Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jalal cikin gida ya tafi domin samun yin hira da daddy, yana zuwa ya tarar da Ilham a babban palour da waya a hanunta tana waya, kotakanta bebi ba yanufi part din daddy, bayansa Ilham tabi da kallo "muje zuwa Jalal zakaga tsiya" Jalal yana zuwa ya tarar da daddy a palour dinsa suna hira da mummy, daddy na ganinsa yai murmushi "dan halak kaki ambato, zancenka nakeyi a a raina karaso Dama inason ganinka dan gidan daddy"
"to gani mezaka bani, Jalal yafada yana zama akan kusa da daddy"
"Jalal magana nakeso muyi da kai, Mum dinka tazomin da magana nayi murna da jin hakan shine nakeson ji bakinka" Mummy tai farat tace
"Ba dai maganar da mukayi dazu bane, ai mungama magana dakai, meye kuma na tada wannan zancen, kayi abunda yakamata kawai" daddy yace
"A a Madam karmuyi gaggawa, dole mubi komai a sannu sannan inji ta bakin kowannensu" "A'a fa ai mungama magana wannan kawai maida hannun agogo baya zakayi"
Jalila da sallama ta shigo palourn, Ilham na palourn amma tai mirsisi taki amsawa, "Aminiya Ilham amsa sallamar ma seyazamo miki aiki, amsa sallama dabi ace ta kyakkyawan musulmi, karki zama irin yayanki nan mana" tsaki Ilham tayi tareda fadin
"meye hakane wai? Ke kullum in baki shiga sabgata ba bakyajin dadi ko? Ina ruwanki da nida danuwanane mayya"
"Aini indai a irin sha'anin nan ne to nafi uwar mayya naci, mayya in akayi magani ana samun nasara nikuwa babu abunda zakiyi kiyi nasara akaina, sannan duk abunda ba'aso ni shinakeyi dan aji haushi, and the most craziest part of me is that bana riko, yanzu zamuyi fada yanzu zan manta, duk abunda na rike a zuciyata nake fushi akansa to yanada mahimmanci a gurina, dan haka nibana gaba dake Ilham dan bakikai inyi hakan ba dake, sannan kuma bazan fasa bata miki raiba in har kikayi abunda yaci karo da Ra'ayina sedai kiyi hakuri "
Lallai Jalila tacika yar rainin hankali, wulakanci goma da ashirin.
Duk yada Mummy tayi a wayance kar Jalal yaji zancen nemamasa auren Ilham daddy yaki, karshe a fusace Jalal yace" waini meye hakane daddy, afadamin komene mana, inbaza ayiba meye na dakko maganar agabana, nibanason irin haka fa"
"Ohh ka kwantar da hankalinka yaron kirki, aiba abun tashin hankali bane, maganane me dadi akanka, maganane nacika maka burin rayuwarka, Mummy dinka tagama yimin bayani akan komai, nagame da abunda ke tsakaninka da Kanwarka Ilham, dan haka zanje muyi magana da mahaifinta asa rana, nayi farinciki da har kafara tunanin aure Jalal, cigaba yafara zuwa a rayuwarka kaga......
"Enough daddy" Jalal yai maganar a fusace, "Wannan maganar daga ina? Duk matan duniya in rasa wadda zan aura se wannan, in har farinciki kake nafara maganar aure, to da saurana, wait wai wama yagaya maka wannan maganar, kodayake base ka gayamin ba nasani," ya kalli mummy "Ke kika gaya masa nasan haka, nidake na taba cemiki ina son wannan yarinyar ne? Meyasa kikemin hakane, meyasa kikeson kuma rusa al'amuran rayuwata, ke a ganinki Ilham ta dace da zama matata, kimin adalci kiyiwa kanki mana, akoda yaushe kidena duba maslahar kanki kawai, kuma Ilham tunda Ubanta na raye se ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane ba, akanme za a dinga batamin rai haka, wallahi sena kakkarya yarinyar nan inga uban da ze tsayamata" daddy yai gaggawar mikewa da nufin tare Jalal amma Jalal ya kauce ya nufo hanyar fita,
Ilham taiwa Jalila wani mummunar kallo "ai dama da ganinki base an fada ba ke mayyace, bari inkuma jadadda miki, duk maitarki kurwata data Jalal tafi karfinki haka kika ganmu haka zaki kyalemu, nidashi mutu ka raba" "to dan kincemin mayya ai ba haushi zanji ba, ko ina cin kurwa bazanci taki data Jalal ba saboda bazanci kazamar kurwa ba, kuma kina bani mamaki, dakikancinki yayi yawa Ilham bansan lokacin dazaki gane cewa niba abunda zanyi da wannan dan giyar ba, kuma kema dakike ta wahala akan se ya aureki don cikar burinki, ABDUL JALAL baze taba aurenki ba Ilham, tunda yace baya sonki baze sokiba, kuma kinsan daddyn sa yana goyon bayansa, nasan hanya dayace dake dazakibi ki aureshi hanyar sihiri kuma wannan hanyar bata bullewa" da sauri Ilham ta kalli Jalila tanaso tayi magana amma takasa,
"Karya kikeyi, Yaya Jalal yana sona kuma bani da wani mugun nufi akansa, ubanwa yagaya miki saboda wani dalili nakesonshi, munafuka duk masifarki wallahi haka zaki kyalemu, dan banga uban daya isa ya hanani auren Jalal ba"
"Eh kinyi mamaki ko? Ya akayi nasani, da bakinki kika fada, ba a gurin wani naji ba sannan.....
" A gidan ubanwa na taba gayamiki ina sonki meyasa ba kya ganewa, sa'anki neni, mahaukaciyar inace ke dakike tunanin zan aureki? Yau zaki tattara kibar gidan nan tunda bana ubanki bane, akanme zaki dage cewar nikikeso nace bana sonki bana sonki meye haka wai, mekike nema a gurina ne Ilham" Jalal ne yakewa Ilham magana cikin fada, da sauri daddy ya fito tareda Mummy, daddy ya karaso inda Jalal yake "haba Jalal ai duk abun be kai hakaba, koba komai kanwarkace, kayi hakuri"
"Daddy wace irin magana kakeyi hakane, seta bar gidan nan koni inbar muku gidan, akan me za a takurawa rayuwata, for what reason dad, ace kullum mahaifiyata batada buri se ganin bacin raina" Jalila rasa abun cewa tayi, ta kalli wannan ta kalli wannan,
"Haba Jalal ya ina matsayin mahaifiyarka zakace bana son cigabanka, Aurenka da Ilham alherine ni banga aibun Ilham ba, a tunanina komai ya wuce" wani mugun kallo Jalal yaiwa Mummy duk ya birkice idonsa yai jawur "Kikace komai yawuce, karki yaudari kanki mana, kodayake son zuciya baze barki kidinga ganin gaskiya ba, nayi dana sanin kasancewarki mahaifiyata, kullum bakida burin daya wuce gayyato matsala cikin rayuwar dan dakika haifa, haka sauran iyaye sukeyi" Jalila kasa jure abunda Jalal yake tayi , wanda hakan yasa ta mike ta fice daga palourn jikinta a sanyaye, tafito ta jingina da bango tai shiru tana tunani "meyake damun Jalal ne? Dole nasan dalilinsa na cin zarafin iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina tausayawa Jalal ya mutu yana sabawa iyayensa, zanso inji dalilin hakan kozan iya temakamasa, wulakanta iyaye ba abune me sauki ba"
Ilham se kuka take, duk yadda daddy yaso ya shawo kan Jalal ya kasa, seda yai me isarsa sannan ya bude palourn ya fito a fusace, yana fitowa Jalila tana gurin a tsaye akan hanyar daze wuce, hannu yasa ya hankadeta gefe yai gaba abunsa ya nufi part dinsa, mamakine yacikata, kodayake ba abun mamaki bane kadan daga aikin giya. Jiki a sanyaye ta baro gidan, sedai me tana fitowa taga motar Hannah a kofar gidan, ta fito tana ta kiran lambar Jalal amma yaki dagawa. Jalila a ranta tace "lallai Jalal kana cikin iftila'i" dayake duhun magariba yafara yi, Hannah bata gane wacece ba, dan haka tace "Dan Allah baiwar Allah naga kaman daga gidan kika fito Jalal na ciki ne?"
Karasawa Jalila tayi gabanta "kalli da kyau baki gane wacece bane?" se yanzu Hannah taganeta "dama kece?
" Eh nice, meyasa bakyajin kunyar zuwa neman Jalal ne? Mace da aji akasanta abunda kike zubarda mata kike" "Ke kome nakeyi beshafeki ba kingane bana son surutu, Jalal yana nan ne?"
"Eh Jalal yana nan, amma kaman yanda nagaya miki kwanaki yauma hakanne baze zoba, huwaila kike kowa, ni mamaki kike bani meyasa bakida kunya ne, me yayi miki haka kika uzzurawa rayuwarsa"
"Ke dakata, ba abunda yadameki, Ko agaban uban waye zan fada son Jalal nake, nan da kankanin lokaci ze aureni" murmushi Jalila tayi "to Ilham dinfa? Kokina tunanin zuba miki ido zatayi ki aureshi, naga kaman tafiki sonshi dan tafiki himma ina tunanin za'asa sa ranar aurensu" zare ido Hannah tayi "dagaske kike?" "nasankine dazan tsaya ina miki wasa"
"Ni Jalal zewa haka wallahi basu isaba dagashi har kanwar tasa, Nikadai zan aure Jalal in rayu dashi sena lalata komai, in bahakaba sena masa sharrin da nan duniya babu wanda ya isa ya fiddashi, nayi wannan alkawarin" "kaman ba yanzu kika gama cewa kina son aurensa ba, kin dade kina cutar da rayuwarsa, ranar birthday dinsa kun shirya yimasa wani abu, ni nasaka aka dauke shi daga gurin bayan kin bashi kwaya kin bugar dashi, a wannan lokacin nakara tabattar da bakinku daya da da wannan dan iskan, sannan kisani babu wani sharri dazakiyi masa yayi tasiri akansa Allah yana tareda shi, dan haka wannan ba soyayya bace, ba kyasonsa dan Allah, ku saurari yadda karshenku ze kasance " Jalila ta juya tai gaba, da sauri Hanna tabi bayan Jalila tana mata magana akan dan Allah ta tsaya, amma Jalila taimata banza tai wucewarta zuciyarta cike da tunani. Ba karamin mamaki Hannah tayiba, gaskiya Jalila tabata mamaki ya akayi haka, dama ita tasaka aka dauke Jalal, ita ta turasa wannan shirin da suka dade sunayi, to meye manufar Jalila akan Jalal.
Jalila kam Tana zuwa gida ta tarar da Nana ta dawo daga gidan Yaya mairo, ta tarar dasu a palour Nana tana kuka, Maama tana rarrashinta, kaman ta wuce seta fasa ta tsaya "Nana lafiya kuwa"
"ke bana son gulma ina ruwanki, wuce kitafi inda zaki, uwar tsegumi kawai" ba Jalila ba hatta Nana seda taji babu dadi abunda Maama tayi.
Dakinsu ta wuce taje tai alwala tai sallar magariba, tafara tilawar al'qur'ani, wayarta se ringing takeyi amma bata dauka ba harseda ta idar da karatunta, tana duba wayar bakuwar lamba ce da akayi ta kiranta da ita ranan, dan haka ta ajiye tacigaba da sabgoginta, har bayan sallar isha'i Nana bata shigo dakin ba Jalila kuma bata nemeta ba, wayarta ce takuma daukar ringing, a fusace Jalila ta dauka "Wai ya hakane ankira ban daga ba kuma se kuma kira ake, haba inkuma ina wani uzurinne fa?"
"Tuba nake, adon gari, nakasa samun sukuni ne amin afuwa"
"waima wake magana?"
"Suleman ne" "waye kuma Sulaiman ni bansan wani suleiman ba" "yi hakuri, wanda kuka hadu shekaran jiya kika bashi lambarki" seda Jalila ta dan yamutsa fuska dan ita ta manta dashi,
"ohh nagane sannu yakake?" "lafiya amma ba lauba, nakira nakira baki daga ba, inata kewar muryar nan taki" "Hmm to ai yanzu gashi kaji" "Hakane nayi farinciki fatan kina lafiya" "eh lafiyata kalau" haka sukayi waya da Jalila kaman ammata dole, ita kunya ma yake bata da haushi inyayi wani abun tsoho dashi se wani tabara yake mata.
Nana ce ta shigo jikinta a sanyaye, Jalila bata kulata ba taje tazubo abincin dare tanaci, bayan tagama tai shirin bacci ta haye gado tana chatting dinta, Hanan tana online, suka fara hira kaman abun arziki, har Jalila take bata labarin Alhaji Kabiru, dakuma wannan dansandan, Hanan tabata shawarwari, Jalila tagaya mata abunda yafaru yau agidansu Jalal, Hanan ta fara kunna Jalila "queen gaskiya Jalal is destined to be in your life, dan haka ki kauda wata Ilham da Hannah gefe kisa kai dan kun dace sosai, ke kadaice zakiso shi tsakani da Allah ki temaki rayuwarsa"
"Ke bana son shirme Allah ya kiyaye meye abunso a gurinsa, meye abun birgewa a gurin mashayin giya"
"A'a adena zakewa dai, kar nan gaba azo a gigice akan sa ehee dan bazan bawa mutum shawara ba"
"Narasa meyasa kike likamin wannan sakaran, inada Yaya Jawwad ba abunda zanyi da wani Jalal"
"Ke dakata, Jawwad nawane kuma ni kadai, gara ki rungumi Jalal tun lokaci be kuremiki ba, Jawwad baze aureki ba nina gayamiki" rufe data Jalila tayi, dan hartaji wani bacin rai yana tasomata" Nana ta kalli Jalila tace
"Jalila bazaki tambayi meyasameni bako? Kina kallo ina cikin wani yanayi" tashi Jalila tayi takoma kusada Nana "Nana hawayen nan naki jinake kaman ni nake zubar dashi, kinji abunda Maama tace dazu, shiyasa ban takuramiki inji meyasaki kuka ba bansaniba kobe shafeniba"
"haba Jalila har akwai abunda ze sameni dabe shafekiba?" "to yanzu kiyi hakuri gayamin meya faru?" Nana ta share hawayenta sannan tace
"Jalila wai kiran da yaya mairo tayimin, waiso take ta hadani da Nura waiya aureni"
"Waye kuma Nura" "babban danta ne, wallahi Jalila inda abunda natsani na bude ido ingani be wuce wannan Jakinba" "Amma Nana meyasa?"
Wasu hawayen ne suka kuma zubowa Nana "Jalila dan dabane fa, mugun tantirine har prison yayi, ga shaye shaye na masifa, ba ilimin addini bokon ma secondary ya tsaya, wai dan zalunci shi takeso ta hadani aure dashi, wallahi akace sena aureshi sena kashe kaina, inkuwa aka kaini gidansa sena ksheshi na kashe kaina"
Da sauri Jalila ta rufemata baki tareda fadi "subhanallah, Nana karki kara fadin hakan, wannan maganar tayi tsauri, amma me Maama tace?" "cewa tayi inyi hakuri, zatasan matakin dazata dauka, nikam hakan beminba kawai ajanye wannan maganar, inbahakaba gara in bar gidan nan" "Nana nace kidena irin wannan zantukan mana, kiyi amfani da kwakwalwarki, kina tunanin Abba ze yaddane, baze yadda ba dan haka kiyi hakuri, ba abunda zesa ki aureshi Insha Allah mutumin kirki zaki aura, zan tayaki addu'a kinji My Nana kidena kuka, banaso" gyada kai Nana tayi sannan tace "Saboda tsabar son zuciya irin na matar nan waishi kuma Yaya Jawwad da Naja za'a hadasu, wallahi inshi ya yadda nibazan yadda da auren dan daba ba, gara in kashe tsinanne in huta"

Comments nakeso ba sticker ba, kokuma just thanks,
A kullum ina alfahari daku masoya wannan novel
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
07063065680



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 9️⃣/62_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]



_MY FIRST NOVEL _



Seda gaban Jalila ya fadi, kirjinta ya buga da karfi, amma ta dake ta maze, ta lallaba Nana suka kwanta, amma bacci ya gagari Jalila, gaba daya abubuwa sun cunkushe mata ta rasa menene mafita, dan haka ta tashi taje tayo alwala ta tada salla.
Washegari da safe seda Jalila takusa sasu su makara sannan suka tafi makaranta, yauma sir hafiz yashiga ajinsu Jalila, har yayi lectures yagama hankalinsa yana kanta, ita kam ko a jikinta, abubuwan dasuka dameta kawai take lissafawa, na farko damuwar Jalal, ga abunda Hanna tace, Hanan ma ta dage akan son datakewa Jawwad tana lika mata Jalal, ga abunda Nana tagaya mata jiya da daddare, gaba daya zuciyarta a cunkushe take tanason sanin waye Alhaji Kabiru ta hanyar yarsa dake ajinsu wato saleema, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, sir hafiz yana monitoring din duk moves dinta sam attention dinta baya kansa, dan haka yace ta tashi tsaye, ba musu ta mike, ya dinga yimata tambayoyi amma taki kulashi tayi masa shiru, lamarin yarinyar nan ba karamin daure masa kai yake ba, daya dameta ma kawai seyaga idonta ya cika da kwalla, tana nema tafara kuka. Dan haka ya kyaleta yacigaba da lectures dinsa ba tareda yace ta zauna ba, yagama tsaf sannan yace ta biyoshi office, banza tayi masa, tanemi guri tai zamanta ta kifa kai, tarasa meyake mata dadi, hawaye tafarayi tanayi tana gogewa, zahra ta dafata tace "Kiyi hakuri kidena kuka, nikaina banajin dadin abunda lecturer din nan yake miki, nasan ba dadi amma dan Allah kidena kuka kinji" sam zahra batasan meye damuwar Jalila ba dan haka tabita a haka, zahra tace "bari inje in siyo miki ruwa kisha ki wanke fusakarki" Jalila ba tace komai ba, zahra tafita taje siyo ruwa, a hanyarta ta dawowa, Su Samira suka datseta, suka sha gabanta, samira ta kalleta sama da kasa sannan tace "A tunaninki tarayyarki da wannan dakikiyar yarinyar zesa in fasa bibiyarki ne, wallahi yazama dole ki amince da bukatata, komai kike bukata na more rayuwa zanbaki shi, amma muddin kika cigaba dabin yarinyar nan, ina tausaya miki abunda ze biyo baya, saboda rayuwar taki dakike takama da ita, ita zansa a tarwatsa yadda sekin wulakanta a idon duniya " a firgice Zahra ta kallesu, Saleema tace "Zahra dama ce a gareki kina ganin su zee da salma duk asirinsu a rufe sunata hutawa, keme yasa bazaki yadda ba, waike ta Allah ko, wallahi duk matakin data dauka akanki kekika jawa kanki, sannan yazama dole kiyi gaggawar rabuwa da wannaan dakikiyar yarinyar. Daga nan suka wuce suka batta a gurin, a hankali ta furta" Nashiga uku, Allah ka tsareni daga sharrin wadannan mugayen" jiki a sanyaye tafara motsa kafarta
"Ke! Ke!!" taji ana mata magana a baya, tsayawa tayi ta waigo, setaga sir Hafiz, "kigayawa kawarki kice mata bataji kiran danayi nata bane" jinjina kai kawai tayi, ta tafi aji ta kaiwa Jalila ruwa ta sha ta wanke, fuskarta Jalila ta kalleta, a sanyaye zahra tace "sir hafiz yace meyasa bakije kiran da yayi miki ba" jin maganar zahra a sanyaye yasa tace "lafiya naganki wani iri, me yafaru" zahra bata boye mata komai ba tagaya mata, "Jalila inaga dole mudena hulda tunda suka sakoni gaba, inacikin tashin hankali" ran Jalila ba karamin baci yayi, ta kalli zahra "har yanzu babu uwar datayi nakuda ta durkusa ta haifi wata shegiya dazata sa inyi wani abu ku indena wani abu dan ina tsoronta, dan haka nasiyi wannan rigimar koni kosu, musamman Saleema, bada ita zanyiba sa makyankyashinta zanyi" mamakine yacika zahra kaman ba Jalilan da take kuka ba yanzu abun tausayi amma yanzu itake masifa haka "Jalila meye kuma makyankyashi?" "ba ruwanki, kuma bazan dena hulda dakeba sedai kibar department din nan, in yaso ba tarwatsawa ba in sunga dama susakawa rayuwartaki bom, ba abunda ya shafeni bane tunda kedai bakida wayo bakusan yancinkiba, seki zauna wasu yan kwaya suna raina miki hankali saboda bukatarsu" tanagama fadin haka tatashi ta dau Jakarta tabar ajin, tabar zahra baki bude.
Office din sir hafiz ta tafi, tana zuwa su samira na fitowa, kallon Samira tayi ido cikin ido tace mata "Kiki yayi shiga hurumina, karki yadda kisanni a ainihin kalata" ta juya ta nufi office din, tayi knocking yace ta shiga, yana zaune yana breakfast yana shan tea, dan kuramata ido yayi ya dauke kai yacigaba da abunda yake, har kasa ta durkusa ta gaisheshi dan dagowa yayi ya amsa mata, bata jira izininsa ba ta haye kujerar dake fuskantarsa ta maze hada jujjuyawa, aransa yace "Ikon Allah wanna yarinyar ba dai mulkiba" seda yagama abunda yake yayinda still yanzuma tunani take tanayi tana kokarin maida kwallar data taru a idonta, ya dan dubeta yai nazarinta nawasu seconds sannaan yace "Wayabaki damar ki zauna?" bata kalleshiba tace "bana son tsaiwa dazu ma daka tsayar dani a aji kafata ciwo take" "Kodayake bakiyi kakar wahala ba, amma Meyasa kike kokarin boye baiwar da Allah yayi miki, meyasa kika zabi kidinga dizga kanki agaban yan ajinku? Kika fi maida kai akan tunani kullum?" shiru ta danyi idonta taf hawaye tace "ai kai ka janyomin, nagaya maka kadena tambayata agaban yan aji amma kullum seka tambayeni danka wulakantani, ni bazan bada amsa agaban yan ajiba, bana son sa ido"
"Wayece miki dan in wulakantaki nake tambayarki?" "Zuciyatace tagayamin" murmushi yayi "tagayamiki ba dai dai ba, amma meyasa kike boye baiwar da Allah yayi miki, ga yawan tunani a class, you are too young ace kina tunani dayawa?"
"Akan me zan nuna ni watace? A hakanma wasu sun tsaneni a ajinmu nibansan menayi musu ba,"
"Suwaye suka tsaneki?"
"Samira da gangs dinta mana, kuma wallahi in basu fita sabgata ba senayu maganin yarinya "
Kallonta yayi "I like your confidence, amma kidena wannaan maganar, yarinyar nan tanada manya karki sa kanki a matsala kinada kwakwalwa me ban mamaki, ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai" Jalila a zuciyarta tai murmushi "tab aikuwa bazan bar gurin nan ba senaji Labari sosai akansu, bari inbi da mutumin nan a sannu"
Dan zumbura baki tayi "ni ina ruwana da wasu manyanta akan me zata takuramin, nima inada Allah kuma babana yana sona dan haka ba wanda zemin komai"
"No bahaka bane, yarinyar tasan manyan yan siyasa, gata fitinaniya har yan daba ne da ita karkije tasa a miki Illa" Zare ido Jalila tayi ta lura yanajin dadin hirar dasuke dan haka tace "to sir amma aka kyaleta a cikin school din nan haka kawar nan tata tafi tsanata taana cemin dakikiya fa,
They are terrorist in har mace za'ace tanada yan daba tazama hatsari a society" "Hakane amma ya zamuyi, hukumar makaranta bata dau mataki ba ance babu kwakwkwarar hujjar data tabattar dahakan kinga se hakuri, dan haka ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai kidena wannan tunanin"
"To nagode sosai Insha Allah zan kiyaye, amma tunani yazamemin dole, anyway am very grateful with your advice nagode, Allah ya jikan mahaifa" murmushi yayi yace "Nima nagode Allah ya wuce mana gaba" ta dakko Jakarta ta fito.
Jalal jiyake kaman inyayi kykyawan yunkuri zuciyarsa zata fasa kirjinsa dan bakinciki da bacin rai, daren ranar kasa bacci yayi, yasha giyar amma batayi masa komai ba, haka Jawwad yazo yasameshi da safe, juyin duniya yaki kula Jawwad balle yagaya masa meyake damunsa, haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi makaranta, yana nan zaune a palour yaji bacci ya sace shi, kira'ar Karatun Jalila ya dingaji a mafarki, wadda yagani a gidan telabijin shekarun baya koda ya farka daga baccin se yaji babu damuwar a taredashi, yai ajiyar zuciya yai shiru yana tunani wayarsa ce take ringing, kallon wayar yayi, sunan Hannah yagani, tsaki yayi yaki daukar wayar.
Ilham hankalinta yagama tashi jin abunda Jalal yace jiya, kwana tayi batayi bacci ba, aiko sama da kasa zata hade bazata bar gidan nanba ba tareda ta samu abunda take soba, dan haka da sassafe ta tafi dakin Mummy,
Kuka sosai tasakawa Mummy, "Mummy kingani ko, baya sona kinga wulakancin dayayumin, betabamin goriba se jiya dan kawai ance asa ranar aurenmu nikam nashiga uku Mummy, wallahi inban aureshi ba mutuwa zanyi"
"Ilham meye hakane, kibi komai a sannu mana, kiyi hakuri bazaki bar gidan nan ba shima bacin raine yasashi fadin abunda yafada amma kiyi hakuri zan shawo kan matsalar"
"Mummy nan da yaushe to? Nifa gaskiya na damu, bantaba tunanin Yaya Jalal zemin haka ba, anya kuwa ze yadda da aurena"?
"Nace kiyi hakuri nasan abunda zanyi, aure keda Jalal ba fashi, kigoge hawayenki kidena kukan haka ya isa, tashi muje palour"
Ilham ta goge hawayenta suka fito itada Mummy.
Hannah tarasa meyakemata dadi, dagaske Jalal za'asamasa ranar aure da Ilham, aikuwa da Ilham ta tafka mafi girman kuskure a ratuwarta, to amma Jalila fa meye nata manufar, amma yakamata in gayawa Jeje wadda ta rusa masa shiri, amma yakamata inyi magana da Wannan yarinyar yana da kyau insan meye manufarta, wayarta ta dauka tayiwa Jalal message
Jalal ya shiga yai wanka, message ne ya shigo wayarsa, ya dauka ya duba
"Wallahi Jalal inbaka amince da aurena ba, narantse maka sena nuna maka ni cikakkiyar yar bariki ce, wallahi sena maka sharrin da harka mutu ba wanda ze yadda bakai kayi ba, ka rubuta ka ajiye gara tun wuri kanemamana mafita karka kuskura kayi ganganci auren wata, dan wallahi bakai ba kwanciyar hankali
"Hmm bakida hankali" Jalal ya furta a hankali, yafito ya tafi cikin gida dan yunwa yakeji, a palour yaga Mummy da Ilham, be kulasu ba yaje ya dakko abunda ze dakko ya nufi part din daddy, Ilham ta zata yanzuma zemata masifar yace tabar gidan amma taga be kulata ba, yaje part din daddy ya zauna yaci Abincinsa suka sha hira, a haka daddy yaita masa nasiha akan hakuri dakuma yadena kyamar Ilham, se Jalal yaji

Please Login or Register in order to submit comment