Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Me ya faru a masarauta?

Sai da ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa da kyar kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa ya ce" ALIYU, ya amsa kiran mahalincinsa

Da wani irin sauri ta zabura tana furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Yaushe? Ciwon ne ya tashi? Ina yake? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Sai ga hawaye a kan fuskarta
Cikin matsanancin tausayinsa take kallonsa tana nin mutuwar dan jikan nata, sai kuma lokaci daya ta ce" ina mahaifiyarsa? Ina zinariyar take ne?

Ya salam, wani rudun ta shiga sakamakon tunawa da ta yi irin yanda zinariya ke takama da yaron nan
Takan daki kirji cike da gadara ta furta wata rana itace gimbiyar masarautar nan domin ta rigaya ta haifi magaji
Koda jikin yaron ya motsa takan tirsasa shi fita ya zauna kusa da mahaifinsa wai dan ya koyi yanda ake tafiar da sharia
Akoy ranar da ta yi wata magana a gaban amarya cewa" ya dace a ringa kiran yarima da mai martaba, dan ko a yanzu ba'a iya cire rai da hawansa kujera, bale idan mahaifinsa ya yi kaira da wuri

Wannan magana ta matukar girgiza amarya harma ta kasa riketa take sanarwa Gimbiya

Hannayensa ya saka ya maidota ya zaunar da ita yana dubanta a hankali ya ce" tun wajen karfe biyu da rabi ya rasu Anmy, tana bangarenta ta yi salama da shi na yi mata kiran likita ne ta dubata domin ta fara zubar da jinni sakamakon tashin hankalin da koke koken da ta ringa yi gashi cikin bai yi kwari sosai ba

Sosai mutuwar nan ta daki Gimbiya, ta kara tsoron Allah sannan ta tausayawa mahaifiyar Aliyu da mahaifinsa
Mahaifiyarsa ya kasance tana ta kuka a fili, mahaifinsa kuwa ba wanda ya ga kukansa sai dai ya sada kai sannan ya sauke ajiyar zuciya


Nan da nan masarautar ta cika makil da jama'a, yan uwa da aminan arziki kowa da kararsa

Da wuri wuri aka kaishi makwoncinsa sannan aka shinfida tabarmi dan amsar gaisuwa inda wajen ya cika makil ana ta amsar gaisuwa

Baki daya ahalin gidan Mutalab sunna wajen rasuwar tun da sasafe

Gaba daya matan sunna bangaren Gimbiya, nan du aka taru da yake falon ba karami bane harta Zinariyar nan take da yayarta sunna zaune sai kuka take har bayan magariba sam ta ki ta kwontar da hankalinta ta bi yaron da adu.a, idannuwanta sun kasa gane mata irin suturar da Allah ya yiwa yaron nata irin yanda aka taru ana amsar gaisuwa

Lakada lakadan kafet uku ne shinfide, daya GIMBIYA ce zaune da tarin y'ayanta wato su NAJEEBA

Daya Zinaria ce da yar uwarta da abokanansu dake ta shigi da fici

Dayan kuwa idan baki sun shigo nan suke zama a amshi gaisuwa

Bangare bangaren gidajen kowa ya tara jama'arsa yana amsar gaisuwa
Sai yanke yanke ake ana sadaka, rasuwar dai taro na mamaki tamkar wani tsohon magidanci ne ya rasu

Babu wace ta koma gida, a nan bangaren suke kwana wajen Anmynsu wace ke shiga tsakaninsu su layu du su lalafe mata domin baki daya wayoyinsu ta karbe ta kashe dan ta lura wayar NAJEEBA bata daina kuka gashi ita kuwa ta jima tana son ta kasance da y'ayan nata haka

Iyayen daidaiku sun zo har masarauta sun yi gaisuwa, mahaifiyar NAJEEBA dake saudiya ta yi vidio call sai dai sam NAJEEBA ta ki amsarta, sai da Anmy suka gaisa

Yau akaiwa yarima adu'ar uku
Yau ne jama'a ta ringa ragewa tun bayan adu'ar
Kafin ake cewa azahar ta shigo kai ya kasance du sai na kusa wato na kud da kud

A yaune kuma jirgin mai martaba sarkin agadez ya sauka da abokannan tafiyarsa suka yi tataki da kansu dan zuwa gabatar da gaisuwa wa sirikinsa da kuma yarsa na rashin dansu daya cilo da sukai

An masu tarba irin ta bajinta
An sauke su a bangaren Mai martaba Sarki SHAHEED, ya sauke su tare da mutanensa na arziki su ABIH, su DAYABU, su liman Baba,
Dogarai kuwa sun cika ko'ina sai kai kawo suke sun tatare ko'ina

Cike da kamala ta mike ta kai dubanta wajen ZAHRAU, da UMMULKHAIR da UMMUKULSUM, da NAJEEBA
Cikin nutsuwa ta ce" ku tashi ku min rakiya mu gaishe da mahaifin ZINARIA

Mimikewa sukai yan matan reras , baki dayansu sanye suke da bakaken abayayoyi yan saudiya masu shegen kyau da tsari ga tsada
Wani sirrin kyau ne da y'ayan nan tamkar idan kana kallonsu kar ka daina
Bakin fatarsu irinsa ne ke wartar farar fats harma ta yi mangarin idan ta samu kalar nan ai sai yi
Ga najeeba dake anfani da roger cavalais, sannan sabululukanta na anfani tana hada kayanta ne da kanta ciki kuwa harda su kurkum da sabulun victago da zuma da su kankana da dai sauransu hakan ya saka fatarta ita kadaima sheki take tana haskawa, sai haskenta ya fi na sauran ya kasance bakin nata irin na American din nan ne mai kyan gaske

Ko yanzu da take zaman makokin bakinta baya rabo da dan jan bakin nan, hakama idannuwanta bata cire abin nan ba, gata da kallon kasa kasa sai ta lumshe idannuwan nata

Anmynsu ce gaba
Su kuwa sai sukai biyu a bayanta, biyu a bayan biyun wato sun jeru sunna wata irin tafia mai cike da kasaita idan ta ajiye kafafuwanta sai ta dauke su zahrau dake bayanta ke ajiye nasu, sannan su Najeeba su ajiye nasu

Jakadiya na tafe tana shelar fitowarsu hakan ya sa du wani bawa ko wanda Anmy ta girma ya ja ya tsaya ya sada kansa dan girmamawa ga uwar gidan marigayi sannan uwar mai martaba

Fuskarta sake take daga kanta a hankali sannan da dan murmushi tana amsa irin gaisuwar da ake ta jefo mata, da yawa cikin manyan samarin gidan sukan bi y'ayan dake bayanta da kallo, da yawa sun dauri niyar isar da sakonsu dan a kara kulla zumunci, wasun kuwa na masu kallon sha'awa da tsoro domin su din dai ba dai kyau ba sai dai masifa!
a haka har suka karasa wajen shigar

Dogaran kofar dake tsaitsaye da jakadiyoyin ne suka kwashi summa nasu kirarin da kawo mata gaisuwar da adu'ar Allah ya jikan yarima karami da fatan Allah ya jawo masu zama

Babar jakadiya, tsohuwa ce ta shiga ta duka ta sanar da isowarsu

Tana fitowa anmy ta shiga da bismillah sannan kanta a sade dan girmama sarkin garin agadez duda tana kyautata zaton ta girme shi domin shima ba wani tsoho bane

Saman kujera ta zauna kafin ta ja alkyabarta ta gyara

Baki dayansu kasa suka zazauna kusa da kafafuwan Anmy,
Tun da suka shigo ta lumshe idannuwanta sakamakon kanshin turaran nan dake matukar kasheta a duniya
Sunnan turaran *MUSKI-JAH* sakamakon jinsa da take a wajen wannan bawan Allah ya sakata nemansa a lokacin da suka fita waje a paris
A ranar baki daya tanadinta ta saka ta siyo turaran nan, tana bude shi ta ga wata yar karamar kwalba sannan ba'a cike ba dan ko rabin kwalbar bata kai ba aman kuma yakeda muguwar tsada mai rikitarwa
Daga ranar ta nemi waje ta ajiye maganar turaransa, yanzu abinda ta fi sakowa a gaba irin yanda yake saka tufafinsa
Tana son ta ji wai du suturarsa daya zata kai nawa? Ba dan komai take son gane wasu al'amura nasa ba sai dan ta gane shin gayunsa da sarautarsa na bagidaji ne ko ya waye? (Ji fa rigima)


A hankali ta dago da idannuwanta a lokacin da dogarin nan ke ta fadin" saraki sun amsa gaisuwarku jinnin MUTALAB, saraki sun ji dadin kulawarku .....
Bakinta ta tabe tana ayanna ko a ina mukai magana?

Idannuwanta ta sauke a fuskar mahaifinta wanda akaiwa sasaukan rawani
Irin yanda yake dan murza goshinsa ya sakata sakar masa murmushi domin kwarai ta fanr ya takura da rawanin nan ne
Dubanta ta maida wajen DAYABU, hararar da ya sakar mata ta sakata yi masa murmushi har hakoranta suka bayana domin ta san hararar baya wuce numbersa da wasu daga cikin samarinta zasu dama dan ta tabata zai sha kira domin akoy masu numbersa a cikinsu idan sun sha mata kai ta hada su da yayanta takan basu ba abinda ya shafeta

Kalle kallenta ya kai fuskar sarkin Gadez , a hankali ta bi wajen da ya kurawa ido
Zahrau ce ke kallon Dogarin dake ta zuba ta san tausaya masa take a cikin ranta, sai dai irin kuretan da ya yi da ido ya saka NAJEEBA sakin murmushi har tana dan dantse lebenta na kasa

Idannuwanta masu kale kale suka kaita wajen fuskarsa
Irin yanda sukai ido hudu ya sakata da saurin gaske ta sada kanta sakamakon kallon nan na tsana da ya wurga mata wanda ke sakata jin faduwar gaba da tambayar kanta shin me ta masa? Sam bata iya kallon cikin idannuwansa, dan bakinta ta murguda a kasan zuciyarta kuwa fadi take" wai shi hala dan daudu ne da yake saka kwali?

Kara bin fuskarta da ta sada ya yi da ido, lebensa dake cikin rawaninsa ya datse da hakorinsa na sama
A kasan zuciyarsa ya furta" wani rashin jin maganar kika shirya da ya saka ki sakin murmushi Majanune?
Dubansa ya maida wajen Dayabu, sai kuma ya lumshe idannuwansa yana ayanna ya zama wajibi a koya mata biyaya da bambancin sarkinta da yan iskanta! Irin yanda ta tsinke fuskar Zinaria da mari a gaban sarkinta ta yi rashin kunya mai tsauri!


Muryoyin dogarai da jakadiyoyin dake kofa na shaida karasowar Zinaria ya saka NAJEEBA kara janye kafamfafuwanta domin ita ta fi kusanta da hanya ta kuma tabata idan har ta shigo ta ganta a bakin hanyar nan zata baje tafiyarta ta yanda zata taka mata kafa ne ita kuwa ta kara mata na biyu a gaban ubanta!













Za ina tsalake ranakun posting idan har baku daukaka comment dinku ba=ØÞ
[1/20, 9:50 AM] Ummu Suhan=Ø
Þ: >ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



9



Cike da wata irin kasaita da alkyaba a jikinta ta sanyo kai, bayanta kuwa jakadiya ce, sai bayi mata uku du suka duduka sannan suka dukar da kawunansu kasa

A hankali ta ringa takawa har ta karasa kusa da Anmy ta samu waje saman luntsumemiyar kujerar dake nan ta zauna hakan ya kasance Zahrau na zaune kusa da kafarta ne

Sai da ta sada kanta a hankali ta gaishe da Anmy, sannan ta juya ta yiwa sarakan gaisuwar tare domin ba wanda zata fara gaishewa ta bar daya dan rabonta da mijin nata kusan kwana uku kennan

Sarki SHAHEED ne ya dubi dogaran dake tsatsaye kansu dan su san maganar tasu ce

Da yatsunsa ya yi masu nuni kan su fita

Da sauri suka ringa zagayowa sai su zube har kasa su kara neman afuwa sannan su fice a haka har ya zama daga su sai su a dakin

Kanta dake kasa ta dan dago ta dubi mahaifinta dake dan nesa da ita

A hankali ta saki kukan da ta aura harma ya zama abokin yinta ba dare ba rana kan rasuwar yaron nata

Mahaifinta yana gannin yanda Anmy ta girgiza kai ta sada kanta hakan ya saka shi yin gyaran murya yana kallonta

A nitse ya ce" shin baki yarda ba a maido maki yaronki ne ZULAIHAT?

Da sauri ta sada kanta dan a kausashe ya yi maganar wace ke nuna ransa ya baci da irin kukan nata, wanda ya tabata kafin ya zo sarakuwarta da mijinta ba zasu kasa rarashinta ba harma su nuna mata adu'a ya fi bukata ba kuka ba

Muryarsa ya kuma budewa a dake wanda hakan ya saka yan matan Anmy baki daya dagowa suka zuba masa ido wanda idan sarki baba na magana haka du kowa kansa yake sadawa

Da sauri Anmy ke saka kafarta tana dan zungurinsu, ta hakan suke tunnawa sunna mayar da dubansu kasa
Sai dai Zahrau haka kawai ta kara kure rawaninsa da kallo kafin ta sada kan nata

Cikin wata kakausar muryar ya ce" wannan ai aikin banza ne bayan kema kin san idan yanzu wanda ya halice ki ya yi kiranki koda duka duniya ne gatanki bamu isa mu tare maki ko mu hanna ki ba ko a dadaure ko a nitse sai kin amsa dan shi ya amsa zaki auri kuka ki ringa yi masa kina hanna shi sukuni a inda yake, shin a kanki aka fara rasa yaro ne ZULAIHAT?

A hankali , cikin tatausar murya Anmy ta ce" Zulaihat na neman afuwa Allah ya huci zuciyar sarki mai adalci

Dubanta ta kai wajen Shaheed wanda ya dace ya nema mata afuwa aman ya yi biris, san hararansa Anmy ta yi hakan ya sa ya kawar da dubansa daga kanta

Abih ne ya dan gyara zamansa shima a nitse ya ce" Allah ya huci zuciyar adalin sarki

DAYABUma ya kara sada kansa cike da girmama sarkin ya furta" a yiwa zinaria afuwa mai martaba

Anmy ta ringa zungurin su NAJEEBA,

Najeeba ta saki murmushi ta ki yin magana, a hankali ZAHRAU ta sada kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar sarkin abzin

Haka su Ummu suka ringa furtawa a hankali aman cikin ikon Allah NAJEEBA sai ta sada kanta kawai tana murmushi a saman lebenta wanda bata boye ba

Da yake basu da yawa a dakin dole a fahimci wanda ya yi magana da wanda bai yi ba, gashi maganar a nitse ake yinta ba da hayaniya ba, sannan ba a tare ake yin maganar ba idan daya ya yi sai ya ajiye harma ya saka sekwani sannan wani ya yi cike da biyaya

Da sauri ta zamo kasa ta dukar da kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar Aba

SHAHEED ya kawar da dubansa daga kanta, ya maida wajen sarki, da idannuwansa ya risinar da idannuwan nasa sosai sannan ba rufe su ya yi ba haka kuma ana gannin samansu da gashin girarsa
Hannunsa na daman ya dan daga daga ajiyen da yake ya dan dunkule shi sannan ya kara sada kansa

Murmushi sarkin garin Agadez ya yi da kansa ya iya amsa masa shima kafin cike da farin cikin kasancewarsa sirikinsa sarkin da ko cikinsu sarakunna suna maganar irin yanda sarauta ta zauna masa a jinnin jikinsa

Dubansa ya kai wajen Zulaihat a hankali ya ce" na san da kin san cewa dukan mai rai mamaci ne, sannan kin san cewa mamaci baya son kuka
Ba za'a hana ki zubar da hawayen rasa gudan jinninki ba, aman kuma ba za'a barki ki zubar har zubarwa ta dawo ta zama ba kyau
Idan kika tuna shi, ki yi gagawar yi masa adu'a
Idan soyaya ce nuna masa ta hanyar adu'a
Sannan ke kanki ki shirya naki zuwan inda ya tafi

Kanta take gyadawa hakan ya sa NAJEEBA ta kara dagowa ta tsura mata ido

Sai yau ta ji tausayinta, gaskiya ta ji tausayinta har cikin ranta
Kwana ukun nan koke koken da suke a bangaren Anmy sai ta dauke shi kawai na a ringa basu hakuri ne a hadu a lalace, tabas mutuwar Aliyu ta daketa domin yaron ba wanda ya batawa, yaro be mai shiru shiru sosai sai idan kun hada ido yakan sakar maka murmushi
To baima yi maganar ba bale ka ce ya maka ba daidai ba
Sannan koda yaushe yana wajen mahaifinsa sunna zaman fada, bai cika zama a gida ba dan mamansa bata barinsa zama a gida kulun korarsa take ya je ya koyi irin yanda ake juya kujerar da wata rana zai mulka

Idannuwanta ta lumshe ta maida kanta ta sada har ya gama sannan du suka shiga fadin godiya take da dai sauransu

NAJEEBA kuwa abinda ya fi bata daria kennan, irin yanda sha'anin sarauta yake tafia, irin yanda sarki ke zaune magana na masa wahala aman wasu na ta faman Allah ya huci zuciyarsa
To waima me aka masa da za'a ringa neman afuwar mutun? Anmy kadai take iya yiwa wannan kazagin itama sai idan ta tabata cewa ta bata mata to fa takan yi gagawar zubewa kasa ta ringa Allah ya huci zuciyar Gimbiya

Sai da komai ya nitsa Sarki ya nemi da yaran su fita

Du mimikewa suka yi, Zinaria ta fara godiya sannan ta juya ta fita
Su Ummu da zahra dukansu sai da suka yi godiya sannan suka firfito aman NAJEEBA kanta kawai ke kasa a hankali kuma cikin tafiarta wace ake gannin yanga ce ko takama da isa ce bayan haka take tun kankannuwarta bata iya sauri ba a haka ta fita a falon

Kansa kawai ya girgiza......bata nemi afuwar sarki ba, bata yi godiya ba, sannan da zata fita bata gode ba

DAYABU kansa duka abubuwan nan yana hankalce da ita harma ya gama ganewa NAJEEBAR so take ta jaza masu baki daya tashin hankalin Mai Martaba wanda hakan ba zai masu da sauki ba


Sunna tsakiyar tafia NAJEEBA ta ja ta tsaya, sai kawai ta shiga daria tana girgiza kanta

UMMU ta harareta ta yi tsaki ta ce" ke dai, ke dai akoy fitinaniya, wai ke mai martaba sa'ankine da zaki ringa kokarin kawo raini kai tsaye tsakaninku? Kin ga sarai dai yaya ya girme shi aman yake masa biyaya, kin ga Anmy mahaifiyarsa ce aman kasancewarsa sarki idan tana gabansa a lokacin da yake saman mulkinsa takan sanyaya kalamanta sannan ta tafiar da lokacin cikin sada kai
NAJEEBA kina ji kowa na rokar afuwa ke ba zaki yi ba ko?

Ummulkhair ta ce" kin ga, ni kaina dan Anmy ta min wani mintsini ne ya saka ni magana, haba dan Allah matar nan ta Mai martaba bata da mutunta mutane, kunna fa ji ranar nan yanda ta zagi Najeebar

ZAHRAU ta ce" ku dai ku daina irin haka, ina anfanin masifa wai?

NAJEEBA ta ce" ku dakata ni du ba wannan ba so nake ki auri ubanta

Zahrau ta zabura, dan har ga Allah gabanta ne ya fadi jin abinda NAJEEBA ta fada

Ummulkhair dake tare mata ta girgiza kai ta ce" zuwa yanzu na yarda baki da hankali NAJEEBA

Gaba suka fara yi hakan ya sakata itama daga kafarta tana biye da su bayan ta turo bakinta

Sai da suka shige uwar dakan ANMY NAJEEBA ta fada saman bed da baya tana murmushi

Juyawa ta yi tana kallon ZAHRAU ta ce" aunty, yaushe rabonki da ki ga fuskarsa?

Zahrau ta waigota ta ce" wa fa?

Najeeba ta ce" shi SHAHEED din

Da sauri ZAHRAU ta zaro ido, Bilkissu kuwa ta tura kofar da sauri ta rufe wace shigowarta kennan itama da mamaji ta ce" aunty NAJEEBA sunnansa ne kika kama kai tsaye haka?

NAJEEBA ta dubeta ta tabe baki bata bata amsa ba

UMMUKULSUM dake cire mayafinta ta dubi Bilkissu ta ce" ke fice mana a nan muna tataunawa yara sai shiga maganar manya

UMMULKHAIR kuwa itama bakin gadon ta karasa ta zauna tana fadin" walahi aunty ko, nima inaga a yanzu ba zan iya nuna kalarsa ba dan rabona da shi fuskarsa a waje tun kafin a nada shi sarauta

NAJEEBA ta ce" sai dai a yi masa hoto a boye a fitar da shi bayan mun san hotuna yanzu ana iya kara masa haske ko a kara masa girma bayan yaro ne karami

Da sauri Zahrau ta kai hannunta ta buge bakinta ta ce" ke dai neman fitinarki zai saka watarana a yanka maki bakin nan naki gutsi gutsi, ni ba zan manta lokacin da suke hawa dawakai da yaya ba, a lokacinma ya girmi yaya a girman jiki sosai har yaya na nemansa da rigima yana ce masa an hura shi shi din kyankyasar inji ne, shi kuwa yakan ce da yaya shi kuwa dan tamowa ne
Sannanma ina ruwanmu ne muna cikin gidansu muna irin magangannun nan idan ya ji kun san da zai iya sakawa a dauke mu ya halaka mu shikenan ko?

NAJEEBA ta koma ta kwonta tana kada kafarta ta ce" ina tausayawa talakawansa ne, kin ga ya ci ya cinye ya tayar da kai
Turaran nan da yake anfani da shi sai da ya cinye min tanadina na shekara biyu a paris bayan kun san nima mai kudi ce
Ta karashe tana kanne ido daya ta ci gaba da fadin" ku duba ku ga irin yanda fallonsa yake, Ac ban san adadin ko nawa bane, labulayen da karafunnan labulayen dakin nan sai ka rantse ba a africa bane,
Cafet din falon, da kujerun falon kadai ya isa ya haukata wanda bai taba fita ba
Duba ki ga irin dankara dankaran TV da windows da maficin nan dake kyali wanda aka ce da ruwan zinari ake wanke shi
Kausasa dubanta ta yi ta ce" ku kun san me nake nufi da ruwan zinari dan irin tsadar da wankin sarka yake a kasar nan!

Zobunnan hannunsa, da agogon hannunsa da takalmin kafarsa da shadar jikinsa da zubin da ake yiwa suturunsa kan sakani tunanin anya y'ayan mutane dake bata ba mafiya mai garin garin yake ba?


Zuwa lokacin Ummulkhair mayafinta ta dauka ta ce" kun ga, ba'ai min aure ba bale na haihu na haifi mai min adu'a, haka kawai na zauna a je wani tsanwan kuda ya kai labarin nan kunnayen fadawansama ba shi ba walahi sai sun ci ubanmu ko kannensa muke ba cousins dinsa ba

Tsakaninki da Allah NAJEEBA mutumen da ake yiwa maganar adalci wanda mutane suka shaida ake yabonsa ke jarababiya har kika iya kurewa rayuwarsa kallo kina neman masa shari?

NAJEEBA ta mike zaune tana kallon Ummulkhair ta ce" Ummu, wata uku fa kika bani a duniya kin ga yaya baya nan idan kika kuma zagina Allah sai na mare ki! Kuma ai ba shari na masa ba gaskiya na fada da yake hararena yana min kallon tsana me na masa yo ni bayan shi da kudaden talakawa yake takama? Ni kuwa neman na kaina nake walahi!


Zahrau ta girgiza kai ta ce" Allah ya shirye ki NAJEEBA, aman shi yaya SHAHEED din ne zaki ce ya dogara da kudin masarauta? Mutumen da shi ke zuba dukiyarsa dan gyaran gidan nan da kuma talafin gajiyayu da talakawansa?
Najeeba kin kuwa san meye aikinsa? Kin kuwa san shagon kasuwanci nawa ya malaka wanda idan aka siyar da daya zai isheki rayuwar duniya? Kuma ma wannan falon ai ba ainahin falonsa na dayan bangaren da yake hutawa bane
Baki san a wancen bangaren yaya yace harda su picsine, da wajen hutawa rikake? Da jardin da komai, shi ke fada min Sarki Shaheed sarki ne mai adakci wanda idan zai kwonta yake cike da damuwar shin yaya talakawansa zasu kwonta baci? Ke ba kyau tone tonen alkahairain mutun idan har yana yi domin Allah aman mutumen nan ya yi nisan da ba zaki iya fita cikin garinsa ki zage shi baki samu wani ya dauke numfashinki ba dan sunna kishinsa
A gidan redio kin ji me ake fada kuwa? An jima ba'a yi sarkin da talakawa ke kishinsa suke kishin komai nasa suke kare komai nasa irin sarki SHAHEED, ke ina alfaharin kasancewata yar uwar bawan Allahn nan dan kasaitarsa ba ara ya yi a jinninsa take!

Bakinta ta tabe ta koma ta kwonta saman bed din ta yi lamo

A hankali ta ce" kun san shan koko bukatar rai, abin dauka dauka ne

Sai da ta ja numfashi kamar zata yi baci ta buda idannuwanta ta ce" *ni sam bai min bane, sai nake jin na tsane shi sosai!*

Itama Zahraun mikewa ta yi a kusa fa ita tana juya kanta ta lunshe idannuwanta inda Ummulkhair ta fita ta shiga zaga gidan ita kuwa Ummukulsum ta he ta harhada sauran baki dayansu sukai cikin falon cin abinci ta shiga zuzuba masu dan su ci abinci

Aba ne biye da Anmy sai yaya DAYABU a bayansu suka shigo falon

Mutanen Falon suka ringa gaishe su sunna fita dan sun ga yannayin na Anmy da alamun magana zasu yi da dan uwan nata da kuma y'Ayansa

Zama suka yi ita kuwa ta shige ciki wajen yaran dan ta san sunna ciki

Karar bude kofar ya saka su tashi da sauri

NAJEEBA ta saki murmushi ta ce" Anmy ki rufa min asiri ki bani wayata na bude na ji yaya shagona da jama'ata kin ji?

Anmy ta zabga mata harara ta ce" ku fito

Tana fada ta juya ta fita suka kalli junna Zahrau ta ce" Allah dai ya sa ba laifi kika yi ba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment