Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya da kaɗan kuma daɗi ke gareshi, gashi Alkhairin da yayi ma mata san a lokacin da aka yaye su, har shi ya girbi abinda ya shuka.

Sun mashi godiya matuƙa, yayin da Al'ameen ɗin ya bashi ƙaton shi, gami da cewa bayan hidima ta kwaranye ya neme shi su sake gaisa wa sosai, har bakin motar su ya raka su, yana mai ɗaga masu hannu har suka fice daga plazar, sannan ya juya da maɗaukakin farin ciki, dama tini ya daɗe yana addu' ar Allah ya haɗa shi da Al'ameen ɗin ko a hanya ne ya ƙara mashi godiya, domin ya san ba lallai bane in ya neme shi ya same shi.

Daganan suka zarce kasuwa, inda suka shiga neman kayan kwalliyar doki, da ƙyar suka samu, domin har Al'ameen ya gaji har ya fara faɗin su koma gida hakanan shi fa ya fara gajiya da wannan wahalar sannan suna da sauran ayyukan da zasu aiwatar da yawa kafin zuwan daren.

Kalar kayansu kowa ya ɗauka, sun kwaso kayan kwalliya doki sosai, bayan da Bilal ɗin ya tambayi abokin nashi dokin da zai hau, "Farar Goɗiyar" ya bashi amsa a taƙaice cikin gajiyawa.

Ɗan murmushi yayi shi kuma yana faɗin "sai in hau gwaska ni, shi kuma Abie ya hau kule"

Bai tanka mashi ba har suka iso gidan, Barde mai tsaron barar suka kira gami da bashi kayan dokin suna faɗin ya shirya su goben bayan gama cin abincin ɗaurin auren, sannan suka faɗa mashi dawaman da zasuyi amfani dasu a cikin dawakan dake gidan.

Saida suka ajiye kayan sannan suka watsa ruwa gami da cenza kayan jikin su zuwa ƙananan kaya sannan suka fice daga cikin gidan bayan sun ajiye motar suka cenza wata.

Ganin yau bamu da aikin komai, ya sanya mu kwanciya muka huta bayan mun ware duk Abunda muka san zamuyi amfani dashi gobe, to bamu da yawa dama, mu bakwai ne harda amaryar sai mai kwalliyar mu da suka taho ta ita tinda ga Katsinan yasa muka kama mu takwas, ɗaki ne tanƙameme da toilet, bamu takura ba sosai komai namu tsaf yake, kaka zuwaira kaɗai muka fita muka gaida yau sai hafsat ɗin da taje Sashen mamanta, cen ta tadda ummata har take tambayar ta ina ina? Take ce mata ina ɗaki lafiya ta lau.

Washegari tin da asubar fari aka farka kusan ince dukka gidan, bayan gama sallah ne aka shiga ɗora Abunda za'a karya, tinda dugu-dugu aka yi break fast, sai kuma aka shiga hidima wanka, masu girka abinci nayi masu sake shirya harabar gida inda za'ayi zaman cin abinci nayi.

Mu dai bamu tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe, mun tadda an kawo mana kayan karin mu, hakan yasa saida muka gama wanka duka sannan muka zauna zaman karyawa, amarya aka fara shirya mawa, mai kwalliya ta hau aikin ta na cakare amaryar, yayi da muku a muka hau gyara ɗakin namu tsaf.

Tin da aka fara hidimar biki banga afnan ɗin taje sashen nasu ba, Sam ta fita harkar su kaman ba ƴan uwanta ba, koda yake hali ya bambanta Shiyasa basa shiri, Amman da yake halin na Saudat da Nihal ɗin ɗaya ne gashi nan kansu a haɗe yake kaman ƴan biyu, saidai wani lokacin aunty Feena kan aiko mata da Nasreem da Ayan masalan ma in tana wata hidimar da yake ita a ɗaki ta ta sauka da yake cikin babban sashen gidan inda aka sauki ƴan uwa Hajiya Kubran.

Dama tini ta maido kayan ta kaf da ta san zata yi amfani dasu cikin hidimar bikin.

Mun gama gyaran kenan muna hutawa wata ƴar matashiya budurwa tayi sallama, yaran dangin hajiya kubran ne, da suke cike da jiji da kai da tinƙahon su ɗin wasu ne, babu wanda ta gaida ta shiga faɗin "wacece suhan wai? To taje Aunty Saudat na kiranta a ɗakin nasu" tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta tsaya jin me za'a faɗa ba.

Tinawa da wulaƙanci da sukayi mani shekaranjiya ne ya sanya ni zamana ba tare da na raya ma raina zuwa ba, har aka gama ma Hafsat ɗin kwalliyarta aka fara ma Afnan da tace lallai sai an fara yi mani ai ina gaba da ita, kuma nice babbar ƙawa, daƙyal dai ta haƙura aka fara mata, ganin yanda nakafe sai an gama mata sannan za'ayi mani.

Ba sallama saidai muka ganta tsulum cikin ɗakin.

Da matuƙar fushi ta maida kallon ta a kaina, bayan tabo kowa dake cikin ɗakin da kallon baku isa ba.

"Dame kike taƙama ne da har zamu sanya a kira ki kiƙi zuwa? Ta jefo man tambaya, Afnan ce riƙe da ƙugu ba'i na cin ta cikin zuciya, ko kallon inda take banyi ba, haka in bangon dake ɗakin ya tanka mata tau nima na tanka mata.

Hakan yayi bala'i ƙona mata rai kuwa, cikin hasala tace

"Aikin mu anan gidan shine aikin ki, kuma a ƙarƙashin Alfarmar Ya Ameen kuke zaune acikin gidan nan, sannan ina so ne in faɗa maki cewa ke baki kai matsayi da har mu zamu ce ga Abunda mukeso kiyi mana ba ki ƙiya, kuma ba zaki taɓa kai matsayi ba, kwaɗayayyun banza da wofi, ke da waccen sululu kasa ɗin uwar taki..... "

*" Aunty Nihal ya isa"*

*"Ya Isa Hakanan, in ba haka ba wallahi zanje na faɗa ma Ya Ameen ɗin"*

Afnan ce take dakatar da ita cikin ƴar tsawa, ranta in ya kai dubu tau ya ɓaci, bata ma san ta ƙwace fuskar taba daga kwalliyar da akeyi mata, ni kau tini fuska ta ta jiƙe da ruwan hawaye, ji nake kaman ƙjrji na zai tsage zuciya ta ta fito.

Wannan cin fuska yayi yawa, gaban ƙawayen Hafsat da basu san ko ni ɗin wacece ba ta biyo ni nan tana ƙasƙantar dani, tini na ruahe da kuka mai sauti, domin ina jin in har banyi ba zuciya ta zata iya bugawa, Hafsat ɗince ta ƙara so wajen da nake zaune bisa gado bansan lokacin da na tashi zaunen ba.

Bubbuga baya na ta shiga yi, ganin haka ne ya sanya ni rungume ta, Allah ma yaso bata kai ga sanya kaya ta ba, da tini zan cukuikuye su, iri. Daƙumar da nayi mata.

Ita kau Nihal jin hakan da tayi ya sanya ta ficewa tana mai saukin maganganu masu zafi a kaina da umma ta, Afnan ɗince ta miƙe gami da ƙarasowa inda nake ta shiga bani haƙuri, gami da cewa "Bari inzo, ai sai na faɗa ma Yayan tinda su dai basa son zaman lafiya"

Nice na riƙo hannun ta ina mai girgiza mata kai cikin kuka, fasawa tayi gami da shiga lallashi na, daƙyar suka samu nayi shiru, babu wanda bai tausaya man ba a cikin ɗakin Allah wadai suka shiga yi ma Nihal ɗin Afnan na jinsu ƙala bata ce ba, to me zata ce ai halinka shi ake faɗi ko bayan ba ranka kuwa.

Manyan kuloli ne aka shiga shigowa dasu cikin gidan, rumfa guda aka ware da aka jejjera abinciccikan, sai ma'aikata masu serving da aka zube saidai Abunda mutum yake da buƙata a kai mashi, babu kalar nau'ikan abincin da babu acikin gidan nan, har ma da na gargajiya ga masu buƙata, kama daga su Alkubua, fankaso, waina, dambun shinkafa lafiyayye da ya sha zkgala da kayan lambu, to dama dai kowa ya san Katsina wa da wannan cimaka kuma bikin nasu ne, wannan ce ta sanya basu yada al'adar tasu ba.

Kaman yanda aka jejjera abinci cika da lemuka kala kala, haka ma acen tanƙameme hall ɗin da yake mallakin Alhaji Mustapha inda za'ayi walimar cin abincin aka har haɗa komai da taimakon su Al'ameen ɗin da Bilal, basu bar wurin ba hr saida suka ga komai ya kammala, kuma an ware ma manya iyayen ƙasa nasu ɓangaren ta inda babu ma mai ganin su, sannan suka wuce gidan domin shiryawa

Ƙarfe ɗaya ƴan Katsinan suk iso iyayen khadeejar Yaya Aleeyun da yake ma harda shi aka je ɗauko suruka nashi, ya sanya shima saidai abokanan shi ne suka taimaka mashi har haɗa komai.

Har zuwa ƙarfe ɗayan ban yadda anyi mani kwalliya ba, yo ni kwalliyar ma me zanyi? Saida Afnan da Hafsat ɗin suka matsa ne gami da tsoratar dani zasu gaya ma Ya Ameen ɗin Abunda ya faru to, sannan na yarda aka yi mani ƴar Light ba mai yawa ba, duk da haka nayi kyau ba laifi kam.

Kowa na ɗakin namu ya haɗe cikin ƴar ubansun ashoben yinin da ta kasance ƴar ubansu atamfa, fara ce tas sai ƴan pattern na dark blue da Orange, atamfar bata da hayaniya, hakan ce ta sanya tayi matuƙar kyau da haskawa gashi zanenta ba mai irin yawan nan bane jefi jefi ne.

Haka muka shirya cikin atamfar, Nidai kasa tashi ma nayi saboda Hafsat ce ta bada mana ɗinkin da aka yi mana, kasancewa ƴar ƙibar dake gareni ya sanya skirt ɗin kama ni tsam, duk nabi na tsargu kaina, yayin da su kuma sauran suka ruɗe da ganin ƙirar da Allah yayi mni suna cewa dama su.

Gyalena da takalma na masu tsinci duk blue ne, yayin da siririyar sarƙar dake wuya na ta kasance fari tar ɗin duwatsu da kar ta Orange, lallai munyi kyau, kaman yanda vail ɗina yake blue haka na kowa dake ɗakin namu ya kasance, banda Hafsat da ita kalar golden ne gabaɗaya jikin ta hatta sarƙar gold ɗin dake wuyan ta da Sadeeq ɗin ya zubo mata su cikin lefe kaman ba kuɗi ne ya siya ba.

Masu aiki ne suka leƙo sashen namu gami da faɗa mana mu fito za'a fara cin abincin kaman yanda aka tsara.

Tin daga nesa ake kallonmu, domin dai yau duk hassadar ka ba zaka kushe mu ba haka ma amaryar tamu, runfuna ne guda bakwai kaman yanda aka tanada, Hajiya Kubra, Hajiya Zainab, Kaka Zuwaira da tawagarta, sai ta Saudat, Nihal Da Hafsat ɗin. Kowa da tawagar shi yake zaune.

Hajiya Kubra ce na fara hangowa, saboda wani irin kwarjini da cika idanu da take yi, ta kame ɗaya daga cikin kujerun Alfarmar dake ƙarƙashin haɗaɗɗiyar rumfar tata da taji ado da silkin yadi da balam balam.

Sanye take cikin wani ɗanyen pink ɗin lace anyi mata ɗinkin bubu, wuyan nan nata babu Abunda yake yi in banda walƙiya, haka ma kunnuwan ta da hannayen ta da suke cike taf da zobuna da abun hannuwa na gold

Yau ko gyalen ma babu a wuyan ta, sai ƴan fadan ta da suke zaune kujerun da suke gefen nata, sauran kuma duk kansu kujerun ƙarfe ne anyi masu ado da fararen ƙyalle in ka cire na kaka zuwaira da na Hajiya zainab, sai na amare da suke royal chairs kaman na kamu haka.

Rumfar da babu kowa sai kujeru muka nufa gami da zama idanun kowaa kammu masalan ma ni da bani da alama da ƴar aiki ayau, ba wata wata ma'aikata suka fara serving ɗin mutane, baka jin komai sai ƙarar chokulla, ni kau na kasa cin ma abincin sai juya cokali nake ta faman yi.

Da na ɗaga idanu na kuwa sai su faɗa cikin na Hajiya Kubra, data ƙure ni da kallo tana so ta gano Abunda yaja hankalin yaron nata a jikina, saidai duk iya kallon nata bata gano komai ba, domin in hasken fata ne ko hanci babu kalar wanda yaron nata bai gani ba har cen ƙasashen ƙetaren

Da mun haɗa idanu kuwa zan saurin sadda kaina ƙasa saboda irin kallon tsanar da take bina dashi, sa'a ta ɗaya ummata bata wurin domin dukka ƴan aiki acen sashen nasu suke in abincin, hakan ce ta sanya su zama sashen namu, ita kau ummata ma ɗaki ta shiga gami da kwanciya saboda ta gaji gashi har juwa take ji..

Ƙarfe biyu daidai dubban mutane suka shaida ɗaurin auren Saudat Almustapha da Kamal jamu, akan sadaki naira dubu Hamsin, sai Zuwaira (Nihal) da Nuradden Baffa itama akan sadaki naira dubu hamsin, sannan Hafsat Auwalu da Abubakar Sadeeq Muftee itama akan sadaki naira dubu Hamsin ɗin Sannan na Aleeyj Auwalu da Khadeeja Ibrahim akan sadaki Naira dubu ɗari domin su ne suke da alhakin sanya ma ɗiyar tasu sadaki ba Alhaji Auwalu ba, tinda su cewa sukayi ba kuɗin ke gaban su ba albarka auren da ɗorewa shi suke so.

Bayan kammala ɗaurin auren ne, haka dubban jama'ar suka shaida naɗin ya Ameen ɗin a matsayi *Yariman Matasan Arewa*

Bayan kammala naɗa mashi rawani ne da miƙa mashi sanar girma sai aka lulluɓa mashi alkyabba fara ƙal da surkin royal blue

Tini fa Yariman namu ya Faso, cikin salon tafiyar shi ta ƙasaita, yau kam tafiya ta tabbata, shi ba gadon sarauta ba Allah ya ci dashi, bayan ya kai gaisuwa ne ga dukkanin sarakunan dake wajen mai girma shugaban ƙasa ya mallaka mashi makullin dunƙulalliyar mota ƙirar royce - royce 2019 da lambogini 2019 collection a matsayi kyautar shi shi kuma, nan fa aka yi ta mashi kyaututtuka, fadawan da aka mallaka mashi suna mashi godiya, a haka ya nufo cikin gidan Bilal ɗin na take mashi baya domin zuwa kaima tashi mahaifiyar gaisuwa.

Matasa kuwa ya gansu kowa so yake ya gaida shi, don ma fadawan na buɗe mashi hanya, a haka ya ratso dimbin mutanen nan har zuwa cikin gidan nasu.

Tin daga nesa mahaifiyar tashi ta hango shi, Miƙewa tayi gami da isa wajen shi, baiyi wata wata ba kuwa ya sunkuya ya kai gaisuwa gareta, itama bata yi wata wata ba ta sunkuya gami da rungumo shi cikin ƙirjinta ta miƙe tsaye dashi, sowa aka ɗauka da tafi kowa sun burge shi, yanyameshi aka shiga yi ana ta kai gaisuwa, abokan wasa na yankar shi, hatta da kaka zuwairan da take tafiya daƙyar saida ta taso ta iso gareshi.

Sa hannu yayi ya rungumo ta gami da ɗora mata peck a tsakiyar kai, dungureshi tayi tana mai cewa "ja'iri girma ya hau kanka yanzu saura mata"

Haka yabi yana rungume ƙannen nashi amare da suka kai gareshi Hafsat ce kawai bai runguma ba, saidai ya kamo mata hannu yana mai cewa "Congrat ƙanwa ta" da murmushi ta bishi tana mai cewa " Same Yaya"

Duk yanda dogarawan nan suke kaffa kaffa da daƙunar da ake kai mashi, dole suka haƙura, domin sabon babin ɗaukar hotuna ne aka buɗe kowa so yake ya shiga ayi dashi, masalan dangin Hajiya Kubran da suke ji su wasu isassu ne.

Nikau da nake zaune sai sarkin murmushi nake yi akai akai, domin sun matuƙar burgeni, sarauta yayan namu tayi mashi kyau matuƙa, sai naga har girma kaman ya ƙara da cika ido, sai faman murmushi yake yi, shi kau Bilal bakin nan nashi kaman gonar auduga.

Maida kaka zuwaira aka yi aka zaunar da ita, domin ta gaji sosai gashi shi kin rana suke sosai, domin duk sun baro wurin zaman nasu.

Binshi kowa ya shiga yi da idanu ganin ya sulale ya fara tafiya, ƴar razana nayi ganin ya nufo inda nake zaune, waigawa na shiga yi domin ganin ko akwai wani kusa dani da yake nufo inda nake zaune.

Ganin da gaske yake yi ni yake tunkaro wa ya sanya ni sauke kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuwa na duka biyu, bansan ma me zanyi ba, wane kalar tinani zanyi, gashi dai kowa mu yake kallo.

Hannuwan nawa Naji an kama, bansan lokacin da na miƙe tsaye ba, jana ya shiga yi zuwa wajen mai ɗaukar hoton, saboda tsabar ruɗewa ni kuwa har gyale na yana sumɓulewa, daidai cikin taron jama'a yaja burki ya tsaya, hakan ce nima ta sanya ni tsayawa don dole, uwa ƙasa ta tsage in shige nake ji, gashi kowa ya zuba mana idanu, Hajiya Kubra kuwa kaman idanun ta zasu faɗi ƙasa saboda tsabar yanda ta ƙwalalo idanu tana kallonmu.

*Ke ba zaki zo ki ɗauki hoton bane da mijinki?*

Maganar da ya raɗa mani a kunne kenan daidai lokacin da ya zuƙunna yana mai ɗauko Gyalena daya sumɓule ya shiga yafa mani.

Ai bansan lokacin da na ƙwalalo idanu ina mai Binshi da idanu ba na shiga rufe bakina da hannuwa na ina girgiza kai na.

Ɗaga murya yayi sosai yanda kowa zai iya ji ya shiga faɗin

*Alƙasim ga mata ta ina son ka ɗauke mu ni da ita kaɗai bana son kowa ya shiga in banda amini na Bilal*

Ya faɗa da wani killer smile a saman fuskar shi yana yi yana cije leɓon shi guda ɗaya gami da kafa ma Mahaifiyar tashi idanu.....


🤣🤣🤣🤣🤣



~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._



*Page ~28~*


*A madadin ƴan Banfi ƙarfin ta ba Fans*

Gaisuwa da saƙon ta'aziyya zuwa ga ƙawarmu kuma ƴar uwarmu mai bada goyon baya da ƙoƙarin comment, (Salamatu Muhammad) a bisa rasuwar mahaifinta da tayi, Allah ubangiji ya jiƙanshi ya sanya ya huta y baku haƙurin rashin shi, ya sanya kwanciya hutu ce, ya bashi ikon amsa tambayoyin kabari,ya raya Abunda ya bari yayi masu Albarka Ameen. 🤲🏻


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Hajiya kubra wadda ta zabura da niyyar isa wurin da yake tsaye riƙe da hannuwan Suhan ɗin, da sauri Hajiya Sa'a ta riƙo hannun ta, domin ta kula sarai da niyyar hajiyar yanda take fitar da huci kaɗai ya isa ya shaida maka Allah ne kaɗai zai kare Al'ameen ɗin daga marukan da taso zazzagba mashi.

Ganin za'ayi abun kunya ne a wurin Hajiya sa'ar ta shiga jan hannuwan ta zuwa cikin gidan ba tare da kowa ya ankare ba, domin kuwa kowa hankalin shi na kan Al'ameen ɗin da dogarawanshi suka zage suna ta gyara mashi malum malum da take suɓulewa.

Rasa inda zan tsoma rain inji daɗi nayi, lallai wannan maganar tayi man tsauri, ƙwaƙwalwa ta har bana jin zata iya ɗauka, tini naga duniyar na juya mani, duk da hasknn flasher ta ko ina da take ta haske mu, ƙoƙarin zare hannuwa na nake yi domin in samu in ruga, na kula ma saboda tsabar yanda na tsorata numfashina har wani ɗauke wa yake yi.

Gabaki ɗaya hankalin ƴan matan dake wurin ya tashi, waɗanda ma basu kula da ko waceceni ba, son sanin ba'asi suke yi.

Ran kaka zuwaira kwal, lallai yau kowa ya shaida Al'ameen ɗin akwai wacce yake so, mutane da dama zasu dena yi mashi kallon mai ɗaga ma ƴan mata kai, saidai ita ɗin wannan wacece?

Daga baƙin ƙofar gate, makaɗa da mawaƙa ne da masu kirari suna ta wasa Al'ameen ɗin da mahaian shi, Abie ne ke ta masu ruwan kuɗi fuskar nan taf da fara'a, duk wainar da ake toyawa a harabr gidan ma bai sani ba.

Bilal ne ya zare jiki daga wurin da yake tsaye zuwa sashn Al'ameen ɗin, sannan ya ɗauko waya ya latso lambar Al'ameen ɗin.

Daga cikin Aljihu yaji wayar tashi na vibrating, hannuna ya saki da niyyar ɗauko wayar, ni kau ganin wannan damar ta samu na zare hannuwan nawa gami da nufar sashnn namu kai tsaye harda haɗawa da ƴar sassarfa.

Ganin Bilal ɗinne ya sanya shi ɗan juyawa bai hango shi ba, domin shi dai ya san tare suka shigo gidan, to ina kuma ya nufa? Bai ɗaga ba har ta katse, yana ƙoƙarin bin kiran wani ya sake shigowa ɗagawa yayi sannan ya kara akunne

"Malam wai me kake yi ne haka? Menene dalili ka nayin hakan? Baka gudun kaja ma yarinyar wata matsala kuma? Ka saki yarinyar mutane hakanan, kuma ka shirya amsar hukunci daga wajen Mom domin ba don Allah ya tsare ka ba an janye ta da kasha maruka a gaban bainar jama'a"

Bilal ɗin ya faɗa ta ɓangare ɗaya, shi kau gogan kasaƙe yayi da wayar har bai a san Bilal ɗin ya kashe ba, ƴar dariya yayi mai cike da yaƙe lokacin da yaji "ƴaƴan Goggo Fatima na yankar shi wai dole sai sun ɗauki hoto dashi tinda amaryar tashi mai kunya ce ta gudu, shi kau da baya da kunya dole ya tsaya.

Ganin da yayi zai ɓata ma kanshi lokaci ne wajen ɗaukar hoton ya sanya shi juyawa kai tsayezuwa ga sashen nashi, baya ma jin yunwa, ko da yana ji kuma baya tinanin ma in zai iya kai wani abu bakin shi.

Daga bakin ƙofa dogaransuka ja suka dogare, kai tsaye ya kutsa kanshi har cikin bedroom ɗin nashi inda ya tada Bilal ɗin nata faman kaiwa da komowa.

Da ƴar sassarfa ya isa inda Al'ameen ɗin ke tsaye, cikin ɗan ɗaga murya ya shiga faɗin "me kayi haka ne? Hakan da kayi kana ganin daidai ne? Kana nufin zaka ja da mahaifiyarka ne? Ta wanna sigar ya kamata ka ɓullo ma Al'amarin?" ya ƙarshe yana mai zagaye Al'ameen ɗin ya nufi jikin window ya tsaya ba tare ma da ya san ya isa wurin ba.

Yana tausaya ma abokin nashi, Abunda zai je ya komo baya hasashen idan zai zo ma abokin nashi da sauƙi, amsar shi kawai yake jira, saidai jin Al'ameen ɗin bai tanka bane ya sanya shi juyawa domin yaga halin da abokin nashi yake ciki.

Shi kau ta ɓangaren shi, duk da kalamnn abokin nashi sun Dakar mashi zuciya kuma ya jisu har cikin ƙwaƙwalwar shi hakan bai sanya yaji ko ɗar a cikin zuciyar shi ba, karaya da wuri ba nashi bane ba, wannan karon dole ne ya nuna ma magulmata cewa hassadr su da baƙin cikin su babu inda zasu kai su sai fagen nadama.

Takawa ya shiga yi har zuwa gaban gadon nashi, har yanzu bai ko tanka ma abokin nashi ba,baya so ne ya kai shi ga faɗin dukkan Abunda ke cikin zuciyar shi a fili, shi yafi so saidai kawai aga yana aikatawa.

"Kanajina malam kayi mani banza, wato baka ma da lokaci na ko? To inaso ka sani dukkan Abunda ya taso kar a ƙasa ran zaka tunkaro ni ka samu mafita, maganin kar ayi to fa kar a soma"

Bilal ɗin ya faɗa sannan ya juya da niyyar barin ɗakin.

Al'ameen ɗin da yake ta ƙoƙarin cire kayan nashi domin ya watsa ruwa, barin cire kayan nashi yayi sannan ya juyo a hankali yana faɗin "Dakata Malam"

Dakatawa bilal ɗin yayi ga barin ɗakin da yayi niyya.

A hankali Al'ameen ya shiga ta kowa kaman mai jin tausayin ƙasa, har zuwa inda bilal ɗin yake tsaye, a hankali ya sanya dukkan hannuwan shi ya dafa ka faɗar bilal ɗin, sannan ya shiga faɗin

"Ni Moh'd Al'ameen nine mazinaci, fasiƙi mai neman yarinya da lalata har cikin ɗaki na, ni take tallata ma kanta ni kuma nake biye mata alhali ina cikin hankali na...."

Bilal ɗinne ya dakatar dashi ta hanyar sauke dukkanin hannuwan da yayi amfani dasu wajen dafa kafaɗar bilal ɗin

" Dakata Friend, kana cikin hankalina kuwa? Kasan me kake faɗa? Ya zaka dinga jifar kanka da waɗannan mugayen kalaman? Ko dai ka fara shaye shaye ne ban sani ba?"

Bilal ɗin ya faɗa cikin ɗaga murya, ga dukkan alamu kalaman abokin nashi sun ɓata mashi rayuwa gabaɗaya.

" Na sani Bilal, na san me nake faɗa, kuma waɗannan magangannn ba daga bakina suka fito ba, daga bakin mahaifiya ta suka fito, and kuma bansan wanene ya faɗa ba, shine naga tinda har neman yarinyar akeso inyi to zan fa nema ɗin Amman ba ta hanyar da su suke nemana da ita ba, ta hanyar da shari'a tazo mana da ita, watauta hanyar *Aure*"

Ya faɗa shima cikin ɗan ɗaga murya kaɗan, saidai Sam na bakin ƙofa ko na cikin falon ba lallai ne ya iya jiyo Abunda yake faɗa ba.

" Huh"

Bilal ɗin ya sauke ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi, a hankali shima ya shiga takawa har zuwa gaban gadon, daɓas ya zauna yana mai dafe kanshi da yake sara mashi uwa zai rabe gida biyu, wannan shine dalilin

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment