Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar da kuma duk duniya mahaifiyarshi batada wadda take wulaqantawa irinta, amman ko menene ya sanya ta nace ma zaman gidan? Oho!


Dukda lokuta da dama yasha taddata bangaren masu aikin, ya sanya su kebe ya yi mata tayin barin aikin shi zai kula da ita da duk bukatunta batare da kowa ya saniba

Amman ta kan ce mashi " karka damu muhammadu komai lokaci ne". Iyakar abunda take fada kenan tayi mashi sallama tabar wurin

"Huh" 😯
ya fada tare da guntsar iska ya fesar alokaci guda yana mai kad'a kafad'a "Haka ne umma kamar yadda kika fada Allah yasa lokacin yazo mana da Alkhairi" ya fada a fili yana mai mik'ewa tare da tattara shimfid'ar tashi.


••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Wanene Moh'd Al'ameen?

'Da na biyu wajen Alhaji Mustapha Dambulan, kuma d'a mafi soyuwa a zuciyar Alhajin,ko dan ya gado shi ne ta fannin harkokinshi? Ko dan shine yaro mafi sauki tareda jinkai da taimakon na qasa dashi? Ko don shine kadai baya daukar irin zuga da halin mahaifiyarshi? Sau dadama ma yana mata nasiha wasu lokuttan dukda yasan ba ta dadin rai suke rabuwa ba, dukda yasan ba dauka takeyi ba, amman yana fata wani lokaci tagane gaskiya kuma tadawo kan hanya.

Kyakkyawan namiji ne ingarman namiji ka fasalta duk wani kyakkyawa da kasani tau YaAmeen ya wuce shi d'an boko ne na bugawa a mujalla kuma dan gayu ne, mutum ne maison tsafta yana da ladabi sosai, bayason bacin ran iyayenshi, matashin mai naira ne domin wasu daga cikin abokanshi kan mashi laqabi da yaro da kudi...,

miskili ne na gidan gaba sau dadama yana kallo anayin abu amman yakasa tankawa saboda k'yashin magana da Allah yayi mashi, kokuma yayi kaman ma baisan anayi ba, bashida business da mata

mace komin kyaunki komin haduwarki Baki kai ya kalleki ba, yana da shekara talatin da biyu a duniya, idan an mashi maganar aure kaka zuwaira wadda suke kira da Hajiya kan ce akyaleshi komai lokaci ne, yayinda Alhj isuhu kan matsanta da maganar, ita ko Hajiya kubra tana ganin an matsanta ma d'and'anta ita har yanzu ma bataga matar da ta kwanta mata ba da zata iya barin d'and'anta mafi soyuwa a wajenta ya aureta ba ta zame mata suruka a ganinta har yanzu cikin masu cewa su a son YaAmeen din da wad'anda iyayensu ke son had'a su dashi har yanzu arzik'insu bai kai mata wanda zata iya had'a zuriya dasu ba,balle tana ganin Al'ameen dinta saurayi ne na nuna ma tsara, yaro ne da kowacce budurwa kan so ya zame mallakinta.


Tanason suruka 'yar babban gida, 'yar masu naira, masu fad'a aji a fadin duniya.

bama Nigeria kadai ba, in haka ta faru ita fiye da burinta ya cika saidai abunda ba'a rasa ba, tinda kishiyace mata ke gudu ita kuwa tasan ta wuce wannan level din koma kawo wannan tinanin a ranta batayi.

Dukda halin YaAmeen na miskilanci hakan bai hanashi tausayi da jin qai na talaka ba, sau da dama ma zaiga su saudat na wulaqanta masu aikin gidan ya tsaya ya tsawata masu, saboda akwai ma lokacin da ya taba marin nihal saboda ta watsama wata mai gyara mata daki ruwa, (tin ma suna farkon dawowa k'asar, kafin zuwan su suhan gidan) saboda tayi mata mopping din daki, bata kunna air conditioner ba ta sanya mata room freshner shine ta taddata harabar gida ta watsa mata ruwa, akayi sa'a akan idanun YaAmeen din ne,aikau batayi aune ba ta ji saukar mari a kuncinta,

wannan ne ya sanya sukejin tsoronshi, saboda ko sun fada ma hajiya kubra bata mashi fad'a sosai saboda irin son da take mashi.

Da wannan ne ma'aikatan gidan suke samun salama indai yana qasar idan kuma yayi tafiya suke kaffa kaffa saboda sanin halin 'yan gidan.

=======================

Da sallama na shiga tanqamemen falon da ya lashe kujeru saiti hudu acikinshi,dukda nasan babu mai jina kuma da wuya ma ka tadda wani a falon, shima a hakan wai an ginashi ne saboda sauke baqi, dukda hajiya kubra ta mai dashi na sauke baqin da sukazo daga kauyen su alhajin, amman batare da saninshi ba.dukda babu kowa dake zaman falon, dukda haka sai na shareshi kullum nayi mopping, wannan shiyasa kullum nake kwana da uban ciwon jiki, wani corridor mai zurfin gaske nabi, banyi wata tafiyaba na tadda kofar falon Nihal da saudat din, kwankwasawa nayi dukda nasan bazan samu amsa ba amman haka dokar take garemu dukkanmu ma'aikatan gidan, kuma ko ma a musulumci haka dokar take shiyasa ma abun baya b'ata man rai.

sallama nayi tura qofar ahankali na shiga cikin salon tafiya ta (kamar ta masu akwai😜) falo ne madaidaici jere da kujeru kyawawa kalar sararin samaniya dukda cewa komai na falon haka yake, kama daga su labulaye Chinese carpet dakuma tiles din da ke malale a dandamalin falon.
K'ofofi biyu ne rak cikin falon, karkatawa nayi nabi ta gefen haguna inda zai sadani da asalin dakin Nihal din, hannuna dauke ba bowl na ceramic cike da fruit salad daya sha madara da zuma, nayi sallama a dakin bayan na murd'a handle din dakin.

Kwance na hangota nutse cikin gadonta da zan iya cewa yafi auduga taushi (🤔 oh ko ina suke samun irin wadannan katifun?) Ni kuma nace kaji suhan da k'auyanci😉.

Hannunta rike da waya k'irar Samsung a hannunta tana waya ga wata ahannunta daya k'irar iPhone tana latsawa,dagani dai da wannan dan gayen saurayin nata takeyin waya.

"Aunty Nee gashi" nafada ahankali saboda kada tace nayi mata ihu a kunne, ko kallona batayi ba balle tayiman magana,dama nasan hakan zata kasance, in kuma ban mata maganar ba ba zata sha ba, kuma nayi laifi, sai an hukuntani, wannan ce ta sanya nake cemata gashi tinda ni ke qasa da ita kuma nema nakeyi.

Takawa nayi na ajiye mata a kan wani qaramin stool dake gefen gadon mai kyau kaman da gold aka qerashi tsabar kyau, na juya da nufin ficewa a d'akin.

"Hey" abunda naji tace kenan cikin maganarta mai cike da shagwaba-shagwaba gadara gadara, isa isa, tinani na ya katse lokacin da naji tace "ki wanke mun toilet dina" abunda tace kenan ta cigaba da wayarta saboda nidai banajin me take cewa a wayar saboda munada dan tazara.
Gaba na ne ya fadi tino danayi naga text din aunty saudat a waya ta,itama tanason meatpie dashi zatayi dinner gashi kuma yanzu lokaci yakusa qure wa inda Allah ya taimakeni ma akwai means meat a fridge..... "Ko bakiji bane?" Ta fad' a sound so harsh
"To aunty" nace tareda shigewa toilet din wanda nidai a iya dubana na tsanaki babu abunda toilet din yayi, saboda dasafe na wankeshi kuma ita kadai take using abunta kawai tsabar mugunta da son sanya aikin.


Agurguje na gama mata na fito tareda shigewa kitchen din da yake main falour din na gasa ma aunt saudat meatpie din tareda hada mata meant juice,saboda nasan k'a'ida duk dare saita sha shi,wai saboda batason tayi k'iba. Fitowa nayi tareda zuwa na sake wanka, nayi alwala na kabbara sallah tinda anriga anyi magriba ban tashiba saida akayi issha'i,

na fito da niyyar zuwa inyi serving dinsu wajen cin abincin da ummata ce ke girka masu wai basu iyacin abincin kowa dagani sai na ummana shiyasa ma mu dakinmu daban ko acen boys quarters din masu girkama 'yan cikin gida abinci da gyara masu sashensu, wannan ka'ida hajiya kubra ce ta sanya ta dole dukansu suke haduwa, wajen yin breakfast da dinner ko da kuwa Alhaji Mustapha na nan hardashi ake haduwa wajen cin abincin

Ummana ce ta katseman hanzarin barin sashen namu da nakeyi "mamana ga abincinki nan kizauna kici naga yau kaman a gajiye kike ni zanje na zuba masu abincin" ta fad'a tana mai kallona cike da tausayawa saboda tasan irin yanda yaran gidan ke gallaza man ta wajen sanyani girkinsu da aikace aikacensu na babu gaira babu dalili,
"No umma banason ayi maki abunda zai bata maki rai, ko kinje zasu maki wulaqanci ne kiyi zamanki yanzu zan dawo ai YaAmeen yana nan basa min wulaqanci sosai in yana wajen jiya ya dawo k'asar kinsan" nafada ina kamo hannuwanta, gyada man kai tayi tareda cewa "Allah yayi maki albarka d'iyata yanda kikeyi man Allah ya baki maiyi maki kema ya baki miji nagari, kicigaba da hakuri watarana sai labari" "to umma nafada" tareda wucewa ina cemata "kije kici abinci kisha magani ki kwanta yanzu zan dawo insha Allah" "to" tace tareda komawa dakin namu, nikuma na wuce dasauri domin nasan suna cen suna jirana.



Ilai kuwa a zaune na tadda su a dinning area din dayake yakusa girman wani qaramin gidan, kaitsaye kitchen din da yake cikin dining area din na shiga tareda kinkimo manyan warmers da plates plates nazo ina jerawa, har na gama na fara serving dinsu ko kallon fuskokinsu banyiba, saboda nasan ko kalla nayi saqon harara ne zan samu, masalan daga 'yan matan gida buyu kyawawa da suke jin Kansu babu ya su a fadin Nigeria, shagwaba kawai suke zubawa, yayinda Hajiya kubra ke biye masu tanata murmusawa irin na manyan hajiyoyi da suka yarda kuma sukejin sunkai ko ina, labarinsu ya baza ko ina a fadin qasar tamu, abie ne ke latsa waya abunshi ta bangare daya yanada kyalkyala dariya, shi ko YaAmeen baima wajen, ahaka na gama serving nasu nayi masu sallama zanbar wajen,

Ya shigo fuskar nan tashi murtuk kaman kullum yake takowa cike da izza da kamala kai kace dandan sarkin kano ne sanusi lamido🤪

"Suhan zo kiyi serving YaAmeen" dayake itama hajiyar haka take kiranshi dashi......"No am ok green tea kawai zansha" ya fada kaman bayason magana yayinda sauran qannen nashi duk suka natsu suna cin abincin su bayan sunce "bigboo u are welcome"

"OK ki jira mu gama ki tattara wurin" ta fad'a tana mai faracin abinci, "to Hajiya na fad'a ina mai dan rissinawa irin na biyayya sannan na juya na wuce babbanb falo domin jiran su gama din tinani fal araina, " Saudat had'a man Lipton din" naji ya fad'a daidai lokacin da nake idasa ficewa daga dining area din.


Sun shafe awa biyu kafin duk suka tashi tareda yima juna sallama hajiya ta haye sama inda abi ya shige sashenshi suma su nihal suka shige nasu sashen sai kuma Allah ya kaimu.

Tattara plates din nayi nakai kitchen na juya zan koma dauko sauran, naga ya shigo da wasu bance komai ba saima dukar da kai danayi na jaye na bashi hanya ya wuce cikin kitchen din nima na fice dan dauko wasu, ahaka ya tayani kwashe kayan dukda hankalina bai kwantaba saidai nasan cewa hajiya na iya saukowa taganshi aiko da na kade har buzu na, bansan me yasanya shi aikata hakan ba yau lokutta dadama naga ko kallo ban isheshi in ka cire 'yan kwanakin nan da yake yawan bina da ido, shima na dauka hakan na da nasaba da tausaya wa duk wani mai aiki ne na gidan daidai da masu sharar lambu, nikau ta bangarenta baisan wata irin kacha bace yake sanya wa yana daure illahirin jiki da jijiyoyon jikina ba,ba bazai hantareni ba amman ko kallo ban isheshi ba, babu fuskan tambayan yasanya naja bakina na tsuke, na isa wajen sinc din ina dauraye abun da suka b'ata naji maganar shi a bayana don har ga Allah na dauka ya fita.

Wannan tasanyani zabura na juyo mamaki fal a raina wanda har saida ta bayyana fuskana

Wace irin mai sa'a ce yau ni?🤩 ni suhan ce yau YaAmeen ke cewa zaiyi magana dani? Tau wacece irin magana? Kodai wani laifin nayi mashi? Kodai bai hakura ba dazu dana tureshi? Ko dai........"Ko baakijii ba ne? Nace inaso muyi magana"
ya fada hankali kwance da maganar nan tashi ta rowa da muryarshi mai kama da goge a cikin kunnen 'yanmata

"Too yaya"
na fada a ahankali cikin dardar tareda juyowa na fuskanceshi zuciyata kaman za tayo tsalle ta fito waje, saboda tsabar kad'uwa

Guntun murmushi yayi iya lebo shi aganinshi nan ya k'okarta hakan sai tasanya kyaun shi ya k'ara fitowa afili kasancewar ba halinshi bane ko da murmushin amman ko baiyi ba kyaun shi na d'aya daga cikin abunda ke fizgar yanmata. Kallona yayi na tsawon second biyu, gamida gyara jinginar da yayi da cabinet ya motsa bakinshi ahankali kaman mai maganar saidawa ya fara da cewa.........




~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.


*Page* ~4~


°^^^^^^^^^^^^°

"Ajinki nawa a makaranta?" Ya jefa man tambayar bazata.

A d'an firgice na dago ina kallon shi, gami da ɗan zaro idanu na, da sau da dama na sha jin ana cewa kaman na mai jin barci amman suna da girma sosai,tambayar ce ta zo man a bazata, ko da alama ban taɓa kawo tinanin magana makamanciyar irin wannan zata iya shiga tsakaninmu ba;

"na'am, ni?" Na Maida mashi da tambaya a ɗan firgice kuma cikin sigar mamaki,

Shiru yayi na wani lokaci, kaman ma baya da alamar sake tanka mani, nikuma alokaci guda tambayoyi suka ziyarci kwanyata, har banma san mun shafe kusan minti biyu a haka ba, Yayinda shikuma ya kafeni da idanunshi masu kama da na wanda soyayya taci ta cinye😜
"Banjin akwai wani da nake magana dashi a kitchen dinnan da ya wuce ke; Ai ina tinanin mu biyune kadai a nan ko?"

Ya faɗa a gajiye kaman, wanda akeyi ma dole, "Na gama makaranta. "

Na fada a gajiye ciki-ciki ina mai gyara tsayuwata, Tare da janyo hijabi na, na rufe gefen fuska ta, saboda kallon da yake yi man yana distracting din attention dina;

Jina nakeyi kaman a gaban miliyoyin mutane, kai gara ma ace a kotu nake, da sainafi sake wa, Da ace a gaban mutum nake kaman YaAmeen muna magana dashi one on one.

'Yar guntuwar dariya yayi, "Wow kina fadin har kinyi degree da masters, A hakan nan yanda kike yar mitsitsiya?"

Ya fada yana mai nuna ni da duk kan hannun shi yana sama da ƙasa da su saitin Inda nake tsaye, Da wani yanayi, wanda nidai nakasa ganeshi; don bazance zaulaya ba don nasan ba halinshi bane yin hakan.

Sai a lokacin nagane kuskuren danayi,dan zaro idanu nayi alamar wayyo Allah, Gami da Jan sauran hijab dina, na ruge fuska ta ruf, ina dan mai sakin ɗan k'aramin murmushi;

A hankali nace, "am sorry secondary nake nufi yaya"

"OK good " ya fada a gajarce, Yana mai ƙara nazarinta, ko buƙatar da yake da ita zata samu karb'uwa awajenta?

"Ina so kici gaba da makaranta, domin zaman ki a haka kina wahala ba abune mai dad'i ba; ko babu komai ilimi yanada dadi, zaki taimaki kanki ki taimaki ummanki" Ya tsagaita yana mai zura mata idanu da ke taimakawa wajen ƙara ruɗa ta; Domin yaga yanda zatayi, Nikau bansan lokacin da nabude fuskata ba gabaki daya, ina mai sakin murmushi har siririyar wushiryar dake saman hakora na ta bayyana.

"amman kije ki shawarci ummanki, kuma ina so maganar ta tsaya iyakar ni, da ke, da ita; Don bana so wani ya sani kaf gidan nan, idan ta yarda sai ki kawoman takaddunki, da kuma zabin makarantar dakikeso kiyi da abunda kikeson karantawa, kibar sauran maganar a hannuna. Kome zamu ji, ko zaku gani, Ku kauda idanunku gabaki daya, Babu ruwanku a ciki, Ni nace zan yi, kuma insha Allah zanyi;"

Yana gama fadar haka ya juya, Yana mai barin tanqamemen kitchen din, da kai ka rantse da Allah ba'a Nigeria yake ba.

Dakallo na bishi, a yayin da kwalwa ta ta cunkushe,

"tabbas tabbas mafarkina zai tabbata, tabbas lokaci yayi; Alhmdllh naketa faɗa, a cikin raina, saboda na ma rasa tinanin da zanyi, bayan wannan; Juyawa nayi, gami da ci gaba da aiki na.

A gaggauce na gama na rufe kitchen din, gami da barin part din baki daya zuwa namu, Amman zuciya ta cike da tarabbabi, domin nasan halin umma ta, Sannan ni na san kafin in dosheta da maganar, Sai nayi nazarin abunda zance mata tukunna, Don na san ta da gudun duniya da abunda ke cikinta balle wulaqanci irin na hajiya kubra.

Ko da na isa part din namu, Na tadda umma ta, tasha magani amman takasa yin barci, saboda taga na dade har wajen karfe goma da wani abu, Alla Alla take yi, ya kasance lafiya, Gashi ko abinci na ma ban ciba, ina shiga kuwa na taddata zaune bisa sallaya.

Allah sarki umma ta, Mace kamila mai gudun duniya, Mace mai ibada, da rashin hayaniya, Amman dukda wannan halin nata, hakan baisa Hajiya kubra ta ɗaga mata ba, Ni gani ma nakeyi kaman babu wad'anda ta tsana irin mu acikin masu aikin dake gidan, Wanda munfi mu goma sha wani abu, ummata ce ta katseman saqa da warwarar da nake tayi cikin zuciya;

"lafiya dai ko mama na?" ta faɗa tana mai miƙewa a hanzarce, sannan ta ci gaba da magana cikin dan firgici kaɗan; "Naga dare yayi sosai, ya kamata ace yanzu kin kwanta ki huta hakanan"

Ta faɗa cikin sanyinta, mai sanya ni natsuwa, duk da a ɗan firgice take; Kome nake yi, ko ban fad'a ba, son da ummata keman yafi wanda nakeyi mata, Duk da kau a duniya babu wadda tafi soyuwa a raina kamanta, Tinda ita kadai na sani, ita kadai na tashi na gani , ita ce uwata, itace ubana, ita ce yayata, abokiyar shawara ta kuma, ta fanni daya kuma abokiyar wasa ta;

"Ina hankalinki yake ne ummina? Ina ta magana kinyi shiru" ta faɗa tana kamo hannuna, bansani ba ashe har ta nade abun sallar ta iso inda nake tsaye daga bakin ƙofa a tokare.

"Umma saida najira suka gama sannan na wanke kayayyakin kinga gobe in Allah ya kaimu mun rage aikin;" na faɗa, ina mai kama mata hannu nima, muka zauna gefen katifar tamu dake yade a tsakiyar dakin.

"ga abincin ki tau, maza kici ki kwanta, kinga karmu makara gobe dasafe in Allah ya kaimu banaso kullum muke b'atawa hajiya rai;" ta faɗa tana jawoman kwanon abincin.

Kwanon silver ne amman tsaf yake, kaman sabo sai sheqi da walwali yake yi, kaman yau aka budeshi a leda, Allah sarki ummana akwai tsafta, dakin namu ma sai k'amshi yake yi, an goge tiles dinnan sai daukar ido yake yi, abunka ga fari, dakinmu tsaf yake babu tarkace da karikitai, in ka cire katifarmu, sai labulaye da wani teburi a gefe, inda muke ajiye daddumar sallah tamu, da sauran litattafan addini himili guda, kasancewar ummata tayi karatun addini mai zurfi, sai take k'araman duk bayan sallar subhi, akwai wardrop ta bango a dakin, wannan shi ya tak'aita mana tarkace, tinda ba yaro ke garemu ba, kwata kwata ma babu yaro a gidan, kowa da locar ta inda ni biyuma ke gare ni, kasancewar guda uku ce a dakin, amman ajere suke, sai ummata ta dauki daya, tabar man biyu saboda ni budurwa ce zan fita karikitai.

Abincin naci, naje na daurayo bakina na cenza kaya zuwa kayan bacci, muka kwanta umma tayi mana addua muka shafa kowa ya juya cikeda tinani kala kala.

Nikam ta bangare na banyi bacci ba, amman ummana tayi baccinta saboda maganin da tasha, kuma ko ba hakaba, ita bata kwanciya da damuwa ko haushin wani a ranta, takance ba'asan gawar fari ba hakanan kaje lahira da haushin wani duk abun da gaƙuri bai bayar ba ai rashin shi baya badawa.

Gari na waye wa muka gama komai, kama daga salla, karatu, da wanka; zuwa karfe bakwai, kowa yayi shirin fara aiki kaman yanda yake a al'adar gidan namu. Amman mu bamu kai ga fita ba, sabo da ƴan cikin gidan ma basu kai ga tashi ba, kuma ina so in yima umma ta maganar karatu na; sai dai ina zullumin tunkararta da maganar, sabo da na san halin umma ta sarai, wani d'an qaramin yak'i ne gabana, Amman duk da haka hakanan zan daure in tunkareta da maganar domin ga dama ta samu, kuma ko ba komai hakan ci gaba mu ne ni da ita baki daya, fata na dai da addu'a ta Allah ya ɗora ni akan ta, ta yadda ta amince mani, sabo da wannan karon ina tsoron YaAmeen ya ji haushi ya janye burin taimakon mu a ranshi, saboda ba wannan ne karo na farko ba da umma ta ke daƙile shi akan duk wani burin taimaka mana da yake yi, Wanda shi a ranshi har ga Allah taimakon ummana din ne kan ingiza shi ga hakan saboda rashin hayaniyarta da biyayyar ta ga iyayen nashi.

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.



*Page* ~5~


°^^^^^^^^^^^^°


Bayan mun gama karyawa ne, muna zaune a ɗaki ni da umma ta,Tana yanke farcen ta na hannu, Yayin da ni kuma nake zaune gefen katifar tamu da littafin hisnul musleem a hannu ina karantawa.

Rufe littafin nayi tare da maida shi ma'ajiyar shi, na dawo na zauna daf da ita, tsawon second biyar na dauka ban iya cewa ƙala ba, tabbas abinda nazo mata dashi ni kaina na san mai girma ne, to sai dai ba yadda na iya, shahada nayi na bude baki na a hankali nace;

"Umma don Allah ina so muyi magana dake" cike da mamaki ta ɗago idanun ta tare da tsare ni da su, take guntun tunani yazo a ranta, wacce irin magana ce wannan da maman tata bazata iya tunkararta kai tsaye da ita ba? Koma dai menene tana fatan ɗiyar tata ba zata zo mata da wani abu akasin tunani nata ba;

"ina jin ki mama na" ta bani amsa tana mai dakatawa daga yanke farcen gami da sauke hannun kan cinyoyinta.

"Umma don Allah ki saurare ni kuna ki fahimce ni, wannan karon izinin ki nake nema; ki duba halin da mu ke ciki na rashin sanin madafa, dama ce ta zo mana da zamu fita daga cikin wannan ƙangin bautar da mu ke ciki, dama ce da zata sanya mu dogara da kanmu har ƙarshen rayuwarmu."

Tinda na fara magana ta tsira man idanu ba tare da tace kanzil ba, sai dai ni bazan iya karantar abunda ke cikin zjciyar tata ba;

Ganin yanda ta kafe ni da idanu ya sanya ni sauke kwayar idanu na ƙasa ina mai murza yatsu na suna bada sauti ƙas, ƙas.
" Uhm, ina jinki mama na, wannan wacce irin dama ce?

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment