Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

take irin kar a gane mata jikin nan.

Murmushi ya kuma saki kafin ya nufi bayi.

Sai da ya tara ruwa masu zafi , sannan ya cire tawul dinsa.
Wanka ya fara yi dan tsaftace jikinsa ya cenza wani tawul din sannan ya fito cikin nutsuwa.

Dan tsayawa ya yi gannin ta sauko k'asa tana ta son mik'ewa.

A hankali ya k'arasa inda take ya kuma dan dukawa dan d'aukarta uwa wata yarinya k'arama.

Najeeba da idanuwanta ke bud'e ta kuma rufewa da sauri jikinta bai daina b'ari ba, muryarta a ciki ciki ta ce" dan Allah kar ka tab'a ni, ka barni zan iya da kaina."

Bai dai ce da ita komai ba daukanta ya yi ya nufi bayin da ita.

Kallon ruwan yake yana tunanin ciki zai sakata? Bai tab'a dan ya samu mace a budurwa ya gasata ba, bai taba dan ya wahalar da mace ya kula da gashe gashenta ba, yakan yi kokarin ya kirayi wani baba naki ya taimaka maki, aman yau sai yake jin me zai hana ya kwatanta?

A hankalo ya idasa ya rage tsayinsa kafin yake tsumbulata cikin ruwan.

Wani ihun ta saki tana ririk'e hannayensa had'i da k'irjinsa.

Tun jikinta na wani irin bari har ruwan ya idasa ratsata kafin take sasauta masa rik'on da ta yi masa
cike da muryar kuka ta ce" Ban tab'a jin kyamar rayuwata irin ta yau ba."

Idanuwansa ya lumshe yana sauraronta
Idonta ta bude da kuka da dan ihu ihu ta ce" ka daina kallona, ban san me na tsare maka a duniya da kake yiwa rayuwata katsalandan ba, ka sake ni na roke ka."

Idanuwansa dake kanta ya kara d'orawa a leb'unanta.

A hankali ya kai hannunsa cikin ruwan ya ji ya rage zafin, bude wajen gudadar ruwan ya yi ya tafi kafin ya kamo mesar ruwan ya kunna na ruwan zafin.

Sai da ya zuba a hannunsa ya ji tana iyawa sannan ya yi kasa da shi ya ci gaba da cika jakuzi d'in.

Ita kam kuma hade kanta ta yi da gwuiwarta, so take ta kukurma ashar kala daban daban aman ta kasa domin dai ashar dai yaya DAYABU ya hanna su yiwa ko k'annensu bale baba.
So take ta dago kanta ta fafad'a masa magangannu ta k'asa, kwata kwatama ya cika bayin baki daya ya gaje ko'ina ita ko numfashin kirki ta kasa.

A hankali ta ji ya ce" me yasa kike so na sake ki?"

Dago dubanta ta yi ta sauke kakausan kallo a kansa ta ce" Dan na tsani aurenka, bana son ka!"

Sai da ya sauke yar ajiyar zuciya kafin ya ce" toh fa, nima ai ba son naki nake ba kau?"

Kuturun kare, tabdijan, sai ta ji abin ya mata ciwo, yo ita tunda take anya wani namiji mai lafia ya tab'a furta mata baya sonta?
Sai da ta firfito idannuwanta ta budi baki a hasale ta ce" kan......

A sanyayen ya ce" ki rage k'arfin muryarki mana, kar ki fad'i wata muguwar maganar da zata saka na cenza shawarar k'yaleki a wannan daren."

Ido ta ringa binsa da shi, a sanyaye yake budar bakinsa ya yi magana, a sanyaye yake binta da wani sansayen kallo.

Shima ita d'in yake kallo, *bana son ka*, kalmar nan ta masa nauyi a cikin ransa, bai san dalili ba aman ta masa tsauri da yawa, yafa san cewar bata son nasa, ya kuma san wanda take so aman du idan ta kara jadada lamarin sai mamakin abin ya tokare makoshinsa.

Me ya yo zafi haka? Yau gashi zaune, a arha a irin lokacin nan ya zauna yana kallo ana furta masa ba'a sonsa? Idanuwansa ya kuma budewa a kanta, maganganu ya yi a lokacin da yake saduwa da ita, tabas ya kayatu da wani lamari mai girma wanda a kallon da yake mata a haka da ace zai iya kuma damkarta idan har zata masa shiru da kalaman tsana kuma zata iya d'auka, ba abinda zai hana shi mayar da ita doki daga nan har safe.

Hannayenta da ta hade ya saka shi tsayar da tunaninsa.

"Tunda kaima ba sona kake ba, tun fil'azal nake ganin k'iyayata a tatare da kai, nima inada wanda ke jirana, me zai hanna ka sawake min?"

Sai da ya aika mata da killer smile kafin ya ce" saboda bana so ran su Anmy ya b'ace, kin kuwa san irin yanda suka ringa rokon na kawar da kai a yarintarki?"

Kai? Kai? Kai? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ta fada tana mai fashewa da kuka.

Mik'ewa ya yi daga tsugunon da yake lura da ya yi ta fara kawo hankali yanzu so take ta nuna masa taken rashin kunya, so take ta hargitsa masa tunani, ao take ta hanna masa kyakyawan nazari bayan yana so ya kadaice kansa, so yake ya zauna ya yiwa kansa fada
So yake ya idasa baje lamarinta a rubuce ba a cikin kwonyarsa ba
So yake ya faro labarin daga tarihin rayuwarta
So yake ya gane, meye sirrinta? Me yasa ta ringa fade faden samari? Me yasa take nunawa duniya ita din wata aba ce da ya dace duniya ta kyamata? Me ya sa ta mayar da namiji wani abin da take iya takewa? Idannuwansa ya rintse a lokacin da ya zo fita kunnayensa suka jiyo masa muryarta sama sama tana fadin" walahi, sai ka sake ni! Koma me zai saka ka sake ni sai na aikata! Ba ance zina da kisa ke sakawa ku yi saki ba? Sai ka sake ni, ni bana son farin mutun mugu mai cinye kudin talakawa!

A irin juyowar da ya yi ya lura cewar a tunaninta har ya fice domin kanta cikin cinyoyinta ruwan dake diga sosai yana kara jikata.

Irin yanda bak'ar fatarta mai haske ke haske wajen da yanda ruwan ke hauhawa jikinta da irin tsugunninta ya sanyaya cije leben da ya yi da niyar karasawa ya dagota da wuyanta ya hadeta da garun bayin dakin nan ya bambance mata sokayen da take farfadawa magana da shi! Tabas shi mijinta ne, aman karyarta ta sha karya ya zamo bawa a daka, shi sarki yake a kowace fada yana fatan hakan ya dore har ya daina numfashi

A hankali ya dawo, wannan karron maimakun ya tsuguna sai ya dan dafa abin, a hankali ya ce" da ace zaki iya aikata zina, da kin aikata kin rabawa gayu domin kuwa sosai kin karci wuyan shashashai,
Dan numfasawa ya yi yana gannin yanda ta zabura irin ta tsoratan nan da jin muryarsa a kanta ya kai hannunsa a hankali wajen idannuwanta hakan ya sa ta rintse idon nata da karfi.
Murmushi ya yi ya ce" ko wani irin aure ke kan matar da na aura, zan so ta kiyaye abu guda, *had'a ni da wani* dan cije lebensa ya yi ya ce" ki gane, Allah ya killaceki dan zai malakawa wanda yake killatace! .......Sai da ya kara cije lebensa ya kara rage muryarsa ya furta" kuma ma ni bana iya k'yale mace ta ringa min magangannu haka *koda ina sonta*!"

Gashin idanuwanta ya ringa shafawa a hankali yana kallon kyakyawar fuskarta wace a yau ta idasa k'awatuwa a idannuwansa
A sanyaye ya ce" hakama da haram d'in zan ciyar da ke."

Kara matsawa ya yi ya kai harshensa mai dan dumi dumi hade da leb'unnansa ya mana mata kiss mai zafi kafin ya furta" *nima bana son bak'ar mace ai*"

Yana gama fad'a ya kara mikewa yana jin kansa har sarawa yake, shara'a yake irin mai rikicewar nan , aman ya fi magana da hannayensa da gangar jikinsa da, idannuwansa
haka kawai fitsarariyar yar nan ta wani saka shi maida mata martani kamar mace?

Har zai fita ya juyo ya ce" saura na dawo na kuma yi maki wankan Janabar idan har kika kara d'aukan lokaci!"

Baki ta saki ta raka bayansa da kallo, wannan karon a kasan zuciyarta ta ayanna" Allah ya isana mugu, ai nima me zan ci da farin mutun? Nan da nan ka wani koma ja uwa k'osai, daga an yo abu fuska ta zame maka ja, ko rana ka shiga sai ta dafe maka fata, Allah na tuba na ci me a farin mutun banda mugunta me ka iya, ka ci nasara ta biyu a kaina aman ba zaka kuma gannina bama bale har ka wulakanta ni! Kuma na fada mai cinye kudin talaka, yo in ba cin haram ba ji bayin da ake wanka ko na Anmy albarka, sai na yi girki a wajen nan na ci, to na godewa Allah nima ba mabaraciya bace, da sana'ata bale har kaka naka yi ta kawo ni neman taimako."

Wankan take da ruwan masu zafi tana ta fadace fadacenta a kasan zuciyarta har ta gama ta dauki sabon tawul ta lulubama jikinta tana jin kirjinta na mata nauyi domin bata saba wanka tsakiyar dare haka ba gata da ciwon huka.

A hankali take takawa, du irin ruwan da ya ringa sakata ji take uwa ana tsikarinta da allura, haka kuma wani fayau take jinta uwa an wawushi wani nama mai yawa a kasanta.

A hankali ta idasa fitowa daga bayin tana sando, so ta yi ta ficewarta komai ahirun fadar da abubuwan tsoro yau a wajen Anmy zata idasa wayewa.

Sai dai tana fitowa ta ji an kama tawul din nata an shiga gogoge mata ruwan dake jikinta.

A tsorace take binsa da kallo har ya gama ya karb'e ya yi gaba da shi.

Da sauri ta nufi wajen da take gannin abin rufa dan rufe jikinta sai kuma ta rage tana furta" aushhhhhhhh!"
A k'asan mak'oshinta

D'akin ya d'auki dumi mai dad'in gaske sakamakon abin dumama daki da ya kunna ya kashe AC din domin ya san tana da ciwon Athsma ga garin ba laifi garine wanda daukan zafi du kiwa da irin manyan duwatsunsu

Lulubawa ta yi ta yi zaune a bakin gadon tana binsa da kallo dan gannin karshen gudun ruwansa

Shima saman kujerar dake facing din bed din, inda take zaunen ya hau ya zauna, sai da ya dan gyara zamansa irin na sarakai sannan ya kura mata ido irin yanda take kallonsa

Furtawa take" mugu, azalumi, mai kwacen abinda ba nasa ba, sai Allah ya saka min irin hararan nan da kake min, kuma na rantse daya bayan daya sai na tarda matanka na daki banza har dakinsu idan ya so ka kule ni a dakin kaji!

Shi kuwa fuskarta kawai ya kurawa ido, yana furta" inama ace baki da taurin kai? Da na kwatanta mayar da ke yanda nake son ki kasance, idan dare ya yi ki kawata min lokacina ta hanyar wankeni da bakon yannayin da kika sakani, shin me kike tunani? Yanda zaki yi da ni ko? To nan gani nan bari, kuma ba dai saki ba? Ba zan sake kin ba, tunda na ci wake a lambun nan, ba wanda zai ci irinsa, MAGE KAWAI MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI!

...........ma ji, ma gani, ma gane waye Magen tsakanin mutanen nan biyu........baci dai ya iya sata........kuma baya yafe bashi.

Talatainin daren nan ya faru cikin wani lamari mai wuyar fasara
Mutun biyu ne tsaye a cikin duhu, sunna magana wace bata fi a irga ba aman yannayin taba hannayensu ya fi yawa

A shafe nake, tun shekarar da aka so shafe shi ta same ni, gashi ya ajiye har uku yana bin daya bayan daya bayan ni nawa iyalan sun barni

Dayan ne ya furta" kai naka iyalan ai ka tara, ni ban tara ba, ba kuma zan tara ba har sai na rama!

Abubuwan hannayensu suka cenza kowane ya dauki hanyarsa suka shige ciki

.........................................
Kowa da irin shiryawar da ya fi ganewa da ita

Kamar yanda magaifiyarta ta fantsama neme nemen malaka, abubuwan da zata kasance ta malake shi sai yanda ta yi da shi, tana zuba tsabar dukiya tana amso yan kuli bisa yarda da ta yi cewar wanda ya bata kulin ya isa ya zartar da hukuncin abinda take so ita da yarinyarta ta dawo ta kuma dukufa ta ci gaba da dadaure Zinaria da kalamai irin na....ki turara, ki tsuguna, ki yi wanka, ki kurba, mu binne inda aka ce a binne, ina mai tabatar maki na lungu baya karya

Cike da kalaman nan har hankalinta ya fara dawowa jikinta, hakan ce ta kasance a yau tsakiyar dare suka fito suka yo bine binen, kafin ta bude mata abubuwan turaren ta saka mata
A lokacin da ta fara turaren ne ihun NAJEEBA ya karade wajen, wanda in dai ka kusanci bangaren tabas zaka jiyo sai dai ka yi kamar baka jiyo din ba

Wannan ihun ya kusan summar da ita harma ta shiga kuftayar son zuwa dan ta ga ko menene

Janta uwar ta yi, a lokacin suka hade da munafukin nan

Murya a kausashe Gimbiya ta furta" ko da rai, ko ba rai, ko da hankali, ko babu, ko da yarda ko da karfi sai sun bara maki fillin mulkin ki! Tana maganar tana idasa janta cikin bangarenta ne hankalinta du a tashe domin kuftaya Zinariyar ke yi kan lale lale sai ta je bangaren Sultan dake zazagaye da dogarai

Niyarta daya ta idasa shigewa falon da ita tana kara rike abinda ta amsa a hannun mutumen kafin ta shiga kai kawo yayun Zinariar na tambayar abinda ke faruwa

Rai bace ta ce " wani irin rashin mutunci ne za'a ringa jin ihun mace a bangarensa? Ba zai iya hannata ihun ba sai ya buda an san abinda ke faruwa da ita ko sallon iskanci ne tsagera ce itama wace yake taren da ita? Wacece? Me ta zo da shi? Tabas zan nemi mu je Agadez da Zinaria, dole zan kai y'ata na shiryata a wajen da zan yi abinda na ga dama ba tare da an dakatar da ni ba, dole zan nemi layin Sarki na fada masa rashin lafiyarta sai mun zo gida!

Su dai yayun nata sunna son danarta ne, aman sun san da kamar wuya mahaifinsu ya yarda da a zo da ita gida,

Zinariya kuwa bata taba jin tsana mai tsanani irin ta yau ba, bata san da wace yake tare ba aman abu daya da ta sani koma wacece sai ta ga bayanta, har ya kai ga zuwarma wata?
Gujin kuka take ido rufe hannayensa a daidai kirjinta
Hasko irin tsarin mijinta, sansanyan kamshin jikinsa, ni'imatacen laushin fatar jikinsa, takamarsa mai kara sakata macewa a kansa, kamshin bakinsa mai sanyi da saka nutsuwa, du ya anfanarwa wata? Sam bata son kawowa ranta cewar zai iya kusantar Najeeba, qbu daya take son tabatarwa cewar Nadia ce, idan kuwa ita din ce ta rantse sa hannunta zata kwakule mata du wani abin anfanuwa na jikinta! Ta tanata a irin yanda ta lura sam Najeeba bata cikin wa'inda zasu iya samun alfarmarsa, hakan ya sa ta yarda da maganar mahaifiyarta cewa ta sada kanta, ta yaki lamarin a hankali ta kasan kasa,
....................................

A hankali wani baci mai nauyi ke fuzgarta , ga ciwon da jikinta ke mata , a zaunen nan da take ita kadai ta san irin azabar da take ji a kasanta , ta luluba sosai har kuma zafi ya fara damunta aman ta ki sararawa jikinta sonin tsoronta Allah gudunta ta kuma rufe ido wa'innan idannuwan nasa masu dauke da kwali da wani irin launi da ya tsaida tar a kanta na sakata cikin yannayi na shaku da taka tsantsan

Daga inda yake zaune, bai taba kasancewa a nishadi irin na yau ba, dadin kallonta yake ji a kasan zuciyarsa, murmushi yake a boye wanda sam ba'a gani
Sarai ya san tana jin wahalar zaman nan, aman yana kallonta dan ya ga irin jarumtarta, ai ko da yar yatsa aka kaiwa wajen nan zihara za'a ji jiki bale uwar yatsa

Muzgutawa ta yi , baci na rinjayarta, kanta na kara nauyi ga ciwon da yake mata ta kwonta a karkace tana hangensa

Tun tana ganninsa har ya kasance kamar ta sume, ta daina fahimtar komai ta daina gannin komai, ta shige wani irin baci mai tsananin nauyi

Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen agogon dakin

Gannin karfe biyar ce ke shirin yi ya saka shi mikewa a hankali ya nufi wajenta.

Hannunsa ya saka ya gyara mata kwonciyar da ta yi ya kuma zubawa fuskarta ido na dan lokaci
" *Who are u NAJEEBA?"*

Karasawa ya yi bayi ya kuma dauro alwallah ya fito.

Kad'aice kansa ya yi ya shiga bautar ubangijinsa cike da nutsuwa mai girman gaske.

A inda yake zaune sai da haske ya fara nuna kansa kafin ya d'ago kansa daga dukufar da ya yi yana jan carbi.

Adu'a ya yi ya shafa sannan ya mik'e ya koma d'akin.

Tun kwoncinta ne dai bata juya ba, da ka ga kwonciyar ka san a takure take, a gajiye take.

Ya saba komai gajiya a irin lokacin nan yake shiryawa, du irin bacin da yake ji kuwa ba zai iya zama bacin ba.

Wanka ya tsalo ya dawo ya shirya kansa cikin shiga ta alfarma kafin ya fita ya yi zaune saman kujerar dake facing d'in wace komai ya wakana tsakaninsa da ita a tsakiyar daren nan.

Idanuwansa ya lumshe yana girmama lamarinta a cikin zuciyarsa.

*"SHAHEED, BANA SON KA, MUGU, BANA SON FARIN MUTUM, SAI KA SAKE NI, HUZAIFA."*

Kalaman nan ya yi wani waje mai girman gaske ya ajiye su,
zai iya rantsewa ko Anmy sai ta kakare take fad'in sunansa kai tsaye.

Ko da ranta a b'ace yake zata sanyaya muryarta cike da rarashi ta kwatanta masa.

A fannin mace kuwa, bai tab'a had'uwa da macen da ta kalleshi shi SULTAN SHAHEED ta kama sunansa gatsai haka ba, sannan a irin damk'ar da ya mata ta kuma duban idanuwansa ba.

Murmushi kawai ya yi, idan har bai zurfafa a sanin wacece ita ba , akoy damuwa.
.....................................


Hannunta da ta tokare gefen kumatunta UMMU ta kama ta cire tana kallonta ta ce" yaya wai meye wannan dan Allah?"

Anmy ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta wajen agogo ta ce" MARIAM, karfe goma ta gota bai yi kira a je a rako min yarinya ba, Maryam ko dai zuwa zan yi?"

Idanuwanta ta zaro cike da mamaki ta ce" Anmy, ki je ina? Sai ki je ki ce me ya tsayar maki da yarinya? Kin ga fa su Zahrau du sun yi wani iri yau na ga ikon Allah, ita Zahrau tun dazu jake fama ta tashi ga mai kitso da kunshi a shiga yi mata domin gobe walahi zata juya gidanta aman ta ki tashi da waya a hannu wai ko zai kirayeta? To cinyeta zai yi ni NANA MARYAMA? kun ga Bayan kun san yau DAYABU ke kawo yarinyar da yake nema kuma du sai ku wani baje a nan? Dan Allah ku tashi hakanan."

Jakadiya ce ta shigo ta duk'a ta shiga kwasar gaisuwa.

Du Anmy ta yi tsai tana jiran ta ji labarin NAJEEBA ne sai kawai ta ji wai MARDIYA ke neman iso

Da sauri ta kai dubanta wajen Ummu, ta kai bayan UMMU tana goye da NUSAIBA ne wace ke dan zazabi tana dan rigimar zazabin

Mardiya? Ta tabata yarinyar a yanda bata da kunya zata iya yin wani abin na rashin kunya, du abinda ke faruwa ita dai tana kiyaye abinda za'ace an yi da ita, du tsakaninta da yara suke fadace fadacensu
Aman tana tsoron idan har UMMU zata iya hadiye wani iya shege duda yanzun UMMUN ba irin ta da bace aman duda haka tana shakun UMMU.

A hankali Anmy ta ce" ita da waye?"

Jakadiya ta k'ara sada kanta sosai ta ce" Ita da wata mata ce wace zasu yi sa'anni, inaga ana yawan zuwa shara'a da matar wannan wace ake kira da wudiliya."

ANMY ta kuma kallon UMMU sai ta ga ta koma wajen Zahrau ta karb'e wayar hannunta ta nunata da yatsa a kausashe ta ce" ZARA MUTALAB , ko ki mik'e ki cire hijab d'inki a maki kitson nan ko na jibgeki na rantse a wajen nan!"

Da sauri Zahrau ta mik'e tana cire hijab d'in, muryarta a raunane ta ce" Ai da wuri yake kira a d'auko wace ta fara kwana b'angarensa, ai da wuri yake kira tun da duhu duhu, *ina NAJEEBANA? LAFIA HAR YANZU BA'A NEMI A ZO A RAKOTA BA KAR DAI A JE ABIN YA MASA YAWA NE UMMU?"*

Ummu ta saki baki gannin zata tona masu asiri dan kawai ta firgice.

Anmy ta kalli jakadiya ta shiga tunanin me zata ce mata? Baki daya y'ayan na nan, Dayabu na hanya uwa uba UMMU, NAJEEBA na iya shigowa yanzu ko idan an jima,
Shin zata yarda ta shigo bayan ta santa da neman fitina ta tada mata rigima a irin wannan lokacin ko zata hannata shigowa ne?

A sanyaye Anmy ta kuma kallon jakadiya dake jiran amsa kafin ta bud'i bakinta ta ce"...>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



45

A sanyaye Ammi ta ce "Ki shigo da ita"

Har ta mike za ta fita Ammi ta kuma faWin "Ki kai gaisuwata Sangaren Sultan"

Kuma Wukawa ta yi cike da ladabi da biyayya ta amsa kafin ta tafi.

Ba'a Wauki lokaci ba suka shigo.
Wata irin kwalliya ce jikin Mardiyya, ta sha wani rantsatsen lesh an yarfa mata mak'up

Tunda suka shigo hankalinta ya tafi wajen yaran,
Bayan wacve ke goye da Nusaiba kawai take iya hangowa, Ummu kuwa na tsaye ne tana nuna irin kitson da za'a yi wa Zahrau.

Zama suka yi saman kujera sannan suka shiga gaishe da Ammi

Ammi ta amsa masu cike da kulawa tana Wan satar kallon yaran , sam ba wadda ta yi yun™urin gaishe da Mardiyya, ko damuwa basu yi da ita ba
Kwarai bata ji daWin hakan ba duk da mutum shi ke janyowa kansa mutumci ko akasin hakan, amman ai tarbiyyarsu fa?

Sai da ta sadda kanta a hankali ta ce "Allah ya taimake ki, dama kan maganar Abban Nusaiba ne na zo, kwata kwata ya zubar da ni, ya yi block din numbobina ba gabaWaya da nake samunsa, hatta Mama sai da ta saka a neme shi amma ya ki zuwa, gashi ni ba sakina ya yi ba"

Dan saurarawa ta yi ta dan dago dan gannin shin tana sauraronta?
Gannin Ammi na kallonta da kyau ya saka ta ci gaba da faWin "Idan laifi na masa tsakanina da shi ai ya ci ace ya yafe, idan kuwa fadana da yara ne ba ruwansa ya fita a ciki domin tsakanina da su ne"

Da mamaki Ammi ke kallonta a kasan zuciyarta kuwa faWi take
'Ikon Allah, wai ita a gidansu ba'a fada mata ka so mutun ka so d'ansa ba?'

Dubanta ta kuma kai wa wajen Ummu dake dan jijjiga Nusaiba, ko nauyinta bata ji haka take jibgata a baya ta yi ta jijjigawa, a yan kwanakin da ta yi da yarinyar ta matukar sabawa da ita domin yanzun Mama sak take kiran Ummu da shi kamar yanda sauran yaran ke faWa.

Mikewa ta yi ta nufi wajen
Muryarta a dan dake ta ce "Sannu fa?"
Dakatawa Ummu ta yi ta juyo daga wajen yaran dake ta mata surutu

Ido cikin ido suka kalli juna, ita dai bata santa ba, sam bata taSa haWuwa da ita ba, ko hotonta bata sani balle ta shaida ta.

Ba wata shigar firgita mutum ce a jikin Ummu ba, domin riga doguwa ce sakakkiya baka a jikinta
Sai dai yannayin tarin kamalar da fuskarta mai cike da yalwataccen gashi da Wan murmushi ya saka Mardiyya jin shakkun yi mata magana a gatsai gatsai
Dan haka sai ta dan kakari murmushi ta ce "bani ita na rarrasheta ko zata yi shiru?

Kallon da Ummu ke mata dan ta fahimci ko wacece ita, sarai ta san matar ta hoto amma ko ita bata taba haWuwa da ita gata gata ba

A hankali ta ringa kunce goyon kafin ta juyo da Nusaiba ta mika mata ita

Da farko idon yar a rufe yake, hakan ya sa ta yo lufff a jikin Mardiyya, sai da Mardiyya ta ce "A'a, bata da lafiya ne? Jikinta zafi haka me yake damunta?"

Jin muryar ya sakata buda idannuwanta
Kallonta take kafin ta fara rigimar sai ta koma wajen Ummu (idan baku manta na Nusaiba yarinya ce karama, ko a haka
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment