Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mikarta yanzu zata rikita masa lisafi yana zamansa kalau

Kamata ya yi ta mike tsaye, kuma yanzun jikinta sam ba zafin ko daya, haka kuma bata kama da marar lafia

A kofar bayin ta ja ta tsaya tana dan tura shi irin kar ya biyota

Murmushi ya yi ya tsaya har ta rufe bayin sannan ya samu waje ya zauna yana jiran fitowarta

Shi kadai yake godewa Allah irin baiwar da ya yi masa, Nadia na dauke da ciki har na sati uku , ta fara rashin lafia ne sosai yau har AMMI aka fadawa shine ta kiraye shi ya yi kiran likitar dake duba matansa ta zo ta dauki jinninta da fitsarinta ta koma, har ta dawo ta kawo result shine ya dakatar da ita cewa ta baiwa Najeeba maganin zazabin dare, s nan ne AMMI ta yi nuni da kar a bata ba'ai mata gwaji ba tukuna, domin ita dai ta san abinda take ganni a jikin Najeebar gashi ba kowani magani ba mai ciki ke iya sha ba

Yana nan zaune ya jima sosai kafin take fitowa daure da tawul a kirjinta

Cikin nutsuwa take kokarin karasawa wajen kayan salarta da abin sallah

Duka yana kallonta har ta idasa sallar sannan ya kurawa fuskarta ido da ta yiwa takwaf takwaf tana karasowa inda yake zaune

Sai da ta dare kan cinyoyinsa sannan ta sarkafo hannayenta a wajen wuyansa ta shiga zuba shagwaba tana kara tabe dan bakinta ta ce" Ni kiwuyar zuwa falon AMKI nake yanzun "

Murmushi ya yi yana kallon yanda take yiwa fuskarta a hankali ya ce" Ni kuwa bana tunanin zan iya katabus jin kin jima kina kwana da zafin jiki "

Kara langewa ta yi a kirjinsa ta ki cewa komai sai dan kukan shagwaba da take tana kara shiga jikinsa

Idannuwansa ya lumshe, a yanzun ya fara tunanin yarnan zata zauta shi ne idan ya yi da wasa fa

A hankali ya mike da ita a jikinsa ya shiga takawa yana mai kara gyara rikonta a jikinsa

Idannuwanta lumshe tana shakar dadadan kanshin turaran dake fita a wuyanta har ta ji tsittt kamar hayaniya ta dauke

Da sauri ta dago dubanta, ba shiri ta dirko daga jikinsa tana zazare ido gannin yayunta da kanwarta zazsune kawunnansu a kasa, wata datijuwa a gefen AMMI itama kanta a kasa, sai AMMI da ta kawar da dubanta kamar ba abinda ta gani zuciyarta kuwa wani irin mamakin SHAHEED din ne ke neman halakata, a da takan aunawa a ranta cewa shi din bai yi halayen mahaifinsa ba na kulawa da mace, aman a yanzu sai ta karyata wancen tunanin

Cike da mamakinsa ta kale shi , bakinsa ya dan tabe ya kama hannunta ya ce" Mu je mana "

Da sauri ta juya cike da wata irin kunya ta koma hanyar da ya biyo da su, ita ta yi nisan kiwo a sinsinar wuyansa ashe har ya kawo kofar bata sani ba har ya bude ya shigo da ita a haka tana nanakarsa ita kam me zata cewa yan uwanta da ta gama kurantawa bata son sa, da wani ido zata kalli AMMI ta ganta kwonce rashe rashe a jikinsa

"BEEBAH, wai ina zaki je ne haka?" Ya fada yana saurin cin mata dan da gudu ta fala

Birki ta ja ta ci a lokacin da ta saka kanta cikin dakin ta juyo tana dago hannayenta ta ce" Fisabililahi SHAHEED ka san su AMMI na zazaune da su Aunty Ummu ka shiga da ni a nanuke da kai salon su ce da ni munafuka, AMMI kuma ta yi tunanin na zama marar kunya? "

Irin yanda take bayanin tana nunawa tana yawo ta kasa tsayawa waje daya hannayenta a sama ya bashi daria sosai, sai abinda ya kara birge shi gannin fada ake masa yau kuma, ikon Allah kala daban daban a wajen yarinyar AMMi, sai kawai ya hade bayansa da garun wajen ya harde kafarsa sannan ya dage mata girarsa ya kane mata ido daya ya ce" Zo nan "

NAJEEBA ta yi sakalo tana kallon yanda ya yi da fuskar tasa, sannan ta kai dubanta wajen da ya nuna ya kuma daure gida

A hankali ta karasa ta tsaya ta sada kanta, hakan ya kara bashi daria, wai kunya ta ji ko me? Lalema

"Mu je a duba min ke" ya fada yana kallon fuskarta

Tana murza yan hannayenta a hankali ta ce" Dama lafiata kalau nakan yi masasarar dare wani lokacin "

Kansa ya girgiza ya ce" Bana so kina rashin lafia "

Dago da dara daran idannuwanta ta yi tana kallonsa, cikin nutsuwa ta idasa jikinsa tana mai dora kanta a saman kirjinsa, muryarta ciki ciki ta ce" Ni allurar cema bana so a rayuwata, ka barni haka na tuba "

Du idan ta kusanta jikinta da nasa sai ya ji kamar zai tsere domin abin bambarakwai yake zuwar masa, bai saba ba ko kadan bai saba ba ko Nadia bata shiga jikinsa, takan sada kanta a gabansa dai sannan takan damuwa da cin sa ko shan sa, ama Najeeba ta mayar da shigewa cikin jikinsa aikin yinta

Hannun nasa na dama ya dora a bayanta, a sanyaye ya furta" Ki ce kina so na BEEBAH? "

Shiru ta yi na lokaci kankani, hakan ya sa kirjinsa ya yi ta bugawa harma yannayin ya so ya dagule masa

Yar karamar wayarsa ce ta dauki tsuwa , yana dubawa ya san AMMI ce ya daga

Bayan ta yi magana a hankali ya furta" AMMI ta tafi, bata son allura "

Ammi da ta yi zaman son gannin irin farin cikin da zai nuna itama idan aka tabatar mata irin farin cikin da zata ji sai ta yi turus da maganar da ta dauko ta ce" Shaheed, ka kawo kin ita nan, ko ta tsaya yanzu yanzu ana kawo mata abin fitsari maza ta yi a kawo min "

Bai saka komai a ransa ba sai tsayuwar da ya ci gaba da yi da ita a jikinsa har kunnayensa suka tsinkayo masa tafia kafin ya ji an tsaya

Bai bude idannuwan nasa ba ya furta" Bani "

Ummulkhair da ta juya da sauri ta juyo har jikinta na rawa ta duka ta miko masa robar da aka bata ta kawo

Najeeba kuwa sai ta kara boye fuskarta a kirjinsa ta kasa dagowa dan tana jin kunyar Ummulkhair da kuma irin abinda ta tabata zasu yi mata idan sun hade

A hankali ya kuma shiga da ita yana janta a jikinsa har suka dangana da bayi

Sunna shiga ya shiga son cire doguwar rigar dake jikinta ta sallah
Bata iya yi masa musu ba har sai da ya cireta baki daya kamar wata wada zai yiwa wanka, ya mika mata abin muryarsa ciki ciki ya furta" Ki yi ki bani "

Da bakinta ta ringa mutsu mutsu tana tunanin kuma a gabanka zan yi?

Tsumamun idannuwansa da suka cenza kala dan rashin samun amsa daga gareta ne ya kura zuba mata hade da kakausan kallo

A hankali ta juya ta nufi wajen WC

Ta haka ta yi tabara ta zuba fitsarin ta cire hannunta kanta a kasa ta dago hannunta tana mika masa

Idannuwansa a kanta har ya amsa sannan ya juya ya fita

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana cije lebenta na kasa tana shafa mararta tana jin irin fitsarin da take yanzu mai yawan gaske ne ya fi na da yawa, sannan idan tana yinsa har ji take mararta ta yi mata sakayau sannan ta dan kwashi dumi
A hankali take huci mai hade da tsantsar kaunar bawan Allahn nan
Acting dinsa na tsaye mata a zuciya, irin yanda baya kyankyaminta na halaka tunaninta

Ta jima a cikin bayin wannan karronma domin tunani ne ya yi gaba da ita har sai da ta ji ta kage a zaunen da take sannan ta janyo ruwa masu dumi sosai ta kimtsa jikinta ta sake yin wanka ta ja rigarta da tawul ta fito

Du a tunaninta ya jima da barin dakin domin a kadan ta dauki minti talatin a bayin nan fa, sai dai yana tsaye ne jikin bango kansa a kasa yana tunani, kwata kwata yarinyar ta iya dauke natsuwarsa da kwonciyar hankalinsa, bai san ta yada zai kwatanta irin yanda take tafia da shi ba, bai san ta inda zai bi ya samu ta furta masa kalmar nan ba, du ji yake komai nasa ragage ne, yaya zai yi ta yafe shi? Shin bata son sa? Me ya rasa ne? Kar dai har yanzun wancen din ne a ranta? Kar dai du wannan bata lokaci da falasa akwatin sirrinsa da ya yi mata ita din a banza take kallonsa?

Hannunta mai danshi ne ya taba damatsunnansa masu cika,
A hankali ya dakata yana kallonta

Dan murmushi ta yi a sanyaye ta ce" Me ke damunka? "

Bai bata amsa ba, sai hannayen nata dake rike da damtsensa, dayan kuwa na rike da tawul din da ta dauro da ya kurawa ido

Sannu a hankali ta ce" Ina missing din buga basket, zaka je terrain mu je mu buga kwalo? "

Leben nata yake kallo har ya saka hannu ya janyota gaba dayanta jikinsa
Kyakyawar runguma ya bata kafin ya shiga aika mata da zazafan sako wa'inda suka saka jikinta ya dauki rawa idannuwanta suke marmarmar kamar zata side dan azabar shaukin da ya dauketa
Ihu ne kawai bata yi na, tana rike da kansa idannuwanta rintse hakama lebenta dantse

Dif ya yi sakamakon kiran da ake ana karawa, kuma kukan kiran AMMI ne

Da sauri ya laluba idannuwansa na rufewa yana bude su da kyar dan jarabar dake cinsa ya daga kiran aman ya kasa yin magana domin komai ya ki fitowa daga bakinsa

A hankali ya saki wayar sakamakon wani irin abu da ya tsirga masa tun daga kansa har kafarsa sanadiyar abinda AMMI ta fada tana ta daria tana ambaton Alhamdulilah Alhamdulilah

Cikinta dake shafe ya kurawa ido, da duba irin na tsanaki,
A hankali ya yi sama da dubansa har zuwa fuskarta,

Sannu sannu ya mayar da ita saman bed din ya kwontar da ita
Kasa ya yi sosai nd verry slowly ya dora jajayen lebunansa a saman mararta
A hankali ya ciro harshensa mai dumi ya ringa lasar marar tata, hakan ya sakata rintse ido da karfi ta rike kansa tana jin jikinta na kara dauka

Bai bari ba har sai da ya ji zata sume tana fadin" wayo Shaheed ka bari wayo wani yamyamyam ake min "

Cikin gagawa ya ringa ruda mata jikinta, da kyar bakinsa ke kwacewa yana fadin" tell me you love me , kiss me baby, please lv me hearty "

Rukunkume shi ta yi hawayen shauki na zirara daga gurbin idannuwanta muryarta na rawa ta ringa furta kalaman a rarabe " *i..........l................o........v.......e............JJJJJJJJJJJJJJJSHAHHHHHHHHHHHAD* "

Kamar ky din kara kunce dokin jikinsa ne, sai da ya zabura baki dayansa ya saki hanniniya sannan ya ringa tafiar da su cikin salama idannuwansa na zubar da wasu irin tsadadun hawaye masu yawa da shauki, tamkar zai hadiyeta, ba tare da ya ji mata rauni ba yake nuna mata wata irin soyayar da ita kanta ta saki sansanya kuka mai ratsa zuciya tana rungume shi a jikinta, ta yi sadaranda ta zubar da makaman yakinta, ta yarda Allah shi ke dasa so a zuciyar bawa a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yau gata ta zubar da komai a gaban dan fari mai mata mai sarauta, yau gata ta gane dan Namiji na saraki ba zai hanna masa nunawa matarsa soyaya da bata kulawa ba, a hankali ta ringa kara yarda da shi harma ta buda idannuwanta ta sauke a kyakyawar fuskarsa mai saje a lokacin da yake tatareta yana mai furta" Ki bi min a sannu kar ki sauka da karfi, dan Allah ki hau bayana na goya ki na kaiki falon mana to waina Sapni Suhani din nan a wace tasha ne ake yinta, ni banma san akoy tashar ko babu ba dan bana iya rabona da kallon TV BEEBAAH"

Najeeba ta sauke ajiyar zuciya ta daidaita ta haye bayansa, ya mike da ita tamkar wata yar baby ya karasa falo da ita a jikinta gajeran wandonsa ne sabo da farar rigarsa, ta kame gashin kanta ta soke da macajin kansa

Tana bin dukan motsinsa ne har ya gama hada TV din dake makale a bango wace rabonsa da kunnata har ya manta, kai shi mantawa yake akoy TV a duniya, ko labaru yakan dubawa ne ta yanar gizo

Zama ya yi bayan ya dauko masu abinci ya sakata jikinsa da spoon yana ciyar da ita tana ciyar da shi cike da farin ciki da kwojciyar hankali sannan sunna kallon series din na indiyawa wato YOUNG LADY (SISINA GATA FA MUTUNIYAR TAKI) cikin shauki

............................................

Alhamdulilah maganar auren Yaya Dayabu ta kankama, an gama komai rana kawai ake jira wace aka tsayar nan da wata biyu da sati biyu domin mahaifiyar amaryar ce ba lafia an fitar da ita waje

Zuwa lokacin cikin dake jikin matan Shaheed ya gama fitowa ya girma ya idasa bayana kansa, domin na Najeeba watansa takwas da sati uku
Na Nadia kuwa watansa bakwai da sati hudu
Rayuwar zamantakewar dake gudana tsakanin Nafia da NAJEEBA zan iya kiranta tsaftataciya, akoy kishi a tsakaninsu, sai dai tsaftatace, kishin yan gayu wato kishin cikin daka wanda kowace burinta fuskar mijinta, idan kuwa suka hadu sukan sha hira harda wasa da daria da matsanancin kulawa da damuwar dan uwa idan har damuwar ta bayana a fili
Idan wani abu ake a familly dinsu Nadia duda baya son fitar Najeebar yakan kaita da dare da kansa a cikin motarsa, ta shiga ta yi barka ko jaje sannan su ja su yi wajen hutunsu, wajen da a da sukan hadu ne dan su yi fada, harma su buga basket ball wanda yake bin takunta a hankali yana tareta dan kar ta fadi takan yi sport dai amta haka kafin su biyo wajen mai kilishinta su siya sannan su shiga ta boyayiyar hanyar da sarkin Dogarai ya saka aka fasa yake gadinta da kansa idan SULTAN zai fita har ya dawo

A gidan Abih ana zama ne na fahimtar junna, hakuri da junna, juriya da tarbiyar y'aya, dan kuwa Nana Maryama wato UMMU ta zame masu uwa, wace haihuwarsu ce kawai bata yi ba aman dukan wata dawainiya da su dariarsu ko kukansu a kafadunta suke zube su, inda mijinta ya zame masu uba tsayaye, mai basu kulawa ta musaman, mai gindaya doka a wajen da ya dace sannan baya tashi a kanta, mai saka ido sosai a kan tarbiyarsu, mai dafawa matarsa yana bata gudunmuwa a dukan abinda ta yanke masu na zaman rayuwa, hakan ya sa su dukansu suke tafe da rayuwarsu bisa aminci, kulawa da junna, ladabi da biyaya a tsakanin junna, sannan ko yanzu idan ka yarda ka taba daya a familly dinsu to fa ka janyowa kanka rigima ne da ahalin gidan MUTALAB......sannan a yanzu fadan ya cenza salo ne maimakun daga kan DAYABU sai ya faro daga kan MUTALAB ya zarto kan NANA MARYAMA ya dire kan NAJEEB!

...........................................

Masarautar Agadez

Wahalar da suka sha ta tsayin wata biyar biyar kowace a gidansu a karkashin ikon wanda ya isa da su ta saka sukai sanyi tamkar kazar da ta sha dukan ruwan sama

Sun yi sototo da su harma suke labewa a lokacin da aka fitar da su aka gabatar da su suka dawo mutane sak kamar kowa
Sarkin garin agadez ya yi duka da kyakyawar bulala ya gindaya rantsuwar cewa ba zai iya dagawa du wani mai wulakanta dan adam dan kawai Allah ya bashi dama ba, ya kawo misalai da ayoyi ya fasarce kan ko musulunci ya hanna da irin alkawarin azabar da zata tabata a kan masu irin halayen Gimbiya da zinariya kafin ya sanar da gayar daurin auren Yarima da Gimbiya Ummukulsum rana daya da yaya Dayabu, hakan ya saka Gimbiya kara rintse idannuwanta domin kuwa wannan lamari har ya taba lafiarta dan a yanzu fama take da hawan jinni mai karfin gaske domin bata taba tunanin zata wayi gari ita Gimbiyar sarkin garin agadez a gidan horo a gidansu ba, hakan ya sa sunna komawa ta salami masu hidimarta dan idannuwanta ganni suke daria suke mata, sun gama rainata sun gama ganninta a wulakance a yanzun kam bata da wata daraja da fada a ji a masarautar Agadez
Inda Zinaria take kara daga mata hankali da koke koke da magiya da rokon a taimaka a mayar da ita dakinta ta tuba ba zata kuma ba

A yanzun masautar na tafia ne bisa mutunta bawa, daraja dan adam, bayin masarautar kansu sun samu inci daidai misali, domin ba zaka kiraye su da bayi ba sai dai mahidimta haka
kuma har salarry ne da su

GIMBIYA Zahrau kuwa na dauke da cikinta wata hudu abinta, inda Sarki ke nan nan da dan cikin nan yana mai bata kulawa ta musaman

___________________________

A yau ya yi wani irin baci ne mai cike da mafarkai wai ana miko masa jarirai

A lokacin da ya farka salar asubahi ne ya sauke dubansa a kan Nadia, baiwar Allah ta kara budewa ta zama wata irin rusheshiya, gashi yanzu bata samun wadatacen baci sai goshin asuba, a haka yake tashinta ta gabatar da ibadarta, mahaifiyarta ta nemi alfarmar ta koma gida ta haihu aman ya kasa bari

Da sauri ya kimtsa ya gabatar da sallarsa, kafin ya zauna ya shiga tashinta

Da kyar ta iya tashi ga nauyin jiki ga nauyin baci ya taimaka mata har zuwa bayin sannan ya dawo ya zauna da carbinsa a hannunsa yana ja

Wayarsa ya dauka ya shiga dubawa dan gannin sakwanin da ya samu

A yauma ya ci karro ne da message din Zinaria, bai duba ba ya goge shi ya ajiye wayar gefe

Sai da ya ga ta tayar da sallar sannan ya mike ya nufi bangaren AMMI dan du idan aka ce ba kwanakin Najeeba bane hankalinsa kacokam na kanta, yakan kwana ya a mafarkai wani mafarkin har da su gudu zai kaita asibiti

Tun da ya buda ya fara cin karro da yaran gidan, ga wani dadadan kanshin turaran wuta da ya daki hancinsa, sai shige da fice suke murna kwonce a kan fuskokinsu, hakan sai ya bashi mamaki domin su din ba masu tashin asusubar nan bane

A hankali ya idasa kutsawa ya shige falon, nan kunnayensu suka fara jiyo masa muryarta a sanyaye ta ce" AMMI, ba zan iya shan kunnu ba ni dai , kin ga kunnu na busa mutun haka kawai na zama katotuwa a ringa yi min daria?"

Ammi na daria ta ce" NAJEEBANA, ki taimaka ki sha kunnunki kin ga yaran nan da suke mutsu mutsu da baki, ina tsoron su yi tsotsau, idan kuwa babu ruwa za'a sha rigima a gidan nan"

Wata irin zabura ya yi har yana jin zai fadi a kas dan karasawa wajen da suke hayaniyar

Da sauri ya bayana a gabansu, gaba daya jikinsa ne ya dauki rawa harma ya rasa me zai furta a lokacin da ya ga NAJEEBA zaune saman katifa mai daukan mutun biyu gefenta sange ne irin na jarirai da wasu jajayen jarirai sunna kwonce lufff sai yan uwanta da suka zagayeta

Ammi ta ringa murmushi tana gannin yanda ya rikice ya kalleta , ya kalli yaren , ya kalli Ammi, ya kalli yan matan da du suka sada kawunnansu sunna gaishe shi

"Ammi yaushe yaushe? Ammi biyu ne? Ammi yaya aka yi ba'a kirani ba? Ammi wai da gaske ko daya daga cikin mafarkaina ne?" Ya ringa fadi bakinsa na rawa kamar zai fadi ya haye saman katifar

Salamr su Yaya Dayabu da Abih ne ya saka su juyawa
A lokacin shi kuwa ido rufe so yake ya shafa gefen fuskarta koma ya sumbaceta sai kusantarta yake tana dan kaucewa tana sada kanta

Yaya Dayabu kansa sai ga hawaye yana ciro yaran yana mikawa yan uwansa da mahaifinsu sun kasa furta wata kalma mai nauyi, sai cen yaya dayabu ya ce" AMMI, wai dama ba wahaka haihuwar? Ni kulun da tunani nake kwana, irin yanda Najeeba take da son jiki idan ta tashi haihuwa du sai mun fita hayacinmu, wai sai kawai yanzu na ga message"

Ammi da farin ciki ya kasa boyuwa a fuskarta tana daria ta ce" tun karfe daya take nakuda, shima ogan ai tun lokacin na gwada kiransa ama ba'a daga ba sai na masu uzuri kawai
Muna tsaye muna kulawa da ita har abin ya idasa kankama, walahi Allah ya bata mai sauki tunda an sauka lafia, ama ai haihuwa haihuwa ce DAYABU"

Yaya Dayabu ya ringa jejera mata sannu, shi kuwa Shaheed ya rike hannunta na dama yana kallonta, wani irin farin ciki, da madaukakiyar kaunarsu baki dayansu ya saka shi jin son ya rukunkumeta ya kwala ihun sunnansa ya yi ta murna

Karshe dai a wajen nan har Nadia a nan ta same su, inda ta ringa santin babis din maza baki dayansu masu girma da kyau kamar zata hadiye su haka take ji a cikin zuciyarta

Sun hade, sun cakule, harta da yaran sun saki jikinsu a gaban Sultan wanda ya kasa ya tsare yara a hannunsa haka kuma hannunta a hannunsa ya kasa saki sai faman murzawa yake a haka har aka zo maganar shayarwa nan ya kura mata ido cike da birbewa yana kallon yanda suke kiciniya ita da Ummulkhair

Kansa ya dan girgiza yana murmushi ya mike ya bar wajen dan a baiwa masu son shigowa barka danar shigowa domin an dakatar da su a waje





Saura daya kwalin kwal=ØÞ=ØÞ in sha Allah
[3/31, 11:36 PM] BAK'A CE: >ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



*68*


*ND*

*ND*

*ND*

*ND*

*ND*

*ND*


An sha Sunna lafia, sunnan da idan na tsaya zane dole ne mu shekare a wajen nan, harka ce ta manya, manyanma saraki dan haka ki hasaso yanda lamarin ya wakana hajiata, yara sun ci sunnan ABDALLAH da MUHAMMAD

Sunna yin sati biyu da kwana biyu auren yaya Dayabu ya rage saura sati uku Nadiama ta haihu, ta samu yaronta namiji fari tass shima kato da shi

Nan aka kuma yin wani zaman sunnan, inda baki daya Najeeba ta hargitsa taron ta hanyar shigar da take sakewa, gata jegon ya karbeka fatarta ta kara murjewa , sai kawai take baza abin kallo da kanshi idan ta gita, haka kuma a tsaye take kan kafafuwanta a kan al'amura
Uwa uba mawakiyar nan ce ta larabawa ta sake zuwa, wada a lokacin da kidan ya tashi SHAHEED sai da gabansa ya fadi da sauri ya bada umarni a kaiwa Najeeba karamar wayarsa dan ya san batama san inda tata wayar take ba

Murmushi kawai take zubawa a lokacin da take jin kashedinsa na kar ta kuskura kar ta yarda, kar ta yi gigin yin rawa

A hankali ta furta" Haba takawa, haba uban gudan Beebah......zan yi maka rawarka a daki ne zan juya maka har na kada maka kugu na yi maka rawar kalangu daga ni sai kai, na daina rawa ko dan su Abdallah "

Murmushi ne ya

Please Login or Register in order to submit comment