Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaɓo wadda tayi daidai da ra'ayin shi, kada ya je yayo zaɓen tumu dare, kinsan matan yanzu ɗin yanda suke" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran.

"Haka ne Alhaji, sai ya duba cikin lokaci, in bai yi yanzu ba, sai yaushe? Ko so yake ayi mashi tare da Afnan ne? "

Ta faɗa tana mai goge baki da soft tissue dake ajiye gefe da gefen dining table ɗin, miƙewa tayi tare da faɗin Al'ameen ɗin ya biyo ta domin su rubuta Abunda za'a buƙata tare, gami da ficewa ta haye sama nata.

Al'ameen ɗin ne ya bita a baya, tare suka isa falon yayin da ta wuce bedroom ta ɗauki wata jotter mai kyau ta zauna ta shiga zana abubuwan da za'a buƙata cikin isa da taƙama, yayin da suka baro Alhaji Mustapha ɗin da sauran ƴaƴan nashi yana jin damuwoyin su, domin shi mutum ne mai yawan jiɓintar Al'aamarin iyalan nashi, dama kuma haka ake so, haka ya kamata ace ko wanne mai gida yana ma iyalanshi, komin girman shi kuma komin matsayin shi.


Bayan Hajiyar ta gama rubuta komai ne ta miƙa mashi, gami da cewa ya duba in da wani abu sai a ƙara, dubawa ya shiga yi cikin halin ko in kula da isar da mahaifiya tashi take ta zubawa, babu komai ya faɗa mata gami da miƙewa don barin ɗakin.

Dakatar dashi tayi, tare da ce mashi ya zauna zasu yi wata magana ne, zaunawa yayi bisa sofar dake kusa da tata ya bata dukkain natsuwar shi, domin shi mutum ne mai biyayya da son gamawa da iyayen nashi lafiya, shiru ne ya biyo baya na ƴan dakiƙu, domin ta san abun da zata zo ma ɗan ɗan nata ba lallai ya ɗauka ba domin ita ta haife shi, ta san halin shi sarai.

"Al'ameen watau na lura ka fiye shiga Al'ameen Suhan da maman ta, bana so fa raini ya shiga tsakanin ku, kuma da me suka fi sauran ma'aikatan gidan nan ne da kafi basu cikakkiyar kulawa, ko dan Kaga mahaifi ka ya ɗaure maka wutsiya ne? Tau fa ka sani ni bazan lamunta ba, tinda Alhaji ya ce a ƙyale su da aikin gidan, da ta samu lafiya ka faɗa masu su tattara su koma cen inda suka fito tinda ba zata faɗi ainahin daga ina take ba ita daƴar tata, kuma ina so ka samo mana kuku cikin ma'aikatan company ɗinka guda biyu, wanda ka san sun ƙware sosai, saboda Sam girkin talatun nan baya man daɗi" ta faɗa cikin muryar ta, da ta koma ta mulki gaba ɗayanta.

"Mahaifiyar tashi ya tsura ma idanu har saida ta kai aya, ba tare da ya katse ta ba, sannan ya muskuta ya gyara zama," Mom ina so ki sani, ni duk cikin ma'aikatan nan babu wanda na fifita, duka matsayi su ɗaya ne a wuri na, mom rashin lafiya tafi gaban komai, kuma ko da sun bar aiki, bana da hurumin korar su, kin manta ne dad yace gidan shi ne? Kuma ya basu izinin zama har zuwa lokacin da suke so, ko kuma suka gaji dan kansu, babu wanda zai hana su tafiya, so mom ina ganin wannan maganar yafi da cewa ku tattauna ta da dad, duk hukuncin da ya yanke a kansu is better" ya faɗa kan shi tsaye, domin Al'ameen ɗin mutum ne da yake kai tsaye, watau babu munafunci ko ɓoye-ɓoye a al'amurran shi.

Sannan ya cigaba da faɗin "maganar kuku kuma zan magana cikin ma'aikatan sai a turo su ko zuwa da safe ne" ya furta cikin salon miskilanci shi, tare da miƙewa ya bar ɗakin ranshi a cunkushe, bai san sai yaushe ne mom ɗin tashi zata bar halin ta ba, bai koma gidan ba ma ga baki ɗaya sai da ya tabbatar ya haɗa komai da aka bashi list, sannan ya kai ma Aunty Feena, domin yin packaging ɗinsu ko wajen mom ɗin tashi bai koma ba ya wuce part ɗinshi kai tsaye.

Yana kai kafaɗar shi bisa gadon nashi, tinanin su yayi mashi sallama, kenan umman tata ta bata dama domin tayi karatun? To ko Dad ɗin yayi mata magana ne? Allah sarki umma baiwar Allah, har yanda take ma ba cikin hayyacin ta ba, maganar ta Suhan ɗin tabi iyayen shi, abun da shi kuma Mahaifiyar tashi ta gaza fahimta, me suka tsare mata? Menene ɓata fi su dashi ba? Koda yake ya lura akwai ƴan zuga cikin Al'amarin, dole ya taka masu burki, dole ya gargaɗe su indai suna son zama cikin gidan, ba zai lamunci munafunci da haɗa husuma ba, hakanan su sanya ma bayin Allah karan zuƙa ba tare da sunyi masu wani abu ba daidai ba.

Yayi Alƙawarin taimaka ma Suhan ɗin domin jin ta yake kaman Afnan ɗinshi, da ƙaunar da Afnan ɗin ke mata da sanyi halin ta da kuma tarbiyyar da ta samu daga wajen umman tata, sai kuma halin da suke ciki da musguna masu da Mahaifiyar tashi ke yi, su suka ƙara mashi ƙaimi wajen ganin son ya taimaka masu bil haƙƙi da gaskiya, baya jin wani abu dangane da Suhan ɗin illa wani narkon tausayinta da ke malala cikin zuciyar shi, yarinya da ita, ba tafi shekara ishirin ba Amman tana fuskantar wannan waƙi'ar, wannan halin da suke ciki kan ƙara jefa zuciyoyin su a damuwa da shi kuma baya jin zai iya lamunta.

A haka ya samu bacci ɓarawo ya sace shi, zuciyar shi fal da tinanin halin da umman ta Suhan ɗin take ciki.



~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~12~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Washe gari kuwa tin da safe kowa ya shirya a gidan, wannan umarnin Alhaji Mustapha ne domin yana so su isa da wuri domin ticket ɗin safe aka samu, aika Afnan yayi tayi kiran Ya Ameen ɗin da shi kaɗai ake jira bai fito ba, sai gashi kuma cikin takun shi na ƙasaita da sanyin shi da kan ƙara mashi kwarjini a fuskar jama'a

Sanye yake cikin wani lallausan yadi kalar sky blue, an mashi ɗinki Abuja style, da gani dai yana son ɗinkin, rigar iya rabin cinya ta tsaya bata kai guiwa ba, hakan ya ƙara fiddo da asalin kyawon halittar da Allah yayi mashi, kan shi babu hula sai dai gyaran fuskan da kan ƙara ƙawata fuskar tashi. Takalmin shi da hankachip ɗin da ke hannun sau ciki, shi duk kalar kayan ne sai zuba ƙamshi yake yi. Cikin ɗan sassarfa ya isa ga Lahajin dake tsaye da alama jiran shi yake yi ya fito.

Gaida dad ɗin nashi ya shiga yi cikin girmamawa, yayin da Alhajin ya miƙa mashi hannu don suyi musabaha, na daga cikin halin Alhajin ne sauƙin hali da sauƙin kai, hakan kan ƙara mashi shaƙuwa da ƴaƴan nashi fiye ma da mom ɗin tasu.

Matsawa yayi ga Hajiya Kubran da fitowar ta kenan cikin shigar wani ɗanyen boyel mai taushi da walƙiya, ɗan rungumo ta yayi cikin murmushi mai ƙara ƙayata kyakkyawar fuskar tashi, amsa gaisuwar tashi ta shiga yi cikin jin daɗi da ƙauna ga ɗanɗan nata, duk da bata manta ƙin yarda da maganar tata da yayi da a daren jiya, Amman ta bar ma zuciyar ta, ta kuma sha Alwashin ganin zargin ta da hasashen nata bai zama gaskiya ba.

Sauran ƙannen nashi suka shiga gaida shi yayin da ya duka yana ma Nasreem wasa da miƙa ma Ayan hannu sukayi musabaha yana mai gaida yayar tashi cikin sakin fuskan da sai yana cikin family ɗinshi ne kawai zaka ganta.

Shafo kanshi tayi tana faɗin "Brother fatan ka tashi lafiya" ta faɗa cikin murmushi da kan ƙara nuna tsantsar ƙaunar ta ga ƙanen nata.

Alhaji Mustapha ne ya kauda masu gaisuwar da suke yi cikin cewa "Al ameen ina ganin ya kamata mu zo mu wuce ko kasan da ƙarfe 08:00am ne lokacin tashin flight ɗin. ɗan sosa kan shi ya shiga yi da ɗan makullin motar shi da ke hannun shi sannan ya shiga faɗin" Dad ina ganin ni ba zan biku ba sai dai ko zuwa gobe ko jibi ne zan iske ku cen ɗin, saboda aikin construction ɗin nan naga yana neman tsayawa, Eng ɗin ne naga yana san sanya shiririta dan yaga na cika mashi cikon kuɗin shi, and Bilal ma yace man yau zai iso ina jin ma sun taso yanzu, Ga kaya da kamfani zai fitar yau ina so inje ayi komai gabana, kasan yanzu rashin gaskiya ta yawaita" ɗan murmusawa Alhajin nashi yayi, sarai ya fahimci Ya Ameen ɗin baya son bin nasu ne, May be dan yana gudun maganar da Hajiyar tasu ta taso ita ne jiya, tana iya zuwa ta zuga Granny Zuwaira akan zancen; ɗan ƙara murmusawa yayi yana faɗin " is ok Al ameen Amman wanne kamfani ne zai fidda kaya yau?" (Domin Al'ameen ɗin shine manager ɗin duka kamfanonin Alhajin duk da shima yana da nashi) "Eh sabon na costimetics ɗin nan ne" Ya shiga faɗi da ɗan guntun murmushi akan fuskar shi yana mai son Alhajin nasu ya yarda da uziri nashi, "Tau ba matsala for now, Amman dai ina fatan zaka je cen ɗin cikin lokaci, Kaga ka kwana biyu ba kaje ba, duk da kuna waya, ya kamata kaje kaima Kaga lafiyar kakannin naka"

"to Dad" ya bashi amsa yana mai buɗe mashi gidan baya ya shiga ya zagaya ya buɗe ma Mom ɗin tasu, da bata ƙara tankawa ba don duk ya tushe mata plan ɗin nata, amman ba komai, ai bata ma jin sai tayi kamun ƙafa da wani akan al'amari yaron nata, duk isar ta da dukiya ta, ita ta haife shi in ya san wata ai bai san wata ba;

Mota biyu sukayi ɗaya Alhaji Mustapha da Hajiya kubra sai driver kawai, sai kuma ɗayar da ta ɗauke Aunty feena da yaran nata sai Saudat, Nihal da kuma Abie da ya hakimce a gaba.

Kai tsaye motar shi ya nufa, bayan yaga ficewa mitocin daga cikin harabar gidan nasu, restaurant ya fara tsayawa ya siya abun break fast sannan ya wuce Asibiti da ya kwana tinanin su duk da son kauda tinanin nasu da yake yi daga cikin ran shi, sai dai baya iyawa, sau da dama shi karan kanshi kan shiga tinanin kan shi da kanshi, tabbas ya san yana tausayin na ƙasa dashi, da marasa galihu, da ƴan aikin nasu, tau sai dai yana mamakin kan nashi, su salon yanda yake tausaya masu ma daban ne, amman ya kan alaƙanta hakan ne da rashin lafiya da take damun Maman Suhan ɗin.

Sallama yayi daga bakin ƙofa, tsam na tashi daga kan kujerar da nake duƙunƙune tin bayan da na gama sallar asubahin na kuma komawa na kwanta domin in ɗan rutsa, don cikin dare umman tawa ta farka, cikin ƙarfin hali irin nata har fira muka ɗan taɓa tana kara jaddada man maganar karatun nawa, da kuma roƙo na akan in bama dukkan Abunda zan gani a rayuwa ta ta gaba baya.

Daga ciki na buɗe mashi, ina mai janyewa na bashi hanya domin ya wuce. Kai tsaye ya shiga har bakin gadon umman tawa, yana mai ajiye manyan ledojin take away da yayo mana; ɗan rankwafawa yayi daidai saitin gadon umman tawa, yana mai kallon bugawar lumfashin ta.

"ta samu bacci ne?" ya jefo man tambaya yana mai janyo kujerar gefen gadon ya zauna idon shi cikin nawa, "Eh ta samu bacci, Amman ta farka cikin dare jikin da sauƙi, don har ma fira mun yi" na faɗa ina mai ƙoƙarin janye nawa idanu, tinani na ke yi, shi wanne irin mutum ne? Mutum mai daraja irin ta Ya Ameen da ba ko domin arziƙi shi ba da na iyayen shi, shi mutum ne daban ko cikin matasan garin na Abuja akeji dashi, shine yake bamu kulawa haka? Gaskiya ya cencenci a yaɓa mashi, ya cencenci a girmama shi, da dukkan iyawa.

"Hop dai bata wahalar da kanta ba wajen magana? Kin dai san dokar likita, ki dinga kula" ya faɗa yana mai kauda idanu shi daga gare ni da har yanzu nake rakuɓe daga bakin ƙofa, kwarjini shi baya bari in sake a duk lokacin da nake gaban shi.

"To zan kula insha Allah" na faɗa a hankali iya fatar baki, miƙewa yayi cikin halin ko in kula da tsayuwar da nake tayi, sannan ya shiga faɗin "Dictor ya shigo?" Lokacin da ya shiga ta kowa a hankali zuwa ga bakin ƙofar domin ficewa, amsar da na shiga bashi ce ta sanya shi ja ya tsaya ga barin ficewa, hakan ce ta sanya muke tsaye gaf da gaf, duƙar da kaina na shiga yi, bazan iya jurar haɗa idanu nashi ba, idan ma zan kula da jikina wata ƴar kyarma nake yi a hankali, me ke damuna ne ni Suhana? "Bai shigo ba yaya, Amman Nurse ta shigo sannan tace idan ta farka a bata abinci mai sauƙin nauyi, sannan mu kira ta, in kuma likita shigo shikenan" "Is OK Let Me Check On Him" Ya faɗa cikin salon turanci shi da yake kama da na turawan amurka da nake kallo a Tb ɗin babban falon gidan, ficewa yayi cikin salon tafiyar shi ta jarumin namiji, idan yaso komai cikin zafi zafi yake yin shi, idan kuma yaso kai kace wahainiya ce ke tafiya masalan ma idan yana jin ƴan miskilancin.

Office ɗin likatan ya shiga yayi daidai da isowar shi kenan Dr Ashafa ne yayi azamar miƙa mashi hannu yana faɗin "Yallaɓai ba dai har ka shigo ba? Gaskiya waɗannan patient ana ji dasu, Fatan dai jikin na maman tamu da sauƙi? Ya faɗa cikin murmushi da san ɓoye wani abu acikin ran shi;" Zamu iya zuwa ka duba Dr saboda ina so idan jikin nata ya samu sauƙi kayi discharge nasu, zanyi tafiya ne kuma bana son barin su anan babu mai kula dasu, gara su koma gida" ya maida ma da likita amsa cikin ɗan ɗaure fuska, bai san me Dr ɗin ke nufi ba, Amman ya kula tin jiya da yanda yake kallon Yarinya da take ta fama da jinya mahaifiya tata, ko menene ma nashi na damuwa? "OK to shikenan muje rana ya daɗe" likita ya faɗa yana mai ɗan sanya shakku a ranshi, Amman dai koma minene ai zai fahimta, gaba Al'ameen ɗin yayi Dr Ashafa ɗin yana biyo shi a baya tare da kayan aikin su na likitoci

Sake shigowa naga sunyi shi da likitan, watau sai da ya kira likitan kenan? Haka na cigaba da rayawa a rai ina mai janye idanu a ga barin kallon su, bakin gadon suka ja suka tsaya, hakan yayi daidai da farfaɗowar umman tawa.

"Ƴan mata zo ki taimaka ma umman ki ta tashi zaune kinji, zamu auna ta ne" likitan ya faɗa yana mai waiwayowa ya kalle ni da nake zaune ina aikin binsu da idanu da nayi nayi ga barin kallon su Amman na kasa, Ya Ameen ɗin yayi kyau, wani abu ke taso man cen ƙasa rai duk lokacin da ya bayyana inda nake, tasowa nayi a hankali na kama umman tawa ta zauna sosai, shi kau gogan ko kallo na ma bai yi ba, kaman ma bai san ina ta wurin ba, ya koma mani Yaya Al'ameen ɗin da na sani tin cen baya, da baya ɗaukar wargi, fuskar shi Sam babu walwala saɓanin yanda ya fita ba daɗewa.

Aune aunen su na likitoci ya shiga yi, sannan ya ɗago yana mai faɗa ma Ya Ameen ɗin komai normal, za ta iya cin komai, kuma ta kula da shan maganin ta akan lokaci, zamu iya tafiya gida, Amman nan da sati ɗaya mu dawo a sake gwada ta a gani, dokoki sosai aka shinfiɗa ma umman tawa, sannan aka hana ta cin wasu abubuwa da dama; wayyo likita, bai san ma abincin sai wanda aka ga dama aka bamu ba, in kace ba zaka ci ba sai yunwa ta kashe ka babu mai sani.

A haka na kama umman tawa muka fito, bayan motar na saka ta, ta ɗan kwanta na koma na kwaso sauran kayan da suke mallakin mu, har da take away ɗin da yayo mana da ko kallon shi banyi ba, balle in buɗa inga Abunda ke ciki.

Har zan shiga bayan ya tsattsare ni da idanun nan nashi masu rikita dani, sannan ya mani alama da in shiga gaba, haka kuwa aka yi shiga nayi na takure, masalan ma ga umma ta acikin motar kuma idanun ta biyu ba bacci take yi ba.

Kai tsaye naga mun nufi hanyar kasuwa, ban da hurumin tanka wa balle in tambaya me zamu yo a kasuwa, ƙila uzirin shi ne zai kai shi; parking yayi bakin tanƙamemen suoer market ɗin da yake bakin kasuwar, fita yayi ya shiga ba dadewa sai gashi ya fito yaron shagon na biye dashi a baya, hannun shi niƙi niƙi da kaya, but ya buɗe mashi tare da Sanyawa ya rufe, ya zagayo ya tada motar muka shiga cikin kasuwar, nan ma soyayya yayi sosai, cikin ni da umma ta babu mai tankawa, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai.

Gida muka nufa kai tsaye, yayin da yake parking ya yafito mai gadi da hannu, cikin hanzari ya iso inda muke ƙoƙarin fitowa daga cikin motar; umarni yayi mashi da ya kira mama talatin a sashe namu na masu aiki, aiko ya ruga cikin hanzari, sai gashi da mama talatun ta taho cikin sauri, umarni yayi mata da ta kama man umman tawa mu kai ta ɗaki mu kwantar, yayin da ya kirayi mai gadin da isa da yake tsaye yana gyaran flowers da suka taimaka wajen ƙayata gidan, kayan yace su kwashe su shigar mana dashi cikin ɗakin mu, yayin da ya ja motar shi yana mai barin gidan.


Kai tsaye ɗakin namu muka nufa da umman tawa da take ɗan iya taka wa a hankali a hankali, kwantar da ita muka yi, yayin da su isa suka shisshigo mana da kayan namu suka fice suna ma umman tawa sannu da Allah ya kyauta, ina kallon mama talatun tana jinjina kai tana mai ƙare ma niƙi niƙinbkayan da ta gani tare da mu, ta dai san wannan aikin Alhaji ƙarami ne, wato dama ya ƙi bin su Hajiya Babba ne domin ya tsaya bauta mana kenan ko? Wai menene haɗin shi da mu ne? Su dai basu ga wata alama da ke alamta masu akwai wani abu tsakanin Suhana ba da Alhaji ƙarami ɗin balle ace dan ita yake yi? Koma minene zata yi ƙoƙarin sanar da hajiya ɗin, me hakan ke nufi ne? Ya kamata hajiyar tayi wani yunƙuri akai wallahi, ita ta ma ga sanyar Hajiyar wannan karon akan yanda ta santa da in ta ƙi abu duk yanda zata yi akan taga bai faru ba ta sani, tana cike da tsantsar mulki da kuɗi, naira shegiya ce, mai maida tsoho yaro ta maida yaro babba.


(Humm🤔🤔 Ya Allah kayi mana tsari da Hassada, ƙyashi, ganin gari da munafunci ameen ya Rab🤲🏻)

Bayan duk sun fita ne, na gyara komai a ɗakin na adama komai inda ya kamata, kayan ciye ciye ne da basu da illa ga masu ciwon zuciya irin wanda likita ya bada umarnin aci, su ne ya kwaso mana su sosai da sauran kayan buƙatu har da kayan marmari ma da zasu yi ma mai rashin lafiya daɗin ci, gyaran ɗakin nayi nayo wanka na shirya kaina cikin baƙar doguwar riga mara nauyi na tattara gashi na na ƙulle cikin ribom sannan na ɗaura ɗan kwalin rigar a bisa kai na, nayi kyau daidai misali, sannan na ɗauko ledar take away ɗin da yayo mana tin asibiti na buɗe da niyyar zuba mana muci ni da umma ta, lafiyayyen chips ne da plantain, sai soyayyen ƙwai da miyar kayan ciki, sai ƙamshi take har yanzu da sauran zafin shi, saboda mazubin na glass ne, da gani dai abincin zai yi tsada, sai dai baya cuwuwa ga umma ta saboda farin mai da aka yi using wurin suyar, kaina kaɗai na zuba mawa na fidda sauran ga ƴan uwa na ma'aikata da har yanzu sun gagara shigowa yi mana koda sannu saboda tsabar hassada, Abunda na san zata iya ci wanda likita bai hana ta ci ba na zuba mata, saida na tabbatas taci na ɓalli maganin ta na bata tasha sannan na gyara mata kwanciyar ta, na koma gefen katifa na zauna ina ya ƙunar abincin ahankali

Fira mukeyi jefi jefi da umman tawa da take bina da kallon tsantsar ƙauna ga ɗiyar tata, addu'a dai kam Al'ameen ya sha ta daga bakin umman tawa, godiya take jerawa wanda hakan ne ta sanya ni ɗan murmusawa a hankali dai ina ci gaba da cin abinci na; Sallama yayi daga bakin ƙofar ɗakin yayin da umma ta ta bashi izinin da ya shiga daga ciki, lokaci ɗaya tana mai umartata da shinfiɗa mashi darduma.

Kasa tashi nayi, domin jikina babu hijabi babu gyale, gashi rigar mai bin jiki ce ta fidda duk surar jikin dake Sanye da ita, kuma a zahiri bai kamata ya ganni haka ba, saboda shi ɗin ba muharrami na bane, hakan ce ta sanya na shiga bin ko ina na jikina da kallo kaman mai son gano wani abu.

"Hauwa'u dake fa nake magana fa, nace ki shinfiɗa mashi darduma ya zauna kin bar shi tsaye" umman tawa ta faɗa tana mai yunƙuri tashi, a haka ta samu ta zauna daidai domin Nidai na gagara koda motsi balle in taimaka mata har ma nayi mashi shimfiɗar

Hankalin shi ya maida kanta da take ajiye plate ɗin abincin kaman mai tausayin ƙasar, ta shiga miƙewa a hankali, lura da yayi da Abunda take ɓoyo ko ji ma kunya ne ya sanya shi kauda kanshi gefe, ya maida hankalin shi kan umman tawa yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya laɓɓa, ko me take ɓoyo? Wannan mitsitsiyar yarinyar ma, da yake kyautata zaton garin jiki ne ya kwashe ta, ita har tana ganin ma ta cika ta kai mace, ƙara murmusawa yayi daidai lokacin da take shinfiɗa dardumar ɗan nesa kaɗan da katifa tasu.

"Nagode" ya faɗa iya maƙoshi maganar tana mashi wahala, yana mai zama ya tanƙwashe ƙafafun shi irin zaman salla, lokaci guda yana mai gaida umman tawa, cikin sakin fuska ta amsa mashi, sannan ya ƙara mata ya jiki da Allah ya sauwaƙe.

Godiya ta shiga jera mashi da kuma fatan nasara da cigaba a rayuwa, harma da iyayen shi, hakan ce ta sanya shi jin daɗi, yana mai ƙara ƙaunar matar da son taimaka mata da duk ahalinta.

Ikon Allah, abikan aikin mu da tin ɗazu suka kasa leƙowa su ga jikin umman tawa su gaida ta, sai gashi ɗaya bayan ɗaya yanzu da suka ga shigar Ya Ameen ɗin ɗakinmu suna shigowa gaida ta da ganin ƙwam, kowa ya fita kuma sai ya ƙara da abin da ya gani gaba.

Sake natsuwa yayi yana mai ɗan yin gyaran murya a hankali, sai da ya maido kallon shi inda nake rakuɓe bisa katifa gefen umman tawa, sannan ya saki wani ƙayataccen murmushi ganin ta sanya hijabi da shi bai ma kula da lokacin da ta ɗauko shi ba, haƙuri ya shiga ba umman tawa, da mata Alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba, ya faɗa mata afnan ce ta sanar dashi komai; ɗan faɗa umman tawa ta shiga yi tana faɗin hajiyar ta isa ne ya sanya tayi masu faɗa, ai ba wani abu bane, gyara ne take so ayi, kuma mun ɗauka insha Allah.

Haƙuri ya ƙara bata sannan ya shigo mata da maganar makarantar tawa, ta bacin yardar ta ta ƙara bashi, sai dai tana mai shawartar shi da yayi komai a hankali kada ran hajiyar ya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment