Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da laluma ya yi mata damkar da zai iya halakata

Ba zata iya yarda ya tafiarsa ya barta a wajen nan sannan ya dawo ya sameta ya idasa halakata a daren nan kwaya daya da ya yi mata saura na amarci, a gaskiya ta daina mamakin irin ihun da Nadia ta ringa yi, sannan ta ji takaicin Zinaria dake kishi da wannan abin, wahalar? Tashin hankalin? Azabar? Kai gaskiya bariki hauka ne, a haka yan bariki ke rayuwa da maza kala daban daban? Wani daidai su wani ya girme masu, a haka su kamu da cutar kaikayo da sauransu (Allah ka shirye mi, ka rufa mana asiri, ka shiryi zuri'armu , ba dan halayanmu ba, ba dan wata ibadarmu ba, Alfarmar fiyayen halita da alkur'ani, ka raba mu da zina koda ta ido ce, ko wace iri ce), ita bata ga abinda zata yiwa kishi ba in dai ba dan dan kyan nasa da dan kudin nasa da dan farin nasa ba, to meye abin kishin? An ce mata shi sukewa kishi, ashe kuwa mata basu san ciwon kansu ba? Ita kam gaskiya ya fi karfinta, gaskiya sam ya fi karfinta...

A hankali ta idasa saukowa ta shiga bin bango bayan ta idasa zuge zif dinta ta rufe bayanta da kyau

Zama ta yi waje guda ta ringa sauke ajiyar hutawa, zamanma ba wai rasras ne ta yi shi ba, baki dqyanta dan dosanuwa ne ta yi a babar kujerar dake da wani irin tsari ta dafa hannayenta suka tatareta tana kara rintse ido

Sama sama ta ringa jin magana, ta yi dan tsai dan jin maganar ta dan lafa sai kuma ta ganshi ya shigo da wani irin sauri

Da kallo ta bi shi a dan tsorace gannin abinda ya dauka a hannunsa ya kuma ficewa tamkar bai kula da ita a zaune ba

Irin yanda yannayinsa ya nuna tashin hankali sai du hankalinta ya tashi

A hankali ta kuma cicibawa da kyar ta mike tana jin wata irin juwa na zuwar mata na yinwar da ya gama cinye du wani dan abincin dake cikinta ta nufi fallon

Bayansa take hange, yana tsaye hannunsa daya a goye a bayan nasa , sai mutane biyu da take jin kukan daya, dayan kuwa kansa sade yana ta murza hannayenta ya kasa wani motsi kirki

A hankali take kara matsowa, sai dai bata idasa matsowar ba ta fara fahimtar matar dake zaune, hakan ya sa gabanta yankewa ya fadi

Muryar jakadiyar sarki ke neman iso,
Mai tsaya wata wata ba ya bada damar shigowa

Mutanen da suka shigo dauke da mutun ne ya saka Najeeba ja ta tsaya gabanta na dokawa

A lokacin da suka shinfideta a wajen da ya nuna sunna ta kakareta da alkyabarta ya saka Najeeba jin kafafuwanta sun fara rawa sosai da sosai

Sai da suka fita sannan ya karasa wajen da mamanta ke son isawa aman mijinta ya riketa, ba dan komai ba kuwa sai dan kasancewarsu a gaban mai Damagaram, koma menene basu da damar idasawa wajen nan a irin wannan lokacin har sai an basu dama, duda kuwa y'qrsu ce ta cikinsu, shi din ai sarkinsu ne

Alkyabar tata ya yaye, lokaci daya idannuwansa suka sauka a wajen kafafuwanta da suka yi wani irin sundum

Da sauri ya shiga bin kafafuwan da kallo har Allah ya saukar da dubansa a wajen da ya ga wasu yan kannanun kofofi biyu da suke shige da yan tiloli kananu sosai

A hankali ya kara kurewa wajen da kallo nan ya fahimci san hakori ne na macijin da ya yi sara, sara kuwa irin ta kokowa

A hankali ya kara dukawa, bai taba daidai wajen ba sai kara kusanta dubansa da ya yi sosai da sosai, sam ba alamun rai a tatare da ita aman bai yi gagawar sarewa ba har sai da idannuwansa suka sauka a irin yannayin kofar

Da wani irin sauri ya mike ya yi wajen jakar nan da ya dauko daga daki ya ajiyeta ya budeta

Adu'a yake a kasan zuciyarsa Allah ya sa saran bai kai tsayin minti arba'in da biyar ba, sara be na maciji mai kala biyu, iein macijin nan mai kalar ash color da baki, irinsa ke dauke da hakora daya ya fi daya girma, hakoran daya ya dan fi daya tsayi , mai tsayin shike da tsini, wanda bashi da tsayin kuwa shine mai kakauran waje
Hakan ke sakawa ana iya gane cizonsu idan aka ga yar karamar kofofin daya ta dan fi daya girma, sannan idan ya yi sara yakan sumar da mutun ne, summa mai tsananin dake nuna tamkar mutun ya mutu ne, sai dai a hankali mutun ke kara nisa, idan har aka dauki lokacin nan ba'a yi gagawar tsayar da dafin ba, ko aka sadaka da asibiti suka yi gagawar yi maka nasu dabarun ba lalle kana iya rasa ranka

Wata aska ce ya ciro mai kaifin balaki sannan yar siririya ce

Bai tsaya wata wata ba ya kamo kafar nan wajen gwabrinta ya daidaita askar nan tun daga gaban saran ya shiga yin baya baya da shi yana kara sauka

Wani irin bakin jiki ne ke fitowa mai tsarara, har ya kai wajen da normal color din jinni ta fito sannan cikin wani saurin ya kuma huda dayar kofar har ya kai wajen da ya tsaya shima inda kamar yanda suke da bambanci haka yannayin yaduwarsu take a jikin dan adam

Buda wata kwalba ya yi mai dauke da alcohol na asibiti ya dauki auduga da sauri sauri ya zuba alcohol din nan wanda hakan ya saka baki daya wajen ya shiga wani bori tamkar ana kone wajen kafin ya lafa sai wajen ya yi fari fat har ana gannin dan nama naman wajen hakan na nufin wajen ya wanku tas tas tas kennan

Bai yi kasa da gwuiwa ba ya saka audugar nan ya ringa wanke wajen da wanki na kirki wanda ke darzar wajen sosai

A hankali ya dago ya sauke dubansa a kan mahaifiyarsa, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" inaga kukan nan bana son sa"

Da sauri ta kuma duban fuskarsa, aman sai ta mayar da kanta kasa sakamakon tsagwaron bacin rai da ta hanga a tatare da shi

Shigowar iyayensa ya saka shi lumshe ido, dama ya san a rina domin ta wajenta suka bi kafin a karaso da su nan, harda Abih da UMMU

Baki dayansu son su san abinda ke faruwa suke, shi dai shirun da ya yi kallon agogo yake yana kiyasta iya adadin lokacin da ya ci ace jikinta ya fara daukan dumi ya rage sanyin nan kau kamar gawa

NAJEEBA dake tsaye sai a lokacin idannuwanta suka gane mata lale da gasken NADIA ce

Baki daya sai ta ji ta kasa iya rike kanta, a hankali ta silale daga inda take a tsayen nan ta zauna saman cafet din kamar yanda baki daya mutanen falon suke ciki kuwa harda SUKTAN da ya zauna a kasan shima dan ya dubata da kyau

Abih ne da yannayi na tashin hankali ya ce" SHAHEED mu kaita asibiti mana? Menene ya sameta? Meye wannan akai kamar an yanka ne? Me ke faruwa ne?"

Sai da SHAHEED ya dauki kamar minti uku yana mai ci gaba da dan taba yannayin jikinta da yake jin kamar yana cenzawa kamar kuma baya cenzawa sannan ya kalli ABIH, A sanyaye ya ce" wannan din shi ne treatment din da zasu yi mata ko kun je, ku mu saurara kadan, idan har da sauran numfashinta zata farka"

Ai Najeeba na jin haka sai ta fashe da wani kuka kasa kasa tana mai dora hannayenta saman kanta hankalinta tashe da jin kalaman SULTAN, me? Aida? Me ya same ta? Wani irin treatment ne wannan ya yi mata? Bakin jinnin nan na meye? Me ke faruwa ne da gidan nan da shi kansa SULTAN?

Ammi da ta fi kusa da ita ne ta kamo hannunta irin ta karaso jikinta

A hankali ta jarasa ta zauna a karkace ta dora kanta a gefen jikin Ammi, tana mai fitar da wani marayan kukan da ya saka cike da tausayawa, sannan jin irin yanda jikinta itana ya dauki zafi ta ringa dan taping din bayanta dan ta samu ta yi shiru, domin kuwa a irin yanda ya hade ran nan su kansu sun yi shirun ne sunna masu adu'ar Allah ya sa ta tashin

Cen kamar minti goma sha uku sai kofofin fatar jikinta suka fara fitar da alamu da mutun mai rai ta hanyar fara fitar da zufa
A hankali jikin nata ya ringa rage yannayi na sandadan din da fatar matace ke dauka ya fara dan rage sanyin da ya dauka sai dai sam bai dauki dumi irin na fatar yawancin mutane masu lafia ba hakan ya saka shi kai dubansa wajen mahaifiyarta, cikin nutsuwa ya furta" idan tana cikin halin rashin lafia takan yi nawa temperature din fatarta?"

Mamanta cikin shakakiyar muryar wace ta ci kuka ta koshi ta ce" bai taba haura 38 ba, domin ita din sam jikinta baya daukan zafi koda kuwa bata da lafia"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta" da ranta, zata farfado in sha Allah dafin bai ratsata sosai ba"
Dubansa ya kuma kaiwa a karro na shida kan NAJEEBA, ajiyar zuciya ya sauke a karro na ba adadi kafin ya mike yana dubansu kasa kasa ya ce" to ki daina kukan mana?"

Su duka shi suka kalla kafin kuma su kalli inda yake kallon, Njaeeba ce ke ta shashekar kukanta, baki daya abin ne ya zo mata a lokacin da bata tsamata ba, tarin tsoro ya sakata neman sikewa da tuna Bintu

Bai kuma kara wani lokacin ba ya juya ya fice a fallon

Wannan karron ta babar kofarsa ya fita da kansa

Tsayuwa ya yi yana bin gidan da kallo

Muryarsa dake ya kai dubansa kan sarkin zabga, liman, amintacensa, sarkin kofa, da du wani dogarin da ya kwana ya waye a fadar dake tare bisa umarninsa, inda ya saka aka zubo masa polisai suka hau wajen aiyukan ma'aikatansa kafin ya gama abinda zai yi

Ya yi kai kawo kamar sau hudu wajen nan yana kallon du wani wanda ke wajen kansa a kasa

Sai da ya ja ya tsaya ya furta" kowa ya dago kansa ya kalle ni "

Baki dayansu mamaki, tsoro, da al'ajabin a dago kai a dube shi ya dirar masu, wani irin su dago su dube shi? "

Gannin du sun kasa ya yi wani murmushin yake a karro na biyu ya furta" umarni nake baku "

Ai kuwa baki dayansu sai sauka ringa dago kawunnan nasu, sai dai da wani irin sauri suke sada dubans7 sakamakon arba da ainahin fuskarsa a bayane, rawanin ya mayar da shi iya kansa, baki daya kamanin mazan da suke hasashe ya bayana a gabansu, irin yanda suke hasashen daurewa irin na sarkinsu sai abin ya dame tunaninsu ya shanye hakan ya saka da yawansu jikinsu kwasar rawa sai daidaikum da suka kasance jaruman jarumai ne suka sada kawunnansu hankalinsu sam ba a jikinsu ba, baki dayansu sunna cikin fargaba da wannan lamarin da bai taba faruwa ba

Affuwa dai Takawa, Allah ya huci zuciyar MAI DAMAGARAM, ALLAH ya sasauta fushin JIMINA, Allah ya huci zuciyar SARKINMU.......Amintace ya fada yana kara sada kansa cike da biyaya

SHAHEED ya budi bakinsa a sanyaye ya furta " Menen laifin su da ake son daga na kawo su a ringa binsu ana kashewa tamkar kiyashi? Shin daukar fansa ne ko kwacen kujera ne? Menene ribar biyowa ta bayan fage bayan ni ake son kuntatawa gani a bagas ba zan iya yin komai ba ana iya koda gile kaina ne domin nima mutun ne kamar kowa, sai dai maimakun mai aikatawar ya biyo kai tsaye sai yake lungu lungu da ni yana cutar da y'ayan mutanen da basu ji ba basu gani ba"

Dan sasautawa ya yi gannin da yawansu basu san inda zancen ya nufa ba, hakan ya sa sukai sakayau da su, a cikinsu kuwa akoy wa'inda suka san inda zancen ya nufa suma sai kara yi suke irin zancen basu gane inda ya nufa ba

A hankali ya dora da fadin " baka jin tsoron Allah ne? Baka tuna akoy ranar tsayuwa ne? Wa'innan da kake kashewa dan son zuciyarka baka tsoron irin huja da hisabin da Allah zai wanzar a kanka a gobe kiyama ne, ko kai zuciyarka ta kekyashe ka zabi duniyar ne wace baka san iya adadin wa'adin da ya rage maka ka cika ba? Shin idanma Allah ya ara maka nisan kwanan ka tabata ita duniyar da kake tunanin yi domintan zaka samu abinda kake son samun ne? Idan *MACE CE?*, idan *LAFIA* ce, ko tunanin mulkin da Allah ya nada bawansa bai cencenta ba dan kannanun shekarunsa ne? Ko wani lamari naka na kanka da ka barawa zuciyarka?, shin ana anfani da damar da aka sani a kaina cewa ko jama'ar garina da inada hali da na hanna masu saka laya a cikin kasata ne ake son kasara min tunanina ta hanyar kashe min iyalaina?"

*ALLAH ya huci zuciyar maza* aka ringa maimaitawa, kowane na tsarge da dan uwansa, sannan magangannun Sultan karara sun fito fili

SHAHEED ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da hucin bacin rai yana ayanna irin hukuncin da koma wate ya dace da shi ya ce " Ba zan saka alkur'ani mai girma dan samun mai yi min zafon kasa ba, sai dai ina mai shaida masa mumunan labarin cewa ya mayar da rigarsa ta zuwa makabarta dan birne Gimbiya NADIA bisa abinda ta jiyo, domin kuwa bata mutu ba, da ranta "

Du yawanci mutanen wajen ne suka dago kawunnansu a firgice, mutuwa? Da yawansu tsananin mamaki da tsoron furucinsa ne ya saka masu dagowar nan, cikinsu kuwa mugun da ya aikata ne ya dago a firgice shima da jun wannan lamari, bata mutu ba? Tana ina? Da ranta? Me ta ce? Yaya aka yi bata mutu ba?"


"Yaya wanda ya aikata aikin nan zai min daukan wawan da ban san abinda nake yi ba? Harma ya yi tunanin a lokacin da na wanki gawar matata da kaina na suturtata aka kaita ba zan lura da saran macijin da ya kasheta ba, ko kuwa ya yi tunanin da yake ni din wawa ne zan iyakance binkicena a kan macizai da irin hatsarinsu bayan na kasance jinni ga ABDUL MALIK ALI BUZU BA?, shin kun manta sanadiyar sararsa da maciji ya yi a filin daga ya saka shi zuba kiwonsu har sai da ya lakanci raba gangar jikinsu da hakoransu kafin ya iya fitar da karinsu, ya san yanda ake magance dafinsu idan bai gama shiga jiki ba, ya iya bin rawarsu har kuke tunanin zai iyakance sanninsa a kaina ni SULTAN SHAHEED?" ya karasshe da dan daga muryarsa sannan a kausashe ya kaiwa garun da yake tsaye suka mai karfin gaske sannan ya maido dunkulelen hannun nasa ya daki gefen kirjinsa ya ce" lungu lungu camera ce biyayiya a gidan wada ba kowa ya san da ita ba, sakwani tsakiyar dare, kulawa da kuncewa baki daya a tafin hannayena suke, droon kadai kuka san da shi a tunaninku shine kawai zai ringa aiki idan safiya ta yi ina zaune na ringa bi da shi yana dauko min rahitanni kamar wani gaula?"

Dan murmushin takaici ya kuma yi a hankali ya furta" kunna iya tafia "

Ba wanda ya iya koda kwakwaran motsi ne a cikibsu, shi kuwa a tsayen nan da yake idannuwansa kyam a kan mutun biyu da suka yawaita haduwa da junnansu a cikin masarautar idan dare ya raba, wa'inda yake gannin haduwarsu lokaci zuwa lokaci

Shi ne ya fara juyawa, lokaci daya suka kwashi kirari hade da neman afuwarsa, basu su yi shiru ba har sai da ya shige baban falonsa

Idannuwansa ne suka sauka a kan ZINARIA da ya aika kiranta

Bai yi komai ba sai karasawa da ya yi wajen wayar cikin fada ya yi kiran comandan din da aka ajiye yake jan ragamar bada tsaro wa gidan

A kausashe ya ce" ko karamin yaro ne kar ku bashi damar fita daga kowace hanya, ku zuba ido ku yi taka tsantsan dimin na zunguri wanda ya aikata, kuma ya san da shi nake daga yanzu zuwa dare komai na iya faruwa ciki kuwa harda barazana fadawa"

A dake shima ya amsa kafin ya kuma zagewa ya kara tada jinnin ma'aikatansa ya gingindaya sharudan cewa ko mace ko namiji ko yaro ko tsoho ko a halin rashin lafia ko a halin hauka ko a mace kar a fita fa kowa daga masarautar DAMAGARAM!

Ajiye wayar ya yi ya kuma juyowa gare su

A hankali ya karasa ya zauna

Gannin numfashinta ya dawo, hasalima baci take yi mai nauyin gaske wanda daga shi ne komai zai saketa ta farka ya maido dubansa wajen AMMI da ta aiko masa da tambayar da ya zama wajibi ya amsata

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" EH ba'a rufe wajen, haka ake barinsa ya bushe dan kansa ko ruwa ba zai taba wajen ba.
Dan shiru ya yi na dan lokaci kafin ya dora da fadin " Ba'a taba raba gidan sarauta da abubuwan tashin hankali, zagon kasa, munafurci, hade hade, fitintinnu, rigingimu, da dai saransu, ciki kuwa harda kisa,
Wanin kan tsinci kansa ne a wajen da bai dace da shi ba, wanin kuwa yakan kawo kansa wajen ne dan a ganninsa ai nashi da wani waje da ya fi nan din, dama dan irin rayuwar aka haife shi.

Dubansa ya kai wajen UMMU dake rungume da NADIA, zuwa yanzun sun rage mata nauyin suturar dake jikinta sosai dan ta sha iska, hakama ya kai kan AMMI dake rungume da NAJEEBA wace du ta makalkaleta idannuwanta lumshe tana kwonce a samanta sosai sai ajiyar zuciya kawai take saki,
Sannan ya kai kan Zinaria, sai ya ga sam ba wani yannayi na damuwa ko alhinin gannin yar uwarta kwonce sheme sheme a halin rai ko mutuwa, hasalima dan girgiza kai take irin idan mace na cikin neman balakin nan

Ya kuma saukewa a kan iyayen Nadiar, mahaifiyarta na kusa da bayanta, tana rike da hannunta cike da yannayi na tashin hankali, mahaifinta kuwa kansa a kasa ya dan dafe kai malunmalun din jikinsa a dan tatare, hularsa ta yi gaban goshinsa kadan.

A hankali ya ce" AMMI, kwanaki an kashe Bintu ta hanyar saran maciji, shine a yau ya sari kafar Nadia,
Dan sasautawa ya yi ya sada kansa a hankali ya furta" Ina cikin zargin mutun biyu ne, duda na san cewa zato zunubi ne sai dai na fada a wannan zaton ne bisa hujojina, mutanen nan kuwa sune *Amintacena da kuma sarkin Bulala*, kara sada kansa ya yi kafin ya dago ya sauke idannuwansa a kan Zinaria ya ci gaba da fadin" faduwar gaban kar a je da iyalina a ciki ya hanna min gannin amsoshina a fili, sai nake ta zagayewa ido rufe sai na samo hujojin dake hada matata da shi, koda kuwa ya kasance tsoron saurayinta, koda kuwa ya kasance bawa a gareta a yanzun, aman kiri da muzu na kasa samun kakarfan dalilin da zai iya hadata da shi a talatainin dare a wajaje uku, harda mahaifiyarta,, me suke fada? Me suke amsa? Me suke aiwatarwa? Meye tsakaninsu da shi? Shin kishi ne ya rufewa iyalina ido har ta kaita haka ko son zuciya, ko kuwa ramuwar na shiga tsakanin soyaya da soyaya ne? "
Ya karashe yana mai kara son dole ta dago idannuwanta da ta shiga wuwurgawa a tsorace dukan alamun rashin gaskiya ya gama bayana a tare da ita , wanda hakan ya sakata inda inda harma ta dauki magana a firgice cewar " Ni dai ba abinda na aikata "

Idannuwansa ya rintse sannan ya bude ya kalleta, hakama dukan mutanen wajen,, a takure a birkice , a wahalce ya ce" Shin na kama sunna a furucina ne a nan? "

Gannin ta sada kai baki daya jikinta ya kwashi rawa sai kawai ya mike tsaye, ransa bace ya shiga kai kawo

Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce"




=ØÞ
[3/31, 11:30 PM] BAK'A CE: >ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



56



Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce" shin kin aikata abinda zai sakani a cikin halin tashin hankali, kunya, matsanancin bacin rai? "

Kuma dago dubanta ta yi, baki daya jikinta bari yake ta rasa ina zata kalla, gani take ko'ina na dakin ya zama idannuwa ne, baki daya ta ringa gannin tamkar an tsatsarata a gaban alkali ne, duda kasancewarsa miju a gareta wanda ta yi rayuwar shekara da shekaru da shi aman sai ta tsinci kanta da kasa kallonsa sai tsabar tsoronsa da ya rufeta ta shiga barin jiki baki daya

Kai ya dan juya a hankali ya juyo dubansa kanta a lokacin da ya rage tsayinsa

Da dan karfi, zuwa lokacin muryarsa ta fara amayar da tsarin dake cikin zuciyarsa, tamkar zai hadiyeta danya dan bacin rai ya ce" Zaki budi baki ki bani amsa ko sai na aiwatar da abinda zai tayar da hankalin kowa a nan? "

Da sauri AMMI ta dora hannunta na dama ta saman kan NAJEEBA da ta cusa kanta cikin jikinta sakamakon irin yanda amon muryarsa ya yi mata rashin dadi a cikin kunnayenta

AMMI na shirin yin magana suka ringa jin maganar Nadia a firgice sannan muryarta a shake, sai ta shiga dan harbe harbe irin zata tare wani abin sannan ta kwala razananen ihun da ya saka baki daya akayi kanta

Ido rufe take fadin" kar ya sare ni, ka dauke min shi zai sare ni, walahi ba wanda zan fadawa, tsoron maciji nake ka kama shi yana lauye min kafata innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wayo Allahna, wayo zai kashe ni "

A rikice mamanta ke ta girgiza hannunta dake cikin nata tana kama sunnanta sai dai kamar bata san ana yi ba

Da sauri ya duko da wani abu a cikin kofin glass da ya jika ya dan yi gyaran murya hakan ya sa UMMU bashi damar kama kanta

Bakinta ya gumtse da hannunsa sannan ya dura mata abin nan ta hancinta hakan ya saka baki dayanta ta yi wani irin tasowa a gigice sannan ta koma ta zube ta shiga amai ta hanci ta baki
Lokaci daya kuma idannuwanta suka bude jajajir da su tana ta zubar da hawayen wahala baki daya jikinta rawa yake tana bin dakin da mutanen dake wajen da kallo

Wani irin kuka ne Zinaria ta fashe da shi gannin Nadia ta tashi,
Ba wanda ya kula domin Nadiar du aka fi baiwa hankali wace gaba daya jikinta na rawa sannan ba karfi ta shiga fadin" Ban fada ba ko? Bai bari ya sare ni ba ko? Ba zan tona asirin ba kar ya kashe ni dan Allah "

Najeeba dake kallonta tana jin hawaye na ziraro mata daga gurbin idannuwanta zuciyarta cike da tausayinta, ta san za'a rina ne irin tsoron NADIA bare wannan abin ita kanta ta tsorata, ba zata manta ranar da ta ganshi yana ta damukar maciji ba, sai kawai ta shiga tsoron ko dai shima macijin ne?

Sai da ya yi iya yinsa sannan ya dan sasauta muryarsa ya shiga kiran sunnanta

Kanta take girgizawa tana maimaita ba zata fada masa ba

Mahaifiyarta ce ta kama hannunta ta rike a cikin nata da kyau ta ce" Nadia, kale ni, na zo, na zo fa, ba na fada maki zan zo ba? Kin ganni ni ce, fada min meye? Me kika gani, me ake fada? Idan har kika ci gaba da boyewa kin san da sannin ba barinki zai yi ba, domin kuwa ba zai taba yarda cewar kin rufe masa asirinsa ne, zai dauka cewar kina son tona masa a kowani irin lokaci, ki sani da ba dan Allah ya yi kina da sauran numfashi ba da yanzun an jima da goge babinki a duniya, ki sani kafin ke an kashe wata, idan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment