Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma zama da ita"

Ganin kaman abokin nashi ya zare be, ya sanya ce ma sauran abokan angon su koma motoci su, ba matsala yanzu zasu gyara

Suma dai basu kai ga fahimtar inda kalaman abokin nasu ya suka dosa ba, suka koma mota jiki ba kwari, inda sukayi ma motoci key suka sake ɗaukar hanya.

Shima Bilal tada motar yayi yana mai girgiza kai yake faɗin "you are not fine gaskiya friend, baka da lafiya ga dukkan alamu, Allah dai yasa ba stress bane ya kama ka."

"Ba wani Stress Bilal, I AM Al'ameen Dambulan, and I am fine is u can see"

"Girgiza kai Bilal yake" Kafin ka ɓata mani rai, zaifi kyau kayi shiru kawai friend, hawa ba fashi kaman yanda dinner ma haka babu fashi insha Allahu, yanzu haka ma nayi waya an gama shirya komai, kawai isar tamu ake jira.

Cikin serious tone Al'ameen ya shiga kallon ya Bilal, sai kuma ya fara magana cikin ɗaga murya *"NACE BA ZANJE BA KUMA KAI BAKA ISABKA SANYA NI INYI ABUNDA BANYI NIYYA BA BILAL, U KNOW WHO I AM, BANA MAGANA BIYI, DON HAKA SAI KUJE KU KUYI TA YI, AURE DAI NE NA FAƊA DA BABBAR MURYA CEWAR NAYI NADAMAR YINSHI SAI KUMA YAYA???"*




~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



Zikiri in an zauna a wani Majalisi

Ibn Umar ya ce; an kasance ana kirgawa ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majalisi guda kafin ya tashi, yana cewa sau dari.
رَبِّ اغْفِرْ لِي، وَتُبْ عَلَيَّ، إِنَّكَ أَنْتَ التَّوَّابُ الغَفُورُ.
Rabbigh-fir lee watub 'alay, innaka antat-tawwabul-ghafoor.

Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ka yi tuba a gare ni. Lallai Kai ne Mai yawan karbar tuba, Mai yawan gafara.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~62~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



Ai sai jikin shi yayi sanyi kuma ya shiga bin Al'ameen ɗin da kallo, wanda idanun shi kulle yake ta surfa bala'i.

Bai kuma ce mashi ƙala ba har saida yayi ya gama, ya koma yana mai jingina da ma karin kujera cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya kaman wanda yayi uban gudu.

Maida hankalin shi yayi akan tuƙin da yake yi, bayan ya janye idanun nashi da suka fara cenza kala daga kan abokin nashi.

Allah ma yaso suhuɗu ne kawai cikin motar, shi da Al'ameen a gaba, sai Abir da Sadeeq ɗin Hafsat a baya.

Motar ta ɗauki tsit na wani lokaci.

Sai cen ne Bilal ɗin ya kuma nisawa yana mai cewa "Friend you am very sure you are not in your mind, defenetly akwai Abunda ke damun ka, ni dai nasan baka shan komai balle ince ko ka kurɓa ne..."

"Wuta nasha, Kaga Malam kada ka sake man maganar da ta shafi yarinyar nan, kada ka tunzura ni, ince a maida ta gida"

"What?" Bilal ya tambaya cikin wani irin mamaki. Anya kan abokin nashi ɗaya kuwa? Ta baya yana iya hangen jerin motocin abokan nashi na ta sharara uban gudu, saboda su isa da wuri a fara shirya Abunda za'ayi. Girgiza kai kawai yayi, haƙƙun Al'ameen fa na neman dagula komai, to indai ba aljani bane suka kama abokin nashi ba, shi bai san ma me zai kira hakan ba.


Abie dake baya shi kanshi kulle yake, yana ce ai Yayan nashi ne ya nasta akan sai ya auri yarinyar, a yanda yake samun labari, to in ko haka ne lallai ba banza ba, ruwa baya tsami banza, bai san halin da Mom ke ciki ba game da auren, hakan ya sanya sai bai tanka ba, kawai ya ɗauko wayar shi ya shiga rubuta ma Mom saƙon halin da ake ciki.

Shima Sadeeq mamaki yake yi sosai, to ai in yanda Hafsat ke faɗa mashi gaskiya ne, bai ga dalilin Al'ameen na yin hakan ba, Al'ameen da yake mai halin dattako irin na manya.

Aiko sai ga kiran Mom ya shigo wayar Al'ameen ɗin.

A hankali ya ɗaga wayar, yana mai lumshe idanu, bai ga dalilin bijire ma Mom akan maganar auren ba, gashi tin kafin aje ko ina yarinyar ta fita a ranshi, ko sunan ta ma baya son a ambata mashi.

"Idan kun iso ka shigo ina neman ka da gaggawa"

Mo ɗin ta faɗa cikin ɗaga murya da tashin hankali sosai. Tana jin zata iya saɓa ma Al'ameen muddin yace zai kawo tangarɗa ga kasancewarta Surukar masarautar da take da tarin girma da ɗauka ka.

"OK Mom" Abunda ya iya faɗa kenan, ya zare wayar a kunnen shi, yana mai sauke wata ajiyar zuciyar, ya tabbata kiran Mom ba zai wuce ƙila ya rabu da yarinyar ba, inko haka ne, babu Abunda zai hana shi yi mata biyayya a wannan karon, Sam basu dace da Suhan ɗin ba, shi bai san ma menena yaja ra'ayin shi akanta ba.


Cikin tashin hankali Mom ta sauke wayar a kunnen ta, sai kuma jikin ta ya ɗauki ɓari, kadai ace aikin Malamin su Hajiya Sa'a ne yayi aiki.

Cikin rawar hannu ta shiga latso number ɗin Hajiya Laila, tana mai gangarowa daga saman ta, ta ratso ta cikin jama'a manyan mata da ake zazzaune a fali nata suna ta zuba isa.

Part ɗin Alhaji ta nufa kai tsaye, tana mai buɗewa ta shige.

"Hello Laila, kuna ina ne? Kun kusa ƙarasawa ne?"

"Uwar ango kenan, eh bai fi saura awa guda ba, mu ƙara so, Lafiya dai ko?"

"Ina fa Lafiya Sa'a, aikin malamin nan wlh ya fara aiki akan Son, please ya za'ayi, ki sake kiran shi fa akan ya warware komai, yanzu na gane kuskure na, bana so wani abu ya kuma ɓullowa, tinda na gwada ma kowa na amince sai a cigaba da tafiya haka, ni yanzu ko da KUNYAR alhaji ma aka barni ai na sha ta."

Ɗan waiwayawa Hajiya Sa' a tayi, ba ita kaɗai bace cikin motar, infact ma harda Ammin Sir Salim.

" Kinga Hajiya Kubra, ki bari idan mun ƙaraso ma tattauna, yanzu muna bisa hanya ne"

Jin haka daHajiya Kubran tayi ne, ya sanya ta gane cewa ba Hajiya Laila ɗin kaɗai bace a motar.

"To shikenan Allah ya kawo ku lafiya"

Ta faɗa tana mai katse kiran, sai kuma ta koma bisa sofa ta zauna, tana mai maida numfashi, zaman ba zai yuwu ba, ta miƙe ta shiga kai komo. Sanin da tayi ya zuwa yanzu ana cen ana neman ta ne, ya sanya ta fitowa jiki babu ƙwari ta koma sashen nata, saida ta biya sashen su Kaka zuwaira tayi masu ɗan yaƙe haka tana mai sanar dasu kusan ƙarasowar amaren.

Da wani irin kallo suka bita, "uhmm to Allah ya ƙaraso dasu lafiya" da Abunda ƴan kankiyr suka bita kenan, suna mai jinjina hali irin na Hajiya Kubran, ta raina ma kowa wayau, gani take ita kaɗai ce ƴar bokon da zata yi masu wani ilaye duk cikin su babu wanda bai san bata son auren ba, yanzu haka wani munafuncn ne ta kuma ɓullowa dashi, tinda ko da safe tana ta ruwan bala'i da masifa, dandai basu kula ta bane.



******




Ni kau ina ƙumshe cikin alkyabbar da aka yafa mani, zufa nake ta haɗawa, duk kuwa da Ac ɗin dake busowa ta cikin motar, har ƙarƙashin kujeru, ma'ana wajen ƙafafun mu.

Nasihar Su Umma kawai nake tunowa. Tabbas Umma tayi gaskiya, yanzu ba da bane, duk Abunda na gani wannan haƙurin da na saba shi zan cigaba da yi, domin yanzu ne ma zanyi haƙuri, saboda na kuma komawa ƙarƙashin inuwar mulkn ta.

Gabana ke tsananta faɗuwa bansan dalili ba, ko zullumin shiga gidan ne nake? Tinda indai ta Ya Ameen ne bana jin shi, ya zuwa yanzu na gama gazgata irin ɗinbin son da yake mani, nima da wanda nake mashi. Na sha alwashin bashi dukkanin wata kulawa da soyayya ta, domin Ya Ameen ya wuce cencentar hakan a wuri na. Lafiyayyar rayuwa aure nayi niyyar shimgiɗa mana, mai cike da ƙauna, da zallar soyayya ta kula da tattashi.

To inko haka ne, menene dalilin da yasa zan zullumin wani abu. Ba Hajiya Kubra na aura ba, ba kuma da ita zanyi Rayuwar aure ba, balle su wata Nihal cen da Saudat.

Addu'a na cigaba da yi ɗauke a baki na, domin dai duk yanda naso in kauda wani zullumi, har yanzu zuciya ta ci gaba take yi da bugawa.

Zna iya hangen motoci reras a gaban mu da bayan mu, wai duk ni za'a je kaiwa ɗakin nawa, to wannan wane irin gata ne kuma ban samu ba? Murmushi na saki, ina mai sake tunowa da cewa nan da zuwa gobe fa mun zama abu ɗaya da Ya Ameen ɗin.

Hakan ta sanya ni sauke hamdala da wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, ina tuno moment da wasu kalamai da yake faɗa mani, masu cike da alƙawurran zaman lafiya da ƙaunar juna.


*******


A Masarauta kuwa ya rage daga Umma sai sauran matan sarki da haɗimmai.

Har yanzu akwai ɗinbin jama'a, ana ta cigaba da shagulgulan biki, duk kuwa da cewa an tafi kai amarya, Amman duk da haka wasu mutanen ne ke sake ɓulɓulowa.


Manyan Motoci ne guda biyu ƙirar 4matic, baƙaƙe sal, suke tafe cikin masarautar har suka samu wurin da suka yi parking.

Da kallon mamaki yake bin cikin masarautar, da gani dai wani abu ne yake faruwa, kaman wata hidimar akeyi, to Amman in haka ne kuwa shi yayi mamakin da babu wanda ya sanar mashi, ko kuma iyaln nashi, tin da ya shigo garin yaga alamun ana hidima, jama'a sia hada hada akeyi, ga manyan motoci da suke ta shiga da fita, a hanya ne ma yaci karo da motocin shugaban ƙasa sun riga sun wuce, hakan ce bai samu damar tsayawa ya kai gaisuwa ba.


Fada ya nufa kai tsaye, to babu kowa dai ciki, da gani tau ba'a zaman fadancin ne, kai tsaye ya wuce zuwa babban falon sarki na cikin gida, haɗimmai da fadawa sai zubewa suke suna kai gaisuwa, yana mai ɗaga masu hannu cikin isa da taƙama.


Shigar tashi ne ya sanya kowa miƙewa, banda Mai martaba, to shima dai duk manyantakar shi saida ya isa gaban mai martaba ɗin, yana mai duƙawa ya shiga kwasar gaisuwa.

Cikin sannu da sauka mai martaba ke mashi magana, inda ya shiga bashi haƙuri akan abubuwa sun faru da yawa masarautar ba tare da an sanar mashi ba, hakan ya faru ne akan abubuwa sun zo ne a ƙurarren lokaci.

Har yanzu dai bai gane inda kalaman sarkin suka nufa ba, matsa mashi akayi gefen sarkin ya zauna. Inda mai martaba ya sallami sauran fadawan dake wurin, saboda yana so yayi bayani, kuma ba hurumn su bane.

Saida duk suka kwashi gaisuwa suka fita, sannan ne mai martaba ya gyara zaman shi a hankali yana mai fuskantar waziri.

"Mai girma waziri, muna maka maraba da sauka, kuma muna mai baka haƙuri a bisa rashin shaida maka dawowr hasken masarautar, hakan ya faru ne kaman yanda na shaida maka cewa abubuwa ne suka zo a bisa ƙurarren lokaci, idan zaka iya lura ma tau masarauta tana cikin hidima ne, a bisa auren yarinyar hasken masarauta da akayi, watau Gimbiya Merama"

Duk wannan bayanin yana yi mashi ne a rausashe, saboda ko ba komai Wazirin yayi sa'a da mahaifin shi.

Cikin tsabar kaɗuwa da ɗimbin mamaki Wazirin ya ɗago yana maibkallon mai martaba ɗin.

"Allah yaja zamanin ka, kace fa Merama ta dawo?"

Gyaɗa mashi kai mai martaba ya shiga yi.

Nisawa yayi yana mai cewa "amma Allah ya taimake ka, ka taɓa ganin inda matacce ya dawo? Sanin kowa ne anan cewa Gimbiya Merama ta daɗe da shuɗewa tsawon shekaru, to kuma tayaya za'a ce wata ta bijiro da sunan ta? Anya kuwa mai martaba wannan maganar ba abun dubawa bace?"

Ɗan murmushi mai martaba ya saki, na daga cikin abunda ya sanya bai cika saka waziri a hidimar tashi ba kenan, shi tsoho ne gaddamamme, ga nuna isa da iko, wani lokacin har sarkin ma yana nuna mashi cewa shine gaba dashi tinda yayi sa'a da mahaifin nashi, kuma shine ma yayi ma mahaifin Sarkin waziri a zamanin shi, tin tsohon mai martaba ma yana raye.

"Wannan magan taka haka take waziri, Amman al'amari ne da yake buƙatar dubawa a tsanaki, Amman Gimbiya Merama don ita, ita ce fa, saboda haka ne, muke so idan an gama shagalin bikin nan zamu zauna da ita mu tattauna, yanzu haka tana cikin gidan nan"


Shima cikin wata kaɗuwr ya shiga cewa "ba komai Mai martaba, Allah ya sanya muji alkhairi, Amman abun da mamaki da ɗaure kai kam, ni zan shiga cikin gida saboda in samu in ɗan huta, a tashi lafiya" ya faɗa yana mai kuma russunawar ya miƙe gami da ficewa.

Da kallo kowa ya shiga bin shi a fadar, wannan fa fararren abu bane, hasali ma kowa ya saba da hakan, shi fa duk Abunda za'a kawo maganar shi sia ya ja da ita, gashi da mugun son kanshi, shi yau bai ƙi ace an naɗa shi sarautar ba ma gabaki ɗaya kuma kowa ya san haka.

Cikin gida kuwa tin da labarin dawowr Wazirin ta karaɗe, abun ka da gidan sarauta,labarin yaje har kunnen Umma, tin a lokacin ne aka rasa gane kanta, daga baya ma ɗakin ta cen ƙurya ta shige, tana mai cewa ayi mata haƙuri kanta na mata ciwo, Amman a zahirin gaskiya koda ta shige kuka ta shiga saki mai cin rai, gani take kaman mahaifin nata ma zai dawo, duniya babu gaskiya, zata ga da wane ido waziri zai iya kallon ta ya gaya mata wata magana, tinda ta samu labarin abokin cin mushen nashi ya daɗe da gushewa, sai shi kaɗai aka bari yana watayawa a duniyar, ba tare da abunda yake so ya samu ya samu ɗin ba kuma.


*******

Suna isa ya ɓalle murfin motar yana mai ficewa, ko parking Bilal ɗin bai gama yi ba.

Kai tsaye cikin gida ya nufa, babbar rigar ma yana tafe yana zare ta, har ya gama, daga shi sai fara ƙal ɗin shadda wadda rigar take iya cinya da wandon kayan. Shaddr ta haɗu, ta ji ɗinki sai walwali take yi.

Mutane sai magana suke mashi "ango kasha ƙamshi, ran ango ya daɗe, masalan ma abokan wasan su na kankiya. Ba wadda ya tsaya kulawa balle ya bata amsa, fuskar nan tashi haɗe kaman an aiko mashi da saƙon mutuwa, duk da haka bai gusar da kyau da walwali da yake yi ba. Ga gyaran fuska da tasha abun sai wanda ya gani.

Haka ya tsara falon, babu wadda ya gaida cikin matan dake zaune falon.

Hayewa yayi sama, yana mai tura ƙofar ɗakin mom ɗin, tana zaune ita da wasu manyan mata da suka taho ƙafa da ƙafa tin daga Katsina yi mata murna, da taya ta murnar cewa ta samu suruka ƴar gidan manya.

Kaman zaki saidai ta ganshi cikin ɗakin nata tsulum, matan da basu san meke faruwa bane, suma shiga washe baki suna faɗin "a'aha ai gama angon nan ya ƙaraso, ango ya hidima?"

Ba wadda ya kalla still cikin su.

"Mom gani kince kina nema na?"

Itama miƙewa tayi cike da kaɗuwa da ruɗu tace "Eh kaje sahen Dad ɗinka ka jira ji, ina zuwa yanzu bari in sallama baƙi, aunties ɗinka ne, baka san su ba? Ka gaida su mana"

Ɗan waiwayowa yayi, yana mai gaishe su, har yanzu fuskar nan haɗe, su kuwa washe baki suka shiga sake yi, kaf cikin su ba wacce bata yi ma ɗiyar tata sha'awr Al'ameen ɗin ba, saboda babu wadda ba zata so ya zama aurukin ta ba. Kuma sun ɗauka hidimar biki ce da jama'a suka hana shi walwala.

Juyawa yayi ba tare da ya ko jira amsawr su ba ya fice, gangara wa yake daga bisa matakalar benen da uku uku. Nan d anan ya fice daga dakin kaman kububuwa, to suma sauran matan da kallo suka kuma bin shi, suna ayyana ma ransu cewa anya kuwa lafiya?


Part ɗin Dad ɗin yayi ma tsinke, yana mai zare farar rigar shadda ɗin, ya rage daga shi sai farar singlet da dogon wandon shaddar.

Kan Sofa ya zauna, yana mai ɗaukar remote ɗin Central Ac dake ajiye bisa stool ya shiga ƙara mata gudu.

Ji yake duk duniya ta mashi zafi, babu Abunda ke mashi daɗi, kaman ba shi ba, kaman ba Al'ameen da yake awanni da suka wuce cikin farin ciki ba.

Zamewa yayi ya kwanta samɓal, yana mai ɗora hannun shi ɗaya bisa fuskar shi, ɗaya kuma ya daɗe saitin zuciyar shi da yake ji tana habawa da matsanancin duka kaman zata tsago ƙirjin nashi ta fito.

Shigowar Mom ce tayi sanadiyyar tashin shi zaune.

Da sauri ta ƙaraso kusa dashi ta zauna, tana mai ɗan rungumo shi zuwa jikin ta.

"Son baka lafiya ne?mr ke damun ka?"


"Mom lafiya ta lau, saidai kawia ina so a fasa wannan auren ne, kije ki sallama kowa mom a shirye nake da inyi maki biyayya kaman yanda kika buƙata a cen baya"

A zabure ta tashi tana mai matsawa daga inda take zaune riƙe dashi.

Zuciyar ta na ta habawa "son kada kaja in kwaɗa maka mari fa, kada ka ja in maka mummunr magana wallahi, wane irin a fasa bayan an riga an ɗaura? Ya ne banyi dakai ba akan a faɗa ka kafe, sai yanzu da na riga na yarda har na tara mutane kace wani a fasa? Daga ina wannan tunanin yake?"

Itama ta faɗa cike da nadamar, tana cewa aikin su ne ke aiki a jikin yaron nata.

"Mom nine nace ina son ta, nine kuma yanzu nace bana son ta, Mom ki kira Dad a warware wallahi na fasa, bana jin son yarinyar ko ɗaya a zuciya ta yanzu"

Cikin rawar hannu ta shiga latsa number ɗin Bilal, tare da ce mashi ya shigo sashen Dad ɗin, aiko sai ga Bilal a sukwane, domin suna cen har sun fara cenza kayan yin hawan takar angon, dawakan ma har an shisshirya su.


Da sauri ta ƙara sa inda Bilal ɗin ke shigowa ta riƙo hannun shi "Bilal abokin ka baya lafiya, kayi mashi addu'a please, wallahi ina tunanin aljannu sun kama man shi"

Cikin sauri ya ƙara sa ga Al'ameen ɗin da yake zaune dafe da kai, tallafe da fuska wadda har ta kaɗa tayi jajawur.

Da sassarfa ya ƙara sa wurin shi yana faɗin "Friend what happened? Talk to me now"

Zare tagumin yayi yana mai miƙe wa tsaye ya fuskanci Hajiya Kubra da Bilal, sannan ya shiga faɗin "Friend nothing to say, i have already said it! Ba zanyi ba na fasa, ai sai kuyi tayi, Mom ce da kanta tace bata so, and kuma na mata biyayya, ku kira Dad kawai kada su ƙaraso da ita nan gidan"

Yana gama faɗin haka ya saɓi rigar shi ya zura, yana mai zagaye su ya wuce.

Da kallo galala suka bishi.

Bilal ne ya juya ga Mom da tsantsr tashin hankali yake bayyane a fuskar ta.

"Mom kiyi haƙuri, ina jin akwai Abunda ke damun shi ne, zan san yadda zanyi dashi, Amman fa bana tunanin zai cigaba da bada goyon baya bikin nan ya cigaba kaman yanda aka faro shi, Mom ki natsu kada mutane su fahimci halin da ake ciki fa,i'ill tackle the isue"


Shima yana gama faɗin haka ya sanya kai ya fice daga palon, barin Hajiya Kubra yayi da tsantsar tashin hankali, yana tafe yana girgiza kai, wannan duk sharrin Mom ne, gashi kuma ta fara gurbar Abunda ta shuka, shi bai san ma dalilin ta na yarda da auren har haka ba, balle dan Al'ameen yace baya yi har zata ɗaga hankalin ta haka, koda yake abun a bayyane yake, cewa yanzu ta san ko wacece Suhan ɗin, ba zata taɓa yarda wannan damar ta kufce mata ba, tinda B a shi kaɗai ba, har abokin nashi da kowa ma yasan dalilin ƙin auren nata, inko haka ne ta tabbata mai son abun duniya, wanda nata ya rufe mata ido kuma tana hangen na wasu, shi tun da yake duniya ma bai taɓa cin karo da mace kaman Mom ba, ga zafin nema, ga wulaƙanta wanda basu da shi, idan ba zai manta ba, friend ɗin nashi ya sha mashi complain akan halin Mom ɗin tashi, cikin halin damuwa, har yana faɗin da akwai yanda zaiyi ya cenza ma Mom halin ta da yayi, shi dai baya jin daɗin Abunda take yi. To sai gashi yanzu abun ya rikiɗe zai fara affecting ɗin Abokin nashi, ba zai taɓa sanya sanya ba, har wankin hula ya kai su dare, shi ya sani, jikin shi na bashi da hannun Mom a faruwr komai, saidai yaci alwashin tsayawa ga abokin nashi har ya samu Abunda yake so, Mom ba zata taɓa zama tarnaƙi na farin cikin ɗan nata ba kuma abokin nashi.

Da haka ya ƙara sa inda auran abokan suke ana ta faman shiryawa, mai naɗi suka taho dashi sukutum daga masarauta saboda ya naɗa masu rawani na hawan da bar da za'ayi.

Ce ma abokan yayi su cigaba da shiri kawai, Angon baya da lafiya, Amman insha Allahu zai sha magani, idan ya samu sauƙi zai fito.

Da to suka bishi, basu kawo ma ransu komai ba, kawai dai Abie da Sadiƙ ne kawai zasu iya cewa sun fahimci me ke faruwa, shi kau Sadiƙ baya fata Hafsat ɗin taji wani abu, saboda halin da take ciki na tsohon cikin da har yanzu bata haife shi ba, domin dakyal take taka wa, tin da suka ƙaraso ma ta kasa fitowa, saidai shi ne ya shiga ya ganta kwance ɗakin Kaka Zuwaira, har tana mata faɗan shegen taurin kai ne ya sanya ta fitowa tana cikin wannan halin, ita fa sai taga ma kaman sonsomin naƙuda a tare da ita, Amman hafsat ɗin ta kafe cewa ita bata jin wani ciwo daban, idan ka ɗauke na yau da kullum irin wanda take ji.


Yana fita daga part ɗin Mota kawai ya faɗa, driving yake Amman Baisan inda zai nufa ba, idan ya tuna wai shine yau ake ɗaura ma aure, sai yaji wani irin daɗi, Amman cen Ƙasan ra shi haushn kowa ma yake ji, masalan da yaga garin ya ɗinke ana ta hada-hada, sai cin karo da mutane yake haye cikin kayan hawa bisa dawakai, da yaga haka yake ɗauke kanshi, ba sai an faɗa ba, hawan da bar nashi zashi.

Kai tsaye guest House nashi ya nufa, bai nufi na Dad ba, domin yanzu yana cen cike suna cin abinci shi da baƙin shi.

Ko da ya shiga ɗakin, bai ko tsaya cire rigar ba, haka ya faɗa saman gadon yana mai sauke ajiyar zuciya kaman yayi gudu.

Kan shi ke matuƙar sara mashi, shi baya ma jin idan nan da gobe zai iya barin gidan. Ya gode ma Allah da babu wanda yasan inda yake. Ya kai kusan minti talatin, sannan ya tashi yana mai faɗa wa toilet ya sakar ma kanshi ruwa masu sanyi, sai a lokacin ne kuma yaji wata ƴar natsuwa tana kama shi, saida ya gama wankan ne ya fito ɗaure da tawul, *innalillahi wa inna ilaihi raji'un* kawai yake

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment