Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cin abunsa zeyi)
"
Daddy yace "Jawwad baka cin Abincin nan fa, nifa banason fulatanci, ka saki jiki kaci Abinci"
Jawwad murmushi kawai yayi yakuma sunkuyar da kai.

Bayan sun kammala, Abba ya gyara zama sannan yace
"to Captain ni dai da farko Jawwad be gayamin yana soyayya da Hanan ba, har nayi masa zabin matar Aure nida mahaifiyarsa, Amma yanzu nagane akwai matsala a dangane da zabin da mukayi masa, kuma Kanwarsa Jalila da Dan uwansa suka sanar dani halin da'ake ciki har kaima ka kirani a waya kazomin da wannan zance na Jawwad ya fito in dagaske yake"
Daddy yace "Hakane, nima mahaifiyar Hanan dince ta sanar dani halin da'ake ciki, kuma gaskiya yarinyar tanada manema dayawa kuma ta nuna shi Jawwad din takeso, shiyasa nima nayi maka magana"

Abba yace "Hakane, Amma zangaya maka wani abu, inkaga zaka bawa Jawwad 'yarka a haka to shikenan, inkuma kaga baze yuwu ba semu hakura"

Daddy yace "ina jinka fadi muji"
Abba yace "kaga maganar gaskiya a yanzu a bangaren mahaifi Jawwad bashida kowa se Allah sekumani, sedai bangaren mahaifiyarsa, banida wa bani da kani, kani na ďaya shine mahaifin Jalila kuma Allah yayi masa rasuwa tun Jalila nada shekaru biyar, kuma daga ni har mahaifinta babu wanda yasan suwaye dangin iyayenmu sakamakon suma gudun hijira sukayi daga garinsu, in kana ganin zaka iya bashi 'yarka a haka shikenan "
" Haba Alhaji Usman, Ai Jawwad ko ďan tsintuwa ne babu abunda ze hana in bashi' yata indai yana sonta, yanada hankali ga nutsuwa da tarbiyya wannan ba abun damuwa bane ba, bari muje ku gaisa da Mahaifiyata semu karasa gidan Yayana, shi ze karbi kudin Auren"

Abba yace "Nagode kwarai da wannan karamcin naka general, Allah yasaka da alkhairi"
Daddy yace "tsakanina da kai babu batun godiya, bari muje".

Jalila takoma gida ta fara baccin dole saboda azabar zugin da hannunta yakeyi, se kusan la'asar ta tashi, shima hayaniyar Naja ce ta tasheta dayake ita Naja wani lokacin kaman banza haka take bata magana a hankali, ga hauma hauma kamar rainon gabuwa, wannan hargowar ce ta tashi Jalila.
Sannan da alamu har yanzu Maama bata gaya mata sakon Abba na tabar masa gida ba, dan har yanzu tana giginta da rawar kai, Jalila ta tashi tayi sallar la'asar tanemi abun zubawa a cikinta.

Shikuwa Jalal tunda yaje ya sha giyarsa yayi tatul wani nannauyan bacci ne ya kwashe shi be farkaba se magariba, ya shiga yai wanka yai sallolinsa, bayan ya idar ne ya dau wayarsa yakuma kiran Jawwad, wannan karon Jawwad ya dauka Jalal yace "wai dan Allah ina ka shiga ne haka? Tun safe ban ganka ba, na tambayi kanwarka tace bata san inda kake ba"
"Aiba bata nayi ba, kuma ba saceni akayi ba kaganni tareda Abba muna Bauchi"
"Bauchi kuma? Me ka keyi a Bauchi?"
"bazaka gane ba, sena dawo kawai akwai Labari"
Murmushi Jalal yayi, yadda yaji muryar Jawwad yasan yana cikin farinciki, Jalal yace
"To seka dawo din, amma tafiya ba sallama haka?"
"Nima ban san da tafiyar ba, babu shiri Abba yace inzo mutafi"
"to shikenan Allah yadawo daku lafiya"
"Ameen ya Allah" sukayi sallama
Bayan sunyi sallamane Yusuf ya shigo palourn daddy, Sallama yayi suka amsa gaba daya, Yusuf ya kalli Abba ya durkusa ya gaisheshi ya amsa masa cikin sakin fuska, ya juya ya kalli Jawwad ya mika masa hannu suka gaisa.
Daddy yace "Yusuf ga Abban Jalila fa"
Murmushi Yusuf yayi yace "Ai ina shigowa jikina yabani, ina kallonsa naga akwai alakar Jini, wannanne yayanta kenan sirikinmu"
Daddy yace "ya akayi kasani?" Yusuf yace
"Kai daddy yadda yarinyar nan ke fadarsa, ko kunya ba taji ranar inajinta itada Nawwara (matarsa) tanata yabonsa hada yi masa waka, kaf estate din nan ba wanda besan haidar ba ko ince Jawwad"
Gaba daya sukayi dariya, Yusuf yace

"ďan uwa Allah yabaka wuyan ďauka, dan wallahi Autar daddy fitinanniya ce, ga yarinta a cikinta" haka sukaita taba hira Yusuf yajanye Jawwad suka fice zuwa bangaren Inna.
Suka shiga da sallama, kamar kullum tana kan darduma tana lazimi, suka zauna a gefe suna taba hira harta idar, sannan ta juyo ta kallesu dan kura musu ido tayi, Jawwad yace "Sannu Inna"
"Yawwa ďan nan, Yusuf wannan kuma ina ka samoshi, kar in fadi wani abu ace nayi rikici"
Yusuf yace "Inna Yayan Jalila ne"
Murmushin fuskarta ya faďaďa sannan tace "Masha Allah, Nayi farincikin ganinka yarona, Kanwarka me kama da mairota da na dauka itace, ashe ba ita bace ba ina kabaromin me sunan larabawan?"
"Tana lafiya Inna, tace a gaisheki"
"Allah sarki yarinyar kirki me hankali, idan ina basu labarin kanwata se suyita lallabani wai kar in rikice musu da kuka, itakuwa kanwarka zama take muyita hira naita bata labarin wannan kanwartawa"
Yusuf yace

"zaki farako inna, dan Allah kiyi hakuri, kekowa sekin bashi labarin kanwarki, ko labarin tsofaffinki ba kyayi kamar ita, kimsan bakida cikakkiyar lafiya"
Jawwad yace

"A'a kabarta ta fada maybe hakan ze rage mata damuwa, tunda kaji haka akwai kyakyawar alaka a tsakanin su"
Yusuf yace "Ai intana wannan labarin nata daga nana zata fara kuka, kuma in tafada bata iya cin Abinci jininta ya hau sosai"
Sallamar Su daddy ce ta katse musu hirar suka amsa musu Sallamar amma banda inna da ko juyowa takasa yi.
Daddy yakaraso gabanta ya durkusa yace
"Inna ga baban Jalila, kuma sirikinki yazo ya gaisheki ne"
jinjina kai tayi ba tace komai ba, Abba ya zagayo gabanta ya durkusa gaba daya ta zuba masa ido ko kyaftawa batayi, tace
"Imamu ne? Imamu ina Mairona" cikin sanyin jiki Abba yasa hannu yakamo Hannunta ya rike a nashi a hankali ya furta "Innarmu.... Inna Hafsatu, Allah yasa kece, kece wadda Inna take bamu Labari Yayarta"

Fashewa da kuka tayi ta rungume Abba tana fadin

"Alhamdilillah nagaya musu, Amma sunki yarda suna ganin kaman rikici nane kawai, tunda naga yarinyar gurinka nasan tsatson Mairamunace, nasan zuwa yanzu ba lallai tana raye ba, amma ina son inga ahalinta"

Hawaye sharkaf a idon Abba yace
"Na dade ina bulayin neman ki Inna, Allah ya karbesu gaba daya, dasu da tilon ďan uwana, ya mutu yabarmin 'yarsa Jalila se yarana biyu, ban taba tunanin Allah ze karbi Addu'a ta ba, yau naga dangin iyayenmu"
Gaba daya jikinsu yayi sanyi, kowa seda yayi hawayen tausayi, Abba yasha wuyar bulayi da yawo garuruwa ko Allah zesa yasamu wani nasa ashe suna kusa da juna, alakar yara ta haďa amma basu saniba, Ashe shiyasa kamannin Jalila da Hanan sukayi yawa, hatta yanayin halayensu iri daya.
Abba yasa hannu yana gogewa Inna hawaye cikin zolaya yace "Kamanki daya da Innarmu, sedai duk babanmu yafi ku kyau"
Murmushi tayi tace "Ai shima ďan uwana ne, kuma mairo tafishi kyau, Allah yayi musu rahama gaba ďaya.
Nan hirar asali da tushe ya barke, nan da nan Labari ya karaďe estate din nan cewar ansamo dangin mairo kanwar Inna, nan da nan gidan yafara cika da dangi da 'yan uwa don ganewa idanunsu hakikatul Amri.
Daddy yace tunda hakane kadasu Abba sukoma yau, su ďanyi musu ko kwana ďayane Inna taji ďaďi kuma sannan suga' yan uwa.
Haka kuwa akayi, Abba yakira Maama yace bazasu dawo a yauba saboda wasu dalilai, ba wanda suka gayawa abunda yafaru, hatta Daddy be gayawa su Hanan ba.

Jalila takira Ahmad ya sanar da ita cewar baze shigo yauba, saboda yayi dare a hanya sedai zuwa gobe Insha Allah, seda suka sha soyayya sannan sukayi sallama gefe daya kuma hannunta se ciwo yakeyi, da wanine yai mata abunda Jalal ya mata yau da seya gane bashida wayo, shima ďin dan yanzu bata son yawan fitina da shine saboda gaba ďaya yanzu tausayi yake bata, da dane da seta rama. Amma to meyake damunsa haka? Lokaci ďaya mutum ya rikice kaman wani me tabin hankali, yana zaune lafiyar Allah amma ya birkice lokaci daya wai seyasha giya.

Jawwad kasa boye farincikinsa yayi, seda ya kira Jalal a waya, yana ďagawa Jawwad yace "My man kana inane?"
"Ina gida mana, ina zanje tunda baka nan? Wai yaushe zaku dawo? Tun dazu nake zuba ido amma baku dawo ba"
"Ai mu ba yau zamu dawo ba"
"Se yaushe?"
"Ai bazaka gane ba Jalal bansan yadda zan fasalta maka farincikin danake cikiba"
"Abba yaje nema maka Auren Hanan a Bauchi" Jalal yafada kai tsaye
Da mamaki Jawwad yace "ya akayi kasani?"
"Zuciya tace tagayamin"
"ban yadda ba dama can kasani kai shiru kaki gayamin, amma akwai saura ai"
"to gayamin inaji"
"Abba ya gano danginsu daya daďe yana nema"
Murmushi Jalal yayi yace "Alhamdilillah, na dade ina fatan hakan ya tabatta, kakarsu Abdallah ce Inna Hafsatu da Inna mairo take fada take bamu Labari ko?"
Cikin mamaki Jawwad yace "wai dan Allah ya akayi kasani?"
"Allah ne yasanar dani, dan Allah kadawo da wuri, ni bana jin dadi in baka nan"
"wai kana in dawo da wuri, kamanta in Allah ya kaimu next week zan tafi inda aka turani aiki"?
"kumafa hakane se yanzu nakejin babu daďi, amma Insha Allah hakanne mafi Alkhairi agaremu baki daya"
"Amma ni ina mamaki yadda akayi duk kasan wannan zancen ni ban saniba" dariya Jalal yayi yace
"Ba abun mamaki bane, kai dai seka dawo kawai
Seda suka gama hira da Jalal ya katse wayar, Jawwad yaji kaman ya kira Jalila amma ya fasa, dan yasan idan ya kirata farinciki seyasa yagaya mata abunda ke faruwa kuma Abba ya gargade shi akan kar kowa yasan wannan zancen a yanzu harse sun koma gida.

Maama tarasa ta inada zatayiwa Naja bayanin Abba yana bukatar ta bar masa gida, saboda tana matukar Jin tsoron Masifar Yaya Mairo, tarasa abunda yake mata dadi, yanzuma da Abba yayo waya seda ya jadadda mata baya son ya dawo ya tarar da Naja cikin Iyalinsa, tarasa ta inda zata fara harga Allah bazata iyaba sedai inya dawo shiya koreta da kansa, can wani bangaren na zuciyarta yake cemata banda ma ya raina miki hankali, ita Jalila dake zaune a gidan meyasa bece ta bar gidan ba, shekarar Jalila nawa a gidan, se yanzu zece Naja tabar gida, indai Naja zata bar gidan nan to dole Jalila ma ta kama gabanta, Maama tayi kwafa tace
"Zaka dawo ka sameni, dai2 nake da kai"

Naja se iyayi take tana wasu irin abubuwa na ban haushi wai ita zatayi Aure, A gaban su Nana take waya da kawarta sunata shirye shiryen abunda zasuyi da biki, ba kunya Naja take cewa a mata booking na kayan mata na tashin hankali, masu tsada, se wasu irin lissafi takeyi, kala2 party da zatayi, da irin expensive clothes da zasu saka itada kawayenta.
Tagama wayarta su Jalila suna jinta, tana gamawa Nana ta tinstire da dariya,
cikeda tsarguwa Naja tace "ke Nana meye abun dariya haka?"
"A'a ni ba dake nake ba, mahmud ne yabani dariya a waya"
Itakam Jalila bata samu zarafin dariya ba tana fama da ciwon hannu, ko uffan ba tace ba.
Nana tagayawa Jalila Abba yace bazasu dawo yauba, Akwai abu me mahimmanci daya rikesu, Jalila a ranta taketa addu'ar Allah yasa abunda take tsamanni ne ya tabatta.

Washegari da safe Monday ce Jalila tace bazata makaranta ba, Dan haka Nana ita kadai ta tafi, tai kwanciyar ta tana bacci, Zahra takirata a waya tagaya mata zasuyi test karfe goma shadaya da rabi na safe, Jalila sam bata da niyyar zuwa makaranta haka ta tashi tana tsaki tayi wanka tasaka kaya, doguwar riga pitch da mayafinta se wata 'yar karamar Jakarta ta dauka, iyakacin Jakar nan ta dauki waya da kudi da ďan abunda baza' a rasa ba sekace jakar roko,
Jalila Ta fito fuskar nan babu walwala, ta tarar Maama na palour tana karyawa itada Naja, yanzun ma hirar bikin suke, Jalila ta durkusa tace

"Maama zan tafi school, yanzu aka kirani zamuyi test anjima"
Banza Maaman tayi mata taki kulata, dama batayi tsamannin Maama ta amsa ba, tayine dan hakan shime tarbiyar da Ummi ta dorata, ta mike jiki a sanyaye Zata fita Naja tace

"Aikin banza wai za'a school za'a tafi yawon gantali dai irin wanda uwale ta saba yi"
Maama tace "dan Allah kidena shiga harkar yarinyar nan shiyasa take kara rainaki"
ai kafin Maama ta gama magana Jalila ta waigo tace "ta Uwale tayi kyau, kekuma ki saurar kiga naki sakamakon, anzo an bararaje ana cin duniya babu a house, gara ki zage ki ciki kafin ki kara gaba, Akuya kawai"
Ashar Naja ta mulmulo zatayi Maama ta dakatar da ita, Jalila kuwa tayi ficewarta ranta bakikkirin babu dadi.
Maama tace
"kyaleni da ita, ki zuba ido zakiga matakin da zan dauka akanta"

Jalila na fita ta hango Mummyn Jalal tareda Ilham da alamu wani gurin zasuje, da kaman ta basar tayi tafiyarta sekuma taga hakan be dace ba, dan rabonta da taga Mummy harta manta dan ko gidan bazuwa takeba yanzu, dan haka ta nufi inda motarsu take, Mummy tana kokarin shiga, Jalila da fara'arta ta karasa ta durkusa ta gaida Mummy, amma ga mamakin ta taga Mummyn tayi mata wani irin mugun kallo kamar bazata amsa ba sekuma ta amsa da kyar, Jalila taji ba dadin abunda Mummy tayi mata, amma ta dake ta mike tace "Mummy Adawo lafiya sekun dawo"
Mummy ta yamutsa fuska tace "Yawwa dama ina son ganinki kuwa, akwai magana me mahimmanci da nakeson mu tattauna dake, dan bazan saka ido abunda ke faruwa yacigaba ba"
Seda gaban Jalila yai mummunar faduwa, wannaan wane irin abune ita kowa ma laifi take masa, kowa ya tsanenta a fili tace "to Mummy Allah yasa ba laifi nayi miki ba? Zanzo Insha Allah, Adawo lafiya"

"Munafukar banza barauniya, me bin ďan mutane, Akuya kawai"

Taji sautin maganar Ilham ta sauka a kirjinta saitin zuciyarta, dukda yadda maganar tayi tsauri tareda dukan zuciyar Jalila, amma ta danne taki juyowa ta kuma kallon inda suke, ta mike tacigaba da tafiya.
Jefa kafarta take ba tare da tasan ina take saka kafar tata ba, Hawayene yake bin idonta, Allah ya temaketa unguwar tasu se kayi minti goma babu wanda yazo ya wuce, kuma wajen karfe tara ne duk wasu sun riga sun fita, hakan yakara bata damar zirarar da hawayen ta son ranta, tana cikin tafiya ne taji ana mata horn kaman za'a kashe mata kunne, ita dai iya saninta ba a tsakiyar titi take tafiya ba gefen hanya ne, Amma an cika mata kunne da horn, banza tayi tacigaba da tafiyar ta.
motar aka sa aka sha gabanta, sannan yafito daga motar yace
"Bakya jin ina miki horn ne ? Sekace wata kurma, Kuma Se yanzu zaki tafi school karfe tara? Allah ya shirye ki, zo muje in ajeki ta nan zan wuce" ya dinga jero maganar daya bayan daya
Juyowa tayi ta kalleshi, ya saka farin yadine dukda kansa babu hula yayi kyau sosai, dan zata iya kirga sau nawa taga Jalal da dogayen kaya, kallonta yayi sosai yaganta kaman a birkice, hawayene a fuskar ta, idonta har yafara Ja, cikin tsiwa tana hararsa tace
"bazan hauba ai da can ba kai kake kaini ba, salon in hau motar ka, ka karasa karyani bazan hauba"
"hmm bazaki hauba ko? Bazaki hau motar mahaukaci ba, Dama interview din nan zani, Amma tunda bazaki hauba se inkoma kuma bazan kuma zuwa ba"
Cikin sauri tace "A'a yi hakuri zan hau, Amma dan Allah karkayi gudu dani" tafada hawaye na zubowa daga idonta
Gaba daya tausayinta ya kamashi, kome yasata kuka haka a titi, itada take da dakakkiyar zuciya? Abunda ze satana tafiya tana kuka ba karami bane ba
"bazan ba, a hankali zan tafi" ya faďa a takaice
Ta bude motar ta shiga, shima yazaga ya bude ya shiga, ya kunna motar yai mata key, suka fara tafiya, ya kalleta yace "Kukan me kike?"
"bakomai"
"bana son karya fa"
Shiru tayi masa, ta maida kanta titi kyaleta yayi tunda yaga batasan faďa masa, maybe is her personal issue. Suna cikin tafiya Jalal yayi parking ya kalleta yace "Zoki rakani zanci Abinci, banyi breakfast ba"
"Ni bazaniba, kaje ka dawo, nibana son ana ganinmu tare" ta fada tareda dauke kanta daga kallonsa
Ba tareda ya kalleta ba yace
"ohh yeah, be kamata adinga ganinki tareda ďan iska mara tarbiyya ba, kar azata irinmu daya, bari yanzu zan dawo"

Ta fuskanci haushi yaji, amma ta basar dan itama ranta a bace yake Befi 5 mintues ba ya dawo da leda a hannunsa, ya kunna motar suka cigaba da tafiya, yana tuki tana goge hawaye, sekace kurame, baya son ya kalleta yaga tana kukan nan, kukanta yanasa shi tuna lokacin da Umminta ka gudn abunda ze sashi kuka shida Jawwad, gani Jalila tayi ya canza hanya dan haka da sauri tace "A'a yanaga ka canza hanya?"
Be kalleta ba yace "Wani guri zaki rakani"
Zare ido tayi "saboda me makaranta fa zani, zanyi test"
"Nasan makaranta zaki, amma tunda kika shigo motata sekinje, don't mind club zamuje kawai, zan danyi caji"
(🙄🙄 tab ba ruwana, yan ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP, kunji Jalal dinku da rigima,)

Abba sunga "yan uwa sunga dangi, Abba be taba tunanin suna da wannan dangin ba, a hakanma sunada 'yan uwa a wasu garuruwan, A yau Abba yace lallai zasu koma kano saboda yanada ayyuka dayawa, se sun dawo ziyara ta musamman dan kara sanin juna, ba karamin farinciki akayi ba ganin Inna ta samu zuri'ar Kanwar ta, Ashe ba a banza ba Jalila da Hanan suke wannan kamannin.
A ranar su Abba suka dawo gida, tun Asuba suka taho, basu baro bauchi ba seda aka yanke watanni hudu, a matsayin lokacin Auren Jawwad da Hanan, sedasu Abba sukayi maganar Ahmad, Abba yace duk abunda daddy ya yanke dai2 ne, daddy yace "se Jalila ta kammala Makaranta ze bawa Ahmad, saboda yanayin karatunta dakuma aikin Ahmad
Su Abba se karfe shadaya suka sauka a kano, Suka sauka da matukar farinciki.
Abba na shiga cikin gida yaci karo da Naja, a palour tana waya, bece mata komaiba ya wuce part dinsa,
Maama haushinsa takeji akan yace Naja tabar masa gida dan haka tana jin sun dawo taki zuwa inda yake, ya shiga part dinsa yai wanka ya canza kaya, da kansa yaje ya sami Maama a daki Yace
"kina jin mun dawo amma kikasa fitowa kiga yamuka dawo? Shikenan ina miki Albishir Anbawa Jawwad Auren 'yar wajen Captain Abdurrasheed wato Hanan nan da wata hudu Insha Allah"
Wani mugun kallo tayiwa Abba tace "kamar yaya? Yaza' ayi akaiwa Naja kudin Aure dan munafunci kuma aje akaiwa wata, mata biyu ze Aura kenan, Jawwad din kwaya nawa yake daze auri mata biyu?"
"mace ďaya ze Aura wato Hanan, maganar Naja na soketa an barmusu kudin Auren, zanje da kaina in samu iyayenta, Sannan kije ki sallami yarinyar nan tabarmin gida, tun kafin raina ya baci, bana kaunarta a cikin iyalina, kema yakamata kuje ku kara binkice akanta"
"Impossible" Maama ta fada da karfi



Masoya kaunar da nake kumu tasa nai muku dogon page gashi nan, senaji Comments dinku love you all
😍😍😍🌹❤️❤️❤️🌹🌹🌹🌹


Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣2️⃣95

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _


Cikide fusata Maama ke fadin "ni zakayiwa haka? Ka watsamin kasa a ido, a kai kudin Auren yarinyar mugama gayawa duniya za'ayi biki sannan kazo min da wata maganar banza, wallahi baze yuwu ba Jawwad bashida matar data wuce Naja
Abba yace
"Shikenan tunda ke zaki daura masa auren ai seki aura masa Najar in gani"
Ya juya ze fice tace
"Kuma wallahi bazata bar gidan nan ba, in dai Naja zata bar gidan nan to Jalila ma seta bar gidan nan"

Cak Abba ya tsaya ya juyo yace
"gida nawane, duk wanda yake ciki a karkashin ikona yake, idan yarinyar nan ta kai magariba a gidan nan to Wallahi zaku tafi tarene, ta tattara tabarmin gida nagaya miki, Jalila nan gidansune, nine mahaifin Jalila, Jalila bata da uwa ba uba seni, ita kuma wannan tanada iyaye dan haka ta koma gidansu, kowa ya zauna a gidansu" yana gama fadin haka ya juya ya fice.

Jawwad yana zuwa ya canza kaya, ya nufi gidansu Jalal amma yatarar baya nan, dan haka ya koma gida ya samu guri ya kwanta dan ya huta


A fusace Jalila tace
"Wallahi bazani club ba, ka tsaya in sauka in yaso kaje inda yafi club be dameni ba"
Shiru yamata ya cigaba da tukinsa, yana satar kallon yadda ta rintse ido tana masifa, ganin yaki kulata yasa a fusace tace
"Magana fa nake maka, wai meye haka?"
Fitooo yafara yi mata yana murmushi, Jalila ta kai karshe a kuluwa, ya dan kalleta yace
"meye kuma na tashin hankali bafa cewa nayi zamuje Kisha giya ba rakiya kawai zakiyi insha mutafi"
Ta fuskanci so yake ya raina mata hankali, dan haka tayi shiru taga gudun ruwansa, ta dauke kanta zuwa ga kallon window tana share kwalla lokaci zuwa lokaci gani tayi tafiyar taki karewa dan haka takara fashewa da kuka me sauti Da sauri Jalal yace "Ke meye haka kuma? Nifa ba Jawwad bane da zakimin shagwaba"

Ido duk hawaye tace "Eh aida Yaya Jawwad ne yasan inada test bazemin haka ba, kuma Allah ya kiyaye in maka shagwaba in maka shagwaba ince nayiwa wa?" tai maganar tana harararsa da kumburarrun idanunta
Dan hade rai yayi yacigaba da tukin ba tareda yace komai ba itakuma tana hawaye.
Wata unguwa suka shiga, wadda kome za'ayiwa Jalila bata san inane ba, wani katon dogon gini ya nufa, kana ganin yanayin ginin da girmansa kasan kamfani ne, yana zuwa aka bude masa wani katon nannauyan gate ya shiga da motar, tundaga bakin gate din ma'aikatan ke durkusawa suna gaisheshi, dagani gurin kamfanine, yaje yasamu guri yayi parking, da sauri akazo aka bude masa motar ya fito, ya zagaya yace mata
"fito"
"ni bazan fito ba, kawai ka maidani inda ka dakkoni"
"Wallahi in baki fito ba zakiyi biyu babu, kirasa test dinki kuma inki zuwa interview"
Kara hade rai tayi sosai ta bude motar ta fito tana zumbura baki, fuskarta tayi jawur, yayi gaba ta bishi abaya.
Babban abunda ya daurewa Jalila kai be wuce yadda taga duk inda Jalal ya ratsa ma'aikata manya da kanana suna girmama shiba, dan wasu har kasa suke zubewa suna gaida shi, Akayi sa'a in suka gaisheshi yana daga musu Hannu, Haka Jalal ya dinga ratsawa da ita tsakanin ginin katafaren gurin daya kayatu yadda yakamata, ko ina tsaf dashi, suna zuwa wata kofa sukaga wani mutum, ya girmi Jalal sosai ya mika masa hannu sukayi musabiha, mutumin yace

Please Login or Register in order to submit comment