Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kowa baya ga ita. Kaman yanda tun bayan mutuwar mahaifin nata babu wanda ya ɓulla yace shi ɗan uwan mahaifinta ne, ashe ma bata sani ba Muhammadu ya riga mahaifinta mutuwa, kuma mahaifin nata yana da hannu a mutuwar ɗan uwan nata, kuma ɗanɗa ga ɗan uwan nashi tilo.

Al'ameen kuwa zaune kawai yake kaman mutum mutumi. Idanun shi zan iya cewa sun fi garwashi ja. Shi kanshi baisan a wane hali yake ba. Illa iyaka dai har yanzu ya kasa koda motsa yatsan shi ne. Jira kawai yake Umma ta ɗora daga inda ta tsaya, domin a yanzu ba zai iya cewa ga matsayar da yake kai ba. Har sai yaji ƙarshen ta'asar da Baban Mahaifiyar tashi ya tafka.

A ga jali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai sauke kanshi ƙasa, inda yayi amfani da yatsan shi, wajen ɗauke guntun hawayen da yake neman gangaro mashi. Wani irin son Suhan, kewarta da tausayin ta yana mai ratsa mashi zuciya, ashe haka tasha gwagwarmayar rayuwa?tazobkuma ta ɗora wata a gidan nasu. Duk ta dalilin mahaifiyar shi da mahaifin ta? Da wanne ido zai kalle ta. Son zuciyar na kakan nashi har ya kai haka?. A hankali ya runtse idanun shi, yana mai hango fuskar Suhan, yake ayyano kamannin mahaifin nata a cikin fuskar tata. Tasha faɗa mashi cewa Umman ta tace mata ita marainiya ce, saidai zata so ace ko hoton Abban ta ne Umman ta ta nuna mata. Bata taɓa sanin sarƙaƙiyar labarin ta, na mahaifinta ba da mutuwar mahaifin nata da take da alaƙa da shi kakan nashi ba.

*Duk ranar da ta san hakan da wane irin ido zata kalli mahaifiyar shi dashi kanshi? Kuma ya alaƙarshi da ita zata cigaba da kasancewa? Kuma ya al'amarin auren nasu? Shin zata yadda ma tacigaba da zama dashi a hakan kuwa? Duk da tasan cewa kaf wahalhalun da suka sha, da mutuwar maiahin nata, suna da alaƙa da Hajiya Kubra da mahaifin ta?*



_Hmmm Muje Zuwa Fans_












~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~75~*






*Abin Da Ake Fada don kawar da kaidin shaidanu Masu Taurin Kai.*


أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.


A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.



Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!




*Ban manta dake ba ƙawata, koda yaushe ina faɗin _Ilove u wujiga wujiga, haƙiƙa Alkhairin ki gareni ba zai kisaltu ba, saidai kawai ince Allah ya barki tare da baban Al'ameen ya raya mana Ameen kuma ya shirya mana shi. Kiji daɗin ki ki walwala ki shana duniyar taku ce. Lahirar ma haka insha Allahu Mrs Daura*






i͠n͠a͠ k͠i͠k͠e͠ ƴa͠r͠ d͠a͠r͠u͠ t͠a͠ s͠u͠m͠i͠e͠e͠ b͠. (a͠m͠i͠n͠t͠a͠ & m͠i͠j͠i͠n͠ b͠a͠h͠a͠u͠s͠h͠i͠y͠a͠) w͠r͠i͠t͠e͠r͠. h͠a͠ƙi͠ƙa͠ g͠o͠y͠o͠n͠ b͠a͠y͠a͠n͠ k͠i͠ d͠a͠ s͠o͠n͠ i͠n͠y͠i͠ m͠a͠ f͠a͠n͠s͠ t͠y͠p͠i͠n͠g͠ y͠a͠n͠a͠ d͠a͠g͠a͠ c͠i͠k͠i͠n͠ a͠b͠u͠n͠d͠a͠ k͠e͠ ƙa͠r͠a͠ m͠a͠k͠i͠ ƙi͠m͠a͠ a͠ i͠d͠o͠ n͠a͠. a͠l͠l͠a͠h͠ y͠a͠ b͠a͠r͠k͠i͠ d͠a͠ m͠a͠s͠u͠ ƙa͠u͠n͠a͠r͠ k͠i͠. m͠a͠ƙi͠y͠a͠n͠k͠i͠ k͠u͠m͠a͠ a͠l͠l͠a͠h͠ y͠a͠s͠a͠ s͠a͠i͠d͠a͠i͠ s͠u͠ d͠i͠n͠g͠a͠ h͠a͠n͠g͠o͠ b͠a͠y͠a͠n͠ k͠i͠. a͠i͠ i͠n͠a͠ y͠i͠n͠k͠i͠ t͠a͠ w͠a͠j͠e͠n͠a͠


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



Rage sautin kukan Umma tayi, tana mai share hawayen da suke kwance male-male a kan fuskar ta. Lokaci guda ta ja majina a hankali, tana mai muskutawa. Lokaci guda kuma falon ya ɗauki tsit. Kowa da Abunda yake saƙawa a cikin zuciyar shi.

Ci gaba tayi da cewa; "Tafiya nake cikin hasken alfijir daya keto, wanda da kyar nake lalubawa ina jefa ƙafa ta duk inda ya samu, lokaci guda kuma ga wani irin juyi da yunƙuri da naji cikin nayi, wanda na daɗe rabon da inji ya motsa, tun rasuwar Muhammadu. Haka naci gaba da tafiya har haske ya fara bayyana, rana ta soma ɓullowa. In naji cikin ya katsa mani sai in samu wuri in duƙa inta nishi da murƙususu har dai in samu ya lafa, sannan in tashi in dasa tafiyar tawa.

Kuka nake sosai, ina tunanin halin da zan jefa rayuwa ta ciki data mahaifa na. Abbana ni kaɗai ya mallaka, tabbas nasan wani mummunan abu zai iya samun shi, muddin aka neme ni aka rasa, sai dai na zaɓi hakan ne, kasancewar domin in tsira da rayuwa ta, data abunda yake cikin ciki na, wanda ko iskar duniyar ma bai kai ga shaƙa ba, Amman ana so aga bayan shi kan abun duniya da ya kasance mai wucewa ne. Koma menene na haƙura dashi.

Da kyar na samu na siya ruwan leda da ake ƙuƙƙullawa a tasha nayi alwala, na koma ƙarƙashin wata runfa ta mai siyar da abinci a cikin tasha na tayar da salla. Mai abincin dai sai kallo na take yi. Kayan dake jikina da komai nawa bai yi kama dana mai bara ba, sai dai a yanayin da ta ganni turtse-turtse da ciki tasan ba lafiya ba.

Abincin da ban taɓa cin irin shi ba tun da uwar data haife ni, yau shi na siya naci da kuɗi na. Ba daɗi Sam hakanan na gama turawa na bata kuɗin ta, sannan na tashi na ƙara gaba.

Cikin tasha na shiga sosai, ina jin ana ta ambatar garuruwa, Amman sam banji an ambaci sunan garin da ya kamata ace naje ba, wanda yake cikin lungu, inda ba lallai bane ko sun biyo ni su cim mani da wuri.

Garin Jigawa, shine sunan da naji ya kwanta mani arai. Ko ba komai zuciya ta na raya mani idan naje cen zan tsira da rayuwa ta, ba ɓata lokaci ko shawara na faɗa motar, ina mai samun kujerar can baya na zauna.

Motar ta daɗe bata cika ba, har na gaji da zama, ga ciwon mara sosai da yake murɗa ta. Har matar da take zaune kusa dani take ce mani "Baiwar Allah kodai naƙuda kike yi ne?" saidai in girgiza mata kai. Haka motar nan ta tashi, ina ji ina gani na bar gari na, mahaifa ta, mahaifar iyaye na, inda nake da gata da galihu.

Tunda motar nan ta tashi nake kuka mai cin rai, ina kallon matar nan saidai ta kalleni ta girgiza kai. Har kai lokacin da muka isa.

Gari ne mai yalwa da ni'ima sosai. Hakan ta sanya saida nayi salla. Sannan na siya bredi da lemo na sake ci

Wata motar na kuma shiga, inda Naji suna ambata sunan wani ƙauye da yanzu na manta sunan. Ba tare da sanin inda na dosa ba na kuma shiga motar. Kuɗin da suka buƙata na ciro na basu. Gashi dai marece ya kawo jiki sosai da sosai. Gashi bansan inda zan nufa ba, wurin kwana ma kawai ya isheni tunani.

Motar bata sauri, saboda haka ga wari ga tsami na tashi daga cikin motar. Hakan ya sanya zuciya ta tashi na dinga kwara amai a cikin motar, ga kuka inayi ga ciki yana ta motsi da son fitowa.

Mun yi tafiya mai nisa sosai a cikin ƙauyuka motar ta lalace. Dole muka firfito ana dudduba motar. Muna wajen har magariba tayi, ba abunda nake tunani sai Abbana da Mai Babban ɗaki.

Ina ji ina gani dole sallah ta gagareni a wannan lokacin. Gashi ƙarfina ya fara ƙarewa, masu surutu dai saiyi suke ina ji. Wai tayaya ma za'ayi nasan ina da tsohon ciki in tattagi tafiya irin wanna? Masalan ma da hanyar bata da kyau.

Jin hakan da nayi ne ya sanya ni sake tsurewa, gashi naga sai sulalewa suke suna tafiyar su gami da yima driver ɗin Allah ya isa. Har yanzu kuma babu mota ko gida data doso hanyar da muke. Gashi naji suna faɗin cewa hanyar wai fashi da makami akeyi.

Jin hakan nima na fara tattara kayana da kyar da niyyar barin waje. Matar da muka shigo mota ce da ita, ta ɗago ƙafa da kyar tana kai cimma ni, inda nake nufar wata hanya wadda bansan inda zata sada ni da ba.

"Baiwar Allah ina zaki ne haka? Gashi kuma naga kina cikin halin rashin lafiya, sannan ga dare yayi, idan ba zaki damu ba ki biyo ni zuwa gida na mana cen gaba kaɗan, alabasshi da safe kya wuce, hanyar garin namu ce bata da kyau ko kaɗan"

Da idanu nake binta, ban iya ce mata komai ba, ba yunwa ga ƙishi. Da kyar nayi mata murmushi ina mai cewa "Nagode baiwar Allah"

Bayanta na shiga bi, inda ta kama mani jikkar kaya na. Gata da sauri, ni kuma ban iya sauri ba, uwa uba turtsetsen cikin da nake ɗaga ƙafa da kyar ina nishi.

Sai tayi gaba sosai sai ta jirani in iske ta, da ƴar cocilar da take haskawa har muka isa cikin ƙauyen. Bamu wani yi tafiya mai yawa ba muka isa zuwa gidan da yake kaman shine nasu. Saboda kai tsaye naga ta cusa kanta zuwa cikin gidan.

Ba kowa a tsakar gidan da yake ginin ƙasa da danni. Da sauri ta ɗauko mani kujera ƴar tsugunno ta ajiye mani gindin wani ɗaki.

Da kyar na zauna. Kai daka kalle ni kasan bana cikin hayyaci na.

Ɗakin da yake kusa da inda nake zaune nan ta shigar mani da kaya na. Tana mai fitowa da sauri kuma ta shige ɗan madafar da yake cen gefe ta hura wutar kara, sannan ta ɗora tukunyar ƙasa, duk ina hango ta, ta hasken farin watan da ya fara ɓullowa.

Zaman kujerar fa ya gagareni, dole na sauke ƙasa ina mai miƙe ƙafafu na. Inda nake zaune ta dawo tana mai jawo kujerar ta kai zaune.

Macece wadda zamu iya kiran ta da matashiya, duk da ta girme mani sosai, saidai ba zata haifeni ba, duk da a lokacin kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci tsantsar halin babu dake tattare da ita.

"Sannu baiwar Allah, ni sai nake ganin ma kaman naƙuda kika fara tsai tsaye, gashi kuma ba ƴan uwan ki kusa, kodai delu unguwar zoma zan kira ta duba ko haihuwar ce?"

Girgiza mata kai na shiga yi. "A'a Adda bama sai an kira ta ba, cikin nan yafi shekara haka ina fama dashi..."

Katse ni tayi cikin firgita da kaɗuwa "Ke baiwar Allah, kinsan me kike cewa kuwa?"

Katseta nima nayi ta hanyar ɗaga mata kai. Shiru tayi tana mai sake kalle ni tsaf, sai kuma ta nisa tana mai faɗin "Bari dai Malam ya shigo to muji idan da wani taimako da zai iya baki, kenan cikin kwantawa yayi, ikon Allah"

Tana gama faɗin haka ta tashi ta shige madafar, tana ta aikace aikacen ta cikin ɗan hasken wata, har kai lokacin da ta gama girkin. Tuwo ne ta girka da miyar kuka. Nan ta zubo mana muka ci, tana ɗan yiman fira jefi jefi, har take tambaya ta inda na nufa, ganin nayi mata shiru ne ya sanya sai kuma jikin ta yayi sanyi. Kada fa ace tayi gangancin jawo ni gidan ta, ba tare da ta san koni ɗin wacece ba.

Muna tsaka da cin abincin ne Malam ɗin ya shigo bisa ɗan keken shi. Shima ba tsoho bane kaman yanda na zata, dan a lokacin ba zai haura shekara arba'in ba.

Jiki na rawa ta tsame hannun ta, tana mai miƙewa take mashi sannu da zuwa, kunsan mutanen da, har ƙasa ta duƙa tana gaishe shi, sannan ta wuce kai tsaye cikin ɗaki ta ɗauko kofin silver mai kyau ta ɗiba mashi ruwa a randa ta kai mashi ɗaki. Duk da ya kula da wata zaune, sai baiyi mata maganar ba har saida suka shiga ɗaki.

Tarar numfashin shi tayi da cewa "Yauwa malam dama bari nayi kasha ruwan sannan,..." nan ta kwashe duk yanda mukayi har zamana a gidan ta faɗa mashi.

Cikin tausaya wa yace mata ta gyara man ɗakin in kwana, zuwa safe saji koni ɗin wacece da kuma cikin dake jiki na.

Nan ta dawo ta iskeni zaune. Nima na kasa ci gaba da cin abincin. Na tsame hannu na, har na siɗe shi tas na rafka uban tagumi.

Ba sai na faɗi Abunda ke damuna, Tunda duk wanda yaji labari na yasan ina da dalilin damuwar. Taso ta fahimci wani abu, Amman sai ta share ta shige ɗakin tana mai gyara man, tare da umurtata da in shiga ciki in yi sallah sannan na kwanta.

In taƙaice maku dai daren ranar ban samu runtsawa ko ɗaya ba. Tun da safe sai gata ɗauke da ƙwarya da ruwan ciki, miƙo man tayi tana mai shaida man ruwan addu'a ne inji malam.

Cikin ɗan sakin fuska na amsa, ina mai godiya haɗu da gaishe ta. Tana gama amsawa ta fice, tana mai shaida man cewa lallai in tabbatar na shanye ruwan duka.

Gari na idasa wayewa duka, sai gata ɗauke da kunun tsamiya da ƙosai kai zafi ta shigo, shima banƙi ci ba, saboda yanda nake jin yanayin jikin nawa da yunwa, duk da ciwon marar ya bari, saidai juyin da cikin ke tayi.

Abun mamaki duka yinin ranar wannan matar bata tambaye ni komai game dani ba, haka bata sake man maganar tafiya ba, ashe wai sunyi magana da malam mijin ta yace su ɗaga man ƙafa, duba da yanayin da nake ciki.

Haka kuwa akayi na share kusan sati a gidan, mutane ne masu girma da daraja sosai, saboda a zama na dasu banga wani abu da yaci karo da addini ba, ko kuma suyi Abunda zai dagula man lissafi, ita matar mai suna Hajjo ce ma ke yawan lallashi na, duk lokacin da ta kula na faɗa komar tunani. Ya zuwa yanzu har na ɗan sakin jiki dasu, daga ita har malam ɗin da nake mashi kallo kaman na mahaifi na. Duk da na lura kaman Allah bai basu haihuwa bane su, Shiyasa suke murna da ɗokin cikin dake jiki na, duk da basu san asalin cikin ba.

Abun ka da ƙauye, sai gashi raɗe raɗi na yawo a ƙauyen cewa wai ni ƴar uwar matar malam ɗince naje nayo ciki, shine nazo nan zan haihu, akan hakan har mai garin saida ya sanya aka kira malam. Saidai bansan yanda sukayi ba, nidai kullum kuka, baci ba sha, duk na rame na ƙanjame.

Su Malam ɗinne ke saka ni gaba da lallashi da komai, har yanzu cikin su babu wanda ya tada mani wata magana. A haka aka samu gulmace gulmacen yayi sauƙi, babu inda nake zuwa kullum ina gida, saidai na kan ɗan taya Hajjo aikace aikacen gida, duk da ba wai sabawa nayi ba, Amman ina ƙoƙarta wa a hakan inayi,kasancewar babu Abunda ban iya ba, Tunda ni ke girka ma Muhammadu abinci da hannu na lokacin da yana raye, har yake yaba mani kullum, wai gani gimbiya Amman abun duniya bai dameni ba, shi bai taɓa ganin gimbiya iri na ba. Nakan yi mamaki ince mashi "Ai aljanna nake so, ita kuma aikin ladar mace ga miji ba ruwan ta da sarauta" ya kan yi dariya shima ya rungume ni ya shiga taya ni aikin.a haka rayuwar cikin sashen mu take gudana, Allah sarki, ashe shi ɗin Allah yayi ba mai yawan kwana bane, sun kashe man shi, sun kashe shi yabar duniyar, ya barsu suci abunda zasu ci ciki. Duk lokacin da nayi irin wannan tunanin saidai Hajjo taga ina kuka, da kyar take samu ta lallashe ni.

Sai danagaji da ɓoye ɓoye sannan na ɗan shaida masu malam ɗin halin da nake ciki, Amman na ɓoye masu ni ɗin wacece da kuma su wanene iyaye na. Hakan ce ta sanya su ƙara tausaya man, tare da Alƙawarina zama dani har sai komai ya kwaranye.


Ranar wata Lahadi ina cikin bacci, sai naji kaman an tsunkuleni, firgigit nayi na tashi, sai ciwo kuma yace man salamu alaikum.

Nishi da murƙususun da Hajjo ta jiyo ne, yasanya ta fitowa da sauri, aiko sai ta taraddani ba yanda nake ba. Da sauri ta zari hijab cikin dare taje ta kira delu unguwar zoma, saboda taga alamun haihuwa ce.

Masha wahala sosai kafin in haifo yarona santalele namiji, murna kaman me, cen kuma sai ga mace ta biyo baya watau Suhan.

Ansha murna sosai, inda aka gyara ni. Yara kyawawa dasu kaman su sukayi kansu, saidai namijin baya da lafiya sosai, ko numfashi da kyar yake yi.

Kafin gari ya waye yaron ya koma. Nan aka gyara shi gami da shirya shi, zuwa safe aka binne shi a cen gefen gidan. Saboda irin kukan da nakeyi ya ɗaga ma kowa hankali, tun da na haihu banyi shiru ba, gashi dai na haihu lafiya, Amman sai komai ya dawo man sabo, ni gimbiya nice da haihuwa irin ta marasa galihu, gashi yau na haihu ba gaban Mai Babban ɗaki ba, Muhammadu baya raye, haka kuma Abbana baiga yaran ba.

Duk wani abu da akeyi mai jego sunyi mani shi, saidai godiya tsakani na da mutanen nan. Mutane dai shigowa suke barka, duk da wasu da biyu suke zuwa suna gani na da jaririyar da ta rage mun.

Haka akayi taron suna, inda ni da kaina na zaɓa ma yarinyar Sunan mai babban ɗaki, na cika ma Muhammadu burin shi, da wasiyyar da ya bar mani. Yarinya taci suna Hauwa'u, sunan Mamana kuma sunan mai Babban ɗaki kenan. Dalili da hakan ne ya sanya nake mata laƙabi da Suhana,ko kuma ince Mama a


Haka rayuwar mu taci gaba da gungurawa, yau fari gobe baƙi, dole na fara ƴan aikace aikace, saboda in samu in samu Abunda zan kula da rayuwar yarinya ta, abun tausayi sai ga gimbiya da surfau, dakau da wankau, hakan bai dameni ba. Saboda har ga Allah nasan hakan ya fiye man in zauna inyi rayuwa a inda yake da haɗari.

Allah ya sanya man ƙaunar yarinyar sosai a raina, gashi ta taso da kyau da wayau sosai abun ta, kowa so yake ya ɗauketa yayi mata wasa, ta saba da malam kaman shine mahaifin ta.

Watarana ina wankin da aka kawo mani, Hajjo na madafa tana tuƙa tuwon dare, Suhana da malam na zaune a ƙarƙashin wata ƴar baranda da take ƙofar ɗakin malam, sauraren radio malam ɗin yake yi abun shi, wanda ya zame mashi al'ada. Akai akai yana yi ma Mamana wasa, ita kuwa sai ɓangala dariyar ta take ta faman yi. Kwatsam sai naji ana sanarwar rasuwar mahaifi na. Salati Naji malam ya sauke, yana mai tafa hannaye, kasa cigaba da wankin nayi, na zare hannu na ina mai miƙewa na isa inda malam yake zaune shi da Suhana, itama Hajjo da sauri ta fito jin salatin malam ɗin

"Malam Lafiya kuwa? Me ya faru? Wanene ya mutu?" cewr Hajjo da take goge hannayen ta jikin zanen da take ɗaure dashi.

"Bawan Allah! Allah kenan, sa'i yayi, ina sarkin da nake baki labari cewa ɗiyar sa ta ɓata? Wadda na taɓa shaida maki cewa an sanya cigiyr yarinyar tare da kyautar maƙudan kuɗi ga duk wanda ya gano ta? To ai shine tun lokacin sarkin Baida lafiya sai an kwantar sai an tayar, kinga dai har yanzu ba'a ga yarinyar ba, gashi har Ajali ya cimma shi, Allah ya jiƙan adalin sarki ya gafarta mashi, haƙiƙa anyi rashin sosai, saidai muce Allah ya kyautata makwanci... "

Ai ban ƙara sa jin abunda malam ke faɗa ba, saidai suka ga na sulale ƙasa a some. Sai kuma suka yo kaina a sukwane, inda Hajjo ta shiga girgiza ni tana kiran sunana," Maryama! Maryama ki tashi subhanallah, me yake faruwa ne? Malam dama baka faɗi wannan tashin hankalin a gabanta ba, Kaga Maryama mutum ce mai rauni, na tabbata tausayi ne ya kama ta"

Sakina tayi tana mai rugawa randa ta kamfato ruwa a kofin silver, tazo ta miƙa ma Malam suka shiga shafa man. Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sai kuma na saki kuka mai haɗe da sauti da kururuwa, ina ta surutai marasa kan gado.

Basu fahimci komai ba, haka kuma basu tsinci ko kalma ɗaya danake faɗa ba, Hajjo ta janye ni zuwa cikin barandar, kan shimfiɗa malam ta shiga yi mani firgita da maficin da malam ya miƙo mata. Har yanzu hankalin su a tashe yake sosai.

In taƙaice maku kusan kwana nayi kaman na zare na haukace, sai inyi kuka sai inyi dariya, abun duniya duk yabi ya damu su Malam, sai tofi malam ke man a ruwa Hajjo na ɗura mani, wani kuma a shafa man.

Haka muka kwana muka yini, ko nono naƙi ba Mamana, juyin duniya na hana ta, haushinta ma nake ji, sai faɗi nake "Meyasa na zaɓi farin ciki na, rayuwa ta? Ta ɗiya ta, nayi wasarere da ta mahaifi na? Ta dalili na ya mutu, nice na kashe shi. Baƙin ciki na ne"


Basu dai fahimta ba, duk sun ɗauka tsabar ruɗewa ne, har Hajjo ke cewa wai kodai iska ne suka kama ni? Malam ne ya kwaɓe ta da cewa "Ba wata iska bana son Jaye jaye Bahijja kawai ki taya ni muyi mata addu'a"

Cikin ikon Allah washe gari na samu sauƙi sosai, saidai kuka da nake ta rizga, ina haɗa kaya na nake cewa ni tafiya zanyi. Sunyi lallashn duniyar wanda ba zasu fahimci me nake nufi ba, har yanzu ni kuma zuciya ta bata Aminta da in shaida masu meke faruwa ba.

Da kyar suka shawo kaina na zauna, nima nayi tunanin zaman ne saboda kada in koma su ganni da ɗiya kuma su halaka mana rayuwa, anyi biyun babu kenan, gashi sun yi sanadiyyar mutuwar mijina, uba na, kuma suyi sanadiyyar mutuwa ta data ɗiya ɗaya tilo ɗana mallaka tare da Muhammadu.

Addu'a sosai na dinga yi ma mahaifi na. Kullum ina ganin mutuwar shi kaman sanadi na ne, saidai ba yanda za'ayi na kuma dosar masarautar tamu, masalan ma yanzu da nasan burin waziri daf yake da cika, watau na hawan karagar mulkin mahaifi na, wanda yake yanzu mallaki na, mallakin Muhammadu da yanzu ya riga ya kushe.

Wata zuciyar na tunzari ni, gami da ƙarfafa mani guiwa, Amman wata na kwaɓa ta, akan in ƙyale masu ko wanne irin mulki ne a duniya ake barin shi, gashi yanzu mahaifina ya tafi ya bar shi.

An yi kusan wata muna haka, kullum tsakani na da Malam da Hajjo nasiha ce ta kuma ƙarfafa guiwa, duk da har yanzu basu san ne ke faruwa ba.

Watarana da asuba na fito na shiga bayan gida saboda in kama ruwan alwala, sai naga kaman giccin mutum ta cikin hasken farin wata.

Da sauri na fito ina mai komawa ɗaki inda Mamana take kwance, sai na tadda tana ta kuka sosai, kuma ba'a inda na ajiye ta take ba, bayan na fita ba barta ne tana bacci, da acibalbal ɗin dake hannu na na haska, banga komai ba, in baya ga cenjin wurin dana iske ta. Sai ban kawo ma raina komai ba, saboda yanzu tana rarrafe ne, sai nayi tunanin rarrafowa tayi da bata ganni ba.

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment