Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa wajen motar nan bai ko dauki sandar ba ya karasa kusa da kafafuwan dake sanye cikin wani fari kar din silifas irin shirin da ake yiwa amare dai
hakan ya saka Gimbiya saurin rike hannun Fulani ta lumshe idannuwanta tana tunanin irin abinda yaron nata zai iya ji, dan ta tabata yarinyar nan yana sonta duba da har aka ji kamshin turaranta a tufafinsa kuma bai musa ba har aka bashi damar aurenta ya amsa da murna ta zama matarsa a dan kankannin lokaci ashe ba zasu raya zaman auren tare ba?

Fararan hannayensa ya saka da suke dake ya dora saman fararan kafafuwan nata

A hankali ya idasa saka hannunsa ya saka kansa cikin motar baki dayansa
Daidai lokacin da kunnayensa ke jiyo masa kukan tsofafin da suka rakota dakinta kamar haka" ashe ba zaki ga dakinki ba Bintu, Allah ya jikanki da rahama Binta, Allah ya haskaka makwoncinki salihar yarinya mai hakuro da nagarta

Zuciyarsa ce ta doka da sauri ya saka hannun nasa ya yaye rufar da akaiwa fuskarta

Fuskar nata ya tsurawa ido
Fara ce sal, sannan fuskar nata ya amshi mahaukaciyar makup mai iya doka zuciya ta saka a ji an kamu da son mai dauke da ita
Irin gashin idon nan natural ta saka mata shi ya yi mata wani irin gazar gazar duda idannuwanta a rufe suke ruf domin Anmy ta rigaya da ta shafe mata ido

Dagowa ya yi a karo na farko ya bi mutanen sake wajen baki daya da kallo

Muryarsa a saukake ya ce" ku je

Daga ku je din bai dora komai ba, sai dogarai dake faman aikinsu
Ya rage daga Anmy sai y'ayanta sai manyan datijan dake wajen

Kansa a kasa ya furta" iyayenta sun ji?

Anmy ta gyada kanta ta ce" yaya ya tafi wajen mahaifinta dan na jima ina kiran layinka bana samu, sai daga baya na kirayi amintacenka

Kansa ya gyada a hankali ya kuma fadin" zan kimtsata da kaina, zamu kwana yi mata adu'a, Anmy in sha Allahu zata samu sutura nagartaciya zata yi makotaka da Abih da kuma Aliyu, ina fatan da kuma adu'ar ta kasance a fadar ma'aiki

Salalahu alaihi wa salam suka amsa a hankali

Anmy ta ce" a ina zaku yiwa gawar karatun? A ina zaka kimtsata?

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa mai zafin gaske ya ce" a bangarenta

Hannunsa ya kara mikawa ya kamo na mahaifiyarsa ya ce" Anmy, ku je bangarenki, ba komai ku yi ta adu'a

Kanta take gyadawa ta maida dubanta wajen motar ta kuma kallo

So take ta fashe da kuka, so take itama ta saki zafin da take ji ta yi kuka sosai, sai dai ba halin hakan, an jima da horar hawayenta da tsayawa a lokacin da ya dace ta zubo su, an jima da horar zuciyarta da wata irin dakiya wace ke ritsa zuciyar ta yiwa zuciya lahani
Hakama yaronta ya taso da horo wanda ya fi wannan tauri a matsayinsa na d'a namiji kwalin kwal a wajen mahaifinsa wanda ya rayu, ba wai ba'a taba haihuwar wssu mazan bane, no, an haifa du basu zauna ba sai mata da suke yayunsa du ba a nijer din bama suke aure hakan ya sa basu halarci auren kannin nasu ba bama kowace ta ji zai kara aure ba dan shi din ba mai magana bane kuma basu yi waya da anmy ba, shirye shiryen zuwansu da suke na su yi jajen rasa Aliyu ne

Baki dayansu suka rankaya suka tafi bangaren Anmy

Yana nan tsaye da dogaran yana ta dube duben cikin motar da komai mahaifinta ya karaso da mahaifiyarta

Sosai mahaifiyarta ta yi kuka ta rungumeta a jikinta ta furta" kamar yanda kika kasance yarinya mai faranta min, mai yi mana biyaya, Allah ya karbe ki da ni'imarsa Bintu, Allah ya yafe maki kurakuranki mu kam mun yafe maki dukan laifinki
Kansa a sade yake yana dauraron irin adu'ar iyayenta a kanta, kwarai ya kara tabatarwa kansa cewa ya yi rashin mace mai daraja, irin yanda du bakin da ya bude tun zuwansa wajen yabonta ne da fatan alkhairi a gareta sai ya ji yana mangarinta, sai ya ji yana mai adu'ar Allah ya sa idan tashi ta riske shi ya samu irin wannan shaidar ta duniya wace itace ta lahira
Mahaifiyarta ta dora kanta a gefen hannun mahaifinta dake dan dadaba bayanta a hankali dan ya rarasheta ta ce"ta rayu da son gannin sarki a rayuwarta, tana son ta ganta gata ga sarki,
Sai gashi yau Bintu gaki ga shi aman baki san yana wajen ba,

Maganar ta kuma dukansa, dan haka sai ya nemi da su je ciki a kaita ciki kawai

Sai da ya gama dukan abinda yake na bincike sannan ya kamata, ya cicibata ya dorata a gadon bayansa dan kuwa ya ki dogarai su kama masa du irin nauyi na gawa ya dorata a bayansa ya nufi bangaren da aka kawata mata

Shinfideta ya yi saman cafet ya zauna a hankali ya cire babar rigarsa

Karatu ya saka ya shiga cire mata takalman kafafuwanta, ya ringa cire mata komai a hankali sai da ya cire mata komai ya dauki sabuwar zanin rufar da ya kawo ya rufa mata shi har kanta

Mikewa ya yi ya je ya yi waya da anmy sannan ya karasa ya bude ya amshi likafanin da ya bukata har an kawo masa, a lokacin yake son shiryata

Dukan abubuwan bukata ya kawo kusa da shi ya shiga binta a hankali a laluma yana lalabata yana yi mata alwallah

Dakatawa ya yi dan dole sai an cire masa abin idannuwan nata da kuma su sarka da yan kunnayen dai da sauransu

Gaba daya jikinta rawa yake, tun da ta dawo ta tardo wannan lamari ta ji gaba daya hankalonta ya gama tashi jikinta kuwa ya kwashi rawa yanda ka san mazari

Bata furta komai ba, tafe dai suke ita da Zahrau har suka shigo falon

Gabanta ne ya yanke ya fadi a lokacin da ta gansa zaune a kasa ya sada kansa gaban gawar yana karatu muryarsa a bayanne aman a hankali kuma a sanyaye
haka kuma bai cire rawanin dake jikinsa ba aman baya dauke da babar rigar
Gaba daya zaka fahimci yana cikin tashin hankali ne idan ka kalli jijiyoyin hannunsa irin yanda suka mimike suka yi wani irin tsanwa da su abinka da farin mutun

Hannun Zahrau ta damka wace ta jata suka karasa baki dayansu

Bai dube su ba, sai hannunsa da ya saka ya bude fuskarta ya kasance fuskar ta bayanna

Irin yanda fuskar ke fitar da annuri dole ka ji hankalinka ya tashi, gata dai kamar wace take bacin gangan

Sai a lokacin ya dago ya dube su
Ya san cewa itace mai iya fitarwar dan haka ya nuna mata kusa da kan Bintun yana nufin ta karaso ta cire mata

Jikinta na ci gaba da rawar ta karasa ta tsugunna
Dan man dake hannunta ta lakuta hannunta na rawa ya kai wajen idannuwan bintun
A hankali ta shafa mata a idonta na dama ya dan dauki dan time ta janye shi ta cire shi a hankali ya biyo hannunta ba saura ko daya a jikin

Dayanma ta saka hannunta ta shafa sai kawai ta ji ta kasa rike kukan nata a wannan karon
Hakan ya sa ta zabura ta mike tsaye da niyar guduwa waje ta ci kukan dake wuyanta, shikenan? Yanzu shikenan? Yarinyar da ta je dazu ta yiwa kwaliya har sunna tsokanarta wajen turara mata turaran wuta itane kwonce haka gawa? Sai an juyata sai an kwontarta?

Hannunta da ta ji an damka ne ya sakata saurin juyowa

Bai bata damar fahimtar komai ba ya risinar da ita kusa da shi sosai har ya kasance sunna gugan jikin junna

Sakin kukan ta yi da karfin gaske hakan ya saka shi janyo kanta shima da karfin ya dora saman kirjinsa ya saka hannunsa ya tare keyarta da shi har yana hade hijab dinta da shi sannan ya shiga girgiza kansa a hankali ya ce" yaya zaki yi irin kukan nan a kan gawa? Kar ki kona min jikin matata

Muryarta cikin kuka ta ce" ta mutu? Shikenan ta mutu? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Zahrauma ta janyo kafafuwanta ta hade da gwuiwarta ta fashe da kuka tana mai tausayin kanta da dukan musulmai

Ya zama dole dai sai an mutu? Kowani mai rai mamaci ne , ya zama dole kowa ya dandana zafin mutuwa

Jin ta sasauta kukan ya saka shi cire kanta daga kirjinsa yana yi mata wani kallo mai cike da fasarori irin na jin haushinta, na gannin rashin dacewar ta yi masa ihu a ka ga kuma gawa haka kawai, ya dauki hannunta ya nufi wajen fuskar domin ba idasa cire abubuwan ta yi ba shine zata wani tsere ita ga mai neman balaki!

Hannunta na rawa tana dan cije lebenta na kasa ta idasa cirewa

Gannin ya nuna mata yan kunnayen da sarkar ya sakata zaro idonta

Mikewa ta yi da sauri ta fita da gudu tana kara sakin kukanta

Da ido suka bita daga shi har zahrau, dan haka sai ya nemi da Zahrau ta cire dan shi baima san yaya ake saka abubuwan nan ba

Zahrau ta taimaka masa suka cire yan kunnayen

Sun zo cire na wuyan ne suka ga wani bakin abu ya bushe a wuyan nata

Da sauri ya saka yar auduga a ruwa ya shiga goge wajen
Wasu yan hudoji ne biyu rak suka bayanna a gefen wuyanta

Hannunsa ne ya shiga dan rawa a lokacin da wani tunani ya darsun masa a zuciyarsa dan haka bai yi kasa da gwuiwa ba ya kama wajen ya matse da karfin gaske dan gannin idan har abinda yake zato ne

Irin ruwan da ya fito, kafin wani bakin jinni ya ci gaba da fita ne ya saka shi rintse idannuwansa yana jin wani irin zafi da ciwo a zuciyarsa

Bai ce da ita komai ba sai salamarta da ya yi

Bai yi mata wankan ba sai da ya tabata saran na wani kalar maciji ne sannan ya kimtsata tsaf cikin suturarta ta karshe kafin ya tatare komai ya yiwa malaman dake jira iso suka dukufa suka shiga sauke mata alkur'ani mai girma, sannan liman ya je masalaci ya yi shela da kuma raraba kulhuwalahu dan yi mata shinfida ( ya Allah ka bamu irin gatan nan )

Sai da aka yi saukar fari sannan ya fito ya kara komawa wajen motar nan

Da hasken wayarsa ya kara hahaskawa tare da amintacen dogarinsa
Gaba da baya basu ga komai ba dan haka suka buda boot

A tare suka zabyra sakamakon gannin wani dan saurayi dake daya daga cikin yaran gidan dake gyara wajen dawakai, yaron maraya ne gaba da baya yana aiki ne a gidan sarki a mace shima da kuma macijin nan a raye ya nanade jikinsa sai kansa dake dan gilo a sama kadan

Da sauri amintacen mai martaba ya so matsa mai martaba gefe dan kare shi daga macijin nan

Sai dai ya tare shi ta hanyar bashi wayar hannunsa

Cike da kwarewa ya damki macijin nan ya yi masa rikon nan da ake yiwa makogwaron maciji ya janyo shi inda macijin ke ta fitar da dan harshe yana wani irin kara sssssssssssssss

Yar yatsarsa ya saka bayan ya kara tabe bakinsa sosai ya cire abida ke watsa dafin sannan ya mikawa amintacensa ya maida dubansa wajen yaron

Harbin bindiga ne kansa harbi daya tak wanda ke fasara komai wato yaron ya yi aikin kashe amaryar mai martaba wanda ya saka shi aikin kuwa ya kashe shi

Sai da ya yi kiran asibiti aka tafi da yaron dan aune aunen bulet din da sauransu sannan ya wanke hannayensa ya koma ya har amintacensa da macijin nan inda ya nufi cen cikin fada da shi dan ganno na waye domin akoy yaren dake wasa da macizai a cikin gidan sannan da masu koya masu yanda zasu tafiar da maciji


..........................................

An yi sututar bintu cike da daraja da tarin al'umah
Ta samu adu'a'u, tana cikin samu domin mijinta ya dauri niyar jerota a cikin mutanen dake samun adu'ar nutsuwar kabari har karshen rayuwarsa bayan kuluhin musulmai da yake bi da shi

Gidan ya kuma daukan haramar jama'a, mutane zuwa suke ta kowani gefe ana yiwa sarki da ahalinsa ta'aziya ciki kuwa harda yayunsa da kanwarsa daya kwal dake garin Niamey wajen yayarta

Yana zaman makoki ne hankalinsa a rabe, sosai ya kara sakawa rayuwar gidan ido inda bincike ke tafia ta kasa yana son sannin abinda ya kawo maciji da mai wasansa cikin sabuwar motar da ya ware a boye dan dauko masa matarsa motar da ta kasance mutun shida kawai suka samu ganninta suka san da ita su ne : Sarki, Anmy, amintacen sarki, Zinaria, Abih, sai liman baba

Gidan bai samu sasaucin jama'a ba har sai da aka yi satin Bintu
Daga lokacin gidan ya fara samun daukewar sahu kadan kadan sai masu zuwa ziyara masu zuwa gaishe da sarki daidaiya

Zaune suke kowane da yamutsen zogalensa a cikin plate sun saka Anmy gaba sunna dan ci kadan kadan

Daya daga cikin kawayen matar ambasador ce akayiwa iso tare da mijinta zasu yiwa Anmy gaisuwa duda ita ba sanninsu ta yi ba aman da yake sun saba sai ta umarci a shigo da su
dan

Ajiye nata plate din ta yi sannan ta dan fito daga cikin yaren nata ta zauna inda take karbar baki

Tun da suka shigo suka zube sunna gaishe da Anmy
Mijin nata ba wani tsoho bane, hasalima Ambasador ya girme shi a shekaru

Anmy na amsawa tana mai nuna masu jin dadinta

Matar ce ta dago da yannayi na iya yi , kana ganninta ka san wannan kamar itane mijin shi kuwa matar dan ita ke ta yawan magana shi kuwa kamar mai jin kunya kansa a sade kawai yake

Tun da suka shigo Najeeba ta shaida matar
Itace take kakabewa matar Ambasador jikinta tana nuna mata ta bari haka gamuwa ta biyu zata kara daukan fansa

Da iya yi matar ta ce" na jima ina son samun shigowa nan Gimbiya Allah bai nufa ba sai dai mu tsaya daga waje idan mun zo, wannan mijina ne sunnansa MOUSTAPHA likitan zuciya ne baban likita ne da ake ji da shi a kasar nan
Ni kuwa sunna na AISATA yar kasuwa ce ni ina hada kayan lefe da komai da komai masu kyau na manyan mutane

Gimbiya na gyada kanta kawai, dan bata son ta ga mace na zubar nan kamar wace aka tambaya, ita da ta zo ta'aziya sai ta bige da tallah?

NAJEEBA ta ringa juya dan spoon din hannunta dan karami mai yatsu wanda take dibo zogalen da shi tana kara juya shi tana kallon matar da kallo irin na....ta kawo kanta har gida

Cike da sarauta Gimbiya ta juya wajen y'ayan nata

A nutse ta ce" NAJEEBA ta'al

Mikewa Najeeba ta yi daga zaunen da take
Hijab ne ja a jikinta mai tsayi har kasa sai hannayenta da ta fitar ta jikinsa ta shiga takowa a hankali

Tun da ta taso matar ta kai dubanta wajenta
Kamar wace aka yiwa kidan maruka a kumatu haka ta ji zuciyarta na yi mata balin balin
Idannuwanta ta kara fitarwa dan tabatarwa kanta shin itace ko mai kama da ita ce?

A lokacin ne kuma NAJEEBA ta idasa karasowa falon tana dan yatsina fuskarta da yannayi na sangarta ta rage muryarta sosai ta shagwabe yannayinta sosai sannan ta ragewa idannuwanta girma ta ce"""""":






..........zuwa
ah....
.....
......
...............mu je zuwa>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



18




A cikin wata irin sansayar murya ta ce" Anmy, zuciyata ke min zafi ban san dalili ba tun jiya da safe

Anmy ta dubeta da duba irin na kula sosai ta ce" subahannalah wani irin ciwo ne haka Najeena? Tun yaushe? Zo mu ga?

Karasawa ta yi ta dan duka gaban Anmy ta dora hannunta saman mamanta na hagu daidai zuciyarta ta ce" Anmy, nan ne, sai yana min zafi , yana sukana yana min ciwo, ni dai tun da gabana ya fadi rasuwar matar yaya nake jin haka

Sosai hankalin Anmy ya so tashi tana ta dora hannunta daidai wajen ta ce" idan na danna akoy zafi?

Da sauri ya ce" aa kar ki danna Allah da ja da rai, ba'a dannawa da garage har sai an je an yi mata gwaje gwaje, inaga tunda daidai zuciyarta ne ta samu ta leka clinik dina gobe da dare bake hawa in sha Allah sai na yi mata dukan binciken da ya dace

Gaba daya matarsa ta zazaro ido ta aniya zazago girmansu da rawar lebe

Gashi dai a gaban idannuwanta komai ya wakana wanda ta rantse da Allah karya ne

Gabanta ne ya kara faduwa a lokacin da kalaman Najeeba suka dawo kunnayenta da irin rantsuwar da ta yi kan sai ta rama baki dayansu

Kafin ta ankara tuni an yi mai yiwuwa domin wayar mijinta ne a hannun Najeebar har ta dora number Anmynta wai dan ta yi serving, a haka cikin gagawa ta dora nata number ta yi dialing, yana shiga ta kashe sannan ta mika masa wayar harda dan risinawa

Sai kawai matar ta zama wata wawa sai zarar ido take har suka mike suka fita

Tun kafin su karasa fita ta ja ta tsaya ta ce" bani wayarka

Dubanta ya yi da mamakinirin yanda ta yi tambayar wayar
Du tsakaninsu basa taba wayar junna, sam basa daukan wayar junna dan gudun fitintinnun yau da kulun sai gashi haka kawai wai ya hata wayarsa?

Karasowa ta yi ta ce" ka ga aban Barira wayar nan taka walahi ko ka bani ko yau na fasata na karya layinka dan karuwar nan ba zata daukan min numberka haka kawai ta tayar min da hankali ina zaman zamana dan nan kawata ta kawo kararta da yake gidansu ne sai aka bige da daure mata karshe sai kawar tawa ta dauki laifi an shanye mata miji ita ba aurensa ta yi ba sai tatikarsa kudi take, shi bai zauna a gida ba sai yawon binta yake sunna yawon iskanci!

Girarsa ya gama hadewa ya juya yana tafia da wani irin sauri
Har sai da ya fita sannan ya duka ya dauki takalmansa ya saka ya karasa wajen motar

Da yannayin karkamba ta karaso tana ihun sai ka bani wayar nan idan ba haka ba kowa ya mutu

Motar ya ja ya mako da karfin gaske tana tsaye a waje ya sauke madubi ya ce" ki nemi ubanda zai maida ke gida, kin san ko ji waye na rantse maki zan lalasa maki jiki na daki kodadiyar fatar nan taki, idan ba jaraba ba mata bi danki ne da zaki ringa yi min ihu? Kin san ko ni waye kin san irin tashancina, sannan idan har y'ar na ja haka zamu ja sai ki yi ubanda zaki yi

Wata ashar ta lalayo ta afka masa tana dukan motar ta ce" motar banza gareka? Ka je sai me zan nemi mai kawonin kuwa , kuma komai jarabarka a gidanka zan kwana sannan in dai una rate ba dai bakar y'ar nan ta kwace min miji ba kawayena su zageni

Yawun bakinsa ya tofa mata har zuwa gaban rigarta ya ce" da ace ke farin naki ba na kanti bane da sai ki zagi wani da cewa baki, ke na rantse da ace ta aureni ko? Zan sake ki ne da ke da y'ayan da ban yarda cewa nawa bane ku kara gaba na huta da jarababiyar mace mai warin jaba! Sannan zaki dawo gidan zamu gwada karfi ne da ke mu ga wanda ya fi wani banza mahaukaciya mai kai kamar baro

Yana gama fada ya tayar ya fice da wani irin gudu kamar ba shine yanzu a gaban gimbiya kansa a sade kasa ba, kamar ba shine shiru shiru da lafia ba, kamar ba shine mai yin shiru ita na magana
Dama sun zo ne dan su kula alaka da ahalin gidan, sai yau suka samu gannin Gimbiyar dan su kula alaka duba da ita babar yar kasuwa ce shi kuwa likita ne yana so idan da hali ya zama likitansu na cikin gida fannin zuciya
Sai gashi sun samu nasarar kula hakalar domin har number Gimbiya ya samu yau a wayarsa aman shine matarsa ke cewa ya fasa wayar ya karya layin? Yo shi ko ubanwa ya fito masa da maganar nan ai bama zai dube shi ba zai yi ya gama ne ya bashi lafia yau ya ga iskanci
A takaice dai wannan mutane da suke mata da miji dama haka suke, sukan tayar da balaki su daki junnansu har titi ne
Tabas matar bata zauna dam ba, shi kuwa mijin hakan ya saka ya zama wani irin marar tausayi da daga mata kafa a rayuwa
Idan ba yan anguwarsu ba a wajen anguwar ana zaginta cewa ta fi karfinsa ta hanna masa zaman lafia
Yan anguwar kuwa sun san waye shi domin mutun ne mai dukan mace kamar ya samu ganga, yaka daketa ta rama daidai gwargwadon iyawarta su yiwa junna gori sannan su koma cikin gidansu,
Y'ayansu ba mai mutuntasu, yawonsu suke son ransu ba matan ba mazan ba wanda ya isa ya hana su ko ya saka su a cikin iyayen nasu...........................

Wayarta ta ciro ta nemi layin wani farkanta ta koma gefe tana juran karasowarsa dan ba zata je gida a yanzu yanzu ba a yanda ta zage shin nan ta san a irin lokacin nan sai ya kusan kasheta

Anmy kam ko bayan tafiarsu sai ta kasance mai baiwa Najeeba kulawa duda ta ga ta dan warware ta shige cikin yan uwanta sunna cin abincisu aman sai ya kasance tana yawan tambayarta yaya take ji har suma suka so tayar da hankalinsu sai ta basar ta nemi zuwa kwonciya

A ranar da Bintu ta cika kwana tara da rasuwa da safe ya kasance du an watse sai masu hidimar gidan sai yan matan Anmy da basu tafi ba sai an yi sati biyu zasu koma gida

A yau da safen ne kuma suka soya fara, sukai mata suya mai dadin gaske suka zauna a nan falo tare da Anmynsu itama tana cin kambolinta basu saka mata yaji ko daya ba

Sunna yar hirarsu falon sai ya su ya su, hirar ba wani ta shan dariya bane aa, aman lokacin sunna raba shi ne da wani irin shakuwa da kulawa da junna

Maganar da jakadiya ta duka tana fadi ne cewar matar Abih na neman iso ya saka Gimbiya kallonta da kallo irin na son ta maimaita

Kara sada kanta ta yi ta maimaita maganar

Dago kanta gimbiya ta yi daga kallon Jakadiyar ta sauke saman yaran

Ta dan jima kamar second talatin tana kallonsu sannan ta cire kanta a kansu ta gyadawa Jakadiya kai

Mikewa Jakadiya ta yi ta juya, dan ta gane amsar cewa eh aman ba yanzu yanzu ba

Cike da kauna Gimbiya ta kalli yaran ta dan gyara muryarta ta ce" kunna ji?

Du dubanta suka juyo yi

Gimbiya ta yi masu murmushi ta ce" bana so a raba hali

Du sun fahimci inda ta nufa aman dan ta tabatar cewa sun fahimtar sai ta masu shiru daga haka itama ta ci gaba da dan daukan kambolin farar tana dan ci har tana mamakin kanta yanda aka yi take cinsa da yawa haka ko dan tare da mutane ne

An dauki kamar minti goma zuwa lokacin Har Gimbiya ta wanke hannunta, yaranma kananun ne basu gama cinye fararsu ba

Da salama suka shigo falon

Masu yi masu jagora ke amsawa da karfi karfi sunna fadin" ku shigo a hankali, Gimbiya na falo
Ku sada kanku kasa ku gaishe da mace daya tamkar da goma mama a wajen sarkin damagaram
Ku tako sannu sannu

Bakinta ta dan tabe tare da yayarta suke wace ke biye da jakadiyar dan aiwatar da abinda ake nuna masu

Sunna zuwa du suka nemi zama a kujera
Sai dai basu kai ga karasa nufinsu ba da sauri Jakadiya ta tare tana nuna masu wajen da ya dace su zauna domin idan ka ga Gimbiya na sama wani na sama toh sarki ne, sai y'ayanta dake hayewa jikinta su dora kansu a saman kafarta, su kansu idan ka ga sun layi da ita to a

Please Login or Register in order to submit comment