Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne malale a falon da ya ƙawatu da wani makeken chinese carpet da ya lashe fin rabin falon bayan su babu komai sai center table na zallan glass fari tar dashi mai haɗe da tumtum irin na gidan sarauta guda biyu tsakiyar falon, akwai stools suma kwara biyu tsakanin kujerun, sai saitin kayan kallo ƴan kamfani Samsung haɗe da Italian Tv stand, up White ne fentin falon yayin da ya dace da cottons masu matuƙar kauri suma kalar golden, sai na'urar sanyaya ɗaki da water dispenser dake maƙale a saƙo guda na falon. Kai kanka in ka kalla sai ka sake kallo, iya tafiya da imani falon ya tafi da nawa.


Corridor ne gefe guda daga bangon hagu da ke falon, idan ka bishi shi zai sadaka da ɗaki ɗaya tal acikin shashen da yake mamallakin shashen, sai ƙofar ɗan ƙaramin kitchen da yake ta cen ƙuryar Corridor ɗin da yake ɗauke da madaidaicin dining area a ciki, kitchen din ya tsaru kaman na wata macen komai na aikin gida akwai shi ciki, sabo da Ya Ameen ya iya girki, in ƴan miskilancin nashi suka taso shi ke girkawa da kanshi yaci abun shi ko kuma in yayi baƙin shi yakan dafa masu abinci simple kuma ya wanke dishes ɗin da kanshi.

Yanda falon ya tsaru sai naga ma kaman bedroom ɗin yafi ƙayatuwa, shima komai upwhite ne da kwalliyar golden, saɓanin toilet ɗin da yake kalar sararin samaniya da fitilu farare, sai ya zamana abun burgewa da ban sha'awa.

Zagewa nayi na gyara ko ina na ƙalƙale, shi tas na kunna boner ta ruwan ƙamshi, take part ɗin ya ɗauki ƙamshi mai sanyaya rai, sannan na kunna na'urar sanya ɗaki domin ƙamshin ya kama ko'ina,bayan na gama na kashe komai na janyo part din na kulle gami da mayar ma da Mama Talatu makullin.


*******************************

Ƙarfe biyar sakaliyya suka iso gidan, yayin da dukka mu ma'aikata muka fita taro su da yi masu barka da zuwa, harda umma ta baiwar Allah da take sanye cikin zurmemen hijab ɗinta, wanda bata ma lafiya kwance take zazzaɓi ne rau a jikin ta, Amman hakan bai hana ta fitowa ba, tinda haka aka saba kafin su shiga part ɗin nasu sai an gaggaisa da kowa tare da jin lafiyar kowa, wannan doka ce daga Alhaji mustaphan wanda a haka dole suke tsayawa suna zuzzunɓura baki suna aika mana da harara su sun dawo a gajiye amman baza'a bar su su shiga ciki su huta ba. Hakan baya damun Alhajin domin ya saba da halinsu tsaf halin mahaifiyarsu ne hakan ta saba masu dashi, halinta ne tin kafin ya aure ta kyamar talaka, masu aiki, sai dai yana tausaya masu har faɗa yana masu a lokutta da dama yakan ce "ku shiga taitayinku kuma ku natsu kusan inda yake maku ciwo, faɗi baya dauwama, haka ma wuya, kuma aure zakuyi ba kuma kusan gidan wanda zakuje ba" Hajiyar kan amshe da cewa "a'a alhaji ka rinƙa faɗar alkhairi a bakinka fa, yaran nan fa kai ka haife su"


Wannan karon da Afan mutuniyata aka dawo, sai aunty Feena da yaran ta guda biyu ɗan shekara shidda mai suna Ayan sai ƴar karama da ba zata fi shekara biyu ba Nasreem.

Aiko tana hangoni tayo kaina da ɗan gudun ta, maimakon in ce mata oyoyo sai itace ta rigani cewa "oyoyo aunty suhan sai kuma gaki" ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya gami da daka tsalle ta rungume ni sai kace wata 'yar yarinya, Afnan ba zata kai tsara ta ba, ko ba komai zan iya bata shekara uku haka, riƙe take da hannun Ayan, hakan ce tasa nima murmusawa gami da tsugunna wa bayan na bamɓare ta a jikina; tsugunna wa nayi na cicciɓi Ayan din ina cewa a hankali "aini fushi nake yi da ke, ko waya Afnan kinma manta dani kwata-kwata, sweet Ayan ne kaɗai nawa ni, shi da nasreem.

Ƙyalƙyalewa tayi da dariya," Allah Aunty suhan ba haka bane, karatu ne yayi zafi Amman Allah Allah nake lokacin zuwan mu hutu yayi inzo inga ya kika koma, na san kina nan kin ƙara kyau abunki". Murmushi nayi ina cewa nima nayi missing ɗinki Autan Hajiya, ya kamata kuje ki huta hakanan".


Ashe bamu sani ba duk hankalin su ya dawo kaina Alhaji da Aunty Feena sai murmusawa suke yi, ita aunty Feena ɗaukar da nayi ma Ayan ce ta burge ta kunsan mai ɗa wawa, yayin da su kuma su Aunty Nihal haushi ya cika masu rai, Afnan ɗin na basu haushi, tana zubda masu daraja, wai ace House maid ce take yi ma haka?, dubeta ita kuma dalla har da wani daukar Ayan salon ne ta shafa mashi datti. Tsoki suka yi cikin rai, su kuma sauran ma'aikatan haushi ne ya cika masu rai na fifita ni da Afnan ɗin keyi akan su,basu yi la'akari da cewar su sun girma ba sun manyanta.


Gogan naku na gefe jingine da motar shi, ya harɗe ƙafafu yana ta kallon su, bai ko murmusa ba Amman dai sun burge shi cikin ranshi, shi yasa yake masifar son Afnan ɗin ita ce ƴar gaban goshinshi, saboda ko kusa ba halinta daya da sauran yayyen nata ba.

Mu kuwa hankalin mu ma bai kai kanshi ba da yake gefe yana ta zuba mulki da miskilancin har aka gama gaggaisawa muka juya zuwa shashen mu su kuma suka nufi cikin babban apartment ɗin nasu, har sun kai babbar ƙofar da zata sada su da cikin gidan, Afnan ɗin ta juyo gami da kwalla man kira, "Aunty suhan.!, in na gama hutawa ina nan shigowa ki ajiye man abun daɗin nan" ta faɗa cikin ɗaga murya gami da yin ɗan tsalle ta kashe man ido daya, bata jira cewa ta ba ta shige cikin gidan riƙe da hannun Ayan yaro ɗan gayu ɗan hutu gashi mulmul dashi, hakan ce ta sanya kallo ɗaya yaron ya shigar man a rai tin Wancen zuwan da sukayi, tin kafin ma ayi mashi ƙanwa ne; murmushi nima nayi gami da ƙada kaina "hooo Afnan ba dai rigima ba" na faɗa a fili ina shige wa shashen namu, ko ba komai zan ɗan samu sassauci zuwan Afnan ɗin domin tana ɗebe man kewa, tin umma na hanani har ta haƙura ta barni domin ta kula cewa halin Afnan ɗin ya banbanta da sauran ƴan uwan nata.

**********

"huh...." ajiyar zuciya yayi tare da guntsar iska ya fesar, a hankali ya fara taka wa gami da nufar nashi apartment ɗin domin ya gaji over, makullin dake hannun shi yayi using ya buɗe sashe nashi; Turus ya ja ya tsaya, wani sas-sanyan ƙamshi ne ya bugi dogon hancin shi, lokaci guda ya maida kallon shi bisa kowanne lungu da saƙo na falon, kaman dai an cenza komai?, Amman inaaaa..... Su ɗin dai ne, hmmmm? 🤔 Wanene yayi wannan aikin? Ta bayar kanshi yake Amman ya kasa lalubo amsa.

Jiki a sanyaye ya nufi Corridor ɗin da zai sada shi da bedroom ɗin nashi, still dai nan ma haka, aah! Mamaki bai gama cika shi ba sai da ya murɗa handle ɗin ɗakin ya shiga.; gadon shi an lailaye shi da zanin gado mai kyau da yayi order daga dubai bai iso ba sai da baya nan, hakan ce ta sanya Talatu buɗe ɗakin ta ajiye a cikin wardroop, ni kuma da nazo gyara na gani na yaye na sama duk da baiyi dauɗa ba na shimfiɗa na saka Wancen cikin laundry basket. A hankali ya taka kaman mai tsoron ɗakin, gami da isa bakin gadon ya zauna a hankali.

Taushi da sulbin zanin gadon gami da ƙamshin da suke tashi daga saman gadon ne suka sanya shi sulale wa ya kwanta bisa gadon sosai yana mai kallon POP din dake saman ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke a jere har sau uku gani da furta "Suhan" a hankali domin kuwa ya san wannan aikin ba na kowa bane sai ita.......





~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven, No pain, so Magical Our creative golden pen, Be hold our words, A production of our pen, savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Gaisuwa ga ƴan golden pen, expecially ~Yaya Umar Dalhat Funtua~ muna godiya da ƙoƙarin editing, na baka kyautar wannan Page ɗin, kayi yadda kake so dashi. Allah ya ƙara haɗa kawunamu ameen*



*Page ~7~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Haka kau aka yi, ina gama sallar magariba sai ga afnan saɓe da Nasreem a kafaɗa, riƙe da hannun Ayan tana jan shi a hankali, sallama tayi fuskar ta cike da annuri da fara'a ta shigo, yayin da ta ajiye Nasreem bisa katifar tamu, ta janyo Ayan shima ta zaunar dashi, wutsil yaro ya haye kan cinya ta da nake zaune bisa dadduma.

"ku ji mu da yaro dan Allah, sai san jiki kaman mage" Afnan ɗin ta faɗa tana mai kama baki alamar mamaki, murmushi baiyane a saman kyakkyawar fuskar ta, lokaci ɗaya ta maida duban ta wajen umma ta da take zaune itama bisa tata daddumar domin bata tashi idan ta gama sallar magriba har sai ta kammala isha'i;

"umma ina yini ya kwana biyu ya jiki-jiki, dan ko ba'a faɗa ba naga kaman baki lafiya" ta faɗa cike da girmamawa, Afnan yarinya ce mai cike da natsuwa, biyayya da girmama na gaba da ita ko da kuwa ta fishi da komai, shi yasa rayuwar ta da ta Ya Ameen ta kusan zuwa daya bambancin kawai shi akwai ɗan miskilanci a al'amuran shi in ya so, saɓanin ita mai walwala ce da zaulaya in taso, ta ɓangare daya kuma ga sangarta idan taso gami da shagwaba sabo da ita ce auta, tana da wani hali guda ɗaya da yake burge Alhaji mustapha, hakan ce tasa idan tazo mashi da buƙata ba dai ya Musa mata ba, yakanyi duba na tsanaki ga buƙatar tata, halin kuwa shine *manyance* watau tana da tinani irin na manya, lokutta da dama Alhajin kan zauna yayi magana da ita ta tsanaki idan ya je cen ko kuma idan ita tazo nan.


"lafiya ƙalau Afnan, kun iso lafiya ko,? Ya gajiyar tafiya? Kunsha hanya, maimakon ki zauna ki huta Alabasshi idan mai duka ya kai mu kin shigo ku sake gaisa wa, shine kika kwaso yara kuka taho, kika rabo su da umminsu kika zo nan dasu kina kwasar masu sanyin nan" umman ta wa ta ƙarashe tana mai duban afnan ɗin tare da miƙa ma Nasreem ɗin hannu alamar ta taho, ai kuwa ba musu yarinyar ta muƙe cikin salon tafiyar ta irin ta ƴaƴan turawa ta isa wurin umman tawa tare da ɓangala mata dariya, cikin gwarancinta take ta mata jagwalgwalon surutun su irin na yara; Afnan ce ta amsa mata da cewa "Ai umma ba zama in har banzo mun gana da aunty suhan ba, in wanke laifi na sannan in sake kafa wani gwamnatin domin naga Ayan yana neman kwace man fada, don ma na san ba zaki barta ba da cen ɗakina muka tafi muka sanya labule Alabasshi sai ta kwana cen da safe ta dawo" murmushi kawai umman tawa tayi alamar ba zata bari ba, sannan ta maida hankalinta kan Nasreem ɗin lokaci daya tana cewa "to kiyi maza ki gama kinsan ba daɗewa za'a neme ki sabo da yaran da kika taho dasu" "toh umma insha Allah" Afnan ɗin ta faɗa tana maido hankalinta kaina da nake ta wasa da hannun ayan, son yaron ya shiga raina sosai na rasa dalili, kuma ni ba mugun daɗi ma nake da mahaifiyarshi ba duk da dai cewa tafi su Saudat kirki ko don ta girmesu ne, ta fisu hankali shi yasa? Oho

"Aunty Suhan kinga yanda kikayi shar abunki? Hutu ya ratsa ki wallahi kin ƙara kyau fatar ki sai sheƙi take yi minene sirri?" ta faɗa muryarta cike da zaulaya, ni sai ma ta bani kunya wallahi, sunne kaina nayi cike da kunyar umma ta da take zaune wajen, kuma tana jiyo duk abun da muke faɗa, ita kau Afnan na lura da ko ajikinta ma........" ba wani nan afnan kece zan cema haka Allah" na faɗa cikin murmushi, har cikin raina ina ƙaunar afnan ɗin, sabo da ko ba komai zuciya tana son mai kyautata mata, Afnan ɗin na son mu har cikin ranta, bata gudun mu ko kyamatar mu kaman yanda sauran suke yi, hakan ce tasa daga ni har umma ta muka sakankance mata muka saki jikin mu da ita.

"Humm,,, haka dai kika ce Aunty na, ya Maganar karatu kin ƙarashe kuwa?" ta jefo man tambaya cikin halin ta na manyance; Lokaci guda gaba na ya ruguje ya faɗi, saurin saisaita kaina nayi domin kada ta fahimci wani abu, sannan nace mata "har na gama fa Afnan" "wow, har kin kammala aunty suhan?, wane course kika karanta ne?, na fa dade rabo na da nigeria wlh" ta maido man tambaya cikin tsammanin samun amsa daga gare ni, hakan shi ya ƙara ruɗani har firgici na ya fito fili cikin inda inda na mayar mata da cewa

" Secon. dry school fa na.. ke nufi Afnan" zaro idanu tayi jin abunda na faɗa "meh😳" ta tambaya cikin son jin ba'asi "eh" na mayar mata ina mai gyaɗa mata kai kaman ƙadangaruwa, "look aunty suhan kibar wasa, ni na san umma ba zata hana ki ba, kuma nasan tinda Ya Ameen yana ƙasar ba zai sa maki ido kina zaune baki aikin komai ba kuma ke ba karatu kike yi ba" (kuji Afnan ɗin nan ma, wai bata aikin komai🙄) ta mayar mani cikin ɗan ɓacin rai, sabo da na kula hakan baiyi mata daɗi ba.

Tsam umma ta tayi tana mai son jin amsar da zan bata, yayin da ni kuma nayi ƙasa da kaina ina mai cije laɓɓa na kamar zan huda su, alama nake yi mata da tayi shiru, Amman kaman ma bata san ina yi ba, cigaba tayi da cewa "kinga kin girmeni, Amman kina nan kina kallo zanzo in gama makaranta ta, na fiki ƙananan shekaru amman na fiki sanin abunda zai amfane ni nan gaba, gaskiya in wani ya baki shawara tsaida karatun ki daga iya Secondry bai kyauta ba, sabo da dashi ne zaki tallafi rayuwar ki nan gaba har ma da ta umma" tana kai aya naji kaman in zunduma da gudu, kaman in ɗora hannu a kai🙆🏻 in ta zunduma ihu😵

"afnan ya kamata mu bar maganar karatun nan hakanan shi komai da kika gani muƙaddari ne, idan da rabon inyi nan gaba sai kiga Allah ya kawo wani sanadin" na faɗa ina mai son ta fahimci umma ce ta hanani, ta kuwa fahimta domin naga ta dan zaro idanu waje sai kuma ta gyaɗa kai gami da cewa "tau ai shikenan Allah ya kawo aunty Suhan, dama zuwa nayi in tambayi umma don Allah ko zata barki ki raka ni siyayya zuwa gobe insha Allah ba daɗewa zamuyi ba" ta maida maganar tata kan umma ta da take ta jijjigar Nasreem har ta samu tayi bacci, "Allah ya kai mu" umma ta bata amsa cikin yanayi da na kasa karanta, Sam ba zata iya nuna ma Afnan ɗin ɓacin ranta ba domin ko babu komai maso uwa tau lallai yaso ɗanta, Afnan ɗin na daga cikin mutanen da take ganin girman su duk da ƙarancin shekarun nata kuwa,.

Miƙewa Afnan ɗin tayi gami da gyara gyalen dake saman kafaɗar ta, tana mai cewa "To umman mu, aikau godiya nake yi bari muje sai da safe kinga ma kuwa ta maganar ki har sunyi barci, bari in kai Nasreem ɗin in dawo in ɗauki Ayan ɗin, tinda ban iya ɗaukarsu su duka" "a'a bari Mama na ta ɗaukar maki Ayan ɗin ai ba kin ta jigila ba tinda ga wadda zata iya taimaka maki, kuje ta kai maki shi, sai da safe ki gaida hajiyan da yayar taku" umma na ta mayar mata cikin ɗan murmushi, "to umma aikau na gode, aunty na taso muje aiki ya ganki na ɗaukar wannan gabjejen saurayin haka gashi yayi bacci ya ƙara nauyi, ko in goya Nasreem ɗin muyi kama kamar Ayan ɗin" ta faɗa cike da zaulaya da son sanya ni dariya da ta kula kaman walwala ta duk ta tafi, tinda aka yi maganar karatu, aikau ta ci nasara murmusawa nayi ina mai Miƙewa tare da faɗin "ance maki kowa ma raggo ne irin ki, da sai munyi ma yaro na kama kama?" na mayar mata cikin nima tawa zaulayar daidai lokacin da muke ficewa daga cikin ɗakin a tare.


Ko da muka isa muka kwantar dasu sai da tace zata rako ni, nice na hana ta, ganin dare yayi, nima ina komawa nayi sallah na kwanta tinani fal cikin raina na Afnan ɗin da ƙarfin hali, ko ma dai miye ina fatan ta bar maganar karatun nan haka nan, bana son Abunda zai jawo man matsala da umma ta muna zaman zaman mu lafiya ƙalau, tinda na kula har cikin ranta ba son maganar take ba.

~~~~~~~~~~

Bai san lokacin da bacci ya kwashe shi ba a haka, sabo da sanyi da tsaftar ɗakin gami da taushin zanen gadon, sai dai farka wa yayi yana mai jiyo kiraye kiraye sallar magrib na tashi a laud speaker ɗin masallacin da ke gefen gidan nasu, a kasalance ya tashi gami da cire kayan, ya faɗa toilet domin yin wanka da alwala, mamakin yarinyar yake yi sosai, a ina ta iya irin wannan tsaftar haka? Gashi komai a nutse, ta ajiye komai inda ya kamata, hatta da towels ɗin wanka ta cenza mashi wasu, ta dauraye waɗanda suka yi dauɗa ta shanya a ɓangaren shanya na toilet ɗin, ta kwashe tarkace robobin shower jel da hand wash liquid soap ɗin duk ta zuba su a shara taje ta zubar, toilet ɗin ƙar, kaman an cenza komai na ciki ya koma sabo, shi kanshi cikin jin daɗi yayi wankan, ya fito yana mai jin daɗin jikin shi da ƙamshi da jikin nashi yake yi, shi ya siyo product ɗin Amman ta zaɓi waɗanda suka dace ta ajiye mashi.

(yo Al'ameen wannan ai aikin Suhan ɗin ne a cikin gidan ko baka sani ba?)

Bai sha mamaki ba sai da ya buɗe wardroop ɗaukar kaya,, ya tarad da komai ta ware mashi wajen shi ta kimlace su, ta kwashe duk wasu tarkace masu datti ta zuba a laundry basket; cikin natsuwa ya shirya gami da taje sumar kanshi tayi luf abun ta, ya fesa turare, gami da zura Jalla biya, ya fito yana taka wa cikin salon tafiyar shi ta ƙaƙƙarfan namiji, domin zuwa sauke farali sallar magariba.

*******************************

Washe gari ma da nake nawa aikin, haka Afnan ɗin tazo tana taya ni, rabi surutu rabi tsaukana, yo eh tsaukana mana zance, tinda da ta fara shara ko goge goge sai ta duƙe ko ta faɗa kan sofa tace "wash wlh aunty suhan na gaji da yawa, gaskiya kina ƙoƙari" na kan yi dariya ince "Afnan kenan, miye na gajiya a nan?, aikina ne fa"

A haka muka gama tana mai ƙara tuna man da cewa ƙarfe biyar fa na yamma zamuje shopping ɗin nan don Allah inyi shiga ta kece raini, (Lol🤣 Afnan kenan)


Ƙarfe biyar tayi daidai da shiryawa ta, doguwar riga na sanya irin dubai abaya ɗin nan, da Alhaji mustapha ya taɓa yo man tsarabar ta, abayar na matuƙar karɓa ta, baƙa ce sosai har ƙasa sai dogon wando daga ciki, haɗe take da gyalenta, saboda haka sai Kaga dama sannan ka sanya hijab, kwalliyar golden ne jikin ta da adon wasu duwatsu farare daga sama har ƙasa, wannan shi ya ƙara ƙawata rigar, banyi wata kwalliya ba sosai domin ni ba ma'abociyar shafe shafen nan bace rambatsai.

Hoda kawai na murza, sai kwalli da na zizara ma idanu na, haɗi da shafa lipstick mai ƙamshin Apple shima fari ne da ɗan sirkin Light pink haka, parking ɗin gashina nayi, tini ni dama ba ma'abociyar kitso bace sabo da gashina irin na asalin Fulani ne, mai taushi da sulbi, ga yawa da tsawo, wanda saidai in wanke shi kawai in shafa mashi mai in haɗa shi in ƙulle hakan ya wadatar dashi, turare irin namu na mata mai taushin ƙamshi na fesa haɗi da shafa humra ƴar Sudan da aunty saudat ta bani kwanaki cikin kwalimar ta, sai ƙamshin ya haɗe ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi.

(ka ganni kaman ba yar aiki ba😅)


Afnan ce ta shigo cikin saurin ta tana cewa "Aunty Suhan maza ki fito, ga yaya cen yana jiran mu na lallaɓo shi, zai kai mu kinsan halin nashi baya son jira, ɗan oya oya ne." Turus ta ja ta tsaya lokaci guda mamaki fal bisa fuskar ta, lokaci guda ta shiga taɓa hannuwa, 👋🏻 sannan ta shiga faɗin "Aunty Suhan wannan kyau haka? Dubeki dan Allah kaman wadda zata je gasar kyau, kina da irin wannan kyaun haka kike boye wa?" jan hannuna ta shiga yi tana faɗin masha Allah wannan ai ni sai ma inji kunyar jerawa dake wlh abu kaman ƙyanƙyasar inji? " ta ƙarashe da zaulaya

Ja nayi na tsaya ina cewa "Afnan Allah in kwalliyar tayi yawa bari in rage, yo ni wa zan ma kwalliya har haka?" murmushi ta sake yi, da ya riga ya zama ɗabi'arta, "ke wasa fa nake maki, Ya Ameen ɗin ne zai tsaya wani jiranki? Har ma fa ya shiga mota mu kaɗai yake jira, kuma yace in na ɗaɗe zan ga wayam, saidai idi dreba ya kai mu" ta shiga faɗi tana mai sake jan hannu na, ni kuma na shiga binta kaman raƙumi da akala.

A tsakar gida muka haɗu da umman tawa, tana shigowa dan shirya zuwa girkin dare cikin gida, da addu'a da fatan dawowa lafiya ta bimu, sannan ta mana gargaɗi da mu kula da kanmu ƴaƴa mata muke, to muka amsa mata gami da jerawa da Afnan ɗin kai ka rantse ƙawaye ne, domin Afnan ɗin ta taddoni a jiki, saidai ɗan tsawo ne kawai zan nuna mata, ba kowa ne ma za'a gaya ma na girme ta ba ya yarda.


Bayan motar ta buɗe mani na shiga, wani sanyi ne mai ratsa zuciya ya mani sallama, ban san lokacin da na ja mun fashi ba, gami da runtse idanu na ba sannan na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya, mota ce mai suna mota, na tabbata ban taɓa shiga mota makaman ciyar wannan ba, duk kuwa da tarin motoci na alfarma da suke gidan.

Tada motar da yayi, shi yayi sanadiyyar dawowa ta cikin hayyaci na, daidaita kaina nayi cikin sanyin magana nace mashi "ina yini Yaya" duk da bana iya hangen shi sosai bayan shi kawai nake iya gani don ta saitinshi nake zaune sai ayan da ya kwanta bisa cinya ta, ina iya hango motsawar shi da motsawar bakin shi ta cikin mirror dake maƙale na driver, "lafiya" ya bani amsa a taƙaice, ban kuma cewa komai ba, sai wasa da na shiga yi da ayan, yana bani labarin school ɗin su a hankali, ina jiyo Afnan ta cika shi da surutu da take zaune gidan gaba wani abun ya amsa mata, wani kuma yayi murmushi kawai ya share ta.

A haka muka isa tanƙamemen super market ɗin da ya haɗa komai, komai na kayan more rayuwa ana saida shi a ciki; ɓalle murfin motar nayi naja hannun ayan muka fita, yayi daidai da fitowar Afnan ɗin tana cewa "Yaya kai ba zaka shiga ba?" girgiza mata kai kawai yayi yana miƙa mata ATM ɗin nashi gami da cewa "30mnt na baku kuma, kuyi maza ku fito ina jiran ku, ina da nawa uzirin rigimar ki ce kawai bana so Lil" (da yake ya kan

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment