Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa, ki manta dashi"
Sa'adah ce ke wannan maganar cikin fitsara da rashin kunya, Abba ya mike yana kokarin bar musu palourn su Jawwad suka shigo jin hayaniya yasa
Jawwad yace "Abba lafiya kuwa?"
"Rufe mana baki kasurgumin munafiki daga kai har ubannaka da waccan makirar jarababbiyar, kun shiga kunfita kafasa Auren yarinyata dan ku kunya tamu a duniya to ta Allah ba taku ba, Matsiyatan banza dana wofi hadda wai tabar gidan nan dadinta tanada gidan uba ba'a titi take kwana ba"
Yaya mairoce ta wangale makogaro taketa zazzaga rashin mutunci san ranta, ta kalli Naja tace
"Jeki kwasomin kayanki mu tafi, Nina gayamiki sekin samu wanda ya fishi, Azzalumai kawai"
Maama ke kokarin kwantarwa da Yaya mairo hankali ta hanyar cewa
"Yaya dan girman Allah kiyi hakuri, zan shawo kan matsalar nan, dan Allah"
Naja tace "ba wani shawo kan matsala, ni bana son karya irin wadda kika saba yi, an kaimin kudi kin lallaba kun hada kai ze auri wata, kuma ana kokarin yimin sharri wallahi Allah ya isa ban yafe ba aikin banza kawai"
A harzuke Jawwad yace
"Wallahi kika kuma zagarmin uwa sena wanka miki mari, baza'a Aureki dinba, waze Auri mace irinki ace itace uwar yaransa, Kika kuma zagarmin iyaye sena bata miki rai"
Aikuwa Yaya mairo tayi kansa ta hanyar cewa
"Rufemin baki mara mutunci, har kanada bakin magana, iyayennaka ba kananan mutane bane, masu baki biyu, matsiyacin ubannaka dan Allah ya bashi Arziki ze wulakanta munida yarana"
A fusace Nana tace "A'a kinga Yaya mairo dakata, ubanmu fa ba sa'anki baneba, Maama ce 'yar uwakki dan haka kuje kiyi keda ita, da kike kiran ubanmu matsiyaci ya gama muku komai, dawainiyar ku ba wadda baya dauka yayi muku rana, da tsiyar tasa da kike fada ya muku rana ya maganta muku abubuwa dayawa, meye ba' ayi muku a gidan nan, wani abunma ku sata sann.........
"Ke Nana rufemin baki, Yaya mairon Sa'ar kice? Maama ta katse ta,
Jawwad juyawa yayi ya fice, dan a rayuwarsa baya son tashin hankali sam,
Nana tace "Allah sarki Jalila baiwar Allah, dukda abubuwan dakike mata Maama nasan Jalila bazata taba kallon tsabar idonki takira ki da makaryaciya ba, yau sega wanda kikeso din suna zagin ki, dama Allah ai ba Azzalumin sarki bane, musamman Naja tazo gidan nan danta kori Jalila, ga reshe ya juye da mujiya ai, bata kori Jalila ba, bata auri Jawwad ba kuma ita an koreta"
Nana tai wucewarta zuwa daki ta barsu a tsaye cirko2 suna cigaba da masifa.
Nana na shiga dakin ta tarar da Jalila ta kima bargo akanta tanata bacci duk hayaniyar nan baccinta take, Nana ta tatttaro kayan Naja ta fito mata dasu palour ta ajiye,
Tace "ga kayanki nan, daga nan bama bukatar ki a dakinmu"
Ta juya takoma daki tasa key, ta barsu da Maama a gurin.


Jawwad sam ransa ba dadi, bangare daya yana cikin farinciki, bangare daya kuma ransa a bace yake ya tafi dakin Jalal domin suyi hira, yagaya masa halinda ake ciki, Amma abun haushin yana zuwa ya tarar da gogan yayi mankas baccin sa kawai yakeyi, dan dafe kai Jawwad yai ya zauna ya tattare kayan shaye2n gefe daya, ya zauna a gefen gadon Jalal, yana kallonsa garin da dan sanyi sanyi ga fanka ga A. C Amma Jalal gaban goshinsa se zufa yake, Jawwad ya dan girgiza kai, tareda fadin
"Allah ya shirye ka dan uwa" sannan yasa hannu ya daddaki pillow da Jalal yake kai, a hankali Jalal ya bude ido ya saukesu akan Jawwad ya mayar ya lumshe idonsa, Jawwad yace
"Jalal ka tashi kai salla" dan karamin tsaki Jalal yayi yace "nika kyaleni please"
"haba Jalal bakayi salla ba, ka daure ka tashi mana"
Juyawa Jawwad baya yayi ya rungume pillow se ya tuna maganar Jalila
"Inkaana Ibada, kana Addu'a Rage wasu Abubuwan"

Sekuma ya danyi juyi ya mike da kyar yaje yai wanka da Alwala yazo ya gabatar da sallar Azahar da la'asar, fuskar nan tasa murtuk kaman be taba dariya ba.
Jawwad ya dinga masa hira yana bashi labarin abubuwan da suka faru a Bauchi, da dramar da aka gama yi a gidansu yanzu, Amma se ya lura sam hankalin Jalal baya kansa yayi zurfafa a tunani ne, lokaci zuwa lokaci ya kanyi tsaki.
Jawwad yace "Jalal wai me yake damunka ne? Ina ta magana hankalin ka baya kaina, se faman tsaki kake, menene?"
Ajiyar zuciya Jalal yayi sannnan yace "Bakomai don't mind me"
"ban yadda bakomai ba, ka gayamin please"
"Am serious bakomai, kawai yanayin ne bayamun dadi"
"to Allah ya sawwake, Amma Jalal kwana biyu ina ta murna ka dena zuwa club, shaye shayen ma kaman ka dena amma nazo na tarar kasha giya, haba Jalal why"
Dan shiru Jalal yayi dan yanajin muddin baze rabu da wannan damuwar ba akwai yuwuwar yakoma ruwa tsundum, dan maganganun Jalila sunyi matukar tasiri a zuciyarsa, a fili yace
"Am sorry Jawwad, ina bakin kokarina, kasan wani lokacin halinda nake shiga idan ban shaba, Amma Insha Allah very soon zan dena gaba daya"
"to Allah ya amince"
Daga nan Jawwad ya lallaba Jalal ya jashi suka fita zaga gari da nufin ya debe masa kewa.

Seda aka gama wannan tarzomar aka gama su Yaya mairo suka tafi sannan Allah ya nufi Jalila da tashi daga baccin da take, ta kalli Nana tace "Nana meyasa baki tasheni ba? Gaskiya na sha bacci tunda na dawo na kwanta se yanzu na tashi"
Nana tace "Mhmm ke kinta bacci bakisan drama da'akayi ba yau"
"Tame fa?" Jalila ta tambayi Nana irin bata san meyafaru ba,
Nana ta labarta mata komai, Jalila ta jinjina kai ita babban abunda ya bata mata rai be wuce yadda Nana ta gaya mata irin cin mutuncin da suka dingayi wa Abba ba, hatta zagin da sukayi wa Maama yabata mamaki, bata taba zaton zasu yiwa Maama hakaba saboda yadda take kyautata musu.
Nana ta gayawa Jalila cewar tunda Abba ya shige daki da wannan abun yafaru ko Abinci be ciba, ba karamin tausayin Abba ne yakamata ba takara tabattar da Yaya mairo daga ita har Yaranta basuda tarbiyya dan haka Jalila salla kawai tayi ta shiga kitchen ta dora Abincin dare saboda Abba ya samu yaci.

Sunkuma waya da Ahmad ya gaya mata yauma tayi hakuri abubuwa ne sukayi masa yawa shiyasa baze samu zuwa ba, Jalila ta karbi uzurinsa saboda yanayin aikin nasa.
Jalila ta shirya Abinci me rai da lafiya, bayan sallar magariba ta kaiwa Abba nasa har daki, Amma da mamakin ta ta same shi cikin fara'a, yace "'yar gidan Abba Girki akayi min haka ne?"
"Eh Abba, gashi nan kaci ka koshi sannan inzo inji Albishir din da zakayi min"
Yai murmushi yace "Ai Albishir din bana kine ke kadai ba, ki kira womin sauran' yan uwanki muci Abincin tare"
"to shikenan Abba yadda kace haka za'ayi"
Haka kuwa akayi taje ta kira Nana, ta wuce dakin Jawwad dan kiransa, Amma Jawwad yanata rubuce2 shikuma Jalal yanata babbakawa cikinsa hayaki.
Dauke kanta tayi kaman bata ganshi ba tace "Mutanen Bauchi, Yaya Jawwad ko kanemeni ko?"
Haka nan jin muryar ta yasa gaban Jalal faduwa har yake kokarin boye sigarin hannunsa
Jawwad yace "nina isa, dazu na shiga cikin gidan amma na tarar ana fitina shiyasa na tafi"
"to shikenan, Abba yace in kiraka duk tare zamuci Abinci saboda Akwai Albishir daze mana"
Jawwad yace "Allah Auta, wane Albishir zeyi mana?"
"Ahh kajika ai kai yakamata in tambaya, tunda tare kuka dawo"
"to shikenan gani nan zuwa" Jalila ta mike ta fice, Sam Jalal beji dadin wannan dauke kan da tayi masa ba, Jawwad yace "Jalal zo muje"
"A'a jeka seka dawo" Jalal ya bashi amsa, Jawwad yace
"Wallahi baka isaba, tashi muje, Abban bakonka ne? Yakamata muje tare"
Jawwad ya takurawa Jalal, badan yaso ba ya bishi, suna shiga palourn Abba Idon Jalal akan Jalila yafara sauka, tana sanye da riga da skirt na Atamfa, kaman ajikinta aka dinkasu cif dasu, tayi parking din gashin ta, ta kashe dauri ba kwalliya a fuskar ta amma tayi kyau matuka, bata kalli inda Jalal yake ba suka cigaba dayiwa Abba surutu ita da Nana, Su Jalal suka Zauna, Jalal suka gaisa da Abba, Abba yace Jalila zubawa su Jalal Abincin mana"
Ba tace komai ba ta fara zuzzuba musu Abinci, dakin yayi shiru suna Cin Abinci se surutun Nana dake tashi, gaba daya Jalila takasa sakewa taci Abinci saboda tsabar kallon da Jalal yake mata, bakowa ze gane ita yake kallo ba amma ita tasan ita yake kallo, shi kansa ba iya cin Abincin yake ba jujjuya cokali kawai yakeyi, Jalila tace "Abba ka gayamana Albishir din naka, nifa duk na kagu inji"
Abba yayi murmushi ya kalli Jawwad yace
"Jawwad gaya musu mana" sunkuyar da kai Jawwad yayi yana murmushi, Abba na yayi murmushi sannan yace "Na canza maganar Auren Naja da Jawwad, zuwa Jawwad da Hanan, nan da wata hudu Insha Allah"
Wata irin Ajiyar zuciya Jalila tayi, Nana tace "dama ni zuciya ta tabani, Masha Allah, Allah yasanya Alkhairi ya nuna mana lokacin"
Jalila tace
"Abba ni na rasa abunda zance gaba daya, mungode Allah daya sa ka gano abunda nake ta maka nuni, Abba Allah yasaka da alkhairi wannan aini akayiwa ga Yayana Kuma 'yar uwa ta, Amma shine Yaya Jawwad baka gaya mana ba, itama Hanan bata gayamin ba"
Abba yace "Itama Hanan din bata sani ba ai, daddynta be gaya mata ba, sannan babban Albishir na biyu shine; Kakar Hanan itace yayar mahaifiyar mu, Inna Asma" au"
Da Sauri Jalila ta waiwaya gurin Jalal dan in bata manta ba sunyi zancen da shi, amma kawai ta basar tace "Abba tunda naje tabani Labari nayu tunanin hakan, Amma nayi shiru ban fada ba saboda bani da tabbas, godiya ta tabatta ga Allah"
Jalal yai karfin halin cewa "Abba kaga yadda Allah ke juya lamarin sa, a baya kayi ta bulayin neman danginka, ashe suna tare da kai baka sani ba, ina tayaku farinciki Abba, Allah yakara hada kan iyalanka"
"Ameen Ya Allah ABDUL JALAL, Amma naji dadin wannan Addu'ar taka, kuma zance ka gaskiya ne, na dade ina bulayin nemansu amma ba zato ba tsammani na samesu ta silar 'yar Auta ta"
Sukayi murmushi gaaba daya. Abba ya dora da cewa " munyi magana da daddynka, Jalal ranar Asabar Insha Allah zasu kawowa Mahmud kudin Aure, suma tareda na Jawwad za' a hada, gaskiya zanso a hada da naka, yadda kuka taso tare ga aiki ya samu kamata yayi a hada da kai gaskiya"

Dan guntun murmushi Jalal yayi wanda iyakarsa lebensa yace
"Abba Jawwad dai yayi, nikam se yadda Allah yayi, babu uba nagari da ze bawa ďan shaye2 auren 'yarsa, koda za' a bani saboda dukiya ta ne"
Gaba daya tausayinsa seda yakama su
Abba yace
"karka damu kaji Jalal, babu wanda ze hanaka 'ya, kai mutumin kirki ne, wanda ya zauna da kai ne ze gane hakan, Insha Allah komai ze wuce, ka cigaba da Addu'a sannan ka dinga kokarin ka dena shaye2, babu abunda ze hana abaka' ya Aure" jinjina kai Jalal yayi yace
"to shikenan nagode Abba"
Nana ta dan zumbura baki tace
"Abba wai meyasa baza'a hada dana Jalila bane?"
Abba yace "Saboda ban gaji da ganinta ba"
"Auni ka gaji da ganina kenan?" Nana tai maganar kaman zatayi kuka.
Abba yace "A'a Munyi maganar da Babanta, yace; Abari ta kammala karatu tukuna saboda yanayin Aikin Ahmad din, nan da shekara daya ne zata kammala in Allah yasa zamu gani itama zan Aurar da ita ga Ahmad"
Gaba daya kunya ta kama Jalila ta mike tace
"nikam seda safenku Abba" ta mike da sauri ta bar palourn, gaba daya Jalal ji yayi kaman Abba ya masa yayyafin wuta a kirjinsa, shima ya mike yai musu seda safe.
Haka suka watse daga palourn Abba, babu wanda yabi takan Maama balle susan halin da take ciki, ta kule a daki ta rasa abunda yake mata dadi, bata taba zaton yaran yaya mairo zasu iya zaginta ba, gashi mijinta da yaranta ma sundena shiga harkar ta suna fushi da ita.

Koda Jalal ya shiga gida, part din Daddy ya tafi, yana zuwa kaman wani karamin yaro ya tarar da daddy yana aiki akan system, Mummy na gefe suna hira, yana zuwa ba tareda ya cewa kowa komai ba ya zauna kusa da daddy ya kwanta akan cinyar sa yayi shiru kaman mara lafiya.
Daddy yace "Jalal lafiya kuwa?"
Jalal yace "daddy Anmin screening da interview, an turani Lagos zanyi wata uku acan, Jawwad ze tafi nasa gurin Aikin next week Monday "
Daddy yace "Eyya shiyasa ka damu haka? Kayi hakuri kaji yaron kirki, yasa haka shine mafi Alkhairi a gareku"
Mummy tace "nifa gaskiya bana son wannan aikin da zeyi, meya nema ya rasa da ze tafi wani yawo daban"
Mikewa Jalal yayi tareda yin tsaki yabar dakin, ya koma Part dinsa, koda ya koma ya sauya kaya ya kwanta domin yayi bacci amma abu ya ga gara, juyi kawai yakeyi idonsa ya bushe, ta shi yayi zaune ya kurawa teddy dinta da carbin da ta bashi ido, abubuwa da dama na masa yawo a kwakwalwa, Espicially lokutan da sukeyi tare, yana kallon teddy ya tuna lokacin da take rike da teddy ga sweet abakinta tana dariya, yana tuna tsiwarta, kwarin gwiwa, tausayinta, nasiha da murmushinta, ya tuno maganganun Abba dazu wai za'a Aurar da ita ga wani AHMAD!!! gaba daya yaji kansa yana juyawa, yazama dole ya nisanta kansa da duk wani abu da zazesa ya dinga tunata, Baze manta Alkhairan ta ba, tunani yakasa barinsa dan haka ya mike ya fice daga gidan gaba daya.

Jalila ma juyi ta dingayi tana tunani da tausayin Jalal, tabbas Jalal abun tausayi ne, yana bukatar me jansa a jiki musamman yanzu da Jawwad zeyi nesa dashi, tana fargabar yakoma shaye2 kamar da, Amma a yanzu bazata iyayi masa komai ba, dan gudun kuma fadawa mummunan zargin da mahaifiyarsa ke mata. A takaice se gefin Asuba bacci ya dauke ta

Jalal be dawo gida ba se Asuba, yaje club ya kwana yana shan giya, seda yayi mankas, da Asubar ma bata sake shi gaba daya ba ya dawo gida cike da maye.

Yau tun bayan da Jalila ta dawo daga school, tayi waya da Ahmad ya gaya mata yau zezo, dan haka se shiri take domin tarbarsa.

Jalal tunda giyar ta sake shi, yai wanka ya shirya kayansa daze bukata a Akwati, yaje cikin gida yai sallama da Daddy, yaita saka masa Albarka tareda fatan Nasara, tunda Ilham taji batun yasamu Aiki ta hanyar Jalila, kuma zeyi wannan tafiyar akan Aikin, hankalin ta ya tashi, wai se yayi wata uku acan, to in baya nan tayaya zata cigaba da gudanar da aikinta akansa?.

Karfe biyar yagama shirinsa, saboda Jawwad ne ze kai shi Airport, ya sa hannu ya dauki teddyn Jalila da Alqur'anin nan da kuma carbin data bashi, ya nufi gidan su Jawwad, saboda so yake ya nesanta kanshi da dukkan wani abu daya shafe ta.

Amma abunda yayi tozali dashi bayan ya shiga gidanne yasa yaji tamkar jijiyoyinsa sun dena harba jini yadda yakamata.
Autar Ummi wato Jalila ya gani tayi kwalliya cikin wani dankareren leshi, tayi kyau matuka suna hira da Ahmad, kai da gani suna cikin shaukin soyayya, Jalal yaji wani Abu ya tsarga masa tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, kirjinsa yai masa nauyi matuka A hankali yafara jan kafarsa dayake ji tamkar ba nasa ba ya nufi inda suke.
Idonsa Akan Jalila har ya karasa inda suke, Jalila ce tafara daga kai tana kallon sa, gani tayi kamar ya danyi rama, yana zuwa Ahmad ya miko masa hannu da nufin su gaisa, kawai Jalal ya daga masa hannu, ya zubawa Jalila idanunsa da sukayi jawurr wanda yasa hantar cikinta kadawa,
Ya ajiye mata Alqur'anin, a gabanta da teddyn, ya juya ya nufi hanyar fita




Masu kirana a waya please am sorry, ku dinga min magana ta what's App, ina kokarin duba messages, amma kira musamman idan ina aiki, bana samun daga bakuwar lamba am sorry.
Ina godiya da kulawa.



Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Watpad @Ayshercool7724



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣4️⃣97

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Shiru Jalila tayi ta kalli kayan daya ajiye mata sannan tabi bayansa da kallo har ya fice daga gate, din shiru tayi ta tafi tunani, Ahmad yace
"my queen, meya farune?"
Da sauri ta dawo hayyacinta tace "bakomai fa"
"Amma waye wanan?" ya tambayeta yana me kureta da ido, ta dan sauke numfashi tace "Yaya na ne"
"Yayanki queen, ba Jawwad ne kawai Yayanki ba?"
"Abokin Yaya Jawwad ne, dan haka Yayana ne kawai"
"Amma babu wani abu a tsakanin ku kuwa?"
"Meyasa kake min wannan tambayar? Ko baka yadda dani bane?"
"Ahh haba waneni ince ban yadda da gimbiyata ba, ina so ne in tabattar da abunda ke tsakaninku, dan da idonsa yana shaye2"
Ba karamin haushi maganar Ahmad ta bata ba, kenan shima yanayi, in ba yanayi ba, ba abunda idon Jalal yayi dayake nuna yana shaye2, dan haka tace
"baya shan komai, kawai bashi da son magana ne, baya kula mutane"
Kyaleta Ahmad yayi yaga alamar bata son zancen suka cigaba da hira, Jawwad ne ya fito ze wuce su Jalila ya tsaya suka kuma gaisawa da Ahmad dayake dazu sun gaisa, Jawwad yace "to sirikina zan iya ce maka se anjima, ni zan tafi kai Jalal airport ne"
Da sauri Jalila tace "Ina zashi?"
Jawwad yayi murmushi yace "Aiki mana, an tura shi Lagos, se lokacin biki inaga ze dawo, bari inje karyai ta jirana, kin san baya son jira, se anjimanku" Sukayi sallama da Ahmad ya fita.
Ahmad ya maida idonsa kan Jalila yace "Gimbiya naso a haďa bikin nan hada namu, na kagu in mallakeki"
Murmushi kawai tayi amma hankalinta baya kansa, tanata zancen zuci ne, dayaga haka yace "queen naga kaman Akwai abunda yake damunki, bari in tafi semunyi waya"
Ta mike ta rakashi har bakin gate sannan ta dawo ta zauna akan kujerun tana nazari
"At least yakamata ace sunyi sallama da Jalal, tayi masa nasiha, Amma bata tunanin zata iya kuma rabarsa ba saboda mahaifiyarsa.

Jawwad ya ga sam fuskar Jalal a daure take, babu alamar walwala ko fara'a, Jawwad yai masa magana yafi a kirga, amma ko daya be bashi amsa ba, dan haka ya kyleshi suka cigaba da tafiya a haka kaman kurame.

Gajiya Jalila tayi da zaman tunanin ta mike ta tafi cikin gida, Nana tana zaune a palour suna waya da Mahmud,
"Nana waike dan Allah ba kya gajiya da wannan wayar ne? Kuyita surutu tun ana fadar gaskiya se an koma fadan karya"
Nana taki kula ta seda ta gama wayarta sannnan tace
"waike Baby an gaya miki kowa irin kine me tsarin tsiya, ke yadda ba kya son yawan waya kowa ma hakane, ai a rana inji muryar Mahmud sau hamsin bazan gajiba, musamman mu da muke distance relationship, ai Ahmad din nan ma ban wani yadda kina sonsa ba"
"Inasonshi sosai, amma hakan bashi ke nufin a dinga uzzuramin da surutu ba"
"Hajiya Jalila, kyaji da shi dai"
Hanan ca ta kira Jalila a waya, ta daga tasa a kunnenta
"hello Baby, 'yar uwata rabin jikina ashe Family dinmu daya Baby? Narasa inda zan sa kaina dan farinciki, dazu Abba yake gayamin kuma wai an kawo kudin Aurena da Haidar, Baby na rasa me zanyi dan farinciki"
Murmushi Jalila tayi tace "na riga ki ji ai, kiyi Azumi ki godewa Allah"
"queen na rasa inda zan saka raina dan farinciki, daddy yace zasuzo karbar kudin Nana, narasa yadda zanyi dan murna"
"haka Al'amarin ubangiji yake Hanan, yana juya komai yadda ya so"
"Hakane Queen, amma naji haushi da baza'a hada da nakiba, ni ina Jalal ne ma?"
"yaje interview din nan ai, an turashi lagos zeyi wata uku"
"Allah sarki bawan Allah, wallahi Jalila bana kaunar Aurenki da Abokin Yaya Yusuf din nan, in duniya da gaskiya Jalal ya kamata ki Aura"
Wani dogon tsaki Jalila tayi ta kashe wayarta, dan bata son Hanan ta bata mata rai.
Jalila ta mike har zata bar palourn taga Maama tazo ta wuce kitchen, gaba daya Jalila bata jin dadin yadda kowa ya fita harkar Maama, dukda abubuwan da Maaman tayi mata, Akwai lokutan da ta kyautata mata, dan haka taga be dace ta mata hukunci da laifin da take mata ba, dan haka tabita kitchen din, Maama na kokarin kunna gas Jalila tayi maza taje ta karbi lighter tace "Maama kawo in kunna miki, me zaki dafa?"
"barmin Abina zanyi"
"A'a Maama, tunda ba abunda nake ki barshi in dora miki"
Jalila ta karbi lighter ta kunna gas, dan jimm Maama tayi tana Kallon Jalila, yadda Jalilan ke Acting kaman Maama bata taba yi mata wani abu na bacin rai ba.

Jawwad suka isa airport yayiwa Jalal Sallama amma ya amsa masa a ciki, sam baya walwala, yasan halin Jalal baya son takura, tunda be niyyar gaya masa meke damunsa ba, ya ja Akwatinsa yayi gaba yabar Jawwad.
Haka Jawwad ya taho yanata tunanin me akayiwa Jalal yake wannan bacin ran haka?

Bayan Jalila ta gana yiwa Maama girki, ta koma daki, ta dauki Alqur'anin nan tana ta jujjuyawa, Kamshin turaren Jalal yakeyi, hakama dan teddyn ta, tasa hannu ta ta dinga duba Alqur'anin nan page by page, amma sam bata ga komai a ciki ba, kodai Jalal dama yana son raina mata hankali ne kawai?
Shiru tayi ta tuna yadda taga yana yinsa bayan ya gansu tareda Ahmad, Fuskar nan tasa a daure babu alamun sassauci, tayi shiru ta cigaba da zancen zuci, ;yanzu ze tafi lagos bashi da kowa a can, babu me kula dashi, Allah kadai yasan meze aikata,
"kinfi so in cigaba da shaye2 na ko? Ke Garkuwa ce a gareni" ire iren wannan maganganun nasa da Maganganun Antynsa da take gaya mata tabata amanar Jalal ne yasa take tunanin Anya hukuncin data yanke yayi dai2 kuwa?
To Amma nikuma mutuncina fa? " gaba daya ta rasa me yakamata tayi? Yanzu tana gaya Hanan, tasan Hanan zata canza mata magana tafara kawo wani abu daban, dan haka tabar Abun a ranta ta cigaba da Yiwa Jalal Addu'a.

'yan kwanakin nan sam Abba ya dena shiga

Please Login or Register in order to submit comment