Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura dani ba, Hafsat ce kawai zaune tana waya da angonta, ita kau Afnan ta shiga watsa ruwa toilet.

Lallaɓawa nayi gami da kwanciya kafin Hafsat da take tsaye bakin window ta ganni.

"Tashi Tashi na ganki wallahi, gaya man daga ina kuke?" Abunda Naji hafsat ɗin ta faɗa kenan, bansan ma lokacin da ta katse wayar ba, sai ganin ta nayi har ta ƙara so inda nake kwance bisa katifa.

Tashi nayi duk borin kunya ya kama ni, cire hijab ɗin na shiga yi, ina cewa" uhmm wai daga ina muke? Ko dai daga ina nake, ko kin ganni da wani ne da zaki ce daga ina muke?"

" Eh" ta bani amsa kai tsaye, sannan ta ɗora da cewa "ke da Yaya Al'ameen da Yaya Bilal da ganku kun dawo yanzun nan"

Ɗan zaro idanu nayi, kaman ƙasa ta tsage in shige nake ji uwa wadda tayi wa sarki ƙarya.

"Kinga fa wallahi shine ya......" fitowa afnan ce daga toilet ɗin ɗaure da towel ya katse man maganar da nayi niyyar faɗa ma hafsat ɗin.

"Humm" kawai afnan ɗin tace tana ɗan murmusawa, da alama duk taji zancen da mukeyi, saidai ƙala bata ce ba.

Lura da ita ne da Hafsat ɗin tayi ya sanya ta basar da zancen itama, tana mai miƙewa zuwa toilet ɗin.

Duk ina zaune ina saƙawa da warwarewa, har afnan ɗin ta gama shirin kwanciya, lokacin ne Hafsat ta fito da alama itama wanka tayo, "Ki tashi ki bar tinanin hakanan Aunty Suhan kije kiyo wankan kema" Abunda afnan ɗin tace man kenan, ta sake gyara kwanciyar ta gami da juyawa tana murmushi.

Duk fa na bi na tsargu kaina, kaman wadda kwai ya fashemawa haka na miƙe ina jan ƙafafun nawa har na shige toilet ɗin. Da murmushi itama Hafsat ɗin ta bini, tana fatan Abunda take zargi ya tabbata, da tafi kowa jin ɗaɗi, kuma taga ƙarshen Hajiya Kubra da ta ɗauki son duniya da burin duniya ta aza shi akan yaron nata.

Makullin sashen kawai ya miƙa mashi, yana mai cewa "bari in nemo mana Abunda zamu ci" Amsa Bilal ɗin yayi gami da juyawa ya nufi sashen aminin nashi, yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya kaɗa kan motar gami da sake ficewa daga cikin gidan.

A bisa kujera 3seater ya zube, gajiya fal a cikin jikin shi, Amman ba ita ce tafi damun shi ba, ganin aminin nashi da yayi da yarinyar da yake iƙirarin auren ta, kar dai ace da gaske abokin nashi yake akan zancen yarinyar, saidai lura da yayi da yanda ya gansu, da kuma irin zaman da aka yi cikin motar har kawo dawowar su gidan babu wata alama dake nuna maka cewa su ɗin soyayya suke, Amman in ko haka ne, menene dalilin Al'ameen ɗin na yawo da ita cikin mota da daddare haka?

Ya daɗe nan kwance yana saƙawa da warwarewa har Al'ameen ɗin ya dawo, nan ya tada shi kwance yayi zurfi a tinani, ɗan dukan shi yayi a cinya yana "tashi yallaɓai, ba dai bacci kake yi ba haka, ko wanka ba kayi ba balle kaci abinci"

Tashi yayi yana murje ido, yayin da Al'ameen ɗin ya wuce kitchen ɗauko spoons da plate da lemo da ruwan sha, a haka ya dawo ya tada abokin nashi zaune yana narai narai da idanu.

Zuba masu abincin yayi, yayin da ya jawo stool ya ɗora masu akai, Al'ameen ya san darajar baƙo, duk da kasancewar Bilal ɗin ɗan gida kuma aminin shi, haka yake in yaso har ruwan wanka yana haɗa mashi in ya kawo mashi ziyara.

Har suka gama cin abincin, Bilal na ma Al'ameennɗin kallon tuhuma, to abunka da aminai, tini Al'ameen ɗin ya ɗago shi, murmushi yayi yana mai goge baki da tissue

"Bari in gaya maka Abunda kake son tambaya ta tin kafin ka tambaya, yarinyar da ka ganni ɗazu ya ita, na san dai ka santa kasan komai a kanta, kuma har yanzu ina kan baka na a kanta, saidai ita bana tsammani ntasan komai, dalilin da ya sanya kuma ka ganni tare da ita, shine....... " nan ya kwashe komai ya faɗa mashi a gajarce.

Murmushi yayi yana faɗin" Mugu, watau har kasan Abunda nake son tambayar ka ko? To ai shikenan Allah ya zaɓa mafi alkhairi a cikin Al'amarin, Amman dai ka kula gudun ja ma yarinyar matsala ko a wajen mahaifiyarka, kadai ga yanda take iya ƙoƙari wajen bata tarbiyya" yana faɗin haka shima ya ajiye spoon ɗin dake hannun shi ya tashi gami da shige wa bedroom domin yin wanka da rama salloli dake kanshi, sannan ya kwanta, shi kau oga Al'ameen, maida komai yayi kitchen, gami da wanke na wankewa, ya gyara komai tsaf, dama haka yake, baya son ƙazanta ko kaɗan, duk wani abu da ya san zai yi na tsabta baya jira ayi mashi shi keyi da kanshi, saidai Abunda ya san zai ɓata masa lokaci ne. Hatta da girki ba Abunda bai iya dafawa ba, saboda shi ba abincin kowa yake iya ci ba, ko zaman da yayi ƙasashe waje shi keyi a kanshi abinci, matuƙar bai yadda da wanda aka kawo mashi daga cikin hotel ɗin ba.

Sun daɗe suna fira kafin su kwanta, yayin da ni kuma har bayan na kwanta ɗin juye juye kawai nake yi, hafsat ɗin na kula dani, har yanzu bata gaji da wayar ba haka, tinani nake yi na abubuwa da dama, Amman tinanin nawa yafi karkata ma ga Jarabawa da na rubuta kusan kwanaki da dama baya.

Sai daga baya ne tinanin Al'ameen ɗin ya faɗo mani, lallai ni bansan ma me zan kira Abunda yayi mani dashi ba

Gashi in akula har yaja hafsat ta fara mana wata fassara ta daban, ɗan guntun tsaki naja ina mai sake gyara kwanciya ta gami da karanto addu'oin barci, banga dalilin ma ɓata lokaci yin tinanin abun ban haushi ba, ko in kalle shi inji me? Ko ya ɗauka nima ina cikin ƴan matan da suke rububinshin ne oha? 🤷🏻‍♀

Washegari ansha bacci, yayin da maree da mahaifiyarka mama talatun baccin su ragagge ne, suna ta saƙa yanda zasu yi su mallaki Al'ameen ɗin, domin suna hango ma kansu rayuwa ta jin daɗi da zasu iya fuskanta nan gaba kaɗan ba da jimawa ba, saidai Abunda ya ƙara ɗugunzuma hankalinau shine ganin da mareen tayi ma Suhan ɗin a motar Al'ameen lokacin da suka dawo, haka ta koma fa tayi ta rusa kuka, da gaske son Al'ameen ɗin ya kamata, yayinda ita kuma mama talatun ba ta wannan take ba, abun duniyar kawai take hange, haka kawai ta shiga ce ma mariyar zauna nan abun duniy ya kashe ki, akan waccen kucakar da na san ko kyauta aka bashi ita ba amsa zai yi ba, kawai dai ita ce da uwar ta ke shisshigi mashi, Amman zanyi ma abun tufkar hanci.

Kowa hidima yake yi fafa, gida fa ya kacame, wasu irin garƙama garƙaman tuƙwane ake ɗorawa, bayan abincin da ake yo order ɗinshi daga manyan restourent.

Ƴan kankiya sunyi bajinta ta nan fannin, domin duk wata sanwa da za'ayi suna kamawa, yayinda ƴan uwan Hajiya kubra kejin sun wuce nan, kaman su ba zasu iya fitowa yin girkin hidima ba, rarraba ake da abinci kaman ba'a so.

Kowa sai shirin yin ƙauyawa yake yi yau, da yake duka amaren yau zasu yi, ko wanne ɓangare shiri akeyi, sai shigowa akeyi da dami damin kara, da su goruba, magarya ɗinta, nan cikin gida kuma an sanya ayi lafiyayyen dambu, da zogala ɗanya, ga lafiyayyar fura da amma da taji lafiyayyen nono da yoghurt da madarar ruwa, abun dai gwanin ban sha'awa.

Hajiya Kubra taji haushi wannan event ɗin, saida taga cewa kowa na murna dashi ne sannan ta sake, to muma ta ɓangare namu mun yi murna, saboda yau ne za'a zama ɗaya, da mai ji da kanshi da mara ji da kanshi duk za'a zama ɗaya, matan sunyi shiga irin ta Fulanin usul, musamman suka ɗauko wasu Fulani suka zo sukayi masu kwalliya irin tasu ta filani, an zane masu fuksokinsu ram da kalli baƙi da ɗige ɗige, sai suka ba kansu dariya, kuma suka burge kansu, masalan da suka ji angunan na cewa sunyi kyau.

Banso banso nake cewa, Amman a haka saida Hafsat da afnan suka matsa aka yi man saisa saisa, nima kayan Fulanin na sanya sun matuƙar amsa ta, sun yi man cif cif, dama saida Hafsat ɗin ta zaɓo mana saƙi mai kyau harda jikkarsu ta Fulani.

A haka kowa ya hallara aka fara event, kasancewar da marece ne, da sauran Haske kuma ga maza a tattare guri guda, ya sanya ni takura, gefe na koma gami da zama bisa wani kututture ƙarƙashin bishiyar gwaba, ina ta kallon su ina dariya, hannuna riƙe da ƴar sandarsu ta Fulani ina wasa da ita.

Kwallon su nake tayi, ina tafaman murmusawa, yanda maza ke gatsar rake suna sha suna santi, gefe mata masu ji da kansu su wasu ne, sun dage suna ta gwaguyar goruba duk don su faranta ma amaren rai, gefe wasu gunsu ne suna ta faman afa tambu baka, ga wasu dandalin gefe suna ta faman shan fura cikin ƙorai masu matuƙar kyau da suka sha zanen wuta.

Wasu kuma suna zaune gefe wasu kuma a tsaye suna zance da samarin su, kai abun dai kaman a ƙauye, sai abun ya burgeni, hannuna riƙe da taura guda ɗaya ina ta faman jujjuya ta, ina so inci ina jin kunyar ɗimbin maza, abokan anguna da suke ta wajen.

"Allah kuwa Friend ina son leƙa wa wurin cen fa, Naji kiɗan mu na gargajiya na tashi fa a wajen, har ma na ƙagara inje," Bilal ne da yake tsaye bisa kan Ya ameen ɗin, shi kuma yana kishingiɗe yana latsa waya yake bashi amsa

"To kaje mana, ai ni dama ban hana ka ba, Nidai na gaya maka, hidimar yara ce ba zan shiga ba."

Ɗan murmushi yayi, son zuwa wajen na ƙara tsuma shi, "Pls Pls Al'ameen Dont do that to me please i beg u Friend"

Ɗan tsaki yaja a hankali yana mai miƙewa "Muje na lura kai in maye ne ya kama mutum sai ya lashe mashi kurwa tas wallahi"

"Eah Naji ba komai shege, tinda fa ba kai kayi niyya ba, ai komai ma zaka iya faɗa"

Je rawa sukayi suna ci gaba da tafiya, har zuwa tafkeken lambun nasu da ya wadatu da mutane da ɓawon rake da wasu suke gefe suna ta fama n fere bayan suna rage mashi baƙi.

Da ƙafar dama Bilal ɗin ya shiga wurin, domin yana saka ƙafa ya hango one of his colique a cikin abokan ango, ya ja area cen gefe yana ta zuƙar zaƙin rake, hannun Al'ameen ɗin yaja suka isa har inda yake zaune bisa wani dutsi shida abokan shi.

Ji yai an taɓo shi ta baya, ai waigawar da zai yi sai suka haɗa ido da Bilal ɗin, a sukwabe ya tashi yana ihu, "Wow wa nake gani nan kaman Bilal Musaddiƙ ja?" ya faɗa cikin murna, yanayi yana murza ido da gudan hannun da bai riƙe karan ba.

"Nine son Ubanka Mubin, long time not see, ka ɓace ɓat fa baba, ya rayuwa?" y a faɗa yana mai kamo hannun Bilal ɗin.

"bikin wa kazo nan?" Wanda aka kira da Mubin ɗinne ke tambayar Bilal, dariya Bilal ɗin yayi gami da cewa "Kai zan tambaya Mubin ai ni nan gidan mu ne, duka amaren ƙannai ma ne, wannan shine Abokina Moh'd Almustapha Dambulan da kuke jin labarin shi" ya faɗa yana mai juyawa gami da nuna Al'ameen ɗin da yake tsaye yana ta faman doka murmushi.

Su kansu miƙewa sukayi gami da miƙa ma Al'ameen ɗin hannu suna mai girmamawa, "Nyc to meet you our gallant Yaya" suka faɗa cikin barkwanci, har yanzu basu bar shan ka ransu ba.

"Bikin fa Sadeeq Mufti akeyi angon Hafsat, ai mu so mu gayyace ka shi sadeeq ɗin ya hana a cewarshi ayyuka sunyi maka yawa, da wahala ka shigo Nija withing this Period of time"

Mubeen ɗin ya faɗa cikin jin daɗin ganin abokin nashi.

"Braboo, ai banga ta zama ba, muje ka nuna man shegen surukin namu" ya faɗa yana kamo hannun Al'ameen.

Sun gaggaisa sosai, nan suka shiga firar yaushe rabo, shi dai Al'ameen ɗin sai faman murmushi yake, mutane sai zuwa suke gaida shi, da waɗanda suka sanshi a zahiri da waɗanda ma sunanshi kaɗai suke ji, nan da nan fa aka shiga kallon Moh'd Al'ameen ɗin gami da nuna shi, waɗanda ma basu san shi ba yau duk sun sanshi kuma sun ganshi.

Duk abubuwan dake faruwa ina zaune gefe ina kallo, nayi mamakin yanda sunan Al'ameen ɗin ya buɗe wajen cikin ɗannƙanƙanin lokaci, koda yake shi ɗin mai yi ne, na matsa ne, domin kafin ka samu matashi kaman shi da yake da kishin matsa da samar masu da ayyukan yi sai ka tona.

Wani ƙadangare ne da bansan da tahowa shi ba, ga dukkan alamu ma faɗa suke yi, irin manyan nan ne masu jan kai da bindi.

*Jiffff*


Ƙarar fadowar ƙadangare ne bisa kaina ya zabura dani daga faman murmushi da nake yi, ƙara na ƙwalla gami da daka tsalle, bai sauka ba ma, sai ƙara maƙalƙaleni a yayi yana neman shige wa cikin riga ta.

Wata razananniyar ƙara na kuma saki da saida ta karaɗe illahirin lambun nan baki ɗaya, lokaci guda na saki ajiyar zuciya ina mai sulale wa ƙasa sumammiya.

Rige rigen isa inda nake yaushe suka shiga yi, Al'ameen ne, da Bilal sai Hafsat da afnan, tini suka ƙaraso inda nake kwance a sume, Afnan ce ta tallafi kaina tana sakin wani tsumammen kuka, lokacin da ƙadangaren ya sauka daga bisa jikina ya sulale abin shi yanayi yana gyaɗa kai.

"ta suma Yaya ta suma ka taimaka mata" Abunda afnan ɗin ke faɗi kenan, daidai lokacin da su Saudat da Nihal suka iso wurin su da tawagar ƙawayen nasu, da sauran angunan nasu.

Baiyi wata wata ba ya sun kuce ta, hankalinshi a tashe ya nufi cikin gidan da ita, har yanzu bata ko motsi bata san inda kanta yake ba.

Sakin baki sukayi gami da bin shi da kallo, tini ƴan maganganu suka baibaye wurin, wasu na cewa ƙanwar shi ce, wasu na cewa budurwar shi ce.

*To koma dai miye ku biyo alƙalamin ~Oum-Deedat~ domin jin yanda zata kaya*


~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~25~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Rasa inda zai nufa yayi da ita, daya kalle ta yaga yanda take sake a hannun shi, sai ya ƙara ɗaga ƙafa, sashen shi da yafi kusa da lambun ya nufa da ita kai tsaye.

Bai ajiye ta a ko'ina ba sai bisa gadon shi, Bilal Sadeeq Afnan da Hafsat amarya da suke biye dashi, cikin su babu wanda baiyi mamakin shi ba, to saidai shi ɗin ba tasu yake yi ba.

Ruwa yace Afnan ta ɗauko masu sanyi, miƙewa yayi daga bisa gadon yace Afnan ɗin ta shafa mata a fuska.

Ajiyar zuciya na sauke, jin saukar ruwan a fuska ta, har saida ƙirjina ya ɗaga sosai, ƙoƙarin miƙewa nake yi afnan ɗin ta sanya hannu ta maidani kwance.

Lamo nayi ina sauke ajiye zuciya a hankali a hankali, har yanzu jikina rawa yajeyi, tsoro gami da firgici har yanzu bai sake ni ba.

A hankali zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeni, ganin ina rawar sanyi ne ya sanya ta jawo bargo ta lulluɓeni ruf, ga tashin bargo ga laushi katifa, uwa uba wani daɗaɗɗen ƙamshi da nake shaƙa suka taru suka sanya nayi luf abuna.

Juyawa Ya Ameen ɗin yayi gami da fita daga ɗakin, ganin haka ne Sadeeq ɗin da Bilal suka mara mashi baya wajen ficewa su bamu wuri.

Afnan ce ta kalli Hafsat gami da cewa "Aunty Hafsat ya kamata ki koma wajen baƙi, kinga ke amarya ce, ba kin baro mutane kizo ki zauna nan ba, gashi ba'a tashi daga event ɗin ba, ga kuma angonki da baƙin shi"

Miƙewa hafsat ɗin tayi gami da cewa "bari inje in sallama kowa, ni na tashi hakanan" girgiza mata kai Afnan ɗin tayi, kiyi haƙuri, Aunty Suhan ta samu lafiya, kinga ma bacci take yi, kar kiyi haka, kije nima gani nan zuwa"

Hafsat ɗince ta shiga gyaɗa kai, sannan ta juya gami da fita itama, a falo ta taddasu zazzaune ba mai ce a ɗan uwanshi kanzil, gara ma Bilal da yake ta fama latsa waya, ganin fitowar ta ne ya sanya Sadeeq ɗin shima miƙewa yana cewa "ya jikin ta ne?"

"Ta samu bacci ne, kasan Suhan da mugun tsoro, ita fa abu kaɗan ma kan firgita ta balle wannan ƙaton ƙadangaren"

"Haka ne kam, gaskiya dole ta firgita, Allah ya bata lafiya" binta yayi suka fice tare gami da komawa wajen baƙin nasu.

Sun tadda an cigaba da hidima kaman ba Abunda ya faru, baƙin nasu dai ne sai a hankali, ganin yanda amaryar tasu ta firgita ya nuna masu cewa lallai itama ƴar gidan ce, hakan ce ta sanya jikin su yayi sanyi, saida suka ga dawowar su sana suka saki jiki aka yi ta kwasar gara da nishaɗi, su kau dama su Saudat ɗin taɓe baki sukayi, gnai da cewa Allah ya bata lafiya, suka koma wajen ƙawayen su aka cigaba da shagali, domin Suhan ɗin bata kai wadda zasu tashi hankalin su a kanta ba, ko mutuwa tayi balle ta ruguza masu farin cikin da suke ciki.

Har aka tashi Afnan bata dawo ba, ita kau Hafsat dama tinda ta koma bata saki jiki ba, ƙawayenta sai bata haƙuri suke yi gami da ban bakin ƙawar tata zata samu lafiya.

Cikin hanzari ta nufi sashen na Yayan nasu bayan duk ta sallama baƙi masu komawa, na cikin gidan kuma ta raka su sashen nasu na amare, gami da ɗaukar excuse ɗin cewa zata je ta dawo.

Miƙa nayi, salati ɗauke a bakina, sannan na karanto addu'ar tashi daga bacci, wara idanu nayi, gami da saurin yaye bargon da aka lulluɓeni dashi.

Nazarin ɗakin na shiga yi, ba ɗakin umma ta bane, ba kuma ɗakin Hafsat bane, ba kuma asibiti bane, to ina ne nan aka kawo ni, har bisa gado harda kuma lulluɓeni?

Zumbur nayi na tashi, ina mai ƙoƙarin sauka daga kan gadon, dafe da kaina dake saramun alamun ciwo.

Afnan ce ta shigo ɗakin da saurin ta jin alamun motsi, kamfani tayi gami da taimaka man na zauna, ƙafafu a a ƙasa.

Bin ɗakin na shiga yi da kallo, ɗakin Ya ameen😳 bisa gadon shi🤭 ni Suhan???

Aikau a sukwane na miƙe har ina harɗewa da zanin gadon da ya maƙale man a ƙafa.

"Yi a hankali Aunty Suhan" Abunda afnan ɗin ke cewa kenan

"Afnan nan kaman ɗakin Ya Ameen? Wa ya kawo ni nan? Me yasa?" na shiga jero mata tambayoyi a firgice ina mai jiran amsar ta.

Ɗan murmushi tayi gami da jan numfashi, "to miye? Ai ya ameen ɗin ne ma da kansa ya ɗauko ki ya kawo ki nan kuma......."

Katse mata hanzari nayi daga amso shin da take bani, " me? Ya ɗauko ni fa kika ce? Au shine ma ya ɗauko ni ya kawo ni nan?" na faɗa ina ɗan jinjina kai gaba jiran ƙarin bayani.

" To miye ne? Kaji aunty Suhan da wani zance, ke ba ƙanwar sa bace? Kuma ai nan yafi kusa akan cen cikin gida, hankalin mu fa duk ya tashi wallahi, masalan ma shi, mu ai mun ɗauka abun yafi haka, ashe razana ce kawai"

Gaba nayi ina mai cewa "ai na warke, wajen umma ta zanje ni" jawo hannuwana ta shiga yi, ki bari su dawo yaje siyo maki maganin zazzaɓi, kar yazo ya tadda baƙya nan inda ya ajiyeki"

Girgiza mata kai na shiga yi, kayan kunya iri iri ina shan shi ƴan kwanaki nan, kaji fa wai shine ma ya ɗauko ni da kansa, kaman wata baby, kuma wai kar yazo ya tadda bana nan inda ya ajiye ni, kaman wata kayansa😗

"ya baki ki kawo mani, ina sashen mu" Abunda nace kenan ina mai ficewa daga sashen, kai tsaye ɗakin namu na tura na shiga, umma ta da bata nan kuma bata kulle ɗakin ba, hakan ce ta sanya ni kwanciya dafe da kaina da yake ta sara man kaman zai faɗo.

Ɗan murmushi Afnan ɗin tayi, gami da gyara gadon, ta nayi tana zancen zuci, "lallai ya Ameen da gaske yake, kaji fa yanda ya ruɗe, ko mune dai bama lafiya ai iyakar ruɗewa da zai yi kenan" 😉☺

Bilal ne da yake zaune kujerar mai zaman banza, ya kalli abokin nashi gami da muskutawa ya gyara zama.

"Abokina it seems fa labari yana neman ya cenza, naga fa ka damu da lamarin yarinyar nan over, wai whats going on ne? Yayi maganar in a serious tone.

Ɗan kallon shi Al'ameen yayi yana mai maida hankalin shi kan tuƙi, baya da Abunda zai ce ma Bilal ɗin, ba zai fahimta ba, shi ba zai gane tsabar tausayin da yarinya take bashi ba, halin da suke ciki ita da mahaifiyarta kaɗai abun dubawa ne.

"Oh ba ma da amsa ko" ya faɗa cikin son kauda shirun da Al'ameen ɗin yayi mashi.

Ya fara ƙule shi da waɗan nan maganganu nashi, ashe shi ba mai bashi goyon baya ne ba kan taimakon da yake son yi.

"Idan Kaga kare na shinshinar takalmi...."

"ɗauka zai yi" Bilal ɗin ya ƙara sa mashi yana ɗan murmushi.

Gefen damtse hannun shi ya kaima bugu, "watau shege tini ka fito kayi man bayanin Abunda ke faruwa ka tsaya sai kwana kwana kake yi, nima ai na fara gundura da zaman naka hakan a babu mashinshiniya, saidai fa kasan ka ɗauko dala ba gammo, ka ɗebo ruwan dafa kanka mutumena, ina tsoron Allah ina tsoron Hajiya, bana son Abunda zai baka matsala, kuma hakan ba yana nuna bana tare da kai bane, aa am 100% with you abokina"

Ɗan guntun murmushi na gefen baki Al'ameen ɗin yaja, ga dukkan alamu ya zama al'ada shi.

"Tinda haka kake so kaji, na faɗa hankalinka sai ya kwanta, banza magulmaci"

Dariya Bilal ɗin ya saki, saida yayi mai isar shi sannan ya tsagaita. "Kana nufin don inji daɗi kenan ka faɗa ba gaskiya bane"

"Duk yanda ka ɗauka, naga babu haramci a ciki inma cewa nayi ina so"

"ai ba cewa aka yi haramun bane Alhaji, ana so ne dai a nuna maka matsayi ka yafi gaban ace wannan yarinya kake so da aure, shi fa aure ba abun wasa bane, abu ne for life, zama ne na dindindin"

"Naji malam bilalu, ai sai ka faɗa man yanda yake tinda kayi kaji yanda yake" ya faɗa cikin ɗaure fuska da gundura da zancen.

"Oho dai, ai ko banyi ba ina kan hanya, kuma na fika tinda ina da gurin yi"

"Nima ai ina da burin yi ɗin, tinda gashi na samo"

Tsoki Bilal ɗin yaja cikinbƙuluwabyake cewa "kai dai Kwallon ɗan iska ne wallahi, ana cewa ga ruwa kana ga wuta"

"Eh Naji a barni in faɗa wutar in ƙone ba shikenan ba, kowa ya huta, tsuntsu dayaja ruwa ai shi ruwa kan doka" ya faɗa yana mai ficewa daga motar da tini ya isa gidan.

Afnan ya shiga kira a wayar shi, tazo ta amsar mata maganin, tinda shi tinanin shi har yanzu suna sashe nashi, Shiyasa bai shiga ba.

Bayan ta amsa ne ma take faɗa mashi cewa ai ta koma ɗaki su, wai ba zata iya zama ba kunya take ji.

Bajce komai ba ya nufi sashen nashi Bilal ɗin na biye dashi, "Kudai tabbatar tasha maganin, kinga dare yayi, ciwon daren ake gudu" da to ta amsa mashi tana mai nufar sashen su Suhan ɗin.

Umman tawa ma a haka ta tadda ni, ban gaya mata me ya faru ba, illa dai iyaka nace mata kaina ne yake ɗan man ciwo.

Sannu tayi man tana cewa hayaniya ce.

Saida na sha maganin da Afnan ɗin ta kawo man sannan na kwanta, dama ina fashin sallah ne.

Sannu Afnan ɗin tayi

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment