Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawama a cikin gidan kurkukun k'urya ya tabbata a garemu, GURNANIN ZAKI ne ya kira wayana da kansa kuma hankulanmu tashe ban duba ba na daga du ya ji abubuwan da muke fad'a."

Zuciyarsa ya dafe cikin tashin hankali yana jin cikinsa na murd'awa dan mad'aukakiyar tashin hankalin da ya hangowa kansu harma bakinsa ya kasa furta komai.

Mik'ewa yayi ya damk'i hannunsa yace " Tashi mu kuma bin waje wajen da ta saba zuwa, dan ina mai rantse maka ba zamu taba komawa fada ba tare da ita ba!"


Murmushi tayi da jus d'in dake ajiye saman lafiyayen table din da aka jera masu kayan k'walam da mak'ulashe.

Cikin wani irin shauk'inta yake , cikin dabara yake d'an k'ara kusanta kansa da ita yana mai kasheta da kallon soyaya.

Cike da farin cikin ganinta yace "Ban san a kan wani dalili yayanmu ya hana mu ganin junna ba, yace min zai waiwayeni har yanzu shiru, Najeeba ina jin tsoron kar a je ya hana min ke?"

Najeeba ta dan yi murmushi bata ce masa komai ba, hankalinta du yana kan agogonta so take ta mike aman kuma kar ya ga tana wulakantashi da yawa bayan uban nacin da ya ringa mata su hadu koda wani wajen ne bukatarsa ya ganta ya yi missing din kyakyawar fuskarta fiye da tunaninta hakan ya sa ta tsara fitarta yau du ta ringa yarda da yan kwaliya da masu gyaran jiki tun safe take cin wahalalen aiki wajen ya rikice sai shiga ake ana fita sannan ta ki kunna fitilar waje, sai da wajen ya zama sun daina duba wanda zai fita ko wada zata shiga tana hankalce da su kafin suka cenza sutura da AIDA ta fice fittt tamkar Aidar ce ta fita dan takan aiki Aidar siyo wani abin

"Lokacin komawarki ya yi ko?" Ya tambayeta cike da kulawa.

Najeeba ta sakar masa murmushi tace " Ka san doka ce, kayi hak'uri ina ji a jikina zai waiwayeka soon."

Murmushi yayi yana mai jin dad'i har abokansa ya gayyata su ganewa idanuwansa dan su yarda cewar shi d'in fa ba k'aramin k'waro bane, yau shine ya kawo NAJEEBA restaurant.

Mik'ewar da tayi da doguwar rigar AIDA jikinta du bata jin dad'in kasancewarta a cikin rigar mutane ya saka shi mik'ewa shima yana kallon table d'in yace "Baby baki ci komai ba fa?"

Najeeba ta d'an girgiza kanta da jus d'in hannunta tace "Ba ga Jus na sha ba? Ka san bana iya cin abu a gaban mutane haka bana jin dad'in ci."

Murmushi yayi ya d'auki wani croissant ya nufi bakinta da shi.

Sai kawai ta kula kamar an yawaita kallonsu ba mazan ba matan wanda bata san dalilin hakan ba ko dan bata saba zuwa irin wajen takanas ta zauna ta ci abinci bane? Takan zo Abusa restaurant aman ba dan ta zauna ba, daga cikin motarta ake mik'o mata dukan abinda ta buk'ata , aman yau ita Najeeba dan ta farantawa saurayi ta shigo d'are d'are ta zauna saman kujera, hakan ya hanna mata nutsuwa jinta take tamkar a saman k'aya du bata fahimtar abubuwan da yake fad'a.

Murmushi yayi, shi baban soyayya ya kai bakinsa ya gutsura ya tauna ya had'iye yace " Ko tsoro kike a je na saka wani abu a ciki?"

Najeeba tayi yak'e tana d'an zama gefe tana d'an waige waige a sanyaye tace "Huzaifa tafia zan yi dare fa ya yi."

Murmushi yayi yace "Dan Allah manta da wani dare yayi, babbar yarinya da ke za'a wani d'ora maki dokar dawowa gida da wuri sai kace wata yar daji?"

D'an tsai tayi tana kallonsa, a k'asan zuciyarta kuwa fad'i take lallai baka da wayo, ai wayewar tawa bata kai wajen da zan iya bijirewa Gimbiya ba, sai ta daki hak'oran banza a zauna k'alau.

Ambatar Gimbiya da tayi ya sakata jin gabanta ya fad'i, firgigita tayi ta shiga wawurar jakarta mai d'auke da wayarta.

Dubawa tayi dan ganin ina wayar? Sai dai cikin ikon Allah bata ciki, hankalinta ne ya tashi ta mik'e da sauri ta kama hanyar fita.

Shima mik'ewar yayi yana mik'awa abokinsa wayarta da ya zare, ya yiwa kansa alk'awarin zai je ya binciki wayarta du wani d'an iskan saurayinta dake mata magana ya d'ud'ura masa ashar da zumar itace sanan ya masa kashedin sake shiga hanyarta, zai shiga wajen hotunanta da vidos dinta ya tura wa'inda sukai masa kafin ya yarda wayar ya siya mata sabuwa _(HATARA dai yan matanmu, waya ta zama balaki, tashin hankali, fitinar dake hanna kwonciyar hankali a wannan zamani, wasu yan matan kan yarda su ringa d'aukan hotunan wasu sasa na jikinsu haka kawai suna bari a cikin wayarsu wasun kuwa samarinsu suke turawa, zaka ga budurwa ta yi hoto rabin nonowanta a fili harshe a waje tamkar wata karya da k'walelen kai a fili tana wani langwab'ewa ita ga kyakyawa ta ajiye a allon wayarta, shin k'anwata, yayata, y'ata idan wayarki ta fad'i a titi ya kasance wani mugu ya tsinceta ya je ya yi anfani da abubuwan dake ciki, ciki kuwa harda munanan hotunan nan naki ina zaki shiga da ranki? Wani saurayin ya zo gidanku ne dan ya lalata tarbiyar iyayenki ya yi tafiarsa, wani ya zo ne dan ya wulakanta ki ya kara gaba, ciki d'aid'aiku ne suka zo dan soyaya idan wayarki ta fad'a hannun wanda kike wulak'antawar nan ya je ya fitar da vidio d'inki kina wasu irin abubuwa ke ba yar bariki ba ke ba mahaukaciya ba yaya kike tunanin zai yi da su? Dan Allah mu rufawa kanmu asiri da lamarin nan, wallahi, wallahi idan wani abu bai tona mana asiri ba wayoyinmu zasu tona mana Allah ya kare mu baki d'aya)._ Bayanta ya biyo da sauri.

Kusan motarsa take tsaye tana son bud'ewa.

Ta bayanta ya zagayo ya rungumeta a jikinsa hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i harma jikinta ya fara b'ari b'ari.

Da sauri ta ringa kiciniyar k'wacewa hakan yasa ya k'ara ruk'unk'umeta a jikinsa a sanyaye yana furta " Baby meye haka? Ki tsaya na ji d'umin jikinki a jikina, ba wani abu zamu yi da ke ba sai an mana aure aman irin yar rungumar nan ba zan samu ba? Ki duba fa ki ga irin yanda wasu ke tsotsar bakin junna wa'inda basuma kaimu wayewa ba aman ke sai ki ringa guduna?"

"Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ..." Najeeba ta fad'a da k'arfin gaske kafin ta tura shi tayi baya baya ya gamu da jikin motar.

Da sauri ya saketa gannin zata tara masa mutane yana kallonta da mamaki.

Rasa me ma zata yi ta yi, yanzu Huzaifa ne ya ruk'unk'ume mata jiki haka ya d'ora mata kai a wuyanta Idannuwanta ta lumshe tana jin wata tsanarsa na mamaye gurbin birgetan da ya fara.

A sanyaye tace "Wai ko wani namijin ma d'an iska ne, ko dai nice mai sifar yan iskan da bana iya tarayya sai da d'an iska? Wai kowa haka yake soyaya ko matar da zaka aura sai ka nuna mata akuyanci?"

"HUZAIFA." Ta fad'a a sanyaye hawaye tuni ya fara wanke mata fuskarta tace "Dama dan ka d'ana jikina ka shigo jikina har ka saka na kamu da soyayarka?"

Huzaifa yayi gagawar girgiza kansa ya mik'o hannunsa dan tab'a nata aman sai ta kauce da sauri tana kallonsa, shi yama rikice sam bai d'auki haka a matsayin wata damuwa ba, a kan me zata wani damu daga yar runguma, yo yan matan yanzu meye ba'a yi da su? Aman ita daga yar runguma ta kama kuka haka me take nufi da shi?
A sanyaye yace "Najeeba, ba fa wani abu na maki ba, rungumeki na yi a jikina wanda yanzu hakan ba wani abu bane , Najeeba aurenki fa zan yi ko kin manta?"

Najeeba ta d'an lumshe idanuwanta tana d'an girgiza kanta a hankali tace "Da ace ina yarda da rungume rungumen nan da baka tardo ni a haka ba, Huzaifa da ace ban d'auki irin haka a bakin komai ba da ina ga cikin biyu an yi d'aya, ko duniya ta d'ad'a ni da k'asa ko kuwa ina wani wajen da kai baka isa ka hango ni ba, dan na rantse maka tun ina da shekara goma sha hud'u nake tara samari, Huzaifa da ace na biyewa samari mun ringa soyayar zamanin da kake fad'a da na tara y'aya da yawa a duniya, duniyar ta gama yayina ko na zama rik'ak'iyar yar barikin da ba dai k'ananun yara ba sai manya." Tana gama fad'a ta juya a hankali ta shiga tafia a k'afarta.

Huzaifa ya waiga ya ga abokansa biyu na lek'e hakan ya saka ya ji kamar ya k'urma ihu a wajen ( kai, ta zo maka da sauki baka sha mari ba?)
Me ya sa ta masa haka? Shi sam bai ga wani abinda yayi na laifi ba, koda yake zai je ya gama aiyukan da zai yi a wayarta sannan ya je saloon dinta gobe ya shiga koda da gudu ne ya bata hak'uri, zata sauko ne abinda ta fad'a da bakinta cewar ta kamu da son sa?.

Sam bai bi bayanta ba, itama hakan ya fi mata alkhairi tana tafe tana share hawaye ta bi ta gaban comisaria ta kama tudun poste a k'afarta tana tafe tana had'a hanya tamkar zata fad'i k'asa.

Ficewarsu biyu ta hanyar da take bi aman sun kasa ganeta, sai da suka dawo da wani irin gudu suka lura da budurwar dake tafe tana had'a layi kasancewar hanyar itane hanyarta ta bi kullum idan zata koma fada.

Wani irin birki suka ci a gabanta, da sauri d'ayan ya fito hankalinsa tashe ganninta tana ta hawaye gashi ba kayanta ne a jikinta ba.

Bata kula irin rikicewarsu ba ta bud'a baya ba gardama ta shiga ta kwontar da kanta jikin kujerar
*da ban je ba, da ban ga wulak'anci ba, da ban ba da hanya ba, da bai rungumi jikina ba, ni Najeeba, ni ba yar iska bace* wannan abubuwan take fad'awa kanta a cikin zuciyarta har suka k'araso fada.

Su sun fita shiga damuwa domin sun san cewa an san basa tare da ita gashi sun d'ora lokaci sosai a kan lokacin dawowarta.

Tun daga yannayin Amintace suka k'ara sarewa har suka gama parking da motar ta bale ta fita ta nufi b'angaren Anmy su kuwa sun kasa fitowa daga cikin motar domin tsaye yake hakimce hannayensa rungume a k'irjinsa da yanayi irin na zaku ci ubankun nan yana jiran su gama k'umbiya k'umbiya su fito su tarkata su yo b'angaren SULTAN.



*Masha Allah*
[2/12, 6:58 PM] Ummu Sadeeq: >ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



33


Tana shiga ta tarar da Anmy zaune tana rike da wayarta

DAYABU na tsaye da wayarsa shima yana dokawa haka Abih na zaune aman kansa a kasa

Tana shigowa Anmy ta fara ganninta hakan ya saka ta mike da sauri tana fadin" NAJEEBA, daga ina kike? Waye ya daga wayana yake ce min na shafa maki lafia na bar kiran ki? Ina wayarki take? Me ya same ki?

Dayabu ya juyi da sauri yana kallon yanda ta yi wani irin turus sannan kukan da take ga kuma irin yanda jikinta ke bari gabansa ne ya fadi hakan ya saka da wani irin sauri ya karaso ya kamo hannayenta ya yi ciki da ita

Sai da suka shige daki ya zaunar da ita har jikinsa na rawa ya ce" daga ina kike? Kukan me kike?

Anmy da ta biyo bayansu ji take kafafuwanta sai bati suke kamar zasu rabu da gangar jikinta dan tsoro da fargaba

A kidime ta karasa shigowa tana fadin" wani ya maki wani abu? Wani abu ya same ki?

Fashewa ta yi da kuka tana zumburo bakinta ta ce" Anmy, wayata ce ta bata

Ba anmy ba, shi kansa sai da ya ji ya sauke ajiyar zuciya duda ba wani yarda ya yi da maganarta ba

Abih ne ya shigo ya zauna bakin gadon yana kallonta

A sanyaye ya dubi Anmy ya ce" Bilkissu, mu je

Anmy sai da ta kamo hannun Najeeba ta rike tana kallonta a sanyaye ta ce" wannan shine alfarma ta fari da zan nema a wajenki nurul khalb

Najeeba ta kurawa fuskar Anmy ido aman ta kasa tambayar menene har suka fita

Sunna fita Anmy ta ringa sintiri ta kasa zama, dama sun yanke sai dai Dayabu ya tarbeta da maganar dan shi kawai zai iya fatatakarta kuma ta saurareshi


Cikin daki

Na san karya kike da maganar dan an sace wayarki kike kuka, ki fada min abinda ya saka ki kuka tun raina bai baci ba

DAYABU ya fada yana kuma mai jin tsoron abinda zata ce ya sakata yin kukan

Sai da ta rintse idannuwanta wasu hawayen suka kara zubowa daga gurbin idannuwanta, cike da jin kunyar abinda zata fada ta shiga kwatanta masa abinda ta aikata wanda ta tabata sai ya babala mata mari aman kuma da ta rike ita daya ta yi ta jin haushi gwara ta fada masa ya wanwanka mata mari ko zai huce

Da mamaki yake kallonta kafin ya girgiza kansa a sanyaye ya ce " Najeeba, kin san irin darajar da Allah ya yi maki har kike aikata halaya irin na wasu sakakun mata? Najeeba kin kuwa san irin daukakar da Allah ya maki har zaki je ki zubda kanki haka? Najeeba kin kuwa san irin matsayin da Allah ya maki har zaki yarda wani sakarai ya rungumi jikin ki? Yaya aka yi kika kasance mai saurin sakarwa maza fuska bayan ke din kadara ce da ta fi lu'u lu'u daraja?
Najeeba nan da kwana goma idan Allah ya yarda za'a zafa fatiyar daurin aurenki da mutun mafi daraja da mutunci, mai girman mulkin da Allah ya nada tun a kannanun shekaru, mai zamani mai takawa da Alfarmar Annabi, mai watsa taron yan daba mai rikita taron tsageru, Najeeba zaki kasance daya daga cikin mata masu girman daraja wa'inda idan sun zo ficewa ake sada kai ba'a hada ido da su tsabar yanda Allah ya daukaka su ya darajanta su ya fitar da tarmamuwarsu ko da rana take kyali? Najeeba zaki kasance hakima, gimbiya, wace zata zama daya daga cikin wa'inda ko sarakai na jinjina mata kasancewarta matar daya kwalin kwal din sarkin da ya kafa tarihi, Najeeba yaya zaki yarda ki je wani sakaran da ko baran gidan nan ya fi shi mukami a damagaram ya kai hannunsa jikin ki?
*NAJEEBA, ZAKI KASANCE DAYA DAGA CIKIN MATAN MAI DAMAGARAM NAN DA KWANA GOMA KACAL* kike faman saka mu a uku?

Tun daga wannan kalmar kunnayenta suka dode ta daina fahimtar abinda yake fada har sai da ya dasa aya ya ga ta kurawa bakinsa ido kamar wace ta suma a zaune

Hannunsa ya kai wajen kuncinta dan gannin yana furya sunnanta a sanyaye ta kasa amsa shi ya shiga dan taping a hankali ta ce" Najeeba kina ji na kuwa?

Sai a lokacin ta yi wani firgigita ta farka daga summan zaunen da ta yi kafin ta kurawa fuskarsa ido a karo na biyu

Wani irin hantsilowa ta yi daga saman bed din ta fadi kasa har tana take doguwar rigar dake jikinta ta kuma dagowa

Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta kafin ta takarkare ta kwala wani firgitacen ihun da ya saka Dayabu saurin kai hannayensa wajen kunnensa ya dode lokaci daya kuma yana nufarta dan rufe bakinta daga wannan ihu da ta saka daya kwal ta ja shi da wani irin jan da ake yi kamar wace ke kiran sallah...






Happy juma'at jama'atul musulmi=Ø2Þ>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



34


Hannayensa dode da kunnayensa ya diro ya karasa inda take ihun nan
Yana zuwa ya saki kunnensa ya damke bakinta da hannunsa sannan ya saka dayan hannun nasa ya riketa da kyau

Sikewa ta yi, lokaci daya numfashinta ya dauke ta tafi luuu a jikinsa

Ido ya zaro cike da tsoro da mamakin suma ta yi?
Lalle ya dauki abin da wasa ashe har ya kai cen?

Jikinsa na bari ya samu ya kaita saman gadon ya shinfideta sannan ya mike ya karasa wajen kofar dakin

A hankali ya bude hakan ya saka Anmy saurin juyowa a lokacin da Abih ya rike hannayenta yana lalabata cewar kar ta shiga ta bari har su fito

Ummu da Ummulkhair dake tsaye jikin kofar ne suka kutsa kawunansu cikin dakin hakan ya saka ya basu damar shiga sannan ya maida kofar da sauri ya datse dan ya ga Anmy ta zaburo ta nufo wajen

Dakatawa ta yi kusa da kofar hankalinta tashe ta kalli Abih, a sanyaye ta ce" me ya sa ya hana min shiga? Baka jin shirun ya yi yawa ko wani abu ne ya sameta?

Abih ya kara kamo hannunta suka koma falo suka zauna, a sanyaye ya ce" mu yi jira, idan yana irin wannan hali da kannensa nakan basu dama, idan na saki mace na dauko wata haka muke shiga da su du su rikice, shi ke rufe kofa daga shi sai su, ban san ta yanda yake lalaba su ba, in sha Allahu zai lalabata (Ya Allah, du wani yaya da ya dauki girma ya kasancewa kannensa tamkar bango, wajen da suke kai kukansu ya share masu, wajen da sun san uba ne a gare su, Allah ka dafa masa, ka masa albarka, ka kare shi, Yayana JAMILU Allah ya kara daukaka baban yaya=ØOÜ=ØOÜ=ØOÜ)

........................................

Cike da tashin hankali Ummulkhair ta yi kanta, ita kuwa Ummukulsum ta yi bayi da gudu dan dibo ruwa

A rikice Ummulkhair ta ce" yaya, summa fa ta yi? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une daga fada mata ta summa yaya zamu yi da ita ta nutsu?

DAYABU ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Ummulkhair, kar ki yi kuka, kar mu saki ta ga rauni a tatare da mu idan ba haka ba na rantse zata botsare mana ne ya kasance mu dake son tirsasata ta amince da maganar nan mu zamu dawo mu goya mata bayan bata so,abinda bana fata sam, kun dai san wacece Najeeba, tana da karfi a cikin zukatanmu, rigimarta ta fi ta NUSAIBA girma dan haka na roke ku kar na ga wace ta wani zubar da hawaye

UMMUKULSUM ta share hawayenta ta shiga tofa adu'a a cikin ruwan sannan ta mika masa ta jingina da jikin gadon a sanyaye ta ce" eyah, Najeeba ta cika daukan abu da zafi, in ba wannan ba na zata zata kama ihun murna ne, meye a cikin auren Mai Damagaram? Ka ga kamar kaza yanzu ta zama daga abu ya dan daga mata hankali sai kawai ta summe

Zuwa ya yi kusa da fuskarta a hankali yana shafa mata ruwan nan

Kamar second goma yana dan shafa mata ruwan ta ja wata irin doguwar numfashi ta sauke kafin ta buda idannuwanta a tsorace

Ido hudu suka yi da yayanta, sai yayunta da du suka matso sosai kusa da ita

Da sauro ta janye hannunta daga na yayanta ta kai saman hannun Ummulkhair da take yiwa fushi aman tashin hankalin nan ya saka ta manta da wani fushi, hannunta ta damko tana kallonta ta ce" Ummu, mafarki na yi ko? Ki yiwa Allah ki samo wani faskare ko ki dauko wani birgi ki kima min na farka dan mafarkin nan sam bashi da dadi kar na mace a cikinsa

Ummulkhair ta sada idannuwanta tana jin kamar ta mayar da hannun agogo baya ta ce ita zata aure shi da wannan tashin hankalin da kanwar tasu ta shiga, shin tsoronsa ne take har yaka ko menene? Dama rashin kunyar tata a boye ne take yi ko meye?

Jiki a sanyaye ta saki hannun Ummu kafin ta kai hannayenta biyu duka saman kanta ta ce" kennan da gaske ne? Da gaske ake za'a min aure da shi? Da gaske kuke zaku yi min wannan abin? Yaushe aka fara auren dole a familly dinmu da za'a fara a kaina? Kun san ina da wanda nake so, har na gabatar da shi a gidan nan aman shine za'a min haka? Ku ce da shi bana son sa! Ku ce da shi kar ya soma halaka min rayuwa wayo Anmy, wayo Abih zaku halakani da kanku?

Da tsawa tsawa DAYABU ya ce" zaki mana shiru da fadin shirme a wajen nan Najeeba ko sai na tataka ki?

Sasauta muryarta ta yi tana kallonsa ta ce" yaya? Kai da kanka? Kai fa uba ne a wajenmu, kai din uwane a wajenmu yaya yau kaine kake son turani rami da kanka?

Idannuwansa ya lumshe yana control din emotion dinsa kafin ya bude ya ce" kin taba gannin uwa ta tura yaronta rami ne cherie (dear) ? Kin taba gannin inda uba ya kai dansa ga halaka kansa kalau? Na san kin san ba dukiya ko mulki ya saka mu yanke wannan hukuncin ba, ke kin fi kowa sannin ba wani kyale kyale na duniyarnan ne ya kaimu ga haka ba, me yasa ba zaki nutsu ki saurari kalamaina ki yi masu kyakyawar fahimta ba?

Najeeba dai kuka take har jikinta na rawa tana jan hanci ido rufe

A hankali Umulkhair ta dora hannunta gefen kafadarta ta ce" Najeeba?

Dagowa ta yi ranta a bace ta ce" ki bar kiran sunna na, kina kallo za'a min wannan abin ba zaki iya hannawa ba? Kina ganni aka ce ko ke, kin san sarai irin tsanar da ya yi min aman shine kika yi shiru aka dauke ni bayan kin san bakin cikine zai kashe ni a gidansa

A hankali take girgiza kanta tana jin tamkar zata fashe da kuka
Bakinta ta buda zata yi magana sai kawai ta kasa da sauri ta yi cikin bayin dakin ta duka tana kuka, a gaskiya bata san me ya taso mai tsananin girman da ya hadasa tsana a zuciyar Najeeba ba, ta rasa me ya sa zata yi tunanin dan ya halakata, dan an tsaneta ne, aka hadata aure da shi maimakun ta yi tunanin alkhairi
Tabas akoy wani lamari na rashin dadi da yake nuna mata ita sai ta fi ajiye hakan a matsayin dan tana yawan fitar da rashin jin maganarta a fili ne hakan ya saka yake mata irin haka
NAJEEBA a gabansa fa ta mari matarsa, NAJEEBA sau nawa zata kacame da fada a cikin gidansa ko a kofar gidansa a yi ta tashin hankali da ita bayan ta san labari zai kai masa? Idanma ya ji haushinta ai kamar ita take take dokokinsa ne mana, Allah ya taimaketa ta kasance wace Anmy ke yawan rokar Alfarmar ya kawar da kansa daga yarta? Akoy wata shara'a da ya taba zartarwa wace ta raka makociya, a wannan ranar Amintacensa ya yi mata wani duba wanda sai da hanjin cikinta suka motsa kafin ya furta" Hatara yarinya, ki saku daga mayen da ya kama ki idan ba haka ba zaki samu kanki a kabari domin kuwa ba'a hada ido da mai damagaram, ana ganni a gaban kowa ya daga masa hannu, hakan ya saka shi yin gum da bakinsa cike da gannin rashin kunyar yarinyar sannan an nuna a barta kar a hukunta ta

DAYABU ya kurawa fuskar Najeeba ido, gaba daya zufar tashin hankali da ta sakawa ranta ta jike mata fuska da abin hwaye tun daga gaban goshinta har fuskar baki daya hakan ya saka

Please Login or Register in order to submit comment