Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~71~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Tafiya yake a hankali, zuciyar shi gabaki ɗayanta a cunkushe take, fuskar nan tashi sam babu walwala, duk kuwa da ƙoƙarin da nayi wajen ganin ya saki ran shi kafin ya fita ɗin, dama tinda yaga wayar dady ɗin nashi saida gaban shi ya faɗi, har kawo lokacin da ya ɗaga yake sanar mashi cewa ya same shi guest house ɗinshi dake bayan gari.

Yasan maganar, kuma yasan kan zancen, wannan ce ta sanya har yanzu ba zai iya tantance a matsayin da yake kai ba, ya sani sarai Mom ba zata lamunta hakan ba, Amman da ba abunda zai tsaida shi a ƙasar, balle dukkan Abunda zai faru ya faru yana nan, har ya juye zuwa kanshi, to saidai baya jin zai iya barin amaryar tashi da har yanzu basu rufa sati guda ba ma cur a tare, wanda zai iya cewa har yanzu bai san daɗin angonci ba saidai ƙalilan, yana matuƙar ganin ƙoƙarin Suhan, duk da ta fahimci Abunda ke faruwa, Amman Sam bata bayyana mashi fushin ta ba, in banda ɗan tashin hankali ƙalilan da yake iya hangowa a kwayar idanun nata, duk kuwa da ƙoƙarin ɓoye mashi da take yi.

Da haka ya isa ga guest house É—in, inda mai gadi ya buÉ—e mashi gate É—in, a wajen parking ya tadda motar Dad, alamun da ke nuna mashi Dad É—in nashi na jiran shi kuwa.

Kallon agogon rolers da yake hannun shi yayi, lokaci guda yana mai ayyanawa a ran shi dare yayi, dole yayi maza ya kammala abunda yake ya koma ga Suhan ɗin da ya baro ta cikin tsoron rashin sabo, masalan a ɗakin hotel ita kaɗai, girgiza kai ya shiga yi a hankali, irin ƙaddarar tashi kenan.

Da salon tafiyar shi cikin ɗan hanzari ya tattaka zuwa cikin babban falon da ya ƙunshi kujeru da dama, mai ɗauke da manyan ɗakuna da suka taimaka wajen ƙara ma ginin guest house ɗin girma.

A ƙaramin falon dake cen ciki ya tadda Dad ɗin nashi, zaune yake cikin kamala da dattako kaman ko da yaushe, jarida ce ta daily trust a hannun shi yana dubawa, gefe guda kuma Mug ne mai ɗauke da cufee da ƴar ƙaramar buta mai kyau fara tas da ita.

Gefen Dad ɗin ya samu ƙasa ya zuƙunna yana mai tankwa she ƙafa, gaida Dad ɗin nashi ya shiga yi, daga yanayin da Dad ɗin ke kallon shi, ya karanci tsantsrr damuwa dake yawo cikin zuciyar tashi.

Cikin sakin fuska ya amsa, ko ba komai yana buƙatar ya kawo wani yanki na sassauci a cikin zuciyar Son ɗin nashi, tausayi yake bashi matuƙa ainun, saboda hakan ne ma ya yanke hukuncin Abunda yake ganin shine zai kawo masalaha ga al'amarin.

Gyara zama yayi, yana mai nuna ma Al'ameen kujerar da take kusa da tashi, alamun ya dawo bisa ya zauna, ba musu ya miƙe ya koma bisa sofar.

Da hannu yayi mashi alamun da ya zuba Cofee ɗin shima, jim yayi kaman ba zai zuba ba, sai kuma ya miƙa hannu yana mai tsiyaya kaɗan.

Har yanzu Dad nazarn shi yake yi. Gyaran murya yayi, yana mai kallon Yaron nashi cikin wani irin yanayi ya fara magana.

"Al'ameen dalilin da ya sanya nayi kiran ka anan shine, sanin kanka ne cewa ya zuwa yanzu Abunda ke faruwa a cikin gidan namu ya fara zaga kunnen mutane, saboda haka ne bana so hankalin Æ´an jarida ya dawo kanmu, ka ganta nan? (Ya nuna mashi jaridar dake hannun shi) jarida ce ta gobe wadda zata fita, ka duba title É—in dake sama me Kaga an rubuta?"

Ya faɗa yana mai miƙa mashi jaridar.

*WATA DAMBARWA NA NEMAN KUNNO KAI A GIDAN AMBASSADOR ALMUSTAPHA YUSUF DAMBULAN, SAKAMAKON DAMFARAR MATARSHI MAI SUNA DR. HAJIYA KUBRA DA WANI MUTUMI MAI SUNA ALHAJI YARO DA YA KASANCE MIJI GA AMINIYAR TA HAJIYA LAILA MAMUDA, DAMFARA KUMA DA ZAMU IYA CEWA TA MILIYOYIN KUDAÆŠE, WANDA HAKAN NA IYA KAWO RUÆŠANI DA FARUWAR WANI MUHIMMIN AL'AMARI*


A matuƙar ruɗe Ya Ameen ya ɗaga yana kallon Dad ɗin nashi. Duniya kenan kana bacci ana maka munshari. Watau wannan maganar har ta iya fita waje kenan? To wanene ya fidda ta? Ko dai Hajiya Sa'a ce?

Bai iya cewa komai ba, sai bin takardar yake da kallo, kaman tsohon makahon da idanun shi suka buÉ—e a lokaci guda.

"Kada ka tashi hankalin ka, Abunda nake jiye ma Mom ɗinka kenan tun tuni, wannan al'amari kuma na iya kawo mana naƙasu da koma baya ta fannin kasuwancin mu, masalan ma kai da yanzu idanun kowa suke kan ka, saboda ɗaukaka da Allah yayi maka. Wannan ne dalilin da ya sanya na nemeka nan domin in sanar dakai Abunda nake so kayi, domin idan muka daka ta mahaifiyar ka, ba za'a taɓa samun masalaha ba"

Jinjina kai yake yi cikin tashin hankali, me mom ɗinshi take so ta zama ne? Wai shin yin kuɗi ko Arziƙi kansu farau ne? Bai taɓa danasanin arziƙin da yake dashi ba sai yau, bai taɓa danasanin haihuwar shi gidan da suka rufa suka tada kai da Arziƙi ba sai yau, yana ji ace dama gidan da kullum rana ta Allah sai an fita an nemo za'a kawo masu suci, suyi makaranta ta gwamnati, su kwana a saman katifa ko tabarma, aka haifeshi yana jin da hakan da sai yafi zama mashi mafi alkhairi da kwanciyar hankali.

Maganar Dad ɗinne ta katse mashi tunanin da yake yi, "Idan Allah ya kaimu gobe ka ɗauko Matarka ku dawo gida, ni da Mahaifiyarka da Alhaji Yaya zamuje cen garin su Umman ita matar taka, mai martaba sarki na neman ganin mu, saidai ina so kafin mu dawo duk yanda zakayi ka nemo dukkan info akan Alhaji Yaro, da dukkanin harƙallolin da Mom ɗinka keyi ba tare da mun sani ba, wannan kuma zai faru ne tare da taimakon Barrister Kabeer, saboda haka dole ne ka ɗaura ɗamba, ka ƙarfafa zuciyar ka, ni na sani zaka iya cin karo da abubuwa da zasu iya dagula maka lissafi, saboda kasan Halin Hajiya sarai, ba jin magana take yi ba a lokutta da dama, dole ka aro jarumta ka sanya ma ranka, dole ka ƙarfafa ma kanka guiwa, insha Allahu zamu kawo ƙarshen wannan al'amari cikin sauƙi, nima kuma idan na dawo da izinin Allah zan taimaka maka ɗin. Don haka yanzu ka tashi kaje wajen Matarka, zuwa da safe kuma ku koma gida, saidai kafin safen ya kamata kayi nazari ta yanda zaka ɓullo ma wannan al'amari cikin sauƙi ba tare da kaja hankalin ƴan jarida ba, ko gidajen redio"

Sai da ya nisa sosai, sannan yayi ma Dad ɗin nashi sallama, da kallo ya bishi, yana mai kallon Mug ɗin Cofee ɗin da ya ajiye ƙasa, wanda bai ma san ya sauke shi ba, ko sau ɗaya kuma bai kai shi bakin shi ba. Har ya fice daga cikin falon, sannan ya sauke numfashi yana mai cewa "Hakanan zaka ci gaba da haƙuri da mahaifiyar ka, abubuwa da dama da take aikatawa bata yar a ƙasa bane"


*******


Har bacci ya fara fizga ta lokacin da naji shigowar shi, saida ya kulle ko ina sannan ya nufo ɗakin, lokacin har na sauko daga bisa gadon, jiki na sanye da pajamas masu taushi tare da salƙi, kaina sanye da hula mai taushin gashin mage, na cusa dukkanin gashi na da yake tsefe ciki, sai nayi kyau, koni lokacin da nayi wankan na gama shiryarwar kasa dena kallon kaina a madubi nayi, duk da fuska ta babu komai saman ta in ka ɗauke face cream da glow dake sama.

Bakin ƙofa muka ci karo dashi, yana ƙoƙarin shigowa ni kuma ina ƙoƙarin fita, saman ƙirjinshi na faɗa ban sani ba, saidai Naji ya sanya dukkan hannuwan shi ya zagayo bayana dasu, ya rungume ni tsaf a cikin faffaɗan ƙirjin shi.

Luf nayi, ina mai amsar saƙon zuciyar tashi.

Saidai yanayin yanda Naji tana bugawa da sauri da sauri ne ya sanya ji É—agowa cikin hanzari ina mai kallon fuskar tashi.

Idanun nashi a kulle suke ruf, sai zara zaran gashin idanun shi da nake iya hangowa, haÉ—e da girar shi mai kyawon yanayi.

"Yayana kana lafiya kuwa?" Abunda na iya cewa kenan, har yanzu ina cikin jikin shi sosai.

A hankali ya buÉ—e idanun nashi yana mai É—ora su saman fuska ta, sai kuma ya shiga zame hular kaina a hankali zuwa rabin kan nawa, yana mai É—ora bakin shi bisa fore head É—ina ya shiga sakar mani wani irin Kiss.

Nidai har yanzu tsaye nake, hannun shi guda tallafe da ƙugi na, a haka na shiga jan shi, zuwa bakin gado. Safar shi na shiga saɓule mashi, tun da ya riga ya cire takalman already. Bai hana ni ba, sai kallo na da yake yi, wata irin ƙaunar shi na ratsa ni, a yanda nake ji a yanzu, ba zan taɓa iya rayuwa ba tare dashi ba.

Toilet na wuce nan haɗa mashi ruwa, yau kam saidai ni na taimaka mashi wajen wankan, ina lura dashi yanda jikin shi yake sanyaye, kuma yana yawan tafiya tunani. Hakan ce ta sanya koda muka kwanta saidai ya rungume ni yana mai sakin ajiyar zuciya akai akai. Inda ni kuma Naji daɗin jikin nashi, tuni bacci ya kwashe ni, yayin da shi kuma ya zurfafa a cikin tunani, dole ne yace ma Bilal ya dawo, ba zai iya shi kaɗai ba, matsalar Mom zata iya tarwatsa mashi kwanya tuni. Yana buƙatar mataimaki, kuma baya so damuwar shi ta shafi Suhan ɗin, Shiyasa dole ne duk yanda zaiyi ya kauce mata wajen faɗa wa cikin damuwar itama zaiyi.

Da safe bayan mun gama komai na Al'ada ne yake ce mani in shirya kaya zamu koma gida, kaman yanda bai man wani cikakken bayani ba, nima hakan ban tambaye shi ba na shiga haɗa kayan, hakan da nayi ya matuƙar burge shi, kuma hakan na nuna mashi ba zan taɓa bijire ma umurnn shi ba, sannan ni ɗin ba mai shiga al'amarin da aka juna ba'a so da in shiga ɗin ba.

Ya santa da sanyin hali, hakan ne ya sanya dole ne duk yanda zaiyi wajen ganin ya bata kariya daga dukkan wani abu zaiyi, baya jin zai iya lamuntar damuwa da halin da yake ciki ya shafi matar tashi. Bai same ta da sauƙi ba, haka kuma dukkan wani al'amari da ya shafe shi baya jin shi da sauƙi.

Har muka isa gidan motar tsit, ba mai cewa komai, sai naga yau ya koma man kaman Ya Ameen ɗin da na sani da cen baya, muskili mara walwala da fara'a. Nasan damuwar shi, kuma ina ganin ƙoƙarin shi matuƙa, hakan ce ta sanya nima sai ban nuna mashi nasan yawan damuwar da yake ciki ba, gudun kada yace ina shiga sha'anin shi shi da Mom ɗin tashi.

Yayi mamakin da akace mashi su Dad ɗin sun wuce, Nihal ce ke sanar dashi hakan, lokacin da muka shiga cikin gidan, bata tanka mani ba, haka nima ban tanka mata ba, nasha alwashin matuƙar gyara mata zama cikin ruwan sanyi, shi bai ma ko kula da rashin gaida ni ɗin ba, ya sanya kai riƙe da hannu na muka fice daga sashen.

Da kallo ta bimu tana mai taɓe baki cikin ƙaunar zuciya, cikin ranta take rayawa an gama da yayan nata, saidai duk yanda zata yi ta ƙarƙashin ƙasa itama sai tabi domin cusguna ma zaman nawa da yayan nata a cikin gidan, muddin tana cikin gidan (Nace ai sai kiyi ta zama, ki kalli Abunda zai kashe ki da rayuwar ki)

Koda muka shiga sashen namu bai zauna ba, na kula yana cikin sauri ne, sai ban tsaida shi ba, na raka shi har ƙofa ina mai yi mashi a dawo lafiya, saida ya bani peck a goshi sannan ya fice.

A sanyaye na koma cikin gidan, wannan wace irin rayuwa ce? Dama haka Rayuwar masu kuÉ—in take? Ashe hakanan talaka ke sha'awr Rayuwar masu kuÉ—i, ashe matsaltsalun su sunfi na talakawa yawa, takalma ne zai kwana Baida ko sisi yayi bacci hadda munshari, Amman mai kuÉ—in da yake da biliyoyi ya kasa bacci, kaman yanda Ya Ameen yayi a daren yau É—in.

Kitchen na wuce bayan na gama gyara ko ina, dole in sama mashi Abunda zai ci, wanda zai iya sanyaya mashi rai kafin ya dawo, duk da nasan maganin masalar tashi saidai Allah.

*******

Kai tsaye office É—in Br. Kb ya wuce, shi kanshi Br É—in yayi mamakin jin cewa wai Ya Ameen É—in ne da kanshi yazo wajen nashi, ba É“ata lokaci ya sanya aka shiga dashi har cen ciki.

Miƙewa yayi da niyyar kawo mashi abun sha ya dakatar dashi.

Bayan sun gaisa ne ya buƙaci da ya kawo mashi files na dukkanin ƙaddarorin Mom ɗin tashi, da dukkanin wata takarda dake ɗauke da shaidar zuba hannun jari ta, da kuma sauran duk wani abu daya shefi Mom ɗin tashi. Yayi mamakin ganin himilin tarin takaddu sosai a gaban shi. Haka ya dinga bun su ɗaya bayan ɗaya yana dubawa.

Ba zan iya fasalta halin da ya shiga ba, da yana da hali kaf, gabaki É—aya dukiyar Mom sai ya amshe ta daga hannun ta, ko za'a samu zaman lafiya, da zata iya zaman aure, kaman yanda ko wacce mace keyi, Dad ba abunda ya rage ta dashi, saidai har ta kai ga tana yin wasu huÉ—É—oÉ—i da kuÉ—aÉ—ennnata da bata iya sanya wani daga cikin su saidai shi Brst É—in, shima dan ya dama dole ne, gudun irin hakan.

Zuciyar shi sai Fat-Fat take kaman zata tsago ƙirjin shi ta fito. Ba Arziƙi ya nemi Layin Bilal. Daga yanda yaji maganar aminin nashi ya san ba lafiya, Shiyasa tun kafin ma ya faɗ a mashi dalilin kiran ya shiga sanar mashi cewa gashi nan a airport zai taso. Kashe wayar yayi ba tare da ya ce komai ba, ya rufe folders ɗin, yana mai maidawa bisa table ɗin barrister ɗin da ya koma shima ya zauna yayi relax yana ta Kallon al'ameen da sai ka rantse da Allah bai taɓa dariya ba, idanun shi sun kaɗa sunyi jawur dasu.

A hankali ya É—ago yana kallon barrister É—in, inda a hankali ya buÉ—e baki, muryar shi na cracking ya shiga cewa "Ina so in gana da Baba Alhaji"

"OK yallaɓai zamu iya zuwa yanzu"

Abunda Barrister ya faɗa kenan yana mai Miƙewa ya shiga tattara folders ɗin ya zuba cikin wata safe lucker ya kulle da ɗan makulli.

A motar Ya Ameen suke tafe, yayin da Barrister ɗin yake zaune gefen Ya Ameen, shi kuwa mutumen zaune kawai yake, inda tuƙin ma da hannu ɗaya yake yin shi, ya muskuta sosai inda hannun shi guda da yake bisa ƙofar motar ya dafe baki ɗaya dashi, Allah kaɗai yasan ne ke yawo a cikin zuciyar tashi. Mafita ɗaya ke gareshi, kuma ya tabbata da izinin Allah zai same ta a wajen Baba Alhajin, ba zai taɓa barin wata ƙofa ta tozarta da zata iya shafar ahalin nashi ba.

Kusan duk inda suka gitta sai Kaga matasa na É—aga masu hannu, sun gane motar, Amman Sam shi hankalin shi baya kansu, dalili da hakan ne ma ya kira manager É—in shi tun da safe yake shaida mashi yaba dukkanin ma'aikatan leave na kwana biyu, akwai muhimman ayyukan da suka taso mashi, inda dukkanin kanfanonin nashi na gida da na wajen ya bada izinin a kukkulle su gabaki É—aya, zuwa dare zai gana da shuwagabanin nashi na kanfanonin. Amman ya bar hakan ne har sai Bilal ya dawo, inda shine zai aiwatar da kaso 80 a cikin É—ari na ganawar.

Ko da suka isa gidan, shaida masu akayi da Baba Alhajin ya tafi asibiti ganin likita ido, wanda yake fama dashi shekara da shekaru. Dan dole suka dakata a babban falon baƙin, inda barrister ya fiddo system ɗin da yake recording komai na Hajiya Kubran tun daga amsar aikin da yayi nata, daga hannun mahaifin nashi.

Sosai ya natsu tsaf yana kallon komai, akwai abubuwa da dama da bai fahimta ba, yana so ne har sai Baba Alhajin ya ƙara so, inda yake sa ran jin cikakken ƙarin bayani daga gareshi....



**********

Tafiya ce da zamu iya kiran ta da zaman shiru, idan ka É—auke Alhaji Mustapha da kwalli kwal É—in yayan nashi dake gareshi kaf faÉ—in duniya, sune kawai suke Æ´ar firar su jefi jefi.

Har yanzu zuciyar Hajiya Kubra na gargaɗar ta dalilin da ya sanya ta yarda ta biyo su wannan tafiyar, saidai shara ɗin da mijin nata ya gindaya mata, shine kawai Abunda ya katange ta daga cewa ba zata je ɗin ba, zuciyar ta na raya mata har yanzu wani ɓari na zuciyar bai yadda da Abunda aka faɗa mata ba, na cewa Umman ƴar sarauta ce gaba da baya, kuma masu Arziƙi ne, anya ba wata ƙullalla akayi mata ba? To ita yanzu tace taje ina? "Gidan su kishiya" wata zuciyar ta raya mata, ɗan ƙaramin tsaki taja wanda ita kaɗai ce zata iya jin Abunda tayi, wayar ta ta fiddo tana lallatsawa.

Har suka shiga cikin garin tana nazari, ji take kaman tace su ajiye ta ta koma, gabanta na matsanancn faɗuwa, har kai lokacin da suka fara ratsa tangama tangaman gate ɗin tanƙamemiyar masarautr. Duk gate ɗin da suka bi sai driver ya tsaya da motar, kafin a lura da wanda suke ciki a basu izini wucewa.

Sun samu tarba sosai, tun fitowar su daga mota zuciyar Hajiya Kubra ta tsinke, anya ko gaskiya ne Abunda take ji? Kai da sakyal, anya wadda take matsayin É—iya ga wagga babbar masarauta zata iya tafiya tayi zaman bauta na kusan tsawon shekara ashirin, bayan ma kafin tazo gidan ga dukkan alamu ta daÉ—e a wani wajen? Jikinta da komai nata baya nuna cewa ita É—in wata ce, kawai dai kawaici da rashin hayaniyarta ne zasu iya shida maka da cewa ita É—in ba ta son hayaniya, ba daga nan ba, babu shaida ko kama.

Da wannan tunanin suka ƙarasa fadar , inda suka tadda an cika maƙil ana fadan ci.

Cikin girmamawa suka gaisa da kowa, ita dai Hajiya Kubra na zaune lankwashe da ƙafa, kaman yanda suka ga kowa nayi, sarauta ai tafi kuɗi, duk da kuɗin ma na siyan sarautar.

"Wannan da nake gani kaman Kubra É—iyar Ibrahim ko?"

Cewr Waziri da yake zaune a gefen sarkin, duk da yanzu baya da wata faÉ—a aji, kowa ya san matsayin da ya ajiye shi, Amman hakan bai hana aka tilasta shi fitowa majalisar sarki ba.

Cikin mamaki ta ɗago kanta tana mai ƙare ma tsohon kallo, kafin ta buɗa baki tace "Eh nice kuwa Baba"

"Ikon Allah yanzu baki gane ni ba Kubra? Ba mamaki, ai shekarun da yawa"

Shima Abunda ya faÉ—a kenan cike da jimami, lokaci guda kuma gaban shi na sake tsinkewa yana faÉ—uwa.

Ba wanda baiyi mamaki ba, masalan ma Dad da mai Martaba, ikon Allah, shin ko ina kuma Waziri ya san matar da kallon shi É—aya da ita ya kama sunan ta?

Ba tare da sake cewa komai ba, aka sa sarkin zagi yayi kiran jakadiyan.

Cikin gida aka sanya suka shiga da ita, yayin da suke ratsa farfajiyar gidan take bin ko ina da ido da kallo.

Har É—akin Mama Fulani, inda akayi masu iso suka shiga.

Tasha tarba ta ban mamaki, duk da cewa dama ansan da zuwan nata, É—aki guda aka ware mata a cikin sashen Mama Fulanin, inda aka cika mata gaba da kayan ciye ciye, ji take kaman ba ita ba, a yanda su Hajiya Sa'a suka bata labari ma, ai gani take yi kaman yafi hakan. To ina ita Maryamar take?

Tana cikin tunani ne Muryar Umman ta karaÉ—e É—akin da Sallama. Cikin mamaki ta É—ago tana kallon Umman da kuyangi ke biye da ita a baya, suna mai gyara mata zaman alkyabbar tata.

Umurni tayi masu da su basu wuri, zata gana da Uwargidan tata.

Sai da suka fice ne sannan Umman ta maida kallon ta kan Mom É—in, cikin salo irin na sarakai ta buÉ—e baki ta fara cewa "Barkanku da isowa, ya hanya? Fatan kun iso cikin aminci?"

Sakin baki Mom tayi tana kallon ta, anya Maryama ƴar aikin ta wadda ke durƙusa wa a gaban ta ce wannan yanzu zaune a bisa kujera a gabanta kaman yanda itama take? Anya ita ce cikin wannan daula da tsantsar sarauta wadda zata iya cewa bata taɓa ganin irin ta ba?

Saurin kumtsa ta kanta tayi, wanda Umman na lura da ita, murmusawa tayi, lokaci guda kuma ta shiga cewa "Lafiya Lau ya muka same ku?"

"Alhamdulillahi, muna cikin Salama"

Itama Umman tabbata amsa, tana mai Miƙewa ta shiga taka wa tana faɗin "Na barki lafiya, kici abinci ki huta zuwa anjima"

Bata jira komai ba, ta idasa ficewa. Mom ji take yi kaman tayi hauka, komai ya idasa dagule mata, wani irin baƙin ciki tare da tsantsar hassada ne ƙarara ke cin zuciyar ta, ga asara ga ci gaban Umma da ta gani, ita dama tun cen ta tsani wani ya fita, ta fi so kullum ta kasance ita ce sama a kowa, Shiyasa tun tana yarinya kafin ma tabar ƙasar zuwa karatu kowa ke shan wahalar ta, duk wanda yake ƙasa da ita baya taɓa hutawa indai tana ƙasar.

Ba yanda ta iya, ko abincin ma bata ci na wani kirki ba, bata jin idan zata iya daure ma zama gidan, ita fa tana jin idan dai har nan zasu kwana ita zata iya tafiya ta kyale su, tinda bata ga wani amfanin zuwan ba, to Amman saidai wani abu guda.

Wanene wannan wanda ya santa har haka. Lokaci guda, kallo guda ya kama suna ta harda na mahaifin ta? A garin da bata san kowa ba, bata ma taɓa tunanin zata zo shi ba?

Koma dai minene zata zuba idanu taga shin shi É—in wanene haka???

******


Na kira Layin shi sau kusan uku bai É—aga ba, hakan ce ta sanya na tsara text massage na tura mashi .

*_"Amincin Allah ya tabbata a gareka mijina, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina nan ina keearka, na ƙagara ka dawo inyi tozali da wannan kyakkyawr fuskar taka da kan ƙasa saka ni cikin kogin nishaɗi, na tanadar maka abubuwan da kafi so a Rayuwar ka, ina zaman jiranka habibi na, Allah ya dawo man dakai lafiya. Ina ƙaunar ka, Muah"_*

Ashe ban sani ba, wayar ma tana cikin mota ya manta da ita, wajen rawar jikin ganin Baba Alhaji, ko yanzu da suke zaune suna dudduba abubuwa sosai a laptop É—in barrister hankalin shi ya É—auku, yama manta shaf da wayar a babin rayuwar shi, ashe bayan kasuwancin da Mom É—in keyi, akwai wasu É“oyayyun kasuwanci da mahaifin nata yake yi, wanda bata bar shi ba, ta É—ora daga inda ya tsaya, kuma ba tare da sanin mijin nata ko Æ´aÆ´an nata ba.

Ganin hakan ne ya sanya ni É—an kwanciya ina mai lallasa waya ta, pictures É—in da muka É—auka, da na biki da aka tuttura mani nake kallo. Allah sarki Afnan da Hafsat, aseeya, Jiddo Raihana, Khadeeja. duk nayi kewar su, haka na fara binsu É—aya bayan É—aya ina kiran su.

Raihana ce ma ke shaida man wai an fara lectures, yaushe zan dawo? Nake sanar mata cewa zan tuntuɓi Yayan nawa idan ya dawo. Zaulaya ta suka shiga yi, wai har yanzu amarcn bai ƙare ba, ni kuma na maida masu da cewa yanzu ma aka fara. Munsha fira dasu sosai, inda na kira Jiddo da aseeya suma muka sha firar mu gwanin ban sha'awa. Afnan kuwa ɗana kira ta, Firar Sir Salim kawai take mani, inda ta haɗa ni da Aunt Feena harma da su Ayan da Nasreem muka gaisa sosai cikin sakin jiki da jin daɗi. Faɗa man take wai

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment