Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dangi na, zuri'a ta alhali na, irin wannan family mai ɗinbin daraja. Nikau da me zan saka ma Ya Ameen dashi wanda ya wuce soyayyar da nake mashi a yanzu.

Ba wanda yayi yunƙurin hana ni, kaman yanda suke iya hangen irin raɗaɗin da zuciya ta keyi mani, da irin halin da nake ciki saman fuskar tawa.....

Shi kau Ya Ameen runtse idanun nashi yayi, yana mai sauraren kukan nawa dake ta ratsa mashi zuciya,sai yanzu Kunyar Abunda Mom ɗinshi keyi ya shiga bashi matuƙar kunya, a hankali ya shiga jinjina kanshi yana mai hamdala da jin wannan kalaman daga bakin mai martaba, lallai Allah gafurun raheem ne, mai samrr da akwai daga babu, mai samar da babu daga akwai, ya fidda matacce daga rayayye, ya fiddabrayayye daga matacce, mai amshe kuɗi dukiya mulki ya ba wanda baya dashi, mai ba wanda baya da komai mulki da dukiya, mai maida sarki bawa, ya kuma mayar da bawa sarki, wanda bashi da abokin tarayya sai shi kaɗai, azzawajalla.....



*Kuyi manage, walh bana da chaji*



~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'ar Saduwa Da Iyali:
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~60~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Kuka na nake saki bil haƙƙi da gaskiya.

Mai martaba da kanshi ya taso zuwa gareni, haɗi da sanya hannuwan shi ya ɗago ni yana mai rungume ni cikin jikin shi, tabbas ko ba'a faɗa ba, irin kukan da nake yi, yasan rayuwa tayi walagigi dani, ko ba komai ya sha alwashn duk wanda yake da sanya hannu a wannan manaƙarƙashiyar ba zai taɓa ƙyale shi ya tafi hakanan ba.

Rarrashi na ya shiga yi, har yanzu ya Ameen na durƙushe saman ƙafafun shi, dana buɗe idanu shi nake hange yayi kasaƙe yana kallo na, wuyan shi a karye, dukkanin natsuwar shi ya ɗora ta a kaina.

Mahaifiyar shi, ita kaɗai yake hangowa, irin Kunyar da zata kwasa, muddin taji wannan al'amari, saidai koma minene shi yayi imanin farin cikin da yayi ya zarce kaso ɗari cikin ɗari.

A hankali na tsagaita da kukan nawa, har bisa kujera mai martaba ya kai ni yana mai zaunar dani. Da hannu yayi ma Al'ameen alamu da shima ya koma bisa kujerar ya zauna.

Nayi mamakin ganin ya doso inda nake zaune ɗin.

Daf dani ya zauna, yana mai riƙo hannu na wanda yake kusa dashi, cikin nashi, yana mai ɗora su bisa kujerar ta yanda mai martaba da yake gefen mu zaune ba zai iya gani ba.

A hankali ya shiga murza yatsun nawa, alamun lallashi. Ni kau sai faman jan majina nakeyi.

Farin ciki da wani irin yanayi sun haɗu sun tattare mani wuri guda.

Sake bani haƙuri mai martaba yayi, sannan ya miƙe yana mai faɗin "Ku sake tattaunawa, domin dai ita mai babban ɗaki ba zata koma cen ba kuma, har sai an ɗaura auren.

Da kallo muka bishi, muna mai faɗin" a fito lafiya"

Yana ganin shigewar shi yayi saurin juyowa gareni, yana mai zamowa daga bisa kujerar da yake zaune bisa ƙafafun shi ya durƙuso sosai.

Dukkanin hannuwan shi yayi amfani dasu wajen taffo fuskar tawa.

"Kukan na menene uhumm? Ke da zakiyi farin ciki?"

Ya faɗa a tausashe, cikin alamun lallashi da tausaya wa.

Wasu hawayen ne suka sake malalo mani "Yaya menene dalilin Umma nayin haka? Ashe muna da asali Umma take ta faman ɓoye mani tuni?"

Da wani irin yanayi yake kallo na.

"Suhaaann" Ya ambaci sunan nawa bisa laɓɓan shi, kaman bai taɓa furta sunan ba a yanda Naji haruffan sun zauna a bakin nashi, kuma yana furta su yadda ya dace.

"muyi ma Umma uziri, haƙiƙa dole akwai wani abu dake faruwa, koma muce ya faru ɗin, zamu so jin ta bakin ta, kaman yanda Mai martaba ya faɗa, saidai ba a wannan lokacin ba, sanin kanki ne, idan akace yanzu ne za'ayi maganar, to fa wani abu na iya ɓullowa da ka iya kawo cikas a auren namu, muyi haƙurin bayan ɗaurin aure, ke kuma na yarda na amince ki cigaba da zama anan, saidai ina so kafin in wuce gobe mu tattauna abubuwan da kike da buƙata, da kuma yanda hidimar bikin zata kasance, kuma zuwa gobe ina so kafin in wuce ki raka ni sansanin ƴan gudun hijira, domin in bayyana ki garesu, a matsayin wadda zan aura, kaman yanda suka zame mani dangi"

Da jajayen idanu na nake kallon shi.

Wane irin mutum ne ya Ameen ɗin? Haƙiƙa ko tantama babu nasan nayi dacen samun abokin rayuwa, ina mai gode ma Allah akan wannan baiwa da yayi mani, ni Suhan ashe da gata na? Ashe zan mori rayuwa da jin daɗin rayuwa anan gaba?

Hannuwa na na sanya ina mai sauke hannuwan nashi daga tallaffo fuskar tawa, mai makon in saki hannun, sai na sake runtse su cikin nawa.

"Yanda kace haka za'ayi Yaya, ina mai alfahari da samun ka da nayi a matsayin miji na, kuma uban ƴaƴa na, ina mai godiya ga Allah da ya nuna mani wannan ranar, haƙiƙa rayuwar da nayi a cen baya ta zame mani darasi, na koyi abubuwa da yawa daga ciki, na gode da jajircewa da kayi a kaina, ba dare ba rana, ka soni duk kuwa da cewa kasan ko ni ɗin wacece sannan.... "

" Shiiiiit" ya faɗa yana mai zare hannun shi guda ɗaya ya ɗora shi saman bakin shi, alamun inyi shiru.

"Suhan kece rayuwa ta, na daɗe ina dakon sonki ba tare da na sani ba, ki taimaka ki tallafi rayuwar bawan Allah Al'ameen"

Murmushi nayi, yanda ya furta kalaman yana wani karyar da wuya, sai ya bani dariya.

Ganin na murmusa ne ya sanya shi sakin wata wawuyar ajiyar zuciya.

Miƙewa yayi tsaye, yana mai kamo hannuwa na nima na miƙe,, da yatsa yake ɗauke mani sauran hawayen da suka idasa gangarowa, wanda ya zuwa yanzu na tabbata na farin ciki ne.

"Muje ko? Ki samu ki kwanta ki huta, da wuri nake son wucewa, akwai abubuwan da nake son aiwatarwa acen goben, sai ki shirya da wuri, sannan zan rubuto maki programme ɗin da za'ayi, sai ki duba ki gani idan yayi, kinji sweet heart"

A hankali muka shiga taka wa, har ƴar ƙofar da zata sada ni da cikin gidan, inda ya ja ya tsaya yana mai kallo na cike da ƙauna, sadda kaina ƙasa nayi, har yanzu duk da nasan ko ni wacece ɗin, sai nake ganin kaman Ya Ameen ɗin yafi ƙarfi na, shi mutum ne mai kwarjini da cika fuska, ko kyawo da gayun shi zasu sanya ka kasa samun natsuwa in yana wuri.

A hankali ya sake dukkan hannuwan nawa, yana mai furta "Good night dear, sleep tight janam"

A hankali ya shiga steeping back, yana mai ƙallo na cikin shauƙin ƙauna, ni kuma sai na kasa sauke hannuwan nawa ƙasa, ji nake kaman sun fara maraicn tafukan hannayen nashi masu taushi.

"Yaya programme ɗaya ya isa please, dinner kawai za'ayi please" na furta cen Ƙasan maƙoshin.

Cak yaja ya tsaya, sai kuma ya kafe ni da idanu.

"Hakan yayi maki?"

"eh" na faɗa ina mai ɗaga kai sama a hankali.


Hannuwan shi ya ware, sannan ya ɗan sara mani "Consider it done ran gimbiya ta ya daɗe"

Murmushi na sakar mashi mai ƙayatar wa, ina mai faɗin "tare da kai *Yariman Matasan Arewa* "

Ai sai naga ya saki murmushi yana mai sake kallo na cike da shauƙin farin ciki.

"Dama kina sane ko murna ma bakiyi mani ba?"

Ya faɗa shima yana mai sake takowa zuwa gareni.

Daf dani ya kuma ja ya tsaya, daidai lokacin da nima na wara kwayar idanu na cikin tashi na shiga cewa "ai ba kai ne ka sanar dani ba, Kaga baka buƙatar murna ta" sannan na kaɗa kwayar idanun tayi wani far haka.

"ah haha" ya saki wata irin dariya mai ƙayatarwa, har dukkanin kuma tun shi suka loɓa ciki. Da gani na so kashe shi da farin da nayi da ida nu na

A hankali ya cije lips ɗin shi da suke Light pink.

Kasaƙe nayi ina mai kallon shi yana ta sakin dariya.

Ya ƙayatar dani, komai Ya Ameen yayi kyau yake mashi, shi mutum ne mai salo ba tare ma da yasan yana yi ba.

"Lokacin ai kina Suhan ƙanwa ta"

"A'a Yaya, lokacin ina..."

Katse ni yayi cikin kamo hannuwa na still "Suhan please ki dena tuna rayuwar ki ta baya a gidan namu, sanin kanki ne cewa ina baki kariya da dukkan iyawa ta, tun a lokacin bana so ko hakki ya tsire ki, saboda yanda nake jin zafi a lokacin, saidai na kasa yarda ma kaina cewa soyayya ce, saboda nayi imanin soyayya ƙarya ce, ashe bansan kuskure ne nake tafkawa ba, ba yanda Bilal baiyi ba wajen fahimtar dani, saidai na Gaza gazgata shi, yau gani gaban ki ni Muhammad Al'ameen Almustapha Dambulan da ƙoƙunan bara ta, a taimaka a cika man su taf da soyayya, nayi alƙawarin sake inganta rayuwar taki iyakar iyawa ta"

Ɗan murmushi na saki, ina mai faɗin "Soyayya dai ka samu, saura mai soyayyar" nima na furta a hankali, cike da wani yanayi na soyayya, gani nake kaman ba Ya Ameen ba, ashe miskilai haka suke muddin suka faɗa tarkon so?

Hannun nawa ya kai zuwa bakin shi, yana mai sumbatar su a hankali, ya daɗe bai ɗago da fuskar shi ba daga sumbatar, sai kuma ya saki a hankali yana mai faɗin "I am going to miss you dear, take care" yana gama faɗin haka ya juya cike da murmushi cikin salon tafiyar shi, har zuwa ƙofar da zata sada shi da ɓangaren da aka sauke shi ɗin.

Da kallo na raka bayan nashi, har zuwa bakin ƙofa da ya tsaya ya buɗe kofar yana mai waiwayowa ya bani wani irin peck sannan ya shige yana mai ɗaga mani hannu.

Da kallo na shiga bin hannun nawa da ya sumbata, wanda na Gaza sauke su ƙasa, sai kuma na saki dariya, ina mai ɗan girgiza kaina a hankali na duƙa na shige cikin gidan.

Ina fita naga wasu bayi sun kai su biyar, da sauri suka ƙaraso gareni, suna mai faɗin "ran Gimbiya ya daɗe, uwargijiyar mu Fulani ce tace mu raka ki ɗakin ki, kuma mu zauna tare dake har zuwa wani lokaci"

Da kallo nake bi su ɗaya bayan ɗaya "Oh ni Hauwa'u, wai yau nice ake ma biyayya da durƙusa mani, yau nice tare da masu mani hidima, bayan ada nice mai yi ma wasu, rayuwa kenan na baya ya koma gaba" na furta a cikin zuciyar tawa.

A zahiri kuma Fuska na saki ina mai cewa "to muje ko?"

Na wuce gaba suna biye dani, saidai da suka lura ban san kan gidan bane, ya sanya wata wucewa gaba su kuma sauran suna biye dani a baya, suna gyara mani zaman alkyabba ta.

Ko da muka isa ɗakin, na tadda har an sake gyara ko ina tsaf, an kuma haɗa mani ruwan wanka masu masifar ƙamshi, ce mani sukayi zasu zauna falo su jira ni, idan ina buƙatar wani abu inyi magana.

Ko da na fito wankan, na tadda har an kwashe kayan da na cire an ajiye mani wasu na bacci.

Ban ɓata lokaci ba na sanya, ina mai hayewa gado, sai bacci, dama ga gajiya na kwaso da yawa, zuciya ta cike da saƙe saƙe.

Washegari tun da asuba suka shigo suka tashe ni inyi sallah, tin dai da nayi sallar na koma na kwanta ba'a kuma tashi na ba, sai da na gaji na tashi, a ɗan firgice nake, saboda na shafa'a shaf da yaya yace in shirya da wuri.

An kuma haɗa mani ruwan wanka na shiga nayi, su ɗin dai ne suka kuma fiddo mani wasu kayan, ba irin na jiya bane, suma yau hadda alkyabba, su suka taimaka mani na shirya, abincin da suka shigo mani dashi ma sama sama naci shi, ina mai cewa su kai ni wajen Fulani in gaida ta, sannan su kai ni Fada wajen mai martaba.

Haka kuwa akayi, saida na gaida Fulani, cike da ƙauna ta amsa mani, tana hakimce komai haɗimai ne keyi mata, matar ta burgeni matuƙa, tana yi mani kama da wata wadda na sani, Amman na Gaza gane ko wacece ita.

Haka aka kakkaini sauran sashen matan sarkin, duk mun gaisa ba yabo ba fallasa, sannan ne jakadiya tayi mani iso zuwa faɗar sarkin, inda duk an taru ana ta fadanci.

Daga nesa na durƙusa ina mai bada gaisuwa, kowa sai kallo na yake cike da al'ajabi, masalan da mai martaba ya sanar dasu ko ni ɗin wacece.

Nan fa suka yi ta sanya mani albarka, da tofa albarkacin bakin su.

Ban ma kula da Ya Ameen dake zaune gefen sarkin ba, cikin shiga ta sarauta, kaman wani ɗanɗan sarki, sai naga ya mani kyau, ya kuwa tsare ni da idanu, yana ta faman yi mani murmushi ta ƙasan fuska.

Ba wanda ya kula da Abunda yakeyi.

Sallama mukayi da mai martaba akan cewa zamuje mu dawo, sanin ko ina zamu ɗinne ya sanya shi sanya mana albarka, sannan ya bada mota biyu ta dogarai cewa a raka mu zuwa wurin, sannan ya haɗa mu da wasu hakimai guda biyu, manyan mutane.

Ni da Ya Ameen a motar shi muke ciki, wani dogari ne ke tuƙawa, sai mota biyu bayan tamu, da ta hakimmai, sai ta dogara wa, yayin da wata ke gaban mu ta dogarawa.

"kinyi kyau wife" abunda ya faɗa kenan, bayan ya daidaita zaman shi cikin motar.

"Thanks and barka da safiya Yarima" na faɗa ina mai sauke kai ƙasa

Da mamaki yake kallo na, kenan har na fara iya kalaman masarauta?

"Da fatan kin tashi lafiya Gimbiya ta?"

A hankali na ɗaga mashi kai ina mai cewa "kaman yanda yarima na yake"

Murmushi ya saki, yana mai cewa "Yariman ki yana cikin ƙoshin lafiya, masalan da ya tsinci kanshi a gidan su gimbiyar tashi"

Jinjina kai na kuma yi, ina mai sakin ɗan murmushi, a hankali na ɗauke kaina ina mai maida shi bisa titi, yanayin garin nake kallo cike da ban sha'awa, shima a hankali ya shiga nuna mani wurare, kaman dama cen nan ne garin nasu.

Mun ɗan yi tafiya mai nisa naga mun iso wani tafkeken gareji, sojoji ne da ƴan sanda, tare da wasu irin kaki da na rasa gane su, ganin ko daga ina ake ne ya sanya suka wangale mana gate muka shige.

Kai tsaye Office ɗin shugaban su muka nufa, bayan Ya Ameen ya buɗe mani ƙofa na fito, da wani dogari ne zai buɗe mani, sai Ya Ameen ɗin ya hana ta hanyar dakatar dashi da hannu.

Babban Office ne mai kyau, cike da girmamawa aka karɓemu hannu bibbiyu, a take aka cika mana gaban mu da abubuwan sha, ba wanda yabi ta kansu, dayake yarima ba baƙon su bane, su kansu sunyi murna da zuwan nashi, domin sun san duk lokacin da ya kai irin wannan ziyarar ta bazata, asusun nasu na lamusar wani kaso mai tsoka a cikin dukiyar *Yariman Matasan*

Bayan ƴan gaishe gaishe, cike da mutuntawa, masalan ma da muke tafe da manyan mutane da zasuyi sa'anni da su Dad, a gaggauce ya gabatar masu dani.

Nan suka shiga yi mana murna, hadda kawo mani wasu ƴan kyaututtuka, a lokacin ne yake mai buƙatar su da su sanar dashi buƙatocin su.

Bayan sun gama tattauna wa ne, a take yayi masu trnsfer na dukiya mai yawa, ko ni da naji saida na girgiza, ashe Ya Ameen yana da ɗinbin dukiyar da har zai iya sa daukar da wannan kaso ɗin a ciki ba tare da ya ko girgiza ba. Sannan ya buƙaci da akai mu wajen ƴan gudun hijirar.

Nan fa aka fara bada sanarwar su fiffito ga *yarima nan ya zo duba su* aiko sai gasu suna fiffitowa ta ko ina.

Tuni aka zagaye mu, da muke tsaye cikin wata rumfa, domin Yariman yace ba zama zaiyi ba yana sauri ne zai wuce.

Daddaɓe shi sukayi suna ta kai mashi gaisuwa cike da jin daɗi, yayin da ya shiga ɗaɗɗaga yaran dake so ya ɗaga su, da gani ya sabar masu da hakan, da alamu baya ƙyamatar su, suma sun fahimci hakan, da kallo nake binshi da nake tsaye cen baya, sun matuƙar burge ni, masalan Yariman nawa da yake da zuciya ta kwarai irin wadda ake so dukkan musulmi mawadaci ya samu.

Nan fa suka shiga kai mashi koken su, duk da sun san cewa ko ba komai zasu kwashi tsawon kwana goma suna cin abinci mai rai da lafiya, harda shanu ake yankawa, duk lokacin da Yariman ya kawo masu ziyara.

Kuɗi ya koma mota ya fiddo ƴan bandir bandir ɗin dubu dubu, nan ya shiga rarraba masu, sosai sukayi murna da jin daɗi, hatta da tsofaffin da suke kwance basa lafiya sai da ya shisshiga ya gansu, suma ya masu alheri mai yawa, sannan ya buƙaci da a kira likita zasuyi magana dashi.

Koda likita yazo sun tattauna abubuwa masu yawa, ciki harda kai marasa lafiyar zuwa asibiti mai kyau, da kuma zasu ɓullo da har kar samar da magunguna kyauta ga mazauna sansanin, muddin rashin lafiyar bata yi tsanani ba. Sannan yana so zai gina masu asibiti mai rai da lafiya, zai ɗauki ma'aikatan da zai dinga biyan su albashi cikin aljihun shi, tare da kawo waɗanda zasu dinga koya masu sana'o in hannu ga masu buƙata, domin dogaro da kansu.

Aikau kaman su rungume shi, saboda tsabar murna, wasunsu kuka suke yi, Abunda nima ya ƙaryar mani da zuciya kenan na shiga rera nawa kukan, Allah na gode maka, Allah na tuba, rayuwar da nayi sai nake ganin babu wanda ya kai ni shan wahala, ashe akwai waɗanda suka fini, wasu an kashe masu mazaje, wasu sun rasa ƴaƴan su, wasu sun rasa iyayen su. Kuka nake rerawa mai cin zuciya. A hankali ya shiga takowa zuwa inda nake tsaye, ba wanda ya kula da kukan da nake ta faman yi ma, su kansu fadawan hankalin su ya ɗauku wajen rage cunkoson mutanen dake son kai hannun su ga jikin Ya Ameen ɗin da har suna mai neman kada shi, jikin shi kuwa yayi futi futu, masalan ma ƙafufun nashi dake sanye cikin takalma masu lanƙwasar kalar na sarauta. Amman haka yake daurewa yana ta sakin murmushi yana raba masu kuɗi.

Tabbas zuciyar Ya Ameen mai kyau ce, yana da imani sosai, ga tausayn na ƙasa dashi, tin fara soyayya ta dashi, ban ci karo da Abunda ya ƙara sanya ni alfaharn samun shi a matsayin mijin nawa ba kaman yau.

Tausayin su ne ya kama ni, ashe ni ina cikin aljanna ne, ko ba komai zanyi aikin da za'a biya ni, kuma a cida ni, zan ɗinka ma kaina sutura, su kau wasunsu yagaggun kaya ne jikin su, wasu ma kusan kana kallon tsuraicin su, ga rashin ruwa, wasun su yunwa duk ta busar dasu, ga ƙazantar makewayi, "Ya Allah Na tuba Allah ka yafe mani"

Abunda nake furtawa kenan, har zuwa lokacin da naji ya rungume ni yana lallashi na, ai sai na sake sakin wani marayan kukan, "ya Ameen sun bani tausayi, don Allah ka cigaba da taimaka masu" Abunda nake furtawa kenan cikin kukan nawa.

Gyaɗa mani kai ya shiga yi, yana mai ɗan bubbuga baya na, cikin shigar lallashi."I promise u my wife"

Tsaye

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment