Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bai ganni ba

Lebensa na kasa ya tsinci kansa da dan cijewa yana jin kamar damuwar son sannin dalilin hakan na son kutsowa cikin lamarinsa

Tabe bakinsa ya yi ya mike ya nufi bayi dan shiryawa ya gabatar da sallah

A wunin ranar ya yi ta tunanin lamarin duba da Ammi bata yi masa maganar ba, shi kuwa sam bai nemi jin ba'asi ba, sai ya ci gaba da harkokinsa da yau da kulun

Wasa wasa sai da ta kwana uku bata waiwaya turaka ba, domin tun tana na wasa har ta hadu da na gasken domin athsmanta ne ya ringa tashi gadan gadan sakamakon kurar da aka yi ta bude window din dakin da suke
Ammi kuwa ta shaka ne, a ganninta ya dace ya bi bayan Najeeba, ko dan a yanda aka rakota daga bangarensa dan haka itama ta ki kawo masa maganar ko irin gaisheta da yake na asuba bata taba kawo masa maganar

Yau ta kama kwana hudu, a yaune Zahrau ta yi niyar garin Allah na wayewa zata je anguwa wajen Hajia Hadiza Awilo , matar dake gyara kala daban daban

Kamar yanda ya saba zuwa da asusuba yauma hakan ce, AMMI ce da UMMU zaune a dakin AMMI din, a yau tataunawa suke na lamarin da ya shafi AMMI din da kanta
Cike da damuwa take gabatar mata da abubuwa irin na halayan da Zinaria da mahaifiyarta ke nunawa, irin na Nadia da ta shigo jiya tsal itama ko sau daya bata zo ta gaisheta ba, da yannayin damuwa ta furta" ki duba ki ga yaron nan tun da aka rako NAJEEBA bai waiwayota ba, me ke damunsa? Me ya sa matansa basu dauke ni da mahinmanci ba? Ko dai laifin daga shi ne baya saka su a hanyar da ya dace su bani girmana?
UMMU ta ce" eyah Ammi, inaga lamarin nan dole sai da adu'a, bana so ko daya ki ga laifinsu, shima haka ina so ki masa uzuri, kin ga fa abubuwan kansa da yawa, wani abin yana iya shige masa a duhu ne bai san da shi ba
Aman in sha Allah ni zan nemi kusanci da matansa dan na gane meye matsalar, sannan shima zan zauna da shi daga ya samu lokaci

A hankali ya yi salama muryarsa a ciki aman kuma kunnaye zasu iya jiyowa

Amsawa suka yi baki dayansu shi kuwa ya karasa har inda suke zaune wato bakin bed

Hannayensu dake rike da junna ya saka hannunsa ya raba sannan ya shiga tsakiya ya zauna

Da yannayin sakin fuska ya saka hannunsa ya dago, dubansu ya yi da yannayi mai tarin kaunarsu da jin wani irin girmansu a zuciyarsa , a hankali ya furta " barka da asuba ummani"

Murmushi ne ya wadata fuskokinsu, cike da girmamawa, fa kaunarsa suka amsa gaisuwarsa

A hankali UMMU ta ce" Yaya fama da al'umah?"

Sai da ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta" ALHAMDULILAH "

mukewa UMMU ta yi cikin dubara ta furta" zan leka kicin na ga idan an gama Ammi "

Har sai da ta kusan fita ta ji muryarsa cike da kamala yana fadin" shin zan samu dan kwano tare da kowa Umani? "

Dakatawa ta yi ta juyo da dan yannayin mamaki, AMMI ce ta ce" kana nufin zaka karya a nan tare da ni, ko tare da mu?

Murmushi ne ya mamaye fuskarsa gannin yanda wani irin yannayi na farin ciki dake mamayar kamilaliyar fuskar mahaifiyar tasa, yana kallonta ya ce" du wanda zai kara daukaka wannan ni'imatacen farin cikin da nake ganni a kan Fuskar da ta fi kowace fuska tsada a zuciyata "

Mikewa Ammu ta yi tana ta murmushi, sai ta kalli UMMU ta kuma ta kalle shi, idan ba zata manta ba rabonsa da ya zauna ya ci abinci da ita har ta manta, kai an jima, gashi yau yana nufin harda yan uwansa? Sai kawai ta manta dan fushin da take ji a zuciyarta nasa du wani farin ciki ya maye gurbin hakan

UMMU ta fadada murmushinta tana jin wani irin farin ciki ita kanta har AMMI ta karaso da sauri ta rike hannunta
Muryarta kasa kasa ta furta" zaki iya ke daya kuwa? Me ake girkawa yau a kicin ne? Table a goge yake? Yara du sun farka kuwa? An kawo alkyabar kowa kuwa? Shin zasu shirya a kan lokaci kuwa? "

Daga inda yake zaune sai ya tsinci kansa da sakin wani irin murmushi, wai dama haka jin zai kasance da ita ke sakata a farin ciki? Sai ya ringa jin wani irin dadi zuciyarsa
A hankali ya ce" *AMMI, ki bar ahalina su fito cin abinci da ni a kan lokacin da suka saba, a irin shigar da suka saba fitowa, UMANI zan zauna a table din cin abincin falonki ba tare da rawani ba "*

Wannan karron ita kanta UMMU sai kawai ta ringa dan yarfe hannu tana jin wani yam yam yam na bin jikinta, kasa magana ta yi tsabar farin ciki ta juya da sauri dan nufar kicin, domin kuwa abincin kawai zata iya tsayawa ta tabatar an kawata shi

Cike da wani irin farin ciki AMMI ta dawo wajensa, hannayenta ta saka daidai da fuskarsa ta talabo tana kallon kamilaliyar fuskarsa mai dauke da saje, farin fatarsa da kamani na mahaifinsa na tatare da fuskar tasa, hannunta na dama dauke da carbin nan irin na dannawa baki mai dauke da dan abu na yawo a jikinsa mai hasken gaske yana walwali

Idannuwanta cike da kwala ta budi bakinta ta ce">ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



49


Idannuwanta cike da kwallah ta budi bakinta ta ce" ka gani SHAHEED, walahi ina da bukatar zama da kai haka, ka gani ko SHAHEED rabona da jin farin ciki haka an jima sai jin daurin aurenka da NAJEEBANA, sai ko wannan zaman da zaka yi da mu, fuskarka ba tare da rawani ba, ka ga SHAHEED sai nake ji kamar idan muka zauna zan iya yin magana da kai kai tsaye, sai nake sakawa raina dama idan muka zauna zaka yi daria wa shirmen kannenka, ka saurari bukatunsu, ka tambayi muradinsu, harma ka yi wasa da su irin na kowa, sai nake hasaso zamanin mahaifinka, yakan ware lokaci ya zauna da mu baki daya ba rawani a fuskarsa, yakan zauna ana wasa da daria da mu baki daya, sai sai nake jin kamarma ace ba rawanin nan a tsakanin mu, sai nake tunanin rayuwa ba sarauta? Shin zan kasance koda yaushe a irin farin cikin nan na yau ne ko zai kasance gundurare a gare ni? "

Hannunsa na dama ya dora saman nata na hagu dake saman kuncinsa, a hankali ya karkata fuskarsa wajen hannun nata ya mana mata kisss a tafin hannun nata mai sanyi hade da zafin kaunarta dake zuciyarsa tare da lumshe idannuwansa sannan ya dago dubansa yana kallonta, idannuwansa ba yannayi na kuka aman tarin tsagwaron kaunar mahaifiyar tasa ya saka su cenza kala,
A hankali ya furta" Ammyna, a koda yaushe kike da bukatar hakan, koda ina nesa da gari ki turan texte, just write t mom, ko a saman rakumi nake, ko a cikin jeji nake, koda an daure ni da sasari zan kunto, zan zo gareki, zan duka gabanki, AMMI ke ce duniyata, ke ke kawata min duniyata "

Murmushi ta yi mai sanyi da sauri ta kama shi ya mike ta ce" je, je ka yi wanka ka zo, ka yi gagawa ka zo karfe takwas muke breakfast"

Shima cike da farin cikin ganninta a farin ciki ya juya ya fice yana mai takunsa na kasaita da kamala sanye da rigar sallah

UMMU kam a kicin ta gama rikita kowa, an fitar da wasu sababin abubuwan zuba abinci na alfarma, an kara kawata abincincikan, sannan ta baza ma'aikata da wuri wuri su kara bin goge goge da sharen sharen da suka yi duda wajen ko a haka a mugun gyare ne a wajena (=ØÞ), baki daya ta bi ko'ina ta kara zuba turaren wuta a manya manyan abubuwan saka turaran wutar dake gigirke a kowani lungu na tankamemen falon

Nan da nan suka ringa jera manya manyan kulolin dake shake da abincicika,
AMMI ce ta fito sanye da abaya baka har kasa mai dauke da ado madaidaici,

Cike da murna take bin ko'ina da kallo, kafin ta sauke dubanta wajen agogo
Karfe bakwai da minti talatin ne na safe dan haka Direct ta karasa wajen kujerar da UMMU ke tsaye tana kara gogewa da kanta tana ta kara kyalkyaleta

Da murmushi a fuskarta ta ce" UMMU, kujerar nan ta gogu kamar wace kika wanketa haka take kyali fa haba ki je ki huta haka dear"

Da murmushi itama ta dubeta ta ce" kin san ni tunda asuba nake wanka na kimtsa tun kafin na yi sallah, shi ya sa kawai na tsaya na ga komai ya shirya

BILKISU ce ta fara fitowa sanye da wando da riga na baci , dogaye ne sakaku sosai a jikinta ,
Tsayawa ta yi tana kara bin dakin da kallo, domin aiki sai mai shi harta da labulaye sai da aka cenja nan da nan dakin ya dauki sabon tsari

Idannuwanta ta dan zazaro a lokacin da ta hangi saman table din, irin yanda aka kawata shi

Da sauri ta karasa ta duka har kasa ta gaishe da iyayen nata

Da yannayin mamaki batama tsaya ta ji amsarsu da kyau ba ta ce" AMMI, MAMA baki aka yi ne? "

Ummu ta yi daria kawai Ammi kuwa ta mika hannu ta tasheta tsaye ta ce" takwara, ba baki aka yi ba, kawai dai an cenza ne , maza je ki tashe sauran dan yau weekend ne shine ba'a shirya ba ko? To lokacin hawa table ya kusa oya a je a shirya cin abinci "

Ai kuwa da zumudi ta juya ta koma dakinsu na yaran tana ta gumtsa masu irin tarin kulolin da ta ganni a falon AMMI gashi kuma ba birthday din wani ba, kuma ba baki aka yi ba cike da zumudi du ta ringa tashinsu domin bayan gama salarsu da wanka da broch du sai suka nemi waje suka kwonkwonta dan yau din weekend ne malaminsu na islamiya kuwa sai karfe goma yake zuwa

Zuwa karfw takwas du yawanci sun halara a saman table din cin abincin falon sai dai yau maimakun a fara kai tsaye sai suke ta amsa gaishe gaishen iyayen nasu ya kasance saura mutun uku kawai ne basu karaso ba, su ne wanda ake jiran, sai NAJEEBA da UMMUKULSUM

Du yawanci da kayan bacinsu ne jikinsu, wasu doguwar riga har kasa da dan kwali, wasu kansu da yar hula ta baci, mutun daya ce bata fito ba ita kuwa dama ba fitowar take ba sai idan ta ji maganar mijinta

Kusan da minti goma sha bakwai ya bude a hankali ya shigo falon, ya yi daidai da fitowar NAJEEBA da dan gudu gudu tana fadin" AMMI, walahi ki yi mata magana dan kunnena ne fa a zuwanmu Abuja na siyi abuna a chopclass, shine zata ce nata ne?"

UMMU ta ce" karya ne, walahi karya ne wannan yan kunnayen ba nata bane ni na sayi abina a Niamey da kudina a shagon wannan matar SAJIDA mai sunna JADAH na neme su na rasa sai yau tana zazage jakarta ya fado"

Tsayawa ya yi a daidai wajen da ya sanyo kai suka shige da gudu ta yi bayan Ammi tana ta gwalo tana kuma fadin nata ne
Dif ta yi baki bude hannu sangale ido waje tana kallonsa hakan ya saka UMMUKULSUM waigawa a tsorace domin irin kallon nan ne dake nuna karara wani abu ka gani da ya firgitaka har haka

UMMU ce ta waiga itama sai wa'inda ke kallon Najeebar suma du suka waiga dan gannin meye? Lokaci daya Ammi ta saki murmushi tana kallonsa, kwata kwata bata iya boye farin cikin fanar nan
Shada ce jikinsa, dinkin wando da riga , rigar tsayinta daidai gwuiwarsa, kansa ba hula hakan ya sa tsadaden askin kansa da gyarn fuskarsa bayana karara, jikinsa kuwa sanye da bakar shada ne sai dan agogo a tsintsiyar hannunsa ta hagu

Cikinta ne ya bada wani irin kurrrr , lokaci daya jikinta ya dauki bari ta aniya neman dukewa dan boyewa ita kuwa jikinta sanye da rigar baci ne doguwa ruwan hoda mai siririn hannu sannan ko rigar mama babu sai pant dinta da ya bi rigar ana gannin shatinsa

Cirw dubansa ya yi daga kanta ya nufi UMMU da ta mike da farin ciki gannin yaran du sun zuba masa ido gannin daga inda ya fito, gashi ba sannin fuskarsa suka yi ba banda Zahrau da karara fuskarsa ta dawo mata a idannuwanta ta mike itama tsaye da sauri har jikinta na daukan rawa rawa domin da wayonta ta manta ranar da ta ganshi ba rawani, tun kafin a yi masa nadin da Abih ya je da su dan taya shi murna da adu'a

A lokacin da UMMU ta gabatar masu da shi, baki daya sai suka ringa zaro ido, harma suka rasa inda zasu saka ransu, abu daya suka yi a tatare shine mikewa, sannan cike da yannayi na sunna tsoron hada ido da shi du suka ringa kawar da dubansu duda tsantsar son karewa kyakyawar fuskarsa kallo da suke son yi

Murmushi ya saukar a kan fuskarsa kafin ya mamayeta da fara'a ya idasa wajen da UMMU ta bude na zama

Zama ya yi da bismillah sannan ya kara bin mutanen wajen da kallo,
'MASHA ALLAH' yake ayannawa a kasan zuciyarsa, ashe haka yan uwansa suke da yawa da kyan kallo?, yaren du sai suka shige masa idan ka cire daga bakin marar kunyarsa sai namijin sai yar karamar da ta shiga ransa sakamakon wasan da ya ringa yi da ita harma ya rike sunnanta
Ta kasan ido ya saci wajen da ta duke, ganni ya yi sunna yar kiciniya ita da uwar kafin ta dagota tsaye ta dan harareta sai kuma ta waske ta janyota ta zaunar da ita kusa da ita wanda hakan ya zama ta fi kisa da shi a gefensa na dama

A tausashe ya ce" ku zauna mu ci abinci mana "
Du bin umarninsa suka yi, wanda shi kansa ya kula umarninsa ne suke bi kai tsaye domin yar hayaniyar da ya tarar sunna yi sun yi gum sai kallon junna da suke a sace du sun nutsu

Murmushi ya kuma yi, a lokacin da kamar an budi bakinsu da Zahrau ta kawo masa gaisuwa du sai suka ringa yin irin nata sunna fada a tatare

Ba na wace ya amsawa, sai dubansa da ya kai wajen Ammi ya sakar mata murmushi a hankali ya ce" Ammi, y'ayan naki hala makarantar gaisuwa kika saka su? Na ji sai maimaici suke uwa wa'inda suke kawo harda"

Ammi ta yi yar daria a lokacin da ta fahimci ya tsokani yaren ne, hakama UMMU dake ta bubude kayan abincin
Ummu ta ce" aa fa SHAHEED, kar a haskawa my stars "

Shima dan murmushin ya kuma yi,
Ummu ta kai dubanta wajen yan matan da suke serving tare a da, tun daga kan Zahrau har kan Najeeba aman a yau du sun nutsu irin kamar sunna tsoron su motsa su mutun nan

Da kulawa ta ce" yan mata yau ba za'a zuba ba? Oya maza ku tashi ku yi serving dinmu "

Du sai suka kuma mikewa su hudun nan, sai ya kasance sunna hada ido da junna kowace na son fashewa da yar uwarta da kuka

Ammi cikin jin dadi ta ce" Ke NAJEEBA, ki zubawa mijinki "

Gaba daya sai suka waiwaya suka kalleta, hakan ya saka ta dan zaro ido ta kikifta su a kan yan uwan nata da kuma lokaci daya suka dauke dubansu a kanta kafin ta maida kan Ammi,
Ganni ta yi sam bata kuma bi fa kan maganarta ba, gashi shi din kansa ya yi wani irin zama kamar wanda ya lumshe idannuwansa yake barci bayan idannuwan nasa a kanta suke, kare mata kallo yake haka kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa 'yanzun da wani ne ya zo gaishe da Ammi haka zata fito a gujen nan da irin shigar nan kanta ba ko dan kwali' (ta hade gashin kan nata cen sama irin idan zaka yi bacin nan ta daure hakan sai ya kawatata sosai)

Korar tunanin ya yi, ya ci gaba da bin yan uwanta da kallo ya ga yanda suka yi serving din kannensu baki daya bayan sun bubude sunna tambayar kowane abinda yake so

Ajiyar plat a gabansa ya saka shi bin hannayenta da kallo, kamar da wasa sai da ta ajiye har hudu wanda hakan ya saka shi bude idannuwan da dan mamaki yana binta da kallo

Komawa ta yi kujerarta tana maida numfashi kamar wada ta yi tsere kafin ta ja nata da Zahrau ta zuba mata da har cokali mai yatsu ta shiga dan cacaka aman sam ta kasa ci

Na gabansa ya kuma bi da kallo, harda gayya wannan lamari sai kace wanda mutun shida ne zasu ci abincin? Du ta zuba iya kokarinta sannan babu abinda bata zuba ba ta ajiye

Ammi da Ummu kam summa cike da farin ciki suka shiga kokarin jan nasu, a sanyaye Ammi ta yi adu'ar cin abinci a bayane wanda hakan ya saka da sauri wa'inda suka sha'afa suka kama aka idasa da su kafin du a fara cin abincin

Ina iya cewa yaren da su Ammi su ke gwagwarmayarsu ta hanyar cin abincinsu hankali kwonce,
Sauran yan matan da suka dan fara tasawa da wa'inda suka tasa din sam sai suka kasa cin wani abin kirki sakamakon irin yanda tarbiyarsu take na kasa cin abu a waje gaban wani bakuwar fuska , hakan sai ya zame masu wani irin cin abinci su din nan gaban SULTAN SHAHEED

Shima a hankali yake tsakurar wanda ya janyo gabansa yana hankalce da yanda NAJEEBA ke ta wasa da spoon din cikin salak zala da aka zuba mata wai ita ba zata ci mai nauyi ta zama katotuwa ba

Hannunsa ya mika a hankali ya dauki yan kunnayen da suke rigama a kansu, hakan ya sa ta dago da ta sauri ta bi hannun nasa da kallo har ya maida kusa da plat dinsa ya ajiye sannan sam baya kallonta kamar bai yi wani abu ba ya gimtse abinsa

Satar kallon su Ammi ta yi, sai ta ga su ta farin cikinsu suke, duda ba mai magana aman sun kasance masu yalwataciyar fara'a a fuskokinsu

Hannunta ta mika ta dora saman yan kunnen, ba zato tana shirin daukewa ta ji nasa a saman nata
A hankali ya shafa saman hannun nata wanda hakan ya sakata zare ido da zare hannun nata da sauri tana kallonsa

Da sauri Zahrau da su UMMU suka kawar da kai cike da mamaki, ita kuwa sai ta harhade fuskarta kamar zata fashe da kuka sannan sunna hada ido ta murguda bakinta gefe tana kara tura bakin haka kuma tana son zare hannun nata aman jin nasa take ya riketa taf

Ido ya zaro gannin rashin kunyar da take masa, sai ya dan yi murmushi yana gannin su Ammi har sun kamala hakan ya saka a hankali ya kara murza bayan hannunta sannan ya yi aiki da yan yatsunsa biyu ya zare yan kunnayen ya mayar gabansa ya ci gaba da dan cin abincin

Baki ta turo gaba sosai ta ringa kallonsa, shi kuwa sam baya kallonta, su Ammi kansu sun kula da yannayinsu aman ba wanda ya nuna ya ga wani abin

Nan da nan kowa ya gama cin abincinsa banda Najeeba da ta yi ta cika tana batsewa

Ammi ta kalleta ta ce" Najeeba, ya haka? Ki ci abincin mana na ga baki ci komai ba"

Najeeba ta kara takwakwafe fuskarta sai kawai ta saki dan kukan shagwaba ta ce " Ammi, yan kunnayena ya dauka bayan da tsada sosai na siye su fa "

Shi kansa da mamaki yake kallon fuskarta da lebunnanta da take hadawa tana kukan tabarar da su, haka kawai ya samu kansa da kara tsare fuskarta da ido yana jin wani irin abu tamkar tabarar tata na birge shi

Dan tissu ya ja yana goge bakinsa ya tabe bakin nasa bai ce komai ba

Ammi ta kale shi, ta ce" eyah yayansu bata abinta mana baka ga itace karama, ai ummuna ta bar mata ko?"

Ummu ta turo baki itama ta ce" Ammi, to tace na bata sai na bata aman ta daina yin karyar wai ita ta siya "

Najeeba ta gala mata harara ta ki yin magana tana kara matsar kwalar dole sannan baki daya ta saki jikinta rigar jikinta bata dameta ba tana ta kara tura bakinta da yannayi na rigima take ji

Dan murmushi ya yi a lokacin da ya mike tsaye, tura yan kunnen ya yi a aljihunsa sannan ya kai dubansa wajen su Nusaiba

Hannunsa ya mika mata a hankali ya ce" Nusaiba zo"

Nusaiba dake kallon fuskarsa da yar dariyarta ta yi wajensa ta kama hannunsa ta rike tana ta kara kallon fuskarsa so take ta tina inda ta sanshi

Murmushi ya kuma yi mata ya dauketa baki dayanta sannan ya yi wajen babar kujerar fallon ya zauna yana ajiyeta gefensa kafin ya shiga yi mata wasa

Da yannayin farin ciki iyayen suka karasa wajensa gannin da gaske zama ne zai yi tare da su du sai suka bar yaren nan zaune

Kasa kasa Bilkissu ta ce" auntyna dan girman Allah wannan shine sarki?"

Ummukulsum ta gyada mata kai tana murmushi

Bilkissu ta ce" wauh, walahi haka yake da kyau? Kuma ashe ba tsoho bane auntu Najeeba ke cewa za'a aura mata tsoho, kuma Aunty ya fita kyauma ko?"

Najeeba ta ringa share fuskarta ita a dole fushi take, kuma Ammi bata amso mata yan kunnen ba, ita haka kawai take son yan kunnayen ba wani na zinari ba karfe ne sak aman an masu tsari ne sosai,

Yar dariya Ummu ta yi tana kallonta ta ce" SORRY sis, ba zan kuma ba na bara maki yan kunnayen kin ji kanwata?"

Zahrau da ta gama amsa waya kasa kasa ta kashe tana binsu da kallo a hankali ta ce" ta ina zamu fita ne? "

Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu ta ce" gaskiya gwara ya ringa rufe maku kansa, ina wannan da budewa yake ai da rikicin mai yawa ne, lalle Najeeba baki da kunya wannan ne kike cewa ke bakya son fari waye waye? Tap, yanzu dai Aunty Zahrau tashi mu je kawai kar mu yi da sanyi, walahi mu je, kai ni daga yau na daina jin haushin kishin Zinaria a barta ta yi kishin mijinta walahi"

Su dai kannanun karasawa suka yi suka hadu da shi da su Ummu sunna wasan su

Da yake AMMI ta san da fitar salamarta kawai suka yi suka tafi su uku tare da dogaran da zasu dafe masu baya har mutun hudu

Sai da ta gama zamanta saman table din sannan ta mike bayan ta yiwa yaya DAYABU mesage cewar tana son ya shigo mata da babar waya da layi

Niyarta ta ratsa ta yi shigewarta daki domin yayunta fu sun fice, kannen nata kuwa kowane ya shiga wasansa kafin malamin makarantarsu ta islamiya ya zo

A tausashe, yana sauraran hirar iyayensa da suke bashi labaru kala daban daban ya bi bayanta da kallo kasa kasa har ta bacewa ganninsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya dago dubansa ya dora saman AMMI, a sanyaye ya ce" *SHIN LAFIA UMANI AKA RIKEN MATA YAU KWANA HUDU BATA ZO INDA NAKE BA?*

Ammi ta kale shi da sauri tana kara jin dirara magangannunsa a kunnayenta, UMMU kuwa sai ta kaida kanta a kasan zuciyarta tana murmushi, AMMI na kallonsa da kulawa ta ce"








*SAKON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU A DUK INDA KUKE, NA SAN KUN SAN DALILIN SHIRUNMU BAKI DAYA YAN NIGER, ALHAMDULILAH MAY BE KOMAI YA DAIDAITA, SOSAI NA TARAR DA SAKWANI MASU MATUKAR YAWA YAN UWA DA AMINAN ARZIKI, DA YAWA NA NUNA TASHIN HANKALIN
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment