Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaman yai masifa danshi baya son adinga dangantashi da Ilham wai ya aureta, se ya tuno abunda Jalila tagaya masa akan baya yiwa mahaifinsa biyayya, haka yayi shiru daddy yaitai masa nasiha, Jalal yana gama cin Abincin sa ya kalli daddy "daddy kaga naji nadena, yanzu inason in dan fita ne"
Daddy yace "ba dai kasaon fadan danake maka Seka dawo Allah ya kiyaye" "Ameen" ya tashi yabarwa daddy kwanukan Abincin a palour, Ilham tanata fargaba da Jalal yafito amma taga still be kulata ba ya fice daga palour, dakinta ta koma ta dauki wayarta takira yaseera, bugu biyu ta dauka
"Hello yaseera kinajina?"
"ina jinki Ilham lafiya naji muryarki a haka"
"Yaseera ina cikin matsala" "matsalar me kuma?"
Nana Ilham ta gayamata dukkan abunda yafaru jiya akan ance za'ayi maganr aurensu da Jalal.
"tabdijan lallai Ilham akwai katuwar matsala, gaskiya yayan nannaki akwai taurin kai, dole musake shiri amma kunyi waya da ummane?"
"A'a yaseera amma zanje anjima, wallahi banaso ingaya mata ne hankalinta ya tashi banaso ta karaya akan bazan iya cika mata burinta ba, gani nake bazam gayamata ba, gara mubari ranar Sunday muje gurin malam"
"to shikenan yadda kika gani, amma abun da damuwa wallahi, ace duk wani kissa taki tasiri akansa sekace ba namiji ba, anya ba mata maza bane ba
Ace mutum zuciya kaman karfe"
"Hmm kema dai kyafada yaseera, bari ranar ki shirya da wuri muje"
"to shikenan Allah ya kaimu" "Ameen yaseera nagode sosai".
Y'an kwanakin nan, Jalila ta dan sakewa Sulaiman suna gaisawa saboda tasamu damar daze temakamata, amma sam taki yadda yazo gidansu ko susake haduwa, dama ba koyaushe yake zama a kano ba se lokaci2 yake zuwa, aikinsa yafi a Lagos, anan yake gayamata shi kakakin rundanar yansanda ne na jihar Lagos, amma iyalalinsa suna kano, suna hira sosai da Jalila yana bata labarin nasarori da hatsarin ayyukansu, amma daya dakko batun daya shafi soyayya seta kashe wayarta, hakama Alhaji Kabiru Jalila ta sakar masa sosai gani yake kaman sonshi takeyi, a nan takara tabattar da Saleema yarsace ta cikinsa itada faruk.
Yanzuma waya suke da Alhaji Kabiru
"sweet heart wai yaushe zaki farantawa masoyin kine, kinki yadda mu hadu"
"tab waikai bakajin kunyane yarka fa daka nunamin hotonta zata girmeni kawai sesuga ka auri yar yarinya?"
"to meye a ciki gidanki daban zan ware miki, ita Saleema tanacan karatunta tanagama karatu zan aurar da ita, Faruk yana ABU, sukenan yarannawa fa, kuma basuda damuwa da aurena, please my sweet kibari mu hadu mana, yakamata kinunamin soyayya ina Sonki fa" shi sam besan Jalila tasan Saleema department dinsu dayaba, Jalila aranta tace me mutumin nan yake nufine? Amma ta maze tace
"yaushe zakazo ku gaisa da Abba na?"
"Ai wannan ba wani abun damuwa bane, kibari mugama fahimtar juna mana kinki bari inzo gidanku balle mudan dinga fita chilling din nan, bakya wani nunamin soyayya"
"Banda wannan danake maka wacce kakeso kuma?"
"yakamata ace kinkawomin ziyara gidana mu gaisa mana" "haka kurum matarka ta zaneni" "wayace miki nan zakije, gidana danake ganin special guest dina zakizo" murmushi Jalila tayi "hmmm special guest, ashe nima special ce" "sosai makuwa please my sweet yaushe zakizo?"
"karka damu kabari in mungama exams zanzo, ba dai zuwa kawai zanyi shize tabattar maka da inasonkaba karka damu"
"Kai amma naji dadi sweet, Allah ya kaimu kugama"
"Ameen se anjima" koda sukayi sallama Jalila ta kalli wayar ta takunna recording gaba daya wayar datakeyi tana recording dinta, tana saving a Gmail dinta "Azzalumi kawai, shiyasa abunda kakeyine yasa yarka take can take watsewa a makaranta bakasaniba Jaki kawai, zakuga abunda zan muku kaida yartaka sena kunyataka agabanta in nuna mata nafita iya rashin mutunci".
Sosai Zahra ke gudun cigaba da mu'amala da Jalila sedai ta waya saboda kashedin dasu sameera sukayimata, gashi suncigaba da uzzuramata akan lallai ta amince da bukatar sameera, tarasa inda zatasa kanta abun ya isheta, dan haka ta samu Jalila tagayamata halin da take ciki, "Zahra yazama dole ki amince da batun su Sameera"
"haba Jalila so kike rayuwata ta tarwatse ne yazakice haka?"
"basonake rayuwarki ta tarwatse bane, taimakonki zanyi"
"to tayaya Jalila, kinsani nasani dukkansu ba mutanen arziki bane da sharri suke nufina"
"Nasani ai tarko zamuyi musu nasan yadda zanyi dasu" Saleema ce tazo har inda su Jalila ke zaune ta kalli zahra "wato zahra bakiji kashedin da Sameera ta miki bako? Har yanzu kina biyewa wannan yarinyar ko"
"Ke wai dakata, suwaye dinta ku, ana dolene ko angaya muku kowa sakaraine dabba irinku" "Ke shiga hankalinki, bana son shishshigi muna daf dasawa amana maganinki yadda ko hanya muka hada sekin kauce"
"Allah ko? Dama waze hada hanya da kazamai jakuna marasa tsoron Allah, aini base kunsa anyi maganina ba, nizanyi maganinku daga ke har kawartaki ba sameera ba ko langa ce kukiyayeni musamman ke" ta nuna Saleema,
"Asararu ko kunya bakwaji kaf school din nan kowa yasan mekukeyi" kafin Saleema tayi magana Jalila ta dau jakarta tayi gaba tabarsu Zahra a gurin.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah su Jalila suka fara exams din first semester, kowa yana abunda yaga ze fisheshi, wasu sun dukufa karatu, wasu ko sharholiyarsu kawai sukeyi, itakam Jalila ta maida kaine akan lissafin yadda zata bullowa al'amuran ta dasuka dameta,
Yau karfe tara zasu shiga exams, ita Nana sun gama tasu Jarrabawar dan hutu ma sukeyi, gashi Manu direba baya nan Maama ta aikeshi, da karambani Jalila tasaka Manu yakoya mata mota, da mukulli na nan da dakanta zata tafi yau, dan haka ta yanke shawarar tafiya ta hau napep,
Tana fitowa daga gidataga Daddy da dansa Jalal a jikin motar Jalal, durkusawa Jalila tayi "daddy ina kwana?" "Lafiya kalau Jalila makaranta za'atafi ina direban naku?"
"daddy baya nan, napep zanje in hau karfe tara zamu shiga exams"
"kai Masha Allah, Allah yabada sa'a, takwarar Jalal, Allah ya temaka" Jalal ya tsani yaji ance takwarar nan tasa, yawani hade rai, "Ameen daddy nagode sosai Allah yasaka da alkhairi bari in tafi kar in makara" "A'a tsaya, dama Jalal fita zeyi, Jalal kuje seka ajiyeta a makarantar tunda duk hanyace" kallon daddy yayi, ya kalli Jalila ya dauke kansa



I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣0️⃣/63_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]



_MY FIRST NOVEL _



Ita kanta Jalila setaji kaman tace A'a amma taji nauyin yin hakan, daddy yakuma cewa "Jalal maza kunna motar ku tafi karta makara" Jalal kaman yace bazashi ba amma yasan yana fadan hakan tasamu abunyi, bece komai ba ya bude motar ya kunna, Jalila ta tafi ta bude gaba ta shiga, "yawwa Allah yayi muku albarka sekun dawo" Jalila ce kawai tace Ameen, Jalal ya kunna motar yajata da gudun tsiya, yadda yake gudu yasa Jalila ta kalleshi "ni gaskiya in wannan ganganci za'ayi da rayuwata ka saukeni, akanme inkasaba kasada da rayuwarka to badaniba" banza yamata yacigaba da tukinsa, yadda yake ratsa tsakanin manyan motoci yasata runtse ido tana ambaton Allah, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, "dan Allah ka tafi a hankali koka tsaya in sauka" jitayi an tsaya hakan yasata bude idonta, gani tayi yayi parking, yasa hannu ya yana dakko taba yana kokarin kunnawa, "kutmelesi meye haka ne?" banza yayi mata ya kunna tabarsa, sakin hayakin yayi fuuu a cikin motar, juyawa tayi zata bude kofar motar amma taji a kulle gam, yasa lock ta kalli agogon hannunta ta makara sosai ana daf da shiga exams,
"wai meye haka dan Allah nika budeni in tafi zan makara, ga warin hayaki ya isheni" Shiru yakumayi ya kwanta sosai a jikin kujerar yana busa hayakinsa, ji tayi kaman ta wanka masa mari, yanajinta amma yayi banza da ita kamar wani itace, dafe kanta tayi, wayarsa tafara vibration ya dauka yaduba message din Hanna ne danhaka ya ajiye wayar tareda fadin "wasu matan are just useless" Jalila ta dago ta kalleshi, "ai Useless din ba iya mata bane hada maza, dan gara mata da wasu mazan dabasa jin magana" wani dan guntun murmushi yayi, wanda shikadai yasan yayi shi, gani tayi ya shanye sigari kusan uku yakuma kunna wata, hannu tasa ta fizgeta ta jefa waje "wallahi baka isaba, akanme ina zaune zaka dinga shan taba ka cikani da hayaki salon inje aji a dauka ninasha tabar, ka budeni in tafi in yaso kaima kazama tabar, batareda ya kalleta ba yace
" warin taba ai kin dade kinayinsa, ba iya taba ba harda na giyama kinayi, kece baki saniba amma nakusa dake sun san hakan" kallonsa tayi alamar bata fahimta ba
"ya za'ayi nida bana shaye2 indinga warin giya, Allah ya kiyaye" "bakiyi addu'ar a inda ya daceba, dan kinriga kin makara, kuma ba lallai sekina sha zakidinga warinsu ba" hannunta ya kamo, ya nunamata "a jininki abun yake, akwai jinin yan giya a jikinki dan haka sekidena cika baki" ita Jalila sam batagane inda maganganunsa suka dosa ba, wayartace taketa ringing tasa hannu ta dakkota Alhaji Kabiru ne akan screen din wayarta, screen din Jalal ya tsurawa ido yai shiru kaman me nazari, ya kalleta ya kalli wayar, kashe wayar tayi ta mayar cikin jakarta, kallon tuhuma yayi mata na wani dan lokaci, sannan ya dauke kansa, "hmm Jawwad za aci amana, hakan yafi ai, dan baki dace dashiba gara ya auri mutuniyar kirki, dan duk jarabarki bazaki auri dan uwana ba, Jawwad da salihar mace ya dace ba irinkiba" kallonsa tayi sannaan tace "nice ma kai, aigarani da kai, kaima kasan hakan kuma duk bakin cikinka sedai kayi, dan nafi karfin ace za'a kyamaceni a matsayin mata, dan nasan nafi wannan doluwar kanwartaka"
"Hmmm meye kuma nasakota a wannaan zancen? "
"kaika sani, nikawai ka budemin in fita" banza yayi mata yacigaba abunda yake, wasa2 kusan mintunansu talatin a tsaye Jalal yaki tafiya, hannu takuma sawa zata fizge tabar bakinsa cikin zafin nama ya hada da hannunta ya rike, ya juyo yana kallonta, wani mugun kwarjini yayi mata ta kasa magana ta sunkuyar da kanta kasa, "karki kuskura, bar ganin na kyaleki dazu" sakar mata hannu yayi, yacigaba da abunda yake, karfe tara hada rabi, amma Jalal yaki kaita makaranta, tarasa mezatayi kawai tafara kuka, seda Jalal yaga dama sannan yaja motar yacigaba da tafiya, wannan karon kuma a hankali yake tafiya kaman bayaso, hannu yasa ya kunna radio motar inda karatun Al qur'ani yake tashi, Jalila aranta tace "Tab dama yanajin karatun qur'ani" bata gama tunanin ba taji Jalal yanabin karatun a hankali, juyowa tayi tana kallonsa, danta tabattar anya kuwa shine yakeyi, sosai yakebin karatun cikin suratul Ibrahim, dan tabe baki tayi tana jinjina lamarin dama Jalal ya iya karatu haka, amma koda wasa bata tunanin ko bismillah ta tabajin yayi, se masifa da wake2, tana cikin tunanin taji yayi parking, "inkin gama kallon nawa seki fita"
" Baka da abunda zan tsaya ina kallo, ko Meye amfanin zuwanama, tunda dai na makara nasan ba lallai inyi jarrabawar ba, kaida Allah in abunda kayimin dai2 ne, kodayake baka san darajar jarabbawa ba shiyasa kamin haka kuma Insha Allah se" "Ke!!!!" ya dakamata tsawar data tilasta mata yin shiru
"wallahi duk randa bakinki yai kuskuren yimin muguwar Addu'a akanki zata kare, gobe in ankuma cewa kibi namiji mara daraja irina sekikuma biyoni, fitarmin daga mota, inbahakaba na kunna motar nan senaje gida zan tsaya, kyasan yadda zakiyi" bude motar tayi tanata kunkuni gashi ta hade rai sosai, ta fice tabar motar a bude tai tafiyarta, ankai ruwa rana sosai kafin abar Jalila tashiga hall din exams saboda ta makara, Jalila ji take kaman tana komawa gida takama Jalal ta shakeshi seya suma, haka tai exams din ta fito cike da takaici,
Tasamu guri ta zauna a karkashin wata bishiya, ta zauna babu dadewa Zahra ma tazo gurin "Jalila ya akayi kika makara haka yau?" dan tsaki Jalila tayi "kedai bari, wani ne yajamin wallahi, kuma ze gauraya dani" "hmm Jalila kenan me jama'a, Amma ke sir Hafiz fa yace ince miki kije, nifa nakasa gane meke shirin faruwa tsakanin ku" Jalila ta kalleta ta dauke "ki goge zuciyarki tsaf kidena bari tana kawomiki wani tunani" zahrah ta jinjina kai "ke ba wannan ba Jalila, ina mafita anawa lamarin? Ina cikin damuwa wallahi"
"Nasani Zahrah, amma abubuwan dasuke kaina dayawa ga wannan jarrabawar ga sauran abubuwa"
"to nidai kitemaka Jalila, karsuyi nasara akaina"
"Ai yazama dole in temaka miki, sabida indai nayi nasara kikayi yadda nace to nikeda riba, zangaya miki yadda zamuyi, amma banason gaddama da taurin kai, duk abunda nace kiyi, bazan bari kiyi abunda zaki cutu ba"
"to shikenan inajinki" Jalila ta gyara zama "zaki Amince da bukatar su Sameera" zaro ido Zahra tayi "Amma meyasa?"
Nan Jalila ta tsarawa zahra yadda abun ze kasance, zahra ta yadda da abunda Jalila tagaya mata.
Zahra ta tashi ta dau wayarta zata tafi, Jalila ta dakatar da ita, ta dakko wayarta tasaka ta a tsakanin litattafan Zahrah daga sama, sannan ta kalli zahra" harkije ki dawo karki sake ki tabamin waya, jeki dawo ina nan ina jiranki"zahrah ta gyada kai ta tafi, inda tasan zata samu su Sameera, tai sa'a kuwa suna gurin, tana zuwa tasamu guri ta zauna a kujerar opposite din su Sameera ta kalli Sameera tace "Sameera gurinki nazo" Sameera tamata wani mugun kallo sannan tace "fatan kinzo ki sanar dani kin Amince da bukata tane?" "A'a zuwa nayi in rokeki alfarma dan Allah dan annabi kirabu dani kiyi hakuri wallahi iyayena zasu shiga damuwa insuka gane gurbatacciyar hanyar dana fada" Saleema ce ta katseta "Ke saurar bama son shirme , kekinfiso aita nanata magana ko? To bari kiji bata sauya zaniba, koki yadda kokarki yadda bazaki kubucemana ba sannan sekinso iyayenki zasu san abunda kikeyi, abunda kezaki amfana kudi fa zaki dinga samu" Sameera ta dagawa Saleema hannu alamar tayi shiru, ta kalli Zahra "idan baki amince da bukata ta ba, wallahi kartin yan daba zansaka suyi miki fyade" A razane Zahra ta kalli Sameera "yes and i mean it, fyade na wulakanci na tozartawa kuma duk garin nan babu wanda ya isa yayi wani abu, inada yan daban dabakowa ke iya hayarsu ba, sannan inada manyan dasuka tsaya min, babu wanda ze gane ninasaka akayi miki haka balle adau mataki, bakida gatan da za'a iya kwato miki hakkin ki, kinga tarwatsewar rayuwa tagama, karatu ya kare se zaman gida jiran ajali danko waje baki isa ki fitoba saboda gudun kyamar da mutane zasuyi miki" da kyar zahra ta hadiye mugun yawu "shikenan dan Allah kar abun ya kai haka na yadda, na amince amma bana son mutane su gane" Saleema ta kyalkyale da dariya, "ashe bari ba shegiya bace yarinya da wata garan gara wata" Murmushi Sameera tayi, "kin temaki kanki" zahra ta share hawayenta "A ina zamu hadu?" nan Sameera taimata kwatancen wani gida, zahra tace "zanzo Insha Allah, sannan kibani lambarki incase ko zan bata" ba tunanin komai Sameera tabawa Zahrah lambarta, sannan ta karbi ta Saleema ma" har zahra ta mike zata tafi ta dawo ta zauna tace "Amma dan Allah kujawa yar seat dina kunne, nayi2 tadena shiga harkata taki" Saleema tace "banni da ita zanyi maganinta" zahra ta jinjina kai ta wuce yayinda sukuma suka kyalkyale da dariya, zahra takoma inda tabar Jalila, tana zuwa tana niyyar labartawa Jalila abunda yafaru, Jalila tasa hannu ta zare wayarta, sannan ta kalli zahra "shikenan semunyi waya ina sauri zan koma gida" "Amma baki tsaya nagaya miki yadda mukayi dasu ba" "karki damu mu hade ta what's app" cikin mamaki Zahrah ta kalli Jalila "to amma meye amfanin.....
" Shhhhh semun hade "Jalila tayi gaba abunta.
Tana zuwa gida yaya Jawwad yana tsaye shida Abba, karasawa gurinsu tayi" Abba yana ganka a gida iyanzu? "yan makaranta ya jarrabwa" "Alhamdilillah Abba harka dawone?"
"A'a tafiya ce takamani, zanje Lagos" dan hade rai Jalila tayi "Abba da tafiya zakayi ba sallama" "to ai gashi munyi sallamar" Jawwad yace "Abba muje karka makara, wannan babyn taka bazata bari ka tafi ba"
"Nima zan biku Abba" Jawwad yace karatun fa? Naga kuna exams "
" Eh ai bakomai dan Allah ni zan biku" Jawwad yace "rigimammiya yanzufa kika dawo baki gajiba" "bangajiba Allah" Abba yai murmushi "taho mutafi shalelena, ai rakiya zakiyi min" da murnarta ta hau motar suka tafi raka Abba airport, suna tafe suna hira itakuma ta dakko wayarta tasaka earpiece tana kallon video, dazu wayarta data saka a agaban jakar zahra video ta saita ta kashe flash din wayar, duk wani magana dasukayi yayi recording, wanda ita kanta zahra bata Sani ba, aciki Jalila taji kwatancen gidan da akayiwa zahrah a dan bare, ita Jalila bata san ma inane dan bare a kanoba, hiding video din tayi a wani app ta ajiye wayar, suka raka Abba airport, seda Jawwad yabiya ya saimata ice-cream da tarkacen chocolate suna tafe suna hira har sukazo gida. Suna zuwa suka tarar da Maama a harabar gidan, kallon tuhuma takeyiwa Jalila da Jawwad "daga ina kuke?" Jawwad yace "dama Tafiyace takama Abba zeje Lagos kuma bakyanan shine muka rakashi airport" "in kayi salla kazo ina son ganinka" "to Maama insha Allah zanzo" Maama ta juya takoma cikin gida, Jawwad yajuya ya kulle mota, yaga Jalila a tsaye abayansa bata tafiba "ya dai?" "bangaji da ganinka bane" murmushi yayi mata "Babyna kenan, aini nakine zakita kallona sekin gaji" "bazan taba gajiya da kallonka ba, jekayi salla kazo kiran Maama" "to shikenan see u later" daga nan yafita ita kuma ta shige gida, a cikin gida bataga Nana a dakinsu ba, san haka tashiga tayi wanka tai salla. Tana ninke sallayar taji wayarta na ringing Alhaji Kabiru ne wani uban tsaki taja
Ta daga wayar suka gaisa, haka ta dake ta boye damuwarta suka sha hira kamar gaske, Alhaji Kabiru ya matsa matuka akan se Jalila taje gidansa, taita lallabashi tana bashi hakuri daga baya ta kashe wayarta, fiowa tayi palour domin taje kitchen tasamu Abinda zataci, gani tayi anyi bakuwa a palour da alama gurin Maama tazo, suka gaisa da Jalila tace "bari inje in kira miki ita inaga tana daki" Jalila ta tafi dakin Maama danyimata magana Jalila ta jiyo kukan Nana tana cewa "Wallahi Maama gara in mutu da in auri Nura, wallahi yaya mairo kozata kasheni bazan aureshi ba" "nima ban goyi bayan hakanba, bazaki Auri Nura ba, amma yazama dole Jawwad ya auri Naja, intaga Jawwad ya auri Naja zata hakura inyaso kesekice ba kya sonsa" "Maama saboda me shima yayan ze auri Naja yakamata ayi masa adalci abarshi ya zabi wadda yakeso" "ke rufamin baki, dole ya auri Naja saboda bazan bari ya auri wannan yarinyar ba, indai ina raye baze auri Jalila ba saboda bana kaunar uwatta itama bana sonta dana baze auri yar Arniyaba karuwa" Jalila ji tayi kaman ansoka mata mashi a zuciyarta, tura kofar dakin tayi kaman bataji komaiba tace "Maama kinada bakuwa" hade rai Maama tayi "to naji jeki ina magana da yata" juyawa Jalila tayi ta fice tafasa cin Abincin, tafasar da zuciyarta take tasa takasa komai, ga hawayen yaki zubowa balle taji sanyi aranta, a hankali taketa karanto addu'oi domin zuciyarta tayi sanyi, gani tayi inta cigaba da zama bacin raine ze dameta gara ta fita ta rage wasu abubuwan dan haka ta dau hijabinta tasaka ta dau nikab da Jakarta ta fito palour, Maama tana gaisawa da bakuwarta "Maama dan Allah zan dan fita bazan dade ba zanje siyo kayan cake" "sekin dawo" shine kawai abunda Maama tace mata, tana fitowa harabar gidan Manu ya taso "A'a uwadakina ina zuwa haka daga dawowarki yamma tayi sosai" "Manu key zakabani na mota zanfita" "Ahh ai yayi wuri kifara tuki da kanki bakigama kwarewa ba kinsan tuki a kano se kwararren direba" "karka damu ba nisa zanyiba" Manu direba yabata key din mota, ta fita sannu a hankali take tukin da tambaya hartaje unguwar danbare inda su Saleema suka kwatantawa zahra sukace acan zasu hadu, abakin layin tayi parking ta fito sanye da nikab ta shiga layin, layin shiru ba mutane sosai, har kofar gidan taje ta tsaya daga baya, tana nan tsaye sega wata mata tazo wucewa, Jalila ta tare matar suka gaisa sannan Jalila tace "baiwar Allah dan Allah tambaya nake?" "ina jinki Allah yasa nasani"
"Dan Allah ke yar anguwar nance" "meyasa kika tambayeni?" Jalila tace "kinga ba cutar dake zanba wasu yan tambayoyi kawai zanyi miki" matar tace "ina jinki"
"dan Allah waye me wancan gidan" Jalila ta nuno mata gidan "hmm wanna gidan da kike gani wai yan makaranta ne a ciki, kuma bawani yan makaranta taron yan iskane maza da mata bawanda basa zuwa gidan, ke kawaima gidan karuwai ne da yan shaye2 " "Amma kuke zaune dasu a anguwar ina hukuma" "wace hukuma aiko ankamasu se an sakosu saboda ita ainihin me gidan wata yarinya ce, tanada manya a sama ba wanda ya isa yayi mata komai samfirin yan mata samari da yan daba babu wanda babu, har wasu manyan mutanen ma suna zuwa nan"
"Nagode sosai yar uwa, da amsamin tambayoyina" matar tace "bakomai amma fa koda wasa karki sake kice nina gayamiki danba ruwana" "karki damu babu mejin wannan zancen". Daga nan Jalila tayi godiya ta nufo gida, anata kiraye kirayen sallar magariba, tana komawa gida ta nufi cikin gida
"wallahi Jawwad da raina bazaka auri yar arna ba, ko ka auri Naja kokasamu wata ka aura amma ba wannan yarinyar ba, Naana dai zanyi yadda zanyi bazata auri nuraba amma kai kam sedai kayi hakuri bazaka aureta ba wallahi"
"Maama dan girman Allah kiyi hakuri Jalila batayi miki laifin komai ba, wallahi Maama ina sonta dan Allah karki rabani da ita, ina sonta dan Allah wallahi bazan iya auren Naja ba"
"Au har ina fada kana fada Jawwad, nagama yanke hukunci, sedai ka mutu dan bana kaunarka da yarinyar nan baze yuwu jikokina su fito daga tsatson arna ba, wannan fitsararriyar yarinya mara tarbiyya to baka isaba ni na haifeka dan haka na isa da kai, bazaka aureta ba, tun kuna kanan akan uwatta ba irin wulakancin da ban fuskanta ba, ubanku yayi min shi Aliyun yayi min rashin mutunci akan uwatta dama shiba mutunci yacika ba, dan halinsa ta dakko, ga kakarku kowa ya hademin kai Allah ka dai yasan me tayi ta shiga ta fita ta rabani da dangin mahaifinku, suka tsaneni se yanzu kakuma jawomin jaraba baze yuwuba, zamanta a gidan nan ma ba yadda zanyi ne, amma bana kaunar ganinta kusada ku" sunkuyar da kai Jawwad yayi ya dafe kansa da karfi Jalila ta bude kofar palourn gaba daya suka juyo suna kallonta



Daga Alkalamin
Aysher cool 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
I don't want stickers or just thanks, comments nakeso, dan shike bani karfin gwiwa, ina Alfahari daku
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣1️⃣64_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah

Please Login or Register in order to submit comment