Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

seya soki, wani ze nuna a fuska yana kaunarki, Amma zuciyar sa babu wadda ya tsana kamar ke, sedai Jalila kiji tsoron Allah, yadda kika dauki aniyar sauya rayuwar Jalal karki sa ya kauce hanya, kar son da yake miki yasa kisa yaci gaba da fito na fito da mahaifiyarsa dan bata sonki, ki rike mijinki Jalila, Shi Aure idan ka samu wanda kake so ka iya tafiyar da shi yadda shari'a ta koyar, babu abunda ya kaishi dadi, shiyasa har gobe bazan manta Aliyuna ba"

"kai Ummi ko kunya ta ba kyaji?"
Ummi murmushi tayi tana girgiza kai,.
Jalila ta dan bata rai tace

"ummi Jalal tun kan ya tafi Lagos yace kar in kirashi har sati biyu wai bazata shiga ba, ashe abunda ya shiryamin kenan, dan Allah ki kiramin shi a waya, nasan ke ze daga naki Kiran"

Ummi tace

"A'a abunda yake so shi nake so, dan haka se kiyi hakuri se lokacin da yace, ai gara ya rama shima"

Jalila ta dan sunkuyar da kai tace "Ummi ina son ine nemi afuwar Jalal, tun kafin in san dawainiyar da yayi min dake, ina jin nauyinsa idan na tuna abunda na dinga yi masa a baya, dan ma wani abun baki sani ba"

Hira ce sosai Ummi da Jalila suka cigaba dayi, wani lokacin suyi kuka, wani lokacin suyi dariya, Ummi na ta kara yiwa Jalila nasiha, har gari ya waye yayi haske har kusan goma suna tare, aka fara shigowa duba Jalila, aka tarar Jalila ta ware tanata hirar ta da Ummi.

Warewa sukayi aka cika dakin suna ta hira da Ummi, Ummi se lallaba Su Hanan takeyi, Jawwad ji yake wani bangare na farincikin iyalansu sun dawo, koba komai Ummi ba abar yarwa bace, dan itace uwar rainonsu shida Jawwad, Amma shi kansa Jawwad ya sha mamakin abunda Jalal yayi.

Jalila tayi2 wayar Jalal ta shiga amma taki shiga, ta tura masa messages amma shima babu response, abun ya fara damun ta sosai, Harta E-mail dinsa ta tura masa sakkonni amma shiru.
Jalal kam yana sane yayi mata haka, in bahaka ba yasan halinta ta dinga tuhumar sa kenan, koma taita koke2 se ya dawo, wani lokacin ya kan bude system dinsa ya duba sakkonin Jalila,

"zaujee pick my calls please, i have a lot to say"

ire iren messages din nan dayawa a Gmail dinsa, murmushi yayi yace

"Baby na sarkin rigima, dama akwai ranar da zatazo kidinga nuna missing dina haka?"
Murmushi ya kara yi yace

"Yarinya se na rama tukuna, gara kema ki dana abunda nake ji"

Ya dauki wata wayar tasa daban ya kira Jawwad, yana kira Jawwad ya dauka, suka gaisa Jalal yace

"Jawwad ina matata ne? Fatan tana lafiya?"

"ban sani ba, ai kafini kusa da ita, ka wani kashe waya kana wahalar min da 'yar uwa"

Jalal yace

"ba ruwanka, kai waya dameka kai da matarka, kawai kuyi kallo, dan Allah Jawwad tana ina me take yi yanzu?"

"Wallahi tana cikin damuwa Jalal, tayi murnar ganin Ummi sosai, Sannan a gaban mutane take kuka tana a baka hakuri, har gurina tazo tana tambaya ta ko ina samunka a waya? Ba yadda na iya ka sanayi mata karya"

Hanan da take gaban Jawwad yana bata Abinci tace

"Jalal ka temaki sister na, ta horu fa, kullum se tayi zancen ka babu Adadi," Allah sarki Jalal dina, ko yaci Abinci? Ko yayi Adhkar dinsa? Da yana nan dai dai yanzu muke cin Abinci, Allah ya dawomin da shi in bashi hakuri" haduwar ta da Ummi be sa ta manta da kai ba, tana kewarka sosai fa"

Ajiyar zuciya yayi yace

"Allah sarki masoyiyyata wallahi nafi missing din ta, banyi haka dan ta shiga damuwa ba, wannan shine burina, Jalila ta hadu Ummi, bayan Ummi ta warke, nasan Jalila tana sona, Kaman yadda Hanan ke fada ne, tana da taurin kai, bata fiye yadda da abunda zuciyar ta tazo mata da shi ba, Hanan dan Allah ki cigaba da rarrashin ta, in dai na daga wayarta nasan kuka zata yi min, nikuma kukan ta yana tabamin zuciya, naji gobe in Allah ya kaimu zaku tafi garin su Ummi, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya "

Jawwad yace

" Ikon Allah, ji yadda ya wani kashe murya yana gayamin yayi missing din matar sa, kaman ba shine me cewa Mata matsalane, soyayya shirme ce, to yanzu kuma mene? "

Jalal yayi murmushi yace
"a bayan ma duk basaja nakeyi in gaya maka, da zaka tona zuciya ta seka tausayamin, nayi zaton cire soyayya abune me sauki daga zuciya, amma duk lokacin da nayi yunkurin cire son ta a raina, se naji kaman ina kara azabtar da zuciya ne, gashi a lokacin bana ganin komai se kiyayya ta a idon Jalila, se kuma daga baya da Hanan ta nunamin son da Jalila takemin ne yasa take fada da kowa akaina, kishina da take yasa take bani Kariya da dukkan mummunan abun da ya tinkaroni, shiyasa na samu karfin gwiwa na cigaba da kaunar ta, ina son Jalila sosai, kai se anjiman ku, zan fita gurin aiki"

Jawwad yace "har ka gaji da zubar? Da labarin soyayyar taka?"

"ina fa? Ai labarine sakanni, awanni, da wuni, sati, watanni ko shekaru bazasu bada damar gama wannan Labari, me dadi da ban tausayi ba se an jimanku"

Murmushi Jawwad yayi
"A da in aka cemin Jalal yana wannan zazzafar soyayyar zan rantse ince karya ne, yau gashi kunne na yaji min"

Hanan tace "Ain dama tuni nasan yana kaunar ta, kuma itama tana sonshi, shiyasa nai tayi musu Addu'a, nikuma na kafa tawa soyayyar"

Jawwad yayi murmushi yace
"gashi nan an kafa min ita inda ba wanda ya isa ya ganta balle ya taba, mata ta abar Alfahari na, Allah ya rabaki da cikin nan lafiya dake da Nana"

"Ameen my lovely Haidar"

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣9️⃣112

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Shiri sukayi sosai don tafiya garinsu Ummi, da farko akace baza'aje da su Nana ba saboda larurar ciki, amma sukace baza'ayi babu su ba suma suna son zuwa garinsu Ummi.
Shiri sukayi sosai, suka dau motoci suka nufi kwara state.

Tunda suka shiga garin Jalila ta kara tabattar da lallai Akwai banbancin Addini da al'ada.

Jalila tayi mamakin irin kyau da tsaruwar masarautar su Ummin ta, lallai Ummi ta cancanci yabo da jinjina, da ta iya tsallake wannan daular ta zabi Addinin musulunci da kuma soyayya.

Su nasu masarautun basa amfani da doki, se manyan motoci, ga barori nan nata kaiwa suna komowa, gasu da matukar biyayya, duk inda suka ratsa zubewa ake ana girmama su, musamman Ummi.

Seda suka shiga cikin gidan ta kara tabattar da lallai Ummi ba karamar 'yar gata bace ba, Tangamemen hoton Mahaifiyar Ummi ne sakale a wani katon guri kamarta daya sak da Ummi, duk da ta manyan ta seka dauka ya da kanwa ne.

An karbesu cikin girmamawa da mutuntawa, Seda suka huta, Aka dinga gabatar musu da kayan Abinci,
Seda aka jima suka huta sannan Mahaifiyar Ummi ta fito, Mahaifiyar Ummi na ganin Jalila ta rungumeta cikin harshen turanci tace

"ko ba' a gayamin ba nasan wannan itace jikata"
Ummi tayi murmushi tace "Eh itace"

Mahaifiyar Ummi ta kalli su Hanan ta kalli Jalila tace

"wannan 'yan uwanta ne?"

Jawwad yace "Eh duk' yan uwanta ne"

"to wace matar Jalal kenan?"
Nana tace "Jalila ce matarsa"

Mahifiyar Ummi ta jinjina kai tace

"Sunan ta da mijin ta suna kama, mijinki yana da kirki sosai lokacin da mamanki ta dawo gida yana zuwa nan"

Maman Ummi tana da kirki sosai, nan aka dinga gabatar da su gurin mutanen gidan, 'yan gidan sunyi murnar ganin yarinyar' yar uwasu, bayan tsawon shekaru 'yar uwatasu bata tareda su.

Sarkin da yake mulki a wannan lokacin wanda yakasance Yaya ga Ummi shima ya nuna farincikin sa da jin dadi, na ganin su Jalila.

Daddare suna hira, mahaifiyar Ummi take cewa su Jalila,

"nayi dana sanin hana marry ta auri wanda take so a wancan lokacin, dukda ba laifina bane, laifin kakanta ne, yana ganin na auri bahaushe musulmi zaman beyi dadi ba, nayi kewar ta sosai tsawon wannan lokaci, bana iya bacci, sannan mahaifina yace be yadda in tura kasar hausawa a nemo ta ba, duk abunda yafaru da ita babu ruwan wani. Ban taba zaton marry zata iya jure zama tsawon wannan lokacin ba ba tare da mu ba, bayan rasuwar mahaifina shekaru biyar baya, Yayanta ya karbi mulki, shi da kansa yasa a bincika koza'a gano ta amma abun be yuwu ba, na koma Addinin musulinci, Yayana yaba wa kowa damar yayi Addinin da yake so, abun mamaki akan marry na yadda musulmi kuma hausawa mutanen kirki ne, lokacin da ta dawo gidan nan nayi mamaki, labarin da ta bani akan yadda rayuwar hausawa musulmi yake, da kuma karamcin da suka nuna mata, musamman wannan dan kyakywan yaron me dogon hanci, yana burgeni matuka yana girmama ta kaman ta haifeshi, kuma da ta gayamin alakar dake tsakaninsu naga babu wani babbar alaka da suka hada amma yake ta dawainiya da ita shida iyalansa"

Jalila ta kunshe kai tana dariya taji ance Dan kyakywan yaro me dogon hanci

Hanan tace "Dallacan se wani murmushi take dan ance mijinta kyakywa, nima mijina kyakywa ne, dan mijina farine tas"

Nana tai caraf tace "nima mijina yana da kyan ai, tunda kanin mijin Jalila ne"

Sukaita hira suna dariya, mahaifiyar Ummi tana da kirki da sanyin hali kamar Ummi gata da faran faran babu ruwanta.

Amma duk abun nan Jalila hankalin ta yana kan Jalal, ta damu sosai rashin ganin sa, ba karamin missing dinsa take ba.

Kwanan su hudu a garin, sun sha yawo, garin yana da kyau, sun sha hotuna, gasu da yalwar dazuka, Akwai fulani a garin, da babur amma yawancin su yarabawa ne, suma mutane masu kirki da kyakywar mu'amala.

A kwana na biyar suka fara shiri domin tafiya su bar garin.

Mahaifiyar Ummi taji babu dadi, seda tayi mita

"marry meyasa bazaki barmin yaran nan ba su dan kara kwanaki, wallahi sun shiga raina sosai naji dadin zama da su"

Ummi tace

"kiyi hakuri zasu dinga kawomiki ziyara, matan aure ne yaran nan, yakamata su koma gidajen Auren su, sannan Zamuje maiduguri gidan Su Danki Jalal, Abban Jawwad zasu jira mu a can"

"Shikenan amma ba haka naso ba, naso kara zama damu, yanzu na kara tabattar da abunda ake fada akan hausawa musulmai ba haka bane, kuna da kyakywar mu'amala da kuma girmama mutane, Jawwad amma kaima zaka dan dinga zuwa ko?"

Jawwad yai murmushi yace "karki damu, dukkan mu ma zamu dinga kawo miki ziyara, amma kema muna fatan zakizo mana"

"zanzo mana, tunda ina daku, Insha Allah nima zanzo muku"

A kwana na biyar suka karasa shiri zasu tafi, An musu alkhairi me tarin yawa. Suka yi harama Jawwad ya dauke su suka baro garin suka nufi borno state.

A motar ma se hira suke, suna kara yaba kirkin mahaifiyar Ummi da kuma barkwancin ta.

Suka karasa maiduguri a gajiye, bayan la'asar sosai suka karasa, Antyn Jalal tayi murnar ganin su kwarai, musamman da ta gansu tareda Ummi cikin fara'a tace

"kai masha Allah, bakin ba zata, Ummi Kice keda iyalan naki gaba daya kike tafe"

Ummi tace "Aikam dai gasu nan"

"sannunku da zuwa Jawwad, dazu Jalal ya bar garin nan, nasan be san zaku zo ba"

Jalila a ranta taji dama tun dazun sukazo,

"meyasa Jalal yakemin hakane? Duk na damu yaki bari mu hadu sam, why?"

Anty tace

"Jalilan Ummi, gaki ga Ummi, dazu Jalal yabar garin nan, albarkacin ki yasa ya kan leko mu ya kawo mana ziyara, bashi da aiki se yabon matarsa ko kunya ta bayaji" dan murmushi Jalila tayi ta sunkuyar da kai.
Jawwad yayi alwala ya tafi masallaci,

Suma sallolin su suka gabatar, Anty se lallaba su Hanan take saboda ciki da suke dauke da shi.

Jalila tace "Anty ina Husnah ne da Amal?"

"Husnah ta koma gidan ta, Amal kuma tana gidan kanin Babanta"

Daddare mijin Anty ya dawo, yanayin yadda suka gaisa da Ummi ze tabattar maka da sun san juna, nan Ummi take gaya masa daga kwara State suke, ya nuna farincikin sa da jin dadin sa akan hakan, gefe guda kuma ya dinga tsokanar Jalila

"matar so inji mijin ta, ya akayi kukayi sabani da mijin naki ne? Shi ya tafi dazu kekuma kinzo yanzu, ya akayi hakan ta kasance? Gayamin sirrin mana daughter, banda zancenki ba abunda Jalal yake in ya zauna"

Jalila dai kasa magana tayi, kowa tsokanar ta yake saboda Jalal.

Itakam Hanan ana wannan hirar ta silale ta tafi masaukin Jawwad daga ta kai masa Abinci bata dawo ba se bayan karfe daya, Jalila ta dinga ce mata mara kunya.

Washegari wajen Azahar Abban Jawwad da Daddyn Hanan, se Maama da Mummy Hanan suka iso, gida ya dau harami ya cika da baki.

Suna zuwa da suka huta ba tare da bata lokaci ba Daddy ya gabatar da abunda ya kawo su na zuwa su jadadda godoyar su akan karamci da dawainiyar da sukayiwa Ummi.

Abee yace

"babu bukatar ku cigaba dayi mana godiya, duk abunda Jalal yayi wa Wannan baiwar Allah be fadi ba, musamman shima dawainiyar da soyayyar data nuna masa a lokacin da shi da mara uwa kusan daya, mun riga mun zama daya da mu da ku, dan Allah batun godiyar nan a barshi, Allah yakara hada kanmu ya kara mana kaunar juna, Allah ya Albarkaci rayuwar yaran mu, Amma babu godiya a tsakaninmu"

Suka Amsa da Ameen gaba daya.

Kwana daya su Abba sukayi, suka kama hanya zuwa bauchi, kafafuwan Hanan duk sun dan kumbura saboda zaman mota, hakan yasa Jawwad ya damu yace a bauchi ze barta ta huta, in yaso ya biya kudin jirgi su koma Abuja. Tun suna hanya Mahmoud ya kira Nana a waya yace mata yana bauchi, Nana se murna take yi, yau zata ga mijin ta, Jalila ta danyi shiru tana tunanin nata mijin.

A gajiye suka koma garin bauchi, a yan kwanakin nan sun sha yawo, da suka isa bauchi Jalila wanka tayi ta nemi guri ta kwanta tana baccin gajiya.

Jalila bata tashi ba seda Ummi tazo ta tasheta
"ki tashi haka kiyi salla kici Abinci mana, baccin ya isa haka uwar bacci ashe har yanzu baki dena wannan baccin ba"

A shagwabe tace
"Ummi wallahi a gajiye nake shiyasa"
"ki tashi haka dai baccin ya isa"

Jalila ta tashi tai salla ta zubo Abinci ta zauna kenan ta fara ci Nana ta shigo, ta kalli Jalila tace

"se yanzu kika tashi kenan? In kin gama akwai surprise"

"Suprise kuma? Suprise din me?"

"sekin gama tukuna"

Jalila tace "shikenan"

Jalila ta cinye Abincin ta, tanemi guri ta kashingida tana danna waya.

Nana ta dawo dakin ta tarar Jalila tana danna waya, ta dan hade rai tace

"wato baki damu da Suprise din ba ko?"

Jalila tace

"ai naga baki da niyyar gayamin ne"

Nana ta dakko powder da janbaki tazo gaban Jalila ta zauna.

Jalila ta kalleta

"wannan na menene kuma?"

"fita zamuyi, yaya Jawwad yace mu shirya"

Jalila ta dan bata fuska tace

"haba dai muje ina? Banda wannan gajiyar"

"ni dai ba ruwa na, shi yace mu shirya zamu dan fita"

ta shashsha fawa Jalila powder da jan baki sunayi suna fada Jalila tana mitar ita gaskiya bata son kuma fita a gajiye take

Hanan ta shigo tace

"Jalila har yanzu baki je ba?"

Cikin rashin fahimta Jalila tace
"nifa ban gane muku ba, inje ina kuma?"

Nana tace "kije BQ ki duba Suprise din yana can"

"nifa Nana nakasa gane miki, kince Yaya Jawwad yace zamu fita kuma kince zakiyi surprising dina"

Hanan tace

"dan Allah kije ki gani mana, ke ba kyacin ribar abu, ga mitar tsiya"

Jalila tace "saura inje inga shirme, sena muku rashin mutunci"

Hanan tace "in kuma akasin shirmen kika gani fa?"

Jalila tace "Bari dai inje in gani tukuna" ta dauki gyale ta yafa akan riga da skirt din jikinta ta fita

Da taje inda Nana tace taje bata ga kowa ba se Yaya Jawwad a parlor

Jawwad ya kalle ta yace

"Baby ya akayi ne?" ba tace masa komai ba se dai dan shiru da tayi tana nazarin dakin, tana kokarin gano wani abu, kaman kamshin turaren Jalal take ji, Jawwad yayi murmushi yace

"duba wancan bedroom din yana ciki, nasan shi kika biyo"

Ba tareda tace komai ba ta nufi dakin da Jawwad ya nuna mata da sauri, ga mamaki kuwa tana zuwa tatarar Jalal yabawa kofa baya, sanye da dogon wandon jeans da vest a jikin sa yana waya, da gudu ta tafi ta rungume shi ta baya, dan murmushi yayi yai sallama da wanda yake wayar da shi, ya aje wayar ya juyo da ita suna fuskantar juna, har hawaye ya wanke fuskarta.

"Ohhh am sorry dear, waye ya gayamiki ina nan ma tukuna?"

Shigewa jikinsa ta kumayi ta kankameshi kamar wani ze kwace mata shi ta sake fashewa da kuka.

Jalal yace "Subhanallah Kin san bana son kukanki, gayamin me yasa min ke kuka?"

A hankali ta fara magana cikin kuka "Am sorry Jalal, Am sorry"

"Aini bakimin komai ba, kidena kukan nan please"

Kasa denawa tayi, Hawaye ne wani na bin wani keta zuba daga idon ta.

Jalal yace

"Am sorry My love, ni nayi miki laifi, tsawon wannan lokaci dana boye miki nasan inda Ummi take, am very sorry ba laifina bane"
Tasa hannu ta toshe masa baki tareda girgiza masa kai.

"Nina yi maka laifi zaujee"
A hankali ta durkusa akan gwiwowin ta, ta rike kafafuwan sa tareda fadin

"Jalal nagode, bani da kalaman dan zasu nuna maka godiya ta, Allah ya biyaka da gidan Aljanna, sannan Kayi hakuri Jalal abunda na dinga yi maka a baya please forgive me"

Ba karamin mamaki abunda Jalila tayi ya bashi ba, da hanzari ya dagota ya zauna ya rungumeta a jikinsa, cikin sigar rarrashi ya fara magana

"Jalila laifin me kikayi min dana cancanci haka? Nima Ummi uwata ce"

Cikin tsokana yace "yarinya seda Ummi ta sameni sannan ta haifeki fa, kidena min wata godiya abunda nayi kaina nayiwa, sannan ni ba abunda kika yimin dana cancanci ki durkusa kina bani hakuri haka, ni yakamata in durkusa in miki godiya, Bayan Jawwad ban taba tunanin akwai wanda ze damu da al'amurana kamar ke ba, kalli rayuwar da nayi a baya, kalli wadda nake a yanzu, kinsaka rayuwar ki a cikin hatsari saboda ni, wani nasani wani ban saniba, abubuwam da kikayi min a baya kuruciya ce, kuma kinyi ne saboda kina kyamar mummunar Rayuwar da nakeyi, Thank you very much for all what you did for me, kin kawo canji mafi girma a rayuwar ABDUL JALAL, I love you so much my wife "

Ta kara kankame shi tareda fadin

"I love you too, Zaujee"

Yadda tayi maganar yaji wani abu ya tsirga tundaga kansa har tafin kafarsa.

"Jalila Do you really mean what you say?"

Jinjina masa kai tayi

"I mean it zaujee, I love you"

Jalal yaja numfashi yace

"Kalamai masu girma dana dade ina expecting a gayamin, gayamin yaushe kika fara sona ne?"

Murmushi tayi tace

"hmm wani dogon zamani da ya wuce, da farko dai na dauka kishi ne da tausayi daga baya kawai aka shammaceni aka jani fagen soyayya"

Dariya Jalal yayi yace "waye ya jaki fagen soyayyar?"

"Mijina mana daya tamkar da dubu"

"dan Allah ki dan kara cewa kina sona mana"

"I love you Zaujee"

Ya dan kashe mata ido yace "dan kara fada mana"

"Anki din bazan sake fadan ba cikani in tafi"

Kara riketa yayi yana dariya, abu kaman wasa Jalila taji Jalal yana neman wuce gona da iri dan haka ta rike hannunsa, tareda kiran sunansa da dan karfi

"Jalal"
Ya bude idonsa yana kallon ta

"Dan Allah ka kyaleni ba fa a gida muke ba"

"Au a daji muke?"

Kaman zatayi kuka tace

"Ina nufin ba'a gidanmu muke ba, Yanzu Ummi zata iya nemana fa"

"Shikenan karkimin kuka Sarkin kuka, Amma Jalila yakamata mu koma gida fa, yaushe zamu koma?"

"duk lokacin da kake so"

Ya dan lumshe ido yace "ko yanzu?"

Jinjina masa kai tayi alamar eh

"Shikenan ki koma ciki, da safe Insha Allah zan shigo in gaida Ummi, ki shirya gobe zamu fita yawo"

"ina zamuje?"

"Allah ya kaimu gobe zaki gani, in kinyi Salla ki hau online"

Hararsa tayi

"bazan hau ba din, kuma ba yawon dazan bika, kusan sati biyu nayi a cikin damuwa da kewar ka, nima sena rama"

"Haba matar kiyi hakuri, banyi hakan da gangan ba, nasan dana bar wayata a kunne, kirana zakiyi tayi kina koke2, nikuma bana son inji kina kukan nan shiyasa, Allah yabaki hakuri"

Mikewa tayi ta dau mayafinta tace
"kaga na tafi seda safe" kafin yayi wata magana tai waje abunta.

Tana zuwa ta tarar Ummi tana sama ita da Maama a dakin Inna, dan haka kai tsaye dakin da sukw ta wuce taje ta tarar da su Hanan sunyi kwadan garri suna ci.

Tana shiga Hanan kalleta tace "lallai matar so, se yanzu?"
Jalila ta harareta tace "ban sani ba"

Nana tai dariya tace "Jalila ina Jan bakin?"

Cikin ko in kula tace "mun shanye abinmu"

Hanan tace "wallahi Jalila baki da kunya"

Jalila tace "har na kaiki rashin kunya, kudena gulmar nan ku maida kai kuci garrin kwakinku"

Nana tace "zakiga mu maida kai muci garri, kema zezo kanki ne"

Jalila tana idar da sallar isha'i tai Azkar, suka fara waya da Jalal.

Duk soyayyar da Jalila tayi Abaya yanzu take tabattar da shirme ce yanzi ta gane menene hakikanin soyayya, yanzu ta gane se yanzu ta shigo fagen soyayya, Jalal yana tarairayar ta da nuna mata tsantsar kulawa.
Da suka gama wayar ma da Jalal chatting suka koma yi, da kyar sukayi wa juna sallama suka kwanta.

Kusan kullum idan yamma tayi, su Jalal se sun dau matansa sunfita yawo.
Jalal seda ya kyale Jalila takara kwana goma da Ummi sannan yace yana son sukoma Gida, Nana da Hanan duk sun riga sun tafi.

Jalila tunda taji yace su tafi tasan ya mata kara, amma seda tayi kuka, ana gobe zasu tafi Ummi ta kirasu ta zauna da su taita musu nasiha a karshe tace

"Jalila ga amanar dana nan, ki kulamin dashi, kiyaye hakkokinsa ki guji abunda ze bata masa rai koya sa shi yin fushi"
Jalila ta dan tura baki tace

"to shi bazaki ce masa ga amana ta ba"?

Ummi tai murmushi "Jalila ai bazaki taba canza hali ba, ni Jalal ne dana dole in jadadda miki ki kulamin da shi"
Jalal ya dinga yi mata dariya, Jalila tace "Ummi wai bazaki bimu mu koma kano ba?"
Ummi tace

"in biku in muku me? Gidan mu zan koma nima, se an kwana biyu zanzo in ga dakinki, nidai fatana Allah ya zaunar mana daku lafiya a daku nan ku"

Sam ba haka Jalila ta so ba, nan da nan ta fara kuka, Gaba daya yanayin Jalal ya sauya ganin yadda Jalila ta fara kuka Ummi tace
"Jalal tashi ka tafi kyleta, gobe insha Allah zaku tafi"
Haka Jalal ya tashi ya tafi.

Washegari gurin karfe sha daya na safe suka baro Bauchi zuwa kano ba dan Jalila taso ba dan sam bata gaji da ganin Ummin nata ba, ta sha kuka sosai kafin su taho.

Bayan Azahar suka isa gida, Jalal ya tafi masallaci Dan la'asar ta gabato, ita kuma Jalila ta shiga gida da kayan su.
Ta bude Dakin ta ta shiga ta tarar da Akwatina a ciki, set uku blue, silver, da purple kowacce uku da kit.

Mamaki ne yakamata tareda tunanin waye ya kawo wannan kayan? Kuma na menene.

Bata taba su ba, ta ajiye kayan da suka

Please Login or Register in order to submit comment