Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_***


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(SABON TAKU)_


[1:1] بسم الله الرحمن الرحيم


In the name of Allah, the Gracious, the Merciful.💕


SADAUKAR WA GA: BITTI HABIBTY💚(FEEDHOM)💋❤️

TUKWICI GA: DAUGHTER❤️(BILLY S FARI)💕

ALKALAMI TV;
(A shiga domin sauraron shrye-shiryen mu)
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


_*SHAFI NA DAYA_*


*ZARIA*


*2004*

Zaune nake a ‘dan tsukukun gefan kofar dakin mu. Gaba na kuwa wani tsohon kwano ne dake ‘dauke da sandararren tuwon dawa da miyar kuka koriya shar da ita, ina ci ina korawa da ruwan bunu marar sukari, can gefe na kuwa su Alawiyya ne da Hinde sun barbaje suna afka lomar taliya yar mirji data sha manja sun yayyan ka tumatir da albasa a akai. Kuka na na hadiye ina ko’karin ‘karasa cin tuwon gaba na don sauri nake yi zan kai wa yayan mu abinci dake can tsallaken gaban gidan mu can yake bakanikan ci. Fitowar babar su Alawiyya ne yasanya ni hanzarin mikewa, Na dauke kwanon gaba na, Ai kuwa muna hada idanu ta zabga min harara wadda tazame mata jiki kullum sai ta min.

“Mayya! Aniyar ki ta biki. Kurwar mu kur wallahi, anyi gado awajen uwa. Da shegen idanu kamar na ungulu..”

Nai shigewa ta d’aki, Na baro Babar su Alawiyya wacce ake kira da Bintalo tana zuba min kwandon zagi. Na danne bacin rai na na dubi Innar mu dake tsintar hatsi a tire nace,

“Innaar mu bari naje na kai wa yaya abincin sa..”

Na karasa magana, hade da d’aukar wata fashasshiyar kular abincin mu wadda itace me kyau acikin kwanukan mu da ake zubawa yayanmu abinci. Innar mu tayi murmushi tana gyarawa autar mu kwanciya dake baccin ta hankali kwance, gefan zaninta ta sunce ta ciro naira hamsin wadda itace dama a kullin zanin duk ta kanannade ta mikomin,

“Ungo ki taho da man gyadan ashirin sai yajin goma, ki biya ta gurin ladiyo mai koko ki sayo koko da kosai na ashirin.”

Rissinawa nayi hannu biyu na karb’i kudin, idanuwa na suka kawo ruwa cikin tsantsar tausayi nace,

“Innar mu to ke mezaki ci? Kinbar mana tuwon ni da yaya Najib, koko da kosan kuma na Aminatu ne.”

“Banasan sakarci sanda naci abincin idanuwan ki biyu?”

Girgiza kai nayi alamun a’a. Kafin na janyo kodadden koren hijabi na daya zama tamkar na gado na zura shi cike da tausayin innar mu, Uwa kenan gwara muci ita ta zauna da yunwa har sai mun gama sanwar rana. Sallama nayi mata na fito kai na a kasa na wuce ta gaban bintalo ai kuwa ban gama maganar ta a zuci ba ta zubamin rankwashi ji kake .’kwas’.

Su Alawiyya da Hindatu suka tuntsire da dariya suna gasamin magana, share hawaye na nayi, domin inda sabo na saba da irin rayuwar gidan mu. Dakyar na karasa sauka daga benen gidan mu mune a saman karshe mu dasu Bintalo da Usaiba maman su Larai, wato dakuna na uku acikin d’akuna tara dake gidan. Domin kaf layinmu da unguwoyin gaban mu babu wanda bai san gidan mu ba, wanda akewa laqabi da ‘Gidan Mata Tara’.

*HAYIN RIGASA MECHANICS*

Ina tafe a hanya ina bitar haddar Suratul Yasin da za’a karba anjima a islamiyyar mu. Sauri nake yi na ‘karasa na kai wa yaya abincin sa. Cikin nutsuwa na ‘karasa wurin aikin su. Na gaggayshe da abokanan aikin su kafin na wuce wajen daya ke zama. Can ‘karkashin wata mota na hango shi yana gyara notinan taya. Yayi dumu dumu da bakin man fetur. Cike da murmushi na ‘karasa wajen sa. Cikin nutsuwa da girmamawa na dan durkusar da kaina yadda zai iya jiwo murya ta nace,

“Yayan mu! Sannu da aiki. Ga abincin ka.”

“Na’am Batoul! Sannun mu! Ya innar mu da auta?”

“Lapia lou Yayan mu. Bari naje nayo cefane.”

Ina gama fada na mike daga tsugunnan da nake, Yaya ya zura hannu a aljihu yana lalibo kudi. Nera sittin ya ciro duk sun dunkule da junan ya miko min naira arba’in ya maida ashirin din cikin aljihun sa. Na danne kukan daya tahomin ina kokarin mayar da kai na gefe dan kada Yayanmu ya gano yanayi na.

“Yayanmu ALLAH ya kara bud’i. Me zan siyo aciki?”

“Jia kin tambayeni kudin Omo ko? To kiciri goma ki sayo omon. Naira talatin din sai ki sayo abunda babu a gidan.”

Gyad’a kai nayi, Ina tunanin abunda babu,

“Shikenan zan sayo maggi mai tauraro na goma sai albasa da tumatir na sauran ashirin din. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya ‘kara bud’i. Na tafi Yaya sai ka dawo.”

Sallama mukai dashi alokacin yana kokarin bude kular ‘dumamen tuwon jia dana kawo masa. Allah sarki Yayan mu bai ci komai ba ya fita daga gida tun asubah. Hanyar ‘karamar kasuwar sayar da kayan masarufin unguwar mu na nufa. Nan na hadu da Fadila babbar ‘kawata tana sauri itama da alama cefanon zata yo. Dan ‘daga murya nai yadda zata iya jiyo ni na shiga rafka mata kira ina hadawa da sassarfa don cinmata,

“Fadilah! Fadila!..!”

Juyowa tayi da sauri tana kallo na, fuskar ta dauke da murmushi. K’arasawa nayi ina haki. Ta dan dafa ni tana bubbuga bayana,

“Sannu tawaje na, daga ina kike?”

“Wallahi daga gida amman na biya na kaiwa Yayan mu abincin sa.”

Murmushi tayi hade da sakalo hannuwan ta ta wuyana muka ci gaba da tafiya a haka, Har muka karasa wajen Falalu mai kayan miya. Mutum hudu ne a gaban mu. Dan haka muka koma daga gefe muna hira. Fadila ta sauke nannauyar ajiyar zucia tana yar carafke da duwatsun hannun ta,

“Tawaje na nakasa cire Yaya Najib a rai na”

Na muskuta kusa da ita ina mai kallon kwayar idanun ta dake fitar da hawaye, Na kasa gane wane irin so takeyiwa Yayan mu, gashi a gidan su an hanata kula shi ko nace Umman su ta hane ta da kula Yayan mu saboda su sunada rufin asiri mu kuma talakawa ne wanda bamuda tabbacin cin yau ko na gobe. Mahaifiyar ta irin iyayen nanne masu son ‘yayan su su shiga babban gidah. Gashi Yayan namu a babban ajin sakandire na biyu yake ko ‘karewa bai yi ba, ya dena zuwa ya koma sana’ar kanikanci (mechanics) ta haka yake d’auke mana wasu hidindimun na gidah dana makaranta duk kuwa da ta gwamnati muke yi. Ajiyar zuciar nima na sauke, cikin bata baki da kwantar mata da hankali nace,

“K’awata kenan, dan Allah ki ‘kara hak’uri ki fawwalawa ALLAH lamurran ki, na rantse maki da ALLAH idan har Yayan mu mijin ki ne to babu shakka sai anyi auren ku. Sannan ki sani Yayan mu fa har yanzu kinga ba gama makaranta yayi ba ko ince ya dakatar da zuwa makaranta saboda muna cikin halin rashi. Muma kuma duka duka yanzu muke a karamin aji na biyu. Kinga kuwa akwai sauran lokaci, Saura aji hudu mu gama makaranta muma. Kuma ma ai shekarun mu bana zamu cika sha hurhudu fa (14). Dan dai ma kece kawai kina son sa ne amman naga shekaru hudu fa ya bamu...”

Nagama fada Ina murmushi, Fadila ta rafka min hararar wasa tana tsuke baki hade da sakin tsaki,

“Wai an gaya miki kowa irin ak’idarsa ce da ke? Ke wannan yadama amman ni gaskia inason Yaya Najib kuma zan iya salwantar da komai don zama mallakin sa.”

Tabe baki nayi ina sake cuno shi gaba, narasa meyasa take son Yaya Najib, ko yaushe tasan so oho? Kuma ma dai ni abokan Yayan mu wallahi kallon yara nake musu. Ina cikin zancen zuci ashe har layi yazo kanmu. Fadila ta mike ta sayo kayan miyan sai gani nai ta miko min bakar leda cike da kayan miya, Na bita da kallon ‘karin bayani. Duk kuwa da nasan hakan ba farau bane awajen mu. Amman gaskia ni kunya nake ji duk sanda tayi haka duk kuwa da nasan tasan mu ba masu hali bane.

“Dalla tashi mu tafi, kin ‘kuramin idanuwan ki irin na Ashwariyya rai!”

Daria nayi, domin duk sanda ta tanka idona da irin na Ashwariyya abun daria yake bani. Domin nasan ni dai ba jinsin indiyawa bace amman sosai mutane kemin kallon ruwa biyu ce ni. Saboda kyau da tsarin halitta da ALLAH yayoni dashi, wanda kwata kwata nafi yan gidan mu da yan d’akin mu kyau. A takai ce dai kamanni na daban. Na kan sha kuka na a duk sanda Bintalo ko sauran matan gidan mu suka tasani a gaba suna zagi na da aibata ni, koda yake wasunsu a gurin mazajen su suke jin cewar wai ni ba ‘yar baban mu bace, Ni shegiya ce. Nima nakan zauna wani sa’in na tambayi kai na ya akai na fita zakka a gidan mu? Amma kuma me? Ai ALLAH shine mamallakin kowa da komai, a haka ya yoni badan ya tsane ni ba. Cikin tafiya tunanin da nai fatata tai wani mugun radadi sakamon zazzafan mintsilin da Fadila ta sakarmin a dantsen hannu na na dama.

Hararar wasa na jefa mata hade da mika mata hannu na ta ja ni na tashi tsaye. Shagon Habulele store muka je na siyo maggi da da mai da omon da zan wanke uniform dina. Ganin harda rarar canji da na samu sakamakon kayan miyan da Fadila ta siya mana, hakan yasanya na tsaya na sai mana kifin talatin bayan na siyo koko da ‘kosan autar mu. Dadi kashe ni yau zamu ci dadi. A hanya naita yiwa Fadila godiar alkairin da take mana, Saboda kayan miyan yau data siya mana zai yi na nera dari, wanda idan har mun cancana shi zai mana sati munashan lagwada. Har k’ofar gidah Fadila ta rakani saboda gidan su na gaba da namu. Shigewa nai cikin gida fuska ta dauke da murmushi. Banbi takan surutan su Bintalo ba nai hayewa ta sama, dakin mu na shige baki na dauke da sallama.

Autar mu ce kawai xaune akan shamilalliyar katifar mu wadda kallo d’aya zakai mata kasan tayi shekaru a haka. Sai kwanukan mu a gefe nacin abinci. Gefe d’aya kuma kullin kayan mu ne a daddaure kamar kayan wanki. Tamkar dai a kurkin kaji. Domin kwata kwata dakin mu bai fi girman taku hudu na auni ba. Gashi mune a karshe, babu wundo kullum kamar dafamu akeyi Idan lokacin kwanciya yayi. Labulen dakin mu a jeme yake shima, Tun kafin a haifi autar mu makociyar mu inda Innar mu ke wankau a gidan itace ta baiwa Innar mu lokacin banfi shekaru takwas a duniya ba. Kallon Autar mu na sake yi ganin yadda ta dukunku ne tana sharbar kuka da jan majina, kusa da ita na je na janyo ta jiki na ina bubbuga bayan ta,

“Autar mu menene?”

Cikin rawar murya hade da jan majina tace dani,

“Yaya! Kashi ne ya matse ni naje bandaki don kasayar dashi. Ashe wai Kawu ila ya shigar da ruwan wankan sa, shine yai ta mun masifa na fito ko yashigo yaci ubana. Lokacin kuma ciki na ne yake ciwo. Koda na fito sai ya shiga ya dakko bokitin ya juye min ruwan a kai na. Sannan ya ‘kwallama innar mu kira kan ta biyashi ruwan sa tunda na ‘bata ruwan da warin kashi na, Kuma wallahi Yaya ni ko hanyar ruwan banyi ba, Wai lallai sai tabi layin tuk’a tuk’a (borehole) ta debo masa bazai yi amfani da ruwan rijiyar gidan nan ba, Kuma yaita zagin ta yana runkwashi na akai...”

Ta k’afarsa fada hade da fashewa da kuka. Nima kukan na shiga rerawa ina mai yin addua a zucia ta kan ALLAH ya yaye mana wannan ‘kuncin rayuwar da muke fama da ita shekara da shekaru,

“Yanzu ina Innar mu?”

“Ta tafi gangare debo masa ruwan.”

Hawayen dake yar tsere a fuska ta na goge, Sannan na mik’e na fice ina jaddadawa autar mu da taci koko da kosan dana siyo mata kafin mu dawo. Ficewa nayi cikin sauri nayi gangare inda tuk’a tuk’ar (borehole) yake. Can na hango Innar mu a layi, ta dan tsugunna tana duban wasu yara dake wasan yar gala-gala a gefe. Da sauri na nufi wajen ta,

“Innar mu.”

Juyowa tayi ta dube ni fuskar ta dauke da murmushi, dan sam bata ‘bata ranta a duk lokacin dasu Baba Ilah suka sauke mata kwandon rashin mutunci, Saboda batason ‘kimar su ta rage a idanun mu, Saboda ‘kannen uba da yayyun sa suma iyaye ne agare mu.

“Batoul..”

“Na’am Innar mu, Kije gidah zan taho da ruwan.”

Kad’a kai tayi, Sannan ta mike tana nunamin bokitin baba ilan. Tana tafe tana hada hanya saboda yunwa ga masifar su Baba ila da kullum da ita muke tashi. Mutum uku ne a gabana da haka da haka har layi yazo kai na. Na debo taf sannan na tafi gidah. Har cikin band’aki na kai masa, Sannan na haye sama abu na. Autar mu na gefe tana cin koko da kosan ta, Innar mu kuma tana yayyanka tumatir da albasa. Zama nai a bakin kofa ina bubbuga ‘kugu na sakamakon ciwon dayake min,

“Wash Allah Na!”

“Sannu Batoul.”

“Sannun mu Innar mu, Yawwa kayan miyan Fadila ce ta siya mana, nayi karambani na sayo kifi da kudin da Yaya ya bani.”

“Babu komai Batoul. Allah sarki Fadila angode mata Allah ya saka mata da alkhairi.”

“Ameen Innar mu”

Ba adau lokaci ba Innar mu ta gama abincin ranar mu, aka zubawa Yayan mu a roba autar mu takai masa. Mu kuma muka hadu muka ci namu a babban tire, domin haka muke cin abincin mu a tare ko Yayan mu yananan dashi ake haduwa aci. Na tattare dakin na share na kintsa komai sannan na debi uniform dina na makaranta da na autar mu nai kasa, na wanke tas banbi takan ba’ka’ken maganganun dasu Alawiyya ke gasamin ba.

Nasan mai karatu zai yi mamakin irin halin rayuwar da muke ciki a gidan mu, tamkar gidan haya dake tattare da yaruka kala kala. Toh zan baku takaitaccen tarihin mu.

*ASALIN MU*
(TAK’AITACCEN TARIHIN MU)

******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋



MX🧕🏼*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(SABON TAKU)_

_*SHAFI NA BIYU_*


*ASALIN MU*
(TAK’AITACCEN TARIHIN MU)


*GWANI IDRIS NAJIBULLAH*

Marigayi Gwani Idris Najibullah shine sunan mahaifin baban mu, Tare da matar sa Malama Halimatu Alkali. Ya kasance Malami a garin na kaduna, matar sa wato mahaifiyar su baban mu ita kadai ce mai dakin sa, ALLAH ya albarkace su da ya’ya shida: Kawu Ishaq, Kawu Dawood, Gwaggo Aminatu, Kawu Khamis, Sai mahaifin mu Salis, Sai Kawu ilyas wanda ake kira da baba ila shine karamin cikin su. Dukkanin yan dakin nasu a Zaria suke gidan mu d’aya, Banda Gwaggo Aminatu wadda ke aure a Kaduna. Gidan da muke ciki a Zaria gida ne na gado, wanda iyayen mu suka hada karfi da k’arfe suka siya. Dakuna tara ne acikin sa, kowanne guda d’aya d’aya ne ba ciki da parlor, Sai dakin baba ila dake ‘kasa shine mai ciki da parlor. Dukkanin yan uwan mahaifin mu a gidan suke da zama da matan su. Gidah ne mai hawa biyu, mune a saman karshe dake dakuna uku ne: Muna cikin d’aya, sauran biyun kuma Bintalo da y’ay’an ta na d’aya. Sai Usaiba mahaifiyar su Larai da Talatuwa, Usaiba matar Kawu Ishaq ta farko, sai amaryar sa Rabi’atu ita takansace juya ce bata haihuwa, sannan a dakin k’asa take, Dakuna uku na ‘kasan mu kuma, Kawu Dawood ne da matar sa Hafsatu sai yan biyun su Fareed da Fareedah. Sai Kawu Khamis da matar sa Innatuwa da Yayan su maza biyu ‘kanana wato Yusha’u da Bala. Sai dakin karshen saman nasu wanda Rabi’atu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu. Sai Kawu ila wanda ke dakunan ‘kasan karshe shi da matan sa Ummita da Hajara, dakin farko mai ciki da parlor Ummitan ce aciki wato matar sa tafarko Ita da tawagar yayanta su biyar dake yawan haihuwa take yi akub’i akubi. Sai d’aki dayan karshe na amaryar sa Hajara wadda ya aure ta bayan rasuwar mahaifin mu. Takasance tanada tsohon ciki wadda zata iya haife shi a kowanne lokaci saboda ya tsufa.

Marigayi Malam Salis Idris Najibullah shine mahaifin mu, Malama Kaltume Rabiu shine sunan mahaifiyar mu. Mahaifin mu kafin rasuwar sa ya kasance yanada mata biyu, Innar mu Kaltume sai Baba Zara’u wacce ake kira da Bintalo. Mahaifin mu dan asalin cikin garin Kaduna ne, almajiran ta takawo su shida yan uwan sa Zaria. Anan kuma ALLAH yayi zasuyi aure su hayayyafa. Mahaifin mu lokacin da suka fara sana’ar tashi zuwa garin katsina anan Allah yayo zai gamu da mahaifiyar mu a kauyen Shema. Mahaifiya ta irin fulanin nanne na jaub’awa, Mahaifin mu kuwa bahaushe ne gaba da baya. Domin kakan su ma kafin Allah yayi mai rasuwa ance a garin kano yake. Baba Bintalo y’ar uwar mahaifin mu ce, da kakanta da mahaifin baban mu uwa suka hada uba kuma kowanne da nasa. Auren nasu ma auren had’i ne ko nace auren zumunci ne, mahaifiyar mu kuwa itace matar sa ta ladan noma wato auren saurayi da budurwa. Mu bakwai ne awajen mahaifin mu, dakin mu mu uku ne, Yaya Najibulla wanda yaci sunan kakan baban mu ana kiran sa da Najib. Sai ni Fadimatuz-Zahra’u, wadda ake kira na da Batoul. Naci sunan mahaifiyar maman mu wadda ALLAH yayiwa rasuwa tun ina yar ‘kankanuwa. Sai autar mu Aminatu. Wadda taci sunan Yayar mahaifin mu dake garin Kaduna. Sai ‘ya’yan Bintalo guda hud’u, Yaya Zabba’u wacce ke aure a kauyen kod’e dake lahadin makole a Kano. Sai Alawiyyah da Hindatu wacce muke kira da Hinde, Sai autar su Hauwa.

Nasan mai karatu zai yi mamakin yawan gidan mu da kuma ahalin dake cikin sa, Toh kamar yadda kuka gani a baya, ‘Gidan Mata Tara’ gida ne mai dakuna guda tara. Sannan gidah ne wanda mahaifin mu da yan uwan sa su hudu suka hadu suka siya tun kafin a haife mu.

Mahaifin mu marigayi Malam Salis ya rasu ne shekaru bakwai da suka wuce lokacin autar mu Aminatu na jaririya, ya rasu ne akan hanyar sa ta zuwa gidah sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu, wata jibgegiyar gingimari ce tabi takan mashin din da yake kai alokacin yayo cefanen sunan kanwar mu Aminatu. Tundaga lokacin rayuwar mu ta canza zuwa halin rashi da kuma ‘kunci.

Ashe haka ‘kanne da yayyun uba suke? Tabbas mun shiga garari na rayuwa domin duk juya mana baya su kayi, abincin da za’a ci da rasuwar ma sai makwabta ne suke temakawa su bayar, sai da Gwaggo Aminatu tazo daga kaduna ne ta fuskanci halin da muke ciki, ta bamu hakuri sannan ta bayar akayo mana cefanen kayan abinci. Hakika Gwaggo Aminatu ita kadai ce mai kirki acikin yan uwan mahaifi mu, itace keyin mai yiwuwa don ganin ta tallafa mana ta tsaya har aka raba mana gado, mahaifin mu bashi da wata kadara fyace gidan da suka hada kudi suka saya shi da yan uwan sa, inda mahaifiyar mu da Bintalo kowanne ya kasance yanada rabo biyu biyu, tanada mata hudu mu kuma namiji daya mata biyu wato biyu kenan muma. Kowanne b’angare daga cikin mu ya tashi da daki d’aya d’aya. Sai da’ki d’aya wanda Rabi’atu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu, shine ya zamto a tuminin takabar su Innar mu. Nasan zakuyi mamakin toh a'ina Yaya Najib yake kwana ko? Toh Yayanmu yana d'aura net a tsukukun kofar dakin mu ya kwanta a kan yar tabarmar sa, wani lokacin kuma yakan kwana a langa langar makarantar almajiran dake kallon kofar gidan mu.

Tunda mahaifin mu ya rasu mu kai sallama da farin ciki, Innar mu ta kanyi wankau a gidajen masu hannu da shuni saboda rufin asirin mu. Yaya Najib kuma ya kasance yana kanikanci don samo mana abunda zamu afa a baka. Ni da autar mu kuma mu kadai ne keyin makaranta, itama ta gwamnati, wanda Yaya Najib da yanayi ya dakatar saboda bamuda halin da duk kanin mu zamu dinga zuwa makaranta, duk kuwa da ta gwamnati ce, Amman akwai tsarabe tsaraben kudin fom nera talatin duk wata, ga kudin littafi da fensir. Hakan yasanya Yayanmu dakatar da zuwa makaranta ya fara sana’ar kanikanci dan kare mana mutuncin mu, sannan muna zuwa Islamiyya duk wata naira hamsin itama yayan mu ne ke biya mana kudin. Duk kuncin rayuwar nan muka d’ai ne muka shige ta banda Bintalo da ‘Yayan ta domin ita su Baba ila suna taimaka mata. Hakan yasanya na qudri niyyar tsayawa tsayin daka don yin karatu sosai, Saboda inaso nayi amfani da damata na cika mana burikan mu. Hakika ALLAH ya yoni da saurin ‘daukar karatu da kaifin basira, komai yawan karatu cikin sauk’i nake gane shi na kuma hadde shi, Shiysa haddar AlQur’ani da muke baya min wahala, cikin kankanin lokaci nake haddace ta akai na.

Tabbas ALLAH ya yoni da zatin halitta da kyakkyawar sura, Idan ka kalle ni dole ne ka sake kallo na duk kuwa da kankancin shekaru na amman halittar jiki na a tsare take, ko’ina ya cika, sannan na kasance mai wata irin kalar fata ni ba fara can ba ba kuma baka chakulet ba. Na kasance tsaka tsaki wadda turawa ke kira da ‘brown skin’. Inada tsawo sosai

Please Login or Register in order to submit comment