Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsin ta. Zumbur yayi ya miƙe, yana mai dakatar da Dr daga sake jona mashi sauran ruwan nashi, wanda akayi ma allurai da zasu sake taimakawa wajen saukar da bugawar jinin nashi zuwa daidai.

Bai jira cewr komai ba, ya shiga tankawa zuwa ficewa, zagayawa yayi zuwa cikin ɗakin nata. Lallai kuwa, motsi take yi, tana mai ƙoƙarin buɗe idanun nata.

Dire guiwoyin nashi yayi zuwa ƙasa, yana mai tallafo hannuwan nata, wanda ta sake su, kaman zasu faɗo ƙasa. Rungume su yayi tsaf a ƙirjin nashi, yana mai shafo gaban goshin ta.

"Wife wake up please" yake faɗa a hankali.

Duk sai dai aka bishi da kallo, ko shi kanshi Dr ɗin saidai ya bishi da idanu, lokaci guda yana mai nisa wa, sannan ya miƙe, yana mai bin bayan Al'ameen ɗin, shi kanshi mamakin irin wannan ƙauna da ke tsakanin ma'auratan yake.




Sama sama take ƙoƙarin buɗe idanun. Ya ɗauke ta tsawon lokaci kafin ta iya cin nasarar fara ganin hasken duniyar tamu. Juyawa kanta yake yi a hankali, wasu irin siraran hawaye ne suka fara kwaranya daga gurbin idanun nata. Tuni gashin idanun nata ya jiƙe,

"Yaya! Yaya!!"

Take furta wa a hankali, wanda ba kowa ne zai iya fahimtar abunda take faɗa ba.

"Na'am Dear! Buɗe idanun ki please, gani nan kusa dake, Yayan ki ne, gani a kusa dake" ya furta, yana mai sake matsawa sosai, kaman zai haɗe jikin shi da nata.

"Ah Yallaɓai please ka ɗan dakata da yi mata magana, har sai ta dawo hayyacin ta, saboda bama so hankalin ta ya rabu"

Gyaɗa mashi kai Al'ameen ɗin ya shiga yi, kaman wani ƙaramin yaro, shi dai fata da burin shi, ace Suhan ɗin tashi ta tashi.

Shi kanshi Dr ɗin da mamaki yake kallon Al'ameen. Kaman Yariman matasan, ace yana irin wannan abu akan nace? Lallai ya sara ma mata, mata iyayen giji, matan iyayen gida, mata mahaɗin rayuwa, mata sinadarin rayuwar namiji.

Kanta ya rufu, yana mai tofa mata addu'oi sosai daga bakin shi. Cikin ikon Allah kuma sai juwar ta fara sakin ta. Damƙe hannun shi tayi sosai da ƙarfi

*"Innalillahi Yayaaa gashi nan Yayaaaa ka taimake ni"*

Ta furta da ƙarfi sosai.

Duk da basu iya jiyo abunda take faɗa daga ɗakin nata, saidai yanda suka ga Dr ɗin ya zabura zuwa kanta, sannan shi kuma Ya Ameen ɗin yana rirriƙe da kafaɗun ta yana mata magana, ya sanya su zabura su duka, in ka ɗauke Umma da ta samu gefen sofar ta zauna.

Daidai lokacin da Bilal ya shigo shi da Ummin shi ɗauke da warmers na abinci masu kyau, shi kuma hannun shi riƙe da flaks na ruwan lipton da ya sha kayan ƙamshi.

A tare suka ɗunguma zuwa bakin ƙofar ɗakin, inda su Nihal da Afnan suke jigum jigum, sun sha kuka har sun gaji, dan kowa a tsammann shi an rasa Suhan ɗin,saidai basu shiga ba, kaman yanda yake sanin kowa ba'a shiga ɗakin, saidai za'a iya hango komai ta waje. Shima Ya Ameen dokar ce ya karya.


*"Suhan gani nan tare da ke, babu komai ba abunda zai same ki, ina tare dake,"* ya furta a hankali daidai sai tin kunnen shi.

Allura Dr ya matsa, tare da soka mata, ko minti biyu bata yi ba, ta sake komawa baccin.

Sake durƙusawa yayi daf da kanta, yana mai shafo mata fuskar ta, yana mai sake tofa mata addu'oin. Sai ya ga tayi mashi kyau, tayi wani fayau da ita.

Zuciyar shi ce ke mashi saƙe saƙe, ingiza shi take yi akan abubuwa da dama, saidai yanzu ta lafiyar Suhan ɗin yake yi.

Miƙewa yayi da sauri, har yanzu idanun shi ma bisa kan ƴar kyakkyawar zagayayyar fuskar tata. Wanda gashin idanun nata suka jiƙe, sai suka sake miƙewa sosai, kaman zasu tsole idanu.

Hannun likitan ya ja zuwa gefe

"Dr Baby na! Pls ya condition nata yake please Dr, kada ka ɓoye man, ina tunanin ko zamu cenza mata asibiti ne? Zan fitar da ita Dr.."

"Is Ok ranka ya daɗe, both Baby and Momma are in well condition, no need of referring her to another hospital, we are trying our best, insha Allah daga yanzu da ta tashi shikenan, zama a iya sallamar ta, kawai tsorata ne da tayi sosai, saboda a bazata komai ya zo mata Shiyasa, sai dai zamu kafa mata dokoki masu nauyi, wanda Insha Allah idan ta bi su, zata haife abunda yake cikin ta lafiya, duk da a yanzu ma da kyar muka shawo kan lamarin, babu wanda yayi tunanin ma cikin bai fita ba. "

" Huh!!!"

Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, jin cewa Suhan na cikin ƙoshin lafiya, tare da cikin nata, Abunda bai taɓa tsammani ba, kuma ko yanzu baya tunanin idan zai iya ɗaga ma Maree da duk wanda yake da hannu wajen ganin ya salwantar masu da rayuka gida biyu da suke a matsayin su ne rayuwar tashi.

Bai tsaya sake saurarar likitan ba, ya zagaye shi, yana mai ficewa daga ɗakin.

Ko ta kan iyayen nashi dake tsaye bai bi ba, ya shige inda aka kwantar dashi, yana mai zarar rigar tashi, haɗi da makullin motar ya fice.

Ganin hakan da Bilal yayi, cikin azama ya bi bayan shi, inda Alhaji Auwalu da Alhaji mustapha saidai suka bi shi da kallo kawai, suna masu girgiza kai. Sam Al'ameen ɗin ya kasa sama ma kanshi natsuwa, dama sun san halin shi, akwai ruɗewa duk idan irin hakan ta faru.

Da sauri Mom ta ɗaga ƙafa zata bi bayan shi, tana mai faɗin *"Son.."*

Dakatar da ita Alhaji Auwalu yayi

"Ƙyale shi Hajiya, naga suna magana da likita, ƙila wani abu aka buƙata zai je ya kawo, kuma ga Bilal cen ya bishi, ku ƙyale shi, indai har hakan zai sanya ya samu natsuwa"

Ja tayi ta tsaya, saidai har yanzu zuciyar ta na raya mata cewa ba lafiya ce ta fidda shi ba, zullumin ta ɗaya, yaje ya aikata wani abu da ba daidai ba, masalan a yanda yake ba cikin hayyacin shi ba sosai, tunda ta san halin shi sarai, daga yanzu har lokacin da Suhan ɗin zata samu sauƙi, ba zai taɓa sama ma kanshi natsuwa, ita kam ta sare da wannan al'amari, irin son da yaron nata ke ma Suhan ya shallake tunanin ta tuni.





_Toh ko ina kuma su Ya Ameen aka nufa?_







~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Ya Allah muna neman tsari gare ka, daga dukkan wani abun ƙi, na fili da na ɓoye, ya Allah ka san halin da bayin ka suke ciki, kai mai taimako ne, kuma gareka kaɗai muke neman taimako, ya Allah ka yaye mana wannan annoba da ta addabi duniya baki ɗaya (Covid 19). Ya Allah wannan cuta da ke barazana gare mu, da dukkanin wani musulmi ya Allah ka yaye mana ita, Allah ka bamu ikon bauta maka kai kaɗai, ya Allah ka bamu ikon kiyaye dokokin ka, haƙiƙa wannan annoba ce, wanda a zahirn gaskiya take mana nuni da mu sake komawa ga Allah. Ya Ubangiji mun san mu masu laifi ne, masu saɓo ne, masu kuskure ne, sannan masu son zuciyar mu ne, ya Allah ka yafe mana, alfarmar annabi da Alƙur'ani, ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa kuma tsarkaka, ya Ubangiji domin son da kake yi ma Annabin mu, fiyayyen halitta baki ɗaya, ya ubangiji ka amshi tuban mu, ka yaye mana, ka fuwace ma dukkan wani musulmi na duniya baki ɗaya. Ameen*


*Page ~85~*


**************

Cikin sauri ya sha gaban motar shi da tashi motar, ya daɗe yana biye dashi, ganin kaman ma zagaye gari kawai yake ta faman yi, ya rasa wajen nufa takamaimai, sannan ga wani irin tuƙi na ganganci, kaman ma baya cikin hayyacin shi.


Cikin sauri ya ɓalle nufin motar ya fito

"Wai me kake yi haka ne Friend? Ya da hankalin ka, kana neman ka hallaka kanka? Wannan shine tunani? Kada fa ka manta yanzu haka Suhan tana cikin wani hali ne, kuma mu duka abun ya shafe mu, Meyasa kake ganganci da rayuwar ka har haka ne?"

Bilal ɗin ya faɗa, yana mai dafa murfin motar Al'ameen ɗin.

Bai ko kalli inda yake ba, har yanzu idanun shi a ƙulle suke, ya jingina kanshi da kujera.

" Friend please dont lose your mind please, muje gida muyi magana dan Allah! Komai zai daidaita"

Cikin azama ya ɓalle murfin motar tashi shima, yana mai fitowa a zuciye.

"Me tayi masu? Wane laifi ta aikata masu da suke neman rayuwar ta? Wanene wanda har zai shigo cikin gida na ya nemi illata man mata? Garin ya Bilal? In zuba ido kenan? Yanzu da Allah bai tsare ba, kana ganin da yanzu a cikin wane hali take? Bilal ka sani fa, an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, i cant take it any more Friend, ka ƙyale ni zan ɗauki mummunan mataki, shin bana fita haƙƙin su ne? Duk mugun nufin da suka nufe mu dashi a baya bai isa ba? Sun laƙa mana sharrin zina, sun kai Mom wajen boka, duk dan kada in aure ta, sun ja mana laba'i iri iri, duk na kauda kai, na share ne dan bana son wata fitina, ba wai dan bana iya & sukar mataki a kansu ba, ai na ɗauka sun hankalta ne sun gyara, laifin Mom ne, ita ce ta basu dama, da sanin ta suke komai Bilal, please kada ka hana ni, na roƙe ka"

Ya ƙarshe yana mai haɗe hannayen duka guda biyu waje guda, alamun roƙon Bilal ɗin yake. Lokaci guda kuma yana mai faɗawa jikin motar ya jingina bayan shi jikin motar, sai fidda zazzafan numfashi yake yi.

Shi Bilal ma saidai da idanu ya shiga binshi,yanda yake ɗaɗɗaga hannu, yana nuna baya da gaba, kaman zai tashi sama dan masifa. Ikon Allah! Al'ameen dambulan kenan! Al'ameen na da haƙuri da kauda kai, duk abubuwan dake faruwa ya sani, saidai ya zaiyi? Wata irin mahaifiyar ce Allah ya haɗa shi da ita, mai son kanta, mai son zuciyar ta, ta kuma ci sa'a Al'ameen ɗin mai biyayya ne, mai kauda kai ne, saidai ya tabbata wannan abu zai zo da sarƙaƙiya, baya so Al'ameen ya aikata ma mahaifiyar shi wani abu da ba daidai ba, duk kuwa da ita ta jawo ma kanta, duk kuwa da cewa da sanya hannun ta, saidai uwa ai uwa ce a ko ina ne.



Horn ɗin da yaji ana masu ne, alamun sun haɗa ƙaramin go slow ne ya sanya shi takawa da sauri ya nufi motar, yana mai janye ta gefe, ya sakar masu one way, domin kuwa har yanzu Al'ameen yana a jingine jikin tashi motar, ya haɗa dukkanin hannayen shi ya rungume, cike da Ƙunar zuciya.

Wasu da dama gefe kallon Al'ameen ɗin suke yi, yayin da wasu ma har suna ɗaga mashi hannu, alamun sun gane shi, saidai shi ko hankalta da su ma baiyi ba

Saida Bilal ya kulle tashi motar gefe, sannan ya dawo, yana mai cewa da Al'ameen ɗin ya shiga su tafi.

Aminta ce ake yi domin Allah, kowa da ƙaunar gudan a cikin ran shi, sannan basa da nufin juna da komai, suna martaba juna, tare da ɗaukar shawarar juna.

Ba musu ya zagaya a hankali yana mai shiga motar, saida Bilal ɗin ya ƙara Ƙarfin na'urar sanyaya motar, sannan ya tada motar suka hau hanya.


Kai tsaye Office suka nufa, waje tsaf ko ina, ga ma'aikata sai kai komo suke a cikin Company ɗin. (Dayake an koma aiki)

Saida ya ɗauko ruwan gora masu sanyi, sannan ya ɗauko cup cikin mug cove ta roba dake gefe mai kyau.

Miƙa ma Al'ameen ɗin yayi, wanda ya samu gefen sofa ya ƙame.

"Take it easy Friend, every thing will be solve very easily insha Allah"

Ɗaga gorar ruwan yayi ya ƙwanƙwala, sannan ya sauke yana mai maida numfashi.

So yake ya faɗa ma Bilal komai yayin da Bilal ɗin ma Abunda ke wakana yake son ji, tunda sun kwana biyu basu zauna ba.

Tiryan tiryan ya shiga faɗa ma Bilal ɗin komai. Jinjina kai ya shiga yi, shi kanshi kanshi ya kulle sosai, masu aiki da wannan mugunta? Kuma da sanin Mom da sanya hannun ta, akan iyalan ɗanta? Wace irin mata ce wannan?

"Friend kada ka ɗauki mataki cikin gaugawa, zaifi kyau a tuntuɓi Dad akan maganar nan, muji yanda zaice, kada muje mu aikata kuskure ko ba daidai ba"

"Is ok Bilal! Ya isa yanzu ni ban kai matsayin da zan yanke ma kaina hukunci ba? Matata ce fa? Ko ka manta ne? Ba zan jira cewr wani ba, cikin hukuncin abunda ya kamata in ɗauka, idan zaka goya man baya fine, idan kuma ba zaka goya man baya ba, you can remove your Self from my everything"

Ya kula har yanzu bai sauko ba, dole ya lallaɓa shi, dole ne ya mara mashi baya, saidai ba zai taɓa bari dokin zuciya ya sanya ya bar aminin nashi ya aikata abunda zaiyi danasani ba a gaba.

"Noo friend ba haka nake nufi ba, ka fahimce ni da kyau, ka isa, har ma kayi yawa, kasan ko kai wanene, kuma kasan matsayin ka ga al'umma, da kowa da kowa ma, ba gasu kaɗai ba, mu kanmu da muke tare dakai mun san muhimmancin ka, idanun kowa yanzu a kanka yake, sannan hidimar ta haɗa da hannun Mom a ciki, abun yana buƙatar a samu natsuwa sannan, kafin mu aiwatar da komai, yanzu ina so ka kwantar da hankalin ka, kada ma ka bari wani ya gane kasan komai, mu jira muga yanayin jikin Madam sannan, kuma insha Allah ƙarshen komai yazo, tunda ka riga ka fahimci masu yi maka zagon ƙasa, ai dama kasan ance makashin ka, yana tare da kai"

Sai yanzu ya ji sanyi ya fara ratsa shi, lallai amini na gari kaman Bilal abun alfahari ne ga kowa, samun kaman shi ba dai yanzu ba, sai an tona.

Saida ya lallaɓa shi, har zuciyar tashi ta ɗan yi sanyi, sannan ya sanya shi ya shiga toilet ɗin Office ɗin ya watsa ruwa yaji sanyi sosai. Sannan suka wuce kasuwa domin samo abunda xa'a buƙata a asibitin. Saidai fa har yanzu zuciyar shi ma shaida mashi indai yaga Bilal zai ja mashi lokaci ƙyale shi zaiyi ya aikata duk abinda yaga ya dace.



**************


Tulin kaya ne masu kyau ƴan uban su, komai yayi kyau masha Allah. Asiya ita ce gaba gaba wajen ɗaɗɗaga kayan tana mai hasaso Ƙawar tata cikin kayan, lalai kowa yayi imani sai yanzu ne Salim zaiyi aure, sai yanzu ne zai huta.

Easher ce da take gefen Asiya, suna ta kallon kaya tare, ta maida kallon ta kan Ammi dake gefe bisa sofa ita da Abban Sir Salim.

"Granny wannan kayan duka na Aunty na ne? Abbin mu yace aunty sabuwa zai kawo mana, wadda zata dinga mana wanka da dafa mana noodles" ta faɗa cikin murna, duk da take ƙarama Amman ranta fayau yake, dayake kullum sai Salim ya kira Afnan ya haɗa su a waya, suyi ta shirmen su.

Murmushi Ammin tayi mai kyau. Sannan tace; "Ƴar Auntyn ta kenan, nan kusa ba da daɗewa ba, ashe yaji zakiyi mani? Ai gara ku tafi cen, domin ni na gaji da cinye man abinci dama da ake ta faman yi, gashi ayi ta ƙwace man mai gida"

Duka dariya suka yi, hada Abban nasu, sannan suka cigaba da tattauna yanda abubuwa zasu kasance, tunda gobe ne ake sa ran zuwa kai kaya gidan su Afnan ɗin.

Salim dai na gefe, sai sosa kai yake ta faman yi, butsu butsu sai Asiya ta ɗago ta kalle shi, shi kuma sai ya maka mata harara irin ke banson gulmar nan.

Wannan Family suna cike da ƙaunar juna da zaman lafiya, abun gwanin ban sha'awa.

Sallama akayi da ƙarfi daga bakin ƙofa, lokaci guda ana ƙwanƙwasawa da ƙarfi.

Kafin kowa ya miƙe, Easher tayi zumbur ta miƙe ta nufi ƙofar domin buɗewa. Duk da haka Salim ɗin bai zauna ba ya nufi ƙofar shima.

Da gudu ta ƙarasa tana mai buɗewa take faɗin "Yeeh na riga ka Abbi" dariya yayi yana mai cewa "sai a baki ƙwai Amman na jakki"

Taɓe fuska tayi sosai, saboda ata fahimci me yake nufi, saboda haka ne tayi fushi ma kawai cikin wasa, tana mai juyawa ta koma cikin falon.

Malam Yahuza ne mai gadin gidan Sir, Salim ɗin.

Ko tsayawa su gaisa baiyi ba ya shiga faɗin

"Maigida kayi mani aikin gafara, ga uwar ɗaki na cen da yayyen ta, sunzo da wasu masu babbar mota, hada maza majiya ƙarfi, suna ta kwasar kaya suna zubawa a mota, nayi mata magana sai cewa sukayi idan ban masu shiru ba zasu buge ni har lahira, su mazan da tazo dasu fa kenan, Shiyasa na garzayo in faɗa maka, tun ɗazu nake kiran ka bata shiga ba.

Cikin mamaki da kaɗuwa Salim ɗin ke kallon Malam Yahuzan.

"Kana nufin Ma'u?"

"Eh ita ranka shi daɗe" shima ya bashi amsa.

Cikin sauri ya sallame shi, yana mai komawa ciki domin kwasar wayoyin shi, da makullan motar.

"Ina zaka?" Cewar Ammi

"Ammi kina jin fa abunda malam Yahuza yace, ma'u bata da hankali Ammi, ki barni inje in nuna masu kuskuren su, duk sai na sanya an kulle man su"

Girgiza kai Ammi ta shiga yi a hankali.

"Ban baka irin wannan tarbiyyar ba Salim, ka ƙyale su duk abunda zasu yi, idan ma sun lalata gidan ne, ai sai a cenza wani, Amman yanzu ai ba girman mu bane, aga kaje kana faɗa da mata akan kayan gida"

Ta faɗa cikin natsuwa da kamala.

Kallon shi ya maida kan Abban shi. Ko da alama bai ɗauka Ammi zata hana shi ba, duba da irin kayan manyan kuɗi da ke cikin gidan.

Jinjina mashi kai Abban nashi yayi, yana mai nuna mashi gamsuwa da maganar Ammin.

Zaune ya kai cikin Ƙunar zuciya, yana mai cire hular kanshi ya ajiye gefe, daf yake da sahale ma kanshi da masifar ma'u, ya gaji, ya gaji, ba zai iya ba, daga wannan sai wannan.

Ita ko Asiya tuni ta fara tattara kayan tana maida su cikin manyan akwatunan nasu. Dama ita da Ammi da Mama Fulani ne suka haɗu suka zaɓi kayan, sannan aka bada order nasu.

Har cikin ranta tana mai tausaya ma Afnan, gata mara hayaniya, Hasalima kaf rayuwar ta a Turai tayi ta, bata san wani abu wai shi kishiya ba, bata taso ta san menene kishi ba, balle har tayi zaman kishi da Ma'u masifaffa, ita ko tana addu'a Allah ya kawo sanadin da wannan gayyar ta ma'u da yayanta zata watse, bata jin ta su Easher ita ta sani har ga Allah Afnan zata iya riƙe masu su kaman nata ƴaƴan.


Duk da haka kasa zama yayi wajen, zuciyar shi na mashi suya, kwasar tarkacen shi yayi ya haye saman ɗakin Ammin. Bisa gadon ta ya kwanta, yana mai mirgina, zuciyar shi taf a cunkushe, da Ammi zata bari ba zai kwanta ba yau da sauran igiyar auren Ma'u a hannun shi, waya ya zaro gaki da danna ma Afnan kira, ko da hakan zai sanya yaji sanyi.


Suma da wani irin kallon tausayawa suka bishi, lallai Salim na ganin Jarabawa, ai mata irin Ma'u babu abunda ke cikin aurenta sai masifa, ya ma yi ƙoƙari, da ƙarancin shekarun shi ace yana samun irin waɗannan matsaltsalun.

Saidai suka bishi da addu'a. Yayin da Abban ya tashi yana mai ficewa zuwa fada domin tsara yanda za'a yi tafiyar gobe kai kayan auren Salim ɗin.


*********


Da hannu ya dakatar da ita ga ƙoƙarin amsar kayan hannun nashi.

Zagaye ta yayi ya wuce, har yanzu babu wata walwala tattare dashi.

Cikin kasala da tsoro mai haɗe da fargaba ta bishi da kallo tayaya zata gamsar dashi babu hannun ta cikin al'amari?

Kallon ta ta kai kan Afnan da take cen gefe, wayar ta take hankalin ta kwance, ko ba komai dama tasan Ya Ameen ba zaifi fushi da Lil ɗinshi ba. Itama kurar ta ce tayi kuka, da ta riga ta bari ya san cewa ta tsani Suhan ɗin a baya, duk da yanzu ba wannan a cikin ranta, saidai ita kanta ta sani da kanta ta ɗaure akuyar ta a rana a wajen shi.


Zaune suka tadda ta, an cire mata komai na taimakon asibiti, saidai hannun ta da yake sanye da canula har yanzu. Tayi fayau da ita, tayi wani irin haske sosai, duk ta cenza, har ta faɗa sosai, sai wani irin hanci da ya fito sosai, gashin kanta duk ya kwakkwanto gefen fuskar ta, kaman an shafa mashi gel.

Hafsat na daga tsaye tana jijjiga Babyn ta, yayin da Mom ke zaune bisa wata kujera matsakaiciya ta flastic, hannun ta na riƙe da wani bowl ɗan fari tana ba Suhan ɗin Shake.

Kasa amsa take yi, sai Hafsat ɗin ta ɗanyi mata magana. Kunyar Mom ce duk ta cika ta, tana ganin ikon Allah. Tun da ta buɗe idanun ta take ganin Mom ɗin, har kawo yanzu ta kasa tafiya, ta gaza gane wannan al'amari.

Dad da Umma basa nan, tun dai da suka ga ta farfaɗo, sai umma tace ba zata zauna ba, tunda ga Mom nan, ita zata wuce gida ne, tunda ba daɗewa suka samu saƙon waya daga fada cewa gobe ƴan kawo kayan aure zasu iso. Shine tace gara ta wuce taje ta fara shisshirya wani abu, ita da Hajiya Zainab.

Bilal ne ya iya gaida mom da mai jiki, yayin da shi kuwa gogan ya wuce kai tsaye zuwa inda matar tashi take.

Saida ya dire ledojin dake hannun shi kafin ya kai zaune gefen gadon, yana mai haske ta da murmushi. Itama. Cikin ƙarfin hali ta mayar mashi, har yanzu sai a hankali, daurewa kawai take yi.

Ta mashi kyau ainun, dalili da ya sanya ya kamo hannun nata guda kenan da ke sanye da canula ya shiga murza mata a hankali, jin kaman wajen ya ɗan kumbura.

Ganin haka ne Hafsat ta shiga gaishe shi, ɗan juyawa yayi a hankali yana amsawa,fami da tambayar ta Khairi, Hankalin shi kaf yana kan Suhan ɗin, ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin ta tashi.

"Son Kaga ai jiki yayi kyau Alhamdulillah! Dr yace zuwa anjima zai yi discharge namu" ɗan ɗaga mata yayi da kai a hankali, bai kalli ko inda take ba,gani yake hidimar mom ɗin kaman akwai yaudara ciki

Maimakon ya bata amsa, sai ya maida hankalin shi kan Suhan ɗin

"Janam ina ke maki ciwo yanzu?"

Girgiza kai tayi a hankali, alamun dasauƙi

"Kina son wani abu ne yanzu?"

Ɗan shiru tayi, sai kuma ta gyaɗa kai a hankali.

"Tell me Habibty, yanzu zan kawo maki"

"Alale" ta furta ciki ciki. Babu wanda ya iya fahimta, hakan ya sanya shi zakuɗawa sosai, har jikin su na gugar na juna.

"Alale mai yaji Yaya"

Ta sake furtawa.

Kallon kallo suka shiga yi, ido cikin ido, Ikon Allah! kenan.. Yau Suhan ce da cewa tana son tuwo

Da hanzari ya tashi zai fice, duk fa ya bi ya ruɗe, cikin su babu wanda yayi tunanin so zai iya zauta Al'ameen haka. Ashe shiru shiru irin su haka suke soyayya a makance?

Da hanzari Bilal ya sha gaban shi.

"Bari inje Umme ta sama mata yanzu, ka zauna ka huta, yanzu zan dawo"

Gyaɗa mashi kai yayi, yana mai ɗan sanya hannu ya bugi gefen kafaɗar shi, alamu da ke nuna cewa ya burge shi kenan, duk lokacin da yayi mashi hakan.


Inda ya tashi ya sake komawa ya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment