Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyi ta kasa bacci, Jalal da ba ruwansa da mata yaushe ya fara Soyayya? Har yake gaya mata yana son Jalila fiye da komai, yadda taga rana haka taga dare zuciyarta kamar zata fito,tana karajin tsanar Jalila a ranta.

Kamar yadda suka tsara, Jalal da Daddy sukaje suka sai gida a tarauni, gidan yayi matukar kyau da tsaruwa, yanada girma sosai gidan, palour biyu, bedroom uku kowanne da toilet se kitchen biyi da store da katuwar harabar gida.
Daddy ya samu Abba akan, an sai gidan dasu Jalal zasu zauna, Jalal ze sai furnitures, Abba yace be yadda ba shi zewa Jalila kayan daki, Jalal ba dan yaso ba ya hakura, Abba da Maama sukaje suka ga gidan sun yaba gidan sosai, Abba seda ya cikawa Jalila ko ina da kaya, gidan ta yayi kyau ya tsaru matuka.



Sam Jalila bata san abunda ake ba, ita dai taga su Hajiya Salma sunata kara shiryata, Hajiya Salma taje ta samu Jalila a daki tace "Jalila ki ware gashinki, me kitso zatazo ayi miki kunshi da kitso, ranar Asabar zaki tare"
Zare ido Jalila tayi tace "Wai Asabar me zuwa?"
"Eh mana, mijinki yace; se kin tare ya gaji da wannan sintirin"
Shiru Jalila tayi ta sunkuyar da kai, Hajiya Salma tace

"Haba Jalila meye kuma na damuwa? Allah ya baku zaman lafiya, karki damu kinji" jinjina mata kai kawai Jalila tayi ba tareda tace komai ba.



Yau weekends ne, Hanan sun gama cin Abincin Rana da Jawwad, tana ta zuba shagwabarta yana biye mata, dan ba karamin birge shi wannan shagwabar take ba, yace
" Habibty Inaga ranar Saturday fa sister dinki zata tare"

"Wai Jalila?"

Jawwad yace

"eh ita, munyi waya da shi dazu da safe kina bacci, ya gayamin ya sai gida, an gama zuba komai ranar Saturday zata tare, inkuma sunki zeje ya dauketa ne kawai"
Dariya Hanan ta kama yi, Jawwad yace
"ya dai, ya naga kina dariya?"

"Akwai kura ne"

"Kura kuma? Meyasa kikace haka?"

"Hmm bakomai, gaskiya yakamata muje kano, zanso inyi kallon yadda wannan rayuwar masoyan zata kasance"
Jawwad yai murmushi yace "lafiya kalau zasu zauna"

"Hakane wuyatta su zauna guri daya, bari a jima in kirata, naga har yanzu bata da waya, se dai kabani taka in kirata"

Jawwad yace "Shikenan naga be bata wayarba har yanzu"

"nasan ze bata insha Allah"
Hanan ta mike ta tafi bedroom dinta.


Jalila tarasa meya kema ta dadi, wai ita ce zata tare a gidan Jalal, a matsayin matarsa, tanata tunane2, Amal tayi sallama, Jalila ta amsa, Amal tace "Anty Jalila, Mummy tace in kawomiki phone, your sister wants to talk to you"
Jalila a ranta tace ;kai yaran gidan nan sunfiye iyayi, ji yadda take magana kamar me koyon hausa
Jalila tasa hannu ta karbi wayar tareda cewa "Nagode"
Wayar aka sake kira Jalila ta daga wayar tareda fadin
"Salamu Alaikum"

Yanayin muryarta ze gaya maka tana cikin damuwa, Hanan tace

"Amaryar Yaya Jalal, ke ko kirana ba kyayi se idan nina kiraki ko?"
Cikin sanyin jiki Jalila tace

" kinsan bani da waya tun ranar dinner da ya karba be baniba, bana son yawan takura musu da karbar waya"

Hanan tace "hakane ya kike ya shirye2"

"shirye2 me?" Jalila ta tambaya

Hanan tace

"Ahhh Haidar yacemin ranar Saturday In Allah ya kaimu zaki tare"
Dan karamin tsaki Jalila tayi

"shine wani ya shirye2, ba wani shirye2 ni abun duniya ya dameni, ina tunanin irin zaman da zanyi a gidan nan"

"meye wani abun damuwa kuma? Karki dorawa kanki ciwo mana, Allah yabaku zaman lafiya yasa kina zuwa kiyi karo da shi"

Jalila tace "inyi karo dame?"

"ďan baba mana, nan da wata tara muzo suna" hanan ta bata amsa

Wani uban tsaki Jalila tayi "Ke kinfiye shirme wallahi"

"bawani shirme, Addu'a nai miki tagari"

"rike addu'ar ki bana so, ni ba haka naje yi ba"

Dariya Hanan ta dinga yi "Wallahi karya kike, abunda kikaje yi kenan, sekin cika masa gida da 'ya' ya duk shekara zaki dinga haihuwa"
Kashe wayar Jalila tayi, tareda yin dogon tsaki, inta biyewa Hanan bata mata rai zata cigaba da yi.



Shirye2 sunyi nisa, Hajiya Salma da Anty sun tsaya an gyara Jalila yadda yakamata, sun hada mata kayan turaruka daban2, Suka shirya mata kayanta a trolley. Ta wani bangaren Jalila tanata murna zata koma garinsu, ta cigaba da zuwa makaranta,


Anty tace "Jalila na cika alkawarin dana taba yi miki, ga turaruka nan, in sun kare ma kiyi magana se in hado miki wasu"
"to Anty na gode"
Abee yayiwa Jalila nasiha sosai, tareda yi mata fatan Alkhairi, yabata kyautuka na litattafan Addini dana zamani, sekuma kyautar system yace taje taita karatu. Jalila tai tayi masa godiya.

Hajiya Salma sunyi waya da Jalal, cewar zasu taho da Jalila gobe zasu tsaya a gidan su Jalila, sannan su kaita gurin Mummy daga nan akaita gidanta.
Jalal yace "gaskiya bana son ku kaita gidan Mummy, dan seta bata muku rai, kawai ku kyale ta"

"A'a Jalal baza'ayi haka ba, Mahaifiyarka ce akwai bukatar a sauke hakkinta na uwa, yakamata ta sawa Aurenka Albarka"

Jalal yace "Shikenan yadda kuka gani, Amma ni a gurina babu bukatar hakan.




Ilham bata taba sanin tana kaunar Jalal ba kamar yanzu, gaba daya kishi ya hanata sukuni ko Abinci bata iya ci, ita a tunanin ta tana so tayi soyayya da Jalal ne dan cika burin mahaifiyarta, Amma yanzu ta gane kaunar Jalal tayi mata illa, bata bacci sam, yadda taga rana haka taga dare, wai Jalal ke gaya mata shidin mallakin Wata mace ne, macen da ta dade tana cusa masa miyagun maganganu da cin mutunci amma saboda bashi da zuciya yake fadin shi mallakin ta ne, hawaye ne ya gangaro daga idon Ilham tace "Wallahi Jalal muddin baka Aureni ba sena fitini rayuwar Auren ka, sena uzzurawa rayuwarku, se Gidan Auren ka yazama kurku ta fishi 'yanci, idan har kuka ji dadin Aure ba Saudatu ce ta haifeni" ta cigaba da kuka da surutai a daki.





Jalila se murna take zata koma Kano, koba komai zata dinga zuwa makaranta ta rage kadaici, karfe goma sha daya na safe suka shirya, Anty, Hajiya Salma, Husna, da wasu daga danginsu Jalal suka taho yiwa Jalila rakiya Kano,
Se kusan karfe hudu na yamma suka iso, Maama ta san da zuwansu dan haka ta riga ta shirya komai, har 'yan uwanta da makwabta ta sanar, bayan sallar magariba za'a raka Jalila gidanta.
Jalila tayi murna ganinta a gida, Abba yayi murna yadda yaga Jalila tayi kalau da ita tayi fes kaman wata matar hamshaki. Dakinsu taje komai yana nan yadda ta barshi, kewar Nana ta dinga ji a ranta, tana tuno abubuwa da dama da ya faru a wannan dakin, wasu ma farinciki wasu na bakinciki. Maama tazo ta sameta tace

"Jalila ki debi duka abunda kike so akayanki, wanda zakiyi Amfani da shi nan kusa se a tafi miki dashi"
"to Maama zan diba Insha Allah"
Sukaci Abinci sukayi Sallolin da ake binsu.
Anty tace "Jalila yakamata ki shirya muje a kaiki gurin uwar mijinki, kar dare yayi sosai"
Ras gaban Jalila ya fadi! Jikinta yafara Rawa, ta shiga duniyar tunanin wace irin karba Mummy zatayi mata.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta Amsa, seda takuma wanka ta canza kaya, suka nadeta a cikin lafaya, se kamshi takeyi Maama ta kama hannunta ta kaita gurin Abba, ya dinga mata nasiha da Addu'a, Jalila se kuka take, yadda Abba yaji rabuwa da Jalila beji haka akan Nana da Jawwad ba, yana matukar tausayinta. Bayan ya gama ne Maama tayi mata 'yan nasihohi da Addu'a, dan sosai take jin kunyar abubuwan da ta aikatawa Jalila.
Wasu daga cikin' yan rakiyar amarya sunyi gaba dan suje suga ďaki, Yayinda Hajiya Salma da Antyn Jalal suka nufi gidan su Jalal Da Amarya Jalila.





Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
......🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣3️⃣ 106

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724




_MY FIRST NOVEL _




Tunda suka doshi gidansu Jalal gaban Jalila ke wata irin mummunar faduwa ta dinga karanta duk abunda yazo bakinta, suna tun karar kofar da zata sadar da kai da cikin gidan gabanta na cigaba da faduwa kirjinta se bugawa yake da karfin gaske.
Anty ce tafara sa hannu ta murda handle din suka shiga a babban parlour suka zaunar da Jalila, Hajiya Salma ta kira daddy a waya tasanar masa sun iso amma basu ga kowa a parlour ba, da yake daddy ya koma, dan haka ya kira Mummy a waya yace taje parlour tana da baki.
Abun ya bata mamaki sosai, wani irin bakine haka da bazasu kirata ba, fitowa tayi ba tareda tayi tsamanni ba tayi karo dasu Hajiya Salma a zaune a palour, rabon da taga hajiya Salma tun lokacin da ta bar mata gidan, Salma tana nan da gayun ta ba kace ta haifi Mahmud ba.

A fusace Mummy ta dube su a wulakance tace "lafiya daga ina? Mekuka zo yimin?"
Hajiya Salma tace "kwantar da hankalinki mana Hajiya khadija, ba abun zafi bane ba, Matar danki muka kawo miki, ki musu Addu'a ki sa musu Albarka zamu kaita gidan danki"
Wani tsinannen Kallo Mummy taiwa Hajiya Salma tace "Albarkata ake nema a wannan Auren munafuncin, da kuka haďa kai kuka aura masa yarinya ba da izinina ba, shine zakuzo wani wai im sa muku Albarka, bazasu taba samun Albarkata ba, saboda bana son yarinyar nan, na tsaneta tun kafin ta Auri ďana take juya shi, abunda takeso shi zeyi danme zan kaunace ta? Auren nan baze taba Albarka ba, kuma wallahi sena ga bayansa, senaga bayan Auren nan "

Anty tace
"Allah sarki, abunda kike gudune se ya faru, sannan Jalila taimakawa Ďanki take, kin san ba dan mutunci da girmamawa ba, Baza'a dauki nutsatsiyar yarinya abawa ďanki ba"

"tunda ansan ba nutsatsen bane, uban meyasa a lika masa wannaan yarinyar, se a kyaleshi da halinsa in aura masa yarinyar da nake so, wallahi bazan taba son yarinyar nan ba, da nake mata kallon mutuniyar kirki amma tunda tafara bin dana nagane makira ce mara mutunci "

Rirrike Hajiya Salma Jalila tayi ta kara sautin kukanta, Hajiya Salma tace
" ko ki sota ko karki sota Allah ya riga ya haďa Auren nan, zuwa yanzu yaci ace kinyi laushi kinyi hankali amma babu alamar hakan a tare dake, Allah shaida ne ba abunda yarinyar nan ta miki da ta cancanci wannan kiyayyar da mugun bakin daga gareki"

"kinga sauraramin bana son salon munafurci, nafada bana sonta, kuma bazasu taba ganin haske ko albarka a rayuwar Auren nan ba, kuma wallahi sena kashe Auren, babu wani alkhairi ko amfani da take da shi a gurin Jalal, wannan dunkiyar tasa kawai take kwadayi, shiyasa ta aureshi ta juyamin shi, to wallahi bata isa ba, tunda nina haifi ďana, shida abunda ya mallaka nawane, muddin ta shiga gidan Jalal tafara kirga ranakun bakinciki a rayuwar ta har seta kyalemin ďana, shegiyar yarinya mara usuli"

Tunda ake fadawa Jalila rashin mutuncin Mummy bata taba zaton ya kai haka ba, wata hira da suka tabayi da halima ta fado mata rai da halima take ce mata "Sayyada karki bari wani abu ya hadoki da matar nan dan bata da mutunci" sosai Jalila miyagun maganganun Mummy suka daki zuciyarta.

Hajiya Salma tace "Shikenan mungode da wannan karbar da kikayi mana muda matar ďanki, Amma ki sani idan kin rabani da gidan mijina kin zauna lafiya, bazan taba bari ki lalata auren nan ba, Allah yafi ki sannan a wannan karon dai2 nake dake, Aure an riga anyi shi kuma mutuwa ce zata raba shi"

"Se ayi in gani ai"

Anty tace "Jalila tashi mu tafi"
Jalila ta mike wani irin jiri na kwasarta, se rarrashinta Anty take,
Ilham ce ta shigo palourn da alama daga wani gurin take, wani kallon banza Ilham tayiwa su Hajiya Salma kafin idonta ya dira akan Jalila, dukda Jalila tana cikin lafaya, amma Jalila tayi kyau, jikinta yayi sumul sosai ga wani kamshi da dakin yake yi, hannunta ya sha kunshi ja da baki.

Ilham na ganin ta wani azababben kishi ya taso mata, gurin Jalila ta nufa gadan2 idonta ya rufe gaba daya tace

"Wallahi bazan taba yafe miki ba, kin rabani da ďan uwana abunda na dade ina so shekara da shekaru, wallahi zakigane baki da wayo, munafuka kece me cewa babu abunda zakiyi dashi, kinsha kiransa namiji mara daraja, mara tarbiyya da yake makirace kika zagaya kika Aureshi, algunguma.... Sosai Ilham take kuka tana kokarin fizgo Jalila

Hajiya Salma a fusace ta sa Jalila a bayanta tace "Ke lafiya meya haka?"

"ban saniba wallahi sena yi mata rashin mutunci, seta gane ni ba kanwar lasa bace, naga ta yadda zatayi zaman Auren a kwanciyar hankali"
Jalila tasa hannu ta ďaga lifayarta ta kalli Ilham ido duk hawaye, ga idanunta sunyi jawur, kallon da Jalila tayi mata seda gabanta ya fadi yadda taga Jalila ta hade rai tana mata wani irin kallo.

Sunkuyar da kai Jalila tayi ta cigaba da zubda Hawaye, Jan hannun Jalila su Anty sukayi suka fice waje.

Anty tace "Anty Salma su dangin su khadija tun asalinsu basu da mutunci, masifa acikinsu kamar barkono"

Hajiya Salma tace "Allah dai ya kyauta, ki kwantar da hankalinki Jalila komai ze wuce Insha Allah"

Suka sa Jalila a mota zuwa gidan ABDUL JALAL.

Dukda kan Jalila na cikin mayafi amma gidan ya tsaru sosai, suka kaita daki suka ajiyeta, akaita mata nasihohi, daga nan suka tafi suka barta a gidan, sakkowa tayi daga kan gadon ta nemi guri ta zauna a kasa, tana tuno irin maganganun cin mutuncin da Mummy ta dingayi mata da wulakanci, take taji mugun danasanin Wannan Auren yakara rufeta, Hawaye kawai takeyi, Mummy ta riga tayi mummunan furuci akan Auren nan, dama gashi bata tabaccin shi kansa Jalal din yana sonta, ga Ilham ma miyagun maganganun da ta dinga faďa, shikenan ni kowa na raba nazama abar kyama, Allah ka yafemin in wani laifin na aikata.

Har wajen goma na dare sannan Jalal ya shigo gidan, milk din yadine a jikinsa me laushi, da hula akansa, dakin da aka kai Jalila ya nufa dauke da ledoji a hannunsa, yana shiga ya tarar tayi zaman dirshan a kasa tanata zubar da Hawaye, dan tsayawa yayi yana kallinta dan be san ta ina ze fara ba, a hankali ya karasa gabanta, tana jinsa amma ta share ta cigaba da kukanta, ya sa hannunsa ze janye nata daga dukunkunewar da tayi a mayafi, da sauri ta janye hannunta ta ja da baya sekace taga dodo.

"Wai kukan me kikeyi hakane? Ke kullum duk inda kika zauna sedai kiyi kuka ne?"

Kallon shi tayi da rinannun idanuwanta cikin kuka tace "dole kace haka mana, me ya ragemun a rayuwa inji dadi banda kukan? Ka gayamin me ya ragemin? Mahaifiyarka bata sona, bata kauna ta, kaima kasan hakan amma ka Aureni, mahaifiyarka tace; bazata taba kaunata ba, seta kashe Auren nan, kasan da haka amma ka Aureni, anata kwallo da rayuwata daga nan zuwa can, dana fita daga wannan matsalar in fada wannan, zamana da kai nasan wani sabon shafin kaddarar ne, dan Allah ka sakeni in auri wanda yak sona, wanda mahaifiyarsa zatayi farinciki da shigata rayuwarsa,"

Shiru Jalal yayi ya tsura mata ido yana kokarin gano ko har cikin zuciyarta take maganar nan, mikewa yayi ya juya ya fice yabar ďakin zuciyarsa a cunkushe.

Daya bedroom din ya nufa, yana shiga ya sauya kaya, ya ajiye wayoyinsa ya nemi guri ya kwanta, tunani daban2 ya ziyarci zuciyarsa, Kenan Mummy ciwa Jalila mutunci tayi? Shiyasa tun farko be so akaita gurin ta ba, ga shi ta bata komai, Amma ta wata fuskar Jalila tanada gaskiya, babu wanda ya tuntubeta aka yanke mata wannan hukuncin, aka daura mata Aure ba tareda Amincewarta ba, shikenan wannan zaman ze yi a rayuwar Aurensa? Zuwa yaushe Jalila zata yadda da shi a matsayin miji? Haka ya dinga tunani abun duniya yabi ya isheshi.

Yana fita Jalila ma ta cigaba da kukan, karshe a zaune a kasan nan tayi bacci, ko kayan jikinta bata canja ba.

Koda gari ya waye bata bi ta kansa ba, tai sallar asuba tai kwanciyar ta, ta cigaba da baccin ta, lokaci2 idan ta tuna yadda Mummy ta dinga cin mutuncin ta se taji gaba daya haushin Jalal ya kamata, dan me ze yadda da Auren ta bayan ya san maman sa bata so, gaba ďaya Mummy ta gama kwashewa Auren nan Albarka, yunwa ce ta ishi Jalila dan haka ta tashi tai brush tai wanka, ta dauki ledar da ya shigo da ita jiya, ta bude kajine a ciki gasassu, se fresh milk, ko warming dinsu batayi ba ta ci abunta ta kora da madara, ta cigaba da zaman ďaki.
Tun ranar da'aka kawota da Jalal ya shigo bata kara ganinsa ba. A kayanta akwai tarkacen biscuit su ta cigaba da ci, kusan kwana biyar bata kuma haduwa da Jalal ba, da safe tayi wanka ta sa kaya ta fito, tana dan zazzagawa tana fitowa main palourn ta ci karo da katon hotonta da nashi, Hajiya Salma ta sa sukayi, an rubuta Happy marriage life, hoton yayi kyau sosai, ďan tabe baki tayi ta cigaba da za gayawa, gida yayi kyau masha Allah, Amma kwata2 takasa farinciki da hakan, saboda bacin rai da yake cin zuciyarta.

Koda ta duba store Jalal ya aje komai na kayan Amfani, hatta omon wanki akwai, duk abunda yasan na amfanine kona kayan masarufi ya ajiyeshi, fitowa tayi ta fita harabar gidan tana kuma kallo, katuwar haraba ce sosai, tana zagayawa ne ta fara jin kaurin sigari, tunkarar inda take jin kaurin tayi, tana zuwa ta tarar Jalal yanata zukawa cikinsa, yana fesar da hayakin a iska, ta dade a tsaye a gurin be sani ba, kamar an taba shi kawai ya juyo, yaci karo da ita a tsaye tana kallon sa

Jikinsa yayi sanyi da irin kallon da Jalila ke masa, amma ya basar ya cigaba da shan tabarsa, juyawa tayi ta koma cikin gidan ba tareda tace masa uffan ba.

Kusan sati biyu da tarewar Jalila amma ko maganar kirki bata haďata da Jalal, Abun ya damu Jalal matuka, be taba zaton Jalila zatayi watsi da shi haka ba, girki ma batayi, se yunwa ta addabeta zata hada cornflakes ta sha, gashi mafi yawan lokutanta tana karar dasu a kuka se bacci wani lokacin, ya damu sosai da wannan hali da takeyi.
Ko yayi niyyar yi mata magana idan yaga fuskarta da yadda take basar da shi se jikinsa yayi sanyu.

YauDa Asuba da Jalila ta idar da sallah tana zaune akan dadduma ya shigo dakinta, bata ce masa uffan ba, yasa hannu a Aljihu ya dakko sabuwar waya ya ajemata akan side bed, ya dakko kudi ya ajiye mata, sannan yace "ga kudin mota nan kikoma makaranta, ni zan wuce lagos"
Dagowa tayi ta kalleshi, ta kalli inda ya aje kudin

"wai nika dai zan dinga kwana a gidan nan? Gaskiya ni bazan iya kwana ni kadai ba tsoro nakeji"

"to ya kikeso ayi?" ya tambayeta

"Sedai in koma gida in zauna, in dinga tafiya school din a can"
Wani mugun kallo ya mata
"ba inda zakije, daga makaranta ban yadda kije ko ina ba"

"to Amma nifa bazan iya kwana ni ka dai ba, inajin tsoro"

Cikin ko in kula yace "se kisan yadda zakiyi, ni yau zan koma" ya fice ya barmata dakin

Haushine ya isheta, ta yaya zata iya kwana a gidan nan ita ka dai? Zuwa tayi tai wanka tafara shirin makaranta hankalin ta ya kai kan wayar daya ajiye mata, sabuwar wayar daya ajiye mata, dauka tayi ta kunna ta, komai nakan waccan wayar tata yana nan, da lambobinta, amma ya canza mata layi.
Ajiye wayar tayi ta gama shirinta ta tafi makaranta.

Tunda taje take shan tambayoyi daga gurin 'yan ajinsu akan dagaske tayi Aure?
Haka ta dinga basu amsa dai2 da tambayoyinsu,' yan jin kwaf kuwa sukace tunda basuje bikinta ba zasu kawo mata ziyara har gida.

Koda ta dawo gida ta tarar baya nan, ya tafi, da ranan ma tsoro takeji, tasaba ko yaya tana jin motsinsa, tun kan magariba ta kulle ko ina ta koma daki ta rurrufe ko ina ta sa key, Tana sallar Isha'i ko Abinci bata ciba ta haye gado ta lullube tana rarraba ido, sam takasa bacci.

Shima sam Jalal yakasa bacci, yana ta tunanin ko yaya zatayi? Ko tayi bacci oho? Tunani yayi ko ya kirata ne, amma ya tuna a halin da suke shida ita dan haka ya fasa kiranta dan karma ta bata masa rai.

Jalila kam bacci da kyar tayi shi, cike da tsoro, ko yaya taji faduwar abu zata firgita ta tashi. Alla2 ta dingayi gari ya waye saboda tsoro, gari na wayewa take shiryawa ta tafi school.

Wasa2 Jalal seda yayi sati biyu bata kuma jin duriyarsa ba, gashi ita ba lambarsa ce da ita ba, inma tana da lambarsa ta kirashi tace masa me? Amma tasan shida ya canza mata waya yana da lambarta, Amma be iya kiranta yaji wani hali take ciki.

Seta kunna karatun qur'ani a speakun palourn ta take iya bacci, yanzuma tana kudundune a gado ta dau wayarta ta kunna data, taga Hanan ta mata magana ta what's App, chatting suka dingayi can Hanan takirata a waya suka cigaba da hira

Hanan tace "ke by now kamata yayi a ce kina tareda mijinki, Amma kina nan kina chatting"

"ke meya hana kije ki kula da naki mijin?" Jalila ta bata amsa

Hanan tace "Wallahi ya fita siyomin cashew ne"

"cashew kuma a daren nan?"

"Eh mana, ba mijina bane"?

Jalila tace "haba Hanan, ya kike garamin ďan uwane, dare fa yayi zaki tura shi siyan cashew"

"to ya zanyi, wallahi nakasa cin Abinci ne, shi nake son sha"

Jalila tace "hmm kodai kodai abunne?"

Hanan tace "au to ku zamu tsaya jira, kifara saimana feeder da pampers"

Jalila tace "wow masha Allah, Allah ya in ganta"

Hana ta amsa da "Ameen, ke kije ki kula da mijinmi seda safe"

Jalila tace "wai wane miji? Yana lagos fa"

Hanan tace
"dan yana lagos bazaki kula da shiba, keep him busy, kuyita chat kina zuba masa kalamai har yayi bacci"

Dan guntun tsaki Jalila tayi.
Hanan tace "Jalila kaddai har yanzu ba kwa jituwa? Jalila me yasa?"

"Hanan babu wani Alkhairi a wannan Auren namu, Hanan mahaifiyarsa tacimin mutunci fiya da yadda kike tunani, wallahi jin gidan nake kaman kurkuku"

"Haba Jalila, to Jalal ne yayi miki? Meye laifinsa anan, wannan Auren iyaye ne suka hada shi ba Jalal ba, yakamata ki tausaya masa Jalila, ranar suna video call da Haidar ya rame sosai, wallahi ina tunanin bashida lafiya ma, sedai kinsan ba lallai ya fada ba, saboda zurfin cikinsa, in Allah ya dubi niyyarki akan sa seya temake ki, mijinki ne Aljannarki zaki nema, shi wanda kike tunanin kina so din sekiga ba shine Alkhairi ba, kiyi tunani ya zakiji idan ninakewa Haidar abunda kikewa Jalal? " shiru Jalila tayi, Hanan tace

" yakamata kiyi tunani, Jalal mutum ne shima, wannan shareshin da kikeyi ze iya jefa shi halaka fiye da baya, kuma zakiji kunya idan dangin mahaifinsa da suka yadda dake suka gano irin zaman da kike da ďansu, ke hatta Abba bazeji dadi ba"

Haka Hanan ta cigaba da da yiwa Jalila nasiha, sukayi sallama ta kwanta, shiru tayi tana nazarin maganganun Hanan, da kyar tayi bacci tanata tunani, Hanan ta ce mata ya rame kaman bashida

Please Login or Register in order to submit comment