You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
sakawa cikin adu'a da iya daukan wanka
Sai da ya saka abinda zai kara rufa asirinsa duda wandon shadar ba karami bane aman gwara a kara daurewa dan kar a ji kunya
A lokacin da ya dora babar rigar shi da kansa sai da ya tofawa kansa walahaula wala kuwata ila bilah domin dinkin ya dauke shi ya amshe shi sosai haka kuma kalar ta karbe shi sosai
Sai da ya saka farin yadi mai haske a fuskarsa mai shara shara kafin ya yiwa masu jiransa umarnin shigiwa dan gabatar da nadin rawanin da suka takanas dominsa
Su biyu ne, kwararu ne, aikinsu ne, nadin za'a hauda shi daidai yanda zai bada kalar tsuntsun da aka yi dinkin irin kalarsa wato Dawisu mai hasken fari kar kar kar sai dan kalar blue mai haske jefi jefi
Sosai suka gabatar da aikin nadin da ya dauki lokaci kusan minti talatin kafin su saka masa safa fara kar su saka masa takalmi kafa ciki shima farin ne kar kar mai kyan gaske domin fata ce akaiwa adon fari tas tas
Dawisu ya gama bayana a lokacin da suka miko masa sandar sarautarsa,
Sandar baka ce mai adon zeba daga sama
Sandar wata irin sanda ce mai shegen kyau ga tsada
Rike sandar da ya yi a hannunsa na dama a lokacin da ya mike tsaye ya kara masa wani irin cika da girma
Baki daya ya haske wajen har ya kasance su da kansu suka shiga kirarin dole domin kuwa wani yabon zaka yi shi ne a lokacin da kai kanka baka sani ba
Irin yanda karamar wayar da zai rike ta sha masa kai da ringin ya saka shi dubawa
Idannuwansa ya lumshe, bai san yaya aka yi suka cika takura ba , auntyn Nadia ce wace take kanwar mamanta uwa daya uba daya, da kansa ya amshi numberta bisa kwakwaran gargadin kar ta yarda wasu su san yana magana da ita sai Nadiar sai mamanta
Dagawa ya yi ya kara a kunnensa bai yi magana ba
Sai da ta kara sada kanta sosai sannan ta yi tambayar zuwa wani lokaci ne?
Idannuwansa ya daga ya kai wajen agogo, daurin auren a yanzu bai fi saura minti goma na, dan haka sai ya sada idannuwan nasa a hankali ya ce" bayan awa biyu da komawar *GUDGE MOCTAR*
Amsawa ta yi ya kashe wayarsa
Dubanta ta maida wajen yayarta da suka yi tsuru tsuru ita da Nadia sunna jiran amsar
Amsa ta basu dan haka suka shiga neman nikaf da bakin hijab domin kaf a cikin gidan babu ba mai sakawa!
Cike da kasaita ya ringa tafia
Yana fitowa dogaran dake laye a cikin katon falonsa suka kwashi wani irin kirari mai saka tsigar jiki tashi
Busa ce ta karade wajen irin ta sarakai hakan ya saka shi lumshe idannuwansa kafin ya bude ya sauke dubansa kan sarakai hudu da suka halarci taron da manya manyan mutanen da suka zo dan taya shi zaman wannan ranar
Da kansa da kuma idannuwansa ya yi anfani wajen gaisar da kowa ta hanyar dan sada kansa da kuma idannuwansa sai baban dogarin dake isar da sakonsa ya isar yana jinjina da hannayensa, sauran kuwa sai su kwashi kawo gaisuwa sunna fadin Sarkin garin maradi ya amsa gaisuwar *MAI WUKAR YANKA*, yana yiwa *GURNANIN ZAKI* fatan alkhairi
A haka dai har suka kara cinye wasu lokutan masu mahinmanci kafin a fita baki daya a bijiman dawakan dake dauke kwaliya ta mamaki da wata bazara a gefe dogarai majiya karfi suna ririke da ita
Sai da ya taka hannun Amintacensa kafin ya dora kafarsa daya a abin dokin sannan ya hau da kyau indo dogarai suka kare hawan nasa
Sai da ya zauna ya rike sorsin dokin sannan da kafarsa ya dan daki gefe da gefen dokin a hankali, nan fa dokin ya shiga wata tafiar kasaita domin yanda yake tafe fari kar da shi ga irin yanda yake daga wutsiyarsa mai dauke da yalwatacen gashi itama tana sama tana yawo irin ya koshin nan ya gaji da koshi kamar ya fashe tafiarsa ta koma ta kasaita
Haka aka layu anna ta rangada buda ga busa ga yan rakiya har suka fice daga fadar wada ba wanda bai fito gannin kwaliyar sarki da fitar sarki ba
Yayar Zinaria ta juyo tana gyada kanta ta ce" a gaskiya, da kamar wuya SULTAN SHAHEED ya iya zama da mace daya, koda bai je nema ba za'a zo neman alfarmar aurensa
Zinaria, ki duba ki ga yanda baki daya ya haske wajen cen, da ace nice ke, zan yi kwaliya irin tasa na bashi goyon bayan da zai saka ko wa ya karo sai dai ta biyo bayana! To ke Zinaria yaya kike tunanin mutun har haka ya zauna da ke daya? Kin yarda da kanki har haka ne? Wace irin kula kike bashi wace zata saka shi haka? Kar ki manta Aba da Abihnsa suka maku auren hadi, kar ki manta a zamanin nan mutun ko dan rufin asiri yake da shi shikenan ya kama hange hange bare wannan? Zinaria mijinki sarki ne, kuma mai kudi ne....yaya zaki kasa yiwa kanki adalci ki ringa summa dan zai yi aure?
Mahaifiyarsu ce ta daka mata wata irin tsawa ta hanyar fadin" kilishi anya kuwa ke jinni na ce? Baki san mulkinsa da dukiyarsan ne ya saka lale lale zamu tanadesu dan kanmu da y'ayanmu ba? Baban bakin cikina ace har yanzu babu wani abu da take da shi da zan iya fara dora rai a kansa, kilishi, ko ki min shiru, ko na hautsina kwonciyar hankalinki sakarai ke da kika ne kike yiwa kishiya bauta ai ke kika gani!
Shiru ta yi ta koma ta zauna domin ba zata furta wani abin ba kuma cibi ya zama kari, gani take da wannan zaman da suke sunna sake sake da kiraye kiraye da tsare tsare, da mikewa suka yi suka saka akai mata shiri irin na wanda ake yi, suka tarbi amaren nan da kansu da sai sun fi girgiza mutane, aman sun tare a nan sun hadu sunna ta abu kamar wasu jahilai
Ita kam gaskiya ko yanzu zata mike ne ta je wajen kiahiyarta domin tare suka zo da mijinsu sarkin tsatsunburun ne su shirya a tarbi amare da su, ita kam Alhamdulilah tana zaune da kishiyarta lafia, ita ta je ta sameta a gidanta da y'ayanta , matar tana da hali na datako hakan ya saka cikin nutsuwa suka hada kawunnansu suke zaune kalau, ko irin asiran da Gimbiya ke bata ta zuba a abinci dan ta raba su ita kam bata taba anfani da shi ba, tana amsa dan su zauna kalau da mahaifiyarta aman ko nisa bata yi take zubarwa ya bi iska domin ita dai bata dauki duniyar da zafi ba, kuma iliminta ya fi gaban wannan gaskiya, ta gane cewar idan ba kanka ka sauke, ka nemi zaman lafia da kowa ba to da dan da ka haifa ma sai dai ya bika dan dole!
Ana gama salar azahar aka gabatar da daurin aure
Auren da aka fara daurawa shine auren da ya saka zukata da yawa zabura da jin tamkar an dika masu guduma a kansu
A lokacin da aka furta kalmar sunnan nan wato *NAJEEBA MUTALAB* sosai zukata suka rikice, da yawa kuwa suka hangame baki cike da mamaki
HUZAIFA bai iya tsayawa ya ji sauran daurin auren ba ya fita daga cikin tanfatsetsen masalacin yana jin tamkar numfashinsa zai bar gangar jikinsa
Kuka ya fashe da shi a cikin abokansa yana son sai sun barshi ya doka kansa da madubin motarsa
Yana kukan yake fadin" ta cuce ni, ashe dama bata so na? Ashe dama mai gida zata aura shine ta yaudare ni? Dama ashe aurenta za'a daura na dinka sabuwar shada na zo ni ga sirikin sarki? Dama ashe aurenta za'a daura na zo nan? Nadiama ta cuce ni, ashe ta san haka ne ta barni nake ta fama da soyayar Najeeba a zuciyata?
Hannun abokinsa latif ya rike ya ce" Abdul latif, ka taimaka ka kaini wajen Nadia, ka kaini na ji me na mata a duniya? Walahi du rashin jin maganata na ajiye dan kar Najeeba ta kubuce min, ina nan ina ta neman inda zan ganta kulun a kofar shagonta nake wuni dan na sameta ta yi hakuri da abinda na mata, ni ban yi dan bata ranta ba
Ku shaida ne nan wayarta a hannuna na ringa korar du wani mai kiranta dan bana so idan na zo malakarta wani ya zame min matsala
Kune shaida summar da ni aka yi kan wayarta ni kaina ban san mutumen ba aman shine yau zan ga daurin aurenta?
Shi dai Abdul Latif kama shi ya yi domin kwarai ya san yana son Najeeba da gaske, dan haka bai tsaya yi masa shakiyanci ba ya taimaka masa suka shige mota
Yana shirin tayar da motar docter ya fito yana langwui
Tsayawa ya yi ya dafe habarsa ya furta" kan uba, lale na yarda cewar *MAGE, MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI CE NAJEEBA* da ta tashi kawo mana dukan sai ta kawo da wajen da ko mun sha kwaya ba zamu tunkara da salon iskanci ba
Soja ne ya fito har ya zarta ya dawo yana kallon Docter
Daria ce ta kubce masa kafin ya girgiza kansa ya yi gaba, lale ya san yarinyar nan ta fi karfinsa kuma ya yarda Allah ne ya kareta domin matar manya ce, shi irin ya dan yi hira da itama bai samu ba sai dai daga nesa
Da yawa sun ji jiki ciki harda likitan zuciyarta, da ambasador
Ambasador kansa ya sada a cikin masalaci idannuwansa sukai masa wani irin jajajir gashi kuma shi a cikin masalacin yake ba a balbalin masalacin ba bare ya mike ya fita, sai ya zama a lokacin da ya dago dubansa sai da gabansa ya fadi domin yana kallon sarki sai baki daya ya raina kansa, shima shaheed din shi ya kalla kafin ya cire kansa yana sauraron haramar daurin aurensa da Nadia kasan zuciyarsa kuwa haka kawai ta hanna masa sakat, gani yake du inda ya kai dubansa ba zai rasa samarin yarinyar ba, kai da ba dan an masa kwakwaran bincike kan kawar nan tata ba, da ba zai aureta ba, an fada masa cewar yarinyar girman kanta ya saka samari da yawa ke tsoron tunkararta, har fadi ake cewar tana da nauyin jinni, sosai iyayenta ke faman ta tsayar da miji domin kawancen nasu da Najeeba shekara uku ta bata, Nadia na dauke da shekaru ashirin da hudu tana cikin ta da biyar, ita kuwa fitsarariyar na dauke da shekaru ashirin da daya tana cikin da biyu
Idan ya kalli Ambasador ba abinda ke fado masa irin maganar.....ina so na ganki, na zo maki da dukan abubuwan da kika ce kina so na tsarabarki, ina so na ganki ko zaki bani nutsuwa!
Lalle uwa uwa ce
Bai yarda da iyaye a kasar musulmai sun isa da y'ayansu ba sai a kansa
Gashi dai ya kai inda ya kai Alhmdulilah aman kuma gashi a karo na biyu an daura masa aure da zabin da ba nasa ba
Idannuwansa ya kuma lumshewa ya maida hankalinsa wajen da ake kara raraba su goro ne ba kadan ba mutane sunna ta amsa a bokitai anna ta fita da su kafin a shiga haramar wani daurin auren, ga Dayabi, ga ABIH, ga sarkin agadez, ga yarima a kusa da shi sai ya shiga salatin annabi da fatan a watse lafia..........
Hi mutanen arziki,
Zan yi posting na biyu yanzu, idan kuka fitar da shi za'a janye dokar bibiyu>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>�#�>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���>���<���
*Na*
*SAJIDA*
=ث�(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<��
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>��
& *[ T.M.N.A]* & =���=؊��
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
37
Yana langwui ya shige dakin da Nadia ke zaune da kawayenta da auntynta da kuma daidaikun yan uwanta, dakin mai girma ne hakan ya sa kowa ke sha'aninsa an fi raja'a wajen daukan hotunna Nadia ta sha kyau domin aida ce ta zo ta mata mak'up har gida tana shaida mata cewar Najeeba bata fita kwana biyu yayarta ke fita saloon aman da ta fito zata shaida mata, ita kuwa ta dauki niyar ai Sai an nemo mata Najeeba ta tsantsara mata firgitaciyar kwaliyar da zata haukata mata sarkinta
A lokacin tana shirin shan wasu magungunnan hausa ne da auntynta ta dama mata da nono mai tsami, sosai fa Nadia ke amsar tsumi daga wajen iyayenta domin suma wayayun mata ne duda ba'ai mata gyaran jiki ba sun bar hakan a zuwan sai ta tare dan lokaci ya kure yawon neme nemen abubuwansu ya ishe su
Yana zuwa ya zube , mamanta da ta ga yannayinsa ta tsame daga mutane ta yo dakin
Auntynta kuwa tun da ya fashe da kuka ta shiga korar mutane cike da tashin hankali tana kallonsa
Su hudu suka yi saura sai tambayarsa ba'asin kukansa ake
Yana dago kai cike da muryar kuka ya ce" ashe Nadia ta san haka ta barni na yi ta hauka a kan kawarta? Ashe ta san wacece kishiyarta ta kyaleni na ringa barnar zuciyata da dukiyata ina hauka?
Nadia ta ringa kallonsa tana son ta ji abinda yake son fadi
Sai da ya share hawayensa ya ce" Allah ya isa tsakanina da ke Nadia, shine kika kyale ni ina haukan Najeeba ashe da ita za'a daura auren Sultan?
Nadia dake ta kallonsa ta yi wani dan tsam kafin ta taso da sauri ta juyi fuskarsa ta ce" hei dan uwa, me ka ce?
Hannunta ya janye daga fuskarsa cike da jin haushi ya ce" tambayata kike abinda nace? Nace kin ji kunya son kudin naki ya rasa wa zaki cuta sai ni jinnin ki?
Da sauri ta ce " bla bla bla, ba shi din nake son ji ba, auren Najeeba da sultan? Waye sultan kuma?
Lalle kin iyabiskanci Nadia, ya fada
Mamarta ce ta ce" kai Huzaifa wai meye haka? Me kake fada haka?
Huzaifa ya juya wajenta ya ce" mama, ni Nadia zata boyewa Najeeba kawarta ce kishiyarta da za'a daura aure da Sarki yau? Yanzu ina zaune aka daura auren Najeeba da sarki kafin na baro wajen
Nadia ta zazaro ido kafin ta dora hannayenta saman kanta, a rikice ta kara yiwowa kusa da shi ta dafa shi da hannunta da ya kwashi rawa ta ce" yanzu domin Allah me na maka zaka zo min da zancen dake iya halaka ni Huzaifa? NAJEEBA fa tana gida kwonce bata da lafia inji aida da ta zo ta min kwaliya, kai kuwa sai kace wai Najeeba Najeeba Najeeba ce aka daura aurenta da Sarki?
Daria ya fara yana kallonta hade da hawayen dake zuba a idannuwansa
Nunata ya ringa yi da yatsarsa ya ce" wawuya, meye ya tayar maki da hankali? Kema kin san zaki ci kakanki ne? Kema kin rikice ina ni? Kin min bakin ciki yarinya kuma sai Allah ya saka min!
Wani irin ta kurma hannayenta saman kanta ta zube ta shiga burgima fadi take" mama bilahilazi ku yi kiran baba na fasa, walahi na fasa auren mijin Najeeba, dama Najeeba ce dayar? Mama kin kuwa san Najeeba? Mama Najeeba fa kawata wace muke zuwa nan wani sa'in wace kike cewar yarinyar nan tana birge ki dan bata shafe shafen nan na yan matan zamani gata saliha mai kyan hali
Mama na rantse maki da Allah Najeeba kililin kasau ce, kanta a kasan nan take harbi irin na bakin maciji ko harbawa ba'a yi ake macewa
Mama Najeeba ce fa? Walahi halaka ni zata yi, idan wani bai kashe ni ita zata kashe ni dan na tabata sai ta ci uwani da na auran mata miji! To wai me hadinta da shi bayan a duniya ko maganarsa bata so ina mata, irin idan zance ya kawo zance sam bata so a kawo maganar sarautar garin nan bale sunnansa ? Mama ni ke zaune da Najeeba tun safe har dare a saloon dinta, ni ganau ce ba jiyau ba mama da ubwan waye bata dakuwa idan ka kawo mata simple raini bare ni da zan auri mijinta? Mama ki rufa min asiri tun ina numfashi ki hanna abin nan
Da mamaki mamanta ke binta da kallo hakama auntynta ke tareta tana fadin" ke meye wannan, rage muryarki kar ki sa a fara taruwa mana, ki bari mana
Mamanta ta ce" ke yanzu ai abin murna ne ace Najeebar nan dai da na sani ce kishiyar taki, yarinyar da bata taba gaisheni a tsaye ba sai ta duka, yarinyar da in tsintsiya na dauka zata amshe ta share wajen da nake son kimtsaya? Yarinyar da nan in ta zo sai ta baiwa kannenki abin dadi ni kuwa du da ina aiki sai ta min kyautar kudi masu yawa? Yarinyar abin mangari wace nake fadin da Ibrahim dina ya girma sai na aura masa ita domin a duniya tarbiyarta na birge ni shine ke marar kirki zaki ringa fadin kalamai irin haka munana a kanta? Haba Nadia , Haba Nadia nan abanku baya so kina kawaye aman yarinyar nan da kansa ya furta eh lale wannan tana da tarbiya ya yarda ki yi kawance da ita aman shine Nadia zaki fadi haka a kan yar mutane? Ni walahi sai yanzu hankalina ya kwonta zan fita na ci gaba da bikina cikin farin ciki
Nadia ta zabura ta mike tana neman wayarta a haukace ta ce" ina, ina ba zaki gane ba mama, ba zaki gane ba, a daki kike mama, mama baki fita kin san me duniya take ciki ba, mama a zamaninku babu kililin kasau, kai ko akoy ta yanzu nata salon daban ne, mama ki manta wata maganar cewa wai zan je na shinfida sarauta ko na je na yi tinkaho ko na je na kwace miji a hannun zinariya, walahi walahi sai na zama uwa akuya a gaban Najeeba
Kai ina, a watse, walahi a watse an fasa auren nan
Kokarin fita take dan watsar da taron mamanta da kanwar mamanta suka rikota suka yi ciki da ita sunna fadin Huzaifa ya kama masu
Bakinsa ya tabe yana jan hanci ya kama hanyar fita, komawa zai yi wajen auren dan mahaifinsa na cen, zai je na fada masa ashe matar nan da ya fara kekyarawa palas itace aka yi masa wuf da ita
Dannata suka yi ciki suka rufe kafin auntynta ta zaunar da ita tana kallonta ta ce" ke dallah banza zaki mana shiru ko sai na ci ubanki a wajen nan? Dan ubanki kishiyar ce kike yiwa haukan nan? Ke ba mace bace ko ba abinda take da shi kike da a jikinki ba? Dan hauka ko wacece ita zaki nuna ne har ki ringa fadin wai a fasa aure? An ce mana an kashe matarsa kin ce kin ji kin ganima bale wai zama da kishiya? Kishiyarma mamanki na fadin tana da halaya shine zaki zo kina mana hauka a nan? Idan gabdancin ne ke ba zaki iya kwatar kanki a gabanta ba? To Nadia ko a dadaure sai na kaiki gidan nan yau, dan walahi sai an dama da mu, me aka fi mu? Yarinya ke da zaki amshi girma kan girma? Tun da abin nan ya samu nake takawa ina daga kai da bakin gilas a garin damagaram, kin san da rububin kawance ake da ni dan yar yayata zata auri sarki? Zan ci uwaki idan kika raba ni da farin cikin nan walahi! Idonki idonta zaki mata murmushi ki ce da ita" hello yar uwa ki bata hannu ku gaisa!
Sai me? Ke ko yar uwarki ce idan halal ne ku jera an fada maki zamu tsaya ne? Yarinya ko ni uwarki yace yana so idan halal ne bara ki ji zan zo mu jera ne bale wata kawa
Dallah warware mana maza shiga wanka mu fita mu yi jiran dan sahun dan na ga take taken ki yar iska ce ke kina iya saka min hawan jinni!
Mahaifiyarta kam mace ce mai sanyin gaske, kuma ita bata ga wani abin tashin hankali a nan ba, wai Nadia bata ji tsoron an ce ana iya kasheta ba sai tsoron dan za'a mata kishiya kawarta mai mutunci? Du irin yanda suka ringa fadawa mutane auren nan? Ita kanta sanadiyar auren nan yau mai gidansu baki daya ya zo daurin aure tun da safe da shi aka rankaya gidan sarki har ce mata ya yi ta sama masa number sarkin shine wai Nadia zata yi mata haka?
Karshe dai tun a lokacin auntynta ta gama shiryata ta fita ta samu hanya ta ce ta fita gatanan
Ta san sarai wacece auntynta, tabas kamar yanda ta ce ta kiyayeta zata ci kaza kazancinta zata aika dan haka da nikaf din tamkar munafuka ta fice a gidan ba tare da an farga cewar amarya har ta fita ba
Sai da ta bushi kasa ta ce zata je ta karbo dinki da dabara ta fice a gidan banda yayarta ba wanda ya san nufinsu sai mahaifin Nadiar wanda shima sarkin ne da kansa ya masa bayani bayan an gama daurin aure
Bakin titi suka samu suka zauna, Nadia kam wani irin murdawa cikinta ke yi, ita fa kallonsu kawai take, ba zasu taba fahimtar abinda take nufi ba, baki daya wani zumudinta, wani farin cikinta, wata takamar da ta dauko ta yi mata sanyi, abu daya take furtawa auntynta shine" aunty, ni na zauna da Najeeba, Najeeba uwata ce a iya bariki, ki barta kawai inda kika ganta dan na tabata kema zaki so ta idan kika hadu da ita bare mai Martaba, ita fa ba wai bakin hali ne da ita ba, aa, abinda zata aikatawa du wace ta kalar mata sahibi ne mai yawa, takan ce na tsani kishiya, ba zan auri mai mace ba, idan kuwa mijina ya kali wata sai na mata *salatu* irin na maza
Daria auntyn nata ta yi tana gannin yanda ta rikice, lale zata tsaya har a sada Nadia da dakinta domin a irin yanda du irin firiritar Nadia ta haukace din nan daga jin maganar daurin auren nan ina da an kaita gata gata?
Kallonta ta yi ta ce" kin ga, zuwa an jima zamu cika fadar nan kwonmu da kwarkwatarmu, du abinta zata ganki zagaye da dangi dan haka ke da ita sai dai kallo, idan ta zo da mutunci a yi, idan kuwa ta zo da rashin mutunci a yi
Nadia ta dago kanta tana gannin wani adaidaita sahu da bashi da number a jikinsa, sannan sabo ne dal ua tsaya a kusa da su bai masu magana ba aman su yake jira ta ce" baki san su waye MUTALAB FAMILLY BA? ai inda zamu je din gidansu muka je, zamu tardata tatare da iyayenta da yan uwanta danginta, aunty idan ta kama a zane mu za'a zane mana jiki ne tasss walahi
Itama zuea lokacin jikinta ya yi sanyi, sai dai bata nuna ba, ta jara karfafa mata gwuiwa ta ce" Nadia, ai yanzu ba ke ba, ko ni zane ni sai ruwan sama walahi domin na zama uwar matar Mai Damagaram, tashi mu je, mijinki na kare lafiarki kina hauka, na tabata sonki yake a yanda ya damu kar a kashe ki
Haka suka tafi cikin dan sahun nan su duka da nikaf
Abinda aka bincika kawai shine idan basa dauke da wani mugun abun kafin su shige ciki
Sunna shiga kuwa Jakadiya da Anmy ta turo tarbarsu, ita kanta bata san ko su waye ba ta ja su bangaren Amaryar sarkin ta buda masu sannan ta yi baya
A nan suka zauna sunna karewa tanfatsetsen falon kallo cike da wani yannayi
Kai da ace hankalinta a kwonce da idan ta fara daukan hoton wajen nan? Yau itane zaune a cikin gidan sarki, a cikin daki, malakinta, a matar sarki? *Akoy shagali*
A lokacin da karfe hudu ta yi na yama, a lokacin Anmy ta bada umarnin a kai ZINARIA, da NADIA dakin gyaran amaren da tuni aka shige
Book Chapters
Chapter 29
Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58