Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shigo, hannun shi ɗauke da uwar sayayya sosai, har Umman saida tayi mashi faɗa, ya zuwa yanzu ta tabbatar ma kanta ƙaunar dake tsakanin yaran nata, kuma abun alfaharn ta ne ace ɗiyar tata ta samu miji nagari irin Al'ameen yariman matasan.

Washegari kuwa da aiki sosai aka tashi Komai Umma ce keyi, Hajiya Kubra saidai ta kalla, anyi shirin tarar baƙi sosai da sosai, gida fa ya cika da ƴan uwa, abunka ga babban gida, hatta ma'aikata kowa da abunda yake yi, an gyara gida, an ƙalƙale ko'ina. Su kuwa su Nihal da Afnan suna ɗakin Suhan ɗin, suna ta shan firar su, yanzu ta saki jiki da Nihal sosai kaman ba abunda ya faru, anan ne Nihal ɗin ke shaida mata cewa sati mai kamawa take sa ran komawa, domin haka Baby ɗinta ya faɗa mata. Godiya kam ta zuba ma Suhan ita, hada addu'a take yi wai Allah ya sanya Saudat itama ta gane gaskiya.

Saidai Suhan tayi dariya sosai, su duka sunyi kwalliyar su daidai misali, duk da dai maza ne zasu kawo kayan, Amman ai an riga an zama ɗaya, duk Family ne, saboda Ammi ma cewa tayi sai tazo ta duba jikin Suhan ɗin, dan haka da ita aka taho.


Ƙarfe ɗaya na rana baƙi suka iso, tare da tarin kayan Arziƙi, lallai su Ammi mutanen kirki ne, sai gashi Ammi, Umma, Hajiya Kubra, Hajiya Zainab, tare da Mama Fulani an zage ana ta fira sosai, cewa tayi a kira mata Afnan ɗin ta ƙara ganin ta, aiko ta kama ta ta rungume gaban kowa, albarka take saka mata, tare da bata amanar ɗan nata, ba wanda bai ji daɗi ba a wajen, masalan ma Mom, ai sai kuma kunya ta kama ta, gashi ita ta kasa yi ma ɗiyar tasu irin wannan ƙaunar amma gashi ita a gaban kowa take nunawa.

Sunci sunsha sun yi hani'an, wanda duka ƙoƙarin Umma ne. Sai Sam barka ake yi, hada gogan naka aka amshi kayan, da cewa yayi ba zai tsaya ba, saida Suhan ɗin ta nuna mashi rashin jin daɗin ta sosai, sai gashi har Bilal ya kira suka gaggaisa a mutumce wallahi.

Ƙarfe uku suka fara haramar juyawa, aiko kaman kar a rabu, saƙo daga mai martaba ya iske kowa, mutane ne dattijai, wanda suka san me suke yi sosai, ita kanta mom sai taji alfaharin kasancewar ɗiyar tata da Zatayi aure a cikin Family ɗin.

Ko da zasu tafi Ammi kaman kar ta saki Afnan, duk kuwa da yanda take sunne kai ƙasa, shatara ta arziƙi sosai ta kawo ma Suhan da Afnan ɗin, har yanzu tana ƙaunar Suhan, tayi ma Salim sha'awar ta, Amman tunda basu samu ba, ga Afnan nan madadin Suhan ai.

Bayan sun tafi ne aka bar baje kaya sashen Dad ɗin, inda anan ne aka karɓi kayan, Mom sai jin daɗi take yi, lallai ta tabbatar ma kanta taso tafka wauta a baya, abunda yaron nata ya sha nuna mata kenan ada cen baya, Amman ta kulle idanun ta, ta kasa ganewa. Gashi yanzu yaron nata yana fushi da ita sosai daga gaisuwa babu wani abu dake haɗa ta dashi, ko sashen ta ma ya dena shiga sam.


Afnan dai guduwa tayi ɗaki, inda Suhan ma ta ɓaɓɓako da ƙyar zuwa sahen Dad ɗin, duk da tana jin kunya, Amman abu ne na murna, kuma kowa yau yana cikin ta. Ana haka ne sai ga Hafsat itama, tare suka zo da Ummin Bilal, dayake basa da nisa sosai,


Kaya sunyi kyau masha Allah, har ma'aikata sai da akace su shigo su kalla, kai daga baya ma sashen Umma aka maida kayan, ba dan taso ba saidai dan Mom tace haka, ai ita ce Uwar amarya, dan haka wallahi ta bar mata hidimar, aiko an sake shan mamaki, harda Al'ameen da yake zaune gefe saman sofa yana ta faman latsa waya, rabin hankalin shi na kan matar tashi, da ta ƙara kyau tayi wani fayau da ita. Butsu Butsu sai sun haɗa idanu, ita kuma ta haske shi da murmushi, har lumshe idanu yake yi, kai ƙarshe ma har kiss yayi mata gami da hura mata iskar, ita kuma sai ta wani langaɓar da kai, tana dafe saitin zuciyar ta, baisan lokacin da ya saki dariya ba, nan fa hankalin kowa ya koma kanshi, sai ya wayance, yana mai duba wayar shi, alamun wai a cikin wayar ne aka bashi dariya.

Alama yayi mata da idanu, na ta taso ta bishi, kaman ba zata ba, kunya take ji, kada kuma ace har ta fara bin miji daga dawowar su jiya.

Ita ta fara fita, ba jimawa ya bi bayan ta, Hafsat na kula dasu, dariya tayi a zuciya, tana mai ƙara masu addu'ar ƙaunar juna.

A sashen Umman ya tadda ta, ta sha kuwa matsa sosai, yayi missing matar tashi sosai, bata hana shi ba, saidai ta ƙoƙarin daidaita kanta, kada a wuce gona da iri, gashi tana kan bed rest ne.

Ƙaunar juna sosai suke yi, bisa jikin shi tayi masauki, inda shi kuma ya shiga lallaɓa abar shi sosai, kalamai suke musaya masu kwantar da hankali, duk da kowa da abunda yake cikin ran shi, amman ya bar abun a zuciya, dama kawai suke so su samu, kuma ta kuwa zuwa.


Hafsat ce ta fara rutsa su, aiko ya sha caccaka, duk da take ba abokiyar wasan shi ba, sai ga Al'ameen ya zage ya biye mata, har Suhan na shigar mashi, nan ko suka yi ta raha da jin daɗi, har Hafsat ɗin na mamakin Ya Ameen ɗin, soyayyar Suhan ta cenza shi totaly. Sun jima kafin ya fita ya barsu nan tare, shima saida yayi ma Hafsat kandakon cewa ta kula mashi da mata, ko ƙuda baya so ya taɓa ta.





*****************



Cikin kwana biyu jiki na yayi sauƙi sosai, kulawa nake samu daga both side sosai, har mamaki nake yi, Dad da kanshi yake shigowa har ɗaki gaishe ni da jiki, har fira ya kan tsaya muyi a lokutta da dama, masalan ma idan Al'ameen na kusa.

A tsakanin ne kuma maganar komawar Nihal ta taso, ba yanda banyi a barni inje raka ta ba, aka hana ni wai nabi dokar likita dai. Umma da Hajiya Zainab ne suka je suka maida ta, sai Afnan da Hafsat, tasha kuka kaman ba ita ba, Nihal tayi sauƙi sosai, duk wannan halin nata, kaman an wanke mata shi tas, ta canza sosai kaman ba ita ba, godiya dai na shata sosai da sosai, sai gashi washegari Nureen ɗin ya Kira ni yana man godiya sosai.

Kusan zamu iya cewa yanzu kanmu ya haɗu, mom na ɗauke ta a matsayin uwa kuma suruka, so nake na mance komai, kuma ina so na mance ɗin, Amman har sai Naji alaƙar dake tsakanin mu, wadda har ta sanya Al'ameen juya ma mahaifiyar tashi baya, bana jin daɗi, Sam, nasha alwashin yi mashi magana.



kaman kullum
Zaune take falo, riƙe da ɗan ƙaramin littafi na husnil muslim tana karantawa, tayi zurfi sosai a karatun na fito daga ɗakin nawa. Sallama ta kawai ta amsa, tana mai maida kanta ga karatun addu'on nata.

"Umma sannu da hutawa" na faɗa, ina mai zamewa ƙasa na zauna sosai, na miƙe ƙafa ta.

"Yauwa" kawai ta iya ce man ta maida kanta ga littafin.

"Umma magana nazo muyi fa" ɗagowa tayi cikin kulawa sosai, sai kuma tace "Ko dai jikin ne?"

Ɗan girgiza mata kai nayi, ina mai jin nauyin maganar da zata fito daga baki na. Saidai ya zama dole ne a gare ni, indai ina so al'amura su tafi man kaman yanda ake so.

"To menene? Ko ɗakin ki kike son komawa?" ta sake tambaya ta. Kunya ce ta lulluɓeni, ƙasa nayi da kaina, ina wasa da ƴar ƙulalan doguwar riga ta, da akayi mata ado da stone sunyi kyau sosai, kuma sun haska ni sosai, dayake kalar ja ce.

"Umma kiyi haƙuri in magana ta ta ɓata maki rai, banyi da niyya ba, saidai naga kaman lokaci yayi, Umman Dan Allah ki sanar dani wanene mahaifi na, sannan kuma wace alaƙa ce tsakanin mu da Mom ɗin su Ya Ameen?"

Cikin sauri Umma ta sake kafe ni da idanu, kaman zasu faɗi ƙasa, sai kuma ta nisa, tana mai ɗaukar remote na Ac ta ƙara Ƙarfin gudun ta, tayi mamaki sosai, take taji iska ta dena shigar ta, sai wani irin zufa da ta ringa tsiyayo mata ta ko'ina. Bata taɓa tsammanin zan zo mata da irin wannan maganar ba, bata taɓa kawo ma ranta cewa nasan akwai wata alaƙa dake tsakani ba.

"Uhmm" ta kuma nisawa, sai ta ɗauke kanta ga barin kallo na.

"Mamana menene dalilin ki na zuwa mani da wannan maganar? Shin ban hane ki ba? Na rage ki da wani abu? Ko Dad ɗin ku bai cancanci maye gurbin mahaifin ki ba?" ta faɗa a hankali cikin wani irin yanayi.

"Umma kiyi haƙuri nace, haƙiƙa Dad ya cancanci fiye ma da Uba, to Amman kinsan tsakanin mahaifi da ɗa, please Umma ki taimaka ki fada man, ko zan samu sauƙi, ko zan ji sanyi, ko zan samu amsoshin da nake son inji daga gareki, *shin Muna da alaƙa ta jini ne da Mom?"*

"Ya isa Mamana, ki dena man wannan maganar, Mom Mahaifiyar take a gareki, kuma Suruka, ki barshi kawai a haka, bansan jin komai daga haka"

Ta faɗa cikin ɗaga murya, tana mai miƙewa zata bar wajen, bata so Sam wani abun kuma ya taso, duk yanda ta lanƙwasa zuciyar ta, ba lallai Suhan ɗin tayi hakan ba, ta sani, bata so wannan al'amari ya shafi auren ƴar tata, amman sai gashi yau da kanta tana so ta tono Sirrin da ta jima tana ɓoye mata.

"Umma ya kamata ace ta sani tun tuni, ayau zata sani, kuma ni ne zan sanar da ita..."

Muryar ya Ameen ta karaɗe illahirin wajen, yayin da Umma taji ƙafar ta ta ƙafe ta kasa cigaba da takawa, da sauri Umman ta juyo, tana mai ƙafe Ya Ameen ɗin da idanu.

Nima da sauri na yunƙyra na tashi, mamaki fal a cikin raina, cikin hanzari ya ƙaraso inda nake tsaye, yana mai tallafa ta ya mayar dani ya zaunar dani, yana mai jinjina man kai, ganin irin kallon mamakin da nake binshi dashi

_"Mom ƙanwa ce a wajen mahaifin ki, kuma ɗiya ga ƙanen mahaifin naki Suhan"_

Ya faɗa cike da tabbaci, yayin da Umma tayi saurin saka hannun ta ta dafe dukkanin bakin ta, saboda bata taɓa zaton ya Ameen zai iya tona ɗanyen dakwayen da suka lulluɓe ba, na aika aikar kakan nashi, ga mahaifin Suhan ɗin..



~Oum-Deedat ce~
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~88~*


*_#Stay Home_*

*_#Stay Safe_*

*_#Wash your hands_*

*_#Avoide over crowded place_*

*_#Stop spreding the dx_*



*************


"Son me ke faruwa ne nan?"

Muryar mom ce dake tafe cikin ɗan saurin ta, hannun ta riƙe da waya tana latsawa, da alama kira ta gama amsawa ta hango su tana daga sama.

"Ehem Daughter me ya faru ne?!" ta sake maimaitawa, tana mai bin jikin Suhan ɗin da take tsaye bayan ya Ameen da kallo.

Hannun ta cikin nashi runtse, yayin da Maree ɗin ke zuƙunne tana sakin kukan Munafunci.


Kafin ma tayi yunƙurin bata amsa, tsulum Maree ɗin tayi tana mai miƙewa, cikin kuka take cewa "wallahi Hajiya ban kula da ita ba, wallahi Hajiya ban ganta ba, buge ta nayi ban gani ba.."

"Ya isa Maree" Mom ta dakatar da ita, fuskar ta ɗauke da mamaki, ganin Al'ameen tsaye, Amman miskilanci ya hana shi tankawa, ga wani irin kallon Maree da yake mai cike da tsana.


"Wai me ke faruwa ne, Son kayi man bayani mana" Mom ɗin ta cigaba da faɗi, tana mai dakatar da Maree da hannu, wadda ta sake yunƙurin buɗe baki.


"Mom duk abunda ya faru akan ido na ne, da gangan ta ture man ita, and kuma har ta isa tsayawa tana gaya ma Suhan magana, kinji wasu dirty talks da take faɗa ma mata ta. Kaman wannan yarinyar? Har tana cewa nan ba gidan ubanta bane..."


"What?" Mom ɗin ta faɗa da ɗan ƙarfi, tana mai zaro idanu, sai kuma ta koma da kallon ta kan Suhan ɗin, sauke kai nayi ƙasa, to me zance ni? Ita kanta mom ɗin ta sha faɗa man hakan ai a gaban su, May be ma anan taji.


"Je ki kira man Talatu" cewar mom ɗin, tana haɗawa da tsawa sosai.


Ai da gudun ta ta ruga sahen nasu, har yanzu kukan take yi, bata taɓa ɗauka ƙwabar ta zatayi ruwa haka ba.


"Sannu Daughter, baki dai faɗi ba ko? Baki ji ciwo ba ko?" cewar mom ɗin da turanci, tana ɗan dudduba jikin Suhan, wadda Ya Ameen Ya maida ta zuwa jikin shi, duk kunya ma ta cika ta. Saidai ga alama Mom ɗin ma ko damuwa batayi ba.



Kukan da taji ɗiyar tata tana yi ne ya sanya ta yo waje da sauri, zani a hannu, duk a zaton ta, cikin ƴan aiki ne wasu suka ɓata ma Maree ɗin.


"Ke dalla yi man shiru, muje inji wane shegen ne ya taɓa ki a cikin gidan nan? Har zaki wani tsaya yin kuka, bayan kinsan ko ke wacece anan gidan" ta faɗa da ƙarfi, da Mama Saude take, dama jiya sun samu saɓani, akan abincin da Mama Sauden ta zuba masu, wai bai ishe su ba, ita kuma tace bata ƙarawa, dama haushin Talatun take ji, irin yanda take zuba masu mulki da isa, kaman itama ba matsayin ƴar aiki bace.


But Mama Saude tayi itama, tana fitowa daga ɗaki, take sakin guɗa ƙarama. "Ahayye nanaye, Allah mun tuba, yo ai sai ki faɗa mana matsayin ta, wanda ya wuce ƴar aiki kaman mu? Kafin ma tazo ga aikin wace irin rayuwa ce batayi ba? Munafukai ku duka, uwa da ɗiya ba zuciyar arziƙi, kun ɓoye mana ku su wanene ada, to dai a sani, mun san shafe shafe mun san kala, ah to ehe! kuna fakewa da hajiya kuna aikata duk abunda kuka ga dama, mugun abunku zai koma kanku da yardar Allah!.. "


" Kinga Saude ki fita a ido na, naga take taken ki fa, wallahi summa tallahi zanyi sanadin barin ki gidan nan, kinsan na isa, zan kuma iya.. "" Yo kin isa mana, kaina farau? Kafin ni ma'aikata nawa kika saka aka kora da munafuncin ki da tuggun ki? Sai dai ni na riga ki nace Allah, nan gani nan bari wallahi, duk abubuwan da kika saka muka aikata da wallahi nayi nadama, na gane kafurar zuciyar ki, kinso ki ingiza ni, Amman dayake na riga ki nace Allah, sai Allah ya fidda ni, ko akan Hajiya Maryama ya kamata ace kin ɗauki ishara, kin ɗauki darasi, gashi yanzu ta haye ta barki, a matsayin da ke kike hange, dayake ita mace ce mai gaskiya da haƙuri, ba ruwan ta da Munafunci irin na ki, ta aure Alhaji, ɗiyar ta ta aure alhaji Ƙarami, wand akuke ta mafarkar aura, saboda ku samu abun duniya, sai gashi wai saboda daƙiƙancin ku, gani kuke har wannan sandar ɗiyar taki zata iya sace zuciyar Alhaji Ƙarami, har ma ta aure shi, ku mallake gida, duk abunda kuke yi suna tafin hannu na, kuma lokacin da zaku shuke abunda kuka... Ehoo an dai ji kunya, ɗiyar cikin ki, ki zauna tana mulka, ki, kuma wai har kice so kike muyi maki biyayya, ki mulka mu kaman ƴaƴan cikin ki"


Kuka Maree ta sake fasawa, jin muryar Mom tana ƙwalwa ma Talatun kira da ƙarfi, kaman tana dosa dashen nasu


"Wayyo Allah na! Mama Hajiya Babba ce ke kiran ki fa, ni kin wani tsaya kuna faɗa kaman kaji" " Ke dan Ubanki ba zaki bari na ƙwatar maki ƴancin ki ba wajen wannan munafukar matar ba?" mama talatun ta sake daka ma Maree ɗin tsawa.


"To ai wallahi sai ki tsaya kiyi ta yi ni zanje ince mata baki zuwa, baki san masifar da ta tunkaro mu ba ne, kizo muje kawai" ta faɗa cikin gatsali, tana jan hannun Mama talatun kaman ba mahaifiyar ta ba.


"Ko inzo da kaina ne?" muryar Mom ta sake amsa amo cikin ɓacin rai.


Da sauri Mama talatin tabi bayan ta, tana faɗin "Na shiga uku, yau kuma me kika jawo mana ni Talatu? Mariya baki jin magana dan ubanki, nace kar ki aikata komai, Amman saida kika je kika aikata, aiko dan Ubanki saidai ki bar gidan nan, ina zaman zama na, ina cin Arziƙi da daula ta, kika zo kika fara dagula man lissafi"


"Ko ma me zakice saidai kice, wallahi indai na bar gidan nan kema sai kin barshi, ai ke kike bani goyon baya duk abunda nake, ba kece kike zuwa.."


Wata irin wafta ta kai ma bakin, aiko taci sa'a ta samu bakin sosai, tuni ya dare, dama gashi ba cikakkar tsafta, jini yayi tsartuwa. Wani kukan ta sake saki, tana cewa" Kan bala'i.. Ni kika fasa ma baki? Ai wallahi duk Abunda kike yau sai na faɗa, kwarankwatsi dubu kuwa" daidai lokacin da suka idasa inda su Suhan ɗin suke tsaye.


Da wani irin mugun kallo Mom ta bisu, ba tun yanzu ba, duk in Mom tayi ma mai aiki irin wannan kallon, sunsan da matsala, cikin Mama Talatu ne ya hautsina, daidai lokacin da taji muryar mom cikin ɓacin rai tana ce mata


"Ke kika ba wannan yarinyar damar haɗa kafaɗa da zuri'a ta? Nace ke kika ce masu matsayin su ɗaya da ita anan gidan?"


Mom ɗin ta faɗa, tana nuna Suhan da hannun ta kai ɗauke da waya.


"Wah ni Hajiya? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wallahi tallahi bansan me ta aikata ba, ina ja mata kunne hajiya wallahi sosai, dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, ɗan yau ne ka haife shi baka haifi halin shi ba.." dakata Talatu, kina ja mata kunne akan me? Kinsan tana da shirin aikatawa kenan?" cewar Mom cikin wani ɓacin rai ɗin.


"Wallahi tallahi Hajiya.." sai kuma ta saka kuka sosai, tana mai rufe Maree ɗin da duka, tana yi tana kuka sosai.


Gyara tsayawa Ya Ameen yayi, yana mai soke hannayen shi duka cikin aljihun shi, yana mai watching wata drammer mai ban dariya. Saidai fuskar shi sam a turɓune take, babu ko alamun murmushi akai.


"Ya isa, dakata dena dukan ta, ai ta aikata abunda take ganin daidai ne, kuma sanin kanki ne, daidai yake da taka doka ta anan gidan, ban haɗa yara na da kowa ba, *Suhan ƴa ta ce* kuma ba zan taɓa lamuntar duk wani abu da zai faru da ita ba, masalan ta ɓangaren ku, idan da kuna ganin ta kaman matsayin ku, dama tun cen ba ɗaya kuke ba, ke kanki kin sani, kinje kin ga asalin ta, nima kuskure na aikata, kuma na amshi kuskure na, kuma ina kan gyarawa, ba zan lamunci wani yazo ya ɓata mun lamari ba. Nan gida na ne, kuna zaune ne a ƙarƙashin na, kuna aikata abubuwa da ya kamata ace na kula tun tuni, duk wani mugun hali da mariya ta ɗauka, a wajen ki ta gada, dan haka ba zan iya ci gaba da zama daku ba a cikin gidan nan, kuyi hanzarin tattarawa ku fice man daga gida, tun kafin dare yayi maku"


Mom ɗin ta faɗa cikin kakkausar murya, ba abunda ya Ameen yace, da idanu kawai yake binsu, Suhan ɗin ma haka, wadda yanzu Mom ta saka hannu tana mai janta zuwa nata jikin, Idi, da Mudi da Iro, duk suna daga nesa kaɗan suna kallo, masalan Iro wanda ya tattakura ya ɗora hannu bibbiyu a saman kai. Ji yake kaman ya idasa wajen ya ɓaɓɓalla ma Hajiya Mari, ganin yanda take ma Surukar shi, da kuma masoyiyar tashi.


Da sauri Umma ta ƙaraso wajen, jikin ta sanye da Hijab mai tsawo, bayan ta kuma haɗiman ta ne, wanda suka sanar da ita abunda yake faruwa na cewa Hajiya Babba ce, da su Suhan a wajen, dalilin fitowar tata ma kenan, take faɗin "Lafiya dai ko? Hajiya me yake faruwa, tun ɗazu nake jiyo hayaniya haka?" ta maida akalar tambayar tata ga zuwa Mom.


Cikin ɓacin rai ta sanya hannu ta nuna Maree, wadda har yanzu uwar ke dukan ta, tana yi tana fyace majina.


"Mariya mana, wai ta ture Suhan, har ita wacece da zata haɗa kafaɗa da yara na? Bata kula ba ita kaɗai bace, Allah ya taƙaita abun ma, da ai ba haka ba" mom ɗin ta bata amsa cikin kulawa sosai, har yanzu fuskar ta da ɓacin rai.


Ɗan murmushi Umma ta sake, sai kuma tace, "To ai Alhmdllh tunda ba abunda ya faru, ke Talatu bari dukan nata haka, ai tunda Allah ya tsare, sai a kiyaye gaba kuma" ta faɗa, tana mai juyawa zata bar wajen.


Da gudu Mama Talatu ta sha gaban ta, tana mai zubewa ƙasa, Dan Allah Hajiya kiyi man rai, ki ba Hajiya Babba haƙuri, wallahi ba da saka hannu na ba ta aikata, yanzu da akace in bar gidan, ina zani? Wa ke gareni? Ina zan dosa da wannan budurwar ɗiyar haka?"


Cikin mamaki Umma ta saka hannu, tana mai ɗago ta sama sosai take kallon ta." Wa yace ki bar gidan ne?" Ummn ta tambaya, tun ma kafin ta idasa, ta tari numfashin ta," Hajiya ce wallahi Maman Suhana, ban san mariya zata aikata wannan ɗanyen aikin ba... "


Juyawa umman tayi sosai gaban Mom. Tana mai cewa "Ayya hajiya, Haba, wannan ai bai isa yasa ace su bar gidan ba, a gode ma Allah da ba abunda ya faru ma, sai a kiyaye gaba, kiyi masu haƙuri dan Allah komai ya wuce, itama Suhan ɗin sai ta kula nan gaba"


Kallon ta Mom tayi, tana mai girgiza kai, "Ke zan ba haƙuri Gimbiya, lallai fa dole zasu bar gidan nan, na gaji, dama ya kamata ace tuni na sallame su ɗin, sun aikata abubuwa da hankali ba zai ɗauka ba, haɗa ita kanta talatun, to zaman me zan sake yi dasu kuma a gidan? Nan gaba ai sai su nemi rayuwar ɗiyar tawa" cewar Mom.


Itama Umman girgiza kai ta shiga yi " Subhanallah! Hakan ma ba zata faru ba, in sha Allahu, ki dai yi masu haƙuri, ai ya riga ya wuce, kuma duk abinda mutum ya aikata, kanshi yake ƙarewa" itama Umman ta faɗa.


*"Ai saidai kuma wani, dama tuni ta aikata, wannan ma Ƙarami ne"* muryar ya Ameen ta karaɗe wajen cikin kakkausar sauti, karo na farko kenan tun zuwan Umma wajen.


Da sauri kowa ya kalle shi, mamaki cike fal a fuskar kowa. Wani irin ihun kukan Mama Talatun ta sake saki tana mai dafe kai, "Na shiga uku na lalace ni Talatu, mariya tur da haihuwar ki, wallahi haihuwar ki bata amfana man komai ba, haihuwar ki batayi man rana ba, da haihuwar ki gara ɓarin ki wallahi, Allah dai ya tsine...." "Ke Talatu, akul ɗinki da tsine ma ɗiyar ki, ko me ta aikata ki mata addu'a shine mafita" Umma ta sake tarar zancen daga bakin Mama Talatun. Dama tasan za'a rina, tasan za'a aikata, wannan ranar tana zuwa, irin tuggun da Talatu ta haɗa mata, ai Allah ma ba zai barta haka ba.


"Son me ta aikata kuma wanda baka faɗa

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment