Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rashin lafiyrr abokin nashi? To indai haka ne munafukan na acikin gidan, lallai tausayin abokin nashi da na yarinyar da ake neman a laƙaba ma sharri bata ji ba bata gani b ya tsira mashi har cikin zuciya.

Sake miƙewa yayi gami da isa ta inda abokin nashi ke tsaye ya haɗe kai da bango yana ta faman maida numfashi yayi, da dukkanin alamu ɓacin ran nashi ya sake komawa sabo fil a cikin zuciyar shi.

Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo abokin nashi har zuwa lokacin da ya zaunar dashi bisa gadon nasu, shima zaunawa yayi a hankali, shi ya ma rasa tinanin me zai yi a ranshi, llai abokin nashi na buƙatar wanda zai taya shi wannan yaƙin da ya tunkaro ka, ace wai a wurin aiki baka samu matsala ba sai a cikin gida.

Ummata da take kishigiɗe bisa darduma, gama sallar ta kenan ta jawo cesbaha tana ja idanun ta a lumshe, tsulum na faɗa ɗakin namu ina ta faman haki, ni ban ma san umman tawa na cikin ɗakin ba, ai da bari nayi sai na saisaita kaina sannan in shiga.

Da hanzarin ta ta tashi tana mai cewa "ke lafiyar ki kuwa? Ko wani abu ne ya same ki? "

Ganin ban bata amsa ba ya sanya ta ficewa da niyyar zuwa taga menene yake faruwa, saidai bata fahimci komai ba, saboda ko da ta isa wurin mutanen ta tadda wasu suna ta faman cin abinci yayin da wasu ke ta faman ɗaukar hoto da Al'ameen ɗin. Hakan ce ta sanya ta dawowa zuwa ɗakin gami da share ni ta cigaba da laziminta, in na matsu na faɗa mata Abunda ya tashi hankalin nawa.

Ban gama warwarewa ba sai ga Hafsat da Afnan sun shigo cikin ɗakin, cewa sukayi in biyo su muje ko suyi mani tonon silili wurin umman tawa. Ba arziƙi na miƙe gami da yafa mayafi na na bi bayan su, ina kula da Afnan wacce take Ƙunshe dariya a cikinta. Da kallo umman tawa ta bimu tana kaɗa kai, koma miye in tayi wari taji.

Masifa da bala'i ba kalar wanda Hajiya Kubran bata sha ba cikin ɗaki, haƙuri suka dinga ɓata, kada ta ɓata taron bikin nan DON Allah, da ita cewa ma tayi aje a sallami kowa tinda an gama cin abincin.

Shawarwari ba kalar wanda ba'a bata ba, daƙyal suka samu tayi haƙurin zuwa dare ayi wacce za'ayi, cikin gidan zata ga mai zaman wani a cikin su ko ita ko su, lallai wannan aikin asiri ne tsab, kenan ma Abunda aka faɗa ɗin ya tabbata gaskiya ne, inko hakane wallahi Sam ba zata saɓu ba bindiga a ruwa.

Abunda ya faru ɗin sai ya sanya ƴan ƙanannn maganganu suka shiga yawo a cikin gidan bikin, duk inda Kaga gungu an haɗa kai maganar akeyi, lallai Hajiya Kubra ta faɗi ƙasa babu nauyi inko har ta bari ɗanɗanta da aka yi ittifaƙin tafi son shi akan dukkanin sauran ƴaƴan nata ya auri talakrr ƴar aikin su.

To dama itama dai Abunda take gudu kenan, kuma tini labarin gulmammakin da akeyi cikin gidan ya isa kunnen ta, domin duk inda ka zaga maganar akeyi.

Hakan ce ta sanya bata ƙara fitowa harabrr gidan ba, duk wanda yazo saidai a shiga dashi sashen nata, shima ɗin saidai in manya ne, inko jigari jigari ne iyakar su babban falo a basu abinci suci ba ta gudunmuwar da suka kawo take yi ba, Alla Alla take yi dare yayi domin ayi wacce za'ayi.

Kusan ma zamu iya cewa bikin sai ya koma sashen hajiya zainab da kaka zuwaira, dama su ta fannin su abun yayi masu 100% sun yaba da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, alwashi dai sun sha shi indai da gaske Al'ameen ɗin yake yi yana son yarinyar itama tana son shi to fa babu makawa da izinin Allah sai abun ya tabbata, tinda sun san yaron nasu ba irin raggwayen mazan nan bane.

Haka har suka sake shiryawa suka fice dogarawanshi na biye dasu a baya suna mashi kirari da wasa shi wannan karon harda ce mashi Angon Hauwa'u sai dubu ta taru.
Domin duk akan idon su Abunda ya faru ya faru.

Ɗaki suka sanya ni gami da titsiyeni suna tambaya ta wai in faɗa masu lokacin da muka fara soyewa da yayan nasu basu sani ba.

Ba kalar rantsuwrr da banyi masu ba, Amman fir suka ƙi yarda, dole naka bakina nayi masu gum, ina jinsu suka cigaba da zaulaya ta. Afnan ɗince mai cewa

"Ni fa tin lokacin da yaya yazo da maganar auren aunty suhan ɗin na yarda dashi, dama na daɗe ina addu'ar hakan a zuciya ta..."

Hafsat ta amshe da cewa "Kedai bari Afnan, kuma ke fa don ma baki nan, baki ga yanda yake kulawa da al'amarin ta ba ke dakin gani ma kinsan ba banza ba wlh"

"Welcoee to our Family Aunty Suhan" Afnan ɗin ta faɗa tana mai rungumi ni zuwa jikin ta.

Nan suka shantake suna ta zaro fira, ni wani abun ma in sun faɗa saidai in kwalalo idanu, gani nake yi kaman sharrinsu ne kawai Al'ameen ɗin ba zai iya yin hakan ba.

Sauran ƙawayen Hafsat ɗin duk sun dawo ɗaki, nan fa aka buɗe sabuwar fira, cikin su ma har akwai wadda tayi man congrat gami da faɗin "Lallai kunyi matuƙar da cewa, ku duka kun iya zaɓen abokin rayuwa" dariya kawai aka sanya maganar gaskiya zukatn Afnan ɗin da hafsat ɗin cike suke taf da farin ciki marar misaltuwa, yayin da ni kuma ta ɓangareaa na ma rasa kalar tinanin da zanyi, har yanzu ba wai na gaskata bane, gani nake yi kaman mafarki nake yi ko kuma yaudara ce irin ta ɗa namiji akwai Abunda yake son cimma wa.

" ba zata taɓa saɓuwa ba wallahi, ashe yaya bai bar zancen nan ba har yanzu, gaskiya ya zubda mana aji at All wallahi, duk da yau ta kasance ranar farin ciki a gare mu ta wani ɓangaren ranar tazo da akasi"

Nihal ɗin ta faɗa tana mai faɗa wa kan jibgegen gadon nasu inda Saudat da sauran ƙawayen nasu suke ana ta maida yanda akayi

"menene ba zai faru ba? Ai ya riga ya faru saidai Allah ya kyauta gaba kawai, Amman ke kina kallon cikin idanun yaya wallahi kinsan har cikin zuciyar shi ne sonta yake da gaske"

Wata daga cikin ƙawayen nasu ce da ta kasance ƴar uwarsu ta fannin Hajiya Kubra ke faɗin haka, ta bala'n so shi itama a da, ganin ba kula ta yake yi ba, hasali ma ba ta ita yake yi ba, duk iya yin da take dashi da fi'ili lokutta da dama gwasale ta yake yi ko kuma yayi ma kaman bai san ta nayi ba, ya sanya ta dole ta watsrr da makaman soyayyrr nata rabi wani sarkin.
Wata daga cikin ƙawayen ce ta sake amshe zancen da cewa "dalla bari wannan maganar khairi, ai ke kinsan wallahi Ya Ameen ya wuce da ajin wannan ƴar aikin, ni ina gani ko dai asiri sukayi mashi ya aikata a cikin jama'a ba tare da ya san ya aikata ba"
"Confirm cewrr Saudat da take kishigiɗe sai lokacin ta tashi zaune, gaskiya Yaya bai kyauta mana ba Sam, haba ina shi ina wannan kucakar? Duk tarin ƴan matan da suke rububinshi ace bai hango kowa ba sai wannan ruɓusar, ke kiga jikin ta ma fa ko ina a sake take ko irin slimming ɗinnan ma ita bata iyawa saboda duhun kai anfj so a zauna tuɓs ko ina tsoka"

Shewa suka sanya suna faɗin Amman fa Saudat baki da dama wallahi, "Amman fa ni kinsan ina tsoron irin wannan jikin, komai fa suka sanya zama yake das yayi masu kyau daidai jikin su"

Cewar ɗaya daga cikin ƙawayen nasu da suka zo masu hidimar bikin tin daga ƙasar ta ta America.

Nan fa aka buɗe sabon babin yin zancen suhan ɗin duk kusan rabin firar aibantawa yafi yawa a ciki

(Hmmm Allah shi kyauta, Hassada ga mai rabo taki)

Ana gama sallar la'asar aka fara shirin hawan dabar, bayan an ci an sha, anyi hani'an. Sarakunan jihohin namu na arewa suna nan sai washegari zasu koma gruruwan nasu, inda aka yi masu masauki a fadar shugaban ƙasar namu ta nigeria.

Hawan daba fa ya ƙayatar, tashohin gidan talabijin suna ta ɗauka live, matsa dai an gansu a wurin, kowa yayi mamakin irin yanda dawakai suka yalwata a wurin kaman dama an san da naɗin sarautar.

Ƙarfe shida suka gama zagaya duk inda zasu zagaya, manyan namu suka samu suka koma masaukin nasu domin su huta, yayin da cikin gidan yake ɗinke da jama'a gefe guda ga masu kiɗin ƙwarya suna ta chashewa ana masu ɓarin kuɗi, abinci kuwa har kawo yanzu shigowa akeyi da sababbi, duk Abunda kayi sha'awrr ci akwai shi.

Gudun sake tada gulmammaki ya sanya Hajiya Kubran ta dage ta cije, Amman fa har kawo yanzu da magariba ta kawo jiki bata saki jikinta ba, walwalarta har yanzu ragaggiya ce, don ma su Hajiy Lailan na bata baki da shawarwari akan yanda za'a ɓullo ma 'amarin.

Hajiya sa' ar ce tayi mata alwashin ta bar komai a hannun ta nan da kwana uku zata ga Abunda zai faru a cikin gidan. To da haka ne fa ta samu ta lalubo walwala ta yafa a kan fuskar ta Amman ba don har cikin zuciyar ta haka yake ba.

Wannan karon sashen na Al'ameen cike yake da baƙi, abokanan shi da suka zo mashi ɗaurin aure da naɗin sarautar tashi, da yawa ma daga cikin abokan yanzu sunan shi ya tashi daga Ameen ko Dambulan da suke kiran shi dashi ya Koma Yariman Matasa, duk da baya so Amman a haka yake amsawa, saidai kowa ya kula da rashin walwalar tashi, Amman sun mashi uzuri akan cewa hayaniya da jama'a ne.

Gida yayi tsit tin bayan da aka tashi sallar isha'in
Yo kowa ya gaji wasu ma har sun fara bacci, har yanzu zuciya ta a cunkushe take na kasa gane kaina, Alfarmar su Hafsat ɗin na roƙa akan su barni inje in kwana tare da ummata ko Naji sauƙi.

Basu hanani ba, saidai sunce su ba zasu rakani ba, a haka na ratso tsakiyar gidan zuwa sahen namu, ummata har ta kwanta na kwankwasa mata ta buɗe na shiga.

Da kallon ke lafiya kuwa ta bini, yi nayi kaman ban kula da ita ba, kai tsaye na haye katifar na kwanta, yayin da itama ƙalau bata ce mani ba ta hawo itama tare da kwanciya.

Saidai me? Bacci Sam yayi mani ƙaura, idanun a kaman an soya, saboda rashin baccin har wani raɗaɗi suke yi mani. Saidai in juya in sake juyawa, idan na tinank kaɗan sai in ɗan ja tsoki kaɗan in sake juyawa.

Ƙwaƙwalwa ta fa har yanzu a cunkushe take, ina buƙatar wanda zai yi mani fashi baƙi dalla dalla fa, saidai wanene shi?

Wayata ce ta ɗauki haske alamar saƙo ya shigo, da hanzari na jawo ta gami da buɗewa, banyi mamakin sunan shi da nagani ɓaro ɓaro kan screan ɗin a, saidai Abunda saƙon ya ƙunsa shi ne ya bani mamaki.

Ummata wadda bansan da ta tashi zaune ba, kwatsam saidai Naji muryar ta tana mai ceman

"Mamana na kula dake fa tin da rana, ga dukkan alamu akwai Abunda yake damunki, Amman in kinga ɓkyemun shine Abunda yafi ɗin, sai ince Allah ya sanya hakan ne, domin bana so kizo kiyi danasani akan dukkan Al'amurranki, idan kuma kin yanke shawarar faɗa mani tau ina saurarenki"

Cikin ƴar razana bakina na rawa na tura wayar tawa ƙarƙashin follow, bansan lokacin da na shiga ce mata "umma fa ba komai, kawai na gaji ne, kuma gashi kaman ba ɗan jin daɗi ne..."

Na ƙarashe cikin in ina wadda take alamta ba gaskiya a cikin maganar tawa, wanda ni kaina bansan dalilin nawa na ɓoyema umman tawa ba, da duk duniya bani da abokiyar shawarar da ta wuce man ita.

Gyaɗa kai kawai tayi, bata sake ce mani komai ba ta koma ta kwanta, tana fatan Abunda na faɗa ɗin ya kasance gaskiya, duk da bata taɓa kamani da laifin yi mata ƙarya ba.

*_"ki dena yawo cikin dare, sannan ki shirya fuskantar duk wani ƙalubale da ka iya tunkaro mu"_*

Abunda ya rubuta mani kenan, ban iya bashi amsa ba, duk kuwa da karanta saƙon da nayi sau ba adadi.

Ni ya ma ƙara sanya ni cikin wani duhun wallahi, wai ni shin me yake nufi dani ne? So yake ne ya tarwatsa mani ƙwaƙwalwa ne ko kuma me?



~Oum-Deedat ce~

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~29~*




°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



A haka dai na kwana juye juye, zan mabiya cewa ko baccin kirki ban samu nayi ba, umman tawa duk tana kula da dukkan motsi na Amman ƙala bata ce mani ba.

Washegari kuwa tin dasafe aka tashi aka hau shirye shiryen walima da za'a gabatar itama dai a farfajiyar gidan, wannan karon harda dangin anguna duk zasu halarta, daganan ne za'ayi buɗar kai, bayan an gama sai a basu amaryar su su tafi da ita.

Tin da safen kuwa sai ga su Afnan wai sun zo ƙara tafiya dani, aikuwa fir naƙi binsu, ba irin magiyar da basu yi mani ba, Amman na ƙiya, bana so in koma wurin ne a sake samun matsala gashi naga ga dukkan alamu ummata tana shirin zuwa wurin ne.

Kwanciya ta nayi ko bayan fitar su, har itama umman tawa ta kammala shirin ta ta fice, gyara kwanciya ta nayi gami da jan abun lulluɓa domin baccin da ban samu nayi ba a daren jiyan.

An ƙawata wurin fiye da na jiya, tini dangin angunan sun iso tin wajen ƙarfe goma na safiya.

A sashen Hajiya kubran aka yi masu masauki, saidai dangin sadeeq ɗinne suka ce a nuna masu wajen surukar yaron nasu acen ne zasu zauna.

Ba musu aka nuna masu, ganin su manyan mutane kowacce cikin shiga ta alfarma.

Hajiya Zainab ɗin bata yi tinanin haka ba, Shiyasa ba'a shirya masu tarba ba dukkanin kayan tarbar suna cen sashen Hajiya Kubra. Nan fa ta shiga ina taka saka su.

Lura da sukayi ne ya sanya suka ce karta damu kanta, ba wannan ce ta kawo su ba, su yarinya kawai suke so a basu.

Rumfuna bakwai aka kafa ayau, sunsha deciration kuwa, rumfa ta farko ta hajiya kubra ce, sai ta kaka zuwaira, sai ta Hajiya Zainab, sai ta dangin anguna guda uku, gefe kuma ta anguna ce da abokaninsu maza

An zagaye farfajiyar gabaki ɗaya illa iyaka hanyar da za'a bi a wuce.

Ƙatuwar darduma aka shimfiɗa tsakiya inda gefe aka jera amaren kowacce tasha lulluɓi da kalar nata kayan da sukayi masu matuƙar kyau, gefe guda kuma aka jera ƙawayen amaren a yau babu bambanci duk kansu wuri guda suke zaune, cikin atamfar su english, kalar ta yarbawa yellow ne da ɗige ɗigen ja a jikin ta. anyi masu ɗinkin buba duk kansu, hakan ce suka sanya jan gyale da sarƙar murjani a wuyan su ɗaurin zanen ma bisa riga aka yi shi, hannuwan su riƙe da ɗan mafici mai ƴar bazar gashi gashi haka.

Kowa ya hallara, nan fa aka fara gabatar da jawabai da kuma gabatar da kai.

Kowa ka kalla yana cikin farin ciki, banda hajiya kubra da fuskar nan take ba yabo ba fallasa masalan ma data kula dangin iyayen mijin Hafsat ɗin sun zarce na yaran ta gabaki ɗaya a komai kuma.

An kira kowanne ango yazo ya nuna amaryar shi, gami da kama hannun ta zuwa gaban dangin shi ta kai gaisuwa, sannan sauran mutanen, haka suma angunan amaren suka kama su har gaban nasu iyayen suka gaida su. Kaka zuwaira ce duk wanda yaje kusa da ita sai ta zaulayeshi tace ita ba sadaki take so ba na goro take so, haka suka babbata kuɗi gami da komawa suka zauna.

Bayan ƴan abubuwa da aka gabatar aka buƙaci iyayen anguna da su kawo kayan aure.

Nan fa idanun mutane ya shiga buɗewa ganin iyayen kaya na ƙarya da kuma kuɗi da ake ɓari kaman wanda ba'a so.

Ba'a sha mamaki ba saida iyayen mijin na Hafsat suka taso, nan fa wuri ya hau tafi da sowa, ganin irin iyayen kuɗin da suka ajiye gabanta, daloli ne iya kallon ka, tare da sarƙar gwal da abun hannunta da zobunan ta wasu irin manya ne ko daga ina kake zaka iya hango su, tare da makullan mota guda biyu, ita ɗaya mahaifiyarta ɗaya, sai makullin tanƙamemen gida da yake nan cikin abujar da suka mallaka ma mahaifin Hafsat ɗin.

Nan fa ƙaryar iyayen su Nihal ta ƙare masalan dangin Hajiya Kubran, saidai ita ce tayi ƙarfin hali ita kuma taba dangin mijin ƴaƴan nata motoci da kujerar Makka a matsaynn tukuicin kayan auren da aka kawo masu.

Hajiya zainab bata san da wannan al'adar ba, hakan ce ta sanya bata tanaji komai ba, gashi kuma mijin nata baya kusa.

Shiru aka yi, kowa naso yaga me su Hajiya Zainab ɗin zasu bada tukuicin wannan babbar kyauta da aka yi masu.

Takawa ya shiga yi har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya ajiye check gami da wata takadda ya koma ya zauna, Ya ameen ne da yake zaune cikin rumfar abokan angunan, tini kuwa kallo ya koma kanshi, Hajiya Kubra tsabar ƙuluwa kaman idanun ta zasu sauka kan Al'ameen ɗin.

Mai jawabi ne ya taka har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya sanya hannu gami da ɗaukar check ɗin da kuma farar takardar da take ƙar babu komai akai sai Rubutun Al'ameen ɗin jiki da ya gaji da ƙayatuwa.

"Masha Allah, Alhaji Moh'd Al'ameen Almustapha Dambulan ya bada tukuicin Zunzurutun kuɗi Naira Million Biyar tare da kujerar hajji ta kimanin mutane biyar da kuma upper ta ɗaukar matasa aiki a cikin Zuriyar angon Hafsat ɗin ƙarƙashin jagorancin kamfanin, suma kimanin mutane Ashirin"

Tafi aka saki, gefe guda wata zabiya ta saki guɗa, babu Abunda kake ji a wurin illa iyaka hayaniyar mutane data kauraye wurin kowa na faɗin Albarkacin bakin shi.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hajiya Zainab ɗin ta sauke, ganin cewa yaron nasu ya fidda su kunya, duk da ta san cewa ba da son ran hajiya kubran da take zaune cen cikin mutanen ta tana ta sakin yaƙen dole bane, Amman ko ba komai ta san Al'ameen ɗin mutum ne mai alkhairi da zai yi ma daman shi ba tare da hagun shi ta sani ba.

Mutum ne mai hangen nesa da kuma kakkaifan tunani, baya buƙatar in zai fidda family ɗin nashi kunya sai ya jira shawara da wani.

Ta ɓangaren Al'ameen ɗin kuwa idanu sukayi mashi yawa, ilahirin ɗaukacin mazan dake rumfar nan ya matuƙar burge su harda mazajen ƙannan nashi kuwa, wannan ta sanya suka ƙara gane B ƙaramin gida sukayi aure ba.

Bayan kammala wasu Al'adun ne aka yi addu'a tare da ƙarin godiya, sai kuma aka fara shirye shiryen miƙa amaren ga dangin mazajen nasu bayan yi masu huɗuba mai ratsa jiki da Alhaji Auwalun da Alhaji Mustaphan sukayi.

Hafsat tasha kuka, da kyar aka ɓanɓareta jikin mahaifiyr tata, babu wanda bata ba tausayi ba, yayin da su kau sauran ƙemadagas iyayen su ne ma suka sanya su mota babu wacce take kuka cikin su.

To a ganin su dai auren so ne, kuma na wayayyu, auren ma sunan anyi ne, Amman suna da ƴancin da zasuyi komai a sadda suka so, kuma a lokacin da suka so.

Kkwacce cikin su an mallaka mata jibgegiyar mota harda Hafsat ɗin kuwa, wannan kuma kyauta ce daga hannun Alhaji Mustaphan bayan gama masu huɗuba da sukayi.

Har aka tafi kaisu kuma basu ma da alamar kukan saɓanin Hafsat da take ta kuka kuma tana laluben ina zata ga Suhan ɗin Amman ko alama bata hango mai kama da ita ba ma.

Abun ya ɓata mata rai matuƙa, har saida tayi ma Afnan magana, wadda ita Hafsat tace zata bi Alabasshi daga baya zata je gidan ƴan uwan nata.

Motoci ne aka zube bayan wadda su mazajen nasu suka kawo, kowacce amarya kake so kabi akwai mota free da zata kaika ta maido ka, duk da dai galibi wasu acen zasu kwana masalan ƙawayen amaren gashi kuma magariba ta doso ta kawo jiki.

Hatta Hajiya kubran saida taji wani iri rabuwa da yaran nata da zata yi duk da ta san cewa koda yaushe zata iya ganin su matuƙar suna ƙasar.

Bayan kammala komai ne da tafiyar dangin angunan da amaren su, aka hau gyaran gidan

Gidan ya rage ƴan tsiraru sai masu aiki kaɗai ya rage don sashen Al'ameen ma babu kowa duk an kammala hidimar biki sun wuce masu jirgin gobe kuma sun koma hotel ɗin da suka sauka sai a goben zasu wuce.

Kafin isha'i fa tas an gyara ko ina an wanke ko ina, wannan karon harda umman tawa da Hajiya Zainab da wasu daga cikin DANGIN alhaji Mustaphan ne suka sanya hannu aka yi dasu.

Nikau ta ɓangare na, Naji matuƙar daɗin yau, kuma ina cikin farin ciki sosai duk da hayaniyar cen cikin gidan dan loud sleaker da ta dameni kusan ma ince hanani bacci tayi.

Ƴan latse latse na na cigaba da yi ni kaɗai a ɗaki, salla kawai ke ta dani. Ko abinci saidai na sha complax da yake ni ba mai yawan ciye ciye bace ba.

Ina cikin latse latse na a Internet naga alamar kaman an saki Jarabawar mu ta jamb da muka zana kwanaki.

Aikuwa cikin sa'a na tabbatas da gaskiyar Al'amari, wata yarinya da muka zauna kusa da kusa mai suna Samira, ita na kira gami da tambayar ta, cikin farin ciki take sanar dani cin Jarabawar tata, wai ashe ma tin numu'a aka saki ban sani ba.

Roƙonta nayi ko zata je ta dubo mani Alabasshi sai in bata kuɗin scratche card idan na fito, ba gardama ta amsa mani da zata duba mani ma yanzu ba sai na ɓata komai ba, saboda na taimake ta sau ba adadi a yayin zaman namu da ita, nan ne take faɗa man numb ta ce tayi loosing tin bayan canza wayar tata, waccen ta faɗi ne, jajanta mata nayi gami da cewa ina jiran ta sai na jita.

Ko awa uku cikakka ba'a yi ba ta kira ni, tin daga muryar ta na gane kan zancen, ko saurarena ma bata yi ba ta shiga yi mani murna, muryar ta cike take taf da farin ciki ga dukkan alamu har cikin zuciyar ta ne.

"Ƙawata kina da sa'a wallahi, zamana kusa dake ya taimake ni kwarai da gaske, ina alfahari da sanin ki a rayuwa ta, dad da mom duk sunce in miƙa saƙon godiyr su gareki takanas zasu zo har gida suyi ma su mom ɗinki godiya, kuma ina farin cikin sanar dake cewa duk school ɗinmu babu mai highest Mark kamarki insha Allah damun gama zan turo maki score ɗinki ki gani, zan kira ki insha Allah in mun tashi zuwa"

Ko jiran godiyar da zanyi mata batayi ba ta kashe wayar, mamaki na shiga yi wannan wace irin yarinya ce, dama ko da muka zauna kusa da Juna duk da lura da nayi ita ɗin ɗiyar wani ƙusan gwamnati ce, Sam hakan baisa ta ɗauki kanta wani abu ba, tana da yawan dariya ga sauƙin kai don itace ta fara yiman magana ma da roƙon in taimake ta don Allah, wannan ce ta sanya na taimaka mata da iya gaskiya ta tinda ita ta karya kanta ta roƙeni.

Ina hawa WhatsApp kuwa sai ga

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment