Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

surprise din da kika ce min kin adana mana?"

Najeeba na satar kallon budurwar nan tana kokarin fita ta gyada kanta da wani irin sauri ta saki hannun yan uwanta ta finciko hannun budurwar da ta kasance karya uwar fada, domin dai ita sanadiyar fada du an yayage mata fuskarta da reza an yi mata dinkunna hakama a wuyanta tafka tafkan dinkunna ne na ciwo ga kuma wajen girarta

Ai kuwa a shirye take, ita ta fara kokarin kaima NAJEEBA bugu, cikin ikon Allah wajen ya nemi harfitsewa domin kuwa da kyau NAJEEBA ta ware take rama rigimar da bata yi ba na satitika dan kuwa har ta tsigewa budurwar nan kitson kanta jinni ya fara zuba hakan ya sa itama cike da bacin rai ta ciro rezarta ta nemi yanke mata jiki, daidai polisan nan sun shigo da gudu dan Zahrau ta kirasu tana ihun su taimaka, Najeeba kuwa ta saka hannunta ta tare rezar sai aka yanketa a hannunta yanka mai girman da jinni ya bale mata

Yanda suka ringa hankado du wani mai rigimar waje ne ya saka shi kara tsaida abin a kansu yana kallo
Su kansu sai a nan suka ankara da Habu, shima sukai waje da shi

Kokowa ce ake tsakanin NAJEEBA da yayunta, ihu take su saketa sun tatare sun riketa sai tirjiya take ja hakan ke sakawa suke kara matsowa waje ga hannunta da Ummulkhair ke ta kokarin daurewa sunna mata ihun ta tsaya ta tsaya aman firrr ta ki idonta ya rufe ji take baki faya zuciyarta ke son tsayawa idan har bata janyo makoloton yarinyar cen ba

Police din ne ya umarci su saketa, dan kuwa su sunna wajen nan dan su hanna du wata fitina da shigar du wani fitinane ko namiji, sai gashi yau ranar farko an fara a haka? Sunna tunanin hutu ne ya same su ashe dai zasu motsi motsi na arziki?

Zahrau ta ce" ba zaka gane ba, ka bamu hanya mu koma gida da ita idan muka saketa mu muka san wa muka saki"

Irin jarumin nan, sannan yana so su gane shi ko zuwa gaba dan idan ana son tsaro su nemi sunnansa a masarautar ya ce" Gimbiya ki yi hakuri ku saketa , mun san aikinmu zamu iya da komai"

Zahrau gannin Yaya Dayabu yana tahowa da wani irin sauri sai ta saki Najeeba, domin kuwa ta tabata a irin yanda yake jefa kafar nan tasa idan ya iso su kansu sai sun sha mari dan haka ta shirya karbar nata, ita dai kam ta shiga uku, dama Najeeba sai da ta fada mata yau ta tabata sai an yi rigima domin haka ne idan ta jima bata fito ba takan tarar da an shiryawa fitowarta, shine harda fadin ita kuwa ba zata kula kowa ba

Sunna sasauta mata rikon da wani irin karfi ta yi ciki da police din nan, wanda hakan ya saka SUKTAN kara rintse idannuwansa yana jin bugun zuciyarsa ya karu kashi casa'in, numfashinsa ne ya ringa doka masa da karfi yana fita da sauri, idannuwansa suka kara yin ja a lokacin da ya ga ta daki police din nan da hannayenta uwa uba ciki ta yi da shi wanda hakan ya zo masa a ba zata ya nemi riketa ta damki damtsen hannunta da karfi dan ya samu ya hanna mata ficewa,
Dan daudun nan na nesa kadan yana ta dira yana ihun a saketa ya tare mata matsiyaciyar nan shegiya busashiyar karuwa

Juwa ke daukan NAJEEBA dan da gaske jinni take zubarwa mai mugun yawa aman zuciyar ta shuwa ta tashi, idannuwanta sun gama rufewa sai ta cire makwogwaron karuwar cen

Baki dayansa ya mike tsaye, jikinsa har rawa yake tablette din a hannunsa ya saketa sakamakon gannin da gaske Police din nan so yake ya rungume masa mata ta baya dan ya ci karfinta ya hannata zuwa wajen fadan ita kuwa tana son fin karfinsa, gashi dayan kuwa du yana ta fitar da kutane yana fadin kar wanda ya dawo sai da katin gidan sarautar da za'a buga a rarabawa du wani client dinta

DAU kake jin karar wani mahaukacin marin da ya saka NAJEEBA dauke wuta lokaci daya , domin gaba daya hayaniyar nan ce ta dauke mata ta daina jin maganar kowa, sai kuma fatar idannuwanta sukai mata nauyin tsiya a saman lebenta take son furta kalmar nan kwaya hudu wato *yaya ka mare ni?*
Aman fir maganar ta ki fitowa a lokacin da ya warci hannunta dake cikin na Police din nan ya yi mata wani irin ja ya karasa kusan yayunta da du suka aniya kare fuskokinsu sai dai cikin ikon ALLAH da hannun nasa na hagu ya shiga sauke masu tankadeta mareta ciki kuwa harda bakuwar yau tau, wace yau yau ta fara irin haduwar nan da su haka, hakan ya sa ta kwala wata kara idannuwanta waje ta dafe kuncin nata tana zazaro ido cike da mamaki da tsoro da tashin hankali harma ta ringa jin zata saki fitsari

Luuu take yi daga bayan DAYABU wanda bai cika hannunta ba ya aniya zazaga masifa, sai dai lokaci daya ya yi tsittt sakamakon irin yanda jibga jibgan dogaran Fadar suka shiga cika wajen da wani irin bulaloli a hannayensu sunna dakatar da du wanda bai rigaya ya baiwa kafarsa mai ya kara gaba ba, sunna gurfanar da su

Lokaci daya Amintace ya ware babar muryarsa fuskar nan tasa a hade ya furta" ku zube a kasa, ga MAI DAMAGARAM zai karaso, kowa ya kai gwuiwarsa kasa ya sanda dubansa ko kuwa na rantse da wanda raina ke hannunsa zan saka babarbara na yanke kafafuwan mutun sannan na kwakwale idannuwan shege domin ga MAI WUKAR YANKA NAN TAFE

Cikin ikon ALLAH tun daga kan polisan, har zuwa su yaya DAYABU da sauran mutanen dake wajen du suka zube kan gwuiwoyinsu, a nan ne NAJEEBA ta tafi luuuuu ta kusan faduwa kasa, sai dai Yaya Dayabu bai bari ba ya saka hannunsa ya tarota jikinsa yana kallon fuskarta gabansa ya fadi, a hankali ya dora kansa saman goshinta hawayen da yake ta rikewa dan marin kannen nasa da ya yi suka samu damar fitowa, Zahrau kuwa hannunta na rawa kasa kasa ta kara tauke kullin hannun NAJEEBA kafin ta saci kallon dogaran nan da baki dayansu suka yi wani irin gurfanawa hannayensu a jijimke sunna masu kawo gaisuwa sai dai ba magana, wajen kuwa ya yi wani irin dif ba magana sai ajiyar zuciya kala daban daban dake tashi, sai kuma takun tafiyar dake shaida koma waye ke yinta yana yinta ne da fushi, da kuma karfi


Zuciyoyi ne suka shiga tsintsinkewa a lokacin da Amintacen sarki ya kai gwuiwarsa guda kasa dayar a tankwashe ya dago jimkaken hannunsa kansa a kasa muryarsa sama sama ya ce""""""





Hello mutanen yaya ne=Ø
Þ, sorry walahi yarinya ne ba lafia, godia nake da sauki yanzun Alhamdulilah>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß


*Na*


*SAJIDA*


=Ø«Ü(' *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*<Øß
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_>ØÝ

& *[ T.M.N.A]* & =ØÖÜ=ØŠÝþ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



53

Sai da ya ware murya, wanda hakan zai iya tsoratar da wanda bai saba ji ba, ya nutsar da wanda ya saba ji, jikin mutun ya kwashi tsuma ba tare da shi aka koda ba amintacen sarki ya ce" Gagara badau kake dan sarki jikan sarki, takawarka lafia jarumi hamshaki barde, kai ne namu kai ne nasu kai din na kowa ne, tafiyarka ke shaida sahunka Mai wukar yanka, kai ne usulin Babarbara ba itace usulinka ba, daga kasa kake dagowa sai ka nuna sama ka saki, baka fito ba sai da ka shirya *SULTAN SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* Takawarka lafia miji a wajen *ZINARIA, NADIA DA NAJEEBA,*

Idannuwansa da suka cenza launi ya daga a hankali ya sauke dubansa a kanta, gashin kanta da ta daure ribom din ya kunce gaba daya gashin ya sauko sosai yana walagigi
Hannayenta a fili, dama dama rigar bata yaye ba sannan da safa a kafafuwanta

Dan gyaran murya ya yi a sanyaye hakan ya sa amintacensa mikewa da sauri tsaye

Da idannuwansa ya kai dubansa kan Habu dake ta rawar jiki ya dan dantse gefen lebensa sannan ya kuma duban police din nan

Ba magana ya yi ba, aman irin kwatancen ya yi ya saka amintacensa fahimta
Nan da nan aka shiga salamar mutanen banda su biyun nan
Du kawunnansu a sasade suke ba wanda ya dago har aka fitar da mutanen nan baki daya sannan ya sauke dubansa kan bakuwar fuskar dake cikinsu

Bai ce komai ba sai takawa da ya ringa yi har ya karasa wajen da suke tsugune

Hannayensa ya saka ya dan rage tsayinsa
Hannunsa dake talabe da ita ya cire sannan ya dauketa da hannayensa
Muryarsa ciki ciki ya ce" ka kai Bilkissu aeroport yanzu

Daga haka ya juya da NAJEEBA a hannunsa ba tare da ya kuma bi ta kan kowa ba har ya bacewa ganninsu

Sai da Amintace ya basu damar dago kansu sannan du suka dadago a tsorace, dogaran nan ne suka kara korar kowa suka rurufe sannan suka dora gadi a wajen

Kuka Zahrau ke yi bilhaki, domin ko gidan fir an hanna mata komawa , DAYABU ya dubeta yana tuki zasu karasa aeroport murya da fada fada ya ce" Zahrau, ko ki min shiru ko kuwa na baki mamaki a nan, aman kin ban mamaki, kin bani mamaki Zahrau, kina tsaye kina kallo? Da darajarku da komai ku zubar da wannan rashin mutuncin? Zahrau kin san waye SHAHEED a kan NAJEEBA? Lalle ina mai adu'ar Allah ya sanyaya fushinsa, ina rokon Allah ya sasauta masa damuwarsa, Zahrau SHAHEED ne ya fito da kansa a irin wannan lokacin ya dauki NAJEEBA da hannayensa a gaban dogaransa, Zahrau kun bani kunya"

Wani kukan ta saka tana yarfe hannayenta ta ce" yaya dan Allah ka yi hakuri, ni kaina sai da na ga abin ya idasa rikicewa, yaya ban gane ban san SHAHEED a kan NAJEEBA ba?"

DAYABU ya girgiza kansa kawai ya yi mata shiru, har sai da suka karasa gidan jirgin sunna zaune dan bai saura minti ashirin su daga ba a hankali ya ce" Harda dan daudu, ga maza nan sunna son rungumota a jikinsu, shin sake na yi da tarbiyarku har haka ko menene?"
Sai kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga bin gefen kumatunsa, hakan ya mugu mugun kara daga hankalin Zahrau dan haka ta ririke hannayensa tana ta girgiza masa kai hankali tashe muryarta a rikice take fadin" Dan Allah kar ka yi mana kuka, ka dakemu, ka yi mana komai dan Allah kar ka tuhumi irin tarbiyar da ka bamu domin kuwa mu mun san kai din ubanmu ne"

Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Zahrau, Allah ya yi rayuwarmu wata iri, tabas na san ba wanda zai iya raba NAJEEBA da fada, aman ban yi tunanin a yanzu da take amsa kiran matar SHAHEED zata cike mayafinta ta nemi dakuwa da wata matar da bata kama darajarta ba, ZAHRAU kema dake dauke da taki darajar kika tsaya a matsayinki da kasancewarki yayarta kuke danbatuwa, to bara ki ji, wace aka turo din AMMI ta kama wayarta dazu kafin mu iso tana fadin ta tabata idan har aka tsokani NAJEEBA sai ta rama, idan kuwa ta zubar da hauka a cikin masarauta ga kishiyoyi ga mijinta mai zafi ana iya kilaceta a dakin horo, daga nan ko uban me take takama da shi an karya saura uwarta, Zahrau wato maradinku ba zai ji kunya ba? Me zai faru, me zai yi mata, Allah masani, aman kun cutar da zuciyata"

Kanta ta dora gefen hannunsa tana hawaye, ita kanta zuciyar tata ta mugun raunana, shin Najeeba wace irin zuciya ne da ita mai karfi fada haka? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une idanfa aka sakata dakin horon? Idan labari ya kaiwa zinaria fa?"
Motar shiru ta dauka a haka har lokacin tafia ya yi, nasiha ya kuma yi mata mai ratsa zuciya kafin su rabu tana ta hawaye, sai da ta shiga ta ga GIMBIYA hakimce a wajen VIP din, dama nan suke zama hakan ya bata mamaki matuka, ta gaisheta da mutuntawa aman ita sai ta cire kai kamar bata santa ba.

Zaune yake ya cire rawanin, kansa sade kasa ya dafe kan nasa da hannayensa biyu biyu yana kallon kasa

Da wani irin sauri AMMI ta nufi wajen NAJEEBA dake shinfide saman doguwar kujera, UMMU kuwa ta yi wajensa hankali tashe ta saka hannunta ta cire nasa tana kallon fuskarsa har sai da gabanta ya yanke ya fadi

Idannuwanta ta lumshe tana jin wani irin daci a zuciyarta, tabas AMMI ta fada mata komai dangane da wayar Mardiya, ita ta hanna a shaida masu dan tana son gannin yaya zasu tafiyar da abin, sai gashi cikin sauki sun tafka rashin hankalin da abu daya take jira shine gannin farkawarta ta nadi jikinta tamkar an aikota

A hankali ta ce da SULTAN" ka yi hakuri "

Idannuwansa ya lumshe, ya kuma budewa a kan UMMU, ya kama hannun nata na dama ya rike a cikin tafukan hannayensa, a hankali ya kai wajen zuciyarsa ya dora yana kara cije lebensa na kasa

Sosai ta kara tsorata tana kallonsa da dan saurin magana ta ce" subahannalah, menene wannan bugawar da zuciyarka ke yi? BILKISSU zo kama min" ta karashe tana azamar mikewa tana kara tataba jikinsa

AMMI ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Dukanta ka yi ne Shaheed? A summe fa take ka barta kwonce haka? Menene ya yi zafi haka Shaheed, dan Allah ka yi hakuri ka sasauta, NAJEEBA yarinya ce sannan ka san rigimarta a hankali du zata daina"

Idannuwansa da sukai masa mugun nauyi ya cire ya dora kanta, shimatt a kwonce take yar baby face dinta ta fito radau, AMMI na kokarin cire mata rigarta har sai da ta cire mata ita ta kai mata ita wajen cikinta hakan ya bayanar da bras din dake cikin rigar fara tas da lafafen cikinta Ammi na tofa mata adu'a bayan ta gama waya da likitan masarautar

Kuma lumshe idannuwansa ya yi, a hankali ya furta" UMANI,"
Sai kuma ya dan ja numfashi yana ta hucin zafin abinda yake ji a ransa ya dora da fadin" UMANI alkyabarta ta cire, Umani a gaban wani kato dake hadasa husumar, Umani sannan ta fito kofar shagonta a haka, kuma Umani police din nan ya kama damtsenta da hannayensa biyu, ya juyar da ita yake son rungume min ita a jikinsa, Umani ta ja DAYABU ya mari fuskarta mai daraja, ta daga muryarta mai daraja kowani banza ya saurara"
Sai kawai ya yi shiru idannuwansa rintse sosai sannan ya sada kansa kasa haka kuma bugun da zuciyarsa ke yi ba wani sasauci

Da sauri AMMI ta cire kanta a kansa ta sada dubanta itama,

UMMU ta cije lebenta na kasa irin yanda ranta ke baci da wannan lamari, a sanyaye ya kuma dagowa wannan karon har jijiyar gaban goshinsa harbawa take a kausashe ya ce" Na sha wahala Umani, Allah ne kawai ya kare min .........sai kuma ya yi shiru ya ki karasa abinda ya yi niyar fadan a hankali ya daki hannun UMMU ya mike tsaye ya kuma kai dubansa inda take

Wajen frij ya nufa da kansa ya dauko ruwa ya dawo
Budewa ya yi ya duka a hankali ya zuba ya shafa mata ruwan nan
Yana yin na biyu ta ja wani irin numfashi ta sauke, lokaci daya ta buda idannuwanta tana ta sauke ajiyar zuciya

A hankali ya kai dubansa wajen AMMI ya ce" Ammi, kar ki kira likita namiji kin ji? Ki kirawo mace"

NAJEEBA ce ta fashe da kuka muryarta na fita kasa kasa ta ce" AMMI, ni ku barni na je na rama Ammi yaya Dayabu ya mare ni ban masa komai ba, Ammi kuma ta zagemu haka kawai bamu yi mata komai ba"

Da wata irin murya mai nuni da daf ake da aiwatar da kowace irin hukunci UMMU ta ce" *NAJEEBA!*

DA sauri Najeeba ta dago, sai a lokacin ta ga SHAHEED, sannan ta ga UMMU

Ai kuwa da sauri ta ringa kokarin jan rigarta, irin ta rufe jikin nan nata, shi kuwa a tsaye yake kikam yana mai bin du wani take takenta da kallo, idannuwansa kuwa sam basu da dadin kallo a irin wannan yannayi

Lebensa na kasa dake datse a bakinsa ya kuma turawa bakin nasa yana mai binta da kallon nan da ta rigaya ta gama gane na tsana ne

Sai da ya lumshe idannuwansa a karo na uku sannan ya mika hannunsa daya ya damki hannun nata

Da hannun nata daya ya mikar da ita da wani irin janta ne ya yi
Bai tsaya kula daya cikinsu ba ya yi ciki da ita wanda hakan ya saka AMMI mikewa tana biye da su da sauri tana fadin" SHAHEED bani yarinyar nan mu koma bangarena, SHAHEED bani y'ata ka ji ko?"

Da sauri Ummu ta saka hannunta ta riko na AMMI, hakan ya sa ta juyo da sauri tana kallonta ta ce" Mariam kar ya dakar min yarinya cikani na karbota" (=ØDÞ)

Ummu ta girgiza mata kai ta ce" mu tafi, idan ta kama ya saka belt ya zane jikin banza da bata da hankali aman walahi ba zaki hana shi hukunta marar kunya ba ehe!"

Da wani irin mamaki Zinaria ta mike tsaye, idannuwanta baki daya ta fitar waje dan tsabar mamaki ta kai dubanta kan amintaciyar baiwarta ta ce" kina nufin Mai Martaba da kansa ya shaida wannan fada?"

Ai kuwa ta kara gyada kanta ta ce" kwarai kuwa Allah ya taimake ki, babu sanarwa sai zagayen su jan gwarzo a wajen, Amintacen sarki ya shela karasowarsa, zuwa lokacin ita kuwa ta summe, na kaiki karshe shi ya dauketa ya juya da ita"

Jim ta yi jin wata magana kuma, hakan ya sa ta kankance idannuwanta ta ce" kikina nufin ba mari ya wanka mata ba ya yi umarnin a kwasheta koda a mace ne ba summa ba a watsata dakin horo?"

Jin muryar uwar dakin nata ta fara baci ya sakata dan dago dubanta, sai dai da sauri ta maida muryarta na dan rawa rawa ta ce" aaaaaaa, Allah ya ja da zamaninki uwar gida kuma amaryar mai damagaram, a irin yanda ransa ke bace fuzgarta ya yi ya jata da karfi ya juya da ita, na tabata zuwa yanzu ya gama gindaya mata jawabin horonta ya saka a shiryata dan zuwa dakin horo , aman na saka a tare min hanyar horon ahalin gida, idan har ta tabata za'a yi kurana a shaida min"

Katseta Zinaria ta yi tana fadin" maza tashi ki gano min, ina nan ina jiran dadadan maganar da zata sanyaya min"

Mikewa ta yi da saurin gaske ta tafi bayan ta kara yi mata kirari, ita kuwa ta koma ta hakimce tana sakin murmushi a fili

AMMI da UMMU tsuru sunna kallon bakuwar y'ar dake zaune a yannayi na takura, ba halin su bata wata kulawar da take da madaukakin girma hakan ya sa du suka tsura mata ido kawai

Wata gwaurywar ajiyar zuciya UMMU ta sauke a hankali ra kai dubanta wajen yan uwan dake shashekar kuka, dan kuwa fada dai na gidan duniya sun sha shi har kamar zata dake su

Maida dubanta ta yi wajen AMMI ta ga waje daya kawai take kallo, ta tabata a cikin zulumin Najeeba take, ita du ba wannan ba, tana cikin tunanin magangannun da suka yi ne da SHAHEED, me ke damunsa? Menene matsalarsa?

Ummu ta kuma kallon AMMI a karro na biyu, ta kai dubanta kan NUSAIBA
Dan murmushi ta yi a sanyaye ta ce" na amince da komawa dakina, idan da hali a gobe gobe"

Da wani irin sauri Ammi ta kallota, hakama su UMMUKULSUM dake cikin halin tashin hankali

Ammi ta ce" ki, kina nufin zaki auri yaya?"

Ummu ta yi murmushi a bayane ta gyada mata kai, ai kuwa zo ka ga irin yanda su Ummukulsum suka rukunkume AMMI sunna rizgar kukan farin ciki, wayo MAMA,

Ita kanta Ammi sai ta ringa jin wani farin ciki marar musaltuwa, a hankali ta mike ta nufi dakinta, tana da bukatar yin hawayen farin ciki, tabas ta godewa Allah da ya nuna mata wannan rana, ta tabata matar rufin asiri, arziki, hakin rayuwa kam bayan Ummu take, yau Allah ya yi wahalarsa ta zo karshe, dama ta sani idan har ta kaita makura zata shiga gidan ne in ya so sai su raba abinda bata so su raban

UMMU kanta irin farin cikin da yaren suka nuna sai ta ji wani irin abu mai girma a cikin zuciyarta, a hankali ta kamo hannun yar uwarsu dake kallonta ta janyi yarinyar ta hade da hannun su Ummulkhair, lalle Allah ya yi zata rayu, gata kuma tsaf kama da ubanta sai dai hasken fata , murmushi ta saki tana jin wani irin farin ciki mai girman gaske na ratsa zuciyarta

yana shiga dakin da ita rigar da take ta rikewa tana zaro ido ya dora hannayensa ya janyeta ja daya kasa

Ido ta idasa fitarwa a mugun tsorace, da sauri ta kankame jikinta gaba daya jikin nata ya kwashi rawa

Kanta a kasa dan matsananciyar kunyar tsayuwarta a gabansa a irin wannan shigar, bakinta na rawa cike da jin tsoron abinda zai mata a yanzun, dan kuwa ba zata taba manta ranar da ya fara kawo mata hari ba, wannan rana ta ajiyeta a wajen da ba zata iya hada komai da ita ba, kwarai ta ci azabar da ta kusan halakata sannan ta ga abinda ya kusan makantata,

Bakinta na rawa rawa ta ce" dan Allah kar ka yi min ka ji? Walahi na wahala, walahi tsoro nake ji sosai"

Ta sauke dubanta a kansa, gani ta yi idannuwansa kyam a kan gukunta dake kadawa sakamakon rawar da jikinta ke yi, ga kuma dan kukan jigidar dake dan tashi dan ko yaya ka motsa zasu shaida kansu ne

Kafafuwanta ta ringa matsewa tana son rike su dan su bar kukan

Bai bata amsa ba sai saka hannunsa da ya yi ya kuma cicibarta wanda hakan ya sakata zaro ido da tsoro da mamaki, domin na dazu bata san an yi ba a summe take

Bayi ya nufa da ita, cikin halin dakiya ya sabeta da soso da sabulu ba tare da ya cire mata kananun kayan da kiri kiri ya hanna kansa cirewar

Yana gamawa ya kuma nadota a tawul sannan ya tsayar da ita tsaye a tsakiyar dakin

A lokacin da ya saka hannayensa cikin tawul din ya ja pant dinta sai kawai ta hangame baki tamkar wace ta summa tama kasa furta koda A ce , sai jikinta da ya kara kwasar rawa ga wani zafi da jikin nata ke dauka na tsoro

Sai da ya cire mata shi a hannunsa ya zagaya bayanta a hankali ya ringa sabule bras dinta hakan ya sa ta kankame tana girgiza kai tana hadiyar wani wahalalan yawu hankalinta sam ba a jikinta ba ta ce" na roke ka, ka yi min rai bana so"

Idan ya tankata to lalle dakin ya tankata, a haka ya idansa zare mata ita itama ya rike a hannayen nasa

Idannuwansa dake da nauyi ya ringa nuna mata bed da su
Hakan ya sa ta matso daf da shi sosai ta saka hannayenta ta riko hannunsa ta kai dubanta saman bed din ta maido saman fuskarsa, kanta ta langwabe ta ce" eyah yayanmu, dan Allah bana son hawa saman gadon cen ka rufa min asiri *yaya SHAHEED* na yi tafiata wajen Ammi kaina ciwo yake, hakama hannuna ka ga yanda ya tsage kuwa? Idan na ce zan yi komai zai yi ta zubar da jinni ne"

Dan bakinta da take maganar kawai ya kurawa ido, shi bama fahimtar yarenta yake ba, a irin yanda yake jin kansa ne baya son yin wani kwakwaran abin da zai kara birkita masa lisafi, so yake ya kadaice ya huce, so yake kafin ya dauki kowani irin mataki ya huce sannan, baya son daukan mataki ransa bace ya zo
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment