Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani team mai kauri sosai nasha, Sallama aka rubuta mana, haka muka baro asibitin, tare da Jaddada ma Dr da Ya Ameen yayi akan zai koma su ga juna.


Mom kau kaman tayi tsuntsuwa ta taho, har video call take kira a bata, sai gashi an shantake a masarauta. Ganin haka Umma tace a tattara ni a maida ni ɗaki na, suruka ta tana yin kara, gashi tana son ganin baby, amman Dad ya hana ta tahowa, kuma duk ƴan kankiya na cen suna jiran mu, shi kanshi Ya Ameen yayi murna, kafin mu taho saida Salim ya kawo Afnan taga baby dani, santi ta dinga yi, tana kama ƙafar babyn tana mata wasa, yarinya idanun ta tar take kallon kowa, ga hancin har baka ga dimple irin na Ya Ameen ko ya ta motsa sai ya lotsa, sannan ga na gemu, ni kaina cikin dare sai in tashi in ta kallon ta, idan naga kowa yayi bacci, masalan idan ina bata nono, wai yau ni ce ke da ɗiya tare da Ya Ameen, wanda ada nake ta tunanin cewa *Ya Fi Ƙarfi Na* wani shauƙin son miji na ke kama ni, masalan ma da yarinyar ta biyo shi sak, hadda kwantacciyar Sumar kan tashin.


Duk a tunanin shi Sashe na za'a wuce dani, ya ƙagara ya keɓe ni da ɗiyar ya nuna mana zallar ƙauna, da yanda yayi missing ɗina, saidai saɓanin haka, sashen Mom yaga an wuce dani kai tsaye, duka ni da ɗiyar Mom ta rungume, bamu san ya akayi ba, sai gani mukayi tana hawaye, "Ashe da na mutu? Rabon wanann yarinyar sai ta taka duniya, ashe da rabon ta ya kashe ni, ki yafe man Suhan, ki yafe man dan Allah" abunda ta dinga faɗa kenan, har ta fara karya man guiwa nima na fara ƙwalla. Ya Ameen ficewa yayi zuwa namu sashen, duk baiji daɗi ba. Dayake tare da Nihal da Saudat muka taho wanda naga duk ta cenza, sai ta dinga ɗaukar baby tana mata wasa, tare da man wasu ƴan aikace aikacen cikin jin kunya. Suma gida suka wuce, da niyyar washe gari zasu dawo. A ranar sai ga Ummin Bilal, da shi kanshi Bilal ɗin, kai naga jama'a, naga mutane, ashe haka Ya Ameen ke da mutane? Ƴan kankiya ma duk suna nan suna jiran mu dama. Nan fa gida ya ɗin ke, duk inda ka yi labarin kyau da girman baby ake yi, lallai soyayyar Ya Ameen a cikin zukatan ƴan Family ɗin ce ta shafe ni, ni da ɗiya ta, kowa so take insan da ita, kai har maza ma, kowacce so take ta ƙulla alaƙa dani, to nima ina sonsu

Kafin kwana uku sai gamu munyi shar, umma na Adamawa cen muka baro ta, Mai martaba ne yace ta tsaya yana son ganin ta, fna haka babu abunda nuka nema muka rasa. Hatta da kaka zuwaira, kullum sai ta digaro ta zo ta ganmu, ko ƙuda kuwa bata bari ya taɓa babyn.

Kayan barka naji da gani Mom ta haɗo mana ni da baby, Ya Ameen ma ya kawo nashi, wanda zuwabyayi ya zauna dirshan su Nihal suka dinga zaɓar man suna tuntsura dariya, masalan idan yace kada a kashe shi fa, ganin irin expences ɗin kayan da suke ɗaukar man da baby, sai ga Bilal shima da wasu akwatuna, yarinya tayi goshi, ga wayau sosai, wani lokaci saboda ɗauka har cuwon jiki take yi. Saidai Nihal ta goya ta bayan an mata wanka, dayake kullum suna zuwa, yanzu har mamakin Saudat nake ta zama wata cool, magana ma a tausashe take yi man ita.

Ya Ameen yana cen yana jin haushi, Mom ko sakewa bata bari yayi, da ya ɗauki Baby zatace dalla ajiye ta ka futa mara kunya mara ta ido, kawai, dole sum-sum yake yi ya fita. kafin suna naga mutane kala kala, tabbas na yarda cewa jama'a Allah ne ke ba mutane su.



Alhamdulillah zan iya cewa yanzu bana da wata matsala gaskiya, Mom ta zame man Umma number 2, ban ɗauka tuban nata na gaske bane, sai gashi, yanda take so na da ririta ni, ko su Nihal bata ma haka. Aunty Feena ma bata koma ba, duk muna sashen Mom tare dasu.

Ranar suna kwatsam muka ji Sunan ɗiya *Maryam* duk munyi mamaki, ni na ɗauka ma Sunan Mom za'a saka, ashe Mom ce ta tubure lallai sai sunan Umman, tace ita ta yafe, gaba a saka nata.

Munyi kyau mun gaji da haɗuwa, abun mamaki ƙauye Ya Ameen yaje ya kwaso su Hajjo da malam, dasu aka sha suna, daga nan zasu wuce cen Adamawa wajen Mom anan ne muka ji irin abun Alkhairin da Ya Ameen yayi masu. Hada ni wajen yi mashi godiya, saidai ya rufe man baki kawai da nashi, da sauri na matsa, a ɗakin Mom nake, kuma ga ƴan suna suna shigowa akai akai, na kula Ya Ameen duk ya cenza, yanzu jin kan shi yake Daddy, komai na yi sai yace "Yanzu fa ni Dady ne Mummyn Umma"

Haka taro ya watse, kowa ya hakarta, Ranar Sunan Umma ta dawo, ansha suna an gama lafiya, ni kaina ba zan iya cewa ga abun alkhairin da na samu ba, da wanda Baby ta samu, Mom ce tace a buɗe mata Account a sai mata hannun jari, haka kuwa akayi, sai gashi bayan suna muna ta baccin dole da na gajiya.



Gida ya gama watsewa, kowa ya kama gaban shi, daga mu sai halin mu, anan ne fa Ya Ameen ya kulle ido, shi lallai saidai a mayar mashi da matar shi, Mom zata hana Dad ya ce akan me? A maida mashi ni cen mu ƙarata, yanzu haka ginin gida na inda zamu koma mu tare yayi nisa, nan dai cikin layin ne, saidai cen ƙarshen layin ne. Naji daɗi, ba wai dan bana son zama da iyaye na bane, saidai gaskiya akwai takura, baka sakewa ka nuna ma mijin ka ƙauna a ko'ina idan ba kai kaɗai bane a gidan.


Ina da sati biyu aka maida ni sashen nawa, naga zallar ƙauna, ko ina an bibbishi shi da teddys da kayan wasan yara, kama daga su flowers da sauran su, ikon Allah, abu fa ya zo ga ma'iya, kukan aure da sallallami. Yarinyar da dududu 2wks har an fara mata kwashe kwashe.



Zama ne muke cikin so da ƙaunar juna, mukan kwashe awa uku da ya Ameen cikin gidan nan yana ma yarinya wasa, tun bata fahimta, har ta fara fahimta, kullum cikin mata hotuna yake yana sanyawa a status da dp, IG da FB. Nan za'a yi ta liking ana mashi comment, kowa yaba kyaun ɗiyar yake, da wayon ta, da tsabar kamannin ta da mahaifin ta.


Hankali na ya kwanta, har ƙiba ta na narka, in ba Feeding na Baby nake yi ba, to indai yana gidan za kaga yana ɗauke da ita, ko aiki yake latsa system ma da yake yi da ita a saɓe a kafaɗar shi, na rasa inda ya koyi reno, da nayi magana sai yace wai nima haka yayi man, har fitsari da kasho ya wanke man, kunya ce ke kama ni, saidai na shige kitchen ko ma share shi ina dariya.

Har goyo Ya Ameen ya iya, sai ya goye ta tsaf, yarinya har ta saba dashi, da ta ganshi zakaga tana ɓangala dariya. Wata ranabkuma idan baya nan, yini take cikin gida wajen Mom, sai idan ta buƙaci nono ne ake dawo da ita.



Ayyukan shi suna tafiya successfully, akwai albarkar iyaye a kanshi, masalan ma yanzu da Mom ta gane cewa Addu'ar iyaye akan yaran su kaman yankan wuƙa ne, sai gashi Mom na zama Umma na koya mata karatu sosai, suna shiga sashen juna, ko Hajiya Zainab ta ji daɗin hakan, balle da ta sake tara su ta sake yi masu faɗa, yanzu duk inda zasuje zaka gansu a tare, Umma ta ɗauki Ya Ameen kaman Ni, haka Mom ta ɗauke ni kaman Ya Ameen,kusan ma zan iya cewa, duk ƙaunar da take mashi rabi da kwata kan ni da ɗiya ta ya dawo, wanda muke mata laƙabi da *Janaa*

Dole aka tarkata Abie da Bilal suka koma cen American, dan Ya Ameen yace shi ba inda zashi, indai ta kama yaje ya dawo zaije, wannan karon Bilal da Ummen shi suka tafi, da Lil Ameen, nayi kewar su sosai, saboda akai akai ya kan kawo su, ko ni Ya Ameen ya kaini. Wannan shine sirrin nasarar Ya Ameen. Ga komai nashi sai ƙara haɓɓaka yake yi. Abunda ya bamu ɗinbin mamaki shine; yaran da suka yi niyyar raping ɗina a sunkui, ashe wai Ya Ameen ya koma ya neme su, kuma dukkan su ya basu aiki watau ya gina gidan ruwa a nan sunkui ɗin ya basu halak malak suna juyawa da fiddama malam kason shi duk wata, duk bamu sani ba, har saida suka shigo mota suka zo har gida suna mai bani haƙuri, tare da ce man wallahi sun shiryu, dama dai hada ƙari da rashin aikin yi.



Ana cikin haka ne, maganar murabus na mai martaba ya taso, ba yanda ba'ayi dashi ba, yace shi fa lallai yayi alƙawari cewa sai ya maida ma gimbiya Merama karagar ta, duk ranar da ta bayyana. Umma kuka ta dinga yi tana bashi haƙuri, a cewar ta babu abunda zatayi da ita, zaman ta gidan mijin ta shi ne kan gaba akan komai, ba wata sarauta ba a halin yanzu. Kafewa yayi Allan baram fa sai ya sauka, dan haka ne ma aka neme su cen masarautar. Umma Dady da Mom sai ya Ameen, sune wanda suka ɗunguma zuwa Adamawar domun suji yanda komai zai kasance.....








~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._




_The End_



*Kyautar Page ga ɗaukacin ƴan ƙungiyar golden pen writers association, tare da ƴan banfi ƙarfin ta ba Fans Group, Allah ya bar zumunci da ƙauna*




*Page ~92~*





*Happy Ramadan Kareem*






*******************


Dayake gudu yake ta faman shararawa, sai gasu nan da nan sun isa ba ɓata lokaci. Sun tadda masarauta duk ana ta hada hada, ga gyare gyare sosai ana ta faman yi, duk da sunyi mamaki, haka aka sake masu jagora, kai tsaye akayi masu iso wajen mai martaba, to ƴan gida ne ison me suke jira ayi masu, ga maroƙa sosai suna ta yi masu busa, tare da kirari.

Ba ɓata lokaci mai martaba ya sanya duk aka tara hakimman shi, kaman sun san da maganar, sai gasu, duk wanda ya shigo sai yayi ma su Umma jinjinar ban girma kafin ya zauna.


Zuwa kaman minti goma, sai ga Mai martaba ya bayyana, cike da kwarjini ya shiga murmusawa ga manyan baƙin nashi, gefe guda kuma ƴaƴan shi, gasu kuma surukkan shi.


Bayan an gyara mashi ya zauna ne, sannan aka buɗe taro da addu'a, kowa ya natsu yaji bayani daga bakin Babban sarki mai adalci.


Gyaran murya yayi, yana mai bin fuskar kowa da kallo, ciki kuwa hada Ya Ameen da yayi wani irin durƙuso cikin girmamawa, ya sadda kanshi ƙasa, dayake yana zaune ne daga gefen mai martabar, dama haka ya saba mashi, duk indai zai zauna fada, to fa haka yake jawo shi kusa dashi sosai, natsuwa kyawon hali da ɗabi'ar yaron ke burge shi.


"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu, ba tare da ɓata lokaci ba, kowa dai ya san dalilin tara mu anan da nayi, ba tare da wani dogon jawabi ba, inaso ku sani, tabbas zan cika alƙawarin da na ɗauka, dangane da mayar da karagar mulkin ƙasar nan ga hannun mai ita, kowa ya sani cewa, ba wai dan na gaji sarauta bane ya saka aka bani, a'a saidai dan babu wani makusanci da ya kamata ace an ba, tun bayan rasuwar muhammadu, da ita kanta gimbiyar, watau Merama Hasken masarauta. To kaman yanda dai kuke gani, nan ita ce, kuma kowa ya sani cewa, ta bayyana ne a tattare da ita, akwai aure mai girma a kanta, aure wanda ya tabbatar da wanzuwar farin ciki a kan fuskar mu, haka kuma Allah yayi kata zaɓi kafi alkhairi a tare da ita. Haƙiƙa muna mai miƙa godiyar mu ga Allah subhanahu wata'ala, da kuma shi kanshi Alhaji Almustapha Dambulan, wanda ya kasance ba baƙo ba ne ga ɗaukacin mutanen da ke rayuwa a ƙasar nan, alkhairi shi ya iske kowa har inda yake, haka kuma yayi dace da yaro nutsattse, kuma ɗan halak, wanda hakan ne ya sanya muka shawarta bashi sarautan *Yariman Matasan Arewa* cencentar shi ce ta sanya haka, wanda tun bamu san ma zai iya zama ɗaya daga cikin mu ba. Ba tare da ɓata lokaci ba, ina mai sanar da murabus ɗina daga kan wannan karaga, daga rana mai irin ta yau, na miƙa sarauta ga Hannun mai ita, ina fatan zata amsa da hannu bibbiyu, ba tare da ta yi man gaddama ba, a bisa umurnin da muka bata"

Ya ƙarashe fuskar shi yalwace da fara'a, yana mai bin kowa da idanu, ganin yanda zasu amshi batun. Ga mamakin su Ya Ameen, sai ya ga kowa ya yalwata fuskar shi da murmushi, suna mai gyaɗa kansu, alamun amincewa.

Busa aka saki gabaki ɗaya gidan ya amsa, lokaci guda kuma duk wani haɗimi dake cikin gidan, tare da barori, suka durƙusa kansu a ƙasa, alamun yin mubaya'a, su kansu Hakimman ba'a barsu a baya ba, hakan ce ta kasance a fada.

Da kallo duk su Ya Ameen ke binsu, lallai sarauta ma saidai a barta.

Take wasu kuyangi suka shigo tare da jakadiya, hannayen su ɗauke da wasu manyan turay, cike da kayan alatu da ƙawa.

Nan da nan aka zagaye Umma, wanda take zaune gefe naɗe da ƙafa, ita kanta fuskar ta ba yabo ba fallasa. Alkyabbu da kayan ƙawa da alatu aka naɗa mata, lokaci guda kuma fadawa na ɗaukar kirari, tare da take mata baya har zuwa gaban mai Martaba ta zuƙunna ya saka mata albarka ta hanyar dafa kanta, sannan ya muƙe a hankali, yana mai ɗaukar wata ƴar wuƙa cikin kuben ta, wanda wasu haɗiman ke riƙe da wani farin tray ƙarami mai kyau.

Jinjina wannan wuƙar yanka yayi, lokaci guda yana mai miƙa ma Umma ita. Amsa tayi cike da girmamawa, tare da ɗan duƙawa, wata busar aka sake saki, tare da kirari daga sarkin zagi, nan da nan kowa dake gidan suka sake russunawa sosai, suna masu mubaya'a.


A hankali ya shiga matsawa, yana mai nuna ma Umma kujerar sarautar domin ta zauna. Saida kowa ya miƙe domin nuna girmamawa. Zama tayi a hankaki cikin natsuwa, shi dai ya Ameen sai kallon ta yake yi, cikin murmushi sosai, abun ya burge shi sosai, kaman a film, ikon Allah kenan, wai *Maryama mai aiki ce ta koma sarauniya ayau*


Har saida Umma ta daidaita zaman ta bisa karaga, sannan kowa dake fadar ya zauna, ciki kuwa hada mai gidan nata Alhaji Mustapha Dambulan, da ya nuna goyon bayan shi a gareta, fuskar shi cike da annuri, yana mai alfahari da samun Umman a matsayin mata.sannan haka ma Mom wadda ta zama ƴar kallo a wajen.



Wata irin busa aka sake saki, tare da goga goge da busar sarewa mai daɗi, sai kuma masu bindigu suka ɗauka, ji kake daram, daram, sai kuma masu busar ƙahunna suma suka ɗauka "Buuuuu" Masu algaita ma suka ɗauka, gidan fa ya hautsine, kowa ka gani farinciki yake da murna. Da sannu aka dinga shiga ana kwasar gaisuwa ga Umman, wanda har yanzu fuskar sake take ga na ƙasan nata.

Hatta da Su mama fulani da Ammi saida suka shiga suka kwashi gaisuwa, tare da nuna mubaya'a a gareta.



Dama saida suka shirya komai kafin zuwan su Umman, yanzu dai karaga ta zama ta Umma, komai sai yanda tayi. Ba'a yi jinkirin komai ba, aka sake shirya wata liyafar, sarakuna da suka dinga halarta da ɗai ɗaya da ɗai ɗaya, live ake ɗaukar komai, Suhan da kowa da kowa dake babban falo gidan nasu hatta da masu aiki an basu izinin shiga, yanzu Mom nada kyakkyawar alaƙa da kowa da kowa, saboda haka ne ta kira, tare da umurnin kowa cewa yaje ya kalla. Suhan kukan murna da farinciki take yi, ina ma ace tana wajen? Ina ma ace gaban ta ake yin komai? Kowa na gidan murna yake yi, sun san cewa Allah ya kaisu inda basu taɓa tsammani ba.


Anci an sha, an wadata, kowa na ta murna da farinciki, ranar har ƴan sansanin gudun hijira mutanen Ya Ameen saida suka shaida, nan take Ya Ameen ya bada gudunmuwar shi zuwa ga masarauta, tare da bada kuɗi masu tsoka ga sansanin.

Abun da ya fi ɗaure ma kowa kai shine, bayan an kammala duk abunda za'a yi, kowa na shirin tafiya ne, Ummar ta buɗe baki gami da tsaida kowa. Sanarwar maida sarauta ga hannun mai gidan nata ta bayar, wanda ya ba kowa mamaki sosai, nan fa wuri ya sake kaurewa, tabbas Alhaji Almustapha ba ɓoyayye bane, zasu so kuma ace ya mulke su, adalcin da yake nunawa akan ma'aikatan shi, zasj so ace ya kwatanta shi a kansu.

Kuka Mom ta dinga yi, lallai ta so ta tafka kuskure, sosai abunda tayi yake bata kunya, ta ɗauka kuɗi sune sai yanzu ta gane sarauta ma wani abu ce, ko baka da ko sisi dole ayi maka biyayya. Alhaji Mustapha ƙin amsa yai. A gaban kowa, nan fa aka fara bashi baki, ana nuna mashi alfanun hakan, dama girman masarauta kaman wannan bai kamata ace an barta a hannun mace ba, da Muhammadu na raye, tabbas ba abunda zai hana shi sarauta, amman dayake yanzu baya raye, Alhaji Mustapha ɗin dai shine daidai wanda ya kamata ya amsa, dama shi abunda ya hana shi amsa, sarauta na da tarin matsatsi da ƙalubale, yanda yake babban ɗan kasuwa, da siyasa yana ɗan taɓawa, ai zata zo mashi da wahala. Saidai ba yanda ya iya, haka aka sake yin naɗi wa Alhaji Almustapha, tare da naɗa Ya Ameen Yarima mai jiran gado, a matsayin shi na mai auren Suhan ɗin, ɗiya ga Ginbiya Meramar.

Kuka sai ya ƙaru ga Suhan, yayin da wasu ke murna, kiran wasu ta ko'ina Alhaji Almustapha ɗin ya sha shi, nan aka gama daddale komai, tare da tabbatar da cewa dole gimbiya Merama zata koma cen da zama, yayin da Mom zata koma abujan, duk da ita ma tana da sashen ta anan gidan, ba nan zata dinga zama ba dindindin, saidai tazo. Cen baya aka gyara ma tsohon mai martaba ya koma da iyalan sa. Suma su Ya Ameen suna da Sashe, dayake gidan babban gida ne. Sai gashi har shugaban ƙasa da kanshi yazo ya kawo ma Alhaji Mustapha ɗin ziyara, tare da ba masarauta wani sabon grant, domin yanzu ta koma kaman sabuwa ne.


Kwanan su Mom Ukku suka tarkata suka dawo, da niyyar sake shiryawa domin suje su ɗanyi ko wata biyu ne acen. Kowa nurna yake, hada ma'aikatan gidan duk za'a tafi. A gaban udon mom ake ba Umma cikakken girma, kowa ya sani sarauta tata ce, dan haka sai ya kasance ma cewa kaman ita ce uwargida ga sabon mai martaban, hakan baya ɓata ran

Gidan mu ya zama settle, dan haka komai an saka, tarewa kawai yayi mana saura. Abunda ya bani mamaki irin yanda Saudat ta same ni, tare da neman yafiya ta, sannan ta faɗa man duka abubuwa marasa kyau da ta aikata, wanda har rashin lafiya saida ya kaita ga yi, daƙyar ta samu ta shawo kan ta, tare da faɗa man ta tuba har cikin ranta, naji daɗi sosai, ko hakan ma aka tsaya Allah ya nuna masu ni ba wulaƙantatta bace ba. Dan haka na ƙaravmata wasu addu'oi da zata dinga yi, domin neman yafiyar Allah, somin ta aikata abubuwa marasa kyau, da Alah ke fushi da duk mai aikata su. Ko Mama Saude da zata tafi kuka ta dinga yi tana neman yafiyar mu tare da faɗa mana abubuwa marasa kyau da suka dinga aikata mana. To sauƙinta ma Ya Ameen ɗina ya bata jari mai gwaɓi, yanda ba zata tagayyara ba.


Muna ganin gata, ga soyayya, Janaa kuwa ta zama abun so da sha'awa ga kowa, ko yaushe kyaututtuka take samu, idan ka ganmu yanzu ba zaka ce mun taɓa fuskantar barazanar rayuwa ba.

Yarinya tayi kyau da wayau sosai, kamannin ta da mahaifin ta sun ƙara fitowa sosai, gashi sai tace wai surutai take son yi, kullum tana fada wajen nai Martaba Dad, ta cika shi da surutun gwaranci kuwa.

Haka muka cinye kwanakin mu muka juya, kaman kar mu dawozmunji daɗin zama sosai, daga mu har Ya Amewn wanda sarautar tayi mashi masifar kyau soaaizsai manin munje barga yana hawan doki da Jaana, itakuma tana ƙyalƙyala dariya. inda muna komawa zamu tare a sabon gidan mu. Mom ta nuna bata ji daɗi ba, amman ba yanda ta iya, yanzu gudun yin wani abu da zaisa a yi tunanin halin ta nada cen baya yana nan.

Mun tare a babban gidan mu mai kyai sosai komai yaji, Ya Ameen yayi ƙoƙari kullum duk abunda zaiyi inji daɗi shi yake yi, baya abu baiyi shawara dani ba, hatta a harkar kasuwancin shi. Tare da taimakon Ummin Bilal, Hafsat da su Nihal da Saudat muka tare, saida suka kammala mana komai sannan suka bar gidan cike da jin daɗi, da yabon gidan a bakin su, domin dai dukkan su gida na ya shefe nasu kyau da komai da abubuwan ƙawa, domin dai har swimming pool ke akwai, haka kuma ɗaki guda aka fidda na Jaana, inda aka sake cika mata su da kayan wasa, yarinya mai shiga rai da kwanciya a zuciya.




Tabbas ina ganin soyayya cike da ƙauna a tattare da Ya Ameen, kuɗi na da Umma ta damƙa su a hannu na, a cewar ta miji ma ya iya komai na kasuwanci, haka kuwa akayi, ni na danƙa kuɗin duka a hannun shi, zama mukayi ni dashi muka shawarta. Babban shago na kayan costimetics da botique na mata da ƙananan yara aka buɗe, inda aka zuba manyan laces da atamfofi na girma, sai jakunkuna da takalma da blawus na yara, sai vails da kuma ƴan kunne fation, hada golds, ya amsa sunan shi kuwa, *Janaaa Collection* muka sanya ma shagon, inda kai tsaye muke bada order daga waje, ake shigo mana da kaya, hada shaddoji masu masifar kyau ƴan mali da gizners. Nan da nan shago ya karɓu, hada aseobe muna fiddawa, irin na manya, da kuma ya ku bayi, sannan bama sanya farashi mai tsada sosai. Sauran kuma kuɗi na aka siya man ƙaddarori dasu.

Shi kanshi Ya Ameen ya natsu yanzu sosai, gida ya zama kaman ba wani hayaniya da ya taɓa faruwa a cikin shi. Mom na cen daga ita sai ƴan aiki, inda akai akai take zuwa cen adamawar, Umma na Adamawa tare da mai martaba, inda muma muna gidan mu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali.



Afnan ma ta shaida man Ma'u nabta bibiyar Sakim da tashin hankali, da yafa zata ɗaga mashi hankali ya idasa cikashe mata sakin gabaki ɗaya, banso hakan ba, saidai tace Ma'un na neman shi da sharri ne, dile ce ta sanya yayi hakan, ibda yanzu yaran gabaki ɗaya suna hannun ta, ta haɗa ta riƙe gwanin ban sha'awa, duk da tana zuwa aikin ta lafiya lau.


Nayi ƙiba ta sosai, na zama babbar mace mai ji da aji,

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment