Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace

"ke kimin bayani wai ina kukaje akayi muku hakan? Bangane me kike nufi ba"
A fusace Naja tace "Wai meyasa ba kya ganewa ne, nace miki gidan Jalal ta ja mu, yasa 'yan sanda suka kamamu, ni sun sakeni ita tana can"

"A' ahh to me kukayi masa? Wani station dinne?"

"dan Allah ki barni in huta, Allah kadai yasan azabar dana sha ta yunwa amma kin uzzuramun da tambayoyi, niki kyaleni da banyi niyyar zuwa gidan nan ba amma ta jani ta janyomin masifa"

Hankalin yaya mairo ya tashi sosai, gashi Naja taki ta tsaya tayi mata bayani yadds yakamata .

Jalila ta kira Hanan suna ta waya tace

"gaskiya Hanan kina wahalar da bawan Allah, yau kice wannan gobe wancan haka akeyi"

Hanan tace

"Jalila duk yadda zan Gaya miki bazaki gane ba seyazo kanki tukuna"

Jalila tace

"ba wani hadda shagwabarki da neman magana"

"wallahi Jalila ina jin tausayin Haidar sosai, bana laulayi se dai bakomai nake iya ci ba shine kullum ke nema min me zanci, Amma ba yadda zanyi ne"
.
"Allah sarki, Allah yarabaku lafiya, wai watan cikin naki nawane?

" wata na biyar "
Zare ido Jalila tayi " wai har munyi wata biyar da Aure? Amma kina shiga kikayi karo da shi? "

Hanan tace

"ban saniba, da shi naje, 'yar rainin hankali wallahi satina biyu, naita ciwon kai muna zuwa Asibiti aka ce cikine"

Dariya Jalila ta dingayi tace "angama iyayin, ana zuwa akayi karo, Allah yaraba lafiya"

"Ameen dai, ina mijin naki, fatan dai komai lafiya?"

"yana nan lafiya" Jalila ta bata amsa

Hanan tace "Ina fatan komai Lafiya Jalila, Allah yasa kun daidaita"

Jalila tace "gamu nan dai"

"gaku nan dai kamar yaya? Har yanzu ba kwa shirin ne"

"munayi sama sama"
"Jalila waike wane irin taurin kaine dake haka?"

Jalila tace "ke karki min fada mana, kin dameni fa, se anjima tafi gurin mijinki kiyi masa". Seda sukayi dan fadan da suka saba sannan sukayi sallama.



Jalila ta tashi ta dauki zuma ta nufi dakin Jalal, yana ganinta da container zuman nan ya hade rai, murmushi ta farayi tana cewa

"meye kuma na wani hade rai, sekace kaga wani abun gudu"

Jalal yace

"nifa nagaji da shan wannnan abar, kullum kizo kiyita bani, ciwon ciki take sani fa"

Jalila tace

"Ai ciwon cikin ba me damu bane, saboda magani nake baka, so nake inyi substituting din giyar da kake sha da zuma, kuma karatun qur:ani ne a ciki, Insha Allah very soon zaka dena shan giya"

Jalal yace

"ko yanzu ma aina dade ban sha giya ba, dan Allah ki dinga kyaleni da zumar nan, kodai wani abun kike zubamun, dan ki mallakewa Mummy danta?"
Yai maganar yana kashe mata ido, tareda yin murmushi

Dariya Jalila tayi tace

"Kai mallake ka wani wahala zemin ne, ai base na baka magani ba idan ina son hakan?"

"Allah ko?"

Jalila tace "Eh mana, yanzu dai karbi ka sha spoon biyu kawai"

Seda ya bata rai sannan ya karba ya sha yana ya tsuna fuska, dan jan dogon hancinsa tayi tace

"barakallahu fik"

Jinjina kai kawai yayi bece komai ba
A shagwabe Jalila tace

"baka fada ba fa"

Yace "Ameen, thank you"

Murmushi tayi ta shafa sumarsa "weldone dear, bari muyi Adhkar seka kwanta ko?"

Jalal yace "yadda duk kikayi"

Jalila tace "yawwa kafin muyi Adhkar bari muyi magana, wai yaushe zaka koma aiki? Kullum kana gida se dai kaje ka zaga gari ka dawo"

"bazan koma aikin nan ba"

"meyasa?"

" bashi da Amfani ina can zuciya ta tana nan, sam bana samun nutsuwa, ga banbancin Al'adu da dabi'u da muke dasu, gashi nika dai nake tafiya babu ke, akwai damuwane gara inyi zamana inta ganinki kullum ina jin dadi"

Jalila tace

"Haba Jalal, dan Allah ka dena wasa, Aikin nan yana da mahimmanci sosai, at least you have something to do, dan Daddy yana baka duk abunda kake bukata, bashi ke nufin kaima bazaka nemi naka ba"

Jalal ya danyi murmushi yace

"waya ce miki Daddy ne kemin komai? Nasan Daddy yana min wasu abubuwan amma da kudina nake komai musamman abunda ya shafi gidana, da kefa mukaje kika ga kamfani na, Daddy ne kadai da wasu daga ma'aikata na suka san nawa nake samu a duk wata a kamfanina, Allah ya alabarkaci dukiya ta fiye da yadda kike tunani, dukda na kasance me sabon Allah, Amma Allah ya hadani da mutanen Arziki masu Amana da suke juyamin dukiya ta"

Jalila tace "Amma in hakane, yakamata ace ko kamfanin ne kaje ka dinga aiki"

"ke bazani ba ki kyaleni kawai"

Jalila tace "to shikenan na kyaleka, amma gaskiya yakamata a ce munje gida ka gaida Mummy, tunda kaga harta fara magana, baka kyauta ba sam"

Maimakon yayi magana ma harararta yayi yaja pillow ze kwanta, tasa hannu ta rike pillow

"Haba Jalal idan kayi hakan baka kyauta ba, iyaye hakuri ake dasu komai girman laifin da sukayi maka sun gama komai tunda suka kawoka duniya"

Sakar mata pillow yayi ya juya ya kwanta,
gadon ta hau ta cigaba da magana

"Please Jalal, dan Allah yakamata kaje wallahi"

Janyota yayi jikinsa ya rungumeta kam a jikinsa, sosai ta firgice da abunda Jalal yakeyi mata.


"Jalal dan Allah ka bari bana so, ana knocking kofar parlor fa"

Cikata yayi ya lumshe ido, dirowa tayi daga gadon takoma gefe tana kallonsa tareda sauke numfashi, ci gaba da knocking akayi, Jalila tace
"Ana knocking fa"

Jalal yace "kije ki bude mana"

"ni gaskiya tsoro nakeji bazan iya budewa ba"

"ni inje in mutu kenan"

"A'a niba haka ba, kaje ja duba dan Allah"

Jalal ya kalli agogo goma saura, mikewa yayi ya tafi budewa tabiyo bayansa tana labewa a baya, yasa key ya bude kofar parlourn, yana budewa yafara sosa kai yana murmushi, matsawa gefe yayi, Abba da Maama ne suka shigo Jalila na ganinsu tayi tsalle taje ta rungume Maama.

"Maama har na fidda ran zakizo wallahi"

Maama tace "to ki bamu gurin zama mana, har kinfara complain"

Gurin zama ta basu tanata murna, Jalila tace "Abba ina wuni"

Abba yace "lafiya kalau Alhamdilillah"

Jalal yace "Abba ina wuninku?"

Maama tace "lafiya kalau Jalal ya gidan?"

"lafiya kalau Abba"

Jalila tace "Abba shine bakuzo da rana ba, seda dare yayi"

Maama tace "yanzunma Allah ne yayi zamuzo, mun fita gaisuwa gidan abokinsa nace masa ya tsaya mu biyo mu ganki"

Nan suka dinga hira, Jalila tace bari ina kawomu ku Abinci.

Abba yace "ki barshi Baby, yanzu zamu tafi"

Jalila tace "haba Abba, ai ba Abinci me nauyi bane, inada cake a fridge"

Maama tace "Ahh in baya ci ni dakko min nayi missing girke girkenki"

Jalila ta tafi kitchen, ta shiryo cake da lemo a tray zata dakko taga Jalal a bakin kofa yana mata dariya.

Kallonsa tayi tace "dariyar me ka keyi ne?"

Ya karaso inda take yace "juya"
Ba musu ta juya, yasa hannu ya ja zip din rigarta ya karasa rufewa, zare ido tayi tace

"kai wai a bude yake"

Jalal yace "eh ba a rufe yake gaba daya ba"

"na shiga uku, kuma sun gani?"

Dariya ya fara yimata Kamar ze fadi, gaba daya tarasa me yake mata dadi, ta harari Jalal.

Jalal yace "ki kai musu Mana dare yanayi fa"

Ta kwabe fuska kamar zatayi kuka tace
"ni gaskiya bazan fita ba kunyya nake ji"

"kunyar wa kike ji?"

Jalila tace "nikam inajin kunya wallahi"


Jalal yace "karki damu basu gani ba fa, nika dai nagani, dauki muje"

Ta dakko tray din ya biyo bayanta.

Maama taja Jalila bedroom

"Jalila ina datan babu wata matsala, kuna zaune lafiya?"

Jalila tace "babu matsalan komai Maaama, lafiya kalau muke zaune"

"dama an gaya miki, zaku zauna lafiya komai ze wuce, Ya shaye2 kuwa yanayi har yanzu kokuwa?"

Jalila tace "A'a Maama, baya shaye2 yanzu ya dena"

"ki ga yamin gaskiya Jalila, karki kare shi"

"Maama da gaske nake, baya shan komai yanzu"

Maama tace "Alhamdilillah, ki cigaba da hakuri dai, kinsan ita rayuwar Aure gaba dayanta hakuri ce, sannan ki toshe kunnenki akan abunda mahaifiyarsa zatayi miki koma take miki, ni kaina akan Auren nan bakiga bacin ran da mukayi da ita ba, hatta harkar business da muke yanzu ta yanke ta a tskanin mu"

Jalila tace "Ke Maama meye naki a ciki, da zata yimiki haka? Ranar daza'a akawoni ma bakiga yadda ta dinga muzanta Auren ba, shiyasa a tsorace nake da Auren nan"

"karki damu, ki kwantar da hankalinki, komai ze wuce, zataji kunya ne a gaba kaman yadda nima naji"

"Haba Maama wannan wace irin magana ce, meye wani jin kunya, dan Allah kidena wannan zancen, Yawwa Maama nifa shekaranjiya Su Naja sunzo gidan nan, Jalal yasa 'yan sanda sun kama su, na tambayeshi dalili yace babu ruwana narasa ya zanyi"

"rabu dasu Jalila, yaya mairo ta kirani a waya ta zageni tsaf, aina dawo daga rakiyar su, tana' yar uwata amma tana min zagon kasa da hassada a rayuwa ta, dana zauna nayi tunani dukkan shawarwarin data dinga bani a baya, tasa nake aikata wasu abubuwan turin jeka ka mutu takemin, Jalila nayi dana sanin abunda nayi miki keda mahaifiyarki tsawon shekaru, dan Allah ki yafemin"

Jalila tace "Maama dan Allah ki dena wannan maganar, komai ya riga ya wuce fa"

Suka cigaba da hira, Jalal yazo ya samesu yace

"Maama, Abba yace ki fito ku tafi dare yayi"

Har bakin mota suka rakasu, sukayi musu sallama sannan suka dawo cikin gida.

Koda suka koma Jalila ta duba kayan da su Maama suka kawo mata, fruits ne da kayan chocolate, ta zuzzuba a fridge.
Jalal yace

"My wife zomuje muyi Adhkar mana, zan kwanta"

Hararsa tayi tace "tab bazanzo ba, sedai karka yi" ta gudu dakinta, murmushi kawai yayi ya girgiza kai.




Ilham fa tayi rama sosai tayi duhh saboda bacin rai, Ummanta tace zatayi wani abu akan lamarin Auren an amma taji shiru, babu alamar samun wata baraka a Auren, ba wanda yaji kansu, dama bata ta Mummy, Mummy se aukin masifar, Amma babu wani yunkurin daukar Action da tayi, gashi wasa2 soyayya da kishin Jalal na neman ya kwantar da ita rashin lafiya, ba shiri ta shirya ta tafi gida gurin ummanta, koda taje gidan bata nan, dan haka tanemi guri ta zauna tana jiran dawowarta.

Tayi kusan awa guda sannan Umman tata ta dawo, tana dawowa ta tarar da Ilham din a kwance kaman gawa, a dan tsorace tace

"ke Ilham lafiya kuwa na ganki a kwance?"

Ilham ta dan yatsina fuska ta tashi zaune tace

"To umma ba dole ki ganni a kwance ba, Wata nawa da yun Auren Jalal amma har yanzu banga matakin da kika dauka ba, kamar ma baki damu daki dau fansar ba, kuma ni wallahi Umma nagane son gaske nake wa Jalal wallahi, ko bacci bana iyawa"

Umman tace
"tabdijan ashe baki da hankali, sena makeki keda son gaskiyar, kin san irin fadi tashin da nake kuwa? Har kike fadan kinfara masa son gaskiya? Kinsan me fadawa soyayya da Jalal da kikayi yake nufi? Rushewar burinmu na daukar fansa, da farko munyi sake yafada soyayya har yayi Aure, kekuma kina kokarin rusa komai da kanki, ai idan har son Gaskiya kikewa Jalal hakan yana nufin bazakiyi abunda ya dace in rama abunda uwarsa taimin ba"

Ilham tace "Amma Umma ban san ya'akayi nafara son Jalal haka ba, wallahi ina sonshi, soyayyarsa bazata hana in cika miki naki burin ba amma.......

Cikin tsawa ta katseta
"rufemin baki wawiya kawai, tun yaushe nake jiran ganin kokarin da zakiyi hakan ya tabatta, amma ba wani katabus da kikayu, sakacinki yasa har yayi Aure, na tattara abunda nake dashi na bawa malamai amun aiki akansa daga shi har matar tasa, ba ruwana ni daukar fansa ne a gabana"

"Amma umma duk abunda kikayi masa be isaba? Naga ma bashi yayi miki ba fa, fadanku keda Mummy ne meye nasa a ciki? Wallahi bazan iya dena son Jalal ba, bansan ya'akayi nafara yi masa wannan son ba, nikam zan dau matakin karshe da zanbi in mallaki Jalal"

"Aikuwa abunda baze taba faruwa ba kenan, indai bazaki auri Jalal dan burina ya cika bane to wallahi babu ke ba aurensa, dan na bada damar in haukatarwa ce ta kama, a haukata shi, shaye2 ya ninka na da har se ya haukace inga yadda khadija zatayi"

Ilham tayi murmushi tace "Ayya umma kin riga kin makara wallahi, yadda kikace bazan samu Jalal ba indai ba burinki ne ze cika ba, kema ina miki Albishir da cewa indai yana tareda wannan mayyar yarinyar, babu me iya cutar dashi, tunda akayi Auren nake kasa kunne amma babu wanda yaji kansu, na ziga Mummy har na gaji amma babu wani kwakwkwaran mataki data dauka, Umma wallahi na gaji sannan na karaya, mu zubar da makamanmu tun........

"Ke rufemin baki, ko in tattakaki, bana yafiya, ko zan yafe komai banda cin Amanar da khadija tayi min, in kin gaji ki kyaleni ni zan karasa aikina da kaina"

Ilham tace "kiyi hakuri Umma, zan cigaba da tayaki Allah ya cika mana burinmu, Sannan zanyi kokarin na cire shi a raina, inyi tunanin yadda burinki ze cika"

Saudat ta rungume Ilham tace "Yawwa yar halak, haka nake son ji"

Ilham kam goge hawaye tayi dan tasan babu ta inda zata dena son Jalal.







Yaya mairo sam hankalinta yaki kwanciya, tayi zarya station harta gaji amma anki bata Sa'adah, ita kuma Sa'adah taki fadar inda Hannah take, wanke kafa tayi ta tafi gidan su Jalal.



Bayan taje sun gaisa da Mummy, yaya mairo tace "Dan Allah zuwa nayi in nemi Alfarma, kisa baki danki yasa a sakar min yarinya ya, daga zuwa gidansa yasa an kamata, wai seta fito da wata, kuma tace bata san inda take ba, amma yayi mirsisi yaki sawa a saketa, naso inje gidan nasa da kaina amma ina tsoron karnima a kamani "

Mummy tace

"to ni mekike so inyi? Ina yarinyar ku yake Aure kije kisa ta saka shi a saketa mana, tunda yana jin maganar ta fiye dani"

Kuka Yaya mairo ta saka "wallahi ni bani da wata alaka da wannan yarinyar, dan Allah kisa a sakarmin ita ko bacci bana iyawa wallahi"

Tausayi Yaya mairo tabata dan haka A dan wulakance Mummy ta dauki wayarta ta kira Jalal

Seda ta kira sau kusan uku sannan ya daga, daya daga ma shiru yayi bece komai ba

Mummy tace "Jalal kana jina?"

"ina jinki mana, meye faru?"

Girgiza masa kai Jalila tayi muryarta kasa2 tace "greet her, Ka gaisheta mana"

Kamar wanda akayiwa dole yace "barka da yamma"
Kasa magana Mummy tayi, anya kuwa Jalal ne?

Mummy tace "Jalal ne?"

"wai baki san wa kika kira bane?"

"A'a ina son tabattarwa ne, nace yarinyar daka sa aka kama, 'yar uwar Jawwad ga mamanta anan tana Kuka, ina neman Alfarma dan Allah a saki yarinyar nan"

"bani da wani abu dazan miki alfarmarsa, ita kuma ki gaya mata hawaye yanzu ta fara, seta zubar da hawaye kwatankwacin wanda tasa Matata ta zubar saboda abunda suka dinga yi mata itada yaranta, koma yafi hakan,' yarta kuma baza' a sake ta ba setayi abunda nace, Hope i make myself clear"

Daskarewa Mummy tayi a zaune, Jalal kuma ya kashe wayarsa,

Jalila kaman zatayi kuka tace "Jalal abun nan dakake yi, jamin bakin jini kake da tsana a gurin 'yan uwanka da sauran mutane, kuma be kamata ka kasa yiwa Mummy Alfarma ba dan Allah komai ya wuce mana"

"inkowa ya tsaneki ni ina sonki ai, sannan komai baze wuce ba Jalila, Mummy ce silar duk wata mummunar rayuwa danayi, muka rayu cikin damuwa da bakin ciki saboda son zuciyarta, Jalila ban taba tunanin haske ze kuma shigowa ratuwata ba se bayan da kika jajirce a kaina, ko iya kulawar nan da kike bani nasan nasamu sassaucin rayuwa dana fidda ran samu, ki zauna kiyi hira dani, ki bani Abinci, ki saurari damuwa ta, idan raina ya baci ki rarrasheni, wani lokacin kina bani kulawa kaman da da uwa, tun bayan lalacewa ta na rasa wannan kulawar a gurin mahaifiyata da al'umma, wace Alfarma zata nema a gurina inyi mata? "

Kwalla ta taru a idonsa, da alama baya son tuna abubuwan da suka faru, ta kai hannu ta shafa sajensa tace

"Jalal, kowane dan adam kaddararsa a rubuce take kafin a haifeshi, dama can Allah ya kaddara you must go through that situation, koda Mummy ko babu sekayi wannan rayuwar, idan kayi hakuri ka bata matsayinta na uwa, se Allah ya yafe maka kaima, please Jalal forgive your Mum "

" ki kyaleni da maganar Mummyn nan senayi tunani"

Kara marairaicewa tayi tace "please Jalal"

Dan hararta yayi yace "Jalal ko?"

Murmushi tayi tace "Yaya Jalal"

"niba na son wani Yaya Jalal gaskiya, i calls you with different love names, please dukda bani kike so ba, ki dan dinga kirana da suna me dadi nima inji dadi"

Shiruu tayi ba tace komai ba, kasancewar a kwance yake akan cinyarta yasa ya juyo fuskarta tana kallonsa, dan motsa baki tayi amma ta yi shiru

Jalal Yace "Nasan bani kikeso ba, akwai wanda kike so banina ba, kina tausayina ne kawai, Amma please ki gayamin abunda zanji dadi"

Hannu tasa ta Dan shafa sumar kansa tace

"idan nace ZAUJEE yayi?"

Lumshe ido yayi tareda yin murmushi ya maimaita "ZAUJEE, you mean your husband?"

Jinjina masa kai tayi alamar Eh

Jinjina kai yayi yai murmushi yace "I like the Name kwailata"

Ture kansa tayi tace "dagani tunda kacemin kwaila"

Dariya yayi yace "ba zan tashi ba din ai keda cinyar duk nawane, ki shirya nan da next week Insha Allah Daddy ze dawo zamu je gida"









Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣6️⃣109

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



Happy marriage lyf to you sister Amina, may yours be among the best.



_MY FIRST NOVEL _



Mmurmushi Jalila tayi tace

"Masha Allah naji dadi gaskiya, dama bana zuwa ko'ina daga makaranta se gida, gashi an gayyaceni biki 'yar class dinmu bansaniba ko zaka barni inje?"

Dan hade rai yayi yai mata shiru,

Tace "Kace wani abu mana"

"gaskiya bazaki ba" yaba ta amsa

A shagwabe tace "meyasa?"

Jalal yace

"har yanzu baki kama da me Aure ba, kawai kifita wani ya biyoki no gaskiya ki hakura"

Kara marairacewa tayi tace

"please, Allah tunda nazo gidan nan school kawai nake zuwa, dan Allah ka barni inje"

Makale kafada yayi "yace ni dai A'a"

Ya kalli cikin idonta yace

"Allah me yadda yaso, Baby da dane nace karki fita ko kallona bazakiyi ba, ko baki niyya ba sekin fita dan ki ban haushi ko?"

Shiru tayi ba tace komai ba

Jalal yace

"naji zakije, amma ni zan rakaki kiyi minti goma mu dawo, dan bazaki dade ba, kar inje wani ya kalleki koma wani ya biyoki yace yana so, tunda har yanzu baki gama amsa sunan matar Aure ba"

Dan kallonsa tayi tace

"saboda me? A gaban mutane fa aka daura min Aure"

"eh nasani mana an daura miki Aure, har kikace ba kya son mijin da'aka baki, Amma ai bakiyi daya karatun ba daze maida ke matar Aure, ina da dauriya ko Jalila? Akwai dalilina dayasa na kyaleki kike cin karenki ba babbaka, ina jiran time ne"

Yai maganar yana kashe mata ido daya, sarai Jalila ta gane meyake nufi Amma ta maze tace

"karatu kuma? Wane irin karatu ne kuma haka?"

Jalal yace

"Au baki gane karatun da nake nufi ba?"

Mikewa yayi zaune yace

"bari in fara karanta miki kozaki gane"

Ai zumbur ta mike tsaye ta fice daga dakin, Ba karamin dariya Jalal yayi ba yana son ya zolayeta a irin haka yaga yadda fuskarta ke bayyanar da tsoro"

A zaman su Jalila ta gama fuskantar waye Jalal, mutum ne me matukar son a damu da shi, kulawa take bashi ba ta musamman dan kamar karamin yaro haka yake wani lokacin, ko Abinci ta kawo masa indai bata zauna ta bashi ba, ko ta zauna yana ci suna hira ba baze ci Abincin ba, sannan cikin hikima take canza masa wasu munanan dabi'un nasa zuwa kyawawa, ta tsaya tsayin daka akan kula da ibadar sa da kuma Adduo'i, kulawar da yarasa ce a baya ta taimaka gurin kara dulmiyashi harkar shaye2, Mummy harkar kasuwancinta da son zuciya tasaka a gaba, yayinda Daddy ba mazauni bane, Jawwad kuma ga makaranta ga sauran hidimominsa dukda ya taka mahimmiyar rawa a gurin Jalal, ga kyama da al'umma suke nuna masa saboda yanayi na shaye2 da sauran dabi'unsa, shiyasa abun yayi masa yawa, babu me jansa a jiki yaji matsalolinsa kome yake damun shi, wata shakuwa ce ta musamman ke kara shiga tsakaninsu.

Bangaren Jalal ma babu Abunda ze cewa Allah se godiya, dan ya fidda ran yin kyakywar rayuwa kaman kowa, Amma ba zato ba tsammani dawowar Jalila karo na biyu a cikin Rayuwarsa tazo masa da Haske da tausayawa, a cikin rayuwar Auren nan nasu, dukda kasancewar a baya basa jituwa, Amma ta ajiye wannan a gefe tana ta iya kokarinta a kansa, tana masa biyayya dai2 iyawarta, duk wanda yasan irin rayuwar takun sakar da sukayi a baya, babu me cewa zata iyayiwa Jalal biyayya haka, musamman wanda yasan halinta a bangaren tsiwa da rashin daukar raini, tana zama tayi hira da shi, tai masa nasiha, idan abu ya dameshi ta rarrasheshi hakan ya mantar da Jalal duk wata mummunar rayuwar da yayi a baya.

Tun Yaya mairo tana sintirin zuwa gidansu Jalal akan maganar sa'adah harta gaji ta hakura saboda korar wulakancin da Mummy tayi mata a cewarta

"ta gaji da zaryar da take mata a gida suje can su daidaita"

Ba yadda ta iya haka ta tafi gidan Maama kozata sa baki a sakar mata sa'adah, dan yanzu ko zuwa tayi police station ba'a bari ta ganta, ta kwashe duk yadda akayi ta fadawa Maama,
Maama tace

"to ni Yaya mairo ya kike so inyi?"

Yaya mairo tace

"Dan Allah zainab kisa baki, yarinyar nan Jalila ta gaya masa yasa a sakarmin 'ya ta dan Allah"

Maama tace

"Yaya mairo idan mukayi haka ai bamu da kunya kenan, ko kin manta irin cin zarafin da kikasa muka hadu muka dingayi mata? Se yanzu zamu nemi Alfarma a gurinta?"

Yaya mairo tace

"Dan Allah zainab ni dai ki roketa a sakarmin sa'adah, wallahi yaron nan da yake ba dan mutunci bane, mahaifiyarsa tana rokonsa a sakarmin sa'adah se cewa yayi, se nayi hawaye fiye da wanda matarsa tayi"

Maama tace

"gaskiya Yaya bazan iya tunkarar Jalila da wannan maganar ba"

Abba ne ya shigo gidan ya tarar da yaya mairo a parlour suna hira, Yaya mairo na gaisheshi be amsa ba yace

"zainab ban gaya miki bana bukatar sake ganin yayarki a gidana ba? Ban hanaku zumunci ba, amma ku hadu a wani gurin, dan bazata dinga zuwa tana rarrabamin kan iyalai ba"

Abba ya dubi Yaya mairo yace

"dan Allah karki kara zuwarmin gida, in bahaka ba zan dau mummunana mataki akanki, ki tashi ki tafi"

Yaya mairo tace "zainab kina kallo mijinki na cimin mutunci?"

Maama tace

"ba cimiki mutunci yake ba, maganar gaskiya ne ai, tunda yace ki bar masa gida kawai ki tafi"

Haka Yaya mairo ta fito tana rusa kuka, ta koma gida ta rasa abunda yake mata dadi, ga Naja ma kwanan ta uku bata gida, ta kirata a waya tace mata

"karta kara kiranta tana cikin koshin lafiya"

Sa'adah kam da taji uwar bari tuni ta fadi inda za'a samu Hannah, akayi nasara kuwa 'yan sanda sukaje itama suka kamota amma ba' a saki sa'adah ba ma.




Jalila ta gama shirinta tsaf na zuwa gurin biki, ta dakko Jakarta ta fito, tana

Please Login or Register in order to submit comment