Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Hajiya Kaila, wanda suke cikin wani hali, tun lokacin da aka damƙo su aka gano da haɗin bakin Hajiya Sa'a itama aka je aka cafko ta.

Mai martaba ne ya cigaba da magana

"Nasan kowa ya san dalilin taruwarmu anan, saboda haka, ba amfanin sake maida hannun agogo baya, magana ce ta cikin gida, wanda ya zuwa yanzu mun gane ainahin me ke faruwa, kuma su wanene ke da laifi, dan haka ga Baba Alhaji Lauyer nan, zai sake mana bayanin ainahin dukiyar Muhammadu, da kuma ta ɗiyar shi Hauwa'u, sai kuma ta Ita kanta Gimbiya gata nan a zaune. Wanda kowa ya sani, waɗannan kuɗi su ne, Alhaji Nura ya cigaba da juyawa, har Allah yayi mashi cikawa, daga baya dukiya ta koma hannun Hajiya Kubra."

Gyaɗa kai kowa ke yi cikin gamsuwa, in ka ɗauke Hajiya Kubra, wadda har yanzu kanta yake sadde ƙasa.

Nan fa Baba Alhaji ya dinga bayanin komai dalla dalla, kuɗi ne zunzurutun, tare da takaddun maka makan filaye a Abuja, da kuma gidaje a Abuja, da kuma Katsina, haɗa wasu sauran garuruwan da suka haɗa da Kano da Kaduna, sai kuma Binin Sakoto, da kuma jihar Lagos. Sannan da zunzurutun shaguna maƙare da kaya, wanda zasu iya kai adadin shidda, a kasuwn wambai, kwari da kasuwar sabon gari. Sannan gwalagwalai da kuma zunzurutun kuɗi da zau iya kai kimanin million ɗari shidda, wanda a ciki ne Alhaji Yaro yayi nasarr damfarar ta kimanin kuɗi Million ɗari uku da talatin da uku. Sai kum shagon gyaran jiki, wanda ba da daɗewa ba Hajiya Kubran ta buɗe shi, shima dai duk cikin dukiyar su Suhan ɗin ne.

Idan Kaga Alhaji Yaro da Hajiya Laila da Hajiya Sa'a, wanda tun farko ashe ma ita ce ta kitsa yanda komai zai faru, Ita kanta Hajiya Kubran ta sha mamaki, wai ganin mutanen da ta yarda dasu, ta basu amana, da duk wani Sirrin ta, ashe makasar ta suke nema.

Kafin zuwan ranar zaman, saida masarauta ta sanya Alhaji yaro ya yi trnsfer na dukkanin kuɗaɗen dake cikin account nashi, wanda har ya shiga cikin su, ya fara ragargazar su,

Shi kanshi Dad da Alhaji Auwalu sun sha mamakin yawan adadin kuɗin, dole ne Hajiya Kubra ta ruɗe, kuɗin da tayi sama da shekaru ashirin da biyar tana tarawa, tana juyawa, rana tsaka azo ace ba nata bane.

Bayan kammala haɗa jimilla kuɗaɗe da dukiyoyi, mai martaba ne yayi gyaran murya, yana mai sake jaddada godiya ga Baba Alhaji, sannan ya sake sanarawar cewa Alhaji Yaro da Hajiya Sa'a da Hajiya Laila, sai Baba Wazirii, shi ba zai yanke hukunci ba, za'a shigar da magana babbar kotu, domin ta yanke duk hukuncin da ya dace a kansu.

Sannan ya sake cewa "Muna fatan masarauta bata shiga haƙƙin kowa ba, abunda ke nan, kotu ita zata sanar da duk yanda ake ciki. Ko akwai mai magana ne?"

Shiru ne ya biyo baya, yayin da kan Hajiya Kubra ke sadde, tana ta saƙa abubuwa a cikin zuciyar ta, Amman kai da ka kalle ta, kasan jikin ta yayi sanyi ƙlau, masalan da Umma ta sake jaddada cewa ko naira bata da muradin samu daga cikin wannan dukiyar, saura kuma abunda Suhan tace, saboda ba zata shiga haƙƙin ta ba, ta tauye ta wannan karon.

Kowa yagamsu matuƙa da hukuncin Umma, ta ƙara ƙima sosai a idanun Alhaji Mustapha da ma shi kanshi Alhaji Auwaln, har Baba Alhaji ya jinjina halin girma da dattakon da Umman take dashi.

"Idan babu mai magana, sai muyi addu'a, domin mu samu ku koma gida da wuri, kafin nan ni zan tattara komai, in miƙa ga hukuma, domin ta san abun yi." Cewar Mai martaba yana mai gyara zaman shi.

*"Ina da magana Ranka shi daɗe"* Cewar Hajiya Kubra.

Da sauri kowa ya ɗaga kai ya ɗora mata idanu, mamaki kowa ke yi, duk zaman da ake yi, bata cika magana ba, wannan izzar da take cikin jinin jikinta har yanzu tana nan, saidai ba kaman da ba.

"Muna jinki Hajiya Kubra" Cewar mai martaba

"Magana ce ta cikin gida, saboda haka nake so, dan Allah da a barta a cikin gida, ba sai an fidda ba, maganar dukiya, na amince zan ba Suhan dukiya ta, ni da ita duk ɗaya ne, ɗiya ta ce, suruka ta ce kuma, nayi nadamar dukkan abubuwan da na aikata, dama waɗannan (Ta Nuna su Hajiya Laila) suna daga cikin waɗanda suka ƙara tunzura ni, suna daga cikin waɗanda suka daɗa zuga ni, akan aiwatar da komai, na yafe ma Maryama, ina fatan itama ta yafe man, a shirye nake da muyi zaman lafiya, mu haɗa kan zuri'ar mu kuma, sannan na amince da Suhan a matsayin suruka, bana fata kuma a samu Abunda zai sake kawo saɓani a tsakanin mu, tunda waɗannan shaiɗanun zasu amsa hukuncin hukuma, sannan ina mai sake bada haƙuri, a madadin mahaifina da baya raye a wannan duniya, ya aikata kuskure sosai, ya aikata son zuciya, wanda ni ma kaina a bisa shi na ginu, kuma nake jin kaina na kai, nake jin babu wani in ba ni ba, nake jin ba wanda ya isa sai ni, ashe duk ba haka bane, son zuciya ne irin nawa, Alhaji ya sha faɗa, ya sha kwatanta mani, ba ma shi ba, har Al'ameen da yake yaro, ɗan ciki na, ya sha kwatanta man, Amman na kasa ji, na toshe kunne na, na runtse idanu na, huɗubar waɗannan matan na kai komo a cikin ƙwalwa ta, kun cuce ni Sa'a da Laila, sai Allah ya mana sakaya a tsakanin mu, ba ku ba, har Talatu ba zan yafe mata ba, ba kuma zan ƙyale ta ba, saboda a haka nayi nadamar abubuwa da yawa, ina fatan za'a yafe man, yanda xanji daɗin gyara kuskuren da na aikata a haya, Alhaji ka yafe man, Hajiya Maryama ki yafe mani dan Allah, ko dan Albarkacin zuri'ar da muka haɗa"

Ta ƙarshe a hankali, nadama fal a cikin maganar ta. Babu wanda jikin shi baiyi sanyi ba, hajiya kubra, duk izzar ta, duk cikar matsayin ta, duk ji da kanta, yau ita ce ke ambata nadama, tau ita ce ke cewa zata mayar da maƙudan kuɗaɗen da duk ta mallaka, take kuma juyawa ga mai su. Ikon Allah kenan.

Idanun Umma ne suka cika da ƙwalla, duk da haka murmushi ne fal a cikin ranta

"Na yafe maki Kubra, na yafe maki, insha Allahu itama Suhan zata yafe maki, ai ɗiya ce a gareki, kina da cikakken iko a kanta, Allah ya yafe mana baki ɗaya, sannan ina da wata magana, ina so dukkan Abunda mahaifin Suhan ya bari, a lissafa, a bata iya kwatankwacin abunda mahaifin nata ya bari, sauran kuma na Hajiya ne, wahalar ta ce, kuma gumun ta ne, zata cigaba da juya kuɗaɗen ta, da kuma dukkanin dukiyar ta."

Nan ma sai jikin kowa ya sake yin sanyi. Tabbas umma ƴar aljanna ce, mace ce har mace, ashe ma Hajiya Kubra tana tare da irin wannan matar mai ɗimbin daraja da sanin ya kamata a cikin gida? Ta kama wasu shashashai wanda babu abunda suka ajiye sai yaudara?

An taru an yayyafe ma juna, inda aka sake iza ƙyeyar su Hajiya Laila da Hajiya Sa'a da Alhaji yaro zuwa cell, inda shi kuma Baba Wazuri aka mayar dashi inda ake tsaron shi, kafin ranar zama kotu tayi, tunda maganar dukiya an riga an kammala ta, take ma Baba alhaji yayi lissafi, kuɗi iya million ɗari huɗu da sha biyu kuɗin Suhan suka kama.
A take kuma aka yi rubutu, sannan aka zuba kuɗaɗen a cikin account na daban, wanda yake da sunan gimbiya merama, kafin komai ya lafa asan yanda za'a yi dasu, ita kuma Hajiya Kubra aka bar mata sauran, da niyyar zata cigaba da juyawa, da tayi musu, tace a barta zata yi zaman aure kawai, tunda babu abunda Alhaji Mustapha ya rage ta dashi. Saida aka kai ruwa rana, kafin ta yarda ta amsa.

Ba wanda ya kai Alhaji mustapha jin daɗi, ya kuma yardar ma kanshi da cewa lallai Hajiya Kubran ta gyaru, ta gane kuskuren ta, ta kuma ɗauri ɗambar gyarawa.

Ana cikin haka ne, sai ga jakadiya, saƙo daga mama Fulani.

Sai da jakadiya ta gama zayyana saƙon Mama Fulani, cikin wani irin yaren da masarauta ce kawai ta sanshi, babu wanda ya iya fahimta sai Umman Suhan. Wanda take sakin murmushi a kai akai.

Ba'a ɗau lokaci ba, sai ga Mama Fulani, ƙarƙashin jagorancin jakadiyr, sun sake shigowa.

Sai da ta zauna ne, aka sake gaggaisawa, duk an zama ɗaya, sannan mai martaba ya sake gyara murya.

Wannan karon, har saida ya zame rawanin shi daga saman fuskar tashi, yana mai fuskantar su Alhaji Auwalu.

"Sai magana ta biyu, maganar neman auren ɗiyar wajen ku Afnan, ga yaron wajen mu Saleem, tun tuni ke akwai maganar, Amman ganin halin da ake ciki, sai muka ce a dakata, to yanzu dai munzo da ƙoƙon bara a karo na biyu, bayan mun nema a na farko bamu samu ba, yanzu kuma kanmu a ƙasa, muna fatan za'a duba ƙoƙon barar tamu, a taimaka mana da iri fisabilillahi"

Kaf Falon babu wanda baiyi dariya ba, mai martaba mutum ne mai barkwanci, ga Mama Fulani a zaune, wadda take matsayin Babbar uwar ango.

Ba ɓata lokaci aka amince masu, domin kuwa kowa ya yaba da Sir Saleem, yaron akwai tarbiyya tare da kawaici, ya so Suhan, Amman daga baya Allah yayi ashe Afnan ɗin ce matar shi.

Basu baro Adamawa ba, sai da aka tabbatar da cewa nan da wata shidda masu zuwa ne auren Afnan da Sir Saleem ɗin.

An rabu cikin mutun ta juna, tare da daraja juna. Ko a bayan mota, Hajiya Kubra ke ta jan Umma da Labari, saidai bata saki jiki ba sosai, gudun sake samun wata matsalar, sannan gashi ita bata san dalili ba, hakanan sai take jin gaban ta na tsananta faɗuwa sosai ma. Yaƙe kawai take yi, yayin da su kuma Alhazawan suke saƙe saƙe a zuciya, gashi basu sanar ma da kowa ba halin da Suhan ɗin ke ciki, gudun tashin lalurar Umman, wanda kowa ya sani, tana ɗauke da ciwon zuciya mai tsanani

************

Wata irin tafiya yayi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya isa garin na Abuja, Suhan kawai yake son gani, da ita kawai yake son arba, baya so ace wani abu mummuna ya same shi. Amman zuciyar shi, na raya mashi cewa, ba zai iya haƙurin zuwa gareta ba, har sai ya isa gidan ya kunna cctv idanun shi sun gane mashi dalilin faruwar hakan,zucjyar shi ma raya mashi akwai wnai abu a ƙasa, lallai akwai wani abu.

Jigum Jigum ya iske kowa, ko da yayi horn, ba wanda ma ya zaci shi ne, hankalin kowa ya sake tashi, ganin mai gidan nasu, ƙaramin alhaji afujajan. Ba wanda ya amsa ma gaisuwr da yake mashi. Kai tsaye sahen nasu ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya fara cin karo da busasshen jini.

Jinin matar tashi, jinin Suhan, babyn shi, ɗanɗan shi, gudan jinin shi.

Bai tsaya ba, har kai inda Al'amarin ya faru, ji yayi ƙafafun shi basa iya ɗaukar shi, ai a sukwane, ya zame wurin, yana mai sakin kukan da ya kasa dannewa. Ya ilahirrahman! SUHAN ɓari tayi, cikin shi ya zube, ya rasa ɗan shi tilo, da idanun dake tsiyayar ruwan hawaye yake bin sashen wajen da kallo. Yanzu nan ɗanɗan shi ne kwance ko? Har wurin ya daskare ya bushe, menene dalili? Me ya jawo hakan?

Ya jima a wajen, kafin ya iya tashi a hankali ya isa ga bedroom ɗin, ga gadon nan a yamutse alamun an kwana lafiya lau, ga sallaya a gefe, alamun har sallar asuba tayi,

A hankali ya kai zaune gefen gadon, yana mai ɗauko fillo ya rungume tsam a ƙirjin shi, yana mai shaƙar ƙamshin ta, abubuwa da dama yake tunawa. Tayaya zai fuskanci Suhan? A wanne hali take ciki? Meyasa basu ɗaga wayar shi idan ya kira?

Cikin hanzari ya miƙe, yana mai isa ga mini laptop ɗin da ya haɗa da cctv ɗin, wadda ke ajiye a ƴar corner ta ɗakin.

Stool ya ja zuwa gaban system ɗin, lokaci guda kuma yana mai kunna wa daga ranar da yake tunanin an saka masu ɓawon Ayaba.

Dafe baki yayi sosai, idanu a waje, kaman zasu faɗo, na farko dai Maree ce, sai na biyun, wanda aka ajiye mata ɓera, na jiya kenan, an lulluɓe fuska, Amman fa alama namiji ne, sannan ko ma wanenn ya san ta kan gidan, kuma ya san baya nan. Ya kasa gane ko wanene, dalilin da ya sanya ya kashe kenan, yana mai tashi a sukwane ya fice daga gidan.

Direct asibitin ya nufa, Allah ne kawai ya kaishi lafiya, tun a gidan yaso ya fara cin uban Maree, saidai ba wannan ne a gaban shi ba, halin da matar shi take ciki, shi ne farko.

Tun daga nesa suka hango shi, daga yanayin yanda aka shigo da gudun masifa, sun tabbatar ma kansu da cewa shi ne.

Saboda haka jikin Nihal ya sake ruɗewa da ɓari, tuni zazzaɓi ya lulluɓe ta, tun ma kafin ya ƙara sa wajen da suke.

Bai ko tsaya kula Bilal ɗin da ke mashi magana ba, ya nufi Office ɗin Dr ɗin. To me zai ce mashi ne? Bayan yana ta kiran shi, ya gaza ɗaga mashi wayar, balle ya sanar mashi da halin da ake ciki, ko ma wane ɓoyo yake yi, gashi ya iso da kanshi, gashi ya iso yaga Menene ke faruwa ne wai?, kuma ga dukkan alamu Suhan na cikin wani mawuyacin hali, duba da yanda ya gansu Jigum jigum

Jikin shi har kyarma yake yi, ɓari kawai yake yi, duk ya firgice ya ruɗe, Ya Allah! Me ke faruwa ne? A wanne yanayi Suhan ɗinshi take ciki ne?

Da ƙarfi ya sanya ƙafa ya tura ƙofar Office ɗin likitan, ta buɗe kuwa dukan ta.

Da sauri Dr ya miƙe, yana mai zame glass na idanon shi, tare da tattara takardun da yake rubuce rubuce a jikin su. Jin yanda aka banko mashi ƙofa, kaman ba hankali.

Ganin Al'ameen ne ya sanya shi zagayo wa da sauri, yana faɗin "Ranka shi daɗe barka da isowa, ya hanya?"

"Ina Suhan take? Ina Matata? Me ya samu Matata? Ina kuka kai man ita? Kada kuce man wani abu ya same ta, ba zan iya jurewa ba, kada ka faɗa man wani abu daban Dr. Ina Suhan?"

"Calm your Self Engr Al'ameen matar ka tana lafiya, ana ƙoƙarin ceto ta ne"

"Ceto ta like how? Since when take anan? Kun kasa ceto ta, kun san irin jinin da ta zubda kuwa? Tell me whare is she? I'll trnsfer her to another hospital, tinda ku kun gaza, gaya man ina take?"

Yana magana ne cikin tashin hankali da wani irin ƙaraji, Bilal dake bayan shi yana ta taɓo shi alamun ya yi shiru, ya kwantar da hankalin shi, Amman inaaa, baya ma ko sauraren shi. Su kuwa Nihal da Afnan kuka kawai suke yi, Umme ma ta yi kukan har ta yi shiru, ganin ƴan uwanta mata na yi.

A hankali Dr ɗin ya buɗe baki ya ce "A&E"

Ai bai jira Cewar komai ba, ya ɗaga ƙafafun shi cikin sauri ya nufi ɗakin, ko gani baya yi sosai.

Yana banka ƙofar Ward ɗin, idanun shi suka sauka kan wani Dr, dake tsaye, riƙe da wani ɗan abu kaman dutsin guga a hannun shi, yayin da yake ta girgiza kai, kwance take samɓal saman wani farin gado, an ɗaga gadon sosai, jikinta jojjone da wasu irin na'uri barkatai, an lulluɓe rabin jikin nata da fari da blue ɗin yadi mai kyau, komai nata a samɓal taje, kwance take, bata da jaraba da gawa, gabaki ɗaya fuskar an toshe ta da wata farar roba, zaka iya hango yanda tayi fayau, ta cikin fararen ƙwayayen da aka haske ta dasu, raka am. suma sauran likitocin kai suke girgiza wa, gami da salati

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ɗaya daga cikin su ne, ya sanya hannu, gami da jawo farin ƙyallen dake lulluɓe a rabin jikin nata ya idasa lulluɓe mata fuska, yayin da gefe guda, na'urar dake nuna bugawar zuciya, da numfashin mutum ta tsaya cak!

*"Kulli nafseen Za'iƙatul maut"* ɗaya daga cikin likitocin ya faɗa, yana mai zare face mask dake fuskar tashi, lokaci guda, da kuma farin gilashin dake manne a idanun nashi.

*"She's gobe"*

Abunda wani daga cikin Dr ɗin ke cewa kenan, yayin da wani daga cikin su ke cewa, "Anyi jinkirn kawo ta asibiti, gashi abun har ya ci tura, saidai haƙuri."

Iyakar kalmomn da suka samu nasarar shiga kunnen shi kenan.

Idanun shi ne suka firfito gabaki ɗaya zuwa waje, me suke nufi kada dai suce mashi Suhan ta mutu?

*"SUHAANNNNNNN"*

Ya furta da iya ƙarfin shi,

Yana ɗaga ƙafa da niyyar ci gaba zuwa cikin ɗakin, numfashin nashi yayi wani irin mugun ja, lokaci guda ya sulale zuwa ƙasa kawai. Bilal da Umme dake bayan shi, suka ruga zuwa gareshi, yayin da Nihal da Afnan suka jiyo ƙarar Umme ɗin ta na cewa *"TA MUTU BILAL"*




~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~84~*




*_Insha Allahu mun kusa ƙarƙarewa, ayi haƙuri dai dani. Har na gaji da bayar da uziri, Amman na san wasu daga cikin ku zasu iya fahimta ta. Nagode_*


************

Karo na biyu kenan da yana yunƙurawa, cikin sauke ajiyar zuciya, saidai har yanzu idanun shi a kukkule suke.

Sosai kan nashi ke juyawa, a hankali ya shiga buɗe bakin shi yana ambato sunan ta. Saidai ba kowa zai iya fahimtar halin da yake ciki ba, masalan da hankalin kowa yake matuƙar tashe, masu kuka na yi, masu share ƙwalla na yi.

*"Suhannnn"*


Ya furta da ƙarfi, cikin amon murya mai amsa kuwwa.

Lokaci guda kowa ya kai kallon shi inda yake kwance bisa gadon marasa lafiyar. Shi ma hancin shi liƙe da oxygen ta take ƙara taimaka mashi, gefe guda kuma ruwa ne, wanda aka saukar mashi shi da ƙarfi.

Yunƙurawa yayi da ƙarfi, yana mai sakko ƙafafn shi daga bisa gadon, lokaci guda kuma ya fizge ƙarin ruwan da kuma ƴar siririyar robar taimakon iskar.

Da sauri Dad ya sanya hannu ya dafe mashi kafaɗa, ganin ya miƙe tsaye yana neman faɗuwa. Har yanzu idanun nashi basu gama buɗewa ba.

"Calm down Son, Suhan na cikin ƙoshin lafiya" Dad ɗin ya faɗa, shima hankalin shi a matuƙar tashi.

Maida shi yayi ya zaunar dashi bisa gadon, yana mai tallafo dukkanin fuskar tashi, wanda har ta cenza kamanni daga ta Al'ameen ɗin da aka sani.

"Look at there Son, Suhan ɗin ka ce cikin ƙoshin lafiya, bacci take yi"

Dad ɗin ya sake faɗa, yana mai nuni da cen gefen su sosai, inda aka yi ma wajen shamaki da farin glass tar, saidai zaka iya hango dukkan abunda ke gudan ɗakin.

A hankali ya kai kallon nashi, inda Dad ɗin nashi ke nuna mashi, cikin son tabbatar da cewa ba mafarki yake ba, cikin son gasgata maganar Dad ɗin tashi, cikin son tabbatar ma kanshi cewa Suhan ɗinshi bata mutu ba.

A hankali ya shiga jinjina kai, sai kuma wata ƴar siririyar fara'a ta ƙwace mashi gami da bayyana a saman fuskar tashi

"Dad really Suhan ce? Dad tell me please bata mutu ba, Dady ka faɗa man, Suhan bata tafi ta barni ba" ya faɗa souded emotionally.

Gyaɗa mashi kai Dad ya shiga yi, yana mai shafo yaloluwar sumar kan tashi, wadda take a harmutse, kaman anyi dambe cikin ta, duk dai da cewa baƙa take siɗik mai ɗaukar ido.

Sai a lokacin yaji wasu irin siraran ruwan hawaye masu ɗumi sun taho mashi, bai damu da ya sanya hannu ya goge ba, ya shiga ƙoƙarin miƙewa. Ƙoƙarin dakatar dashi Dad yayi, ya sanya hannu ya dakatar da Dad ɗin, inda ya shiga takawa da sauri yana mai nufar glass ɗin.

Da dukkan hannuwan shi yayi amfani, wajen dafe glass ɗin, yana mai ƙura mata ido.

Kwance take sosai, komai nata a nutse, sauke numfashi take yi a hankali a hankali. Wannan karon babu komai a jikin ta, da ya danganci bata kariya. In ka ɗauke yaloluwar rigar ta da take ɗanye fa ita, ruwan bula mai cizawa.


Ajiyar zuciya ya sauke, mai haɗe da ƴar dariya, daidai lokacin da ya dafe glass ɗin da hannun shi ɗaya, yana mai goge ƙwallar da gudan hannun.

Ta bayan shi yaji an dafa shi, juyawar da zaiyi yayi arba da Mom. Hannun ta ɗauke da ƴar jikkar ta ƙarama, sai wayar ta dake tsuwwa alamun ana kiran ta, Amman sai ta sanya hannu ta kuma katse kiran.

Rungumo shi tayi sosai zuwa cikin jikin nata. Baisan lokacin da ya saukar mata murmushi ba sosai, yana mai faɗa wa jikin nata ba yana sakin dariya, kaman wani ɗan farko, itama dariyar take yi.

"Mom Suhan ta tashi, Mom ba zan iya rayuwa babu ita ba please"

"Is ok Son, ba zata tafi ta barmu ba, mu duka muna son ta, and am happy da naga ku duka kun samu sauƙi"

Ta mayar mashi da amsa cikin wata irin ƙauna. Hango Umma da yayi ta shigo hannun ta ɗauke da Food Basket ne ya sanya shi ɗan ja baya daga jikin mom ɗin.

"Alhamdulillahi, Muhammadu ashe jiki yayi sauƙi, dan Allah ka kwantar da hankalin ka, babu abunda zai same ta, Beside ma ai ta tashi fa, yanzun ma bacci take ɗan yi ne, zuwa wani lokaci zaka ga ta farka"

Ɗan duƙar da kai yayi ƙasa cikin jin kunya domin daga shi sai singlet da dogon wando a jikin shi,

"Eah Umma, Alhamdulillah na samu sauƙi, to umma Allah ya tashe ta cikin ƙoshin lafiya"

Ya faɗa shima cikin jin kunya, daidai lokacin da Dr ya shigo cikin sauri.

Ɗan turus yayi, ganin marar lafiyan nashi da iyayen nashi tsai tsaye tsakiyar ɗaki, yayin da shi kuma gogan yake cen dafe da glass, kaman zai tsaga shi ya shige, Dad ne kawai yake zaune bisa wata farar sofa da take ajiye gefen ɗakin.

"Ah ya dai yallaɓai? Ya akayi ka tashi kuma?"

Ya faɗa yana ɗan murmushi, bai ma ko kula ba, yana cen hankalin shi na kanta.

"Da sauƙi ne Dr. Ai ka san dama fargaba ce, gashi kuma ya sha hanya, hada gajiya" cewar Umma

Sai lokacin hankalin shi ya dawo jikin shi. Ɗan juyo wa yayi, yana mai kallon Dr ɗin, sai kuma ya ɗan saukar mashi murmushi.

"To ya jikin naka?" cewar Dr ɗin.

"Dr. Ta samu sauƙi ko? Ya jikin nata? Baby..." sai kuma ya an kare da Umma na wajen, kada yayi abun kunya.

Murmushi Dr ɗin ya saki, har Dad sai da ya murmusa, ita kuwa Umma saidai ta sauke kai ƙasa kawai, tana mai wuce wa ta nufi table ɗin da zata ajiye Basket ɗin.

"Ranka ya daɗe, ta samu sauƙi sosai, yanzu kai ne ma muke so muga ka samu sauƙi, tunda ita yanzu Alhamdulillah, mun mata allurar bacci ne, da zaran ta farka zata warware insha Allah" ya faɗa, yana mai ɗan kamo Al'ameen ɗin ya taimaka mashi ya zauna.

"Dont mind ne Dr. Am feeling beter now"


Sai da ya auna fulse nashi, sannan yayi mashi awon BP, komai dai normal, sai ɗan abunda ba'a rasa ba.

Ɗakin yayi tsit, in ka ɗauke Dr da ke ta faman bashi shawarwarin yanda zai sake kula da kanshi. Saboda akwai matsala indai yana irin wannan faɗuwar.

Ta gefen ido ya hango kaman

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment