Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amana ta ga Hajiya Kubran.

Walima ake gabatarwa mai daɗi, da ƙayatarwa, inda aka shiga gabatar da kayan ƙore ga Uwar ango da dangin ango.

Kowa yayi mamakin iyayen abubuwan da aka basu, wannan ce ta sanya Hajiya Kubra ƙara tsinkewa da Al'amarin na masarautar, duk da kayan da aka bayar, ana cikin walima sai ga ƙatuwar mota daga masarauta inji mai martaba, wai aba ango, wannan tukuicin shi ne, harda motar da ta kasance sabuwa dal kuwa.

Nan wuri ya ɗau sowa da tafi, walima ta ƙayatar da kowa.

Nan su Mama Fulani suka miƙa ni ga Mom, suna masu jaddada amanar ta garesu, duk da su ɗin sun lura cewa Soyayyar da take nuna ma Suhan ɗin kaman ta abun duniyar da ta kula suna dashi ne, duk kuwa da cewa suma kowa ya sansu a faɗin Nigeria cewa indai kuɗi ne sunyi ƙarin suna akan hakan.

Sai da aka sake raka ni sashe na, sannan suka ƙara man faɗa da jan kunne akan in zauna da kowa lafiya, da dangin miji na da ƴan uwan shi, sannan suka fara haramr tafiya, kaman inyi kuka, gashi harda su Asiya da sauran haɗiman guda biyu kawai aka bar mani wai su dinga taya ni aiki, Nidai cewa nayi a tafi dasu zan iya yin aiki na da kaina, to da nayi ma wanda ba gode bare na gode, balle wannan da yake na lada, kuma aikin ma a gidan Ya Ameen muji gareni a yanzu?

Sai gashi ba Afnan ce tayi mani maganar ledar da ya Ameen ya bari ba, wanda ni bansan menene ciki ba, Hafsat ce ta leƙo tana tambaya ta, nuna mata inda take ajiye nayi, naga dai ta ɗauko ta buɗe tana ƙunshe dariya. A haka ta fice, saboda ɗakin cike yake da mutane.

Ko bayan tafiyar Su Ammin shagali aka cigaba dayi sosai, inda Mom ta aiko aka maida ni sashen ta, yanda duk wanda yazo zaiga amarya ba tare da an ɓata man sashen ba a cewar ta.

Ina ta shan amaki fa, Hajiya Kubra da ƴan uwanta da ƙawayen nata sun koma kaman ba su ba, sia kaffa kaffa suke dani, inda Nihal da Saudat suke ji kaman su fashe, masalan ma da suka ga cenzawar da Mom tayi a lokaci guda, sai suka yi shigewar su ɗaki ma ba tare da sun sake fitowa ba, to koma dai minene dan kansu domin Nidai ya zuwa yanzu na san kaina, kuma nasha gaban su Fintinkau, saboda ina auren Yayan nasu.


**********

Komawra su mama Fulani suka tadda sabuwar dambarwar data so ruɗa su a masarautar tasu.

Umma ce ta tubure akan cewa lallai Baba waziri yana da masaniya akan faruwar komai, saboda haka ne take so ayi zama domin ya warware mata dalilin mutuwar mijin nata da yake da masaniya akai, da kuma inda dukiyar ta data ɗiyar ta ta shiga, da kuma dalilin su na aikata mata wannan ɗanyen aikin, ta dena shiru, dawowa tashi ce ta sake tada mata mikin da ta daɗe tana binnewa a cikin zuciyar ta, inda yanzu bata iya jurar ganin wanda yake da hannu cikin rusa mata farin cikin ta, Rayuwar ta, shima yana cikin farin ciki da walwala.

Kuka kawai take, Abunda ya tada hankalin mai martaba kenan, waziri na neman barin gidan, mai martaba ya hana a bar shi ya fita, a cewar shi Umman tayi haƙuri har sauran baƙin dake gidan su idasa tafiya, Abunda ya kuma ɗaga mata hankali kenan, gani take kaman ko da yaushe za'a iya wayar gari ba waziri ba labarin shi....


~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'ar Tsoron Shirka:

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ أَنْ أُشْرِكَ بِكَ وَأَنَا أَعْلَمْ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا لاَ أَعْلَمُ.
Allahumma innee a'oozu bika an oshrika bika wa-ana a'lam, wa-astaghfiruka lima la a'lam.

Ya Allah! Ina neman tsari da Kai da na yi shirka da Kai alhali ina sani, kuma ina neman gafararka ga wanda ban sani ba.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Wannan Page ɗin naki ne @Salamatu kiyi yanda kike so dashi, kuma ki gaida mana da Ya Ameen kice muna mashi Allah ya huta gajiya*

*Dama rayuwa ta gaji haka, sai Kaga wani cen daban wanda baka haɗa komai dashi ba, shine masoyn naka, mai bibiyar ka, Amman wanda kake ganin ɗan uwa ka ne, abokin ka ne, maƙwafcinka ne, ko kuma abokin wasan ka, shi kam baya bibiyar ka, balle ma idan kayi posting ɗan sharhin nan yayi maka, wanda ni kau a gani na ba haka zaman tare yace ba, idan kana son mutum kana son Abunda yake yi, ka faɗa mashi, ka ƙarfafa mashi guiwa, ta hakan ne kaɗai zaka gane cewa mutum ya san dakai kuma shi ɗin naka ne. Hmmm Allah dai ya kyauta wlh*


*Page ~66~*



Walima tayi kyau sosai kam, ni dai ina cen zaune ɗakin da Mom ta sanya aka buɗe mana ni da ƙawaye na, afnan kau sai shige da fice take yi, komai ake buƙata ita ce mai kawo mana shi. Kyaututtuka dai na sha su daga hannun manya, idan Mom taga kyauta ce mai muhimmanci Afnan take ba ta kai mani sashe na ta kulle mani.

Kwata-kwata ban ko ga giccin Ya Ameen ba, ko da wasa, tin dai asuba daya fice.

Mai video coverage yana ta faman aikin yi, yayin da gidajen tv suma suna ta naɗar abubuwa masu amfani.

Hayaniya naji ta kaure sosai a cikin harabar gidan, wai ashe anguna ne suka shigo gaida iyayen su. Da kuma yi masu Allah ya sanya alkhairi.

Sashen Kaka zuwaira suka fara shiga, aiko sun sha zaulaya kaman me? Da zasu fice ne take cewa dasu wai suje su kawo mata amaryar a ɗauke su photon tarihi.

To koda suka shigo sashen Mom ɗinma sun gaggaisa sosai, inda suka buƙaci amarya ta fito za'ayi hotunan tarihi, na wannan babbar ranar.

Haka aka sanya aka sake gyaggyara mani, kaina a lulluɓe aka fito dani, duk kowa ya fito kuwa ana ta son ɗaukar photo da amarya.

Bamu tsammani ba sai ga Dad da Alhaji Auwalu. Suma nan suka shiga akayi ta haskawa dasu, masalan da ƴan uwansu da kuma surukar tasu.

Duk abunnan da akeyi su Nihal na ciki basu fito ba, baƙin ciki da kishi kaman ya kashe su. Nihal hada hawaye tayi na baƙin ciki, saudat ce mai bata baki, akan cewa ai dole ne ma su san abun yi.
Dole aka sanya ni buɗe fuska ta saboda photon, Masha Allah, shine kalmar da kusan kowa ke faɗi, shi kau gogan naka sai tsura mani idanu yakeyi, duk motsi na yana kan idon shi, har tsarguwa nayi saboda kaf iyayen namu suna wurin.

Yayi matuƙar kyau cikin dakakkiyar shadda kalar sararn samaniya, sai ɗaukar idanu take yi, ɗinkin Abuja style.

Da mun haɗa idanu sai ya kashe mani ido guda, ta cikin farin glass ɗin da yake manne a saman kyakkyawr fuskar tashi, wanda ya taimaka wajen ƙara ƙawata fuskar.

Idan aka jera mu kuwa waje guda domin ɗaukar hoton, sai ya ɗan ranƙwafo yace mani "Baby na ya jikin naki?" ko kuma ya kamo hannu na tsaf cikin nashi, kuma idanun kowa a kanmu suke, hakan ya sake tabbatar ma mutane irin zallar ƙaunar dake tsakanin mu, wadda ba'a san tun lokacin da ta fara ba. duk sai kunya ta kama ni, Naji na ƙagara mu bar wurin,tin kafin ya aikata Abunda zan ji kunya sosai, tinda na lura kaf natsuwar shi tana a kaina ne.

Anyi shagali sosai, inda anguna suka fice, duk da haka saida ya kira Afnan gefe, wai idan ta sake ko Ƙuda ya taɓa mashi ni sai yaci ƙaniyar ta, kuma ba zai siya mata motar da take so ba.

Aiko dariya ta fara yi, tana ihun tsallen murna, ta daɗe tana mashi magiyr motar nan, sai gashi yanzu ta dalilin Aunt Suhanan zata samu.

Aiko ta dawo ta fara kaffa kaffa dani, da anyi magana tace ai ango ne ya bata amana ta. Don haka yanzu ita ce matsayin angon.

Sai a sanya dariya, kowa na mamakin irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakani na da Afnan ɗin, duk kuwa da cewa ma girme mata, ba za'a taɓa cewa tsara ta bace.



A hankali mutane suka fara raguwa, sai bayan magariba ne Mom ta sanya aka maida ni sashen na. Inda aka hana kowa zuwa banda ƙawaye, wai a cewar su a bar su su gyara mani sashe na.

Mom ce tace Maree taje ta taya su. Aiko jiki ba ƙwari ta bisu, dalili kuwa shine tana son ma ta shiga sashen da ake ta zuzutawar cewa yafi ko ina kyau a gidan, oh wai yarinyar da suka raina ma wayau yau ita ce Allah ya maida haka.

Ni kam tinda ta shigo tana ta wani kalle kalle da raɓe raɓe, sai Naji na tsargu ban yarda da shigowr tata ba, Afnan nayi ma magana cewa tace nace ta bar shi kawai nagode, saboda ko alama ba zan iya lamuntr barin nata ta shigar mani ɗakin mijina sirri na ba.

Aiko da saƙon ya iske ta, kaman ta fasa kuka, taso ko da kaɗan ne, ta gano wata mafaka da zata iya samu, wadda zata yi amfani da ita ko da nan gaba ne. Ta yanda ko wata ajiyar tayi ba zan iya gano ta ba kai tsaye.


Haka ta fito zuwa ɗakin nasu, kuka ta dasa ma Mama Talatu, laifin ta take gani, ita ce ta kasa bata abunda take nema, ta kasa yin wani kwakkwaran aikin da zai warware wannan al'amarin.

Aiko zagi mama talatun ta hau ta dashi kaman zata bugeta, har tana ce mata, ita fa ta zubda makaman yaƙinta ne, saboda yanzu ta gano cewa Umman mace ce ce mai ɗinbin darajar da idan tayi wasa da ita, zata iya sanyawa a ɗaure su har igiya tayi rara, sannan taja hankalin ta akan cewa itama ta kiyaye, in kuma zata je tyai wani abu da zai sanya a kore su a gidan ne, to ta sani daga ra ar ne fa zata gane cewa tayi wauta, domin cewa zata yi ba ita ce ta haife ta ba, itama tsintar ta tayi, domin ba zata ka. U ta ba, tsawon lokaci tana zaune a gidan cikin rufin asiri kwatsam tazo tayi mata sanadin inda take raɓe ba.

Maree kam kukan ta take, koma fahimtar Abunda mama Talatun ke cewa bata yi, ta ƙudurce abubuwa masu yawa a cikin ranta. Sam ba zata lamunci ganin burin Rayuwar tata tare da wata cen ba.


*********

Da kyar su Mai martaba da Mama Fulani suka shawo kan Umma ta yarda ta haƙura, zuwa bayan hidima, taji ɗan sauƙi, masalan da Mama Fulani ta sanar da ita irin tarba da masauƙin da suka samu, abun sai Sam barka, har suka baro gidan basu ci karo da wani abu da bai kwanta masu ba, sun sake tabbatar da cewa tabbar MUHAMMADU Al'ameen yarimn matasan gadon alkhairi yayi, domin ko kafin su taho siada Alhaji Mustapha ya cika su da sha tara ta Arziƙi, yana ta masu godiya, tare da miƙa saƙon gaisuwa zuwa ga Baffa mai martaba, da cewar sai sun shigo shi da zuri'r tashi kaf bayan biki godiya.

Umma taji daɗin hakan, ta sake alfahari da samun miji kaman Dad ɗin, saidai Abunda ke ɗaure mata kai, cenzawar, da kuma amincewr auren da Hajiya Kubra tayi lokaci guda, saidai ma ko menene tana fatan ya kasance cewa har cikin zuciyar ta ne.


********

Sai bayan isha'i ne suka kammala gyaran ko ina, tsaf kaman ba'a taɓa shiga sashen ba. Su raihana ne ke sanar dani cewa gobe zasu koma makaranta, duk Abunda ake yi jikin khade a sanyaye yake, duk kuwa da cewa tayi sabon saurayi itama mai ji da kyau da naira cikin abokan Ya Ameen ɗin.

Basu bar ɓangaren ba, siada suka jiyk maganar ya Ameen cikin gida, Afnan ce ta janye su, tana mai faɗin "Uhmm kuzo mu bar sashen nan, tin kafin oga ango yazo yayi mana mazurai" dariya suka sanya, suna sake jaddada mani cewa da wuri suke son wucewa, saboda jibi an gaya masu suna da assesment.


Ganin hakan ne ya sanya ni tashi domin rage kayan jiki na, dama na gaji ga kuma nauyi da kayan ke dashi, kallo na nakai kan Kyaututtukan da na samu, harda makullan mota, da kuna gwala-gwalai, sai kuɗi cash ƴan bandur bandur ɗin 1k da kuma check, wanda bansan me ke rubuce jiki ba, dama jira nake sai ya shigo sannan in nuna mashi.

lallai kyautar manya, tabbas wlh wata ma ta riya ce, to in ba haka ba, daga auren yaron su sai su dage suyi ta zuba mani kyauta haka? In ma sunyi don a maida masu ne, to wannan tsakanin su da Mom da Dad ne tinda domin su sukayi


Toilet na shiga na watsa ruwa, ina fitowa Naji waya ta ta ɗauki ruri.

_Hayateee_ shine sunan da na yi saving Number ɗinshi, domin ya zuwa yanzu na yarda cewa shine rayuwa ta.

Ɗagawa nayi cikin siririyar murya ta, ina mai amsa Sallamar da yayi mani, jin muryar shi wani iri ne ya sanya jiki na yin sanyi.

Shaida mani yayi cewa Hafsat ce ba lafiya, gata nan za'a shiga da ita teater, domin sun shaida masu cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba.

Salati na sanya, ina mai kai zaune cikin tashin hankali.

"Ina Sadeeq?" tambayar da na fara yi mashi kenan, domin nasan duk inda yake yana cikin tashin hankali.

"Wallahi baby yana cen yana kuka, bakiga tashin hankali ba, sunce yaro har ya shekara, dama tini suka so suyi tin kafin abun yayi worst haka, sune suka ƙiya"

Nima ai sai Naji kukan ya taho mani, kuka nake yi sosai, ina ce mashi yazo ya ɗaukeni inje in gano Hafsat, kada ta mutu bamu gana ba.

Lallashi na ya fara yi, sai kuma lokacin yayi danasanin kira na, ya manta halin ruɗu da firici na. Yanzu zan tashi hankali na, gashi kuma shi baya jin idan zai iya bari na fitowa a yanzu, dandai kawai sanin yanda nake da ita ne ya sanya shi sanar dani.

Hankalin kowa fa a tashe yake.

Hajiya Zainab dai zaune kawai take tana ta faman addu'a ga ɗiyar tata, domin halin da aka shiga da ita ba'a cewa komai.

An kusan awa sannan aka fito da baby girl samɓaleliya da ita jawur. Saidai jikin nan duk yayi saɓa, yarinyar ido tar sai kallon kowa take yi, caaa akayi ma likitnn da ya fito da jaririyar ana tambayar shi jikin Uwar, bai ce komai ba ya juya ya koma yana girgiza kai.

Sai kuma aka saka kuka sosai wurin ya amsa da koke koke, shi dai Sadeeq zubewa yayi wurin saida aka kwashe shi. Bilal ma idanun shi jawur, tunowa da yayi da tashi matar da take cikin hali irin na Hafsat ɗin, Amman bai sanar da kowa ba, so yake har sai an haihu ɗin sannan, masalan ma da yake shi ba ƙasar bane.


Dfik dauriyar Hajiya Zainab saida ta koka, nima ya zuwa lokacin nasha kuka na na ƙoshi, ƙasa Daurewa nayi, da gudu na fito na samu mudi zaune shima jugum, saboda da shine aka kai Hafsat asibitin.

Umurtar shi nayi da ya kaini nima, musu yaso yayi mani na shiga yi mashi magiya.

Kwatsam saidai suka ganni wurin da gudu, ina ta faman kuka, kukan dana tadda wurin anayi ne ya sanya ni durƙushewa nima, ina mia sake sakin wani kukan.

Kowa yayi mamaki, da sauri Ya Ameen ya isa inda nake durƙushn, Amman sai ya kasa ɗago nin zuwa jikin nashi, Goggo Aisha ce ta matsr dashi da hannu, tana mai ɗago ni itama ta rungume ni sosai, tana mai goge kwlalar ta itama, Hafsat yarinya ce mai shiga rai, duk hidimar bikin nan ta daure ayi ta da ita, ashe ma ba zata ga ko Abunda ta haifa ba.

Abubuwa nake tunowa dangane da ita sosai, yanda take ƙarfafa mani guiwa, yanda idan na shiga ƙuncin hali ita ce mai lallashi na, yanda tayi tsaye kai da fata wajen ganin na samu mallakin zuciyar tawa, sai gashi ashe ko Rayuwar auren tawa ba zata gnai ba, tayo shahada, rai yayi halin sa, naso saka ma Hafsat da Alkhairin da ba zata iya taɓa mantawa ba.

A hankali na zame jiki na zuwa ga Hajiya Zainab da take zaune kurum kaman mutum mutumi. Miƙewa tayi itama tana mai rungume ni, kaf wurin kowa ya tausaya mani, ganin yanda nake da Hafsat ɗin, duk a cikin zuri'r su daga ita sai afnan ne mukayi muguwar shaƙuwar da za'a iya cewa kaman ƴan uwa a suke.

Dangin Sadeeq ɗin wasu suna nan tsattsaye suna ta aikin lallashin mu, wasu kuma suna cen wajen Sadeeq ɗin da har yau baisan wa ke kanshi ba.

Haka aka gunguro gadon da Hafsat ke kwance, an lulluɓe ta dukan ta, fuskar ce kawai buɗe, tayi kyau, tayi haske tayi fayau, kaman ma murmushi take yi, hannuwan ta duka bisa ƙirjin ta, kaman ka kira ta, ta amsa.

Da sauri na fara taka wa zuwa bin gadon, Ya Ameen ne ya sanya hannun shi ya riƙo ni , ganin nafi kowa ruɗewa a wajen, bansan lokacin ɗana faɗa daman jikin shi ba, ina mai sake sakin wani tsumammen kuka.

Bai ƙasa a guiwa ba, wajen rungume ni da dukkanin hannayn shi ba, shi kanshi hawayen ne ke tsiyaya ta cikin farin glass ɗin nashi, kuma na, shine Abunda ke ƙara ruɗa shi, a kunne ya faɗa mani "Hafsat ta tafi Suhan, ba kuka take buƙata ba, addu'a ita ta kama ce ta a yanzu"

"Babyn Yaya, ina babyn take?"

Abunda na samu kaina da furtawa kenan.

Wata mata ce cikin dangin Sadeeq ɗin ta matso kusa damu, haɗi da miƙo mani jaririyar naɗe a shawul, sai mamurar hannu take, alamun nono take so, idanun ta a buɗe rangaram, kaman tayi watanni. Rungume ta nayi, ina mai sake sakin kuka, yarinyar kaf kamannin Hafsat ta kwaso, sai Hasken Sadeeq ɗin.

Muna a haka ne, sai ga su Mom da Afnan, kai harda su Raihana da Khadeeja, Jiddon Dady da shi kanshi dady ɗin.

Nan fa aka buɗe sabon ba in kuka, saboda ɗan zaman da sukayi tare da Hafsat ɗin har sun saba da ita, masalan ma ganin yanda kullum tana zaune wuri ɗaya turus da uban ciki a gaba, sai ka ganta tayi shiruuu, kaman mai tunanin wani abu, cen kuma sai Kaga tana walwala kaman ba ita ba.

Fitowar likitocin da nurses ɗinne yaja hankalin mutane.

Raba jikin shi da nawa yayi a hankali yana mai furta mani "Am coming dear" bayan su yabi zuwa office ɗin nasu.

Ko zama baiyi ba suka miƙa mashi hannu, fuskar su a washe.

"Congratulation ranka ya daɗe, anyi Masarar ceto Hafsat Auwal, yanzu haka tana hutawa ne, saboda haka wannan koke koke da ake tayi please a dena, idan son samu ne ma, mutum ɗaya za'a bari wadda zata kula da baby, zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai ku dawo kuga jikin nata"

Bai ko zauna ɗin ba, sia yayo kwana. Kaman zai taka rawa haka take ji, matar tashi yake tunowa, wane irin farin ciki zata yi? Hajiya Zainab fa? Itama wane irin fari ciki zata yi? Hafsat ma da rai? Bata mutu ba? Alhamdulillah, shine Abunda yake furtawa har ya ƙara sa inda suke tsaye cirko cirko.

"Alhamdulillah, Mama ki dena kuka, Hafsat na nan da ranta, bacci ne take yi, ba mutuwa tayi ba" shima ya faɗa yana mai ramawa zuwa wajen da Hajiya Zainab ɗin ke zaune ya kamo hannun ta.

Ajiyar zuciya kowa ya saki, ai sai kuma aka hau murna, rungume jaririyar nayi ina mai sakar mata kisses, banyi niyyar bayar da ita ba, niyya ta ni ce wadda zan riƙe babyn Hafsat ɗin, nice ya cencenta da in riƙe ta. Wani irin kukan murna na saki mai haɗe da dariya, ai sai kuma aka fara ma juna murna da barka.

Shima fuskar shi washe fal da murmushi yake kallo na. Ɗakin da ka kwantar da Sadeeq ɗin ya zarce kawai ya shiga labarta masu wannan abun farin ciki, ya tadda Sadeeq ɗin ya farfaɗo ana ta bashi baki.

Ai baisan ya rungume Al'ameen ɗin ba, ba zai taɓa mantawa da wannan albishir ɗin ba ɗaya fito daga bakin Yayan nasu ba.

Durowa yayi daga bisa gadon yana mai nufo ɗakin da aka kwantar da Hafsat, dakatar dashi akayi, cewar likitocin sun hana sunce a bari ta huta, ai bai ko tsaya jiran cewar su ba, ya danna kai ɗakin, nima ban jira komai ba na rufa mashi baya, tadda shi nayi rungume da ita, sai kisses yake sakar mata, miƙa mashi ɗiyar nayi, ya haɗa su ya rungume.

Ya Ameen ne ya shigo, gami na tsaye ina goge kwlala da hijab, ya sanya shi kamo ni zuwa jikin nashi, ban gaddama ba nima na faɗa, ina mai sakar mashi wani irin siririn murmushi, a hankali ya kia bakin nashi saman goshi na, yana mai using da hannun shi ya shiga goge mani sauran kwallar data taru, yana yi yana girgiza mani kai,alamun in bar kuka, ɗan duka na kai manƙirjin nashi, ina mai kwantar da kaina, ya sanya hannun shi ya sake lafar da kan nawa.

Mun jima haka, kai kace ba zamu so rabuwa ba.

Sai cen ne muka fito Ya Ameen & in ke shaida masu kowa gida zashi zuwa gobe idan ta farko sai a dawo a ga jikin.

Ban aka fara raguwa, inda Mom ce tace zata zauna da Hafsat ɗin, kowa yayi mamaki, har ƴaƴan nata, har shi kanshi Ya Ameen ɗin. Haka muka baro

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment