Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RASHIN JI NA, DA YAWA NA NUNA KULAWARSU DA SAKON GAISUWA, NA GODE ALLAH YA BIYA ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKHAIRI YA BAR KAUNA, HAKAMA WA'INDA SUKA RINGA SAKWONNINSU NA KYAUTATAWAR DA SUKA YI NIYAR YI MIN DAN JIN DADIN WANNAN NOVEL NAWA SAKWANNINSU SUN SHIGO KUMA AN SHAIDA MIN ALLAH YA KARA ARZIKI YA BIYA, MASOYA, A DUK INDA KUKE SAKON GAISUWATA ZUWA GAREKU, ALHAMDULILAH GRUP MAGE BANI DA TAMKARKU, ALLAH YA BIYA YA KARA DANKON ZUMUNCI, GASU FA, KADAN NE....AMAN IN SHA ALLAHU MUN DAWO BAKIN AIKI=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ, daga taku ce SAJIDA*>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



50


Cike da basarwa AMMI ta ce" eh ta dan yi rashin lafia ne"

Idannuwansa masu girma da ladaftar da mutun ya zubawa mahaifiyarsa yana kallonta, bai ce komai ba aman a yannayin kallon da ya kurawa fuskarta ya fasara irin tarin tambayoyi ko nace tarin son karin hasken da yake,

Cire kanta ta yi daga dubansa ta maida wajen tanfatsetsiyar tV din dake jikin bango wace ke kashe tana dan girgiza kafarta daya ta dora da fadin" idan kuwa ita dinma gaba za'a yi da ita a hanna min ganninta sai na ji karin bayani "

Dan murmushi ya yi yana sauraron Nusaiba na tambayar ya saka mata Game a wayarsa bayan shi ko kwaya babu a cikin wayar, ya maida dubansa wajen UMMU,
Cikin yannayin wadatacen murmushin fuskarsa ya ce" UMANI, me ke damun kawarki ne daga farin ciki sai na ga kamar kawarki zata bata ranta fa ko menene?"

Itama dubansa ta yi, ta yi dan murmushin zata bashi amsa Mardiya ta fito daga dakinta,
Karar rufe kofar da dan karfi ya saka UMMU yin shiru bata ce komai ba

Niyar Mardiya ta fice ta karasa diner, ta gaishe da Ammi kawai, sai dai hango wani mutun mai girman jiki, kyakyawan gaske, uwa uba tarin tarin kwarjinin dake fita daga jikinsa, tarin haske da lamari mai girman dake hanna tunkararsa kai tsaye, irin tarin hasken Azhkar da salar asuba, da tarin nafilfillu dake dakushe du wani karamin tsagera, sai ko wadinnan idannuwa nasa masu zabgawa tsagera mari da suka hadu suka sakata rage saurin da ta kwaso da niyar shigewa

Da dan mamaki ya yi mata kallo daya ya cire idannuwansa a kanta, domin kuwa ya ganeta matar Abih ce, sai dai abinda ya bashi mamaki irin shigar dake jikinta da kuma ganninta kamar wace ke zaune daram dakam haka a gidan?

Tana karasowa ta dan rage tsayinta ta gaishe da Ammi

Ammi ta amsata da kulawa ta ce" Mardiya, mijin NAJEEBA ne ai ku gaisa"

Da wani irin firgici da mamaki ta dago dubanta ta yi niyar kara kallon fuskarsa, duda ba ita yake kallo ba sai ta kasa yin hakan ta tsinci kanta da saurin sada kanta idannuwanta na kara zazarowa tamkar zasu balo su fito waje, what? Mijin wa? Idan bata manta ba SULTAN SHAHEED ne ya auri Najeeba, Sultan din da take tunanin wani margayaye ne bayan rawanin nan dake kansa koda taushe, da yawa a cikin gari na tunanin wai ko dai wata kama ce da fuskarsa dake sakashi kin son bude fuskarsa ko ya ringa yin sasaukan rawani irin na sarakan zamani komai zafi? Bata taba jin du abinda take aikin banza bane irin na yau, ashe haka yake? Tana gannin ta samu galaba a kanta tunda ta aurar mata uba hakan na nufin ta rama rabata da saurayinta da ta yi, sai kuma a yau ta ga wannan bawan Allah da bata san da wani sunna zata sufanta shi ba ace shine SULTAN?

Muryarta na rawa rawa ciki ciki ta kai gaisuwarta kafin ta mike ta juya da sauri ta nufi ciki , wato ta koma tama fasa zuwa table din, sam bata da karfin iya cin wani abu, kwata kwata bata da karfin hakan, a yanzun jin zuciyarta take tamkar zata fashe, ji take tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu, bata taba kawowa kanta Najeeba zata samu irin wannan mijin ba, bata taba tunanin zata kasance a irin wannan ranar ba, itafa bata da makiyiya sai Najeeba da uwarta, wayarta ta warto tana sintiri tana tunanin me ya dace ta yi? Wa ya kamata ta yi kira? Ko dai shawarar bin bokayen take dauka ta fara ne? Domin kuwa a da ta yiwa kanta alkawarin ba ita ba harkar boka ba dan komai ba sai dan ta kawo rantsuwa ta gita kamar yanda Najeeba ta ce da ita ba boka ba malan zata yo andani da lamarinta na mace ta zartar da hukunci ta hanyar haramta mata soyaya da saurayinta, itama ta kawo rantsuwar ba boka ba malan ita kuwa sai ta auro ubanta kuma sai ta hanna mata kwonciyar hankali karshe sai ta yi sanadiyar da ubanta ya kore ta! ,
Sai dai kash, a yau sai ta fara tunani cikin daya biyu.......anya kuwa zata iya ci gaba da gogaya da Najeeba da Uwarta ba tare da ta bi ta kasan kasa ba?

Wayarsa ce ta dauki kuka a hannun Nusaiba

Amsa ya yi ya kara a kunnensa, a tausashe ya amsa gaisuwarsa

Abih dake tsaye kofar dakin ya ce" Allah ya taimakeka, na shigo ne tanzun zamu gaisa da su Bilkissu, shine nace yau ko zaka fita fada ne? Zancen aminin nan nawa dake kwonce wanda nake maka bayanin matarsa ta tashi hankalinta bisa maganar da ta ji makocinsu na yi a waya tsakiyar dare wanda ya saka mata tsantsamta da saka hannunsa kan rashin lafiar mijinta, shine na ce ina so da kanka ka yi shara'ar nan, walahi ciwo gaba yake ya ki ci yaki cinyewa gashi asibiti basu ga komai ba, ana ta na hausa wannan ya ce matabiya ce, wancen ya ce jifa ne, kai dai ka san lamuran kwashe kwashen mutanenmu, shine nace dan Allah a shigar mana lamarin nan"

SHAHEED ya dan gyada kansa, a hankali ya ce" ABIH yau ba zan fita fada ba, ama ka saka a fada masu gobe in sha Allah mu yi zaman karfe tara a cikin gida "

Godiya Abih ke ta yi har ya sanyo kansa falon, sai kuma ya dan yi turus da mamakin Gannin wai da gaske SHAHEED din ne yake ganni a zaune tsakanin UMMU da BILKISSU ba RAWANI??

Murmushi ne ya fadada a fuskarsa kafin ya karaso shima yana kara kallonsa da kallo mai nuni da yannayin farin cikin da ya tsinci kansa a ciki ya mika masa hannu suka gaisa kafin ya samu waje ya zauna yaran du suka shiga dane shi sunna gaishe shi da murna da ihun fadin ABIH ne ABIH ne

Wannan abin shi ya saka Mardiya zabura ta ajiye wayar da suke da kanwarta fitinaniya wace a yanzu haka ta kai wajen da bama a gida take ba ta tafiarta Maradi wajen wani Alhajinta da ya kama mata gida, sam bata ji yarinyar ko a lokacin da mahaifinsu nada rai, da adu'a kawai yake binta , a yanzu da kasa ta birni idannuwansa sai da ta yi bikin bayana cewar ta zama rikakiyar yar bariki sannan ta faso gari da lasisinta take fantamawarta hankali kwonce

Da sauro ta warto hijab dinta maroon ta saka ta bude kofar ta fito

Daidai ta kusa karasowa UMMU ta ajiye masa ruwan da ta zuba masa a cikin copin glass mai dan tsayi mai sanyi ta koma wajenta ta zauna duda tunda ya zo ba wani magana da ta hada su daga gaisuwa sai ruwan da ta dauko masa ta ajiye masa

Du irin yanda Sultan ya cika wajen bai hanna Mardiya karasawa ta dauke kofin ruwan ta je saman table ta ajiye a ranta kuwa fadi take 'karya ne walahi , ba zaki zauna kina gwada min bariki a wajen da mijina yake ba '

Tana dawowa ba ko dar sai ta samu waje dan kusa da Abih kadan ta zauna, ita bata gaishe shi ba, ita bata bar wajen ba, sai binsa take da kallo , sai kawai take ga kamar wanda ya cencara kwaliya domin ya sha sabuwar shada ne ya hade abin dai ba'a cewa komai, hakan ya sa ko dan datijantakar tasa ke son boyewa sai yan tsirakun furfurar dake jikin gemunsa dake iya shaidawa da ya dan kwana biyu da kuma fuska irin ta baba daban take da ta yaro

Sai da ya ajiye wayarsa ya dan matso da zamansa ya hade hannayensa biyu ya dora gwuiwoyin hannayen nasa saman rigar shadarsa da ya dan ja baya kadan yanna kallon Abih, muryarsa a dake kadan tamkar ba sirikinsa ba, ya dauko muryarsa da yake magana da ita a kausashe a wajen shara'a ya ce" *Meye anfanin zaman iyalinka a gidan nan bayan ba wata sabga ake ba ABIH?*

ABIH ya kale shi, sai ya maida dubansa kan Mardiya da sai da ajiyar zuciya ta kwace mata jin abinda SHAHEED ya fada, dama hanya take nema ido rufe dan haka ta samu nauyin da zuciyarta ta yi mata ta fara ragewa

Abih ya maida dubansa kan SHAHEED, a hankali ya ce" gata ai SHAHEED ka tambayeta"

Sultan ya maida idannuwansa dake dauke da yannayin kausasa ya ce" Mardiya, me kike a nan zaune tamkar wace bata da aure?"
Mardiya ta hadiyi wani yawu jin wai a tambayetan da Abih ya ce, kafin muryarta na rawa rawa karshe ta fashe da kuka ta ce" wai yaya kake na yi ne MUTAKAB, yaya kake so na yi? Bayan kana min gabar da ban san a kan me ba dan kawai na fadi gaskiyana shikenan?, ni bani da damar nuna fushina shine zaka nunan na tafi gidanmu? Da zaka ce a tambaye ni a kan me nake zaune a nan so kake na yashi na kara komawa gidan namu ka hadu da wannan kunna cin amanata?

Wannan din da ta ce da wada ta nuna ya saka da SHAHEED, da AMMI, da ABIH baki daya suka kai dubansu wajen UMMU dake zaune
Ga mamakin SHAHEED wanda ya yi jiran jin irin hukuncin da UMMU zata dauka ta hanyar ramawa sanninta da ya yo cewar bata da hakuri da daukan raini, sai ya ga ko nunawa bata yi cewar ta san zancen da ake ba, hasalima abin yanke farce ta dauna ta duka tana dan karkare karamin farcenta na yatsarta karama,

Juyowa ya yi da yannayin mamaki, lalle dunia ta yi sanyi, sannan ya yarda idan ba auren ba babu abinda zai saka ka kalli mutun da girmansa da komai ka farfada masa magangannun da sukai maka dadi dan kawai ya taba auren mijinka bayan ya girme maka nesa ba kusa ba

"Haba Mardiya, me yasa kike da saurin daukan fushi a kan lamarin duniya harma ki rufe ido ki ringa magana na neman magana ne? Me ya hada zamanta da mijinki ne? Me yasa kike ta shigota da gudu bayan tana iya yinta tana kauce maki da dukan karfinta ne?" AMMI ta karasa tana mai kallon Mardiya

Mardiya ta ce" Haba maman Sultan, tsakani da Allah karya na yi ne? Meye hadinta da mijina da zata ringa dauko masa ruwa daga ya zo? Meye zai sa ta zo nan ta tare bayan na san ba danginku bace?"

Da wani mamakin Ammi ta budi baki zata yi magana , Abih ya rigayeta yana dan murmushi ya ce" in ba Mardiya ba macen da ka haihu da ita a yi maganar meye hadinka da ita?"

Da sauri ta tare shi tana dan fido masa manyan idannuwanta ta ce" kana nufin du iyayen y'ayanka sunna iya zuwa nan su tare dan kawai aun haihu da kai?"

Mutalab ya dago idannuwansa da sukai masa ja ya kalleta, ya dauke dubansa ya kai kan UMMU, sai da ya lumshe idannuwansa kafin ya cire ya dora kan SULATAN dake bin du wanda ya dauki magana da ido yana jira su gama, dan murmushi ya yi ya dan cije lebensa ya ce" ka ga ilar rashin zama waje daya ko? , Shaheed a da ce mata na yi ta je gidansu, aman a yanzu ina so ta koma dakinta sai dai da sharadi, dan Allah Shaheed ka rokar min Nana ashuwa ta koma dakinta, ina mai roko da kokon barana uwar y'ayana ta koma dakinta"

Shaheed ya kurawa Abih ido, lokaci daya Mardiya ta zabura , baki daya jikinta ya kwashi rawa, tana mai kukan nan sama sama ta ce" walahi ba dai da ni zan yi kishi da macen da ta girmeni ba, matar da ta haifeni ne za'a hadani kishi da ita? Me yasa ake son kai a wajennan? Kowa idan ya budi baki sai dai ya goya mata baya ni kuwa a kwaye min? To walahi ba zan hada kishi da ita ba sai dai ka sake ni MUTALAB,"

UMMU ta dago daga gyaran farcenta da take ta kai dubanta kan Mardiya a karo na farko kennan, sai da ta rintse idannuwanta ta saki bakinta da ta cije da karfi tana kallonta ta nunata da abin yanke farcen nan ta ce" sannin cewar ke yarinya ce ya saka nake kawar da kaina a kanki MARDIYA! Yaya kike son sai kin kureni wajen da zan iya hukuntaki tamkar yar da na haifa da cikina ta hanyar dane ruwan cikinta na matse bakinki na zaneki da bulala?, ki kiyayi shiga sabgata, na rantse maki zan iya matse hancinki na rufe numfashinki! MARDIYA ke yarinya ce, kuma a duniyar kishi ke yar kauye ce ki je ki zauna da mace ta koya maki kishi, ki bambance MIJI da KISHIYA , ki iya yiwa MIJI magana, ki iya tafia a gaban miji kafin ki dawo ki tantance ni din abokiyar gabarki ce ko makashinki ce!"

Abin yankan Farcen ta ajiye da karfi saman table din glass din wanda hakan ya saka wajen yin kara ta mike tsaye, sannan ta dan duka ta dafa hannayenta bibiyu saman table din tana kallonta da idannuwanta dake nuna tsantsar bacin rai ta ce" zama da tsoho ai ya kare tunda kika auri tsoho da yarintarki dan son zuciya kika zauna, shirme ai ya kare a macen dake tunanin zata ci galaba a wajen namiji bayan tana kin y'ayansa, ke kam wawuya ce tunda har kike yiwa mijinki hauka a gaban kowa, ke din sakarai ce tunda har kike tunanin ihunki zai hanna wani abun rayuwa! Mazan nan da biyayarkima yaya kika gama da su? Bale ke tsagera karamar kwari?, shin mahaifiyarki ta rasu da kika rasa magaya ne ko me?"

Baki Mardiya ta daga zata yi magana da yannayin tsoron da ya darsun mata na yannayin UMMU, sai dai kafin ta yi UMMU ta zabura ta idasa matsawa kusa da ita sosai ta ce" dis, idan bakinki ya furta min A ba cikin kalmar da zaki hada dan gaishe ni ina maki rantsuwa da wanda raina ke hannunsa sai na sauke maki hakori irin yanda zan hukunta dan cikina, domin ke din y'ar cikina ce!"

Wuki wuki ta shiga yi da idannuwanta

Ummu ta juya ta fara tafia ranta a matukar bace, sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli MUTALAB da MARDIYA ta dan daga muryarta ta ce" me zan yi da aurensa? Bana so, ki kwontar da hankalinki in dan wannan kike hauka!"

Wannan kalmar ita ta fi batawa Abih rai, ya muke da sauri ya taka yana biye da UMMU wace ta kara saurinta zata shige dakin su NAJEEBA ya ce" NANA nine bakya so? Nine bakya so Nana? Sai me dan bakya so na, idan baki aureni ba mutuwa zan yi yo? Aman walahi ba wanda zaki aura in dai ina raye , mu zuba ni da ke"

UMMU ta juyo ta zazaro idannuwanta ta ce" mu zuba MUTALAB, idan an zo daura aurena ka hanna! "

Tana kokarin rufe bakinta sukai ido hudu da NAJEEBA wace yar hayaniyar ta fitar da ita, irin kallon da take mata ya saka jin kafafuwanta sun yi mata nauyi,

A hankali ta furta" NAJEEBA"

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta zafafan hawaye suka zubo a kurmin idannuwanta, itama a hankali sannan a sanyaye ta furta" *sai kin aure shi MAMA, idan kuwa ba haka ba mu zuba*"
Tana gama fada ta juya da sauri ta yi dakin kannenta da aka kora su da niyar labarta masu abinda UMMU ke yiwa Abihnsu

Wani irin farin ciki ne ya saka UMMU jin saukar hawaye mai dumi a gurbin idannuwanta,
Ba na komai bane sai na wannan kalma da take ji daga bakunnan y'ayanta goma sha shida banda dayar, a yau ta fito daga bakinta cike da rigima ta hanyar turo dan bakinta mai kyau ta ce *MAMA* ,

Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta da sauri ta bi bayansu dan a yi komai a gabanta

Murmushi Abih ya yi ya juya da sauro da takamarsa ya zo wucewa ya jiyo ihun kulan Mardiya da ta yi dakinta da gudu tana maimaita ba zata yi zaman kishi da UMMU ba ya mikawa SHAHEED da ya talabe kuncinsa yana kallon ikon Allah hannu ya ce" a tayamu da adu'a su kara rikice mata har ta aminta sai ka daura mana aurenmu"

Shi kam Shaheed sai ya samu kansa shima da yin murmushin ya mika masa hannun suka gaisa ya juya ya yi ficewarsa

Dubansa ya maida Kan AMMI dake ta kalle kalle ya sakar mata murmushi ya mike ya karasa kusa da ita

Hannunta ya dauka na dama ya manawa bayan hannun nata kiss a hankali ya ce" AMMI, i lv u"

Murmushi AMMI ta yi tana kallonsa cike da kaunarsa,
Ya ce" zan je, Ammi zan dawo idan har ban samu gamsuwa da irin hukuncin Umani ba"

Ita dai tana mai binsa da murmushin har ya tafi

Kamar yanda ya fada masu hakan ne ya kasance, a zaunen ya tarar da matansa biyu su duka sun sha kwaliyarsu sai kamshin turare dake tashi, aunna zaune a kujeru masu nesa da junna ba wada ke yiwa yar uwarta magana

Da mamakin ganninsa ba rawani, da shiga irin ta jaruman maza du suka bi shi da kallo

Sunna jira ya zauna ya hakimce su kai gaisuwa sai suka ga ya ja ya tsaya a tsakiya,
Muryarsa a dake ya ce" shin daga baya kika fasa ko menene dalili?"

Zinaria dake kallonsa gannin maganar da ita yake ta kara buda kunnayenta dan jin a kan abinda yake magana,
Sai kuma ta ga ya juya wajen NADIA itama a kausashen ya furta" Daga baya kika fasa ko tunda kika zo baki san wannan shine abu na farko a cikin layin abinda zaki yi dan samun dorewar zama da ni tare da kwonciyar hankali da nutsuwa ba? Shin baki san shine dalilin da ya saka na yi dogayen hanyoyin da zasu kai kowacenku wajen ba tare da ta fito ta bi cikin baban gida ba?"

Kara sada kanta ta yi itama cikin rudu, aman ta kasa furta komai domin a ganninta Zinaria itace baba itace ta san kan mai gidan gannin bata ce komai ba sai itama ta yi shirun ta kara sada kanta sosai

SULTAN ya ajiye wayarsa saman table a hankali ya ce" ku kiyaye"

Gannin yana niyar shigewa ciki ya saka ZINARIA kara saukowa ta rage muryarta sosai ta ce" Allah ya taimake ka, shin a kan me kake magana?"

Ja ya yi ya tsaya na dan sekwani sai kuma ya juyo ya ce" ina magana kan zuwa gaishe da MAHAIFIYATA, kowace safia kafin ku gaishe ni ku tabatar da kun fara gaisheta sannan ku biyo hanyar gaishe ni, domin kuwa albarkarta nake nema"

Yana gama fada ya yi gaba, hakan ya saka su bin bayansa da kallo

Ficewar Zinaria ya saka Nadia zabura itama tama sauri ta yi gefenta cike da tunanin bata san ana hakan ba, sai dai ta cika da tsoro, tsoron haduwa da Najeeba domin ta tabata a wajen take, tana tsoron abinda zata iya yi mata idan suka kasance a waje guda!

Zinaria kuwa bakinta ta tabe a kasan zuciyarta tana ayyana 'ai an yi walkiya na ga komai walahi, matar da ta wanke makiyiyata ta baka shine zan ci gaba da jerangen zuwa da zowa dan gaisheta? Ba zan je ba'
...................................

Wasu irin fararen jigida masu dauke da duwatsu kananu yas yas sannan sunna ta zuba kamshi ne Zahrau ta yi cinikinsu har kwaya goma sha biyu biyu gida hudu, hakan ya saka aka zuba su a cikin kwalabensu masu dauke da wani irin ruwan turaran shafawa aka mayar da su gefe bayan ta caje kudadensu masu yawan gaske

Cike da ladabi Zahrau ta ce" Balaba, dan Allah ki taimaka mana da sirrikan sabulan wanka na fatoci kala daban daban mana, kama daga fatar farar mace har zuwa bak'a, Harta da irin wanda wace ke shafe shafe ke oya anfani da shi dan samun farar fata mai kyau da santsi da tsari ba tare da ta shafa mayukan nan masu kona jiki ba?"

Hamshakiyar matar dake zaune cikin madaidaiciyar kwaliya tana zuba kamshi bakinta dauke da hakoran maka biyu sai kyalkyali suke ta dan yi murmushi ta gyara zamanta ta ce" yaya kike so na baki sorrin sana'ata Gimbiya Bilkissu bayan na san kanwarki Gimbiya Najeeba nada saloon? Idanfa ta mayar da wannan sana'arta tawa ta kare domin ina mai tabatar maki da zata kwacen kwastoma, a yanzu haka da wadinnan kawai nake kara kwatar kaina a kan shagonta"

Murmushi Zahrau ta yi ta ce" ba zata mayar da yin sabulai sana'arta ba, na maki alkawari balaraba, ina son ki bani wadinnan sirikan ne dan ina nesa, sannan ina son kanena su uku su lakance su dan yiwa kansu"

Balaba ta kara yin murmushi ta ce" idan akai haka kennan ba zasu zo na ringa hada masu ba?"

Zahrau ta yi wani murmushin ta ce" bayan a yanzu a gabanki na mayar da ke wace zata ringa hada turaran wutar fada? Kin san da mun iya hada turaran wuta irin namu tsumamun turaran wutar da kuke so ruwa a jalo aman kuma na baki wannan damar ai kin san dan mun iya hada sabulai ba zai hana mana zuwa ki hada mana ba idan hakan ta taso, juste ina son na san sirrin nan, ina matukar mamakin matan da suke anfani da sabulun wanka na ruwa da na sabulu fatarsu na daukan yannayi na kwailin dake hanna masu yin bakin nan na hannu da kuma kafafuwa, ina mamakin irin yanda fatarsu ke yin santsi da sulbi , sannan irinmu masu bak'ar fata ina matukar son sannin wai menene sirrin dake sakawa fatarmu na daukan yannayi na sheki , santsi, da wani irin ni'ima tamkar wa'inda bama shiga rana ko ba zafi a garinmu?"

Murmushi Balaba ta yi ta mike ta dauko litafi da byro ta dawo ta mika mata, a hankali ta ce" tabas zan baki sirrikana, bismillah ki rubuta daifai misali, aman kafin nan zan fada maki wani sirrin, wato *zafi*, zafin rana davan, gumi daban, Zafin rana shine abinda fata bata so, aman gumi daifai misali shine abinda fata ta fi so dan karbar gyara.....misali........



Shin kuna son sirrikan nan ne?=ØÞ>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø#Ý, idan kuna so ku lalaba ni na yi tunani sai mu ga abinda za'a yi>Ø#Ý=ØÞ=ØÞ, amanfa iya gyaran fatar zqn bayar, domin kuwa shi baban gyaran cen ai kowama ya iya=Ø Þ=ØHÞ


Taku ce SAJIDA>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_





Please Login or Register in order to submit comment