Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke, ki tashi da jin dumin uminki a cikin jikin ki, ki rayu irin na kowata yarinya mai shekaru kananu irin naki?
A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai kirjinta ta duka ta mana mata kiss a goshinta ta kuma ayanna" ya Allah, kar ka jarabemu da aure aure, wato ka sa dukanmu idan mukai aure ya zama mijinmu shine wanda zai birne mu, Allah kar ka kama mu da halayan mahaifinmu na yawan auri saki, ka sa mu zauna komai rintsi mu rayu da y'ayanmu

Jikinta sanyaye itama sanye da kayan bacinta dogon wando sakake sosai da riga budadiya sosai ta fada saman bed din ta kara rungume kanwar nata kafin ta amsa kiran saurayin nata dake ta maido kiran

Yana nan zaune sai da kowace ta shiga dakinta domin dare ya tsala sosai har sha biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya fita ya ja kofar bangarensu ya nufi nasu shi da kanninsa

Tana shiga dakinta ta cire rigar jikinta

Shafafen cikinta da ta gama cin pizza aman sam bai tasa ba ta kala tana shafawa ta ce" Alhamdulilah na koshi

Mika ta yi ta shige bayi
Wani wankan ta sake daurowa da alwallah sannan ta kuskure bakinta

Tana fitowa eigar sallarta ta saka ta yi shafa'i da wutiri ta yi adu'a ta shafa

Cire kayan ta yi ya rage mata daga ita sai pant, ta dauko bras kadai ta saka domin a rayuwarta sam bata iya baci da kaya masu nauyi, ta fefeshe jikinta da turare ta shafa humura

Madarar da ta kwaba da tumatur din danye ta shashafa a fuskarta kafin ta haye saman lafiyayan bed dinta mai sasaukan shinfida

Sama take kallo kanta saman matashin kan dake ajiye dan kar ta goge abin domin bai bushe ba
Gefe daya kuwa wayarta ne ta shiga shating da tarin samarinta wa'inda ita kanta ba zata iya irgasu ba

Dakinsa daya da kanninsa dan sam bai raba daki da shi ba, gadonsu ne dai daban daban

Sai da ya shinfide shi domin ya yi baci

Sannan shima ya shiga bayi ya yi dukan uzurinsa ya fito
Baki daya yayan MUTALAB sunna da wata irin tsafta da kuma rikon adini, shima sai da ya yi raka'a biyu domin ya yi nafilarsa kafin ya kishingida da wayarsa a hannunsa

Message ya tura kamar haka" Allah ya huci zuciyar kanina


Har ya cire rai da zai bashi amsa domin lokacin karfe kusan daya na dare ne, sai dai cen ya ga amsarsa kamar haka" wata biyu ne ka bani DAYABU

Murmushi ya yi dan ya san dama baya so ya kire shi da kanninsa,

Wani message din ya dora kamar haka" na san ba zaka kulaceni da yawa ba idan ka yi duba baki daya kanena tamkar y'ayan cikina na dauke su, ina kokarin basu kariya da dukan karfina....ka gafarce mu

Nanma ya jima sosai kafin ya bashi amsar cewa" Allah ya shirye mu

Da sauri DAYABU ya dora" amen ya Allah
Sai kuma a kasa ya dora" ka yafe mata, yarinta ce, na mata fada ba zata kuma kai hannunta jikin Zinaria ba

Ya buda message din, ya karanta sarai, aman sai ya ki bashi amsa
Hakan ya sa hankalin DAYABU ya kasa kwonciya, yana rike da wayar a hannunsa ya kasa samun baci, yana tsoron yaki yafe mata ya rama ta wani wajen, yana matukar tsoron shirun Sarkin nasu wanda ake kasa gane inda ya dosa

Shi kuwa sarki dama ba sauka yake ba domin sam baya kashe data , wayar ya ajiye gefen abin bed ya koma a hankali ya kwontar da kansa ya lumshe idannuwansa yana tunnani

Murmushi ya yi yana girgiza kai da takaicin yarinyar cinkushe a kasan zuciyarsa
Kwarai ya ga karfin halinta, ya kuma yarda cewa bata da kunya
Ya kara yarda da shawarar da ya yiwa kansa cewa sai ya koya mata hankali a duniyarta

Zinaria dake falo yana jiyo shashekar kukanta, domin yana zuwa zai kwonta ta zo ta tsaya tana kukan a gabansa aka mareta aman ya kasa datse hannun wanda ya maretan?
Hannunsa kawai ya daga mata ya yi mata nuni da ta tafi, domin sam baya iya hakurin jiyo koke koken nan

Wani murmushin ya yi a kasan zuciyarsa ya ayanna" bayan batawa zuri.armu sunna da take faman yi a cikin garina, yana jaza mani zagi dan kawai mahaifiyata na kanwar mahaifinta ana kiranta da kanwata na zuba mata ido tana tabara, irin yanda wasu ke tunanin samun dagin kafa dan sunna soyaya ko watsewa da ita, shine yau zata nuna gwarjinina baya kaiwa gareta? Shine yau zata nunan ita jinnin shuwa arab ce ta hanyar daga hannunta ta mari matana a gabana?

Kansa aya girgiza yaumshe idannuwansa yana tunanin tafiar da zai yi ya kai yaronsa waje, Aliyu bashi da lafia yana fama da rashin lafia mai tsanani mai tashi lokaci zuwa lokaci
Yaron kan fita a hayacinsa ya mimike ya ringa wani irin zabura wani sa'in harma ya sume
Yaron na fama sosai yana jin jiki wanda hakan ke matukar dagwa mahaifin nasa hankali da kuma mahaifiyarsa wace ta dora dukan so da isarta a kansa cewa yarima ne mai jiran gado.....................

DAYABU kam sai da ya gaji da zaman jiran amsa ya fara gyangyadi ya ajiye wayar bayan ya kasheta ya kwonta a hannunsa na dama da tunanin da izinin Allah gobe daga wajen aiki zai koma cikin baban gidan ya same shi ya bashi hakuri

Tun da asuba kiran sallar fari mahaifinsu ya ringa bi daki daki yana dokawa da karfin gaske
Baya tsayawa su bude yake yin gaba domin yana cikin fushi da su, da da ne sai ya shiga ya ga tashinsu sun dauro alwallah yake barin wajen

Haka kowace ta dauro alwallah suka fito falonsu suka tayar da sallah

Bayan sun gama sun yi adu'o'insu du suka mike suka yi bangaren mahaifinsu zuwa lokacin har karfe bakwai ta yi

Du zama suka yi kamar yanda suka tarar da yayansu kansa sade

A hankali suka shiga gaishe shi, sai dai sam baya amsa masu yana ta danna carbinsa ya kure waje daya da ido

DAYABU ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" ABIH fushi zaka yi ta yi da mu ne? Ba zaka yafe mana ba bayan ka san bamu da inda zamu nufa mu ji sanyi?

Da haushi haushi ya dago ya kale shi ya ce" makaryaci! Makaryaci kawai, karya ne , ni zan matse maku waje ku kai karana a saka min laya? Ba ruwana da ku ba ruwana ku je ku tafiarku

Yar karamar cikinsu ce ta mike da dan karamin hijab dinta cikus cikus tana takawa ta je jikin mahaifin nata ta dora kanta a jikinsa ta yi luff tana sauke ajiyar zuciya

Shima hannunsa ya sa a hankali yana dan talabeta sannan yana bin y'ayan nasa da harara wa'inda suka sasada kawunansu kowane bai ce komai ba

Cen matarsa ta shigo ta dauki kwaliyar safe hannunta dauke da wani irin plat mai yannayin kifi marar nauyi mai kyan gaske da natsakaicin girma

Cikinsa gasashen kifi ne da soyayan dankalin turawa ta rufe shi da farar leda irin yanda ake nadewar nan

Cike da kissa ta duka ta ajiye gaban Abih
Ta koma wajen frij ta dauko ruwa ta dawo ta kuma ajiye masa tana ta takama irin ga matar ubansun nan ta zauna tana kokarin bude masa

Da kallo du suke binta ciki kuwa harda shi da kallon mamaki yake binta
Tsarin gidansa a irin wannan lokacin da y'ayansa ke zuwa gaishe shi a lokacin ake gabatar da kayan karin kumalon da ma'aikatan gidan ke girkawa tun da asuba
Nan suke haduwa su karya kafin du su watse kowane ya je ya shiga shirin tafia wajen aikinsa ko karatunsa

A hankali ya ce" ama yaya haka na ga iya wannan?

Sai da ta juya idannuwanta masu girma da kyau sannan ta ce" iya shi na basu umarnin dafawa

Da wani mamakin ya ce" aman ina abincin *Y'AYANA?*

Itama da wani irin mamaki ta kale shi kafin ta budi bakinta ta ce" y'ayanka fa Habiby? Y'ayan naka da suka kaika suka baka laya a gaban jama.a suka tozarta ka suka wulakanta ka? Y'ayan naka da basa tsoronka basa yi mani biyaya a matsayina na matar ubansu wato uwarsu? Na gaji da wahalar zuwa kicin ina ta faman fadin kowane irin abinda yake kari da shi, na gaji da jido masu kayan kari na kawo masu tun daga kicin su karya kulun, na gaji da rashin kunyar y'ayanka Habiby!


Da mamaki yake kallonta, ransa ne ya shiga tsale yana kunna, y'ayansa ne ta yi tsaye tana wulakantawa dan kawai an samu wannan yar matsalar? Ba ita zata dafa ba, ba kuma ita zata kawo din ba domin daga bakin bangarensa suke kawo mata ita sai ta idaso da shi ciki dan ba yar aikin dake shiga bangarensa
A hankali ya rintse idannuwansa yana kokarin control din haushin da ya kama zuciyarsa domin so yake ya nunawa y'ayan nasa fushinsa a fili dan ko gaba su kiyaye irin abin tozarcin nan da suka yiwa kansu da kansu wanda idan duniya ta ji su za'a zaga bale su matan da suka fi yawa harma suka kawo mizalin aure

Sai da ya samu ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu kafin a hankali ya budi bakinsa ya ce"






>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ>ØzÝ
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


3


Kafin ta ankara ta cire lafiyayiya, kwontaciya, farar fatar matar sarki da wani gigitacen mari wanda hakan ya saka baki daya wajen hankalinsu ya dawo kansu

Yaya DAYABU ne ya zabura ya mike tsaye sai dai hararan da Sarki ya Zabga masa ya saka shi komawa ya zauna jikinsa na rawa hankalinsa tashe

Kai Gimbiya ke jujuyawa a hankali ta saci kallon d'anta, kuma sarkin garinta
Ganni ta yi idannuwansa lumshe tamkar wanda bai ga abinda ya faru ba

Dubanta ta mayar kan yar dan uwanta, mafi soyuwa a cikin zuciyarta sannan wace ta fi horawa a kan laifukanta

Cikin tafiar takama da ta zame mata jiki ba da gangan take yi ba ta tunkaro wajen da suke tsaye wanda sai da NAJEEBA ta yi marin ne kuma baki daya jikinta ya kara kwasar rawa ta shiga jin kamar zata kurma ihu, sai kawai ta shiga yarfe hannayen nata tana matso kwalar da ta yi mata tawaye ta ki zuwa a irin wannan lokacin

Tana zuwa tsayawa ta yi tana kallonsu, idan ta kalli wannan sai kuma ta kalli wancen

Muryarta ta buda, kamar wace idan ta fito zaka ji wani tashin hankali da kururuwa, aa sai muryar ta fito da wani irin sanyi sannan tana kalkaltu irin na larabawa ta ce" Ya salam, yayarki kika mara?

NAJEEBA ta ringa matso kwallah aman ina kukan ya ki zuwa dan ta san tana yin kuka yanzu zata manta fadan ta dawo rarashinta domin ita kanta ta san uwar tasu na matukar son ta

A hankali lebenta na rawa ta ce" *ANMY* (wato mama), ta taba martabar iyayena ne

Gimbiya ta kalli Zulaihat dake tsaye dafe da kuncinta, a hankali ta ce" rama

Sarki dake jin dukan abinda ke faruwa ya kara dan muzkutawa yana sauraronsu

Kamar jira take ba wani kauce kauce itama ta daga hannunta ta dauke NAJEEBA da mari

Karar marin nan shi ya saka kanwar NAJEEBA mai bi mata wato Khairat zabura tana ruko idannuwanta da niyar tashi

Da sauri DAYABU ya saka hannunsa ya mayar da ita ya ringa yiwa kannen nasa gargadin kar wanda ya tashi, ya kara sada kansa kasa

Tun da ta mareta ido kawai ta rintse tana jin yanda jijiyar kanta ke harbawa
Da mamaki ta buda idannuwan nata ta sauke a kan hannun Zulaihat, gata dai farar mace, kana kallonta ka ga laushi sai dai hannunta wani irin tauri ne da shi kamar dutse wanda ba komai ya janyo haka ba sai mayukan bleating din da take shafawa fatarta dan karin haske a kan nata kamar yanda wasu buzayen ke yi ya hadasa mata taurin tafin hannu kamar mai kwaba suminti da hannun nata

Da sauri kuma ta maida dubanta wajen Gimbiya wace itama karan marin ya sakata saurin rintse ido da jin wani irin ciwo da daci a ranta, sannan mamakin rashin kunyar Zulaihat ya darsu a cikin zuciyarta, haka kawai take ayanna Zulaihat ba kara? Ba zaki yafe ba ko dan ni?

Juyawa ta yi bata kuma kallon fuskar NAJEEBA ba dan ta san zuciyarta zata karye ne

NAJEEBA kuwa kallon tsana ta bi Zulaihat da shi wace ke binta itama da kallon tsana harda na kyankyami kafin ta motsa labanta ta ce" kin mari *SHAHID* kuma sai na rama a kan *ALI*!

ido ta ruruko tana kallonta sai dai ba damar kuma tofawa da sauri ta juya ta fita tana jin zuciyarta kamar zata bale , ta yi rantsuwa ta maya ba'a yi yar talakawan da zata zagar mata miji da kuma yarima ba! Sai ta ga bayan wannan tsinaniyar bakar yarinyar mai bakar zuciya!

Kusa da yayanta ta je ta zauna wanda ke bin kuncinta da kallo zuciyarsa na karyewa, walahi baya son abinda zai taba masa kannensa, ko dan ya kasance baba a cikin gidansu, ko dan du yawancinsu iyayensu na fita sunna kannanu ne su bar masa yar jarirai ya raina? Du cikinsu ba wanda uwarsa ta rufa shekara hudu da shi, da wuri take tafiarta inda za'a bar masa shi kuwa ya raina domin mahaifinsu mai tafiye tafiye ne, sunna da masu raino aman baya iya motsawa yana tare da su hakan ya sa yake masu soyaya daya tak tamkar mahaifinsu, gani yake yama fi mahaifin nasu son su domin baya tunanin da shine wata mace ta isa ta shiga tsakaninsa da su ba!

Sai da ta saisaita nutsuwarta daga tsayen da take kafin ta karasa gabansu ta aniya neman zama a kasa saman kafet din

Da wani irin sauri SARKI wato mai martaba ya zabura daga zaune a saman kujerar falon ta alfarmar da yake ya tashi tsaye, da wani irin sauri ya karasa ya saka hannunsa ya tare ta

A tare suka tarota da sauran y'ayan
Sai a lokacin kukan ya zo mata ta fashe da kula tana rike da hannun Gimbiya ta ce" ANMY a kasa kuma?

Irin yanda zuciyarsa ke bugawa gannin majaifiyarsa zata zauna kasa bayan shi yana sama ya saka shi lumshe idannuwansa

DAYABU dake rike da ita shiga ta gabanta ya ce"ANMY ki rufa mana asiri kar ki zauna a kasa

Itama fuskar ta kwabe, wanda sai a nan na gano kwabewar fuskar nan ta NAJEEBA tata ce,
A hankali ta ja shashekar kuka ta ce" ku barni mana, ku barni na zauna kasa nima ya zo ya saka min layar, ku barni ya zo ya mana tsakanin nima kar a je na cuce ku a zamantakewar yau da kulun

Kanta take girgizawa da sauri ta shige jikin Gimbiyar ta rukukumeta ta cusa kanta a kirjinta tana ta juya kanta tana nufin aa, aa

Gimbiya ta kara riketa da kyau a jikinta, ga hannunta na dama dake cikin na SARKI ga kuma DAYABU da ya koma gefen hagu shima ya riketa da kyau, ga sauran yaran du sun zagayeta kowane ya kama kunnensa ya rike

Idannuwanta lumshe ta ce" so kuke ku kashe min shi shima ya kasance bani da kowa? Ai gwara ku hade mu ku kashe sa8 ku huta ya ku y'ayana

Du kansu suke jujuyawa cike da dana sani

Gimbiya ta ce" yaya zaku kawo karar mahaifinku a cikin bainar jama'a? Koma me kuke tsoro shin baku yarda da Allah zai kare ku bane ko kun fi yarda da tozarcin? Yaya ina tashin tsakiyar dare ina rokan Allah ya raba ku da bakin duniya irin yanda kuka sha jinnin rigima aman kunna kara janyowa kunna hada kanku da su? Kai kuwa da na yi hannin ku tozarta mu sai ka nunan ai adalci aka nema ka je ka yi gaban kanka ka zaunar da yayana a gabanka ka bashi laya?

Da sauri NAJEEBA ta kara riketa ta ce" Anmy, Layar fa ba a cike take ba, ya zare abubuwa a cikinta

Da sauri ya kai dubansa keyarta da dan kwalinta ya zame ya fadi sai gashin kanta dake waje wanda yake daure da dan ribom a sama sama ya zubo sosai
Mamaki ne ya kama shi na yanda aka yi ta gane Alkur.anin ba a cike yake ba, ko wani ne ya fada mata?
Kai ina da wuya a cikin mutanensa wani ya fitar da sirrin, hasalima liman baba ne ya cire abinda ya cire a ciki daga baya kuma ya mayar da shi yanda yake , wanda sun yi haka ne daga shi sai shi sai Allahn dake kallonsu
Idannuwansa ya lumshe yana jin mamansa na tambayarsa wai gaske ba cikaken bane?

A hankali, a karon fari kennan da ya budi bakinsa tun farko cikin wata irin murya mai dadin sauraro da nitsar da firgitace ya ce" Na'am

Wata ajiyar zuciya ta saki a hankali ta janyo shi ta hade shi da NAJEEBA dake jikinta ta gefenta ta kuma janyo DAYABU ta dayan gefen ta hade su ta rungume su tsam a jikinta wanda hakan ya sa kwabrin hannunsa na gogan wajen wuyan NAJEEBA

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa na samun nutsuwa kafin ta sake su

Juyawa ta yi da NAJEEBA rike a hannunta du ta yiwa sauran nuni da wajen zama

Baki dayansu a kasa suka zauna, Banda Sarki da ya koma kujerarsa ya lume ciki ya lumshe idannuwansa

A hankali ta ce" yaya zaku biye mata koma me take maku ku fitar da sirrin cikin gidanku waje? Yaya kuke so hankalinmu ya kwonta a yanzu da tsufa ke riskarmu na zamu iya tafia kowani lokaci mu barku bari na har abada bayan kuna kokarin lalata kanku?
Ko da gaskiyarka a lokacin da aka saka maka shi sai jijiyoyin jikinka arba'in sun tsinke
Shine kai da girmanka ka tashi ka yi ja gabar kannenka da ka san cewa ko me za'a yi idan dai fada ya tashi sai sun yi ka zo ka tsugunna aka saka masu layar fada? Wato baki dayanku ku mace ko ku lalace shikennan ko?

Kansa ya kara sadawa ya ce" Allah ya huci zuciyarki

Hannunta ta buga gefen kujerar ta ce" ba wannan na tambayeka malan ka bani bayanin uban me take maku da ya karfina ni ka fada min na magance maku shi?

Rintse ido sarki ya yi a ramsa kuwa fadi yake" subahannalah, itama zata fitan kennan?

DAYABU ya kara sada kansa ya ce" Anmy, tana zargin ko mu ke hada mata fitinar da take yawan samun matsala da Abih, tana tunanin ko zamu hadewa yarta kai ne mu cuce ta, yajin nan da ta yi ta dawo ne da abubuwan nan wa'inda suka birkita mana lisafi
Yan uwanta sun zo har gida da laya za'a saka mana iya mu aman banda ita, mune kawai za'aiwa shingen nan kuma ABIH na kallo bai hanna ba saima fadi da ya yi cewa a core duka, a cire fada, a saka mana iya na magani kar mu yi mata magani domin ya yarda da tarbiyar y'ayansa, bama bin boka bare malan
Anmy to idan itafa ta mana?
Sasauta muryarsa ya yi ya dago yana kallonta da idannuwansa da suka cika da kwallah ya ce" idan ta lalata rayuwar kanena fa?

Idannuwanta ta rintse tana jin har wata zufar bacin rai na keto mata, a saka masu alkur'ani kuma yayanta ya yarda? Ta yayama za'ayi yo shi ya yarda bayan shima ya girma ga kuma soyayar kannensa da yake?

Gyaran muryar da SHAHEED ya yi ne ya saka kowa yin shiru harma suka kara sasada kansu, inda NAJEEBA ta lafe jikin Gimbiya ta dora kanta , a zuciyarta kuwa fadi take mai tsamin bakin ya samu da kyar zai yi maganar ko?

Sai da ya sha fama da mulkin dake cikin jinnin jikinsa kafin ya ce" samu gaskiya ne, haka kuma neman tsari ta hanyar adu'o'i da kiyaye sabon Allah da kadaice kai wa ibada gaskiya ne,

Sai da ya kusan minti biyar bayan wannan maganar yana sauke numfashi kafin ya dora da fadin" ba abinda ke samun nagartacen bawa face kadarar da Allah ya hukunta zai same shi, sannan na yi imanin zai zo masa da sauki a kan wanda bai rike adini ya yi imani ba

Dubansa ya maida wajen yaran baki daya ya ce" baku tafasa bama bale ku kone

Wani kakausan harara ya saukewa NAJEEBA wace ta yi gagawar lumshe idannuwanta daga kallon kyawawan idannuwansa dake bayane tun da ya fara maganar take binsa da kallo, a hankali ya ce" rashin jin magana kuma baya haifar da abin alkhairi

Dubansa ya kara maidawa wajen DAYABU ya ce" haba yaya, kai ka san menene girman hukucin alkur'ani kuma har ka yarda a saka a cikin gidanku?

Ajiyar zuciya ya sauke ta girgiza kansa ya ce" ba zan iya sakawa ba, ba dan na yi zabunta ba, sai dan Abu ne mai hatsari wanda bana garajen sakawa wanda bai malaki hankalin kansa ba


Numfashi ya yi ta saukewa yana hutawa doguwar maganar da ya yi sai ya kuma kallonsu ya ce" hukuncin bulala zata tabata ga du wanda ya fitar da maganar cewa ba cikake bane aka saka

Lale hukunci zai tabata ga duk wanda ya kara kokarin fitar da sirrin cikin gidanmu waje!

Du kawunansu suke gyadawa , sai da ya gamsu da hakan kafin ya maida dubansa wajen mahaifiyarsa ya sada kansa sosai ya ce" ALLAH ya huci zuciyar ANMY,

Su duka suka shiga maimaitawa a hankali sunna fadin" ALLAH ya huci zuciyar ANMY

Ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin dadin yanda suke da biyaya a gare su du kuwa da irin yanda suka kasamce masu fada da taurin kai da taurin hali

Da daidaya suka ringa tafia, inda Dayabu ya fara tserewa da yan kannensa uku domin baya son a barshi daga shi sai kanninsa kuma warinsa sannan sarkin garinsa a wajen nan, dan ya tabata yanzu zai titsiye shi ya karasa sauke masa laifukan da ya aikata

Kanta ta kara shafawa ta ce" daga nan ina zaki je ne NAJEEBA?

NAJEEBA ta kara kwontar da kanta a jikinta a hankali cike da kasala ta ce" ANMY, zan je gida ne kawai

Murmushi ta yi ta dago habarta, hakan ya sa ta dago manyan idannuwanta masu dauke da kwali da kuma karin girar ido, dan bakinta kuwa dauke da jan baki kalar lebenta da dan man lebe daidai da ita yana sheki

Hannunta ta saka ta kara goge mata dan hawayen da ta zubar saman kyakyawar fuskarta da bata da digon hodo ko daya a jiki

Cike da kulawa da kauna ta ce" ki rike mutuncin kanki kin ji? Darajar mace mutuncinta yarinyata


Shi kuwa a kasan zuciyarsa ya furta " wani mutuncin kuma? Ko dama akoy matan dake da mutunci sama da daya ne?


Kanta ta daga a hankali tana jin kaunar maman nasu,
Gimbiya ta shafa wajen da ZULAIHAT ta mareta ta lumshe idannuwanta a hankali ta mana mata kiss a goshinta ta ce" Allah ya tashe mu lafia

Mikewa ta yi ta dauki jakarta, bata dauki dan kwalinta ba ta juya abinta da niyar tafiarta hakannan ba abinda ya shafeta

Gimbiya ta dan daga muryarta ta ce" mayafinki fa?

Juyowa ta yi ta dawo kusa da shi, domin mayafin nata ya take shi da kafarsa mai sanye da safa fara kar

Dukawa ta yi bata ce masa ya daga ba ta janye abinda harda dan kadewa ta yafa a kanta ta yi gaba tana juyinta yanda take so

Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai ya kalli Mahaifiyarsa a hankali ya ce" kin shagwabata, zata sha wuya kafin ta samu mai daukan haukanta, sannan marin matana fa da ta yi?

Murmushi Gimbiya ta yi ta ce" ku kai kararmu, sai mu fada cewa ai itama ta mare mu

Kansa ya girgiza yan murmushi kafin ya mike tsaye ya kara sada kansa ya ce" ALLAH YA HUTA GAJIYA GIMBIYA

Tana murmushi ta ce"
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*




Please Login or Register in order to submit comment