Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda kuruciya ta har kawo I yanzun"

"Ke waini sa'an wasankine? Wallahi koki matsa ko in tattaka ki"
Ya tureta gefe ya fice Abunsa, Abun duniya duk ya dami Ilham, Jawwad ne kadai ke iya sarrafa zuciyar Jalal wani lokacin, yanada matukar kafiya da taurin kai, gaba daya tunanin ta ya kwace.

Jalila takoma cikin gida ta tattara abubuwan dazata bukata dan gobe in Allah ya kaimu zata koma makaranta,
Karamar wayartace ta cika dakin da ringing, Jalila taga bakuwar lamba ta share tacigaba da Aikinta, amma still aka cigaba da kira har kusan karo uku, seda ta danyi tsaki sannan taja wayar tasa a kunnenta
Ajiyar zuciya akayi sannan akace "Masha Allah, kin karyamin record bana kiran mutum sama da sau biyu, komai tsananin bukata ta kuwa, Amma ta dalilin son danake miki har sau hudu ina kiranki"
Sarai ta ganeshi amma ta maze tace "ko zan iya sanin da wa nake magana"
"Ohh am sorry dear, bankoyi miki sallama ba, balle mugaisai nafara miki surutu, Ahmad ne"
"Ok Allah sarki yakake ya gida ya iyali"?
"Alhamdilillah queen, kin tafi bako sallama, ban san zaki koma kano ba ai"
"Aikam abune na gaggawa ya tasomin, in ban manta ba ranar agabanka aka kirani"
"Hakane fatan kowa da komai lafiya"
"lafiya kalau, ya na baroku?"
"komai lafiya amma kintafi kin barni da kewarki, duk lokacin danake wani abu kona rufe idona ke nake gani Jalila, kitemaki zuciyar maraya" ya karasa maganar cikin sigar magiya
"Kai karka bada maza mana, yanzu idan abokan Aikinka sukaji wannan aise suyi Maka dariya, babban soja kaman kai kana haka akan mace, macenma wata 'yar yarinya"
Murmushi yayi yace
"Jalila ai babu wani batun namiji ko soja in ana maganar fage irin na soyayya, ba ruwansa da matsayinka, girmanka ko mukaminka, ba ruwansa da na birni kona kauye, dan haka kidena wani batun maza"
"hmm Wannan bayani haka yakamata ka bude makaranta ka dinga bada darasi"
Murmushi yakumayi yace "Tunda haka kikeso ai se ayi, kece director mukuma dalibanki"
"Tab aini bansan komai a wannan harkar ba"
"Ahh haba dai?"
"dagaske nake fa"
"Aikam zan koyardake yadda yakamata"
"to shikenan seda safe, gobe in Allah ya kaimu zanje school"
"hakane hakan yayi kyau, Allah yabamu alkhairi, zamu hade a dreams zanbiyoki har kano kan shinfidarki"
Murmushi Jalila tayi "Allah yabamu Alkhairi"
Ta katse wayar ta danyi murmushi, can ta hango Nana ta shige bargo ga uban zafi se wani kashe murya take ba'ajin abunda take cewa, Jalila ta mike ta yaye bargon, Nana ta hada gumi amma ko zafin bataji saboda tana soyewa da Mahmud, Jalila tace "Allah ya shiryaki".

Ilham ta dade tana Nazarin me Jalila take nufi da Jalal baze tafi ba, danta fara karaya da lamarin Jalila yarinyar sekace Aljana idan tayi niyyar abu setayi shi.

Jawwad sam yaki kula Jalal gashi gobe in Allah ya kaimu karfe biyu na Rana ze tafi, yanzuma da Jawwad yadawo daga sallar isha'i daki yayi tafiyarsa ya kwanta, Jalal yabishi dakin ya zauna kusa dashi yace "Haba nawan yanzu fushi kake dani haka?"
Mikewa zaune Jawwad yayi yace
"Jalal dan Allah ka kyaleni, kace zaka tafi gaka nan ga hanya seka dawo"

"Jawwad nima inajin abunda kakeji a ranka, A tunanin ka rabuwa da kai abune me sauki a gurina, shekaru Ashirin da bakwai muna tare idan ban manta lissafin ba, Jawwad tafiyata shine samun saukinka, kaima ja maida kai karasa gina rayuwarka, bazan iya barin Nigeria gaba dayaba saboda ku biyu daddy zamu dinga haduwa a can dubai dashi"
"Jalal wannan ba uzuri bane ba, ni na gaba gayamaka na gaza da kai menakeyimaka na wahala, Allah ne ya hada jinina da kai bani da dan uwa Namiji kaidin nan dai tare muke faduwa mu tashi tsawon wannan lokacin, sannan lokaci daya kace Zaka barni tayaya zanyi farinciki Jalal"
"Am sorry Jawwad nasan babu dadi, kuma kana tunanin Wace irin Rayuwar zanyi a inda zanje, Jawwad Ina kokarin dena shaye2, A sanadinka a tsatsonka nasamu me haskamin bakar hanyar danakebi, dama lokaci dayawa kadaici da bacin rai dakuma miyagun abokai kesani kara kaimi gurin shaye2, Amma yanzu an janye miyagun abokai daga jikina, Jawwad idan na tafi inason in koma makaranta "
Sa sauri Jawwad ya kalleshi yace" dagaske kake? Da kanka kake fadin zaka koma Makaranta? "
" Kwarai kuwa zankoma Insha Allah "
Rungumeshi Jawwad yayi yana cewa" naji dadi dan uwana amma naso ace kana nan kusa dani, Amma dukda haka ni zan dinga biyoka Dubai din"
Kasan zuciyar Jalal ba wata makaranta kawai dan hankalin Jawwad ya kwanta ne
"kobakazo bama nizan dinga zuwa akai2"
Haka suka cigaba da hira.
Da wuri Yau Jalila ta shirya manu driver ya kaisu makaranta, 'yan ajinsu Jalila sunyi murnar dawowarta nan aka dinga nunawa wanda basu santa bama, hatta malaman dasuke tsangwamarta suke ganin bata iya komai ba tabasu mamaki kwarai dagaske, saboda ba'a mata tambaya ta amsa a Aji, se lokacin data ga dama take zuwa lectures, wataran ma bata Attending, bata handout sedai in malami zeyi lectures ta dakko jotter, idan malami yayi ba dai2 ba bazatayi shiruba setayi magana, wannan bakin nata kesawa a koreta daga Aji, Akwai malamin da har test ya hanata yi, Amma a haka babu wanda yake da points dinta a kaf department din nan, hakika wasu mutanen 'yan baiwa ne, shiyasa har Abada karka wulakanta mutane dan kowa baka san irin baiwar da Allah yayi masa ba. Ba iya dalibai ba hatta malamai sunyu mamakin Jalila ce takeda wannan kwazon.
Amma ita Jalila abunda yafi daukar hankalinta be wuce yadda har yanzu ake surutu akan abunda yafaru da Saleema da mahaifinta, Saleema ta warke amma bata iya shiga cikin mutane dan gaba daya ta dena zuwa makarantar, Sameera kam da farko ta tausayawa kawarta abunda yasameta Amma daga baya tunda aka sakesu daga police station tacigaba da abunda takeyi.
Jalila a ranta ta dinga jin anya kuwa ta kyauta abunda tayi, yanzu tayiwa Saleema dalilin dena zuwa makaranta, ta kunyata ta a idon duniya itada mahaifinta, Amma data tuna abunda Alhaji Kabir ya aikatawa Jalal, dakuma yadda ya dinga takuramata se yayi lalata da ita, da yadda ita kanta saleema suka addabi makarantar se taji hakan shi ya dace dasu.

Tun safe Jawwad ya bar gida sukayi sallama da Jalal yabar gidan.
Wajen sha biyu na rana Jalal yagama shirinsa tsaf, ya tsaya ya duba passport dinsa don yasa a karamar Jakarsa, Amma passport yace daukeni inda ka ajiye, ya duba ya duba amma be ganshi ba, hankalin sa ya tashi sosai ya duba kayansa be ganshi ba, gidansu yatafi ya duba dakinsa amma be barshi acan ba, yana kokarin fita daga dakin ne Mummy ta shigo dakin.
Ya tsaya yana kallon ta,
"Yanzu Jalal tafiya zakayi ka barni, laifina har ya kai ka kauracemin gaba daya, Haba Jalal koba komai nifa mahaifiyarka ce, kai kadai nake da baka tunanin halin dazan shiga inka tafi ka barni?"
Maganganun Mummy sam basuyi tasiri a zuciyarsa ba, seda yabari tagama gaba daya, kawai yaraba ta gefenta ya fice, danshi mugun haushin ta yakeji.
Mummy tarasa abunda yake mata dadi, ta zauna ta rushe da kuka a gurin, Abunda yakara bawa Jalal haushi be wuce yadda yana fitowa yakuma cin karo da Ilham ba, itama magaiyar take masa amma yai biris yai ficewarsa.

Jalal yayi duk tunanin daze yi amma ya rasa inda Passport dinaa yake, wayarsace tayi kara alamar sako ya shigo, Abuda ke cikin sakon ne ya razanashi sosai yasashi mutuwar tsaye wai an soke visa dinsa.
"Why!!!? Ya fada da karfi ji yayi yana neman ya fadi jikinsa na rawa, yanemi guri ya zauna ya dafe kai yai shiruu to laifin meyayi aka soke masa visa haka? Shidai yasan a Dubai be taba zuwa yayi laifi ba, Meyasa haka kodai Jawwad ne ya dauke masa passport, kai yasan Jalal beze masa hakaba Anya ba daddy ne yasa aka soke visa ba.

"Seka tafi in gani Ai, naga ta inda zaka tafi"
Maganar Jalila ya tuna, "to Amma tayaya Jalila zata iya sawa a soke masa visa, wata sani babba haka dazata saka ayi masa haka? Koma ita ta dauki passport dinsa, kai baya tunanin Jalila zatayi haka"
Amma dayayi shiru ya tuna irin gwaramar data hadawa Jeje da Alhaji Kabir abun ya zarce hankalin sa. Aikuwa a gigice ya tashi ya fito ya nufi gidansu.

Zahra batazo makaranta ba sunyi waya da Jalila tace mata batajin dadi ne shiyasa batazo school ba, bayan sungama lectures din farko Jalila tafita neman abunda zataci, gashi tana son zuwa banki ATM dinta yayi expire, dan haka ta siyi Ruwan jarka da biscuit tasaka a Jakarta ta nufi banki dan taje ta dawo da wuri, wayartace tafara ringing kaman karta daga, ta daga setaji muryar Ahmad, gaisawa sukayi suka shiga hira, Ahmad ya iya hira ga ban dariya shiyasa Jalila take sauraronsa, gashi ya iya soyayya da tattali, tabar department tayi nisa tana tafiya da waya a kunnenta taji Anyi wani jakin parking a bayanta, tsayawa tayi ta waiga a birkice dan ganin wani me kokarin ne haka, Amma wanda taganine yasa gabanta dukan biyar biyar, Jalal ne babu alamun Rahama a fuskar sa, ya tamke fuska sosai kamar be taba dariya ba.
Addu'a ta shiga yi a zuciyarta Allah yasa kar yayi mata tijara a bainar nasi. Ahamd yanata magana a waya amma shiru, Takowa yashiga yi yana nufota, yayinda ita kuma tarasa abunyi, ta kame a guri daya tana zare ido, yana zuwa yasa hannu ya janyo ta, ba musu tabishi ya bude gaban motar ya turata ya rufe, ya zagaya ya kunna motar yafizgeta a guje, tunda suka shiga motar bece mata uffan ba itama haka, Sedai tasaka hannunta ta rike kanta ta sunkuyar da kai dan tana matukar tsoron tukin Jalal, tukine na ganganci yakeyi kamar mara hankali.
Can Jalila taji yawan karar motoci ya ragu, A hankali ta bude ido taga sun doshi wani katafaren gida, yana zuwa masu gadi suka bude masa gate, ya shiga da motar yayi parking, se daga masa hannu sukeyi amma ko kula su beyiba,
bude motar yayi ya fito ya bude mata a tsawace yace mata "fito" ba musu ta fito yakuma fizgarta zuwa cikin gidan dabata san ko inane ba,
A can kasar zuciyarta tana ta Addu'a kuma tanada yakinin Jalal baze cuceta ba.
Suna zuwa wani tankasheshen palour, ya saketa ya kalli cikin idonta da yau ya raina fata take tsuma, a tsawace yace mata "Ina passport dina?"
"Ni ban dauka ba"
"Karya kikeyi"
"Niba karya nakeyi ba, ban dauka ba"
"Jaleela you are lying" jin yadda ya fadi sunan tayi ya tsarga tundaga kanta har kafarta.
"Nifa ba karya nakeba, dan Allah ka maidani, inada lectures fa"
"Ba abunda ya dameni bane, ni kika hana nawa uzurin kike gayamin kinada lectures, kibani passport dina"
"wai waya cemaka nina dauka? A ina zan ganshi?"
"keki gayamin jiya, kuma kika cigaba da rainamin hankali sena kakkaryaki, kibani passport dina ko in babbalaki"
"to Amfanin me zemaka bayan an soke visa?"
"Kekika dauka kenan? Ban abina tunda banaki bane, meyasa kikayimin haka? Akan me? Me nake tsinta a kasar nan banda bakinciki, Wace Rayuwa ce me Amfani nakeyi anan din, kowa yana kyamata da halayena babu soyayyar uwa a taredani ta fifita bukatarta akan farinciki na, se kokarin cusamin yarinyar dake neman halakani take, mahaifina danake da kwarin gwiwa akansa amma shike zargin ina neman mata, zaman menake a Nigeria banda takura da bakin ciki? Kowa kyamata yake akanme? Ba gara inje inda ba'asanniba inyi Rayuwata ba wanda yasanni ba, kibani passport dina" idonsa gaba daya ya koma Ja, jikinsa tsuma yakeyi.

Jalila ta fuskanci idan tayiwa Jalal rashin kunya yadda yake a fusacen nan ze iyayi mata ba dadi, dan haka ta kwantar da murya tace
"Shikenan is Ok, samu guri ka zauna zamuyi magana"
Cikin tsawa yace "bazan zaunaba, kibani passport dina"
"Idan baka zauna ba bazan gayamaka inda yake ba, Zauna tukuna"
Seda ya danyi jimm sannan ya zauna, ta zuge jakarta ta dakko ruwan da ta siya zata sha, ta bude ta mika masa, ba musu ya karba ze fara sha tace "Kayi Bismillah" seda ya dan harareta sannan yayi ya shanye ruwan se sauke numfashi yakeyi saboda bacin rai
"Kasan wani abu? Nina ga passport dinka akan center table na dauka, sannan nina saka aka soke maka visa"
Tsareta yayi da ido amma bece komai ba
"banyi haka dan inbata maka ba, nayi hakane dan sama maka mafita, kasan hukuncin me sabawa iyaye, muddin kayi tafiyar nan bada san ransu ba zaka iya samun matsala, Abokin Yaya laifin da mahaifiyar ka tayi maka wannan tsakanin tane da mahaliccinta, Amma abunda kake mata ba dai dai bane ba, kamata yayi ku zauna lafiya cikin hikima ka nunamata kuskuren da take aikawa, na baka misalai wancan karon daka kusa karyamin hannu, inkaji kaddarar wani zakaga taka ba komai bace ba, nima misali ce a gareka, na tashi ba mahaifi Allah ya karbi abunsa inada karancin shekaru, ga tsangwama saboda mahaifiyata daga baya ta musulunta, yanzu itama babu ita bansan a ina take ba, Natashi da kaunar Yayana, amma mahaifiyarsa batasona inaji inagani saboda kar mahaifiyarsa tayi masa baki na sadaukar da soyayyata na hakura "
Ta danyi shiru hawaye nabin fuskarta "ABDUL nasan dacin a tsangwami mutum amma kai da gatanka kana tareda iyayenka, kana da gata, suna kaunar ka wata kaddarace ta gifta dazaka iya gyarata, yau inka dena shaye2 ka gyara tsakaninka da Allah da iyayenka ze wuce kamar bakayi ba, nikuwa fa? Nasani ko Aure nayi se an gorantamin rashin dangin uwa, na ubanma waye Abba ne kawai, tare kuke da Yaya Jawwad kasan komai wani abunma ni bansaniba, Why Jalal, wanda yarasa iyaye yayi kuka, kai kana taredasu amma idonka ya rufe"
Sosai Jalila take kuka, yayinda jikin gogan yayi sanyi gaba saya, Jikin Jalal yayi sanyi matuka, kura mata ido yayi, yana tuno lokacin dasuke mata wasa shida Jawwad yana tuno abubuwa dasuka shude gaba daya tausayinta ya kamashi, handkerchief ya dakko a Aljihunsa, yana goge mata Hawayane yayinda taketa sheshaekar kuka kaman wanda akayiwa dole yace
"kidena kuka please"
"Ni kylaeni bazan dena ba din" tasa hannu a jakarta ta dakko passport din ta aje masa "ga passport dinka nan, seka dawo" tana kokarin tashi seji tayi yace
"Aina fasa" tsayawa tayi tana kallonsa
"Eh dagaske nafasa"
"Meyasa kafasa?"
"da farko kin dakukemin passport, kuma kin lallaba kinsa an sokemin visa daya zan tafi?"
"Kayi hakuri nasan kaji ba dadi abunda nayi, amma zaka iya nema na wani kasar katafi"
"Nafasa amma ya akayi kikasa aka soke visa na"
Ta goge hawayenta sannnan tace "daddy Hanan nagayawa ranar dazamu dawo, shine yace kar indamu zssa a soke"
Jinjina kai yayi ya danyi shiru tace
"nika tashi ka maidani"
"Saboda me?"
"Saboda haka nace, meyasa zaka kawoni inda ban saniba, ga gidan bakowa ni gaskiya ka maidani"
"hmm hakane nan inda baki sani bane, zan maida ke amma sekin gama kukan, nan gidanmu ne na gadon kaya inda aka haifeni, inda nayi rayuwa me dadi, dukda ba me dadi ce yadda nakeso ba, amma nayi Rayuwa dani da Jawwad daddy Rayuwa me cike da jin dadi" ya mike tsaye yace 'ina zuwa"
Ya hau kan benen ya dan jima sannan yafito da wata Jaka a hannunsa duk ta danyi kura, yadawo yasamu guri ya zauna, har yaje ya dawo Jalila bata dena kukan datake ba, yasa hannu ya dan karkade Jakar sannan ya bude zip din, wasu uban hotuna ne aciki masu tarin yawa, yasa hannu ya debo wasu, ya mikawa Jalila, tasa Hannu ta karba tafara dubawa a tsanake, fuskarta sharkaf da hawaye amma hoton farko data gani yasata yin murmushi, Jalal ne da Jawwad suna kanan basufi shekaru biyar ba sun zazzaro ido suna sanye da kaya iri daya, haka ta dinga kallon hotunan tana dariya, galibin hotunan hada Umminta a ciki kan wani hoto taje, Jalal ya nutsu ya dauki wata Jaririya yana kallon ta,
Tace "Wannan wacece? Kanwarka ce"
"gata nan dai kalleta baki gane wace ba?"
Jinjina kai tayi alamar Eh, karba yayi yakuma duba wani yabata yace "wannan fa" itace batafi shekara biyu ba Idonta duk hawaye Sunsata a tsakiya
Ba karamin dariya hoton yabata ba "Wannan ai nice"
"wancan ma kece ai"
"to a ina kasamu wannan hotunan haka"
"Abee yanada camera da, shiyake mana hotuna in aka wanko daya abawa Ummi daya abani nake tara nawa, wasu kuma a gurin ummi na karbesu, wasu hotunan bani dasu suna gurin Ummi"
"lallai ka iya Ajiya"
Nan tadinga kallon hotunan, har hoton Iyayen Ummi akwai seda ya nuna mata, gaba daya ya manta da fushin dayakeyi, ita kuma ta manta tanada lectures
kan wani hoto ta kai, Ummice a jiki da Abeenta, sunsakata a tsakiya duk sun kalleta suna murmushi, ta tsaya ta zubawa hoton ido, sekuma Hawaye ya shiga zubowa daga idonta kuka sosai
Jalal yai kuri da ido yana kallon ta, hannu yasa ya zare hoton
"Bani tunda kuka zakiyi, ban hotuna na"
Cikin kukan tace "yi hakuri na dena"
"baza'a hakuran ba, bani nan"
Yasa hannu ya tattare su, rikewa tayi "dan Allah kabari in karasa"
Yana kokarin fizgewa ne hotunan suka zube a gurin, idonta ne yakai kan wani hoto dayasa taji hantar cikinta ta kada.
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3๏ธโƒฃ6๏ธโƒฃ89

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]






_MY FIRST NOVEL _

Da sauri ta dauki hoton tace "Wannan wacece?"
Karba yayi ya duba sannan yace "bakisan wannan ba? Kakarkuce wadda ta haifi su Abba"
"Wannan ai kakar su Hanan ce"
"kamar yaya?" ya tambayeta cikin rashin fahimta, nan ta kwashe komai tagaya masa na zuwanta bauchi jinjina kai yayi yace "masha Allah, nina san wannan kamar da kuke ba'a banza ba, tabbas abunda kakar Hanan tagaya miki haka yake, Sun baro garinsune saboda hari da ake kaimusu, amma yanzu karkiyi saurin fada, Abba yakamata kifara samu da wannan maganar, ya dade yana bincike ko Allah zesa yasamu wani daga dangin iyayensa, tunda basu san kowa ba daga family dinsu, Inna kawai suka sani da baba"
"Allah yasa gaskene Su Hanan 'yan uwan su Abba ne, inda suke sunada yawa sosai estate ne guda gaba daya family dayane"
"' yan uwankune Insha Allah, bari in mayarda hotunan nan se in maida ke"
Ta gyada masa kai ta jirashi ya mayar ya dawo, ya kalleta yace
"muje ko"
Ta wuce gaba ya biyo ta abaya ta tsaya ta wigo ta kalleshi "dan Allah karkayi wannan tukin, dan Allah" bece komai ba ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga ya kunna motar, aka bude masa gate ya fita, masu gadi nata daga masa hannu amma yayi musu banza,
"Suna maka magana amma kayi musu banza ba dadi fa"
"to mezan musu? Ko sokike in sauka in tsaya ina surutu?"
"A'a bahakaba at least ko daga musu hannu kayi"
Be kuma kulataba ya cigaba da tukinsa,
Sarkar wuyansa ta kalla, sekace ba ฤan musulmi ba, "Kafasa tafiyar dai ko?"
"baki yadda dame na fada bane?"
"A'a ni banceba, Amma dan Allah kadena yi wa Mummy abunda kake mata, dan Allah"
"Waike ba Adda tagaya miki komai game da rayuwata ba mekikeso inyiwa Mummy?"
"Bahaka bane ba, inka mutu tana fushi da kai Allah ma zeyi fushi da kai, kila sanadiyar yafemata kaga Allah ya daidaita maka Al'amuranka, mutane zasu dena kyamarka"
"Anya Al'amurana zasu gyaru? Mutane bazasu taba sakin jiki daniba kowa ya riga ya gujeni se kalilan din mutane"
"Al'amuranka zasu gyaru inkaso mana"
"Ta yaya?"
"I will help you do that, sekowa ya dawo yana sonka"
"how?" ya tamabayeta a takaice
"Just believe me, you Can change, I will help you change your life, trust me"
Kallonta yayi sannan yai murmushi "I have trust you already, ko iya haka you bring a lot of changes in my world, Thank you"
"kasan wani abu daga lokacin da ka kasance tareda abunda kakeso lokacin kake kara samun nutsuwa da kusanci zuwa gareshi, Iyaye abun sone, dakana kokarin ka manta abunda Mummy tayi maka ka kyautata mata wataran zaka manta da komai"
"bazan manta ba kuma ni yadda take kara cusamin Ilham ke batamin rai"
"wai me Ilham tayi maka haka?"
Kallon Jalila yayi irin kin rainamin hankali
"kinsan komai amma kina rainamin hankali, lokacin dana kwanta a Asibiti kikace musu ina bacci, sunsaki baki itada mahaifiyarta naji duk abunda suke cewa kuma kina tambayta me tayimin bansaniba"
Dauke kai tayi ta danyi murmushi.
Suna shigowa bakin layin suka ga wani dattijo yanata tattare ledojin da suka dan bata layin, da Sauri tacewa Jalal ya tsaya
"me zakiyi?"
"Kaga dattijon can zamu tsaya mu gaisar kaimasa Alheri"
"saboda me?"
"Maganar me mukayi dazu, you want change"
Hade rai Jalal yayi "Wannan mutumin ba irin zagin dabemun ba farkon fara shaye2 na"
"kayi hakuri ka nuna masa ka manta please"
Jalal yaja motar suka karasa inda dattijon yake suka gaisa sukayi masa sannu da aiki, sannan Jalal ya dakko dubu daya ya bashi yasa hannu ya karba ya dinga godiya sannan suka wuce,
"Kiduba Ajiyata dana gaya miki"?
Ya jefo mata tambayar, Jalila bata son rigimadsa tasan intace Ilham ta dauka fada zasuyi dan haka tace
"Wace Ajiyar fa?" ta tambayeshi irin ta manta din nan
Ya gano so take ta raina msa hankali dan haka ya kyaleta yayi parking Akan idon Ilham Jalila ta fito daga motar Jalal.
Ilham aranta tace "dama tazo dazan bakantawa Jalila insa a tsanate" dan haka Ilham da gudu ta shiga cikin gida tana kwalawa Mummy kira ta samu Mummy a daki idonta yayi Ja saboda kuka tana lazimi
"Mummy wallahi Jalal bashida mutunci bashida Imani, duk yadda kikayi kina kuka bakyason ya tafi seda ya tafi, gashinan a banza mace tasashi ya dawo yafasa tafiyar, wallahi gaskiyar daddy Jalal neman mata yakeyi"
Cikin rashin fahimta Mummy tace "Ke bangane me kike nufi ba"
"Mummy Jalal yadawo be tafi ba saboda Jalila"
"Kamarya saboda Jalila?"
"Oho musu dai, wallahi gashi can shida Jalila sun dawo, saboda ita yafasa tafiyar"
"ke ya akayi kikasan saboda ita yaki tafiya?"
Ilham ta gyara zama tace "Mummy nifa shiru kawai nakeyi, Allah kadai yasan abunda nake gani a tsakaninsu, bana son yawan bata miki raine"
A fusace Mummy tace "Ilham bana son shirme da shashashanci, kimin bayani yadda zan gane, ban fahimci ke kadai kika san abunda kike ganiba kimin bayani"
"Wallahi Mummy ba tun yauba akan yarinyar nan bakiga rashin mutuncin da takemin ba, kuma wallahi ita take ziga shi yakemiki wani rashin mutuncin, har dakinsa take zuwa gurinsa, Allah kadai yasan me sukeyi"
Mummy tayi shiru tace "lallai yarinyar nan makira ce, agaban idona take bude baki tacewa Jalal mara tarbiyya, Ashe itama mara tarbiyya ce, tunda take biye masa suna lalacewa, wallahi bata isaba dole in nesan tata da dana, dan bazan zuba ido yana ta'amalli da itaba, akan me na yadda da ita ina mata kallon mutuniyar kirki amma zatayi min haka? Gaskiyar dsddynsa yana neman mata kenan inbahakaba uban me take zuwayi dakinsa, kema banda rashin mutunci ubanme ya hana ki gayamin abun tun farko"
" Mummy dan Allah kiyi hakuri, kawai nidai bana son ki tayara da hankalinki ne a zatona zan iya shawo kan abun, tunda naga abunda yafaru yau kalli banbamin dayake miki dankice kar ya tafi,

Please Login or Register in order to submit comment