Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haifeshi na yanke masa cibi, na goya shi a bayana, ke bari in gaya miki har yanzu ina nan a Jalila na da kika sanni ba abunda ya canza, kuma sedai ciwon son ya kasheki, zan bar Jalal ya auri duk macen da yake so a fadin duniya amma banda irinki, tunda na shiga baki isa ki shigoba wallahi, a baya ma bakiyi nasara ba balle yanzu"

Yadda Jalila ta hakikance yafi komai yiwa Jalal dadi, In dai hakane Jalila ba yanzu ta fara sonshi ba, tunda ba yau ta fara fada saboda shi ba, Jalal yace

"Baby keep quiet, kar ranki ya baci a banza" ya hade rai ya kalli Ilham, gaba daya ya koma Jalal dinsa yace

"idan baki taba ta ba bakya kaunar Allah, mahaukaciya wadda bata san darajar kanta ba"

"Ai babu babban mahaukaci sama da kai, bakaji kunyar yadda kake zakewa saboda mace ba, akan wannan shedaniyar yarinyar, Jalal kayi asara kaji kunya, ka fifita mace akaina, shine kake ciwa Ilham mutunci saboda kake kiranta mahaukaciya, shekara da shekaru tana sonka amma babu tausayin ta a zuciyar ka, kaje ka auri wannan me soyayyen idon" Mummy ce take kumfar baki tana masifa

Wani irin murmushi na rainin hankali yayi, yayin da Jalila ta tsakure guri daya takasa cewa uffan, Jalal ya kalli Mummy yace

"Inason Jalila sosai, kuma kamar yadda ta fada, tunda ta riga ta shiga babu wadda zata biyo bayan ta, wallahi ko Ilham zata haukace bazan aureta ba na tsane ta, tarihi na shirin maimaita kansa Mummy, dama nazo ne dan kiga namijin kokarin da sirikarki keyi akan danki, kuma nason kin gani sedai son zuciyar ki"

"Jalal you have to watch what you are saying, Mummy ce fa, be kamata ka daga mata murya ba, balle ka fadi abunda ze bata mata rai"

"Ohh Sorry dear zan gyara insha Allah" be bar Jalila ta kuma magana ba ya janyeta sukayi waje, yayinda Mummy ta daskare a gurin, Ilham kuwa dora hannu tayi a kanta tana rusa uban ihu.

Suna fita Jalila tace "Jalal meyasa kakemin haka a gaban Mummy, hakan ze kara sawa ta tsaneni ne"

"Jalila wallahi bazanji kunyar nuna miki soyayya ko agaban waye ba, ai ba haramun nayi ba, kuma ina so Mummy taji abunda Hajiyar Daddy taji lokacin da baya sauraren kowa se ita.

"Amma ai ba kai yakamata ka yi ba, komai ya wuce ai, dan Allah Jalal ka dena yiwa Mummy haka mahaifiyarka ce fa, ita ta haifeka, ko yaya she deserves to be respected as a mother"

Jalila kenan dukda abunda yake wa mahaifiyarsa yana jin dadin yadda take nuna damuwarta akan iyayensa

"shikenan naji, amma bazan iya boye soyayyar da nake miki ba ko a gaban waye, muje ki dau trolley dinki, zan tafi airport yanzu"

Koda ta dau trolley seda ya rakata har cikin gidan, yace shi baze shiga ba yasan yanzu suka dawo karya takura musu. Memakon ta tafi tsayawa tayi tana kallonsa
Yace

"ya dai, ki shiga mana"

Dawowa tayi Ta dan langabe kai ta rike hannunsa tace

"bakomai, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya tsare gabanka da bayanka, Allah yabaka abunda kaje nema ya daukaka a harkar aikinka, Allah ya azirtaka da halal ya tsareka da haram, Allah ya wadata ka ya karfafi imaninka, ka kula da kanka kaji, ka dinga cin Abincinka, ka dinga adhkar da sallolinka akan lokaci kaji zaujee na"

Takarasa maganar tareda dan jan dogon hancinsa, Jalal kallonta kawai yake yi, komai nata a nutse ga Addu'oi, yasan da Ilham ya aura baze taba samun haka ba.

Hugging dinta yayi ya kai bakinsa daidai kunnenta yace

"Ameen ya Allah, thank you very much my love, na miki Alkawarin zan kula da kaina, zanyi azkar da sallolina akan lokaci, Kema Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku, Alhamdilillah for having you as my wife, jin wannan Addu'oi seda ga bakin mace tagari, Allah yayi miki tukuici da gidan Aljanna"

Murmushi tayi ta shafa kansa tace "Ameen Zaujee, kaje kayiwa Mummy sallama, sannan kayi hakuri kome zatayi maka, karka fadi abunda ze bata mata rai" jinjina kai yayi ya cikata, taja trolley dinta ta shige.

Tana shiga ta tarar da Nana a parlor, ai da gudu suka rungume juna, Jalila tace

"My Nana kece? Saukar yaushe"?

"Saukar yau mana, dazu Maama sukaje suka dakkoni a airport"

Kara rungume juna sukayi, Jalila tace

"Maama shine baki gayamin zatazo ba"

Maama tace "ai gata nan kin ganta ai"

Jalila tace

"Nana kinga yadda kika zama lukuta kuwa, me kikeci haka wai"

Maama tace

"ku zauna mana se kace kun shekara baku hadu ba"

Ai basu tsaya a parlor ba suka wuce dakinsu na gidan, komai yana nan, taaf da shi ana gyara dakin, suna zuwa Nana ta cire hijjabin jikinta tace

"ga abunda yasani kiba nan, se naga na zama mummuna ko Baby?"

dariya Jalila ta sha cikin Nana ya fito sosai tace

"Allah sarki rayuwa, kaman ba tare muke shiririta a dakin nan ba wai Nana ce da ciki, wallahi ba wani muni da kikayi, kinma fi kyau a haka"

Nana tace "wallahi Habibi ma cewa yake cikin yamin kyau"

Dan ya mutse fuska Jalila tayi tace

"waye kuma Habibi?"

"mijina mana, ko an gayamiki kowa irinkune? Ana so ana kaiwa kasuwa"

Dariya Jalila tayi tace

"ina wane mu, wannan abu ai se su Hajiya Nana manya, to ya Yaya Mahmud da Anty Salma? Ya kuma England da masu jajayen kunnuwa"

Nana tace "suna lafiya, wannan tambayoyi haka"

Jalila tai murmushi tace

"masha Allah, Nana cikin nan da nauyi kuwa, wallahi yayi miki kyau sosai?"

Hararta Nana tayi tace

"ki bari in yazo kanki seki ji"

Haka Jalila taita tsokanar Nana, Abba yayi murna ganin yadda yaga Yaran nasa kowacce cikin nutsuwarta.

Da daddare ma hira sukaita yi, Jalila ta kunna data taga Jalal online, nan ta manta da batun Nana suka dinga chatting da Jalal har Nana tayi bacci

Jalila ta turawa Jalal "bakajin baccine?"

"banaji, nakasa baccin ma gaba daya?"

"me yasa?"

"Am missing your body warm, that make me fall asleep"

"hmm, Performe Ablution, recite qur'an, and hug your pillow, goodnight 😘"

Murmushi ya dinga yi, ya duba agogonsa karfe biyu da rabi na dare, ya tura mata

"ni kike cewa in rungume pillow ko? Zan kamaki ne, let's meet in your dreams" ya rufe data ya kwanta.

Washegari bayan sun kammala breakfast suka dau haramar tafiya bauchi, tunda gari ya waye take trying lambar Jalal amma taki shiga, har suka tafi bauchi layinsa ya dena shiga.

Har sukaje garin bauchi Jalila ji take kaman bata da lafiya saboda takasa samun Jalal a waya,

"dama da gaske yake semunyi sati biyu ba muyi waya ba?"
A status dinta ta rubuta

"I miss you zaujee"

Se la'asar suka isa, sun gaji sosai, musamman Nana ga tsohon ciki ga gajiyar tafiya, suna fitowa daga Mota taga Yaya Jawwad
"Yaya Jawwad i miss you wallahi, dama zakuzo kuma wannan surprise haka ba wanda ya gayamin"

Jawwad yayi murmushi yace "Ai gara da mukayi surprising dinki, Jalal yasan zamuzo ai shine yayi miki lefi"

Jalila tace "yaya ina Hanan?"
"muje kya gani"

suka rankaya zuwa ciki abunda yayiwa Jalila dadi be wuce tozali da Hanan da tayi ba da nata katon cikin itama da gudu ta rungume Hanan Jawwad yace

"A'a Baby ayi a hankali kar aimana barna mun kara yawa"

Nana ta bude baki tana jinjina kai yaushe Yaya Jawwad yazama mara kunya?

Jalila tace "Allah yabada hakuri, zan kula"

Nan gidan yau dau shewa, hatta Mummy Hanan da daddynta sunzo, Daddy yayi mamaki yadda yaga Jalila tayi kalau da ita, kaman ba ita aka dinga fama da ita tana kukan bata son Jalal ba.

Jalila tace "bari inje inga Innata"

Anty fiddo tace "Inna tana lazimi bata son aje dakinta in tana lazimi se dai anjima" daga nan suka baje suna ta hira.

Nana tace

"ni Yaya Jawwad yabani mamaki, ga yadda yake salihi ga kunya, amma waishi ke cewa za'a musu barna, tab matar Yaya Jawwad da ciki abun mamaki"

Dundu Haanan tayi mata tace

"Nana zan miki rashin mutunci akan mijina, ina ruwanki damu"

Jalila dariya take musu

Yusuf ne ya shigo shima dan gaisawa da su Abba, ya tarar da su Nana a parlor suna ta hira, yaga Jalila tsaf da ita ta dan kara kiba ma, Hanan da take dan danna waya ta dago tace

"waike Jalila daga rabuwarku jiya hada wani status wai you miss him, sarkin gulma ashe kun jone? Kamar bake kika dinga kuka kina ba kya so ba"

Jalila ta Harare ta tace

"da kika ce yanzu ina son abuna ai mutu ka raba" shewa sukayi gaba daya
Nana tace "dan bakiga hotunan da sukeyi a wayar ta ba, soyayya suke sha abunsu, ahh komai lokaci ne hakuri me tadda rabo"

Yaya Yusuf yayi gyaran murya, suka nutsu gaba daya sukayi tsit suka gaisheshi ya wuce.

Anty fiddo tafito tace

"ku taho dakin Daddy akwai magana"

Jalila taji dam "Allah yasa lafiya"

Suka mike suka nufi part din Daddy, Jalila na gwada yadda su Nana ke tafiya.

Suka shiga da sallama, gaba daya iyayen nasu sun hallara, Jalila kanta a kasa ta nemi guri zata zauna daga kan da zatayi ta sauke su cikin idanuwan Ummi da ta kura mata ido.

Zumbur ta mike ta fasa zamana tana kuma zaro idon ta waje.

Maama tace "Jalila ki zauna mana"

Wani irin yawu Jalila ta hadiye tana nuna Ummi tareda dan ja da baya zatayi magana Amma taji numfashin ta na sauka da kyar cikin huhunta ta dena ganin komai se duhu.

Da sauri Ummi ta mike ta karasa inda Jalila take, kafin tayi wani yunkuri Jalila ta silale kasa sumammiya a gurin







Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣8️⃣111

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724




_MY FIRST NOVEL _


Ummi ta rungume Jalila sosai a jikinta, Jawwad ya dakko ruwa me
Sanyi a fridge aka shafawa Jalila ruwan a fuska, a hankali Jalila ta bude ido tareda jero ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Ummi, kara kankame Ummi tayi tareda sake fashewa da kuka.

Maama tace

"Jalila ba kuka zakiyi ba, kamata yayi ki godewa Allah ganin mahaifiyarki da kikayi"

Abba yace

"hakane yakamata ki godewa Allah sannan ki godewa mijinki da danginsa"

Kallon Abba tayi cike da rashin fahimtar abunda yake nufi

Daddyn Hanan yace

"gaskiya kam, mijinki ya cancanci yabo, da shi da danginsa, kuma kafa da kafa zamuje domin nuna godiyar mu da farincikin abunda sukayi"

Sam Jalila bata san inda zancen nasu ya dosa ba.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace

"tabbas bayan godiya ga Allah daya nuna muku naku ahalin, zanyi godiya ta musamman bisa Jajircewarku da kulawa da tarbiyya yarinya ta, nagode Allah yasa ku dauka a gidan Aljanna, Jalila bata tana kukan rashin mahaifi ba sanadiyar tarasa wani abu ba nagode kwarai.

Tabbas Jalal yasan inda nake, lokacin dana bar ku nayi sallama domin zuwa garinmu, motar mu ta tsaya domin musulmin cinkinmu su gabatar da salla, bayan nayi salla ne na tsallaka wani restaurant na sai Abinci, na fito zan tsallaka titi mota ta bigeni, mutane suka fara taruwa a gurin, wanda ya bigeni dan sanda ne, dan haka ya nuna musu id card dinsa ya daukeni ya tafi dani.

Ya kaini wani Asibiti na kudi, inda aka tabattar masa dana samu matsala a kashin bayana, sannan nasamu internal injury akaina, lokacin da labarin bata na ya iskeku Jalal ya shiga zuwa offisoshin yan sanda domin an gaya masa dan sanda ne ya bigeni, Allah ya temake shi yasamo wanda ya bigeni yaje har Asibitin da nake, koda yaje yaga halin da nake ciki, yai magana da mahaifin sa akayimin visa zuwa Dubai a wani Asibiti, na dade ina jinya saboda aikin da'akayimin Kashi kashi a bayana saboda matsalar dana samu.
Dana fara samun sauki Jalal yai magana da Hajiya Salma aka maidani Can England gurinta take jiyyata aka cigaba da bani kulawa a can.

Hajiya Salma ta zauna dani kaman 'yar uwatta, a gurinta na warke gaba daya, tun ina Asibiti Jalal yaso ya bayyana muku inda nake amma nahana shi saboda ina cikin mawuya cin hali, bayan na warke nai shirin dawowa Nigeria nacewa Jalal bana son kusan inda nake musamman Jalila, idan har Jalila tasan ina raye bazata taba yadda ta zauna a gurin Abban Jawwad ba, nikuma bana son Abunda ze shafi Addinin ta, Yarenta, da Al'adar ta, saboda ni dangina nada banbancin Al'adu da Addini, kuma yin hakan kaman na saba Alkawarin da nayiwa Aliyu ne kafin ya koma ga Allah.

Jalal da mahaifinsa, Hajiya Salma, wanda ya bigeni da Mijin Antyn Jalal me sunan Abeenki su sukamin rakiya har masarautar mu, Abunda ya bani mamaki be wuce yadda masauratar suka karbeni kai tsaye ba cike da kauna da girmamawa, sannan na tarar anbawa mutanen dake gidanmu damar kowa yayi Addinin da yake so ciki hadda musulinci, mahifiya ta ta musulun ta, kakana kuma ya rasu, Yaya na ke mulki yanzu"

Ummi ta kalli Jalila tace "Jalila ban guje ki ba, a duniya ina matukar sonki ke nake kallo in tuna Aliyu, nayi haka ne domin gyaran rayuwar ki, nayi haka don ki tsaya da kafafunki ko ba kowa tareda ke zaki iya rayuwa keka dai, kin koyi darusan rayuwa daban2 da nake ta nuna miki a baya kika kasa ganewa, lokacin da Jalal ya gayamin an daura muku Aure amma kince bakya sonsa, na shiga damuwa sosai, dan tuntuni nake miki Addu'ar samun miji nagari, kuma koda Ina jinya Jalalya gaya wa Hajiya Salma ta gayamin yana sonki, banji ina kin abunba saboda nasan kina son Jalal kema"

Ummi ta kalli Jalila tace

"Jalila tsawon lokacin dana dauka bana tare dake kowane lokaci kina raina ina miki addu'a a duk inda kike, zaki shiga damuwa idan kika ga halin da nake ciki na jinya, Amma Alhamdilillah naji dadin yadda naganki, Allah ya albarkaci rayuwar ku gaba daya"

Daddyn Hanan yace

"Masha Allah, Kinga abunda muke gaya miki tun a wancan lokacin ko 'yar Baba, yanzu da kin wulakanta Jalal da wani ido zaki kalleshi, ba ke kadai kikayi masa halacci ba, shima yayi miki, da fatan zaki kara rike mijinki ki kula da shi, duk da halayen Jalal na ki, Amma mutumin kirki ne, Abun mamaki duk yadda yake da Jawwad be sanar masa ba, se last month ya fada, watan mahaifiyar ki guda a gidan nan, kuma har can garin nasu muma munje, sannan munje maiduguri ma, Insha Allah a satin nan zamuje dake maiduguri kema ki musu godiya sannan muje kiga 'yan uwan mahaifiyar ki su ganki, dan munji dadin yadda suka karbemu cikin girmamawa da mutunci"

Jalila kasa magana tayi, yanzu take tabattar tayi wauta, da ta cigaba dayi wa Jalal rashin mutunci da wani idon zata kallesu, ta tuno yadda ta kusa bijirewa Auren, Allah sarki dukda halin bakin ciki data shiga a wasu lokuta a baya, Amma ga karamci da kauna da wasu mutane da bata hada dangi da su ba sukayi mata ba tareda ta sani ba, ga jajircewa da wannan dattawa da kokari da suke tayi a kanta da Mahaifiyar ta Abba da kuma Daddy Hanan.

Mikewa tayi ta tafi gaban Abba ta zube akan gwiwowinta ta riko hannunsa amma takasa magana sema wani kuka da ya sake kwace mata.
Ba wanda beji tausayin Jalila a gurin nan ba dan Hanan da Nana ma kukan suke taya ta.

Abba yace

"Jalila kukan ya isa haka, ai murna yakamata kiyi ba kuka ba, kar kanki yayi ciwo sarkin kuka kawai"

Jalila cikin kuka tace

"Abba narasa me zance, Allah ya biyaku ladan dawainiyar da kukayi dani, Ummi dan Allah ki bawa su Abba hakuri, naso na bijirewa maganar Auren da sukayimin a baya, Abba dan Allah kuyi hakuri ku yafemin, Sannan shima a bashi hakuri abubuwan da nayi masa"

Abba yace

"Ai baki bijire mana Ba Baby na, ba abunda kikayi mana, kinmana biyayya yarinya ce ke me matukar hakuri da biyayya, Allah baze tozarta ki ba Jalila, halinki daya da mahaifinki, sadaukarwa da kawaici Allah yayi masa rahama"

Daddy yace "in ce ko yanzu kina son nashi dai?"

Daga kai tayi alamar eh, seda ta basu dariya, amma babu Alamar Jalila zata sassauta kukan da take yi.

Maama tace
"zanyi Amfani da wannan damar in baki hakuri Maryam, na cutar dake da Jalila a baya, Amma nayi nadama, sharrin shedan ne da kuma zigar 'yar uwata, Amma daga baya nayi nadama, wallahi samun yarinya me halin Jalila se an tona, bata taba min rashin kunya ba duk abunda nake mata, dan Allah Maryam ku yafemin "

Ummi tace

"Haba Zainab, wallahi kin gama min komai a rayuwa, tunda kika zauna da Jalila kika rike ta, abubuwan da suka faru da ni da ita itace kaddarar mu, kuma ko yanzu Alhamdilillah, karki damu ni ban rikeki da komai ba, Allah ya yafe mana gaba daya"

Suka amsa da Ameen gaba daya, Babu alamar Jalila zata dakata da kukan nan, dan da kyar take jan numfashi ma.

Daddy ya kalli Anty fiddo yace

"fidausi ku kai yarinyar nan daki ta kwanta ta huta, wannan kukan ze iya jamata matsala"

Haka akayi suka kama Jalila zuwa daki suka kwantar da ita, suka kukkuna mata fanka, tana ta sauke numfashi.

Yusuf yayi mamaki, yaji labarin rayuwar Jalila da kuma waye Jalal, tabbas babu wanda ya dace da Auren ta se Jalal.

Seda aka kira likita yayi mata allura tayi bacci dan bata gane waye akanta, dan kukan da tayi ya saukar mata da zazzabi me zafi da ciwon kai.

Ilham ta shirya ta tafi gidan su Yaseera, tana zuwa tayi sa'a yaseera tana nan, suka gaisa da babar su yaseera sannan suka wuce Dakin ta, suna shiga yaseera ta kalli Ilham tace

"Ilham abun har ya kai haka? Kinga yadda kikayi duhu, kin wani rame ko baki da lafiya ne?"

Ilham tace "wallahi Bani da lafiya yaseera, Amma ban damu da rashin lafiyar ba, ina cikin damuwa kuma mafita nake nema cikin gaggawa ko wace iri ce"

Yaseera ta gyara zama tace "ina jinki, nasam dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki, akan Jalal ne ya ake ciki? Har yanzu baki hakura ba?"

"ta yaya zan hakura yaseera, kinsan son Jalal ya zame min bala'i?"

"ban gane ya zame miki bala'i ba, ina dama can soyayya ta shiri ce zakuyi dan ya aureki?"

"yaseera wallahi ashe son gaskiya nakew Jalal ban san hakan ba seda yayi auren nan, Yaseera yarinyar nan muguwar player ce, wallahi soyayya suke kamar ya hadiye ta, Yaseera uwar sa fa yake gayawa wallahi ko a gaban waye se ya fada yana son matar sa, Yaseera zan iya rasa raina saboda yadda soyayya Jalal ke kara ruruwa a raina"

"tabdijan Ilham kinga da Jalal yana jin maganar mahaifiyarsa to tabbas zata tirsasashi ya aureki, amma yadda yake din nan a duniyar nan babu me iya raba shi da ita, ni tun a baya na fuskanci abun nan nasu akwai soyayya a ciki, Amma nayi gudun in gaya miki saboda karki ji haushi"

"to yaseera meye abunyi yanzu?"

Yaseera tace "wane kokarin ummanki take akan lamarin"

Dan tsaki Ilham tayi tace "itafa kawai burinta ta dauki fansa, bata tausayawa halin da nake ciki, itama Mummy bata ni take ba, kawai burinta ta raba Auren"

Yaseera tace "to mafita daya ce a yanzu, Amma ban san yazaki kalli abun ba"

"nidai gayamin koma meye zanyi"

"kin san da bakinki kika gayamin asiri baya tasiri akanta, sannan tunda Jalal ya riga ya aure ta nasan sun hada shimfida, abu daya zuwa biyu zakiyi yanzu, ki cigaba da hakuri kiyi duk yadda zakiyi ki tabattar babarsa ta raba auren nan, sannan kije ki karya sihirin da kukayi masa, idan har ya karye zeji maganar mahaifiyarsa, in yaso se kiyi kokarin kiyi wani asirin da duk yadda zakiyi mahaifiyarsa ta tirsasashi ya aureki "

Murmushi Ilham tayi tace

"kin kawo shawara Yaseera nagode sosai"

"Amma kije kiyi magana da Umman kiji me zata ce"

Dan zare ido Ilham tayi tace

"wace Umman, wallahi bazata yadda ba tabdijan, tunda naga kowa kansa ya sani nima kaina zanwa fafutuka, ta taba bani labarin inda taje akayi asirin, zan Lalla bata ta kara gayamin yadda abun yake, sena karya asirin dan burina ya cika, nagode sosai yaseera"

Yaseera tace "shikenan Allah ya temaka" daga nan Ilham ta samu relief ta saki jiki suka sha hira.

Kiran sallar Asuba da'akayi ne yasa Jalila ta farka, Addu'a tareda fatan Allah yasa ba mafarki bane, Allah yasa Ummi ce da gaske, ta bude idonta ta juya, kamar yadda ta saba gani wasu shekaru da suka shude,
Da gudu ta sakko daga kan gadon dukda ciwo da kanta yake ta rungume Ummi gam.

Cikin kuka take cewa

"Allah yasa ba mafarki nake ba, Allah in bacci nake Allah kasa in dawwama inayinsa, Allah kasa a jikin Ummina nake, Ya Allah.. Ya Allah...

Ummi tasa hannu ta dago ta, dukda Ummi hawaye take sharewa tace
" Haba Babyna, ba bacci kike ba, nice Ummin kice, kalleni nice"

Kara rungume Ummi tayi dan ji take kaman in tayi wasa Ummi zata kuma tafiya ta batta.

Dakyar Ummi ta lallaba Jalila tayi salla tana idarwa ta kuma kwanciya a jikin Ummi tace

"Ummi meyasa kikaki ki bari in san inda kike, inyu jinyarki da kaina? Na shiga damuwa na shiga kunci, Nayi kuka a lokacin da babu me rarrashi na Ummi, meyasa Ummi?"

Ummi ta numfasa tace "Jalila a lokacin da nake jinya ko kinzo bazan ganeki ba, i partially loose my memory"

Mikewa zaune Jalila tayi tana kallon Ummi, Ummi ta jinjina kai tace
"tabbas Jalila na manta da abubuwa da yawa a wannan lokacin, But Alhamdilillah idan bani na fada ba, babu me gane hakan se su Jalal da suka san nayi, da Mahmud tunda a gidansu nayi jinya"

"yanzu Ummi Yaya Mahmoud ma yasan inda kike amma aka rufeni, shiyasa ranar da ya fara ganina yace nice Jalila?"

"sosai makuwa, sannan duk iya shegen da kika dinga yiwa dana nasani, Inda Allah ya temakeki kema kinyi rawar gani gurin sauya rayuwarsa, Tun kuna kanana na fuskanci Jalal yana matukar sonki, Har Abeenki yace Insha Allah in dai yana raye in har kina son Jalal ze bashi, Abun Allah, Allah ya kaddara ke rabonsa ce, Jalila duk mutumin daze soka tun baka san kanka ba wannan shine masoyi na gaskiya, babu abunda ze sameki ya guje ki"

"Amma Ummi me yasa baki gayamin a baya ba?"

"ta yaya zan gaya miki? Kina fama da rashin ji da tsiwa, a lokacin ma ga abunda kike masa inaga na fada miki, Jalila hatta mafarkin da kike da Jalal nasani, kiyi ta surutai cikin bacci, nidai na dage muku da Addu'a ne"

Dan murmushi Jalila tayi
"tabbas Ummi Addu'a ki bata fadi kasa ba, Amma Ummi na sha wahala wallahi, naga kalubale daban2"

Nan ta labartawa Ummi wasu daga cikin gwagwarmayar da tayi, daga karshe tace

"Ummi da muna mutunci da Mummy sosai, Amma tunda Jalal yafara nuna yana sona ta tsaneni Ummi, kinga cin mutuncin da takemin kuwa?"

"Jalila Kamar yadda Allah ya tsamoki daga cikin kaddara daban2, karkiyi tunanin shikenan, dole ki fuskanci wata kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa da yake sone dan haka ki gode Allah kiyi fatan Allah yasa ki cinye dukkan jarrabawar ki.
Sannan ba abun mamaki bane dan bata sonki, tunda inkika tuna abunda tayiwa kanwarta da suke uba daya, ke a wa daba zatayi miki ba? Tsoronta daya kar a mallake mata da, shiyasa take ganin ke matsala ce a rayuwar danta, duk kirkinki Jalila baze taba yuwuwa kowa ya soki ba, dole wani seya kiki, karki taba tunanin kowa

Please Login or Register in order to submit comment