Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gasken baya son bak'ar fatar ba zan ga laifinsa ba, domin kuwa yanzu zamani ya zo da wani irin kida wanda ya saka mata hawa suka cenza salon takun kidan
Ba komai bane sai irin yanda yawancin maza suka fi son farar fata kan bak'a,
Zaki ji namiji ya furta shi fa farar ko maya ce, ko mahaukaciya ce yana so, koda bata da nasaba!, hakan ya bada gudunmuwa sosai wajen shafe shafen yan matan zamani, Najeeba, ke shaida ce irin yanda kawarki burinta ta taba magana da shi, sai kawai Allah ya malaka mata shi,
Wa'inda basu kaishi bama daraja sun samu ana wawarsu bale shi? Ki cire masa rawanin ki ajiye shi ba ko sisi na tabata jinnin Ammi da mai martaba zai kawatu a idannuwan da zasu furta: ko bashida ko sisi sunna so!"

Hannun Najeeba ta kamo ta rike a nata ta ce" zaki iya zama da shi?"

Najeeba ta kasa budar bakinta, du kuwa da irin yanda take son yin magana, sai ya mata nauyi na gaske

Zahrau ta ce" zaki amshi abinki cikin ruwan sanyi! Bakya son sa? Ai kin fahimci an wuce wajen so ko? Baya son ki? Zamu jaraba mu ganni......, matansa? Zasu yi yaki ne dominsa, kema kuma zaki yaki abinki .......kowa salonsa ya fishe shi"

Najeeba ta kifta idonta a sanyaye ta furta" bana son hada bawa da wata, ban taba tunanin kasancewata a gareshi ba, lalle Allah shi ke da byro da takardar bawansa"

"Hakkun, kuma a yi masa biyaya koda ba'a so a hakan za'a samu rabauta" Zahrau ta karasa fada

Da sauri Najeeba ta kamo hannunta tana kallonta, a sanyaye ta furta" ta ina zan fara? Ta ina zan iya wannan yakin? Aminiyata da kuma ZINARIA, wa ya fi so cikinsu? ta yaya zai dubi bak'ar fata bayan ga farare nan a gabansa?"

Zahrau ta yi yar daria tana jin sanyi a ranta, sannan a lokacin ta ga tsantsar yarintar NAJEEBA, wai ita nan ta yarda da kalamansa cewar ya tsani bak'ar fata? Sai ta tsinci kanta da kuma yin yar daria, tun a yau zata fara gwadawa, ita kanta ta fi so mijinta ya dawo da kansa su koma dan kawai ta maidawa Gimbiya maganar da ta yi cewar ya halarci auren nan dan zumuncin dake tsakaninsu na sarauta ba wai dan zai kara aure ba, bayan auren kuma ta furta mata lalle bakake kun fara kasuwa fa, aman ki koma mu gani.....tana son ya zo da kansa su koma sai ta tabatar cewa lalle bakaken sun yi kasuwa

A hankali ta ce" kan abinda kika fi kwarewa, ina so ki buga wasan da kike bugawa a kan kowa, idanma yana tunanin karantarki ya yi ya san ko wacece ke to zamu yi anfani da sannin nasa mu gwada masa bai san komai ba!

Najeeba kallonta dai take,
Zahrau ta mike tsaye tana mai kokarin kwontar da ita ta ce" abinda nake son ki kula wanda da alama idan kina tare da shi yake bale kansa shi ne *Harshen ki*, ki kiyaye furucinki, ki tsadanta muryarki da kalamanki

Kallon yayar tata take cike da wata kaunarta, tabas ita kanta da ta irga irin abubuwan da ta ringa furtawa sai ta ji wani iri, kamar wata wace aka kunna?

Abin rufa ta ja ta rufa mata har wajen wuyanta kafin ta yi murmushin tsokanarta ta ce" zaki iya jure kwana shida baki je turaka ba?"

Ido Najeeba ta zaro a dan rikice ta ce" Aunty fa"

Zahrau ta yi daria ta ce" yeah, zan rikita iyayenmu, da yan uwanmu dan fara gannin zargin da nake yi idan har gaskiya ne? Ko kuwa hasashena ne

Najeeba kam bata iya cewa komai ba sai rakata da kallo da ta yi kafin ta maido dubanta waje guda, wani irin dukan jikinta ke kwasa du idan ta hango shi a kasan idannuwanta, gaba daya jikinta sai ta ji wani irin yar yar yar take iya bude idannuwanta da sauri
.......................
SULTAN

Yana cikin aiki da computersa bayan ya gama da taron mutanen da ya gama da rigimarsu yan kasuwa ne sannanu da suka kawo karar junna kan a masu tsakani da junnansu bayan sun kasance makota ne sosai, wannan shara'a sai da ta saka aka kirawo manya manyan malaman da suka zo suka ringa kawo manyan ayoyi bisa hakan, dayan ne ya kasance mai neman fitina ko rufe ido ne? Sun hada makotaka da junna, layi daya aman sana'a ta zamo tak tak iri daya, kuma abin kamar da gangan yake yi domin baya tashi siyan abu sai ya ga dayan ya siyo ya zuba shima sai ya kawo da yawa ya zuba sannan da neman fitina ya rege kudinsa sosai ta yanda zai kwacewa wancen mutanensa sai daidaiku, yana yi masa haka sosai da sosai har asara yake saka sho tafkawa wanda karshe ya gane da wata a kasa, domin shima ba wani uban kudi yake sakawa kayansa ba, yar ribar da zai bi shi sai ya ki dorawa ya bada kayan a yanda ya sara, hakan ya matukar saka masa tashin hankali duba da shi din yanzu ya fara tashi yana ta kokari ne dan ya ciyar da iyalansa ya fi karfin yan matsalolin rayuwa, shi kuwa dayan shagonsa cike yake makil sannan zai kai ukun na dayan kuma sana'arsa wace aka fi saninsa fa ita saifa kayan abinci ne, aman tsabar neman fitina a yanzu ba abinda baya saidawa domin daga makocin nasa ya saro wani abin shima sai ya saro ya kima karya, sam baya so ya ga yana samun na rufin asiri shi kuwa abin ya kaishi bango ya maka shi a gidan sarki

Lamarin ya so ya ja daga sosai sakamakon mutumen da aka baiwa damar magana ya nuna Niger din shin ba kasa ce ta republic ba?, yana da yancin yin sana'ar da yake so da zarra ba satar kudin ya yi ba, ya dora da fadin ya san yancin kansa ba zai kawo shi kara kan wannan ba

Wannan lamari ya saka sai da ya yi kira ga manyan malaman fada da na garin baki daya, suka amsa kira kafin a fara gabatar masa da nasiha mai ratsa jiki, da manyan hujoji da ayoyin da suka zo da maganar haka, kafin ya samu ya gabatar da shara'ar

Hakan ya saka kansa ya dauki zafi sosai ga harkar kasuwancinsa da yake son zama ya hada kan irin abubuwan dake shigowa da irin abubuwan da aka fi muradi wa'inda yaronsa baba zai je shaina da kansa ya yi oder su

A hankali ya mika hannunsa ya dauki cofin glass mai dauke da jus din ananas ya kai bakinsa ya dan sha kadan kafin ya ajiye ya ci gaba da dane danensa

Yar karamar wayarsa wace yawanci ahalinsa ke nemansa ta layin ce ta dan motsa alamar vibration

Dauka ya yi ya duba
Sakon Zinaria ne, rabonsa da ita yau zai kai kwana hudu, sako ne tana son zuwa bangarensa idan ya gama hutawa

Amsa ya tura mata da ok kawai kafin ya ci gaba da aikinsa

Yana nan zaune a falon nasa kamar da minti talatin, har ya gama dane danen ya rufe ya daga kansa sama ya lumshe idannuwansa ya tsinkayo tafia daga corridor din dake kawota bangarensa

Bai daga kansa ba, har ta shigo ta karaso dan kusa da shi kadan

Kamar yanda ta saba ta zube kasa kanta a kasa ta jimke hannunta guda ta sanyaya muryarta ta budi bakinta ta fara magana kamar haka"

......................>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



48



Ta budi bakinta ta fara magana kamar haka" Allah ya taimaki sarki, Allah ya ja da rai ya ara maka nisan kwana, sannu da hutawa zakaran gwajin dafa, sannu da warhaka takawa"...................
Lafuzanta ne suka yanke sakamakon hannunsa da ya dora daidai bakinta yana kallonta

Idannuwanta ta dago tana kallonsa itama da duba irin na tarin soyayarsa da tarin jin haushinsa da tarin jin tsoronsa

Dayan hannunsa ya saka ya kama hannun nata dake jimke ya ajiye saman cinyarta kafin ya saka hannayen nasa baki daya ya dagota tsaye shima yana mikewar ya kasance sunna mikewa a tare

Wajen doguwar kujerar falon ya kai dubansa, sai dai yana kallo sai da aka hasko masa lamarinta mai girman gaske a idannuwansa
A hankali ya lumshe idannuwansa ya samu kansa da jin zuciyarsa na rike sunnanta a ciki ciki

Dubansa ya kai saman kujerar da kyau, idannuwansa sun hasko masa abinda ya sha'afa bai goge da kansa ba, dan murmushi yake jin na son kwace masa sai dai ya ki barin hakan ya faru ya gimtse fuskarsa da kyau

A hankali ya karasa wajen zama da ita ya zaunar da ita, sai kara sada kai take irin na girmamawa tamkar wace ta zo gaban sarakuwarta farin haduwar nan

Hannunsa na dama ya saka a nitse ya dago habarta yana dubanta
Muryarsa ya sanyaya sosai, sannan a rarabe a hankali irin ya yi niyar cadin da ita yau ya ce" haba Zinariana, shin bakya gajiya da kirarin nan da kike min bayan daga ni sai ke?"

Da mamaki take kallonsa, shi kirarin ne baya so? Ai ita kirarin nan shine karin fasa kanta da sakawa ta ringa taku daidaya, idan ana kodatan nan ko dogon fushi bata iya yi, kai ita da ko shi zai mata kirarin zata washe masa hakora ne!

Shaheed ya kuma dago dubanta ya ce" ki dubeni cikin ido, ki min magana da girmamawar da miji kan iya samu a wajen matarsa, yaya zan zama sarki a waje haka kuma a dakina? Oya yi min zancen soyaya"

Gaba daya wannan karron ta idasa kuro idannuwanta tana kallonsa, muryarta a dan rikice ta ce" zancen soyaya kuma? Da kai?"

Shima abin sai ya bashi daria a kasan zuciyarsa, sai dai bai yin ba ya ce" Zinaria da wa zaki yi idan ba da ni ba? Na maki tsufa ne?"

Sai kawai ta ringa kakare hada ido da shi, tana ta kare fuskarta cike da wani lamari na mamakinsa, shi sarki guda yake magangannun nan? Su an hore su da yi masa kirari da koda shi da fadin ya yi kaza ya fi wane, haka mahaifiyarsu ke yiwa mahaifinsu ko a gaban waye, ahine shi zai kawo wasu magangannu? Sai kawai ta ringa jin zuciyarta ba dadi sakamakon tunanin da ta saka mata a cikin kwakwaluwarta, 'yaya aka yi a da bai ce yana son soyaya ba sai yanzu? Ko dai wannan karuwar bak'ar yar ya fara kulawa?'
Sai da gabanta ya fadi kafin ta kale shi a tsorace, shi kuwa kallon irin yanda du ta rame, an yi mata kwaliya kamar yanda ta saba zuwar masa da kwaliya sai dai raka sosai ta bayana kanta a tare da ita

A hankali ya kai hannunsa, domin ya rigaya ya yiwa kansa alkawarin zai ta lalabata har ta saki, dan kuwa ya ga wani labari da aka yi posting na irin yanda mata ke ji idan za'a masu kishiya, da irin shawarwarin da namiji ya dace ya bi dan gannin ya kwontarwa da matarsa hankali ta dan nustu a kan maganar, a sanyaye ya furta" yaya jikin ki?"

Zinaria ta kara kikifta idannuwanta sai ga hawaye, a hankalin itama ta ce" jikina gayanan dai, shine na zo neman alfarma a wajenka, ina so mu je gida tare da AYYA a yi min magani sannan hankalina ya kwonta kafin na dawo"

Hankalinsa a kanta sosai ya ce" wani irin magani ne da ba zan iya nema maki shi a nan ba? Ko fita ta kama ni mai kaiki ne da kaina, wani irin kwonciyar hankali kike so wanda sai kin yi nisa da dakin mijinki?"

Du magangannunsa na yau, da irin tsayinsu, da irin yanda yake yinsu cike da kulawa na cutar da ita, domin har baki take saki tana kallon jajayen lebunansa da yake dan motsawa a hankali, da idannuwansa da suka cenza launi sakamakon gajiya yana dan lumshe su yana bude su a hankali, sai kawai ya ringa birge idannuwan ganninta

Ita kanta bata san lokacin da bakinta ya furta" NAJEEBA ta tare ne?"

Kama sunnanta da ta yi ya saka masa jin gabansa ya fadi kamar wani wanda aka kaiwa wawan dukan bazata,
A hankali ya kuma kallon fuskarta, a yanda ya kula ko a haduwarsu ta farko ita ba NADIA bace a gabanta Najeeba ce,
Haka kawai sai yake jin ransa ba dadi sakamakon rashin jituwarsu, yau kuma ya fara jin abin a cikin ransa, sosai da sosai

A hankali yar fara'ar da ya ringa saki ya shiga harhadeta, ba dan komai ba sai dan kawai ba zai iya barawa wata cikinsu daman kawo masa maganar wata ko tambayoyi a kan wata ba, idan sunna so sun hadu su yi kishin su, shi abin daria yake bashi sosai domin ranar da aka yi dramar nan har wani hura hanci ya ringa yi daga bayan rawaninsa a kasan zuciyarsa kuwa ya ringa tunanin dama hudu ya jera ya ga iya gudun ruwansu
Fuskarsa a hade aman bai daga muryarsa da karfi ba ya ce" shin ina iya saka tsorin kar zafin kishin ki ya kaiki wajen da zaki kasa gano hanyar dawowa?" (Lauje)

Idannuwanta kawai ta kura masa tana kallonsa, sam ta kasa bashi wata amsar kuma, zafin kishi ne? Inama ace ana yiwa namiji kishiya da ta gwada yiwa SULTAN ta ga irin nasa kishin, shin shi baya jin kishi a ransa ne? ( to fah )

Hannunta ya kamo ya rike a nasa ya ce" ke ce babba, ba zan taba bada kofar da wata zata wulakanta ki ba, ba zan iya wulakanta ki ba domin ke din ke na fara sanni, ina mai rokonki a yau kan ki sanyayawa zuciyarki, ina da abubuwan yi masu girma da yawa, idan har kika talafa min ta hanyar kwontar da hankalinki kika ja yan uwanki a kan akida guda wato zaman lafia da zaman aure, ina mai tabatar maki zaki fi kowa jin dadin zama da ni"

Ya dan tsagaita yana ta sauke numfashi kafin ya dora da fadin" idan kuwa kika kiya Zinaria, ban san a wani kalar zaki iya wayar gari ki ganni ba, ban san idan zan iya fama kamar yaro ba, ban san idan zan iya zubar da shirme kamar wani wawa ba domin sunna na raya"

Yana gama fada ya saki hannun nata da ya riko , ya yi kokarin tashi ya mike tsaye, hakan ya sa ash color din jalabiyarsa sauka kasa

Da ido take kallonsa, ta tabata, ta tabata kennan ya tare da yarinyar nan? Sam bata wani tsinci wasu abubuwa a cikin bayanansa ba
A hankali zuciyarta ta ci gaba da yin kunci sosai da sosai,
Tabas shawarar da wannan mutumen ya kawo masu koda kuwa sun kiya da farko zasu yarda yanzun,
Ba zata iya yarda ya tara da wannan banzar ba!

Da sauri ta kara neman alfarmar tafiyarta garin agadez

Yana jinta sai kawai ya yi biris tamkar bai ji ba, ya shigewarsa cikin dakinsa mai dauke da harkar takardunsa da abubuwan nemansa

Baki daya sai ta ringa cika tana hawa tana jin idannuwanta na neman kara rufewa, sam bata wani yi yinkurin binsa ko neman kara lalabashi cikin ruwan sanyi ba, saima ta ji ai wannan tsana ce da nuna halin rashin damuwa da ita

Ranta bace again ta fice a fallon nasa ta nufi wajen mahaifiyarta

Tana zuwa ta udasa ta zauna kusa da ita

Wayar da Gimbiya ke yi ne ta ajiye ta ce" yaya ya yardan ne mu saka a kawo mana tkt ?"

Da yannayi na zata iya fashewa da kuka ta ringa girgiza kanta tana daga idannuwanta ta kai kan yayarta daya da ta rage wace itama mijinta a yau ya mata magana ta karshe cewar idan ba zata dawo dakinta ba ta zauna, tana kallonta ta ce" baki daya ya cenza, kamar ba Sultan dina ba, yau ni yake cewa na daina yi masa kirari na masa hirar soyaya, karshema kan maganar bai tanka min ba tun bayan da ya nunan shima yana iya sama min ko wani irin magani na lafiata!"

Gimbiya ta ce" wani irin kirari kuma? A cikin dakin naki da shi kike masa kirari?"

Da mamaki ta kalli mahaifiyar tata, ta ga dai tsakaninta da mahaifinta kirari babu lokaci, to wace irin magana ce wannan?

Gimbiya ta ja tsaki tana fadin" shashashar banza, to ba dole ya gama rainaki ba? Wai ke daga ke sai shima hirarki tsakaninki da shi kirari ne? Arrrrrrr da ke walahi"

Yayarta kuwa banda daria me zata yi ta ce" Auta wai Allah da gaske kike?"

Du sai suka daure mata kai, maimakun kuma su zaunar da ita, su fahimci ai ga matsalar baba da take kara nisantata da mijinta harma su nemi maganceta cikin ruwan sanyi sai abin ya shashance a daria suka shiga neman layin mai martaba dan su bi ta kansa ko zai amince masu da tafia da Zinariar, sai sheda mata ake yana kan waya wanda ya makale da wayar Zahrau yana karbar caji da lamura dan ya kara mata kwanaki cike da shagwaba

........................
Cike da shagwaba Zahrau ta kara rike wayar hannunta tana hangen yanda du yan uwanta ke ta kai kawo dakin NAJEEBA tana dan murmushin gannin zasu ci galabar abinda suke so ta kara rage muryarta ta fan saki kukam rigima ta ce" ur excellency my happiness, idan har ka amince min ne, idan baka amince ba zan taso a yau yau na zo gareka, domin du duniya babu aikin da ya kai min naka daraja wanda ba zan iya takewa saboda kai ba"
Sai kuma ta dan ja shashekar kuka ta ce" Duda nice babba mace a cikinmu, kuma ina son na ga na bara masu du wani farin ciki kafin na yi nesa da su, bale Nusaibana yar jaririya da ita abin tausayi, ina so na je da kaina wajen mamanta mu sasanta huby"

Ido kawai tsoho ke lumshewa yana sauraron wani salo na son rokon alfarmar ta zauna a gidansu ta kara yan kwanaki, shi abin sabo ya zo masa
Tabas a matansa Gimbiya takan tsiri tafiar shakatawa a kadan ta yi wata haka kawai ta je wata dubai ko london ko hawai.....gari dai da zata more rayuwarta ta jima a cen ga kashe kashen kudi ga abubuwa dai sai hamdallah kafin ta dawo, ita kuwa dayar sai ta shekara bata fita ko kofar gida ba, aman itama idan ciwon gida ya kamata takan lula a kadan ta yi kwana hamsin wai tana hutawa domin tana samun balewa daga kusa da Gimbiya bata yiwa abun rikon wasa, tana morewarta daidai gwargwadon iyawarta

Sai gashi ita daga sati daya, duda ya damu ainun domin kuwa shi kadai ya san irin farin cikin da yar karamar cikinsu ke saka shi, aman sai gashi tana neman alfarmar kara sati daya tak a gidansu, ba irin abinda ke birge shi sai idan tana fadim kaf duniya a yanzu yana gaba da kowa da komai nata, sai kuma cikin hikima ta nuna masa yan uwantanma sunna da nasu darajar wada ba zata iya samun farin ciki idan har daya daga cikinsu ya ce washhhhhh

Murmushi ya yi yana dan shafa gemunsa da ya fara furfura farare kal a sanyaye ya ce" Sati daya tak, daga shi kin yarda ba zaki kara ba?"

Itama murmushin ta yi jin sautin muryarsa kafin a sanyaye ta ce" In sha Allah ogana"

Wani murmushin ya kuma yi a bayanne yana jin kansa sai kara fadi yake ,
Sunna yin salama ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta karasa kusa da Ammi dake danna wayarta tana rubuta message

Allert ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga kudi ne zunzurutu daga mijinta
Wani murmushin ta yi ta shiga rubuta masa messafe din godiya, hade da kalaman soyaya ba wani dar ta tura masa sannan ta juyo tana sauraron Ammi

Ammi ta ce" yaya bai kyauta min ba, yayya zai tashi kai tsaye ya yiwa NAJEEBA maganar nan a yanzu bayan ba lafiar kirki gareta ba tsakani da Allah? Gashi du ta rikice min ban san ta inda zan fara ba anya ban shiga hakkin yarinyar nan ba kuwa?

Zahrau ta ji Tausayin Ammi a ranta sosai, sai dai bata da niyar ja da baya dan haka ta kama hannun AMMi ta ce" Ammi, ba wani abu fa, idan har ta samu kulawarmu baki daya zata mike ta warware ne, kin ga abubuwa masu girma har biyu ne suka sameta a yau kadai, dole sai an rarasheta an lalamata

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin ta saki murmushi a sanyaye ta ce" ta ji ciwo ko?"

Zahrau ta dan sada kanta dan kunya, a hankali ta ce" Ammi, kin san tana da saurin warkewa a kan ciwo ko wani iri, bata da kam jiki in sha Allah nan da kwana uku zaki ga ta ware"

Ajiyar zuciya Ammi ta kuma saukewa a sanyaye ta kuma fadin" na so a kira likita kun hanna, bana so ciwo ya hanna mata nutsuwa fa"

Zahrau dai bata gushe da murmushi da son kwontarwa da Ammi hankali ba, har sai da kiraye kirayen salar isha.i ya tashe su

Tabas abinda ta kudiri niya ta samu, domin kuwa ita kanta wace suke tsoron yau hankalinta ya kasu kashi da yawa sannan ita kanta so take ta ga fara'ar Najeebar, uwa uba Ammi dake nan nan da ita, ita kuwa ta karbi jawabi ta langwabe sai shagwaba take sosai, lale tana jin ciwo a jikinta sai dai tunda ta wuni shiga ruwa da anfani da ruwa abin da sauki sosai, sannan lamarin mahaifinta da mahaifiyarta ta yiwa kanta shawarar zata cire wata damuwa, ita dai abinda ba zata yi ba shine ta lalabata ta koma masa, idan ta yi ra'ayi dan kanta halasss

Nana suka hade a dakin sunna ta hira da wasa da daria harda DAYABU da ya fito daga zance, Mardiya kuwa tana dakin da aka kaita ta yada zango da waya sai karbar banzayen hudubobi take daga wajen kawayen duniya, ita a dole miji zai saurareta, kasancewarta a gidan sarki kusa da tsohuwar matar mijinta kuwa ta yishi ne dan ta nunawa shegiyar Najeebar nan cewa uwarta bata isa ta dawo gidan MUTALAB ba!
..........................................

Karfe goma ce ta gota a agogon bangon dakinsa

Kwonce yake saman lalausar shinfidarsa mai dauke da zanin gadon ruwan ashe color irin manyan zanin gadon nan ne da ake dorawa bayan an shinfida bargunnan nan na lybia manya manya masu nauyi da kyau
Jikinsa sanye da riga da wando farare kar na baci, wandon mai dogon kafa ne rigar ce mai yankaken hannu aman itama baba ce rigar domin budadiya ce sosai

A irin gajiyar da ya yi yau, ya hau gadon nan ne da burin rinyse idannuwansa dan ya samu ya shiga baci,
Sai dai tunda ya kwonta din sai ya kai idannuwansa kan kofar shigowa wajen bacin nasa ya kura ido kawai yake kallo
Lokaci zuwa lokaci sai ya maida duban nasa wajen agogo sai kuma ya kalli kofar
Juyawa ya yi ya baiwa kofar baya ya shiga adu'o'in tsari
Ya jima yana yi ya tofa ya shafe jikinsa, sai kuma ya kuma juyo dubansa ya kai kan kofar

Mikewa ya yi zaune a hankali ya sauka daga saman bed din ya kama hanyar fita
Yana fitowa ya shiga bin falon da kallo
Shiru ne falon ba kowa sai kamshin turaran wuta da sanyin AC
Fitilar dake kara haske ya kunna ya kuma bin dakin da kallo
Idannuwansa ya dan kikifta gannin har karfe goma sha biyu ce ta gota

A hankali ya karasa wajen doguwar kujerar falon ya hau sama ya kwonta hannayensa tokare da keyarsa kafafuwansa daya kan daya yana kallon bakin hanyar coridor din bangaren Ammi

Irin motsin da ya yi jin kamar kiran sallah ya saka shi idasa bude idannuwansa da kyau
Hannayensa sun yi tsami sosai ya kai dubansa da mamaki wajen agogo
Tabas lokacin salar asuba ne har ya yi
Da sauri ya kara kai dubansa falon sama ko kasa abinda yake son gannin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment