Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko shi ɗin wanene.


Har abinci an samu yaci, ni ce na bashi, inda yake kauda kai, sai na saka loma ɗaya a baki na sannan shima ya amsa, da haka ya man wayau na ci sosai, shima ya ci sosai ɗin, bayan ganin jikin ya samu sauƙi ne, aka bamu sallama, da zummar cewa zai dinga zuwa ana duba ɗinkin yankan da akayi mashi a damtsen hannu, gefen cikin shi, da bayan shi, sai wajen cinyar shi da kusan ƙirjin shi.

Har lokacin ban dena kuka sama sama ba, gani nake nice sila kawai, anya ba zan fita a rayuwar Ya Ameen ba? Ko da zata daidaita.



Haka muka dawo gida, Amman tsoron sashen namu ya kama ni sosai, saida akayi ta man faɗa, hada Hajiya Zainab, wai wanene zai jinyar mijin nawa? Haka na koma, Amman da Afnan muke yini, dayake baya da ƙan jiki, sai gashi cikin kwana biyu ya soma warwarewa sosai, har fita yake ƙofar gida, shi da Bilal, da kullum yana hanyar zuwa gidan namu.

Alhaji Mustapha da kanshi yayi handling case ɗin mutumen, wanda dai Maree ta turo ne, da taimakon Hajiya Laila, ba'a yi wata wata ba aka tura ƙyeyar shi zuwa gidan maza, ita kanta Hajiya laila ɗin da Alhaji yaro sun ja ma kansu, azaba da uƙuba kawai ake gana masu, ashe har suna gidan gyaran hali ma, halin nasu bai cenzu ba. Maree ma haka, ihu take sosai tana faɗin Ya Ameen, ba wanda ya kula ta, gani ake kaman ta zare, ita kanta saida aka maka ta gidan yarin, Mama Talatu ce aka saki, tare da cinta tarar kuɗi masu yawan gaske, ko kuma ɗauri na talala a wani mugun ƙauyen da ba wuta ba ruwa ba hanya, ga mugun talauci, idan ka ganta sai ta baka tausayi. Gashi tana ji tana gani aka iza ƙyeyar ɗiyar tata, wanda a yanzu mugun haushin ta take ji, gani take hada silar ta komai nata ya taɓarɓare da wuri, ba tare da sun cimma manufarsu ba. (Duk shekarun da suka ɗauka suna aikata mugun abu)




**************



Shiri suke gadan gadan, masalan da hidima ta matso sosai, shi Sir Salim ma so yayi a baje gidan a cenza tsari, Abban shi ne ya hana, inda ita dai Ammi saidai ta dinga mashi dariya, wannan aure yanda yake ɗokin shi, gani take kaman bai taɓa aure ba, koda yake a wannan ne yake saka ran dacewa.

Duk da haka dai, saida aka sake fentin gidan sosai, dayake babban falo ne sai kuma wasu falukan ciki, gami da manyan ɗakuna guda biyu, sai kitchen a ciki da toilet. Dan haka sashen amarya fa an gyara shi gani da zuba flowers wall sosai. Jeren kayan amarya kawai yake jira.

Lefe na ji da gani suka haɗa tare da taimakon Ammi da Asiya, lallai suna ɗokin auren nan, gashi duka yanzu bai fi sati huɗu ba a fara hidima gadan gadan.

Ammi ce ta tura mai gyaran jiki, wadda tayi ma Suhan, a cewar ta, ai Afnan ɗin ba Surukar ta bace, ɗiyar ta ce.

Ba ji ba gani aka fara Gyaran Afnan, tini ta ɗau sheƙi, abunka ga amarya, dayake nima nan ina ɗan bata wasu tips, masalan da hankali na ya ɗan kwanta, ganin Ya Ameen Ya warware sosai.

Hidimar biki ake sosai, siyayya ba kama hannun yaro, tun ana saura sati biyu su Umma suka je sukayi jeren su ɗan uban su, masalan da take ƴar gatan Yayanta, komai take so sai ya siya mata.

Akai akai Nihal da saudat na zuwa, saidai harara ce kawai tsakani na da Saudat, Abunda ma ya bani mamaki, wani uban haske da naga tayi, watau bayan hasken ta, har shafe shafe ma ta fara ko? Mom kuma ta kasa ce mata komai har yanzu ɗabi'ar son yaran nata da rashin tsawata masu na cikin ranta, koda yake haka dama rayuwar wasu masu kuɗin ta gada.

Nihal da yaron cikin ta, ni kuma nawa yayi wani uban tsini sosai, da ƙyar nake cira ƙafa, duk inda nayi sai an jini da kallo. Kowa mamakin cikin yake yi. Shi kanshi Ya Ameen kullum tausaya man yake yi.

Yanzu banda matsala da kowa masha Allah, Mom ta zaman man back bone a cikin gidan, ko wani abu nake so, kafin ma in ma Ya Ameen magana, ita tayi mashi, kuma bana samun wata matsala, saidai ina da burin da Afnan tayi aure, zance mashi ya taimaka mu cenza gida, ina ɗan jin Kunyar Mom har yanzu.


Nima ba'a barni a baya ba. Duk Abunda nasan Afnan zata nema na siya mata, Sir Salim ni yake kira yaji ko Afnan ɗin tana da wata buƙata, shi bata faɗa mashi, aiko zagewa nake in faɗa mashi, masalan ma yanzu da muka kasance ƴan uwa.

Aunt Feena ta iso, dama Abie tun ciwon Ya Ameen Ya diro, haɗa tarkato ƴan kayan shi, yana mai cewa ya dawo kenan wai shima aure yake so. Dariya muka dinga yi mashi, lallai ma Abie, duka nawa yake balle yace aure yake so, ko ya Ameen da yaji zancen nashi, saida yayi dariya wa shirmen Abie ɗin, yana mai faɗin "Yaro ka gama shirmen naka, ana gama biki zaka tattara ka koma."


Nima an gyarani, duk da kunsan mai ciki sai a hankali, ciki na ya shiga wata na takwas fa, komai na saka saidai kawai dan sitira baya man kyau sosai, saidai doguwar riga, Shiyasa ko kayan biki da na ɗinka duk dogayen riguna ne.


An fara hidima sosai, hatta da su Mama Fulani nan suka taho gidan mu, ga ƴan kankiya, hidima fa tana kyau sosai, Mom duk ta cenza, kaman ba ita ba duk da hidimar bikin ta bar ma Umma da Hajiya Zainab, saidai kallo ita, Amman duk da haka ba wata matsala dake faruwa. Ƙawaye na ma duk sun ma kara, haka na Afnan ɗin itama. Ni ce Yayar Amarya, duk inda nake amarya na nan.

Ranar Jumu'a ɗinbin mutane suka shaida ɗaurin auren Afnan ɗin da Sir Salim a gidan Alhaji Auwalu. Nan fa aka sake ɓarkewa da hidima. Amarya sai gobe ne za'a kaita. Dan haka aka sha shagali hankali kwance, hada su Kamu akayi da arecen a nan cikin gidan namu. Butsu Butsu Kaga Ya ameen Ya leƙo kira na. Har Kaka zauwaira na mashi tsiyar wai baya tausayi na, da na zauna zai zo sake kiran a, idan wani abu ne yaje yayi da kanshi mana. Dariya yake yi, yana mai cewa "Ke dai tsohuwa ladar auren da ke kika kasa samu ce, bakya so ta samu, taso muje kinji sweety na" ranƙwashi take kai mashi akai. Kowa na mamakin sauyawar Ya Ameen a yanzu, yaman sake da kowa ayi wasa da dariya, dukda yanayin nashi ne a haka, shi gani yake. yana iya ƙoƙarin shi.


Washegari aka shirin kai amarya, Ya Ameen Ya so hana ni, saida Mom tayi mashi jan ido, ita kanta Umma wai cewa tayi "Me zata je yi da wannan cikin? Salon ta haife mana shi acen?"

Mom ce tace ba komai, indai ta haihu lafiya ai Arziƙi ne, cen ma ai gida ne.

Haka muka tarkata, dayake Cikin motar Ya Ameen sabuwa, haka aka saka amarya, nima haka na shiga gidan gaba, da Umma da Hajiya Zainab da Goggo Aisha da Goggo Fatima na baya, dayake sabuwar mota ce ya siya mai girma sosai da kyau, saboda hidimar Family irin hakan.

Sauran motocin da dangin ango da suka kasance dangi na, haka aka ɗauki hanya, zarya fa tsakanin Abuja da Adamawa ai ta ga Family namu, yanzu duk an zama ɗaya, ita kuwa Mom gida ta zauna tarar sauran baƙin, da wanda basu samu zuwa kai amaryar ba.

Gidan Afnan yayi matuƙar kyau, zullumi na ɗaya Ma'u, bana so Afnan ta shiga wani hali, tana da zuciyar zinari, mace ce mai kawaici, son mutane ga kirki. Addu'oi sosai wanda na koya a wajen umma ta na bata, kafin ta shiga gidan ta karanta. Mun ga gata kuwa, sai nan nan ake yi damu, abunka ga dangin sarauta, nan da muka tadda gida cike da hamshaƙai da manyan mata ƙawayen Ammi da sauran ƴan uwa.


Umma fa Gimbiya tarba ta musamman akayi mata, duk ind ana wuce nuna ni ake yi, ga ɗiyar Gimbiya Hasken Masarauta, nan aka shiga magana caaa, caaa, wasu ma hada cewa ni ce nayi nasarar yin *Wuf* da zuciyar Yariman matasan arewar.


Duk da Mama Fulani taso na bita cen masarautar, ƙiyawa nayi, ina mai ce mata sai dai gobe, dayake ai Kaka ta ce, janta nake yi sosai da sosai.

Ango fa baki har kunne, ya ma manta da mun taɓa wata aba soyayya, dukda har yanzu yana girmama ni a cikin ran shi, ni yake faɗa ma wai na kula da Afnan ɗin, saidai inyi dariya, domin ji dai gani na kawai ake yi, hada ma wani Aunty yake ce man.

Washegari akayi walima sosai mai kyau, sannan ne fa aka fara jidar mutane ana mayar dasu, wasu gidajen su, wasu masarauta.

Ya rage daga mu, sai amarya, muma gyara mata gidan muke.Ya Ameen yana waje cikin mota, ya azalzale mu, wai mu fito mu wuce masarauta, cen zamu kwana sai gobe za'a ɗunguma kuma a juya gida.



Zaune take saman gado, muna gefe ni da Nihal da Saudat da take ta cika tana batsewa, faɗa nake ɗan yi mata, da bata wasu shawarwarin, aka bugo ƙofa da ƙarfi, kaman za'a ɓalla ƙofar, cikin sauri muka juya, domin ganin ko wanene?


*Ma'u ce tsaye ita da wasu zaratan mata sun ci ɗammara, sai faman jijjiga jiki suke yi, hannun su ɗauke da manyan itace, ko wa zasuyi ma rotse kuma?* da ganin fuskar su dai basu gaji mutumci ba.

Gabana ne yayi muguwar faɗuwa, toh fa, abun da nake gudu yana shirin faruwa, gashi angon ma baya kusa, ga Afnan ita kaɗai zamu bari, tinda wancen uban azarɓaɓin ya dame ji, sai doko man waya yake yi.


*Ina Munafukar take dan Ubanta?* cewar Ma' Un, wadda ke tsaye kaman tsohon kumurci, tana hurci kaman tana a filin daga ne, lokaci guda kuma tana mai kai kallon ta saman gadon inda Afnan take zaune fuskar ta lulluɓe da Mayafi na haɗaɗɗiyar lafaya, irin ta masarauta.




*"Sai na ga uban da ya ɗaure maki gindi kika auri miji na, wallahi yau ko ni ko ke a cikin gidan nan, maza ku gama masu aiki kuna ɓata mana lokaci"*

Ta sake faɗa cikin kaushin murya, tana mai nuna mu da muke tsaitsaye muna lallashin Afnan ɗin saboda kukan da take yi.





~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._




*Page ~91~*




*Ya Ubangiji bamu da tsumi bamu da dubara, bama da wayau bama da fasaha, kai kaɗai ne Allah, kai kaɗai muke bautamawa, kai ke jin ƙan bayin ka, dan tsarkakan sunayen ka guda tis'in da tara, dan tsarkakken mulkin ka, domin fiyayyen halitta, kuma habibin ka, masoyi ka, kuma annabn ka, (Muhammadu SAW) ka yaye mana wannan cuta ta COVID-19 ya Allah ka dube mu da idon Rahma, ka yafe mana dukkanin laifukan da kukayi maka, mun ƙasƙantar da kanmu zuwa gareka, muna masu tuba da istigfar, Ya Allah mu masu laifi ne a gareka mun sani, mu masu saɓa dokar ka ne, ka jarabce mu, kuma mun amshi jarrabawa da hannu bibbiyu, kayi mana afuwa, kayi mana gafara, ka yaye mana wannan annoba da ka jarabce mu da ita. AMMEN YA RABBAL ALAMEEN, YA ZULJALALU WAL IKRAM, YA HAYYU YA ƘAYYUM, BIRAHMATIKA ASTAGISU.*





*****************






Da sauri ya ƙara so wajen, ganin danƙareriyar motar Ya Ameen ɗin fake a gefen ƙofar gidan nashi.

Cikin salon girmamawa tare da mutuntawa ya duƙa saitin ƙofar motar Ya Ameen ɗin yana ce mashi "Yallaɓai barka da warhaka, ya gajiya?" ɓalle murfin motar yayi, yana mai fitowa ya miƙa ma Sir Salim ɗin hannu, cikin sakewa sosai, fuskar shi ɗauke da fara'a sosai ƙwarai.

"Ah barka da zuwa dai ango, kai za'a tambaya ya gajiya? Ya fama da jama'a kuma?" cewar Ya Ameen ɗin. Shima dariya ya shiga yi, ƙwarai ɗabi'u da halayen Al'ameen ke burge shi, wanda a yanzu ya zama Yaya za'a ce.

"To Alhmdllh gata nan ana fama da ita dai, wai ba dai shanya ka sukayi anan ba?" Salim ɗin ya faɗa, yana ɗan waige waige, ganin wajen wayam ba kowa sai tsirarun motoci, wanda sauran ƙawayen amarya ne ke zance, dayake unguwar ba mai hayaniya bace.

"Wallahi kuwa, Kaga tun ɗazu nake jira, ba dan madam na tare da su ba ma, wucewa ta zanyi, sun nemo mai maida su" Ya Ameen ɗin ya faɗa cikin ƙosawa, tare da jingina sosai jikin motar, da gani ya gaji sosai.

"Ai kasan lamarin shiriritar mata, ƙila ma yanzu suna cen suna firar su" ɗan zaro idanu Ya Ameen ɗin yayi, yana mai cewa "ah haba? Aiko zasu sake kwana anan" ɗan murmushi Salim ɗin yayi, cikin zaulaya yake cewa "Haba Babban Yaya? Ka san fa yau ne ranar, a tausay man mana, ai ni da kaina zan mayar dasu ma ko ka tafi" bushewa sukayi da dariya su biyun, suna masu tafawa sosai, hada ɗan haɗa jiki Ya Ameen ɗin yayi da Salim. Maza kenan, kaman nema bai taɓa haɗa su ba, gashi yanzu sun sake kamar ba su ba, Shi kanshi Ya Ameen Ya tabbatar ma kanshi da cewa Afnan ta dace miji, Salim yana da natsuwa, ga kamala a tattare dashi, masalan ma da ya kasance ɗan uwa ga Suhan ɗin a yanzu.

Kaman sun daɗe ƙwarai, kaman wasu abokai na haƙiƙa, nan fa suma suka sake, fira suke zubawa sosai da sosai, sai ga Sir Salim hada ɗora manyan ledojin da yayo siyayya dasu a saman mota.

Sun nutsa da fira ne, Ya Ameen yace "Bro please kada mu ɓata lokaci anan, idan ka shiga ka turo man su, but please ƴar ƙanwar nan tawa dai please" dariya suka kuma bushewa da ita, suna masu ƙara tafawa sosai, cikin ƙaunar juna, Salim ɗin ya fahimci me Al'ameen ke nufi, Musabaha sukayi, sannan ya kwashi ledojin shi da niyyar wucewa ciki, sai kuma ya juyo sosai ga Ya Ameen ɗin.

"Ah nace ba! dai ka shiga ka ga ɗakin amarya?" cewar Salim ɗin, ɗan jim Ya Ameen yayi, sai kuma ya girgiza kai, "Zan dawo ne ai kafin mu wuce Abuja ɗin."

Girgiza kai Salim yayi, yana mai kamo hannun Ya Ameen da gudan hannun shi "Ya kamata dai muje ka duba Yaya, kasan fa ƙanwar nan taka ba zata ji daɗi ba" ya faɗa yana mai jan hannun Ya Ameen ɗin. Ba dan ya so ba, ya san yanzu haka Afnan kuka take yi, baya son ganin hawayen ta, abu ne da ya zama dole, zai iya ji kaman ya saka ta a mota ya mayar da ita gida, duk da yasan ba zata rasa komai ba anan.




*********


Gadan gadan matan nan suka yo kanmu, yayin da wasu suka juya zuwa cikin falon Afnan ɗin.

Ƙarar sautin rotsa tv ita ce ta saka mu wata irin zabura, ba ƙaƙautawa muka ji ana ta fasa abubuwa kaman mahaukata, yayin da sauran suka iso gaban mu suna masu mugun huci, wuntsilawa Saudat tayi zuwa bayana, yayin da Nihal ta ɗare bisa gadon cikin tsoro, ita kuwa Afnan saukowa tayi sosai bisa gadon, tana mai sanya hannu ta shiga ja na baya, saboda ka da a samu matsala, ni kuwa ƙafafu na sun kasa ko da motsawa ne. Tsabar tsoro da firgita, Sam babu imani a saman fuskar su.

"Ke ce mai shegen shisshigin da kika yi giggiwar shigowa gidan ƴar uwar mu ko ɗan Ubanki?" cewar wata gansamemiya, da dukka ta kere su tsawo da kauri.


Duk da kuka daya ƙwace ma Afnan, masalan jiyo irin ɓarnar da suke mata, wanda muna iya jiyo su har sun faɗa kitchen ɗinta.

Buɗe baki tayi da ƙyar tana mai cewa" Ba ni ce na auri kaina ba, sannan ita wadda ta turo kun, meyasa bata zo nan da kanta ba? " Cewar Afnan ɗin, tana mai share hawayen fuskar ta, cikin son ƙarfafa ma kanta guiwa.

*" Keeeeh! Ya isa, ba sa'insa muka zo yi daku ba, sawun ku a likkafa ku fice daga nan gidan, tun kafin lahira tayi baƙi, balle ke wannan mai tulelen cikin Munafukar Allah, sai wani zazzaro mana idanu kike yi, tare da wannan taron matsoratan banzan" , ta faɗa tana kai nuna su Nihal dake kan gadon.

Ni kaina na sare, na ga bala'in ƙoƙarin Afnan ma, kenan zata iya ƙwatar ma kanta ƴanci?

Sake buɗe baki tayi Zatayi magana, na sanya hannu na toshe mata baki, ina mai girgiza mata kai.

"Kuzo mu tafi" abunda nace masu kenan, ina mai kaima Hijab ɗina raruma wadda ke ajiye saman gado, cike da kaɗuwa.

"Aunty ina zamu je a haka? Ina Ya Ameen ne? Ba yana waje ba?" Cewar Saudat

Ba ni ba, hatta da Afnan da Nihal saida suka juya suna mai kallon ta, Saudat ce haka yau? Ja'ira! ta ga gura'i, sai gashi da kiran Suhan Aunty.

Ganin irin kallon da suke mata ne, ya sanya ta kauda kai cikin wayancewa, cikin wata kaɗuwar tace" ni dai wallahi ba inda zani, Aunty kira mana Yaya kawai" ta faɗa, tana mai sake haurawa cen ƙarshen gadon

Ban ma yi wannan tunanin ba, cikin rawar hannu na lalubo waya ta a cikin jikka, ina mai latso number ɗin ya Ameen zan danna mashi kira, wani irin duka aka kai ma wayar dake hannun nawa, da ƙaton icce, sai gata ƙasa watsa watsa, da wuya ma idan zata tashi wannan wayar.

Cikin wata kaɗuwar muka bi wayar da kallo, kaman fa wanda ake niyyar kashewa, duk munyi tsamo tsamo, Afnan ce ma kawai mai ɗan ƙarfin hali a cikin mu.

Ihu sosai Saudat ta ƙwalla, karaf sai a kunnen su Ya Ameen da ke niyyar shigowa.

Da ya Ameen da Salim ba'a san wanda yafi wani gudu ba, jin sautin ihu da kuma fashe fashen abubuwa na tashi daga cikin gidan.

Turus suka ja suka yi cikin tsananin kaɗuwa, gami da bin ilahirin falon da kallo. dukka kamannin falon an cenza shi, ya zama kaman anyi yaƙi ko wani damben bala'i a ciki. Hatta da kujeru duk an birkice su, an farfasa kayan kallo, ga show glass mai masifar kyau, da zallan turaruka a ciki, duk an illata su, gabaki ɗaya falon fasassun kwalabe ne a ƙasa barbaje.


*"MA'UUUU"* Cewar Sir Salim ɗin, yana mai rugawa zuwa ɗakin da yake mallakin Afnan ɗin.

Ganin inda ya bi shima Ya Ameen Ya bishi cikin gudu gudu sauri sauri, Suhan kawai yake ji, wadda ke fama da turtsetsen ciki kaman zai ɓallo ƙasa, gashi da gani kuma babu lafiya a cikin gidan.

"Keee" Salim ɗin ya daka ma matar da take tsaye gaban namu, ɗauke da mugun icce, gigita ciyar tsawa, yayin da sauran da suke ta fama farfasa komai na ɗakin suma suka dakata, jin sautin amon muryar namiji.

"Wacece ke? Me kuka zo yi man a gida a daidai wannan lokacin? Wa ya saka ku?" duk Salim ɗin ya jefa mata waɗannan tambayoyin cikin tsawa sosai, jikin shi ma karkarwa ganin irin rashin hankalin da sukayi masu a wannan lokacin..

"Nice nan Baban Esher" Cewar Ma'u ɗin, wadda take shigowa, kallabin ta ɗaure a ƙugu, bayan ta waɗannan sauran zaratan matan ne rirriƙe da itace, kowacce ta ci ɗamara, sai haki suke yi, saboda aikin ɓarnar da sukayi.

Da sauri duk muka juya muna masu kallon su cikin zaro idanu. Lallai ma, Ma'u ce, na shaida Fuskar ta, ai ba zan taɓa mantawa da ita ba.

Kallon ta ta maido saman fuskar mu, "Munafukai masu mugun son abin duniya, ta Allah ba taku ba, nan gida na ne, babu shegiyar da ta isa na haɗa miji da ita.." "Ya Isheki Ma'u, me kika zo yi man a cikin gida, wannan haukan da kuke duk na menene?" Cewar Salim ɗin.

Shi dai Ya Ameen sai kallon ikon Allah yake, nan ne inda zai bar ƙanwar tashi? Da irin wannan kishiyar? Lallai akwai damuwa.

Zuƙunnawa yayi ƙasa, yana mai ɗauko waya ta da idanun shi suka sauka a kanta, ta yi watsa watsa kuwa, ya ci screen

"Ba zanyi ba Salim, wallahi ba zanyi ba, wannan ma Ƙarami ne, Indai wannan ne hauka, yanzu ma na fara, sai ka sake ta, wato an hana ka waccen mujiyar, shine yanzu aka laƙa maka wata nunar ranar ko? Ana baƙin cikin zama na ni kaɗai ko? Ni za'a munafunta? Da kai da tsohuwar mahaifiyar ka...." tsalle guda kawai yayi, sai gashi gaban ta, yana mai sakar mata ɓarin makauniya a duka kumatun nata.

Ihu ta sake ƙwallarawa, yayin da tayi wani kukan kura tana mai cewa" Ni zaka mara akan wannan banzar? Wallahi akan matar ka zan rama, wallahi sai na nakasa ta yau a cikin gidan nan, sai na nuna maku kalar tawa haukar" tana mai yo kan Afnan da sauri.

Baya na na tura ta, ina mai tarar Ma'un cikin dakiƴar zuciya, ba zan iya bari tayi mata wani abu ba, wani mugun naushi ta kai mana mu duka ni da Afnan ɗin, yayin da Nihal ta wuntsilo daga saman Gadon, tana mai tare mu da muke shirin zubewa ƙasa, shi ma Ya Ameen da sauri ya isa garemun, taro mu yayi mu duka, muka zube a jikin shi, ina mai sakin sauti "Wash"

Da ƙarfi Salim ɗin ya sake fuzgo Ma'un, yana mai sake ɗauke ta da wani gigitaccen mari. Zubewa tayi ƙasa tana mai sakin gunjin kuka, Amman duk da haka bata sare ba, ta sake yunƙurawa tana mai yo kanmu, wanda nake tallafe jikin Ya Ameen ɗin, ita kuma Afnan ɗin tana bayan shi a lafe.

Fizgo ta ya kuma yi, ta ja turjiya da wata irin zamiya. Bai ƙasa a guiwa ba, ya ɗauke ta cakkk, yana mai nufar hanyar falo da ita, sai zillewa take, tare da faɗar baƙaƙen maganganu.

Kuka sosai Afnan ke yi, bata san haka ba, Salim bai ɓoye mata komai ba, daga labarin Ma'u ɗin, amman bata ɗauka abun ya kai haka ba, tana sonshi, amman da wuya in zata iya jure ma zama a haka, watarana ai sai ta nemi kashe ta, daga ita sai ita cikin gidan.

Bisa wata kujera da tayi saura basu tuntsirar ba ya wurgi da ita, har saida ta buge kai, sannan ya bita yana mai danne ta, tare da sakar mata nauyin shi sosai. Ihu take yi sosai da sosai, yayin da sauran matan ganin maza, sai jikin su ya fara yin sanyi, duk suka nemi ficewa.

"Kada wadda ta motsa" Ya Ameen Ya faɗa cikin kaushin murya, idanun shi sunyi jawur.

Cak suka ja suka tsaya, jikin su na karkarwa, tun da suka haɗa ido dashi suka fara ɓari, basu ga alamun shi ɗin ƙaramin mutum bane, tun daga shadda, zuwa wayar dake hannun shi, kalar fatar jikin shi, tare da diri na cikakken namiji da Allah ya bashi.


Afnan ya sanya hannu yana mai jawo ta gare shi, rungume ta yau sosai, yana mai share hawayen fuskar ta, "Am Sorry Lil, ɗauko Hijab ɗinki mu tafi" ya faɗa cikin sigar lallashi, cike da tsantsar takaici a cikin muryar shi.

Gyalen ta da ya faɗi ƙasa ta zuƙunna ta jawo, tana mai yafawa. Hannun ta ya kama da niyyar juyawa da ita su fice, ba zai iya barin ta ba, ba zai iya barin ƙanwar tashi da yafi ƙauna a kashe ta ba.

Gaban shi na sha da sauri, fuska ta tam, babu alamun wasa, girgiza mashi kai na shiga yi. Ba'a haka, idan da wani gurmi ma sanyawa a bar gida, da tuni

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment