Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abu dangane dake, sai na saka hannu na ƙwaƙule ta na yarda. Kinyi kaɗan, baki kai ba, wadda ma ta fiki bata kai ba. Waccen ɗin dai, wadda kuka raina, wadda kuke son ganin baya, wadda kuka so jefa rayuwar ta da ta mahaifiyar ta a cikin wani hali, ni ita na gani, kuma ita nake so, mugun nufin ki a kaina, zai tabbata a gareki, ni Al'ameen Almustapha Dambulan, ba zan taɓa iya ƙyale ku ku tafi haka ba, dan haka ku jira me zai biyo baya, kuma ina gargaɗarki da sake riƙe mani jiki, saboda ni ba sa'an ki bane shashasha, wadda bata san ciwon kanta ba, kuɗɗa ballagazar mace" yana gama faɗin hakan ya sanya kai yana mai ficewa. Kuka sosai Mama Talatu keyi, tana bin ƙafafun su Mom da Umma tana riƙewa, babu abunda ya dame su da ita, itama Saude saida tayi kuka, tasan hakan zata faru da ita dama, tayi nadama tuni, taso kuma ta fallasa komai tuni, Amman wannan ranar take gudu. Sauƙin ta ma taji alhaji yace Alhaji Ƙarami zaiyi mata wani abu, kuma ta san ba zai barta da kaɗan ba.

Alhaji ne ya sallami kowa, lokacin salla yayi, ko da akayi haka, sashen Mom ta wuce dani, tana ta lallashi na, wai kukan me nake ai komai ya wuce, indai ita ce, yanzu bana da matsala da ita.

Jiki a sanyaye suka fice, suna ta rusa kuka, Iro ne ya biyo mariya daga baya, yana faɗin "e chilun ki maliya ta, ni ina sonki kuma zan aule ki a haka, ina matuƙar ƙaunal ki, ni ma ba zan zauna ba, zan biku kinji?"

"Kai dan ubanka matsa ka bani waje, shege mahaukaci, ko maza sun ƙare duniya zan iya auren ma ne? Jibi yanda kake tashin ƙarin dauɗa fa, ka saka ido ka gani yanda zan dawo cikin gidan nan in baza haja ta, kowa ya kwasa.."

Maganar ta ce ta maƙale a baki, jin ihu da jiniyar motar ƴan sanda tana mai danno kai a cikin gidan nasu.

Da sauri duk muka sake firfito wa, hada Alhaji da yayo alwala zai fita masallaci, shi ko Ya Ameen yana jingine jikin wata motar shi, hannun shi riƙe da waya yake latsa wa. Kawai nuni yayi masu da su Maree da suke tsaye tsakiyar gidan.

Diddirowa suka yi su biyar, suna masu kakkafa masu bindiga a kai, "Muje Malamai, you are under arrest, muna tuhumar ku da yunƙurin kashe wata, dan haka zaku amsa laifin ku a gaban alƙakili" cewar wani daga cikin ƴan sandan, da gani shine babba.

Aiko sai suka zube ƙasa har Maree ɗin, da taji hanyar cikin ta ta kaɗa, cikin ya hautsina, kaman zata saki zawo.

"Yallaɓai wallahi.." "yi mana shiru nace, duk Abunda kika faɗa man zai zama hujja a gaban alƙali ne"

Take aka buga masu ankwa duka hannuwan, kuka kawai suke yi, wannan shine ƙarshen mai cin amana, munafuki magulmaci. Saida suka iza ƙyeyar su zuwa bayan motar, sannan suka sarm Al'ameen, shi kuma yayi masu nuni da suje zazo.

Da gudun masifa suka fice daga gidan, ba abunda kake ji sai ihun Mama Talatu da mariya, abun gwanin ban kunya da kataici. Ace gida babba irin wanna ka fice daga cikin shi, cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Ɗan girgiza kai Alhaji yayi, bai so haka ba, saidai ya riga ya aikata, kuma ya sani, yanda ran yaron nashi ya ɓaci, muddin ya hana shi, ba za'a zauna lafiya ba, gara ya ƙyale su a hukun ta su, alabasshi gaba wani zai kiyaye. Sauran ƴan aikin kuwa duk jikin su yayi sanyi, sun ƙara tsorata, saidai sam basu ga laifin Al'ameen ba, hakan shine ya dace da mutane irin su Talatun masu baƙar zuciya. Ita kuwa Mama Saude sashen su ta wuce kai tsaye domin har haɗa kayan ta a tsanake.

Muma jiki a sanyaye muka koma sashen Mom ɗin, jiki na duk ba lakka, ga wani ɗan kumburi da naga alamun kaman na fara, ciki na wata biyar kenan a yanzu, har ma yana niyyar shiga na shida.

Fitar da baiyi ba kenan ya koma sashen namu yana jiran shigowa ta. Jin shiru ban shigo ba ne, ya sanya shi sake wanke, gami da sauya kaya marasa nauyi, ya kulle sashen ya fice zuwa wajen Bilal, daga cen zasu wuce division ɗin.




Ni kuwa sai wajen ƙarfe biyar na koma sashen namu, alale Mom ta sanya aka siyo man mai daɗi, mai ƙwai da kifi da anta ciki, sai Alayyaho, gashi tayi saƙa sosai, ko acen saida na kwanta ɗakin Afnan nayi bacci, Afnan ɗin na matsa man ƙafafu na wanda sukayi man fushi, butsu butsu Mom kan leƙo taga ko ina cikin ƙoshin lafiya. Har abun ke ba Afnan mamaki, ta sake tabbatar ma da ka ta cewa Mom ɗin ta shiryu sosai, bayan faruwar abunda ya faru.


Da taimakon Afnan ɗin na kammala komai, duk abunda na san zai nema saida na tanadar mashi. Na san yau baya cikin natsuwa, tun bayan shiga rayuwar tashi da nayi, komai ya sauya mashi, Sam idan Kaga ya Ameen kai kanka ka san ya cenza daga da. Ya Ameen mara hayaniya, ga natsuwa tattare dashi, Amman yanzu da ka kalle shi, ka san akwai wani al'amari tattare dashi, tausayi yake bani sosai matuƙa, duk hanyar da zanbi wajen ganin na daidaita mashi rayuwa ta koma kaman ta da zanbi.

Bai dawo ba sai ƙarfe bakwai, ana yin sallar magrib sai gashi, kaman ma saida ya tsaya masallacin waje yayi sallah sannan.


Nima sallame sallah ta kenan, ban ko miƙe ba daga kan dardumar, ya turo ƙofa, kai tsaye cikin ɗakin ya shigo, daidai lokacin da nake shafa addu'a na ɗan waiwaya haka ina mai cewa "Sannu da dawowa Yayan mu ya hanya?" ɗan murmushi ya sake mani, da gani na son kauda tunanin yana da damuwa ne.

"Fine" ya faɗa a gajarce. Yana mai zama bakin gado. "Wash" ya sake faɗi alamun gajiya, yana mai kai kwance bisa gadon da na lailaye da zanen gado mai taushin gaske.

Kusa dashi na ƙarasa, ina mai zame hijab ɗin na linke, na ajiye ta mazauni ta, bisa dardumar. Zama nayi sosai jikin shi, ina mai ɗan ƙwantawa na tada kaina da hannu na, fuska ta daf da tashi nake cewa Habibi gajiya ko?" na faɗa cikin kulawa. Ɗan lumshe idanun shi yayi, masu ɗauke da zara zaran gashin ido, sai kuma ya buɗe su, yana mai narke idanun cikin nawa yace " Yes Habibty, anything for me?" wani murmushn na sake ina mai cewa" Aloot dear" jawo ni yayi zuwa jikin shi sosai, yana mai cewa "Gist me mom baby" ya faɗa yana shafo cikin.

"Aloot of your love, cant imagine baby" dariya yayi, har kumatun shi na lotsawa, fararen haƙoran shi da suke jere reras suka bayyana.

"Mee to dear, muje ki sama man wani abu for now" a tare muka miƙe, ina cikin jikin shi, har dining. Shi kanshi yayi mamakin yanda na tsara abinci, duk da yanayin da nake ciki.

Yaci sosai kaman ba shi ba, labari ya dinga bani akai akai, abincin ya mashi daɗi, masalan dayake abincin gargajiya ne mai sauƙin nauyi.


Muna gamawa muka koma falo. Aiki ya fara cikin computer, kaina na saman cinyar shi, akai akai nakan shafo sajen shi mai ƙayatar dani.

Har aka kira Isha, sannan muka miƙe, ko bayan da muka dawo daga sallar ma hakan ce dai ta sake faruwa, komawa mukayi yanda muke. Aiki yake sosai a computer yana yi yana ɗan bani labari. Har na miƙe na kawo mashi fresh milk. Ina jin daɗin zama da Ya Ameen, mutum ne mai sauƙi, fiye da yanda nayi tsammani, kowa na mashi kallon mai miskilanci, amman a zahirn gaskiya saidai in baka zauna dashi ba. Hannun shi naji saman fuska ta, yana mai shafowa yake faɗin "Baby na jiki shiru ko kinyi bacci ne? " ɗan zakuɗawa nayi, ina mai damƙe hannun sa sosai da ke kan ciki na. Nace "A'a Yaya" murmushi ya sakar man, tare da bani peck a goshi. Sannan ya cigaba da aikin sa.

Bansan lokacin da nayi bacci ba, ina shaƙar ƙamshin sa mai daɗi, tun da na samu ciki nake jin marmarin ƙamshin, idan har zan rayu dashi, ko yunwa bana ji.

Ko da ya gama aikin, baya son tada ni, gashi ƙafafun shi sunyi sanyi, Amman ko motsin kirki ya kasa yi, saboda yanda take dauke numfashi a hankali cike da gajiya.

Ya daɗe nan a zaune yana saƙe saƙe, yayi mamaki yanda bai sha wahala ba a case ɗin su Maree cikin sauƙi aka tura su cell, tare da filling ɗin case ɗinsu, gobe za'a tura su ga kotu, a bisa tuhumar su da ake da ƙoƙari da haɗa baki wajen kashe Suhan.


Wani irin abu mai ɗan ɗumi naji yana ɗigar man saman fuska, ɗan yamutsa fuska nayi, ina mai gyara kwanciya, still naji ya sake ɗigowa.

Ɗan zabura nayi na tashi, cikin ɗan sauran hasken da bai wadata ba na ke kallon fuskar shi. Lallai kuwa Ya Ameen kuka yake yi, to me ya faru? Ko case ɗin ɗazu ne bai wuce ba?

Baisan na tashi ba, saidai yaji fuska ta kwance a saman kafaɗar shi ina cewa "sorry dear" a hankali da jajayen idanun shi yake kallo na, tare da saurin goge ƙwallar, saidai na riga na gaji, hasalima ita ce ta tashe ni ɗin.

Shafo gefen fuska ta yayi, a kasalance, ban jinkirta ba na cigaba da faɗin "Na nasan ni ce sila, nice dalilin faruwar komai, ina mai sake baka haƙuri, ban shigo rayuwar ka ba, sai domin son da nake maka, ban shiga rayuwar ka ba, dan in cenza komai, ban shiga rayuwar ka ba dan in haddasa fitina, kuma ban shiga rayuwar..." Saurin rufe man baki yayi da nashi, ban musa ba, domin a shirye nake da na lallashe shi ta kowanne hali. Saida ya gaji dan kanshi, sannan ya ƙyale ni. Yana mai goge man hawayen fuskar tawa nima.

Saida ya gyara komai sannan ya kwanta kusa dani, rabin jiki na ma na a nashi, sannan ne yake faɗa man duk yanda sukayi da su Maree. Na sha mamakin da ya sanar mani har yaje bakin Maree wai bai mutu ba, ita fa sonshi take da aure, ko ni sai da nayi dariya, shima dariyar yayi, yana mai cewa "Ai ina jin fa yarinyar nan ba kanta ƙalau ba" ɗan jinjina kai nayi, wani irin kishi na taso man, ko ɗazu da ta riƙe mashi ƙafa, ji nayi kaman in zame daga roƙon da mom tayi man inje in faffalla mata maruka naji, ina kishin miji na, balle da Allah ya mallaka man Ya Ameen da nake ji kaman na fi kowacce mace sa'a da dace da miji na gari. ygyara kwanciya na sake yi, yayin da ya rungume ni na koma bacci na mai daɗi, tare da sauke ajiyar zuciya akai akai, ina ganin matsala ta tazo ƙarshe. Shi kuwa ta ɓangaren shi, bai shaida mata cewa zasuyi dakon mutumen da yazo ya sanya mata ɓera a ɗaki ba cikin daren, inda defenetly Maree ta shaida ma su jami'an tsaro ɗin cewa yau sukayi zai dawo ya ƙarasa aikin shi, da ta ji matsa. Ya san in ya faɗa mata babu bacci a tattare da ita.



Ilai kuwa wajen ƙarfe biyu da wani abu ya fara jin motsi, alamun ana son shigowa ta wajen lambu, lamo yayi sosai, yana mai tabbatar da cewa ko wanene ma yake niyyar shigowa to fa gab yake. A hankali ya sauke kai na daga bisa ƙirjin shi, yana mai kara man fillow, tare da ƙara gudun Ac ɗin ɗakin yanda ba zatayi man illa ba, kuma zan ji daɗin baccin, sannan ya tashi yana mai buɗe ƙofar falon cikin sanɗa ya fice..........






~Oum-Deedat ce~
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~90~*



*Ina Barar Addu'a da bakunan ku masu albarka*

_Allah ya cika man buri na indai da alkhairi, in kuma babu, Allah ya musanya man da wata hanyar, Allah ya zaunar da mu da ƙasar mu lafiya ya ƙara kare mu tare da kiyaye mu Ameen_



*_#Stay Home_*
*_#Stay Safe_*
*_#Wash your hands_*
*_#Avoide over crowded place_*
*_#Stop spreding the dx_*




*Dan Allah a zauna gida, ayi addu'a Allah ya buɗo hanyoyn alkhairi, Allah yasa mu fi ƙarfin abin da zamu ci, zamu sha, zamu suturta da kuma muhalli. Ameen*





******************




Ko wayar shi bai ɗauka ba, duk wani abu da zai alamta cewa akwai matsala a gidan baya sonshi, yana so sai ya kammala koma menene sannan kowa ya ji, hakan ce ta sanya wata ƴar agogo ce kawai ɗaure a tsintsiyar hannun nashi, wadda tun kafin ya kwanta ya maƙala ta.

Bai kulle ƙofar ta baya ba, kuskuren da ya tafka kenan, hankalin shi ya ɗauku da ya kammala aikin.


Cikin duhun dare yake bi, ba zaka iya gane da mutum ba, saidai wajen yana da tsawo da kuma faɗi, dan haka daidai wani saƙo da zai iya sada ka da hanyar garden ɗin ya laɓe.

Ya kusan minti biyar, daidai lokacin da yaji motsin ya lafa, cikin ɗan hasken da bai wadaci wajen ba, ya ɗaga hannun shi, yana mai nuni dashi cikin farin watan daya haske kusa da inda yake laɓe, ƙarfe uku ta kusa, ya raya a cikin ran shi. Ko ba komai ya zuwa yanzu ya tabbatar da cewa jami'an tsaron da ya saka suka lallaɓe a kusa da gidan yanzu haka suna bakin aikin su.


Har saida ya fara gajiya da tsugunno, sannan ya lallaɓa ya ɓalle murfin da zai sada shi da lambun, yana mai bi ta ciki yana haskawa.



**********

Na natsu sosai ina bacci na, naji motsi sosai kusa dani, ɗan miƙa na sauke, ina mai lalubo kusa dani, banji komai ba, illa filon da ya ƙara mani. Zumbur nayi ina mai tashi zaune, da ɗan sauran hasken dum Light nake iya hango mutum tsaye daga bakin ƙofa, saidai ban iya tantance koma wanene.


"Yaya lafiya kuwa? Ko wani abu kake buƙata" na furta a hankali, cikin muryar bacci.

Ba'a amsa man ba, sai ma takowa da aka shiga yi, zuwa inda nake bisa gadon. Ganin hakan sai na sauko da ƙafafu na zuwa ƙasa, duk a zato na, ƴan maganar ne basa kai.

"Yaya na tashi fa, ko kana son wani abu ne?" na sake faɗa, ina mai haske ɗakin, ta hanyar kunna maƙyallin haske.

Wata irin razana naji, tun daga ƙafafu na har ƙwalwar kaina. Baki na buɗe zan ƙwalla ƙara, mutumen da yake kaman basamude yayi saurin zaro wuƙa, yana mai nuna ni da ita. Bashi da kyaun kallo, a tsaye da jiki ya linka ya Ameen uku.

"kina man ihu zan yanka ki" ya faɗa cikin kaushin murya, duka hannaye na na saka, ina mai daɗe baki na sosai, hawaye ne ke malala sosai a idanu na, girgiza akai na shiga yi, alamun ba zanyi ba, lokaci guda kuma ina mai haɗawa da ja baya. Shi kuma a lokacin yana doso ni, wuƙa tsirara a hannun shi, yana mai nuni dani. Ban tsaya ba, har saida naji na dangane da makarin gado,

Hantsilawa nayi bisa gadon, duk da cikin dake jiki na, na ma manta da shi, ina Ya Ameen Ya tafi ne wai? Na shiga uku, wa ya buɗe mana ƙofa? Kaddai ace sunyi mashi wani abu.

"Ina mijin ki ya tafi? Hahaha Naji daɗin hakan, abu yazo da sauƙi, yanzu zan gama dake da kuma wannan shegen cikin da ke jikin ki, ba tare da wani ya sani ba" ya faɗa shima, yana mai niyyar haurowa saman gadon.

Dunƙulewa nayi sosai saman gadon, ya zuwa yanzu sautin tsoro da tsananin tashin hankali ya fara ƙwacewa daga baki na kaɗan kaɗan.

"Zo nan" ya sake furta wa cikin ƴar tsawa.

"Dannn Allllahh kaa... Yi hhhaƙuuri" na furta cikin giggiwa da tsoro sosai, murya ta na karkarwa.

"Ba zaki taso ba? Sai na idasa haurowa saman gadon??" ya sake daka man tsawa.

Sake dunƙulewa nayi, saura kaɗan na saki fitsari, gabaki ɗaya idanu na sunyo waje, na tabbata saura ƙiris na some.

"Wato ke da mijin ki masu tarin kai ko? Zakiga sakamakon tarin kai, gabaki ɗayan ku sai na gama daku" ya sake faɗa cikin amon muryar shi mara daɗi.

Ganin yanda yake doso ni, da wuƙa tsirara kawai na sadaƙas, runtse idanu na nayi gam da ƙarfi, ina mai tattakura na fasa ihun da nasan cewa hatta da mai gadi sai ya jiyo shi.


Wani irin Dammm ya jiyo a cikin ƙirjin shi, sakamakon ihun ta da ya jiyo daga cen sashen nasu. Da gudun bala'i ya juyo, yana mai nufar dashen nasu, da ya hango ƙwan fitilar ɗakin nasu a kunne ƙau.

Ai bai tsaya wata wata ba, ya afka cikin sashen, har yana nemna zamewa da santsin tiles, me kenan? Shi yana cen ya tafi neman mugun, ashe shi yana nan zai mashi ta'asa.

Ɗakin ya faɗa kai tsaye, Allah ya soshi, ɗan ta'addan ya juya baya, aiko ya rarumo shi, duk da tsayi da girma da ya linka shi. Zubewa sukayi saman tiles, yayin dana sake tattakura na fasa kuka cikin ihun amo.

Ai da gudu idi mai gadi, mudi driver da Iro suka yo fitar burgu zuwa sashen namu da suke jiyo ihun kukan.

Faɗa ne sosai ya kaure tsakanin su, duka sosai ya Ameen yake kai mashi, duk a ƙoƙarin shi na son danne shi ya kama shi, amman shi duk idan ya kai ma Ya Ameen duka ɗaya, sai wajen ya fasa, gami da yin ja, yankar shi yake ƙoƙarin yi, Amman bai samu nasara ba, sai sau biyu, jini ne ya fara ɗibar ya Ameen, inda ina ganin hakan naji wani irin jiri na ɗiba ta, sake kwatsama ƙara nayi, ina mai cewa "Wai ba kowa ne a gidan? Azo a taimake mu, zai kashe mu" Amman duk da haka Ya Ameen ta maza take yi, yana sake kai mashi naushi.

Dayake shi baƙi ne Wancen kakkaura, Ya Ameen Ya fishi jin jiki sosai, abunka da fari, har ƙarfin nashi ya fara ƙarewa.

A wahalce ya latsa wani ɗan abu da ke liƙe da agogon da yake hannun nashi, cikin ɗakiƙa ɗaya ƴan sandan nan suka fara diddirowa ta saman katangar.

Su ma su Mudi basu tsaya wata wata ba, suka afka sashen namu, masalan ma da suka ganshi a wangame, sun san da matsala kenan.

Kokowa sosai suka tadda suna yi, duk ya yayyanki Ya Ameen, lallai wannan mutume da ƙarfin hali yake sosai, ni kuwa sai kuka nake na dunƙule saman gado, duk na yayyayo bargon da zanen gadon ma lulluɓe jiki na dashi.

Afka mashi sukayi sosai da sosai. Abunka ga sarkin yawa, tuni suka kai shi ƙasa, Amman har yanzu ƙoƙari yake na ya kufce ya iso gareni.

Da sauri Umma da Alhaji Mustapha suka yo waje, dama Umma na sashen shi, ita ma Mom haka, ita da Afnan, kowa hankalin shi a tashe, masalan da suka ga ƴan sanda rirriƙe da bindigu a cikin gidan, wasu kuma sun shige sashen namu.

Ko da yaga bindiga, dole yayi surrender, tuni suka nannauahe shi, gami da buga mashi ankwa. Afnan har ta fara kuka haka ma sauran ma'aikatan gidan sunyo waje. Hankalin kowa ya matuƙar tashi. Masalan ma Umma. Addu'a take kaddai ace wani abu ne ya faru da ƴar tata. Ikon Allah Suhan dai na gani tashin hankali iri iri.

Saida suka taso ƙyeyar shi zuwa waje ne, sannan kowa ya gane me ke faruwa, cikin tashin hankali kowa ke kallon mu. Masalan Alhaji Mustapha da bai kai ga ma fahimtar me ke faruwa ba. Ƴan sanda a gidan shi? Wanene wannan da aka kama sun fiddo shi daga sashen Yaran nashi?


Ɗan naɗe Jallabiyar shi yayi, cikin son ƙarin bayani ya matsa kusa dasu.

"Kai Lafiya kuwa cikin daren nan? Me ke faruwa..." maganar shi ce ta maƙale, ganin Mudi da Iro sun kamo Ya Ameen rana ranga , gani biye dasu ina rusa kuka. Faɗi nake "Ya kashe shi Dady ya kashe shi" Ai da gudu suka zabura inda muke, Mom ce ta rirriƙe shi cikin tashin hankali take faɗin "Son me ya faru? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Son buɗe idanun ka me ya faru wai?" ta jefo man tambaya cikin tsananin tashin hankali. Da gudu nima na faɗa jikin ta ina mai cewa "Mummy nima bansan me ya faru ba, bansan waye shi ba, sashen mu ya shigo mummy"

Da hannu Alhaji Mustapha yayi ma ƴan sandan alamu da su wuce da wannan mutumen, sannan ya tallafi Ya Ameen yana ce ma Mudee ya fiddo mota.

Dishi dishi yake gani, kuka ya hango ta tana yi sosai, hannu ya miƙa mata alamun tazo gareshi, ba musu kuwa ta tako cikin sauri, tana mai damuƙar shi, duk jinin da yake jikin shi, haka ta rungume shi, ta ma mance su Umma na wajen, ga shi cikin jikin Dady.

"Ya Ameen ka tashi, kada ka mutu dan Allah, jini a jikin ka, Ya Ameen dubi yanda yayi maka fa" na furta cikin ƙarajin kuka.. Umma ce ta matso tana mai zare ni a jikin shi, daidai lokacin da ake cusa shi cikin motar. Mom ma saida taso shiga Dad ya hana ta, daga shi sai Mudi da Iro suka nufi asibiti dashi, yayin da har ƴan sandan sun fice da ɗan ta'addan.

Kuka nake sosai, na ƙi komawa sashen na, dan haka ne ma Mom tace Umma ta wuce dani ta lalasshe ni, Afnan ma binmu tayi. Kusan haka muka kwana a ranar, ba wanda ya rutsa, ni kuka kawai nake, duk yanda Umma da Afnan suka so su lallashi ni kasawa nayi, na tsorata, ga Ya Ameen cikin wani hali, ina ji ɗan ciki na yana dunƙulewa gami da warwarewa a lokaci guda.

Ruwa kawai Umma ke ɗirka man tare da tofi da tayi man ciki, ko zuciya ta zata dangana.

Tun da safe sai ga Dad, cewa yayi mu fito a kaimu asibitin, sallah kawai nayi, ko ruwan tea da Umma ta haɗa man na kasa kurɓa, matsa man tayi wai saboda abinda yake ciki na, aman na kasa sauraren ta. Ita kanta mamaki na take yi, son da ɗiyar tata ke yi ma mijin nata yana da yawa.

Haka aka kwashe mu sai asibitin, jikin Ya Ameen ɗin da sauƙi, saidai yana bacci, inda duk aka nannaɗe yankan da bandage. Ya wahala sosai, duk dan ya ƙare ni, dan ya kuɓutar dani, kuka kawai nake, muna hango shi ta cikin glass, idanu na duk sun kumbura sunyi ja, sai raɗaɗi suke yi mani. Mom ma lallashi na take yi, ganin jikin da sauƙi, tun cikin daren Abie yace zai taho, dayake su cen safiya ce. Haka ma Aunt Feena, Amman sai Mom ta hana ta, a cewar ta, ya zatayi da karatun yaran? Dan mijin ta yana kauda mata kai kuma sai ta dinga tafiye tafiye, kullum tana hanya?

Kusan zan iya cewa Salla kawai ke motsa ni daga jikin glass ɗin, ƙafafu na kuwa har sun kumbura saboda tsayawa. Ko da ya farka, ni ce ta farkon da ya fara miƙo ma hannu, ba'a hana ni shiga ba, saboda ya samu ƙwarin jiki sosai. Ko da na shiga kukan dai nake yi, shi ke share man hawayen yana girgiza man kai. Yayi wani fayau dashi, ya sha duka, duk fuskar tayi kwaɓa kwaɓa, wanda ko ga alama ba wanda zai tunanin akwai wani mahaluƙi da ya isa yi ma Ya Ameen haka, ganin

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment