Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali ta shiga gabatarwa, tun daga Azahar da bata samu damar yi ba, la'asar da bata yi ba, magariba, sannan ta dora da isha'i

Tana salamewa ta ji muryarsa kasa kasa ya ce" du kina me kika tara sallah haka a kanki NAJEEBA? "

sai da gabanta ya fadi, domin ita dai sam bata ji shigiwarsa ba bale takun tafiarsa, uwa uba kanshin turaran nasa dake shaida mata zuwansa waje itama shi din ne ta kilkila a jikinta ya kasance har hancin nata ya daina jiyo kamshin zabar ya shaka da yawa
Sai da ta dauke numfashi kadan sannan ta dan sada kanta da carbin da ta dauka fari mai kyau a hankali ta ce" Nafiloli na yi "

Dan murmushi ne ya kwace masa a kan labansa, bai ce komai ba ya koma ya gyara zamansa saman gadon ya jinginar da bayansa a jikin kan gadon kadan sannan ya ci gaba da binta da kallo kasa kasa yana mai jan carbin dake hannunsa

Du sai ta kasa jan lokaci mai tsayi tana jan carbinta, tana ganawa ta daga hannunta a cikin zuciyarta ta yi adu'o'inta ta shafa sannan ta ajiye carbin ta mike ta dan ninka salayar ta bi wajen kur'anan nan da kallon sha'awa tana ji a zuciyarta inama ace nata ne duka? Kai da ta caba

Dan satar kallonsa ta yi, sai ta ga ashe ya yi baci, dan haka dan ta yi murmushi ta juya a hankali da niyar tafiarta wancen dakin ta kwonta

Kasa kasa ta ji ya furta " Baki ji ba? "

Har sai da ta dan tsaya ta juyo ta kale shi, gannin bai motsa a yanda ta barshi ba sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiarta a hankali

Idannuwansa ya dan buda kadan ya ce" Najeeba idan kika fita ba zatai maki dadi ba "

Juyowa ta yi tana turo bakinta gaba tana dan magana kasa kasa , cewar haka kawai ashema ka san sunana malan

Shi dai kallon bakin nata kawai yake a yanda yake, sai kuma yanda ta tsaya masa wani kerere a tsaye a ka da yake mamaki

Dan buda idannuwan nasa ya yi ya sauke duban nasa a fuskarta, irin yanda ta turo bakinta da tsayuwar da ta masa kamar wata yar baby sai mutsu mutsu take da bakinta

Hannunsa na dama ya mika mata a hankali ya ce " Zo "

Sai da ta bi hannun da kallo , a ranta fadi take, kawai mutun sai fari uwa wani aljanni, irinsu ne kana ta kanka a gida kana faman girki da tsantsara masu kwaliya sun fita waje wasu matan na wawarsu, haka kawai kana ta kanka a jaza maka abinda ba shi ba, sai wani yanga da wani langwui salon ka kara tara matan, to dai matsalarka ce malan idan kana so tara million ma

A hankali ta dora hannunta saman nasa , tana kara shagwabe fuskar tata ita bata ki zuwa ba, ita bata yarda zata je har zuciyarta ba

A hankali ya janyota gaba dayanta jikinsa ya dorata saman jikinsa ya saka hannayen nasa ya bata kyakyawar runguma
Muryarsa sanyaye ya ce" yaya zaki gudu ki barni bayan kin ga matata ma cikin wani hali, nima ina cikin damuwar saka mai so na a wani hali? Duda na san ba so na kike ba aman idan kika zauna da ni zan rage zafi "

Bakinta dake daidai wuyansa ta turo sosai tana tabewa, a hankali ta ce" to ka yafe mata mana, ai na ga ba ita ta kashe maka mata ba, kuma ba ita ta so kashe maka mata ba, bayan wannan ai dan tana son ka ta aiwatar da hakan, kishinka take shi ya sa "

Idannuwansa dake lumshe ya dan kara lumshewa sakamakon abu biyu, gannin kamar maganarsa batai mata zafi ba, da irin hucin dake saukar masa a dokin wuyansa

Sai da ya jima tamkar ba zai yi magana ba sannan ya ce" zan duba maganarki, kafin na yafe mata zan kara aure "

A hankali take jin haushin magangannunsa, to a me wai ya dauketa ne? Ita ga wawa ko? Da dan zafi zafi ta ce " idan ka tashi ka auro farare tas tas tas bakakenma ka sake su SHAHEED "

Murmushi bayanane ya yi gannin a yanzun maganarsa kamar ta mata ciwo, dan haka ya ce" sai nake gani kamar kin ji haushi? "

Bakinta ta yatsina tana dan son tashi aman sai ya kara matseta a jikinsa hakan ya sa ta daina kiciniyar son tashin
Itama sai da ta jima tana tunani sannan ta ce" ba biya ba bege me ya kawo jin haushin maganar abokin zama ?"

"Haka ne kuma, aman ko ba komai zan duba shawararki zan kawo wata tsaleliyar fara, sai dai ni bana ajiye bayi a matsayin matan da zan ringa zagayawa, kema musulunci ai ya yi karfi yanzun ko " Shaheed ya fada yana mai kara rungumeta a jikinsa

Sai da ta datse lebenta na kasa a dan kausashe ta ce" sake ni! "

Kansa kawai ya dan girgiza mata bai sake tan ba bai kuma bata amsa ba

Huci ta furzar kafin ta ce " Allahn da ya sa nima ba ni nace ina son farin ba! "

Murmushi ya yi a bayane bai bata amsa ba, sai kawai ta ringa sauke ajiyar zuciya, sai da ta dan daga dubanta ta sauke a kan habarsa , gannin idannuwansa a rufe sai ta zabga masa harara harda murguda bakinta

Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Na yafe maki "

Ido ta zaro da mamakinsa, wani irin karfin gani ne da shi haka?, wai kuma me yasa ya cika son yi mata komai cikin sanyin lamari bayan shi din mutun ne mai zafi?

A hankali ya ce "BEEBAHHH?"

dagowa ta yi da sauri dan jin muryarsa a wani irin sanyaye sannan irin yanda ya ja sunnan sai ta ji da bambanci sosai kan yanda UMMU ta fada, nasa har wani irin yamyamyam ya sakata ji a jikinta, sam sai ta kasa amsawa kiransa sai wani zuru da ta yi tana kallon wuyansa domin daf take da wuyan nasa numfashinta na sauka a wuyan nasa

A hankali ya ce" BEEBAH ki janye hancinki daga wuyana, kin ga sai wani yannayi nake shiga kar na zo na kara kuma a ce ban kyauta ba "

Idannuwanta ta lumshe a hankali, tana mai jin yanda maganarsa ke sauka a cikin kunnayenta, sunna samun wani muhali mai tsafta a cikin kwakwaluwarta, kasancewarsu ba zafi ba ihu ba kausasa sai take jinsu wani bambarakwai harma ta kasa tuna waye mai furta su haka a sanyaye, a rashin sani ta dan matse masa wajen mararsa da hannunta na dama ke sama hakan ya saka shi rintse idannuwansa a hankali ya furta " Washhh zata kashe ni "

A dan tsorace ta dauke hannun nata, sannan ta yi gagawar janye jikinta daga irin mamukar da sukaiwa junna, cike da kunya gannin ya ki saka mata duwai ya mata wani damka ya sakata dam gyaran murya kasa kasa ta ce".......





.................>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ=ØÞ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ>ØsÝ

>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



58




Gannin ya ki sakar mata duwai ta dan gyara murya kasa kasa ta ce" ka sakar min nan, kana fa gannin inda kake saka hannayenka kana halaya kamar wani........."
Sai kuma ta yi shiru a lokacin da ya kara janyota da dan karfi jikinsa ya mayar da ita irin kwoncin da ta yi dazun a jikinsa sosai, sannan ya rage muryarsa sosai da sosai ya furta " kamar wani kwarto ko?"

Hannayenta duka biyu ta kai wajen bakinta tana rufewa tana zaro ido cike da tsoro da kuma mamakin furucinsa
Sai dai kafin ta kai ga farfadowa sai ta ji ya dora da fadin " Ai ke kika lalata ni, gashi sai haye min jiki kike kina wani shan mur "

" Ka ji tsoron Allah shaheed " ta fada a mugun sanyaye tamkar zata fashe masa da kuka muryarta na dan rawa rawa

Murmushi ya saki ya mayar da fuskarta wajen kirjinsa a hankali yake shafa bayanta ba tare da ya kuma furta mata koda A bane

Baki daya ta ringa kaea gyara kwonciyarta, har ta samu kwoncin da ta ji dadinsa sannan ta lumshe idannuwanta tana mai karanta adu'ar baci

Bacin ne kuwa ya yi awon gaba da ita, hakan ya saka mata sakin nauyinta a jikinsa da kuma kara sakankancewa da jikinsa

Murmushi ya yi a hankali ya juyar da ita saman bed din

Cikin nutsuwa da lalama ya cire mata rigar nan dan ta ji dadin baci
A hankali ya juyar da ita ya bale mata bras din nan ya cire baki daya

Numfashi ya ringa fuzga da sauri da sauri, sai kuma ya ja abin rufa da sauri ya rufa mata har wajen wuyanta sannan ya kara yi mata adu'a ya mike yana gyara jikinsa sannan ya fito daga dakin ya nufi bangaren AMMI

Kamar yanda ya yi tunani hakan ce ta faru, tana zaune saman abin sallah tana jan carbi aman baki daya hankalinta waje guda ta kurawa ido tana kallo hakan na nufin jan carbin ne kawai take aman damuwar da take ciki mai yawa ce

Cike da rauni, rauni irin wanda bawa baya iya boyewa gaban mahaifiyarsa ya karasa ya zauna kusa da ita sosai yana kallonta

Idannuwanta ta lumshe jin sa a kusa da ita, a hankali ta kura masa ido tana nazartarsa

Kansa ya sada kasa yana ta dane halin da yake ciki hakan ya sa a hankali ta saka hannunta ta dago kansa
Hannayenta biyu duka ta saka ta tare fuskarsa sai kuma ta janyo fuskar tasa hakan ya saka shi biyota ya dora goshinsa a kafadarta kamar yanda ta bukata

A hankali ta shiga taping din bayansa, muryarta a raunane ta ce" cry, cry, cry my boy "

Dan shiru ta yi sannan ta dora da fadin " basu kyauta ba, sun ci amanar zaman tare na shekara da shekaru bisa son zuciyarsu, ba laifi akai masu ba, ba tinzura su akai ba ta hanyar wulakanta su a zamantakewar da aka yi ba, niyarsu ne, jst cry SHAHEED , cry a jikin mahaifiyarka domin kaima mutun ne, dan kana sarki baya nufin zuciyarka bata anfani, dan kana sarki baya nufin baka jin rauni irin na kowa, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a zuciyarka sannan ka manta da lamarinsu, Allah ya gama saka maka tunda ya bayana maka komai, Allah ya gama yi maka komai tunda ya hanna su wulakanta ka a idannun duniya, CRY MY HAPPINESS "

Ai kuwa, magangannun da take tamkar tana bashi damar kara hasko irin zaman da ya yi da su, sosai ya yarda da su, sai ga rayuwa ta zo masu a haka daga shi har su, kwarai zuciyarsa ta masa nauyi , bukatarsa samun hawayen, da zai samu ma ya rushe da kuka mai tsanani kawai, sai dai rashin samun hakan ya saka shi ringa sauke tagwayen ajiyar zuciya yana ta kara yiwa komai fila fila yana mai baiwa kansa amsa cewar dan adam kennan, ka shiryawa komai daga gare shi,, a hankali ya ci gaba da jin nauyin nan na ragun masa, a fili ya furta" harda aikata kissa? Lalle shi kansa bai san karamar kiyayata da ya saka a ransa ta yi girman da zata kaishi ga halaka AMMI "

Ammi ta yi dan murmushi jin dumin abu a kafadarta, ta tabata abinda take so ya samu ne ya samun, wato zubar hawayensa dan ya ji sanyi a zuciyarsa, dan haka itama a sanyaye ta furta" Dan Adam kennan, mutun mugun ice kennan "

A hankali ya dago kansa yana kallonta, hakan ya bata damar saka hijab dinta tana goge masa fuskarsa, a sanyaye ta ce" har na tsawon wani lokaci zaka kilace ZULAIHAT a bangaren horo ? "

Sai da ya jima kamar ba zai yi bayani ba sannan ya ce " Idan aka gama bincike suka tabatar cewa laifinta kawai hada kai dan a kori kishiyoyinta ne ba dan a kashe su ba, idan aka tabatar ta hanyar vidios din da gareni a wajena cewar laifinta bai kai na aikata kissa ba, kuma kotu ta ga ba zata riketa ba ba zata yi kaso ba, zan yi kokarin turata masarautar Agadez ta gidan motar haya, zata sauka irin na kowa ta dauki abin hawan da zai kaita masarautarsu
Zan sanar da mahaifinta ya saka jakadiya ta tarbeta daga bakin gate na farko a yi wajen horo da ita zan bata damar zama tare da bayi na tsayin lokacin da zata gane rayuwa, domin kuwa tarbiyar da ta samu sai ta samu wace zata nuna mata ba zahiri aka nuna mata ba, na tabata duniya ce kawai zata ladaftar da ita ta horar da ita, domin kuwa idan ba haduwa ta yi ta kwana ta tashi ta ci abincin mutanen da take wulakantawa ba, ba zata taba gane yaren ba, gidan horon garin Agadez ya tanadi horo ne sak ba dan sarki ba bawa, zata je ta hadu da sabuwar rayuwar da zata hidimtawa kanta komai, daidai da shiga bayi sai ta bi layi kafin ta samu shiga, ba tsaftacen waje ba tsaftacen kayan zuba abinci bare dandannon da bakinta ya saba, ba waya ba tv ba wuta bare ta samu AC ko panka, daga nan zata fahimci darajar ni'imar da Allah ya bata ta yi wasa da ita, zata gane darajar masu hidimta mata, idan na gamsu cewar horo ta samu ba son kai ba zamu yi zama da ita da mahaifiyarta da mahaifinta, idan da hali sai ta dawo ta zauna a karo na biyu , aman fa AMMI sai dai a yi hakuri domin kuwa ba a matsayin uwar gidana zata dawo gidana ba, sai dai a sake dauran aure da ita dan kuwa na rubuta mata saki daya, dukan abin kunyar da take gudu zata same shi da izinin Allah sai mu ga irin daukan da zatai masa "

Ajiyar zuciya AMMI ta sauke tana kallonsa, sai kuma ta dan kawar da dubanta a hankali ta ce" mun yi magana da mahaifiyar Nadia cewar ta saka a kawo wanda zai kula da ita har kafarta ta warke, sannan ta tsorata matuka bangarenta ina ga ko a buda mata bangare na hudu, ko kuwa kawai ka mayar da matanka bangarenka Shaheed, idan Allah ya yi kun fara tara iyali sai su dawo bangarorinsu, aman a haka ni kaina na tsorata da mutun, dan kuwa su nasu ya fito, kamar yanfa ka fada ne gidan sarauta ba'a taba raba shi da ire iren abubuwan nan "

Shaheed ya gyada kansa yana sauke ajiyar zuciya

AMMI ta ce" yaya zaka yi da shi kuma sarkin bulala fa? "

Shaheed ya dan yi murmushi a hankali ya ce" Da ace haushina ne kawai yake ji, bai ji za'a cutar da ni ya yi shiru ba, harma ya bada tasa gudunmuwa ba, da sai na manta da na ji sunnansa a cikin magautana sai dai kiyaya girma take, kuma na tabata karuwa take a cikin zuciyarsa, dan haka zan yaye shi daga masarauta , zan fitar da shi cikin gari sannan na saka ido a kan lamuransa, domin kuwa koda bashi da lafiar aikata mugunta ga y'ayan mutane shi abin a zuciya yake, hanyoyin aikata mugun abun kuwa yawa ne da su, zan kai shi rayuwa cen kusa da baban gidan kaso, sannan zan saka masa ido sosai "

Cike da gamsuwa Ammi ke gyda masa kanta

Gannin sosai ya saku kan dazu sai ta ji dadi, dama ta tabata idan suka zauna zai ji sanyi sanyi a ransa, dan haka sai ta yi niyar kara saka shi nishadi ta hanyar fadin" gobe yarinyata ke gama sati gudanta, a gobe zasu yi zama ko yayane? "

Shaheed ya dan dago a hankali yana kallon AMMI, sai kuma ya yi dan murmushi ya ce" zasu yi zama aman ai sai Nadia ta samu lafia ko AMMI? "

Ammi ta ce" an fada maka ta ce ba zata iya zuwa bangaren mijinta ba dan kawai kafarta na yi mata ciwo ? "

Yanzun kam sai ya yi shiru aman fuskarsa a washe take ba a daure ba

Ammi ta ce" ina yarinyata SHAHEED?"

Murmushin da yake rikewa ne ya bari ya subuce masa
Waje daya ya dan kurawa ido yana kallo, sai kuma ya dan girgiza kansa yana cije lebensa na kasa, kasa kasa ya ce" Bata jin magana, zata mayar maki da yaro mai magana , fada take nema ido rufe "

Wani farin ciki ne ya dira a zuciyar AMMI, dan kuwa irin yanda yake maganar yana dan juya kansa ga murmushi kwonce a fuskarsa sai ta samu kanta da yin yar dariya har cikin zuciyarta, a hankali ta ce" ni dai kar wanda ya cutar mij da y'a, ehe "

Fuskarta ya kurawa ido, a ransa kuwa fadi yake wace zata wani tsaya kallona na cuceta? Ban taba gannin tsaurara irin yarki ba AMMI zata tsareni da ido ta bani umarni ba ko shayina, wai Malan cika ni, wai je ka auro da yawa fararan, wai ni take murgudawa baki a gabana?, sai kuma ya saki murmushi yana ayana sai na cije leben mu ga abin yin tsiwar a gabannan,

AMMI kam gannin sai sakin murmushi yake yana dan juyar da kai sai ta ce" tashi ka duba Nadia sai ka tafi bangarenka ka huta "

Sai da ya kama hannunta kamar yanda ya saba ya dora shi a gefen kuncinsa na dama ya lumshe ido sannan ya kawo shi wajen bakinsa ya sumbaci bayan a sanyaye ya furta" Allah ya sa ki hama da duniya lafia ya datar da ke da shiga gidan aljannah, ya yafe maki laifukanki ya faranta maki zuciyarki, Allah ya nutsar da zuciyarki ya kara maki imaninki yah UMANI "

Ammi dake amsawa da Amen , Amen a kasan zuciyarta kuwa ita kadai ta san irin adu'ar da take masa, har ya gama ya mike cikin nutsuwa ya fice a dakin

Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi sai kuma ta ci gaba da jan carbinta har sai ta ji baci tukun zata ajiye

Irin kwonciyar da ta yi zai nuna maka a takure ne ta yi shi
Tun da Sultan ya shigo ya lura da idannuwanta biyu aman kuma kamar harda hawaye a gefensu
Kasancewar ba wani kwakwaran motsi ya yi ba sai bata ji shigowarsa ba, hasalima ta hanna kanta rintsa ido dan ko a nan din tsoro take ta rufe idonta ta ga macijin idan ta bude

Dan gyaran muryar da ya yi ya tsoratata , hakan ya sa ta zabura har ta bige ciwonta
Fashewa ta yi da kuka tana rinrintse idonta

Da dan sauri ya karasa yana fadin" hey, menene, meye? "

Jin muryarsa ya sakata buda idannuwanta, baki daya hannayenta rawa suke ta kale shi ta ce" tsoro nake macijin ya shigo, wollah ka tambayi Najeeba ko laifi na mata kwari take kamowa ta ajiye min a gabana , ba zan motsa ba sai ta yi hakuri ta dauke, haka Allah ya halice ni da tsoron du wani abu bayan kuda , dan Allah a kaini gidanmu "

Tausayinta ne ya ji ainun, wannan daukan alhaki har ina, gata ita bata mutun ba aman an barta da tashin hankalin tsorata har haka

Hannunta ya kama ya tayar da ita tsaye, a hankali ya ce" ba kyau mutun ya cika tsoro har haka, ki rage ki yaki kanki ki rage sannan ki daina nunawa kina tsoron domin duniya ta ki lafia, baki san da wa zaki hadu ba, baki san inda rayuwa zata kaiki ba"

Yana gama fada ya kama hannun nata ya fita da ita ya nufi dakin UMMU da ita, dan ya san idan ya kaita dakin Ammi to itama Ammin kunyarta zata hannata yin bacin, ita da Najeeba kawai take iya bacinta a cikin matansa

Bayani ya yiwa UMMU, kwarai ta fahimta dan haka ta kamata ta kaita da kanta saman gadonta harma ta shiga dauko abinda zata gige mata dan jinnin da ya zuba a wajen ciwonta

Ajiyar zuciya ya sauke yana dan girgiza kansa ya juya ya tafi

Ummu kuwa da dabara ta saka Nadia ta cire uwar alkyabar dake jikinta sannan ta sakata ta kwonta
Zama ta yi gefenta a bayane ta ringa tofa mata adu'o'i hannunta saman kanta, hakan ya sa ta yi ta jera ajiyar zuciya har jikinta ya shiga warewa ta shiga jin nutsuwa a cikin zuciyarta
Muryarta na rawa ta ce" Mama, zaki kwana da ni a nan gefena?"

AMMI ta yi dan murmushi ta ce" Eh, a nan zamu yi kwonciyarmu Nadia, abinda nake so da ke koda abin tsoron kika ganni idan dai ba waje ya kure maki ba bana so ki tsorata, ke ko waje ya kure maki ridarshi bige banza, ni bana wani gudu sai dai ya lahantanin ta haka aman fa sai na kar shi"

Yar daria abin ya bata, harma ta yi murmushi ta ce" Mama, kennan a wajenki Najeebana ta gaji wannan abin, idan ta ga abu tana tsoro in ya nufeta maimakun ta gudu ko ta yi ta ihun a taimaketa sai kawai ta ride shi ido rufe, akoy ranar da wata irin tsaka katuwa bak'a kirin harda yan gashi a jikinta ta fado mata saman abin kwaliyarta a shago fa, ai kau aka ringa guje gujen guduwa itama tana tsaye jikinta na rawa, sai kayan ta kwashi ayatul kursiyu a bayane tana yi tun karfinta, kuma sai ta warci kwalbar wata hodar ruwa ta shiga dandatsar tsakar nan fadi take idan aljani ne ka bace na maka ayatul kursiyu idan kuwa tsaka ce dan ubanki ba inda zan je, kuma fa harda hawaye domin tana tsoron tsaka sosai fa "

Ai kuwa abinda mama take so ne ta samu, wato ta ringa jin irin halayar gudan jinninta, hakan ya sakata wani irin nishadi, sai kawai ta kara sakin jiki da Nadia, itama ta saki jikinta sosai da maman tana ta bata labarunsu, kuruciyarsu, irin tabin maganarsu, zuwa yanmatancinsu, zuwa yanzun

A haka ne mama ta ce" aman Nadia, me ya sa Najeeba ta tsani Sultan ne?"

Nadia ta dan gyara kwonciyarta a hankali ta ce" Mama, ta dauki wani lamari ne ta sakawa zuciyarta cewar du idan ta motsa yana binta da harara, ya tsane ta, na rasa menene ya ja haka? Me ke damunsu ne baki dayansu, sai dai a yanzu ni ina da ja da maganar kallon tsana yake yi mata, qman ba komai na tabata a hankali ita da kanta zata ganni, zata fada min hakan kuma "

Mama dai murmushi kawai ta yi, lalle ta ji Nadia ta shiga ranta sosai da sosai, dama yarinyar bata da duhun kai, haka sukai ta labari har baci ya dauketa sannan UMMU ta dauro alwallah ta shiga gabatar da nafilfilu domin dare ya yi sosai

Sai da ya gama dukan kimtsawar da yake yi a kowani dare, ya gabatar da nafilarsa raka'a biyu kawai ya yi doguwar adu'a sannan yaike ya cire jalabiyar dake jikinsa

Turare ya fesa a jikinsa sosai sannan ya shige cikin abin rufar da ta kanainaye take baci hankalinta kwonce

A hankali ya janye abin ya maye gurbinsa ta hanyar hade jikinsu sannan ya lumshe idannuwansa ya shiga neman baci bayan ya yi adu'a

Wani irin nutsatsen bacin da bai zata zai samu ba ya samu, a lokacin da ya motsa kiraye kirayen sallar asuba na biyu tuni har lokacin ya yi, da sauri ya diro ya nufi bayi dan kar ya makara

Ko da ya kimtsa ya kai dubansa wajenta bata nan, sai kawai ya fice dan gabatar da sallarsa

Ya jima sosai domin sai da ya leka ya ga kwannan su AMMI da Nadia da jiki, sannan ya dawo, a lokacin tuni takwas ce take neman yi

Kasa kasa kunnayensa ke jiyo masa dan kida na tashi, hakan ya mugun bashi mamaki harda dan zaro ido
Kida? A nan? Da safiyar nan wani iblis ne wannan?

Da sasarfa ya nufi dakin da

Please Login or Register in order to submit comment