da suke kai, juyawa tayi taga jikin Jalal ne yake karkarwa, ta kai hannunta jikin sa taji kamar wanda aka hurawa wuta bata taba jin jikin dan adam yayi zafin haka ba.





Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣0️⃣113

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Da sauri ta janye hannunta daga jikinsa, da kyar ta mike zaune ta janyo rigarta ta saka, a hankali ta sakko daga kan gadon, dan duk wata gaba ta jikin ta ciwo take mata, ta kunna switch haske ya gauraye dakin gaba daya, ta kalli inda Jalal yake har yanzu karkarwa yake kamar wanda ake girgizawa, a hankali ta tako ta zauna a kusa da shi ta dan dora hannunta a goshin sa zafin karuwa yake fiye da farko, a hankali tace
"Jalal meyake damunka ne?"
Shiru yayi be ce komai ba, gaba daya jijiyoyin kansa kaman an kumbura su har jijiyoyin fuskarsa seda suka tashi, ta tashi ta debk ruwa a container da towel me kyai ta dinga tsoma towel din a ruwa tana shafa masa tareda karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, bude ido yayi yana kallon ta, seda gaban ta ya fadi ganin idon sa yana caccanzawa kaman yadda ta taba gani yayi kwanakin baya, salati ta dingayi
"Jalal ko Daddy zan kira ne?" girgiza mata kai yayi ya mayar da idonsa ya lumshe, MP ta dakko ta kunna karatun Alqur'ani ta dora akan mirror.
Ta cigaba da shafa masa ruwa, a hankali jikin sa yafara sanyi ya fara sauke ajiyar zuciya alamar bacci ya dauke shi, seda ta tabbtar yayi bacci ta mike ta tafi toilet dan gyara jikin ta, ji take kaman zata fadi gaba daya jikin ta babu kwari, ga ciwo da jikin ta yake mata, ta gargasa jikinta da ruwan dumi ta fito ta canza kaya, ta koma gurin Jalal ga mamakinta taga ya mike zaune amma har yanzu idonsa wani iri, takarasa gabansa tace
"Sannu ya jikin naka?"
Kallon ta yayi yai shiruu kaman wanda akayi wa dole yace "zan sha giya"
"giya kuma? Amma kasan gidana ba club bane ko?"
Kokarin mikewa ya keyi tai sauri tace "tsaya ina kuma zakaje? Bari in dakko maka ai inada ita"
Ya nemi guri ya zauna, ta fita ta dakko zamzam ta dawo ta tarar ya kashimgida idonsa a lumshe tace
"bude bakinka" ba musu ya bude ta fara zuba masa zamzam din nan me dauke da tofin Al'qur'ani a ciki ya dinga sha ba tareda yasan menene ba, seda ya shanye shi tsaf kawai yafara Tari abu kaman wasa ya dinga tari kaman ze shide, zuwa jimawa kuma yafara amai, wani irin abu yake amayarwa baki kirin me kauri, tun Jalila na iya gogewa ta gyara gurin harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, ta koma gefe ta zuba masa ido tana hawaye.

Seda Jalal ya kusa fita hayyacinsa gaba daya, ya dinga aman nan ba kakkautawa, sedai in yayi yayi, ta goge, yayi awa yana aman nan baya hutawar minti biyar beyi wani aman ba.

Ba Jalal ba hatta Jalila ta galabaita, ga wahalar da ta sha a hannun Jalal shikuma ga wannan rashin lafiyar, da aman ya dan lafa masa ta dakko zuma ta dinga bashi da spoon yana karba.

A hankali ta kira sunan sa "Zaujee" juyo yayi ya Kalle ta idonsa ya koma normal yace "Na'am my love"

"ya jikin naka? Kana jin wani aman ne?"
Girgiza mata kai yayi yace

"A'a bana jin aman yanzu"

"Masha Allah, yanzu yakamata kaje kayi wanka"

Ya Kalle ta ya dan kashe mata ido yace "wankan me zanyi?"
Jalal kenan yana fama da kansa amma tsokanar Jalila yake, ta tura baki tace
"nima ban sani ba"
Murmushi yayi yai kokarin mikewa amma yaji jira yana dibarsa, ya dake ya dafa bango, cikeda damuwa Jalila tace

"Zaujee anya bazamu tafi Asibiti ba kuwa? Na tsorata da abunda ya sameka fa"

"ba se munje ko'ina ba aina warke, karki damu zan shiga inyi wankan im fito"

Haka ya dake ya nufi toilet, Amma gaba daya jinsa yake wani iri garin yana juya masa, kan ya fito Jalila ta tattara kayan da ya bata da amai ta tafi toilet din parlor ta wanke su tas, ta canza bedsheet ta dakko masa wasu kayan, ta kunna burner ta saka turaren wuta saboda karnin aman da yayi, Jalal ya jima a toilet be fito ba, dan yana shiga toilet din yaji wani aman, ya kunna shower yadda Jalila bazataji karar aman da yake ba, gaba daya tausayin ta yake ji, be so wannan dare yazo musu a haka ba, wannan karon hadda jini a cikin aman da yayi.

Jin shirun yayi yawa yasa Jalila tazo kofar toilet din tai knocking tare da fadin
"Zaujee ya na jika shiru ne? Lafiya dai ko?"
Ya galabai ta amma cikin karfin hali yace

"lafiya kalau, kiyi kwanciyar ki yanzu zan fito"

Maimakon ta kwanta guri ta samu ta zauna a bakin gado tana jiran sa, seda aka jima sannan ya murda kofar toilet din ya fito jikinsa daure da towel, da sairi ta nufo shi tace

"Jalal Allah yasa ba aman ka kuma yi ba, gaba daya kammaninka sun canza dare dayan nan baka ga yadda ka rame ba"

Dan Murmushi yayi mata yace "Ashe haka ake sona aka damu dani, nace karki damu ban kuma aman ba ai, wanka nayi na fito"

Haka ta kyaleshi ba dan ta yadda ba, ya tsane jikin sa ya dauki jallabiyar da ta dakko masa ya saka, ya haye kan gado amma ga mamakin ta ya kai hannu ya kashe MP din da amon karatun Al'qur'ani ke tashi.

Kallon sa tayi cike da mamaki tace

"ya haka kuma? Meyasa ka kashe?"

"Naki nake son ji, ke zaki karanta min da sautin muryarki me narkamin zuciya ya sani nutauwa har inyi bacci"

Jalila idon ta har mannewa yake saboda tsabar gajiya da baccin da take ji, Amma haka Jalal ya kwanta a jikin ta, ta fara rero karatun Al'qur'ani cikin suratul Ibrahim da muryarta me dadin sauraro, ta nayi tana shafa sumar kansa.
lumshe ido yayi yana sauraron ta, bacci ne ya dauke Jalal, Abunda ya firgita Jalila be wuce ganin hayaki na fitowa daga hancin Jalal ba.
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" shine abunda Jalila keta nana tawa, ta shiga jero dukkan Addua da ta zo bakin ta, shikam Jalal kara kankame ta yayi yana baccin sa.
A hankali hayakin ya dena fita, mamaki ne ya cika Jalila, ta yaya Hayaki ze dinga fitowa daga jikin dan adam haka? Tana cikin tunanin ne bacci barawo yayi awon gaba da ita ba tareda ta shirya hakan ba.

Ko da Asuba Jalal ne ya tasheta daga bacci, da kyar Jalila ta iya tashi tai salla, da ta idar da sallar ko Addua ba tayi ba ta kwanta akan sallaya ta cigaba da bacci, seda Jalal ya dawo ya same ta akan dadduma a kwance tana bacci, carbin hannun ta ya zare wanda hakan ya sata bude ido Jalal yace
"kin kwanta a kasa se wuyanki yayi ciwo ko? Tashi muje ki kwanta"

Hamma tayi tareda yin miki cikin muryar kasala da jin bacci tace
"Zaujee ya jiki?"

"Aina warke ni, kece baki da lafiya tashi muje ki kwanta"

Mikewa tayi Jalal ya rike ta ya cire mata hijjabin, har kan gado ya kaita ya kwantar da ita, tana kwanciya bacci ya kuma dauke ta, zama Jalal yayi ya kura mata ido, gaba daya tausayin ta ya kama shi, ta sha wahala sosai, dan murmushi Jalal yayi yace

"Babyn Ummi ta girma, Allah karka bani ikon cutar da wannan baiwar taka ko da kiftawar ido"

Ya rungume ta a jikin sa yana shafa gashin kanta.

Ilham kam kwanan ta biyu bata gida, ta cewa Mummy za taje gidan su, Amma ba gidan ta tafi ba gurin malamin da umman ta kwatanta mata, can boarder tsakanin Nigeria da kamaru, a can ne malamin da ya yiwa Jalal Asiri yake, taita bugun cikin umman nata tana bata Labari, ta shirya ta tafi.

Mummyn Jalal tana zaune tana breakfast aka kira ta a waya, daga wa tayi tareda yin sallama
"salamu Alaikum dan Allah Hajiya khadija ce?"

Mummy tace "eh nice"

"Dama Umman Ilham ce aka wayi gari takasa tafiya, bakin ta ya karkace an kaita Asibiti amma babu kowa a gurin ta"

"Subhanallah, ina Ilham din?"

Me kiran wayar tace "Ilham bata nan"

Mummy tace "shikenan nagode"

Gaba daya jikin Mummy rawa yake yi, ta tafi part din daddy bacci yake ko farkawa beyi ba ta tashe shi.

Daddy ya tashi yace "deeja lafiya kuwa? Yana ganki a haka?"

Cikin damuwa tace "Daddy, Saudat na Asibiti wai ba ta iya tafiya bakin ta ya karkace"

"Subhanallah wani Asibitin ne?"

"Nima ban sani ba sedai muje mu gani"

Haka suka shirya suka tafi gidan Saudat daga can aka gaya musu Asibitin da take suka tafi.

Koda sukaje Asibitin idonta biyu an sama ta ruwa, bakin ta ya karkace se zubar da yawu take, fuskarta duk ta kumbura, ta kara duhu kafafun ta kamar an shanye, gaba daya halittun ta sun sauya kamar ba ita ba.

Khadija na ganin ta ta fa she da kuka tana fadin "Saudat meye sameki haka? Garin yaya haka ta faru dake?"

Babu baki sedai ido da take binsu da shi, Mummy tai kuka har idon ta yayi jawur. Daddy ne ya dinga rarrashin ta
Yace
"Wai ina Ilham ne?"
Se a lokacin Mummy ta tuna bata ga Ilham ba, waya ta dakko ta kira Ilham, ta kira ya kai sau biyar sannan ta dauka
Mummy tace "Ilham kina ina ne?"

"ina gidan mu mana"

A fusace Mummy tace "karya kikeyi, gamu a Asibiti tare da Mahaifiyar ki an kwantar da ita ba lafiya"

Da sauri Ilham tace "na shiga uku, Meya same ta?"

"ban sani ba, gidan ubanwa kika tafi"

Kuka Ilham ta fara yi tana fadin "shikenan na makara, dan Allah meya same ta?"

"in kinzo kya gani"

Se shadaya na safe Jalila tai juyi ta farka daga bacci da sauri ta sakko daga kan gado tana fadin
"Subhanallah" Jalal baya dakin ya fita
Toilet ta tafi tai wanka tai brush, ta fito ta gyara gadon sannan ta fito parlor.

Koda ta fito Jalal yana danna waya ya dago ya kalle ta yayi murmushi, seda ta dan tsorata da ganin Jalal, ya rame sosai idonsa yayi zuru zuru, Jalal ya taso ya riko hannun ta zuwa kan kujera, ya zaunar da ita yace

"good morning my Angel, ya jiki?"

Dan murmushi tayi tace
"Lafiya ta kalau ai kai zanyi wa ya jiki?"

"Kin tabattar lafiyar ki kalau?" yai maganar yana kashe mata ido.

Tura baki tayi

"ni cikanizaka canza min magana, baka tashe ni ba gashi rana tayi bamuyi breakfast ba, ya kake ji a jikin ka yanzu ka rame sosai wallahi, na damu sosai da halin da ka shiga jiya"

Jalal yace

"gani nan dai wallahi Jalila ji nake kaman bacci nayi na tashi, gani nake duk abunda ya faru a baya kamar a mafarki, kamaman an sauke min wani nannauyan abu da yake rinjaya ta a kaina, ko kuma dutse haka nake ji"

Jalila ta rike hannunsa tace

"Jalal yakamata mu tashi tsaye anema maka magani, nifa jiya hayaki na gani yana fitowa daga hancin ka fa"

"Hayaki kuma?" ya tambaye ta

"Eh hayaki, hayaki nagani yana fita daga hancin ka jiya kana bacci"

Jalal ya kyalkyale da dariya yace

"i see that you enjoyed yesterday night, bacci ya miki dadi in ba haka ba ta yaya hayaki ze fita a hanci na, mafarki kikayi"

Jalila kaman za tai kuka tace
"Jalal ba fa abun wasa bane"

Ya dan Harare ta yace
"bazaki dena cemin Jalal ba ko?"

"Yi hakuri bazan kara ba, Amma ka dau magana ta da mahimmanci"

"Jalila ki kyaleni da maganar na, yanzu na dafa tea na siyo bread bari in dakko muyi breakfast"

Riko hannun sa tayi tace

"To ko Asibiti muje a dubamin kai, ka rame da yawa jiya ka sha wahala sosai, ni nayi mamaki ma da ka iya tashi har kake harkokin ka"

Dan noke kafada yayi kaman wani karamin yaro yace

"Kece likita na ai, ni ba Asibitin da zanje lafiya kalau nake jin jikina, bayan abunda ya shiga tskanin mu ji nake kaman nasamu wani immunity ne daga gareki, gayamin meye sirrin"

Hannayen ta biyu tasa ta rufe fuskarta tace

"dan Allah ka dena wannan zancen, ni ka dakko mana kayan breakfast din ni yunwa nake ji"

"Dole inyi wannan zancen, Jalila ba haka naso daren jiya ya zo mana ba, Amma babu yadda muka iya da kaddara, A koda yaushe kokarin ki shine ganin kin tabattar da farinciki a cikin rayuwa ta, dukda yanayin da kika kasance a jiya be hanaki nuna tausayi da jin kai a gareni ba, Jalila " ya karasa maganar da kiran sunan ta, ta dago ta Kalle shi

"Allah ya saki a madaukakiyar Aljannah, kada Allah ya kawo second din dan zan cutar da ke a rayuwa ta, ina kaunar ki Jalila"

Ta amsa da "Ameen"

Ya kai bakinsa kunnen ta yace

"you deserve a gift from me in return of what you gave me yesterday"

Idan har ta biye wa Jalal ba zasu karya ba, gashi yanzu sha biyu saura, ba shida niyyar sassauta kalaman da yake zubowa, ture shi tayi ta mike taje ta hado kayan breakfast ta ajiye a gabansa.

Haka sukayi breakfast cike da nishadi da kaunar juna.

A haka cikin hirar ta su, Jalila take bashi labarin irin miyagun mafarkan da ta dinga yi akan sa a lokutan baya.
Jalal ya sha mamaki yace

"that's why I said our souls are destined to be together, ke garkuwa ce ga ABDUL JALAL"

Wayar sa ce ta fara ringing, ya sa hannu ya dauka
Muryar Daddy yaji dan haka ya kara nutauwa suka gaisa.
Daddy yace

"Jalal muna Asibiti fa"

"Asibiti kuma Daddy waye ba lafiya?"

"maman Ilham ce, bata da lafiya sosai bata san waye akan ta ba, yakamata in ka samu lokaci kuzo ku duba ta"

Jalal yace

"Allah ya bata lafiya Amma bazan zo ba"

Daddy yace "Jalal meya sa kake hakane? Narasa me baiwar Allah nan tayi maka ka tsane ta, rashin lafiya ce kuma bata wuce kan kowa ba, At least in kazo ka duba ta mamanka ma zata ji dadi, tunda muka zo ta kasa sakewa tana ta kuka ne"

"Daddy idan fa nazo bani zan bata lafiya ba, kuma bani na dora mata ba, meye dole sena zo, nima bani da lafiya fa, dan Allah kayi hakuri kayi mata sannu Allah ya sawwake"

Jalal ya kashe wayar sa, girgiza kai Daddy yayi yace

"Allah ya shirya"

Mummy dake gefe tace "Kaima kasan baze zo ba, da dai kanwar uwar Jalila ce ze tafi ko bangon duniya ne a kafa, ai na riga nasa masa ido yaje yayi abunda ya ga dama tunda bani da mutunci a idonsa, na barwa Jalila shi dadi mata yaje yai duk abunda yake so kafin in waiwayeshi"

Daddy yace

"deeja bana son wannan maganganun da kike yi fa, ina ruwan Jalila a cikin wannan abun? Naga tun kafin ya auri Jalila basa wani jituwa da Ilham da mahaifiyar ta, kuma in kikayi hakuri watakila kiga yazo, amma be kamata komai Jalal yayi ki dora alhakin akan matarsa ba"

"Eh dole kace haka mana tunda kai ka aura masa ita, da Ilham ya aura nasan duk wannan bakin cikin da ban ganshi ba, yanzu se 'yar mulki taga dama tasa baki sannan zezo"

Mikewa Daddy yayi yace "Sekuma kiyi ke ka dai, ni zan wuce gida"

Dauke kai tayi tai masa banza har ya fice daga Dakin

Jalila tace "Zaujee waye ba lafiya ne?"

Dan bata rai yayi yace "wai babar su Ilham, shi kuma Daddy wai inje in duba ta, in duba ta ince mata me? Nima ba lafiyar ce dani ba ai"

"haba Zaujee meye a ciki dan munje mun duba ta? Dan Allah zakayi kuma Mummy zataji dadi, Akwai lada me yawa a ziyarar mara lafiya, karka duba wai tayi maka wani laifi kowani abu ka duba girman Allah da manzon sa, duba mara lafiya umarnin manzon Allah ne salallahu alaihi wassalam, kuma koyi da sunnar sa ne, zuwan ka da rashin zuwan ka baze canza komai ba, Amma mara lafiya zeji dadi kai kuma zaka samu lada"

"idan na dau carbi ma kona karanta Al'qur'ani zan samu lada"

Jalila tai murmushi tace
"Annabi salallahu alaihi wassalam yasan da hakan yace muyi zumunci, kuma yace muje ziyarar mara lafiya, please Zaujee ko minti kadan ne muje a duba ta"

"to naji amma se nayi shawara"

"haba mijin so be kamata kayi jinkiri a aikin lada ba, a temaka zuwa gobe in Allah ya kaimu muje"

"shikenan Allah ya kaimu goben lafiya"

"Ameen ya Allah, ko kai fa har naji dadi"


Mummy duk ta sanar da 'yan uwa abunda ya faru, ana ta zuwa duba ta, Se bayan isha'i Ilham tazo Asibitin nan, gaba daya ran Mummy ya gama baci, Ilham na zuwa Mummy ta rufe ta da fada

"wai daga gidan ubanwa kike? Tun jiya mahaifiyar ki bata da lafiya amma ba kya gida, ina kika tafi?"

Ko sauraron Mummy Ilham ba tayi ba ta nufi gadon da Umman ta ke kwance, tana zuwa taga yadda kamanin Umman ta suka koma, ja da baya tayi ta fasa ihu tana fadin

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, munshiga uku, wayyo Allah na umma meya sameki haka? Shikenan komai ya warware a haka zaki zauna kenan? Na shiga uku Umma na"

Mummy tace

"Ilham kiyi hakuri mana, dare ya fara yi ga marasa lafiya kiyi hakuri, likitoci sun bada tasa tasai duk anyi amma sunce basu ga komai ba, ni ban san meya same ta haka ba"

Banza Ilham tai mata ta cigaba da kurwa tana surutai. Wajen goma Mummy ta tafi gida, ta bar kanwar Saudat da Ilham a gurin ta.

Da safe Jalila ta lallaba Jalal suka shirya suka tafi Asibiti domin su duba mahaifiyar Ilham.

Da sukaje Asibitin Jalal ya kira Daddy a waya ya kwatanta masa dakin da aka kwantar ds ita, koda sukaje Daddy yana nan ya kai Mummy be tafi ba.
Mummy na ganinsu ta hade rai kaman bata san wani abu dariya ba, Jalila tana gaisheta amma ta dauke kai.
Jalila ta gaida Daddy sannan suka gaisa da 'yan uwan Mummy dake dakin
Jalal ya nemi guri ya zauna ya dora kafa daya kan daya ba tareda ya kula kowa ba yace
"Mummy ya me jiki?"
Daga ido Mummy tayi ta kalleshi tace
"Uwar taka ta barka kazo kenan?"

"wa kenan"? Jalal ya tambaya

"Matar ka mana"

Cikin ko in kula Jalal yace

"Badan Jalila ta takura ba babu abunda zesa inzo duba wannan matar wallahi, Allah ne ya tashi kamata shiyasa ya maida ita haka"

Daddy yace
"deeja bana son irin wannan abubuwan, daga zuwa dubiya kin fara surutai ga mara lafiya a kwance"

Daddy na cikin fadan ne Ilham ta shigo dakin hannun ta dauke da ledar pharmacy, tana ganin su Jalila tayi jife da ledar ta nufi Jalila tana zazzaro ido tana magana cikin ihu Jalal yai maza ya mike yasa Jalila a bayan sa

"Wallahi baki isa ba Jalila saboda ke koma meye ya samu mahaifiya ta, wallahi kema bazaki rayu cikin dadin rai ba sekin wulakanta kuma sena ciki burin mahaifiya ta koda hakan yana nufin rasa raina"

Jalila ta fito daga bayan Jalal tace
"Ilham har yanzu baki hankalta ba ko? Abunda ya sameki be zama darasi a gareku ba? Ashe kuwa zaki kare rayuwar ki a wahala, zuwa yanzu ya kamata ki san baki da abunda zaki iyayi ki cutar dani, wallahi Ilham na miki zarra kuma na riga na miki illa, ya rage naku ku nemi yafiyar wanda kuka cutar, ko Allah ya sassauta muku wannan iftila'in, bakar aniyarki da ta mahaifiyar ki ce ta koma kanku, yanzu seki dau damarar zaman jinya, dama shi Allah ba Azzalumin sarki bane"

Cikin ihu Ilham tace "wallahi karya kike kiyi galaba akaina, sena kasheki na kashe Jalal din"

Jalila tace "sedai ki kashe kanki, Allah maji rokon bawa, Allah be bar gwagwarmayar da nayi a banza ba, Allah ya shiryi mijina kuma ina miki albishir da abunda kukayi masa ya bar shi"

Ganin Jalila ta fara daukar zafi yasa Jalal janye hannun matar sa sukayi waje.

Mummy da Sauran 'yan uwansu da ke dakin kam daskarewa sukayi suna mamakin irin musayar kalaman da suka shiga tsakanin Ilham da matar Jalal me hakan ke nufi?

Mummy tace "Wai Ilham ban gane inda maganganun nan suka

Please Login or Register in order to submit comment